Batuol mamman complete novel - Chapter 34
Batuol mamman complete novel Chapter 34: Batuol mamman complete novel Chapter 34. Alh Baba yace "babu wanda zan tilasta a cikinku na gama wannan yayin.…
3,367 words
Alh Baba yace "babu wanda zan tilasta a cikinku na gama wannan yayin. Tunda ba kya so Allah Ya kawo miki naki rabon. Kai kuma ku gama magana da waccan ina bukatar amsa da wuri" yana kaiwa nan yace duka ya sallamesu su tashi su tafi. Ghazalatu kuka kamar ana yankar naman jikinta amma tasan halin Mummynta da masifa. Idan ta kuskura ta komawa Awwab sai taji babu dadi. Hussaina duniya shar ta kira Nura tace ya fara yakin neman soyayyar Ghazalatu ita ta gama nata aikin.
Awwab bai jira kowa ba ya fita ya bar gidan. Jin kansa yake kamar an zare masa wata kaya da ta tokare shi. Lallai zuciya bata da kashi. Bai tantance zafin so ba sai akan Alheran. Kinsa da Ghazalatu tayi ko kadan baiyi masa ciwo ba don tunda Mummy taje gidansu sau biyu tana cin mutumcin mahaifiyarsa yasan ko ya aureta wani kaso mai girma na kimarta ya riga ya sauka daga idanunsa.
Sallar magariba ya tsaya yi kafin ya shiga gidan. Shigarsa tayi daidai da isowarsu Mami a motar Daddy. Zahra ce ta tuku su Fauziyya na gaba su Mami na baya. Idan ka ga Zahra fuskarta tamkar wadda aka baiwa kujerar Makka. Murmushi ne yaki tafiya kamar an zana mata shi har tsokanarta Daddy yayi yace shima sai ta nemi amincewarsa sannan zai kira Imam Abdulwahab mahaifin Raji.
Kunya taji ta ruga cikin gidan kai tsaye ta tafi dakin Mami. Ummi ta gani akan sallaya ta fada jikinta tana ta dariya.
"Zahra me muka samu irin wannan murna haka"
"Ummi Alh Baba ya amince"
"Da me?" Mairama ta tambayeta tana tayata murna tun kafin taji.
Sallamar Mami yasa ta kasa cewa komai ta tashi ta koma nasu dakin da tsalle. Sai da Mami ta idar da sallah ta fada mata yadda al'amura suka juya. Ummi bata ji dadin fasawar da Ghazalatu tayi ba kuma ga dukkan alamu Mami da 'yan uwanta basu shirya ba. Indai haka ne kuwa to babu makawa Radhiya ma bazata auri Awwab ba. Meye ribarsu ayi auren da ya taba zumuncin iyaye.
Fauziyya da Zahra ma sallah suka shiga yi suka sami Radhiya ta dukunkune kanta ta cure wuri guda tana baccin wahala. Tayi kuka ne har ya saka mata ciwon kai shine bacci ya dauketa. Zayyana ta fito daga bandaki ta yayyenta kowacce da murmushi a fuskarta. Zahra ta rungumeta tana dariya itama tana tayata ta tabbata abinda yasa su kuka dazu ya wuce. Ihunsa ya tayar da Radhiya da kyar ta iya bude ido sun kumbura tayi musu sannu da zuwa.
Fauziyya ta tuna cewa dazu maganganun su Mummy su ma daga dakin Awwab sun ji bare kuma ita da suka bari a nasu dakin. Sai taji tausayinta ya kamata "kinyi sallah kuwa ko sai nazo nayi miki balotelli?"
Murmushi tayi kanta kamar ya tsage ta daure "da almakashina a jaka"
Dariya suka yi su duka yanayin dakin yana chanjawa daga shiru shiru zuwa na 'yan mata wadanda ke tsaka da jindadi. Da bin bango Radhiya ta je tayi alwala ciwon kai yayi tsanani ga zazzabi. Bayan ta idar Zahra ta taba wuyanta ganin duka jikinta yayi la'asar.
"Radhiya baki da lafiya kika zauna shiru a daki. Bari na karbo miki magani"
Da saurinta ta fita taje dakin Mami tana tambayar panadol. Ummi sai da taji babu dadi tasan halin Radhiya da saka abu a rai. Karshenta kuka ta rinka yi ya janyo mata zazzabin da ciwon kai.
"Nemo min Awwab yazo ya kaita clinic dai. Ga gajiyar hanya kuma an taho ana tsaka da biki duka babu wani hutu" Mami ta umarci Zahra tana bin bayanta zuwa dakin. Ummi ko motsi bata yi ba tana addu'ar Allah Ya kawo sauki cikin lamarin saboda tsoro da ya fara darsuwa a zuciyarta.
Hankalin Mami ba karamin tashi yayi ba da ta taba jikin Radhiya. Jiki yayi mugun zafi fuskarta har wani ja take yi.
Awwab yana cikin shiryawa bayan yayi wanka Zahra taje ta fada masa sakon Mami. Ya rigata fita daga dakin da sauri. Sallama ya tsaya yi a kofar nasu dakin amma da kyar ya daure bai kutsa kai ya shiga ciki ba. Mami ta fito da Radhiya da ta tallafo a jikinta.
"Me ya sameta haka Mami?" Awwab yace a raunane. Abinda zai kashe bakin Radhiya da wannan kuzarin nata ba karami bane shima ya sani.
"Kuje mota bari na dauko mayafi. Zazzabi ne ina jin da ciwon kai"
A hankali ta rinka tafiya ganin Awwab ya sake tayar mata da hankali. Tana son shi dole ta barshi idan ba tana son abinda Ummi take guje mata ya faru da ita ba. Wasu hawaye ne suka zubo mata duk yadda taso daurewa ta kasa.
Sai da ya dan matso da kansa kusa da ita yana son rage mata damuwa ya tsokaneta dacewa "come on Schatzi bana son shagwaba fa. Ke da zansa a yiwa allura kamar hudu kuma kike min kuka"
Duk da ciwon haka ta harare shi yayi murmushi yana cewa "in dauke ki ne?"
A dole ta daga kafa tana jin kunyarsa. Da Mami suka je asibitin aka dubata likitan yace banda zazzabi harda damuwa. Mami sai ta alakanta komai ga abinda ya faru a gidan zuwan su Gambo. A take ta yanke shawarar sanar da Daddy yayiwa yaran magana gobe idan sun amince wa juna ayi bikin kowa ya huta.
Da suka koma gida ta fita tana jiran Radhiya shiru Awwab ya hanata fitowa ta shige ciki tana fadawa Ummi wai ta ga alama ciwon soyayya ne yake damunta. Ummi dai dariyar yake tayi, neman abokin shawara take gashi Zainab bata nan.
A wajen Awwab ya tsare Radhiya da tambayoyin son jin damuwarta duk da shima yana tunanin ko abin dazu ne "me kika sa a ranki har ya saka kiki fever?"
"Babu komai Hamma"
"Saboda zuwan Mummy ne dazu ko? Komai ya wuce kinji yanzu babu zancen Ghazalatu ma. Ke kadai ce dani Schatzi kuma kin isheni don son da nake miki bana jin akwai wadda zata sami rabinsa a wurina"
Kalaman sun mata dadi, da babu wannan matsalar da tafi kowa farinciki amma yanzu bata da wani abin yi sama da murmushi ta fake da rashin lafiya. Shima da ya ga shirun nata yayi yawa duk sai ya damu.
"I miss my Alheran, wannan mara lafiyar duk ta hanani ganinta. Kije ki kwanta and please take care of yourself for Awwab"
"Hammana sai da safe" yaji tace da karamar murya tana tafiya sai bayanta kadai yake iya gani.
Haka kawai yaji jikinsa yayi sanyi zuciyarsa tana tabbatar masa da cewa akwai wani babban al'amari a tattare da Alheran. Ko ma meye yayi niyar jira zuwa wayewar gari taji karfin jikinta sai ta fada masa damuwarta.
Daddy kuwa a daren ya kira Imam Abdulwahab ya fada masa basu da masaniya akan cewa akwai alaka tsakanin Raji da Zahra har aka yi mata miji. Imam yace basu yi sati da sani ba shi da matarsa. Sai da suka ga shige da ficen asibitin nasa yayi yawa suka matsa Munnirat kanwarsa ta sanar dasu. A lokacin hakuri kawai ya bashi tunda suna da labarin aurenta ya kusa. Major yace to aure ya tashi saboda ta sanar bata son angon nata. Yanzu haka ya kira ya sanar dashi ne cewa asabar mai zuwa ya kamata daurin aurenta amma za'a basu dama idan sun amince ya turo Raji neman aurenta. Bayerabe yasan darajar alkhairi kuma yana mutunta duk wanda ya karrama shi. Imam Abdulwahab ya rinka kwararowa Major da iyalinsa addu'a kuma ya tabbatar masa in sha Allah ranar asabar Zahra zata yi aure kamar yadda aka tsara tun farko. Da kansa yaje dakin Raji da yake kwance yana jinyar zuciyarsa yayi masa kyakkyawan albishir. A take ya wartsake sai gashi har asuba suna waya da Zahra wadda itama ta ware baka ce ita ce take ta koke koke a kwanakin da suka gabata ba.
SABUWAR RAYUWAR
"To Alhamdulillah al'amura sun daidaita Alh Baba ya amince da auren Awwab da Radhiya sannan duk da ba haka muka so ba Ghazalatu tace ta fasa. Allah Ya sani Ummin Awwab ban so kuka san wannan matsalar ba ko kadan a madadin Gambo muna masu baki hakuri akan cin zarafin da tayi muku jiya"
Ummi ta shiga girgiza kai "bamu hakurin tamkar kuna nuna akwai bambanci tsakaninmu ne Daddy. Wallahi har raina banji haushi ba saboda haka magana ta wuce"
Mami tayi murmushin jindadi sannan Daddy ya kalli Awwab da duk motsin Radhiya akan idonsa yake yana kokarin hada ido da ita amma taki dago kai. Gyaran murya yayi Awwab din yayi saurin juyar da kansa daya gefen yana murmushi.
"Awwab ga kanwarka nan na baka amana ko bayan raina ban yarda ka rabu da ita ba. Idan ta bata maka ko tayi ba daidai ba ka hukuntata amma ban yarda diyar Zayyan tayi kuka saboda rashin adalcin gidan aure ba"
Farincikin da Awwab yake ji a wannan lokacin bazai misaltu ba. Dan taki kalilan ya rage masa da mallakar abar kaunarsa. Yana sake dawowa ko sati daya ne hutun yake so a daura aurensu.
"In sha Allahu bazan baku kunya ba"
"Radhiya baki ce komai ba" Daddy yace yana kallonta yana murmushi.
"Ai ka kashe bakin nata Daddy yau daya dai ga kunya ga sauran zazzabi 'yata bata da ta cewa" inji Mami.
Hawayen zuci Radhiya take yi na samu da rashi da ya sameta a lokaci guda. A hankali sautin kukanta ya fito fili. Yadda Awwab ya gigice sai ya baka tausayi ana ta tambayarta ko jikin ne ta kasa magana. Ummi jikinta yayi sanyi amma ta san har ga Allah hakan da tayi shine daidai. Tafi kowa sanin ciwon da ta kunsa saboda juya mata baya da Salame tayi da rashin kyakkyawar alaka mai tattare da shakuwa da tayi karanci a nasu gidan. Banda ma yanzu da abubuwa suke dan chanjawa amma a da kam gidansu nafsi nafsi kawai akeyi kuma bata cire kanta a ciki ba saboda haka a ka sabar musu.
"Radhiya ko bakya son auren ne?" Daddy yace bayan ya karar da duka tambayoyin da yake jin zaiyi mata.
A razane Awwab ya kalle shi yace "Daddy?"
Ga mamakin su duka ukun Radhiya ta gyada kai. Daddy kansa sai da ya girgiza ba Awwab da ya daga murya yace "karya take yi Daddy"
Daddy yace "Awwab ka nutsu ko ka fita"
Zama ya koma yayi amma babu nutsuwa bare kwanciyar hankali. Ita wadda akeyi dominta kuka kawai take yi idanunta sunyi luhu luhu dama shi ta kwana tana yi.
"Muna sauraronki Radhiya"
"Daddy karatu nake son yi"
"Banda abinki Radhiya waye yace miki aure na hana karatu?" Mami ta tambayeta tana dan sakin rai a zatonta wautar ce ta motsa.
"Ba nace miki zan samar miki admission a Abuja ba?" Awwab ya ce muryarsa tana rawa yana kokarin danne bacin ransa.
"Daddy ni dai don Allah bana son auren nan gabadaya"
"Alheran!!!" Awwab ya daka mata tsawa ta kuwa sake tsorata ta fashe da wani kukan.
Gaban Daddy ya koma ya durkusa "don Allah kada ka saurareta wallahi karya take yi Daddy. Ka aura min ita ko ranar asabar ne tare dasu Zahra please Daddy"
Ummi ma dai kukan take yi tana tausayawa yaran har ta fara jin ko dai tayi kuskure ko matakin da ta dauka yayi tsanani da yawa.
"Ba kya son auren ko Radhiya?"
"Eh Daddy"
"To tashi ki tafi wurin 'yan uwanki na kashe maganar zan nemeki daga baya"
Baki Awwab ya saki yana karyata abinda kunnuwansa suka ji daga gareta da kuma Daddy. Jiki a mace ta tashi zata fita yasha gabanta.
Da fada ya fara cewa "Ni zaki yiwa haka Alheran? Ba sai da na nemi izininki ba kafin nazo na fadi cewa zan hadaki da Ghazalatu ba? Kuma yanzu ta fasa bazan hadaki da wata ba I promise" ya kare da kwantar da murya.
Daddy sai da yayi masa tsawa ya fita a fusace jikinsa yana rawa. Dakinsa ya tafi yana shiga sai ga hawaye. Ransa yaji ya kuma baci ya rasa me zaiyiwa kuka tun girmansa sai mace. Macen ma Alheran da ya bawa dukkan soyayyarsa a cikin abinda baifi wata daya ba amma tasa kafa ta ture saboda dalilin da bashi da muradin sani. Itama tana fita dakinsu Zahra ta nufa tana nata kukan kamar ranta zai fita. Bata hangowa kanta sauran farinciki tunda ta rasa Awwab.
Shiru falon yayi Ummi na goge hawaye Mami ta rasa me zata ce ma. Tashi Ummi tayi zata fita taji muryar Daddy a sojansa.
"Mairama dawo ki zauna ki fada min dalilinki na raba yaran nan"
Gabanta ne ya fadi Mami ta bita da kallon mamaki. Soja ba abin rainawa bane. Yanayinta kadai ya sa shi saurin fahimtar tana da hannu a abinda Radhiya tayi. Zama tayi ta nuna musu babban kuskuren da yake tattare da batawa da 'yan uwansu saboda yara.
"Yau da Allah Ya dauki raina bayan rasuwar babansu Karami ina mai tabbatar muku dawowar nan da kuka yi zaku sami yaran nan cikin mafi munin yanayi ne saboda babu wanda zai tsaya min ya kula dasu a gidanmu yadda ya dace. Gidan nawa mahaifin babu shakuwa babu sabo tsakaninmu sama da mutum ashirin. Wadda muke tamkar 'yan biyu da ita komai namu tare tazo ta juya min baya a dalilin son da ta yiwa Zayyan tun yana raye. Tun kafin muyi aure ta dauki gaba dani har yau bata sake zani ba. Ba yau da muke tare da 'ya'yanmu bace abin ji, gaba da bata da kadan Daddy ita ce abin dubawa. Mami don Allah ki sasanta da 'yan uwanki kafin kiyi tunanin auren nan. Kada ki manta a dalilinsa rigimar ta faro na tabbata ana yinsa sai abin yafi haka"
Sai yanzu Mami ta soma hawaye itama ta san cewa gaskiya Ummi ta fada. Duk da haka Daddy yace "da sai kiyi mana bayani ba sai kin raba su ba. Ummi yau kinsa Awwab da Radhiya kuka anya bazamu hukuntaki ba?" Ya kare da murmushin dattako.
"Nasan idan da ta amince babu abinda zai hanaka daura musu aure. Radhiya dai 'yarka ce wani ma zaka iya bata bare Awwab. Alfarma daya nake nema ayi sulhu a daidaita zumuncin da yake neman lalacewa. Idan haka ta faru ko gobe ne wallahi ayi musu aure"
Tana kaiwa nan ta tashi ta bar falon. Mami tana kuka tacewa Daddy hakika Mairama tayi zurfin tunani bata so kanta ba ta hakura da farincikin 'yarta dominsu. Sun yabawa Zayyan a baya yau suna yabawa matar Zayyan saboda a karo na biyu wannan iyali sun sadaukar da nasu jindadin don su kyautata musu.
BAYAN SHEKARA DAYA
Matashiya ce kyakkyawa sanye da riga mai dogon hannu baka mai kanun fulawoyi jajaye wadda ta tsaya mata a rabin cinya da skirt mai fadi shima baki tayi rolling da mayafi ja. Takalmanta loafers ne bakake da bakar jaka mai fadi wadda ta saka computer da tarkacen litattafai. Siririn agogon hannunta ta kalla tasan cewa kowane lokaci daga yanzu Yousuf zai iya kiranta su tafi gida.
Watanta tara tana daukar kos na koyon turanci da faransanci sannan aka samar mata gurbi a University of Grenoble dake kasar Faransa inda ta fara karatu sati uku da suka wuce a fanin aikin jarida wato mass communication.
Kamar yadda tayi hasashe wayar Yousuf ce ta shigo mata ta taso tana tafiya kai baka taba cewa Radhiyan rugar Barkindo bace. Ta koma hadaddiyar budurwa mai ji da gayu da wata irin nutsuwa kamar ba ita ba.
Kamar kullum sai da ya bude mata ta zauna sannan ya shiga ya tayar da motar. Gaishe shi kawai tayi ta soma waya da Umminta wadda take karatun jarabawa saboda tuni itama ta koma karatu ta sami gurbi a jami'ar Bayero ta Kano tana karanta Adult Education. Mairama Ali Gidado ta zama babbar mace da maza suke kawowa hari ta kowane fanni suna neman aurenta. Da yawa basa yarda ma tana da yara biyu matasa da suke karatu a jami'a.
"Ina Tante din taki ko kina makaranta ne?"
"Ina hanyar komawa dai Ummi"
"Kice ina gaisheta. Gobe zamu je NDA na fada miki za'ayi taro kuma Karami yana cikin masu yin match pass"
Turo baki tayi cikin shagwabar da Tante dinta take kara ingizata take yi yanzu tana biye mata tace "ni yanzu bazan gani ba kenan? To ku daukar min video kinji Ummina"
Dariya Ummi tayi ta rasa yaushe Radhiyanta zata girma "zan dauka in sha Allahu 'Yar soja rigima"
Dariya tayi mara sauti Yousuf ya kalleta yana jin lokaci yayi da zai sanar da mamansa ya mugun kamuwa da son 'yarta. Sun cigaba da hirarsu da suka gama ta kira Ibrahim tana tambayarsa progress din jikin Baba Hadir.
"Akwai babban albishir sai na koma gida zamuyi skype. Ke dai bari kawai na tsakura miki, ya fara tafiya babu sanda"
Wata dariya da tayi sai da Yousuf ya manta me yake yi na dan lokaci. Tana zuwa gida da sauri ta shiga ta haye sama dakin 'yar Mammee wadda ta kasance kanwa kenan ga mahaifinta Zayyan mai suna Nasara ta fada jikinta tana murna.
"Tante Babana Hadir ya soma tafiya babu sanda"
"Da gaske Alheran" tace tana tayata murna.
"Oui Tante" (eh anti) tace tana rungumeta.
"To maza kije kici abinci kizo"
Radhiya na fita Nasara tana kallonta zuciyarta fes.
Bayan fasa aurenta da Awwab wanda yayi sanadiyar da ya bar gidan ana dawowa daga daurin auren kannensa ya koma Abuja kwana uku kafin hutunsa ya kare. Yayi fushi sosai da Radhiya wanda har Daddy yayi masa bayanin dalilin yin hakan bai dena jin zafin abin ba. To bayan komawarsu ne aka turo daukarsu daga Nijar inda suna zuwa Nasara diya ga Mammee tazo hutu da mijinta da dansa Yousuf wanda mahaifiyarsa ta rasu ta shiga rokon arzikin a bata ita. Bata taba haihuwa ba gashi tana da son yara. Ita tana yi mijinta na tayata aka kai maganar gaban Ummi ita kuma tayi kawaicin hadasu da Daddy. Ba tare da bata lokaci ba ya amince ko babu komai yana sa ran zata samu kyakkyawan sauyi a rayuwa. Zamanta tare dasu ba'a cewa komai sai son barka. Nasara tamkar ta goya Radhiya don so. Babu ta inda ta rageta ta fanin gyara shiyasa tun a yanzu tayi fice ta wuce raini nesa ba kusa ba. Kakaninsu ba a barsu a baya ba wurin yi musu aike ita da Emzee duk karshen wata.
Emzee ma sun so rike shi a Nijar amma fafur yaki shi soja yake son yi abinda bai taba fadawa kowa ba. Cikin dan kankanin lokaci Daddy da taimakon Captain Onomza suka samar masa admission. Ibrahim kuma ya sami Law a Buk itama Ummi ta sake WAEC shekara na zagayowa ta koma makaranta. Gidan Zayyan na Kano Alh Sidi yayi mata gyara na gani na fada ta koma tare da kanwarta daya da kaninta wadanda su ma suke karatu kuma take ta kokarin gyara zumuncin gidansu shiyasa ta taho dasu.
Baba Hadir kuma watansu uku suka dawo yana motsa hannuwansa da kafa amma tafiyar bata kankama ba sosai sai yau da Ibrahim ya fadawa Radhiya.
***********
"Dad please kaje dani mana"
"Ke komai kike so sai anyi miki ne kamar wata yarinya?" Inji mamanta
"Kina matsa mata da yawa fa. Meye a ciki don ta raka babanta taron karrama sojoji masu fita (POP)"
"Naga official taro ne your excellency " maman tace tana murmushi.
"Official baya nufin naki zuwa da 'yata. Arifah ki shirya dake zani Kadunan"
Bayan ta fita daga dakin nasa tana dariya mamanta ta sake sako masa zancen rashin aurenta da yake damunta.
"Kasanta da jin kai gashi masu yawan zuwa yanzu yawanci duka saboda mukaminka suke son ace sun zama surukan gwamna"
"Ki dena damuwa mijinta yana tafe in sha Allah. Ni fa tafiyar nan wani dadi nake ji game da ita na rasa dalili."
Murmushi tayi tana tunanin ko don yana kewar harkokinsu na sojoji ne. Gashi a matsayinsa na tsohon soja an gayyace shi bako na musamman a taron POP din sababbin jaruman da kasa zata yaye bana.
[5/22, 11:03 PM] Sis Ruky: Mami sai da ta waiga baya ta tabbatar su kadai ne sannan ta girgiza kai "kinyi sa'a da yara a gidan nan da na miki dan biki. Zan zo har gida na sameki"