Batuol mamman complete novel - Chapter 36
Batuol mamman complete novel Chapter 36: Batuol mamman complete novel Chapter 36. Nasara ta rungume Radhiya tana ta murna. Ita take tuka su zuwa gida yayin…
3,358 words
Nasara ta rungume Radhiya tana ta murna. Ita take tuka su zuwa gida yayin da Radhiya take ta waya da mutanen gida. Ummi, Mama da Baba, Daddy da Mami, Mammee dasu Alh Sidi. Ibrahim da Emzee babu wanda bata kira ba tana sanar dasu cewa su fara shiri tana nan tahowa Nigeria nan da sati daya.
***********
Sai kai kawo Ummi da Mami suke yi a hanyar dakin theatre din da aka shiga da Mama. Ciki ya wuce kwanakin da ake sa ran haihuwarsa harda sati takwas yana cikin wata na goma sha daya yayi mugun girma. An so inducing dinta da wuri taki saboda tsoro ga dadewa bata haihu ba. Daga baya da kyar Baba Hadir ya lallabata sai da Ummansa da Mamanta suka sa baki ma. Shine aka yi inducing din nata kwana biyu tana fama da matsananciyar nakuda amma haihuwa shiru. Yammacin rana ta biyu ne aka yanke shawarar yi mata CS.
Baba Hadir yana mota hankalinsa ya tashi matuka. Shiyasa ya bar inda su Mami suke kada su ga shima namijin yayi rauni. Zainab dinsa bazai taba iya hada soyayyarta da ta kowa ba. Tayi masa abinda har ya mutu bazai taba iya biyanta ba. Inama cikin zai dawo jikinsa da ya hutar da ita. Text din Ibrahim ne ya shigo wanda tun safe yake yinsu ya kasa amsa masa. Sauran kwanakin tana daurewa ta dauki wayarsa su gaisa. Sauransa jarabawa biyu ya gama level 2. Ummi ta riga shi gamawa dama ba department dinsu daya ba amma tare suke tafiya a karatun. Kwana biyu taje tayi a Sumaila ta wuto Abuja saboda sanin halin da Mama ke ciki haihuwa ko yau ko gobe. Yau da ciwo yaci karfinta har aka shiga cs din Ibrahim bai sami kowa ya daga wayarsa ba shiyasa gabadaya ya kasa sukuni.
Baba Hadir yana kokonton amsar da zai turawa dan nasa Major ya kira shi ba wai don ya amsa masa da baki ba, ya dai san zaiji me yace.
"Hadir ka bar mata a ciki suna ta nemanka an fito da Zainab. Mun sami namiji"
Kabbara Baba Hadir ya shiga yi a zuci yana ta kokarin ya iya fitar da sauti da bakinsa ma. Waye zai karyata Kadaitar Allah a matsayin Ubangijin talikai? Shi Hadir da ya shafe shekaru yana kwance sai yadda akayi dashi. Fitsarinsa da kashinsa tun dansa Ibrahim yana da karancin shekaru yake wannan dawainiya shine a karo na biyu ya sake haihuwa da Zainab. A take ya turawa Ibrahim kyakkyawan reply sannan ya fita daga motar ya koma ciki.
Dakin da aka tura Zainab din aka nuna masa. Ummi na rumgume da baby din an nado shi da shudin shawl mai laushi sai raba idanu yake yi. Mami kuwa ta saka shi a gaba wai yasan yana son kallon duniya me ya zauna yiwa kanwarta a ciki.
Sai da ya dan kwankwasa sannan ya tura kofar ya shiga. Zainab baki ya mutu tana kwance allurar anasiziya bata gama sakinta ba. Sai dai da yake ta ido biyu ce tana jin me suke yi tana murmushin wahala. A kusa da ita ya zauna a gefen gadon Ummi ta dora masa jajirinsa a hannuwansa da ya bude.
"Zz..Zayyyyan" Baba Hadir yace da dukkan dagewar da zai iya yana rungumar yaron a jikinsa.
Idanun Ummi tuni sun ciko da kwalla har ta fara zuba Mami ta riko hannunta suka fita domin a basu wuri.
"Hadir magana kayi?" Mama tace tana kallon fuskarsa.
Murmushi yayi mata yana shafa kanta da hannu daya ya kuma cewa "Zayyan"
"Alhamdulillah...don Allah ka rinka kokarin magana kaji. Ina son jin muryarka Baban Ibrahim da Zayyan"
Kai ya gyada yana ta murmushi idanunsa na yawo tsakanin baby Zayyan da Zainab. Tun ranar da aka tabbatar mata da cewa namiji ne ta sani ko bai fada ba sunan yaronta Zayyan. Ko yana da rai tasan su biyun masu musayar sunayensu ga 'ya'yansu ne bare kuma daya baya nan ya bar musu wawakeken gibi a zukatansu.
Kafin gari ya waye duk wanda ya kamata yaji haihuwar nan yaji. Iyayen Mama da na Baba murna ba'a cewa komai. Har waya suka yi suna yiwa juna barka. Soyayyar nan daga Allah ce. Dubi shekarun da tayi a gidan Alh Musa sau daya tayi bari sai gashi daga samun lafiyar Hadir anyi ciki har an haife. Wannan shine dan soyayya inji Mami.
Radhiya kamar ta jawo tafiyarta da ta rage kwanaki uku. Wani babban mall ta shiga ta jidowa kanin nata kaya na ga na fada ta kara akan tsarabar da ta gama hadawa. Duk zuwa gida sai tayi wannan tsarabar saboda bata ga me zata yi da kudaden da suke jibge a account dinta ba. Mijin Nasara yayi daga Nijar kakaninta kamar masu gasa da juna wurin yi musu aike ita da Emzee. Ga uwa uba His Excellency ya mayar dasu kamar masu daukar albashi.
Kwananta Mama biyu a asibitin aka sallamota. Ummi ita ce uwar da tsakaninsa da Mama shayarwa ce sai kuma dare idan zata koma gidanta. Mami kuma duk wata bukatar maijego tana wuyanta. Baba Hadir gani yake sunfi kowa sa'ar zumunta a duniya. Babu ta inda jini ya hadasu amma dangantakarsu kullum kara karfi take yi.
Fauziyya ta matsawa Bilal da zaiyi tafiya Lagos wani aiki ya kaita Abuja ita da Jawad dinta da ya fara yawo ko ina. Zahra ma Radhiya tana sayen ticket ta fara yi mata famfo har yau bata taba ganin Femi a zahiri ba. Ba don yaso ba Raji yace zai kawota amma da sharadin idan ya kasa hakuri zata ganshi kuma dole su tafi. Shima yana son zuwa gaishe da yan uwan iyayensa ne a Osun state shine zasu fara zuwa kafin.ya dawo da ita Abuja.
Gidajen uku sun fara shiri duk da an dage suna ma sai sunyi sati biyu maijego ta kara samun sauki.
Yau da wuri Ummi taje ta yiwa baby wanka ta dawo gida. Dakuna uku ne a gidan daya nata sai na Emzee da Radhiya idan sun zo hutu. Rigima irin ta Radhiya wai dambun shinkafa take so taci shiyasa Ummi ta koma gida ta dora. Idan ba haka ba tunda da Nasara zasu zo tasan sai sun hanata sakat da mita. Hadi na musamman ta yiwa dambun nan da kayan lambu da hanta gida ya kaure da kamshi. A wadace tayi shi kuwa saboda dawowar Radhiyan rana dayane da Zahra. Dama shirya abinsu suka yi wai sun dade basu hadu ba ana kewar juna. Mami ta aiko mata da farfesun kayan ciki cikin flask wanda ta hada dasu da zata yiwa Mama saboda a nan duka zasu ci abinci bangaren Ummin. Fauziyya tuwo tayi musu Zayyana 'yan mata kuma salad da drinks ta hada aka jere komai a gidan Ummi. Su Zahra da azahar zasu sauka Radhiya kuma sai biyar na yamma.
Major jiran zuwanta kawai yake yi saboda murnar nasarar da ta samu na project dinta. Ita da Zayyana da ta gama secondary bana ya tanadar musu wani babban surprise.
Duka suna wannan abu Mama ta kira Awwab kwanaki biyu da suka wuce ta tambayeshi yaushe zai dawo ne yace sai nan da sati uku. Yanzu haka ya koma Germany babbar hedikwatar kamfanin nasu akwai abubuwan da zai karasa ya taho gida.
"Babu yadda za'ayi ka dawo ranar Juma'a?"
"Mama so nayi na gama komai yadda idan na dawo sai na cike wata biyuna kafin na koma aiki" ya bata amsa.
"Ni dai idan da hali ka taho ina son ka taho iyayenka na bukatarka. Ka kusa shekara fa rabonka da gida duka ka barmu da kewa."
"To Mama zanyi kokarin tahowa tare da Zahra tace min jibi zata taho. Idan na kwana biyu sai na koma na karasa aikin"
"Allah Ya shi albarka Awwabun Ummi"
"Amin amma naki ne yanzu. Ummi ta dade da yayeni ai. Kada ma kice musu zanzo ita da da Mami ba murna zasu yi ba."
Mama sai murna ta dana tarko zata sha kallo. Ta san idan Radhiya ta iso baifi sati biyu zuwa uku zata yi ba zata fara aikin da ya dawo da ita. Shi kuma kullum yana sama kamar tsuntsu har sai yaushe zasu daidaita ta ga ta fara shirin bikinsu.
An gama komai dreban Daddy ya tafi dauko masu fara sauka idan ya kaisu ya dawo daukar na biyun saboda motar tayi musu kadan kuma babu mai tuka ta Mama. Ibrahim sai laraba zai dawo shi kuma Emzee nasa zuwan sai kwana biyu kafin suna. Ya gama mita wai kiran me ake yi musu don za'ayi suna Ummi tace yaushe rabon da su taru lokaci guda duka. Kuma ma ana gama sunan Rugar Barkindo zasu je da Sumaila kafin Radhiya ta fara aikinta.
Su uku suka fito daga cikin airport din. Raji, Zahra da kuma Awwab da yake dauke da Femi. Mutan gida kowa yayi mamaki da murnar ganinsa. Yayi wani irin haske da kyau saboda kasar Ukraine akwai sanyi sosai. Ga girma da cika ido tamkar Major zamanin kuruciya. Dukkansu gidan Mama suka shiga ya mikawa Fauziyya Femi ya koma gefen Ummi da hannuwansa a mike yana jira ta ajiye masa baby Zayyan.
"Naki din, yanzu zaka zo Awwab sai dai in ganka kuma jiya ma munyi waya fa" tace tana bata rai.
"Ummi kin dena sona ne, a wayar ma fada kike yi min" yace yana dariya.
Sauran ma sai suka soma dariya ana tsokanar Ummi wai Mama tayi mata kwacen da.
"Ga sabo me zanyi da wannan katon nima. Na barwa Mama dama haka take so"
"Ke dai kawai don kinga munfi shiri yanzu shine zaki tashi hankalinki"
Sosai ta rinka zolayar Ummi ta kuwa hana shi baby din ya gama nacinsa ya hakura.
"Abincinku yana gidan Ummi. Zahra mijinki zai ci a can ko a kai masa dakin Awwab?" Mami ce tayi tambayar tana rike da Jawad da ya hanata zama yace wannan ya nuna wancan.
"Ni dai na koshi" Awwab yace ya tashi zai tafi daki.
Ummi ta tabe baki "kun gani irin halin nasa, mutum yaki cin abinci kullum koshi yake kira alhalin baici komai ba"
"Ummi ki rabu dashi yunwa ai ba kanwar uwa bace. Zata koro miki shi anjima"
Daga shi har su Zahran a gajiye suke. Dakinsa wanda aka gyara domin zuwan Raji suka shiga suyi wanka. Fauziyya ce ta yiwa Femi ya ware suna wasa da Jawad. Mami sai murmushi wadannan yaran jikokinta ne.
Sai karfe shida da rabi su Radhiya suka iso gidan suma a gajiye sai dai murna da doki bazasu bari taji da gajiyar jikin nata ba. Ita da Tante Nasara ne da Yousuf. Suna sauka daga mota tayi gidan Mama da sauri. Irin shigar da ta saba tayi na skirt mai fadi da riga iya cinya mai dogon hannu madaidaiciya wadda bata kamata ba bare ta fito da shape din jiki sai rolling din mayafi da tayi. Yousuf yana kallon yadda take sauri ya girgiza kai. Wani zubin kamar ta girma amma idan abin ya motsa sai tasa mutum dariyar dole. Yanzu ma saurin da take yi wai kada a gama rigata daukan baby ne.
Tunawa tayi da jan kunnen da Tante take yi mata akan rashin nutsuwa sai ta tsaya ta daidaita kanta sannan ta shiga da sallama. Mama tana zaune kasa hakuri tayi ta taso ta tarbi 'yar tata cike da farinciki.
"Radhiya kece kuwa? Bari dai maman taki tazo naji ko an baro min tawa a can ta kawo min ta bogi"
"Kai Mama" tace tana murmushi amma duk iya dauriyarta rashin ganin baby din yasa ta soma bata rai "Mama ina Daada?"
"Wai da gaske haka zaki rinka kiran sa?"
"Oui Maamon" Ta amsa da dariya tana mata salute suka sa dariya tare.
"Yana bayan Mami yanzu ta fita zata dawo am....."
Radhiya har ta kofa tafiyar da bata kai minti guda ba ta kaita gidan Mamin. Tana iya jiyo muryoyinsu Zayyana ta fada da sauri tana murna. Su duka Mami ce tace su fita a bar Mama tayi bacci ko ta huta dai.
Kan kace meye wannan sun cika gidan ba babba ba yaro daga kan Zahra har Zayyana. Murnar ganin juna suke yi sosai. Kowa yayi mamakin Radhiya ta canja sosai ta zama wata rabin baturiya. Ta dauki Jawad da Femi duka lokaci guda tana juyi dasu.
"To dai ku rage hayaniya kunga mijin Zahra yana ciki kada ku hana shi hutawa" Mami ta fada tana ficewa da baby a bayanta don bazata yarda suna wannan hayaniyar ta damka musu dan amana ba. Suje can su karata da nasu 'ya'yan tunda su da kwarinsu.
Zahra ta dora hannu a baki tana kunshe dariya "Hamma Awwab kai Mami, shi yafi kowa gudun hayaniya yanzu."
Dif Radhiya tayi gabanta na faduwa. Hamma Awwab yana cikin gidan bata sani ba. Da yaran a hannu ta juya zata fita ta rasa murna ce ko tsoro ko kuma bacin rai na shareta da yayi. Suna zuwa kofa Femi ya bare baki yana mikawa Zahra hannu.
"Tafi can nima bana yi da kai mai kyuya kawai. Kuma zaka ganni na goya Jawad ne na bashi chocolate" tace tana mikawa Zayyana shi tunda tafi kusa.
Kukansa da Raji yaji yasa shi bude kofar dakin Awwab kuma a lokacin ne tayi wannan maganar a kunnuwan Awwab din. Comb ne mai brush mai laushi yake sake kwantar da sumar kansa duk da yayi aski saisaye amma gashin ya soma fitowa. Dena brushing kan nasa yayi ya kallo kofar yayi sa'ar ganinta tana hararar Femi da ganin babansa yasa shi dariya.
Murmushin da baiyi niyya bane ya kwace masa yana kallon yadda take hararar yaro a gaban iyayensa kuma wai nan fushi ne kawai don yaki binta "Silly girl" ya furta a hankali idanunsa a kanta har ta fita daga gidan.
Ko da ta isa gidan Tante da Yousuf suna tare da Ummi suna cin abinci. Dukkansu dama yunwa suke ji tun a hanya. Wurin Ummi taje ta rungumeta tana dariya.
"Umminaaaa"
"Meye haka, tashi ni ki dagani" Ummi tace tana jin kunyar Tante ba don bata murna ta ganin 'yarta ta ba.
"Alheran rabu da ita kinji. Zuba abinci ki ci"
"Wanka zan fara yi. Ummi yaushe Emzee da Ibrahim zasu zo?"
"Kafin ki fara aikin in sha Allahu. Kiyi wankan sai kuci tare da su Zahra su ma basu ci ba muna gidan Zainab tun dazu ana hira"
"Ai sai an dawo da komai baya bari na shirya dai."
Dakinta ta wuce akwatunan Fauziyya da Zahra suna gefen inda Ummi ta tura mata nata. Su ukun a nan zasu kwana. Yousuf a dakin Emzee ita da Nasara a dakin Ummin. A can gidan Mami kuma Zayyana ce kawai sai Awwab da Raji.
Tana wanka tana tunanin wai Awwab yazo. Yaushe rabon su da haduwa. Gabanta har wani faduwa yake ta koma shiryawa a hankali. Duk yadda yace yana sonta ko sau daya bai nemeta a waya ba tunda ta tafi wai shi fushi. Kwafa tayi ita kadai. Ranta taji ya baci tayi siririn tsaki tana tazar gashinta da ya zarce kafadunta. Dama ita kanta akwai cika ga santsi shiyasa duk gyaran da take masa bai wuce amfani da shampoo masu kyau ba sai steaming da Tante take mata a shafe shi da mayuka. Tana daure shi yake kwanciya a kanta sai tayi rolling dinsa a keya ko tsakiya da ribbon. Ita da kitso sai sunzo Nigeria ko Nijar.
Doguwar riga ta saka ta wani yadi mai laushi anyi mata free style da dogon hannu. Karamin mayafi ta yafa bayan ta shafa hoda, kwalli da wani lip gloss light brown. Sassanyan body spray ta feshi jikinta dashi ta kuma saka turarensa a kayanta. Kamshinsa bashi da karfi very cool daidai da mata.
Ta bata lokaci sosai sai da tayi sallar magariba da isha ta fito. Fauziyya da Zahra ta gani da yaransu su Ummi suna gidan Mama har Tante.
"Kunci abincin?"
"Au wai da baki ci ba Radhiya? Shine kika makale a daki" Inji Zahra
Hira suka dasa suna yiwa juna tambayoyin yaushe gamo ta durkusa gaban kwanukan abincin da aka sauke a tsakar falon ta debi dambun yadda take jin zai isheta da farfesun a karamin bowl. Kan dinning table ta ajiye komai ta karkata kujerarta yadda zata ji dadin hira dasu Zayyana ta shigo tana waya da Emzee. Wuri ta samu ta zauna a kujerar kusa da Radhiya suka ji wannan deep voice din ta Awwab yana sallama.
Kowa ya amsa sallamar harda Yousuf da ya fito daga daki a lokacin amma Radhiya ta kasa bude baki kamar wadda ta hadiyi kota. Ko dago kai ma ta kasa yi tana rike da cokali a hannu tayi kasa da kanta. Zuciyarta na tsananta bugu.
Fuskar Awwab a sake yaje ya mikawa Yousuf hannu suka gaisa tare da fadawa juna sunayensu. Zama Yousuf yayi a kan daya daga kujerun falon suka gaisa da su Zahra.
Shi kuma Awwab ya tako a nutse zuwa dinning table din da yake kusa da bango daga bayan kujerar da Yousuf ya zauna.
"Bani wuri" yace da Zayyana yana mata nuni da kujerar da take zaune a kai. Da sauri ta tashi ta koma wurin su Fauziyya shi kuma ya zauna. Gabadaya ji tayi falon yayi mata kadan tamkar cikin akurki aka kulleta tare dashi. Bai ce mata komai ba ya karbi cokalin hannunta ya zuba farfesun akan dambun ya diba yasa a baki sannan ya mika mata. Sai a lokacin ta dago kanta suka hada ido. Babu wanda zuciya da gangar jikinsa bai aika masa da sako mai girma a tattare da dan uwansa ba. Sun chanja sosai shekara kusan uku ba yau ba. Sauke nata idon tayi da sauri ya sake mika mata spoon din.
Dan cije lebenta tayi tana tuno wani lokaci da abu makamancin haka ya taba faruwa dasu a Kano da Sumaila. Tana ji a jikinta ma mutanen falon kallonsu suke yi sai kawai ta dake ta karba. Idan bata basar ba zato zaiyi ta wani damu dashi ne har yanzu. Diban abincin tayi ta saka a bakinta cike da kunya. Kafin ta mika masa ya zura hannu ya sake karba ya ci sannan ya bata. Falon kamar anyi ruwa an dauke. Ita ta kasa kallon gefen da sauran suke shi kuma nasa idanun a kanta suke ba ma kallon plate din gabansa yake yi sosai ba. Yousuf yana ganin wannan abu yaji wani daci daci na taso masa dole ya tashi ya koma dakin Emzee. Awwab yayi wani murmushin gefen baki. Shi kuwa tunani yake wai dama Hamma din da take fada saurayinta ne ko me? Anya shakuwa zata sa Alheran cin abinci plate daya dashi kuwa? Ko da wasa duk zamansu bata taba kwatantawa ba.
Sun cinye abincin dama ba wani yawa ne dashi ba Awwab ya janyo flask din "in kara miki?" Yace yana kallon zoben nan da ya bata har yanzu yana yatsanta
To a gaskiya ba koshi tayi ba ta langabe kai har yanzu taki yarda su hada ido "kadan"
Zubawa ta ga yana yi fiye da yadda take bukata ta kuma dago kai tana ware masa idanu "its ok"
Sai da ya zuba wanda yake ji zai ishesu su biyun ya sake mika mata spoon din taci ta bashi. Da za'a ce mata kyat a guje zata bar wurin saboda kunyar da take ji amma ita a dole sai ta basar kada ya rainata. Shi kam rabonsa da jin nishadi irin na yau ya manta. Ya kasa dena kallonta kamar ba Alheran dinsa ba. Tayi masa kyau sosai ga wata zazzafar soyayyarta tana fizgarsa kamar yadda ya kamu da sonta farkon haduwarsu. Ba don abinda tayi masa ba da yanzu kila suna da yara kamar nasu Zahra. Ba komai ya kawo shi gidan Ummi ba a lokacin sai zuwansa wurin Mama suka shigo da Tante Nasara. Mama da gayya ta dauko zancen Yousuf saboda yaji. Ai kuwa ta tayar masa da hankali.
"Haj Nasara wato kin mana kwacen 'ya sai munyi da gaske muke ganinta"
Dariya tayi tace "kuma ko na tafi wallahi a bar min yarinya ta sake. Ni da Yousuf duk mun shagwabata. Idan naji ba daidai ba ke zan fara kamawa"
"Bama zaki ji komai ba. Yaron nan naki akwai nutsuwa Nasara. Naji kamar Radhiya tace likita ne ko?"