Kenza eBookz

Batuol mamman complete novel - Chapter 45

Batuol mamman complete novel - Chapter 45

Batuol mamman complete novel Chapter 45: Batuol mamman complete novel Chapter 45. Wurin tsayuwa yake nema inda zasu samu su kadaice babu yayi gajeren…

3,325 words

Wurin tsayuwa yake nema inda zasu samu su kadaice babu yayi gajeren tsaki. Da sunyi aure fa shikenan duk inda yaso zai kaita. Yanzu anbi an cika ko ina an hana mutane sakewa. Ta kula da yadda yake ta kalle kalle tayi murmushi.

"Hammana"

Dama ya lafiyar kura. Ya gaji tilis wannan kira da tayi masa yasa zuciya da gangar jikinsa duka amsawa.

"Nagod..."

"Shhhhh kada ma ki fara. Idan kina da wani abin cewa dai ki fada"

Idanunta fal kwalla tace "ni me zan ce Hamma"

"Ni ina da abin fada Alheran." Da wata irin siga mai shiga rai yake kara hargitsa ta da muryarsa "I am not a soldier kuma bani da zuciyar da zan taba zama. Kuma ni ba likita bane, bana jurar ganin jini....But I love you so much kin hana min nutsuwa tun daga ranar da na fara ganinki"

Kifta ido kawai tayi hawayenta ya sauko "nima haka Hammana"

Ya ce "wayo ko?" Sunkuyar da kanta tayi tana murmushi "ina fata kin shirya aurena yanzu?"

Ba shiri ta rufe fuskarta da gefen mayafi tana neman komawa gidan Mami.

Marairaicewa yayi sosai ya koma kalar tausayi ya shagwabe mata yadda take yi ita ma "Come ooon na gaji fa. I need a wife, a friend....uhummm.... I need you."

Murmushi take yi sosai ta kasa dagowa ta kalle shi ma. Ya duka saitin fuskarta yana neman hada ido da ita tana kaucewa "kin gani ba, ba don kin mayar dani gwauron dole ba da yanzu I have Alheran to hug when I am happy or sad. My Schatzi to kiss when love is in the air right?"

Gabadaya ta rikice masa ta ma kasa gudun ta barshi shi kadai yake ta zuba hirarsa.

"Kinsan me? I am so tired ga yunwa. Mu koma ciki?"

Tausayinsa taji kana ganinsa kasan a gajiye yake sosai kuwa.

"Muje na zuba maka"

"Baki bani amsa ba fa. Na dage ina ta debo zance duk don na burgeki"

Ya bata dariya ta gama kayarta sannan tace "I am all yours Hammana kai nake jira tuntuni"

Amsar tayi masa dadi suka shiga falon tare. Babu kowa su Zahra sun shige dakin Mami su Ibrahim suna dakin Awwab. Zama yayi akan doguwar kujera ta wuce kitchen zuba masa abinci. Akan tray ta hado komai ta dawo sai dai me...Awwab ya mike abinsa wani nannauyan bacci yayi awon gaba dashi abin tausayi. Kallonsa tayi tana jin soyayyarsa tana dada zama sabuwa a zuciyarta.

***********

A kasa Mairama ta zauna Zayyan yana jingine da kujera ta saka plate din abincin a tsakaninsu sannan ta tashi.

"Ina zaki?"

"Hannu zan wanke" ta amsa tana sunkuyar da kai saboda tunanin abinda yayi mata mintuna kadan da suka wuce. Tasowa yayi shima yace zai wanke nasa hannun.

"Yi zamanka ina zuwa"

Bata dade ba ta dawo yayi zaton ruwa zata kawo masa a roba na wanke hannu sai gani yayi ta zauna ta debo tuwon ta kawo bakinsa.

Yau kam bashi da karfin zuciya ko kadan. Yau daya dai a Zayyan mijin Mairama yake wanda ya kwashi dimbin shekaru yana muradin sake ganinta ko da daga nesa ne. Hannun nata ya kama ya karasa dashi bakinsa.

"Ashe haka tuwo yake da dadi muka rinka cewa bama so da muna yara" taji yace ta soma dariya ya fara bin yatsunta daya bayan daya yana sudewa.

Fillo sarkin kunya sai ta kasa kara diban wani ta bashi. Ya sanya hannu ya dago kanta idanunta a rufe "alfarma nake nema Fillo"

"Babu alfarma a tsakaninmu kaima ka sani"

"Yau daya don Allah ki tattaro duka kunyar nan ko Alheran ce ki bawa ajiya. Mairama kadai nake bukata in nuna mata yadda shekaru ashirin da biyu suka galabaitar da Sojanta" [5/22, 11:03 PM] Sis Ruky: 'Ya'yan nasu sun hadu a falon Ummi kowa na bawa Daada labarin kansa musamman game da karatu shi kuma yana rike da Daada Karami. Radhiya ta kalli yaron ya kurawa babanta ido tayi murmushi tana tambayar Mami da suke shigowa tare da Mama suna neman wucewa dakin Ummi wai yaushe zasu yi taron sunansa ne.

Mama ce ta bata amsa "babu wani taro fa Radhiya tunda babansa ya dawo me kuma zai bukata? Masu tahowa dai zasu zo amma barka kawai"

"Yaya zaki yi mana haka babu shawara Zainab?" Cewar Mami tana nuna mata rashin jindadi.

"Ni da dana zata yi min karfa karfa to wallahi ban yarda ba" inji Ummi tana goyon bayan Mami.

Zayyan ya daga hannu kamar dan makaranta "idan kun bani dama in raba gardama?"

"Mun baka" Mama tace da sauri tana neman tsira. Da Baba Hadir suka yi shawarar soke taron kawai kwanaki sun kara ja kuma ma dai dawowar Zayyan ita ce abu mafin dadi garesu.

Kallon iyalan nasu yayi yana jin tamkar Allah Ya bashi fiye da abinda yake nema a duniya. Major da Hadir harda Baban Arifah da ya sadaukar da rayuwarsa dominsu batare da tunanin ko kadan zasu saka masa ba gashi sun rike masa iyali da gaskiya. Idan ya biyewa zuciyarsa kuka zai yi musu daga su har matan kwarai da suke aure wadanda suka karfafa musu gwiwa wajen dabbaka zumunci a bayan idonsa. Shi ba butulu bane da zai manta Mami Hassana wadda mijinta Major da Ummi suka bashi labarin cewa aikatau tayi a Germany domin ciyar da iyalinta amma a cikin abinda take samu Major ya rinka cire wani abu kafin ya fara aiki yana aikowa matarsa Mairama. Babu wanda baiyi masa ba amma Allah Ya sani yana jin girman Mami sosai a zuciyarsa. Daga ita har Mama Zainab sun wuce matan abokai a gareshi sai dai ya kira su 'yan uwa. Sun burge shi matuka yadda suka tsayawa juna a matsayinsu na matan sojoji suke kokarin rufawa juna asiri. Ba don a gidan iyayensa an bar kari tun ran tubani ba ai da kamata yayi ace ya dawo ya sami matarsa a tsakiyar matan su Badaru. Abin takaici shine sun tashi babu wannan shakuwar tsakaninsa da 'yan uwansa maza da mata. Jume tun kuruciya ta koya musu tsanarsa a matsayin dan kishiya. Sai dai yaji dadi da Mairama ta fada masa yanzu kam idan ka cire Maikudi tsakaninsu da sauran musamman 'ya'ya da jikokin Mal Aminu abokin babansa sai dai hamdala. Ita ma a nata bangaren rashin shakuwa da 'yan uwanta da kuma rashin tsayuwar uba akan 'ya'yansa ya sake bata lamura. Da ace zumuncin nasu mai karfi ne ya tabbatar ko a daji iyalinsa suke bazasu wahala ba. Duka rayuwar Mairama bayan tafiyarsa ai a cikin gidan mahaifinta tayi kafin ta koma Rugar Barkindo amma rashin wannan zumuncin ya sa ita da wadda bata tare da ahalinta kusan daya.

"Daada" Radhiya ta dan taba shi saboda nisa da ya soma yi a tunani.

Murmushi yayi a lokacin Awwab, Daddy da Baba Hadir suka shigo su ma yace "indai na isa to na soke taron sunan"

"Kai da danka Daada waye zai hanaka abinda kake so" Mama tace tana murmushi.

Sauran kuwa da gaske sunyi mamaki harda Ummi kuwa. Sai dai abinda yace ya sanya su wani irin farinciki a take.

"A iya sanina Zayyan kaima ba'ayi taron sunanka ba ko" ya kalli Emzee da suke zaune kusa da juna shi da Ibrahim tamkar tagwaye. Dariya yayi yana zaro idanu "Daada ba dai cewa zaka yi a nade ni a shawl a koma baya ba"

Ai kuwa falon ya kaure da dariyar yadda yayi har ya tashi zai bar musu falon da Ibrahim yace "irin jaririn samudawan nan kawai zaka koma".

"Dawo ka zauna in karasa...Zayyanatun Daada kema ba'ayi miki suna ba"

Zayyana sai ta rasa inda zata saka kanta don dadi Zayyan ya fasa mata kai yace ita tashi ce. Ibrahim ya dan kalleta yadda take dariya ta tashi ta koma kusa da Zayyan ta zauna tana narkewa "Daada ba'ayi min ba, ko kayan barka fa bana jin an kawo"

"Kiji tsoron Allah" Mami tace tana dariya.

"Ai kuwa duk wanda bai kawo ba muna binsa bashi. Su Ummi da Mama kowa ta kwance bakin jaka"

Anata dariya ta hada ido da Ibrahim wanda ya kasa gane mata tun ranar da yayi maganar tale baki. Abin ya dame shi sosai ya kasa fadawa Emzee. Yanzu suna hada ido yayi murmushi ita kuwa ta murguda masa baki ta kawar da kai, babu wanda ya kula sai shi.

Zayyan ya dago Daada Karami "kaima bakon duniya nazo na tare hanya ba'ayi maka taro an kawo kayan barka ba. Saboda haka in sha Allahu za'ayi taro na musamman idan komai ya natsa na Zayyan, Zayyan, Zayyanatu da Zayyan."

Hayaniyar murnar da suka cika falon da ita ba arziki Mami tace su tashi su fita. Zayyan ya yafito Awwab da hannu. Tun shigowarsa dama baiyi magana ba sai ma dukufa da yayi yiwa abokin aikinsa text akan abinda zasu yi idan ya koma.

"Idan an gama suna sai mu fara shirin bikin dana. Kunyi min komai daidai amma an bar min yaro ba aure. To mu dai yarinya ko 'yar waye tunda yana so idan ta kama na sato ta ne zanyi na kawo maka kaji ko"

Idanu suka koma kansu shi da Radhiya lokacin suna rige rigen arcewa daga falon. Shi hanyar waje yayi ita kuma tayi kitchen. Su Major ma sai da suka yi dariya.

"Kunga kama kai, yanzu don Allah waye yaji na ambaci suna?"

Da dariya suka fita harda ta kitchen ita ce karshen tafiya. Major yace masa ya fara tara jikoki ya kamata ya rage chalikanci.

"Idan na dena so kake su rinka guduna? Kuma dai shekarata nawa ina danne Zayyan Tureta ta karfin tsiya. Yanzu kuwa lokaci yayi da zai fito yayi kara'i"

"Aiki ya sameki kanwata kiyi a hankali kada mu fara ganinsa da kitso da dankunne irin na matasan zamani" Baba Hadir ya rubuta ya mikawa Mama ta bata.

Zayyan yana ganin tana dariya yace sai ya gani. Daga nan dai hirarsu ce da bata karewa suka dasa. Sai sakon text Alh Salisu ya yiwa Baba Hadir zai zo suyi sallama gobe zasu koma Kano da yaran. Ya kara da dan korafin wai ko basu hakura bane yana ta sa ran zuwansu gidansa ko su ko yaransu amma shiru. Baba Hadir sai yaji babu dadi ya mikawa Daddy wayar. Kiransa Daddy yayi bayan sun gaisa yace

"Hadir yana mai baka hakurin rashin zuwan nasa. Wani abu ne ya taso amma idan babu takura kuma kana da lokaci kafin ka tafi goben me zai hana ka shigo ka ga uzurin nasa?"

"To Allah Ya nuna mana Yasa lafiya. A gaida yaran don Allah"

Da haka suka yi sallama. Matan na daki suna tsokanar Ummi amarya babu lalle babu gyaran gashi ta ce laifinsu ne. Mama tace ba don jego ba da idan ta fara gyarata sai sun biya mata Hajji da Umra.

"Ni dai naga ranar da zaki girma Zainabu. Ina jin halinku ne Sakkwatawan nan. Daga ke har Zayyan sai ku sa cikin mutum ciwo da ban dariya."

"Cewa zakiyi suyi abu su daure fuska ki rantse ba daga bakinsu magana ta fito ba" Ummi ta fada da dariya.

"Baki ji ba wai zai satowa Awwab Radhiya ya kai masa ita. Uban amarya zai saki layi."

Kowacce ka gani tana cikin walwala da annashuwa suna jindadin zama da juna sai fatan Allah Ya kade shaidanu Ya kara hada kawunansu.

**********

Tun dawowar Zayyan yau ce rana ta farko da su ka kebe su kwadai da 'ya'yansu a bangaren Ummi. Ba kowa ne da wannan tunanin ba kuwa sai Mama Zainab. Bayan sun fita ta tura musu Radhiya da Emzee da sunan su je ko babansu yana son hira dasu. Babu wani boye boye tace ya kamata su bashi lokaci yaji matsaloli da cigaban rayuwarsu kamar yadda kowane uba yake yi. Radhiya taji kunya sosai ganin da su Zahra a wurin. Amma sai ta kula babu wadda abin ya dama sai ma goyon baya da su ka baiwa Mama aka korasu yau su kwana a gidansu.

Ummi da Radhiya ne suka yi girki yayin da Zayyan yake sake jin daukakar da Emzee yake samu a NDA tun shekararsa ta farko. Ya yaba kwarai da dan nasa yana jinjinawa a ransa wannan wai magajinsa ne wanda bai barshi ta ko ina ba...suna da aiki.

A kasa Radhiya ta ajiye musu abincin Zayyan yace ta dauko babban plate yau a kwano daya zasu ci ya ga girman lomar kowa. Da dariya aka soma ci sai gashi su hudun sun buge da zubar hawaye lokacin da ya kallesu daya bayan daya yace "ko yanzu mutuwa ta riskeni zan tafi ina mai farinciki da cika godiyata ga Allah."

Ummi ce ta fara hawaye sai Radhiya ta kama harda shessheka. Emzee ma duk dauriyarsa sai da yayi "don Allah ni dai a dena kukan nan abincin da dadi amma zaku sa ya fita daga raina"

Dundu Ummi ta kai masa "acicin kawai"

"Zancen gaskiya Ummi. Ba abin nayi fuska na gama ci sannan nayi nawa kukan ba na rasa me tayani"

"Ashe haka kake Zayyan? Shiyasa Malamijo yace yana nemanka kaje da bindiga ko ta katako ce"

"Nemana kuma Daada?"

Ummi ta amshe da fada musu sakonsa na dazu "sai ku shirya zamu tafi tare. Zamu barku a can mu wuce Sakkwato daga can muje Nijar"

Radhiya ta rike baki "Ummi wai ni din da gaske yace ko dai kin fada ne kawai don kada nace baya sona"

"Kaniyarki" ta kai mata duka Zayyan ya tare yana cewa babu mai taba masa uwa.

"Da gaske nake Daada, cewa fa yake yi idan yaji muryata gabansa faduwa yake yi" ta turo baki da takaici.

"Gonarsa take zuwa tace wai dabba ta kasa tasa a yanka. Ka kuma sanshi da dabbobinsa sarai" Ummi tace tana murmushi.

"Amma anya lafiya kuwa yake nemanmu?" Emzee yaji abin ya daure masa kai. Malamijo fa ko waya baya kiran kowa sai dai a kira shi.

Kowa da tunaninsa amma sunfi kawowa da gaske akwai matsala. Ko ma dai meye jibi da wurwuri zasu bar Abuja. Gara suyi su dawo da wuri Radhiya ta fara aikinta. Zayyan yaji dadin wannan program da zata yi yace idan tana bukatar bayani game da halin da sojojin suke riskar kawunansu a filin daga a shirye yake. Basu ankara ba suna wannan hira sai gani suka yi daya da rabi na dare. Dole aka tashi ba don sun so ba saboda hirar tayi musu dadi. Suna jindadin yadda iyayensu ke zolayar juna. Ummi tace mijinta dan saurayi ne wanda ya tafi yanzu an kawo mata wanda ya fara furfura.

Zayyan yace "ko kiyi shiru ko na tona miki asiri su san cewa a wurin bin kwalaben mutane a gidan biki kina shanye ragowar mirinda muka hadu"

"Bonono rufe kofa da barawo...ai ka gama tonawa"

Emzee da Radhiya dariya harda hawaye. A zahiri idan kewarsa ta ishi Mairama tana bawa yaranta wannan labari amma yadda ya fada yana kwatanta yadda tayi da ya kamata dole suyi dariya. It was a time well spent a tsakaninsu.

**********

"Ikon Allah jama'a dama Zayyan yana da dan uwa da suke mugun kama banda wadda na gani a wurin Zayyan karami?" Alh Salisu yayi magana a lokacin da suke shiga gidan Baba Hadir shi da yaransa ya kasa dauke ido daga kallon Zayyan din.

"Nine dai Salisu ba kama bace"

Gabansa yaji yayi wata irin faduwa ya shiga kallonsu yana jira wani yace wasa suke yi amma shiru kake ji. Radhiya ce tayi dabarar kiran su Halifa da kannensa su ka bita wurin Ummi.

Zayyan tasowa yayi ya kama hannun Alh Salisu wanda jikinsa ya fara rawa sai kuma ya soma hawaye "kai din ne don Allah? Hadir Zayyan nake gani. La ilaha illallahu....Zayyan dai nake gani."

"Nine Salisu Allah Ya dawo dani"

Mamaki da al'ajabi ne ya kama shi sosai da aka yi masa bayanin dawowar Zayyan. Wannan al'amari da daure kai yake.

"Gashi a hanya muke ina da taro gobe da sassafe na 'yan kasuwa. Don Allah ku tsaya a gidana idan kun shigo goben." Ita ce abinda ya fada musu karshe lokacin da suka gama hira ya tashi.

Aka tura kiran yaran sai ga Halifa tare da Emzee yace a tafi a barshi zasu taho gobe in sha Allahu shima yana son zuwa Sumailan. Alh Salisu yace babu matsala a turo 'yan matan. Kusan minti goma suna jiransu suka taho da Zayyana za'a rokawa Hibbah itama ta kwana.

Yayi dariya "Kuna tsareni da ido na isa na hana ne"

Kananan ma sai suka hau rigima saboda kaunarsu dasu Jawad da Femi.

"A'a kuma kada abin yayi yawa. Ku wuce muje su ma zasu taho gobe"

"Ka kyalesu mana nan da can duka gida ne. Dama su Alheran zamu ajiye a Sumaila mu Kanon zamu kwana sai a kawo su gida"

Alh Salisu yaji dadi da Zayyan bai nuna fushinsa ba da ya fada masa laifinsa na rashin kula masa da iyali. Dreban motar yaran ya roka arzikin ya koma can gidan nasa ya kwana gobe sai yazo su tafi shi kuma ya shiga mota suka tafi.

Ga alamu Halifa ya damu kwarai da Radhiya komai ya kira ta ko ya sakota a ciki. Yanzu ma hira suke yi take tambayarsa yaushe rabonsa da zuwa wurin Malamijo yace ya dade sosai.

"Gaskiya kazo muje ka ganshi. Kila ma har Gwaggo Salame ba ka zuwa gidanta ko?" Ta dan dage gira.

"Bazan miki karya ba ita ma bana zuwa yadda ya dace da ya ziyarci mahaifiyarsa. Gidan nata ne ko hadiyar yawu bana iyawa ga yaran nan nata ko sunayensu ban rike ba sai azabar roko"

Dan bata rai tayi "ba cikinku daya ba Halifa, ko zaka so ace wani bare suke roko? Wai kuwa ina dayar nan bana rike sunanta"

"Rahima? Tana can nasu gidan" yace da rashin damuwa.

"Ni kuwa da zaka gyara zumuncinku da ka burgeni. Dube ku duk bamu saba da juna ba haka su Ummi ma. Ita da Gwaggo Salame ban san yaushe suka hadu karshe ba"

"Ke Ummanmu ko gidan Malamijo bata zuwa in fada miki."

Yanayin zumuncin nasu baiyi mata dadi ba. Shi kuma da yake babba a nasu gidan sai taji ya kamata ta bashi shawarar gyara tsakaninsa da kannensa. Ko ba komai yana cikin rufin asiri zai kyautu ya rinka dan taimaka musu. Sunyi nisa suna tattaunawa Awwab ya shigo yaci karo dasu suna dariya hira tayi dadi. Tuni fuskarsa ta chanja ya koma ya kira wayarta. Tana dauka fito kawai yace ta tashi.

A bakin mota ta ganshi ya jingina bayansa ya harde kafafunsa da hannuwa a kirgi.

"Sannu da hira" yace fuska babu fara'a.

"Hira kuma?"

"Ba ita kike yi ba na taso ki"

Duka girarta biyu ta rinka dagewa tana wani juya masa ido da dariya "Chèri kishi kake yi? Oh my, my , my sai naji na koma wata sarauniya"

Sakin baki yayi ya kalleta kafin ya girgiza kai "mutum ma baza'a barshi ya nuna bacin ransa ba"

Kashe masa ido tayi tace "no chance baby" Wani irin kallo ya bita dashi ta tsure "kasan Allah subutar baki ne ba baby zan ce ba"

"Ah kawai kice kin girma. Daga fara saka min sunaye nan gaba ni din zaki dauke"

Kamar tayi masa kuka ta sake cewa fitowa yayi kawai.

"Saboda shine a ranki ko? Kinji me Daada yace dai ki fara hada kayanki"

Dagewa tayi bisa subutar baki ne shi kuma yayo ta zolayarta sai gashi sun koma hirarsu mai dadi.

"Please ni dai bana son yadda yaron nan yake shige miki. Nasan dan uwanki ne bazan rabaku amma ni dai a kula kinji ko. Ina kishinki sosai Schatzi"

"In sha Allah Cheri amma nima fa kada kaje kana yiwa 'yan matan jirgin nan masu dan skirt dariya wallahi. If not za ka ganni a mafarki muna fada"

"Naji...kuma banda zuwa rugar Barkindo ki rinka zuwa hira wurin Dr Zakari. Nasanki da likitoci ba sauki"

Dariya ya bata sosai. Ita sai yanzu ta gane ashe lab attendant ne ba likita ba "ka doke kowa fa ni sai dreba ko ba abin hawa"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull