Batuol mamman complete novel - Chapter 44
Batuol mamman complete novel Chapter 44: Batuol mamman complete novel Chapter 44. Yana juyowa suka hada ido ta gudu duk kiran da yake mata kunya ta hanata…
3,368 words
Yana juyowa suka hada ido ta gudu duk kiran da yake mata kunya ta hanata tsayawa. Bata sake bari sun zauna su kadai ba saboda kunyarsa da ta rinka ji. Da ana daukar hotuna kuwa fafur taki yarda ayi musu su biyu.
**********
Rama 'yar asali ba bogi ba Malamijo ya sake yi gabadaya ya sake karewa sai kasusuwa sai kayi zaton mayun gidansa sun fara lasarsa ne. Gidan gonarsa yaje za'ayi lissafin abincin dabbobin da kuma ware wadanda za'a kai Enugu karshen sati.
Yana zuwa babban yaronsa Talle ya soma cewa "Yallabai an fitar da shanun da ka turo a dauka. Gaskiya kayi dabara da kace a rage wasu saboda nan din ya soma matsarsu basa walawa sosai"
A take ya soma zufa duk da sanyin gari "wadanne shanu kenan?"
"Wanda ka turo dan wajen amaryarka mai zuwa daukan kaji ya dauka mana. An bashi ashirin da uku yanzu saboda motocin sunyi kadan zai dawo a cike hamsin din"
Jiri ne kawai ya soma dibar Malamijo saboda tashin hankali jikinsa yana rawa yace "ni ne zan turo a kwashe shanu? Da can a ina suke ban ce a raba ba sai yau?"
"Ba dai karya yayi min ba yaron nan? Kusan awa guda da tafiyarsa"
Kuka Mamamijo yasa bare da ya soma dubawa a gigice ya fahimci manya manyan bijiman sa aka kwashe "da su taba shanun nan ba gara su lasheni ba ita da yaranta"
Talle dai lallashi yake yi Malamijo ya kama hanyar gida fakam fakam yana zubar da hawaye kamar yaro. Daga tarewarta sunci kaji yafi hamsin. Sau biyu ana daukar tumaki duk yayi shiru don tace masa magana na fita ko ita bata cinyeshi ba yaranta zasu ci. Dakinta yaranta ne a ciki ita kuma ta tare a dakinsa sauran matan basu da girki. Sai dai kowacce ta dora abinda ya samu suna kallo ana wadaka da nama kullum. Babur ya tare ya hau don yayi saurin zuwa gida.
Yana zuwa gidan bata dakinsa ya tafi nata. A can yaji tana waya tana kyakyata dariya "Talle baka da kyau. Kasan shawararka ta maita tayi sosai. Tsohon banza yana son ransa da na kada idanu sai kaga yana tsuma. A sayar da shanun nan ko dubu hamsin hamsin ne tunda kace manya ne kowa ya dau rabonsa"
Wani gululun bakinciki ne ya turnuke shi yadda Hajiyayye tayi masa wasa da hankali. Yanzu yana fito da maganar nan magauta sai su sami abin dariya. Ta ina zai samu ya gasa musu gyada a hannu kafin ya damkawa hukuma? Shawara daya ce tazo masa ga bacin rai ya dauki waya ya kira Mairama.
A lokacin tana ta koyawa Zayyan yadda ake tura sako a waya yana ta mamakin fasaha da kimiyar nasara sai ga wayar Malamijo. A ladabce ta amsa ga tsoron ko lafiya saboda shi dai baya kira sai dai a kira shi. Ko gaisuwarta bai amsa ba ya soma bambami.
"Yanzu Mairama kin kyauta min kenan? Yarinyar nan 'Yar soja ance tazo hutu amma ni ban ganta ba har yau. Naka naka ne Mairama a rinka zumunci."
"Malamijo kayi hakuri dama satin nan zasu zo da Karami sai wani dalili ya gifta amma suna tafe wallahi"
"To ni dai idan da hali su taho gobe ko jibi. Idan ma kudin mai ne babu zan biya. Ina ta shelar akwai jikata a Faransa abokai sunki yarda. Shi kuwa Zayyanu kice ya taho da kayan sojojinsa idan da bindiga ma ya dauko ko ta katako ce."
Jikinta ne ya bata ba lafiya "Malamijo me ya faru ne?"
Kamar ya fada mata amma zuciyarsa na zargin tana cikin masu murna. Duk wanda yaji me ya same shi cewa zaiyi Allah Ya kara. Radhiya kuwa yasan ko zata yi dariya sai ta rama masa su Hajiyayye bazasu tafi haka nan ba. Zayyanu karami kuma ai soja ne dole ya tsaya masa ko baya so tunda hukuma dai anyita ne domin kare al'umma eheee.
Tana ajiye wayar ta kalli Zayyan da 'yar damuwa a fuskarta "ina jin fa an tabo min uba, akwai abinda ke damun Malamijo"
Dagowa yayi daga kan cinyarta da yayi matashi "tun baki tabbatar ba kin soma hade rai"
"Sai naji duk na matsu nima na ganni a Sumailan. Idan wasu ne suka taba shi ba yarda zanyi ba, ina son tsohona"
"Mairama wai ni wa Alheran ta gado ne? Tawa ce ta fito fili amma kema fa ba jin magana kike ba"
Dariya tayi sosai kafin suka yanke shawarar tafiya Sumaila jibi su ajiye yaran su wuce Sakkwato. Daga can kuma suyi Nijar in sun dawo su tsaya a rugar Barkindo kafin su dawo Abuja.
Zuwansa headquarter dazu an kare komai amma duba da cewa dole ya bukaci lokaci da iyalinsa shiyasa aka bashi zuwa farkon sabuwar shekara wanda daya ga wata ake son yin taron karrama shi. Idan an gama zaiyi wata uku yana daukar training da courses domin ayi updating dinsa tunda Nigeriar da ya dawo ba ita ya bari ba a 1994.
Akan wannan shawarar suka tsaya bayan magariba lokacin su Radhiya sun dawo ya shiga wurin Baba Hadir. Nan ya sami Awwab zaune a kasa a gabansa yana rokon shi dai yana dawowa don Allah ayi aurensu da Radhiya kafin ta koma. Ya kara da cewa ya bada cigiya jiya a cikin estate din block C akwai gida.
A dan littafinsa Baba Hadir ya rubuta masa cewa zai yi magana da ita da kuma su Daddy.
"Ni dai Baba da ka kyaleta wallahi tsoronta nake kada a maimaita irin na da. Kawai ka yanke hukunci shikenan"
"Kada ka bada maza mana Awwab ya haka kake tsoron matarka" cewar Zayyan yana dariya.
Awwab sai ya tashi ya fice yana mai jin kunya. Hadir ne ya rinka masa bayani a rubuce na abinda ya taba faruwa da kuma bukatar yaron har yanzu.
Sai da Zayyan ya gama karantawa tsaf sai ya bata rai "nifa na baro A B C D din a Liberia kayi min bayani kawai."
"Zayyan" Hadir yace yana dariya.
"Kaga yara dai naku ne bani da ta cewa akan komai nasu nima dan gayya ne. Fatana Allah Yasa wannan karon babu wata matsala da za'a samu daga Katsinan"
"Baka ji haushi ba?" Baba Hadir ya rubuta masa.
"Ko kadan dan uwa. Major Mustapha da iyalinsa sunfi karfin haka a wurinmu kaima ka sani. Ya kula min da iyali sannan ya kula min da kai. Me zan nema kuma? Maganar yara wannan mukaddari ne idan akwai rabo sai kaga anyi"
"Zayyan" Baba Hadir ya kira sunanshi kawai don jindadin halin abokin nasa.
Dan daure fuska Zayyan yayi "kada ka karar min da suna. Rinka hadawa da wata kalmar don naji dadi"
"Zayyan...fitina" yace yana dariya. [5/22, 11:03 PM] Sis Ruky: Gabadayansa ya bayyana a gabansu kafin muryar ta gama shiga kunnuwansu.
"Daddy, Baba...." Awwab ya soma cewa sai dai tuni Zayyan yayi gaba haka ma Daddy din da Baba sun taso daga wurin zamansu sun tare shi a tsakiyar falon.
"Zzzzayyyannn kaine?" Baba Hadir yace da karfinsa.
Manyan maza magidanta duniya ta sanyasu kuka tamkar yara. A wannan lokacin Hadir ne tsaye a gaban Zayyan dinsa. Hannuwansa yasa yana shafa shi kafin su kankame juna.
Major da ya tabbata ba mafarki ne ba ya ware hannuwansa ya rungume su su duka biyun a tare yana nasa hawayen. Excellency ma nasa yake yi a gefe yana jinjina karfin soyayyar wadannan mutane.
Duk abinda suke yi Mairama tana zaune kamar an dasata ta kasa motsi. Tana iya jiyo kukan Mami da Mama sama sama ita kuwa ta kasa. Wai shin ta cigaba da zama ne a wurin tana kallon Sojanta ko kuwa ta tashi itama taje ta rungume shi ko sau daya ne kafin ta farka daga wannan daddadan mafarki. Tunda take mafarkin Zayyan bata taba irin wannan da zata gansu a wuri daya duka tare ba. Ina ma Radhiya da Emzee zasu shigo suma su karasa cike mata mafarkin.
Tayi nisa a wannan tunani bata san Zayyan ya iso gabanta ya duka ba. Hannuwanta da ya rike masu laushi wani irin shock yaji na soyayya, tausayi da girmamawa a gareta da ta dauki shekaru ashirin da biyu tana dakon soyayyarsa bata yi aure ba. Runtse idanu tayi tana ayyana da gaske ne haka Zayyan zai dawo mata duk ya rame? Ashe kuwa zata dauki lokaci wurin ganin ta ciyar dashi duk abinda zai taimaka ya sake gina masa jiki.
Rikon da yayiwa hannunta da kakkarfan hannunsa sai kuma yatsansa da yasa yana kore mata hawayen dake gudana a fuskarta batare da ta sani ba shine ya sanyata dawo cikin hayyacinta daga tunanin da tayi zurfi tana yi. Tsigar jikinta ke tashi a lokacin da Zayyan ya mikar da ita tsaye ya dora hannuwansa akan kafadunta yana tayata kukan.
"Wai kuka zamuyi ta yi ne? Bazaki yiwa mijinki barka da dawowa ba?" Yayi maganar kamar baya so saboda shaukin dake dibarsa.
Wani hawayen ta matse ta hanyar runtse idanunta sannan ta budesu ta kalle shi da kyau wani abu yana sauka a kahon zuciyarta. A hankali ta daga hannunta daya ta shafa kumatunsa da wahala ta ramar.
"Ashe ba mafarki nake yi ba" tace lokaci guda ta sulale a jikinsa ta fadi sumammiya.
"Fillo" ya kira sunanta hankalinsa a tashe. Mama ta daure tace ya kwantar da hankalinsa abin ne yayi mata yawa. Ita kuma Mami ta samo ruwa a kitchen.
Ana shafa mata ta bude idanu suka sauka acikin na Zayyan.
"Da gaske ba mafarki nake yi ba?" Hawaye na gudana a idanunta take yi masa wannan tambaya.
"Nima tsoro nake kada a tasheni daga bacci"
"Ina ka tafi ka barni?" Tace tana fashewa da wani irin kuka.
"Wurin da ko makiyina bana fatan yaje. Kiyi hakuri Fillo na aureki na barki cikin..."
Kai ta shiga kadawa tana daga zaune akan kujerar da aka kwantar da ita da ta suma "kada kace komai sai godiyar Allah"
Sun bawa kowa na wurin tausayi. Major ya katse maganar tasu saboda kada aji kunya gasu a wurin ga Awwab da yake ta aikin share kwalla ya zama a koke.
Zayyan ya dago ya sake kallonsu yana fitar da murmushin mai karawa fuskarsa annuri. Ya tambayi Awwab "ina kannenka?"
Da sauri ya nemi nambar Zahra tana dauka yace su zo su duka falon Ummi anyi bako. Duka suka taho harda Raji. Baby Zayyan yana kafadar yayansa Ibrahim wanda Allah Ya sanyawa kaunarsa daga haduwarsu jiya.
Daya bayan daya suka shigo falon. Kowa na zaune banda Awwab da yake daga gefen kofa sai kuma wani dogon mutum da suna fara shigowa ya tashi yana murmushi.
Awwab yace da kannen nasa da dan karfi "introduce yourselves"
Radhiya ta juyo suka hada ido ta kawar da kai ita tana fushi kuma a ranta bata da niyar fadin nata sunan.
Fauziyya ce ta farko ta matso gabansa zata gaishe shi ya mika hannu ya karbi Jawad "Fauziyya?"
Tayi mamaki har ya nuna a idanunta. Shi kuwa ya tuna ta ne kasancewar duka 'ya'yan Major ita kadai ya sani fara sauran duka wankan tawarda suke.
Yaronta ya bata saboda ganin wani da yayi a hannun ta kusa da ita ya karbe shi shima "Zahra?"
Duk da bata sanshi ba taji dadi ko waye wannan mutumin mai kwarjini itama ya santa.
Wani jaririn ya kuma gani a hannun wani matashi da babu tantama kamanni sun nuna dan Zainab da Hadir ne. Kafin ya ambaci sunansa Ibrahim yana murmushi tare da mika masa yaron yace cikin alfahari "Ibrahim Hadir da Zayyan Hadir"
Zayyan ya juya ya kalli Hadir ya yi murmushi sannan ya bashi yaron. Wata 'yar budurwa ya gani ta kusa da wadda yake kallo tun shigowarsu wato Radhiya ta turo ta gaba ita kuma sai kunya take ji ya dan rage tsayi "kema in daukeki ne?"
'Yan uwanta ta kalla ta dan marairaice a kunyace "a'a nima ka fadi sunana"
Ibrahim ya girgiza kai, ashe bata dena shagwaba ba. Ji yadda take tale baki ita da ta gama secondary.
"Kiyi hakuri ki fada min da kanki inyi miki babbar kyauta"
"Zayyanatu Mustapha" tace saboda taji Ibrahim ma ya fadi harda sunan babansu.
Baki bude Zayyan ya kalli Major da ya kafe shi da ido kamar idan ya rufe zai bude ya neme shi ya rasa.
Emzee ne ya rage a gabansa. Yaron tunda suka shigo yake ta kallon wannan mutumi yana tunanin a ina ya taba ganin fuska shigen wannan. Kallon kallo suke yi Zayyan yana jin kamar yana kallon younger version dinsa ne. Ashe Radhiya ma ta soma tunanin inda tasan fuskar ita da ta haddace kamanin mahaifinta a hoto.
Emzee ya bude baki kenan ta matso da sauri tana jin jikinta yana rawa. Tunda suka shigo ya gama gane wacece dinsa shiyasa ma ya bar yi mata magana sai a karshe.
"Kamar na san ka wallahi" tace muryarta a kasa kamar mai rada.
Hannu yasa ya janyota gabansa sosai ta tsare shi da manyan idanunta "Alheran Radhiya baki gane Daadaa ba?"
"Ya Allah" ta furta a gigice ta rungume shi tana kuka mai sauti. Bayanta kawai yake shafawa yana kokarin mayar da nasa hawayen.
"Ehemm..ni sunana..." Emzee yayi gyaran murya shima yau dauriya ta kare sai hawaye "Muhammad Zayyan Tureta"
Haba...koda yaji wannan yaro zuciyarsa ta bashi cewa jininsa ne. Sakin Radhiya yayi hawayen da yake kokarin kada ya zubar a gaban 'ya'ya suka fito suka rungume juna cikin farinciki suna kuka. Zayyan ya dago yana ta shafa fuskar Emzee wai wannan ma nasa ne.
"Kafi jindadin ganinsa a kaina ko?" Yaji Radhiya tace a raunane tana kara karyar masa da zuciya.
"A'a Alheran" yace yana sakin Emzee ya sake rungumeta.
"Kenan ni bakayi murnar ganina ba?" Shima Emzee yace yana jin haushin tayi masa kauron jin dumin babansa ya koma wurinta.
Zayyan sai ya rikice yana soma cewa "ba haka bane" ya ga Alheran ta kafe shi da ido shima Emzee ya tsaya yana jiran amsarsa.
Dariya suka ji daga bayansu. Falon da ake ta kuka ma'abota cikinsa sun koma dariyar wannan haduwa ta uba da 'ya'yansa. Hadasu yayi kowanne a bari daya ya rungumesu kamar za'a kwace masa su
**********
Kowa yana son jin yadda ta kasance dashi su duka suna zaune a falon. Emzee da Radhiya kusan danne masa kafafu suka yi kowannensu yana so ya rabi jikinsa.
Dagawa yayi suka hada ido da Ummi da take ta kallonsa sai taji kunya sosai ta kama ta. Major ne yayi gyaran murya yace a yiwa Annabi SAW salati. A tare suke yi da karfi suka karanta Fatiha, Ayatul Kursiyyu da Amanar Rasul sannan ya dade yana jan su da addu'a duka domin godiya ga Allah SWT.
"Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah...wannan rana ce da bazamu taba mantawa da ita ba har mu bar duniya. Amma kafin mu zauna jin yadda al'amura suka kasance Zayyan ka zauna kaci abinci ka huta. Ku kuma kowa ya tashi mu bashi wuri ya huta"
Dukkaninsu suka fita Ummi ta tashi tayi kitchen tana godewa dabara irin ta Mama aka bar Zayyan da 'ya'yansa an rasa wanda zai fara tashi cikinsu.
Emzee yasan ya kamata su tashi amma Radhiya ita ta ga wurin kwana. Kallon babanta kawai take yi tana cewa Daadaa yana amsawa da murmushi. Ta kira yafi sau goma bai gajiya da amsawa.
"Emzee kuma wai nan ba mafarki nake yi ba ko?" Tace tana lumshe ido tana sake budewa a kansa.
"Ko in mintsineki ne?"
"A gabana Zayyan?"
Wani dadi yaji ya kama shi mahaifinsa ga kira sunansa da sunan raba gardama tsakaninsa da Addarsa. Kai wannan abu da me zai kwatanta shi. Muryar Umminsu suka ji tana cewa "in fara kawo maka abinci ko tea?"
"Duk wanda kika kawo zanci Fillo. Saboda jiran abincinki rabona da saka wani abu a bakina tun safiyar jiya"
Wai da irin dabarar nan Emzee sai ya yiwa yayarsa alama da ta tashi su ma su fita. Shiru bata gane rangwada kan da yake yi ba sai da yace "Adda taso muje muma Daada yaci abinci"
Hannunsa da ya riko nata ta ture "kai kyaleni ka tafi idan kana so. Ni ban gaji da ganinsa ba." Matsowa ta sake yi jikin kafar Zayyan tana murmushi "Daada na chanja kama daga yadda ka sanni ko?"
"Kin koma tamkar Innata"
"Bani labarinta"
Emzee sai ya shiga kada kai. Idan abin Addarsa ya motsa fa bata dogon tunani. Yanzu ace daga dawowarsa zai fara bata labari. Ita kuma neman abinda zai zaunar da ita wurinsa take yi kada ta tashi ta dawo ace ya koma inda ya fito.
"Kin yiwa Hamma Awwab godiya ne? Dashi aka je dauko Daada fa naji Mama tana fada"
An tuno mata da Hammanta sai ta tashi tana murmushi "Daada bari naje na dawo kafin nan kaci abincin"
"Sai kun dawo Alheran"
Wani abin ta tuno zata taambayeshi Emzee ya turata waje ta karfi ya rufe kofar.
Ummi tana ajiye tray a gaban Mijinta taji gabanta ya fadi da aka rufe kofar ga kunya kamar wata sabuwar amarya.
Dariya taji Zayyan yayi yana kallon kofar "ina kika samo min wadannan yaran Fillo? Nan fa dabara yayi mata don su bamu wuri"
Sai da tayi murmushi yaji zuciyarsa tana kadawa da tasowar dadaddiyar soyayyarta tace "sakamakon tureni da Tureta yayi ne" ya sake yin dariya.
Ta gama ajiye komai a gabansa zata fara zuba masa tea din domin ya gasa cikinsa ya riko hannunta bai zaunar da ita ko ina ba sai cinyarsa. Kunya matsananciya ta kama ta yayi mata wani irin riko da yaji tana neman tashi. Rungume tayi ya dora kansa a tsakiyar kirjinta. A hankali taji hawayensa yana jika mata gaban riga. Tallabo shi tayi ta sake rike shi itama nata hawayen yana sauka a kansa da ya cire hularsa.
Sunyi kusan minti biyar a haka sai ajiyar zuciya kawai da take yi. Da taji yana neman dago kansa ne ta sassauta rikon "ga tea ka fara sha sai na zuba maka tuwo"
Bai bata damar tashi ba sai lebbanta da ya shiga zanawa da karamin yatsansa ya soma magana a hankali "ban taba dena sonki ba Mairama, ban manta ki ba da kyautatawarki gareni. Idan kunci yayi min yawa sai na cika zuciyata da ranar da na fara kamaki kin saci mirinda"
Murmushi tayi mai hade da hawaye shi kuwa ya cigaba da abinda yake yi "a duk lokacin da zan ganmu cikin wannan yanayin nasan mafarki ne wanda nake kwadayin cikarsa idan mun hadu a aljannah. Ashe zan sake ganinki matata. Ashe da rabon na sake samun kaina cikin farincikin zama miji a gareki..." hannu yasa yayo kasa da kanta daidai fuskarsa "ban sani ba ko na manta ko zan iya tunawa"
"Me?" Ta tambayeshi gabanta yana lugude wai yau ita ce tare da Zayyan.
"Wannan" ya karasa fada da hade lebenshi da nata. Lumshe idanu kawai suka yi kowannensu hawayen farincikin cikar buri yana saukowa daga idonsa suka sake rungume juna tightly.
**********
Gidan Mami suka tafi saboda Emzee ya hango shigar bakon da suka zo da su Awwab din Mama yasan manyan nasu can suka je. Ilai kuwa sun taru can dinne Excellency ya gabatar musu da Chibuzor wanda ya fada musu sanadin haduwarsu da Zayyan. Wannan ake kira al'ajabi su Major sun koka sun murmusa sun dara duk a lokaci guda. Yayin da matansu suke dakin Mama su ma suna nasu mamakin.
A gidan Mami suma a falo aka baje hirar murna ta kaure sun saka Awwab a gaba sai ya fada musu yaya akayi.
"I am exhausted ku bari ayi komai a tsanake"
Sallamar Radhiya yaji ya dago idanunsa da suka soma ja saboda muguwar gajiya da yunwa. Jin kansa yake kamar yana yawo a iska babu kuzari ko kadan.
Emzee ne a gaba ko da ya shigo kai tsaye yaje ya rungume shi.
"Allah Ya baka abinda kake so duniya da lahira Hamma. Thank you"
"Kada kayi min kuka dai bani da karfin rarrashinka" Awwab ya zolaye shi.
Yana sake kallon Radhiya sai ga nata hawayen kamar famfo ya tashi da sauri. Wani irin sonsa take ji ta kuma rasa da wace kalma zatayi amfani domin ya gane girman farincikin da ya saka ta a ciki. Kofa ya nuna mata dama ko zama batayi ba ta fita yana take mata baya suna jin shakiyancin Ibrahim da Raji wai love is in the air.