Kenza eBookz

Batuol mamman complete novel - Chapter 47

Batuol mamman complete novel - Chapter 47

Batuol mamman complete novel Chapter 47: Batuol mamman complete novel Chapter 47. Hannu ta kai ta mangareta "rufe min baki zaki fara sakin karya yadda…

3,375 words

Hannu ta kai ta mangareta "rufe min baki zaki fara sakin karya yadda ubanki yake yi. Kina sana'ar yin kunshi amma 'yar kazar nan ko ki dan kullo kudin ki bani domin saka albarka ya gagara. Kinfi ganewa ki bawa matsiyacin babanki ya ciyar da matarsa da 'ya'ya ni da na tsugunna na haifeki ko oho"

Maman Danmama ce ta dago yagaggen labulen dakin ta leko "ke kuwa Salame ki bar yarinyar nan haka mana. Tun shigowarta kin sakata a gaba da bala'i kamar baki san ciwon haihuwarta ba"

Cike da masifa ta dago "ki dai zuba ruwa a kasa ki sha kawai saboda farinciki. To dai duk tsiya tafi Danmama da yake karen mota a tasha"

[5/22, 11:03 PM] Sis Ruky: "Kinci albarkacin 'yarki bazan biye miki ba" Maman Danmama tace tana sakin labulen.

Bata bar wurin ba Halifa yayi sallama. Muryarsa kamar a kan Salame akayi recording tuni ta gano ko waye tace ya shigo. Sai da ta fita ta harari Maman Danmama irin abin nan na danta yazo sannan tace ya shigo ciki. Kannen nasa ma an sabar musu idan sun ganshi sun ga kudi ko abincin kirki shiyasa suna ganinsa suka fara murna zasu rungume shi ya dakatar dasu. Kazamai ne na ajin karshe shi kuma tsaftarsa har taso tayi yawa. Zama ma kasawa yayi dakin wari da zarnin fitsari kawai yake yi. Rahima da kanta ke duke tana sharar kwalla ta dan dago da murmushi don tasan sunan ko da suke dadewa basu hadu ba.

"Yaya Halifa barka da zuwa"

Wata muguwar tsawa Salame ta daka mata "tashi dan ubanki kwadayayiya. Wuce ki tafi gidanku ai kin dubani mun gaisa ko."

Zabura tayi ta mike a gigice saboda yadda ta razana da tsawar tayi hanyar kofa Halifa ya fincikota saboda gefen fuskarta kawai ya gani ya gane kanwarsa ce.

"Rahima" ya furta a hankali yana kallon jajayen idanunta. Yarinyar da kadan ta fi rabinsa. 'Yar karama ce wahalar rayuwa ta tsotseta.

"Cikani" tace wasu hawayen masu zafi na sauko mata ta kwace hannunta ta fita. Ta sani Ummansu bata kaunarta amma yadda take nuna bambanci kirikiri yana kona mata rai. Mahaifinta talaka ne futuk amma yana kaunarta tamkar rai. Amaryarsa da ta fara son azabtar da ita dashi da babarsa suka tashi tsaye akan ko ta rungumeta kamar 'ya ko ta koma inda ta fito. Kudin sana'arta da Salame take sakawa ido har nawa ne? Zuwan karshe gabadaya ta tattara mata kudin ta bayar. Wannan karon kuma a kofar gida taji wani makocinsu yana yiwa babanta tijara akan ya ranta masa kudin da ya biya mata WAEC da zata rubuta a farkon sabuwar shekara bai biya ba. Tilas da fito da kudin ta bashi ya bawa mutumin ba don yaso ba. Abin ko kwana uku ba'ayi ba kuma babu wanda ta yiwa lalle bayan nan bare ta sami na zuwa dubiyar. Yanzu abin takaici zani daga akwati Salame ta dauko za ta shimfidawa Halifa saboda babansa yana da kudi.

Ta soma tafiya kenan Halifa ya risketa ashe ya biyota "Rahima tsaya mana"

Cak ta tsaya amma bata ce masa komai ba. Hannunta ya kama ya dora mata bandir din naira dari bibbiyu sababbi "kiyi hakuri da halin Umma. Ki rike wannan zan zo gidan naku muyi magana kinji ko"

"Nagode" sai dai kudin mika masa tayi yaki karba sai kawai ta ajiye akan wani bulo da yake gefen hanyar irin wanda ake zama a kai tayi gaba abinta tana goge hawaye.

Ko kadan Halifa baiji dadi ba. Sai ya tuna da Radhiya tace shine babba ya kamata ya hade kan kannensa. Idan suka tafi a haka tabbas Salame zata ginasu da kiyayyar juna ne. Kana ganin Rahima kasan tana bukatar taimako amma zuciya irin tata ta sanya bazata kwantar da kai tana roko ba bare aji dadin goranta mata. Idan ruwa kadai babanta zai iya bata tasha in sha Allahu zata yi hakuri dashi bazata gaza ba.

Da yake ana ji dashi ko fadan bin Rahima da yayi bata masa ba sai kudurin ko nawa ya bata sai tasa ta kawo mata.

"Zauna mana mu gaisa ka tsaya"

"Sauri nake yi Umma. Dama munzo da baki ne gidan Malamijo shine nace ko zaki zo ku gaisa"

Fuskarta ta nuna bata ji dadi ba "can kuma ka fara zuwa?"

"Ko shiga banyi ba na taho nan"

"Su waye bakin?"

"Su Gwaggo Mairama ne..."

So tayi ta kwada masa mari sai dai kuma kada ta toshewa kanta kofar ihsani dan abinda zai bata ya fasa.

"Mairaman zanje in gaisar saboda ka raina uwarka? Me ya kaika wurinta har kake cewa tare kuka zo?"

Shi fa irin wadannan abubuwan ke kara nesanta shi da ita.

"Umma tare muka zo daga Abuja kuma ba ita kadai bace"

Tabe baki tayi "wato ka fara shege mata kawai saboda ance tana wani karatun banza a Kano kuma suna zuwa Abuja ko. To bari kaji in fada maka duka kwarewa ne a maula ita da 'ya'yan suke zubar da mutumcinsu a gaban masu kudi. Ni nafi tunanin aikatau take yi"

"Umma ni zan tafi idan bazaki je ba. Na rasa me tayi miki ba kya gajiya da aibata ta. Ga wannan" ya mika mata kudi a cikin envelop da ya riko dominta.

"To muje bari na dauko mayafi" tace a sanyaye bata kaunar batawa yaron nan rai. Iyaka idan taje ta yanka mata kashedi ta dena bibiyar danta ba tare suka haifeshi ba.

Ba wata tafiyar kirki suka yi ba suka iso kofar gidan Salame tana ta hura hanci ita mai da. Sauran kuwa a gida ta barsu har wadda ta yaye idan ta sami abinci ta tafi musu dashi.

Emzee da Ibrahim suna bakin mota suna sauko da kaya suka iso.

"Drama ta barka Halifa" Emzee yace yana dariya.

"Ko me akayi a dawo dashi farko gaskiya"

Salame ta kallesu ta watsar Emzee sau biyu yana cewa Gwaggo Salame ina wuni tayi kamar bata ji ba. Sai yake ya yiwa Ibrahim shima bata amsa shi ba yace wai kila don tana sauri ne bata ji su ba. Ta kai bakin kofa su kuma suna fitowa. Ummi da Daada zasu yiwa rakiya da zasu tafi yanzu. Sai kuma dreban gidan su Halifa shima zai tafi idan sun tashi tafiya Halifa zai kira shi yazo ya tafi dasu.

Gaban Salame wani irin bugu yayi da ta ga Mairama tayi wani irin kyau ta kara haske. Kayan jikinta a hasashen Salame sai kace wata matar gwamna. Wannan 'yar ta ta mai kama da aljanu itama ka kalleta sai ka kara ga wasu 'yan matan Zayyana da Hibba su ma kowacce ta hadu karahe. Bayan wani ta gani kusa da Malamijo suna magana ta wuce su Mairama a fusace za ta shiga cikin gidan.

"Salame babu gaisuwa? Ko ba ita bace?" Zayyan yace albarkacin Halifa da ya tabo shi yana cewa ga Ummansa.

Ba ta iya juyowa ba sai tsuma da take yi tun daga tsakar kanta har tafin kafa. Tasan muryar nan da irin tasirin da ta jima tana yi mata a duk lokacin da taji ta. Sannu a hankali ta juyo idanunta suka sauka akan Zayyan Muhammad Tureta mutumin da har yau babu wani namiji da ya kaishi daraja da kima a idanunta.

Takowa take yi jiki a mace zuwa gabansa ta ma manta da kowa da komai sai tashin tsumin kaunar da take masa. Idanunta suna kwararar da hawaye ta kusa isa gareshi "Zayyan dama kana raye?"

Malamijo gani yayi tana neman wuce gona da iri yasha gabanta "sai ki ka ga mijin kanwarki ko? Ashe tsahon shekarun nan yana daure a gidan yari"

"Gidan yari? Allah sai Ya saka mana. Ni dama jikina yana bani baka barmu ba Zayyan" tace tana kuka sosai.

"Zai saka mana kam ni da iyalina. Mairama matso ku gaisa mu tafi" Zayyan yace fuskarsa babu digon fara'a ko kadan. Ji wannan zubar da mutumci da take neman yi a gaba danta, mahaifi da kanwarta kuma matarsa.

Ita Mairama dama tsayawa tayi ta ga iya gudun ruwanta saboda yadda ta kula kamar bata cikin hayyacinta. Da ace bata san tana son mijin nata ba sai tayi tsammanin tsabar kaduwa ce kawai.

"Adda Salame yaya gida da yara? Da Halifa bai taso ki ba ma zamu tsaya a gidan naki ai su gaisa da maigidan naki"

Firgigit ta tuna wai tana da aure. Amma Allah Ya isa Alh Indararo. Wallahi tayar masa da hankali kawai zata yi ya sauwake mata ta huta. Sakin fuska tayi don dole suka gaisa da Mairama ta rakata har bakin mota. Ta bangaren da Zayyan yake zaune a baya ta tsaya yayi saurin danna abin rufe window ya dage glass din. Bata bata rai ba ta dawo bangaren Mairama ta leko da kanta.

"Hmm nace bari nayi miki karambani. Kun dai tambayi malamai game da matsayin auren naku ko. Kada aje ana haramtaccen zama. Idan babu auren gara a san me ake ciki tun wuri"

Da Mairama tana zagi da sai ta hado mai kyau ta zubawa Salame. Wannan jaraba har ina. Daga sake haduwa dashi take kokarin dawo da maitarta a fili.

"Kinsan ba sakina yayi ba kuma ban sake aure ba. Saboda haka auren mu yana nan har yanzu"

"Mu tafi mana" Zayyan yace da dreban rai a dan bace tun bayan dawowarsa. Ba don ta gaji da kallonsa ba ta koma gefe aka ja motar tana tsaye tana daga hannu "bye bye, bye bye" take ta fadi tana murmushi.

Hannun Mairama ya rike yana kallon fuskarta "meye na tsayawa yi mata dogon bayani bayan kinsan akan hanya muke?"

Murmushi tayi ya karawa fuskarta kyau "gani nayi gara nayi mata bayani tun wuri kada tayi tunanin akwai wata kofa da za ta iya samu ta shiga gidanka"

Bude baki yayi ya kalleta "kada kice min ta fada miki"

"Bata ji komai ba ta sanar dani kuma shine dalilin mutuwar aurenta kamar yadda Alh Salisu ya fada min jiya da kana waya da Baban Arifah lokacin da yazo. Cewa yayi nayi hankali da ita mai hali baya fasa halinsa kuma gashi na gani"

"Mairama ina so ki sani wallahi ban taba cin amanarki ba akan Salame"

Kanta ta dora akan kafadarsa ta rufe ido "kada zancenta ya bata mana farincikinmu"

Alamun saka zip yayi a baki yana dariya suka cigaba da hirarsu cikin shauki har suka isa Kano. Gidan da ya gina da guminsa da kuma gadon mahaifiyarsa ya shiga yana tuna baya. Saboda hazo ya fara kura amma da gani an kashe masa kudi wurin gyara da kayan alatu. Mairama ya janyo ya dora kansa a kafadarta yana tsaye a bayanta yace "kin tuna zuwanmu gidan nan na farko?"

Sai da taji kunya Allah Yasa baya ganin fuskarta "ban tuna komai ba"

"Da gaske? Ni kuwa kamar a kaina aka ajiye ranakun da Mairama ta rinka nunawa Zayyan soyayya irin wadda nake sa ran a maimaita. Jikina yana bani a nan kika samo Zayyan fa"

"Ni dai ka kyaleni gyaran gida zanyi" tace a kunyace

"Muje na tayaki ai muna da lokaci. Sai jibi zamu tafi Sakkwato in je mu hadu da Maikudi"

Ajiyar zuciya tayi tana hango wannan haduwa bazata yiwa Maikudi kyau ba ko kadan.

**********

Ranar da daddare bayan Yadikko ta dawo ne Radhiya taji komai game da amaryar Malamijo a wurinta. Taji zafin sakin Hajjo ita ma tayi ta bawa Yadikko baki akan kada ta tafi wa zasu gani su ji dadi.

Shima Malamijon kuma sai ya fada mata abubuwan da Hajiyayyen tayi masa.

"Malamijo ai kowa maye ne sai dai idan baiso nunawa ba. Ka rubuta mata takardarta tun dare gobe zaka bata kuma wallahi Hajjo kadai na yarda ka dawo da ita"

"Ba ma sai kin fada ba 'Yar soja ikon Allah. Na ma gama aure yanzu sai dai ku"

"Wai ni su waye ma suke yi maka waliyai ne a aure auren Malamijo?"

"Kaniyarki mai ido a tsakar ka" yace yana laluben takalmi zai biyota dashi ta gudu. [5/22, 11:03 PM] Sis Ruky: Radhiya bata kwanta ba sai da ta gama tsara yadda za ta yi da Hajiyayye gobe. Ba'a taba mata kaka a kwana lafiya. Yadda ta rabe mata abinci bata sami ko loma daya ba haka da daren ma dan kadan ta ce Na'e ta zuba musu ita da yaran. Bakinciki yasa Hajiyayye ta kasa komai saboda sau uku tana kokarin zuwa dakin Malamijo sai ta tarar da Ibrahim da Emzee a kofar dakin kamar suna gadinsa.

Bayan kowa yaci abincin safe ne Radhiya ta fito tsakar gida tana tambayar waye mai girki yau. Yadikko ta kama kunnenta ta rike.

"Na fada miki babu mai girki a gidan nan sai amaryar kakanki. Na'e ma da tayi tuwon dare jiya kawaici tayi miki bata ce komai ba"

Hajiyayyen rabewa tayi a jikin kofar dakinta tana jinsu tayi murmushi. Ashe dai Yadikko tasan matsayinta. Idan suka yi kuskuren biyewa wannan yarinyar za ta barsu da jidali ne idan ta tafi don duk wanda ya shiga gonarta sai ya gane kurensa.

"Tunda babu mai girkin dole ni zanyi kenan da kaina. Bari na leka Malamijo ya bada shanu uku ma sun isa da za'ayi yanka"

"Yanka kuma? Radhiya idan kika zo gidan nan bakya zama kiyi ta mana jaye jaye. Nama kuma kema kin sani ba'a kawowa gidan nan har kike kiran yanka."

Bata ankara ba sai ga Malamijo ya fito yau dai sanyi ya saka shi saka kayan kirki ya rufe kasusuwan jikinsa. Daure fuska yayi yana hararar Yadikko.

"Kinji nace bazan bada shanun bane da zaki yanke min hukunci? 'Yar Soja guda nawa kuke bukata?"

"Uku tace" inji Emzee da suka gama sanin me take da niyar yi.

"Amma shanu uku 'Yar Soja waye zai taya ku aikin naman? Yayi yawa. In baku daya dai yau kowa yaci"

Murmushin mugunta tayi da Ibrahim yayi mata alama cewa fa Hajiyayye ta leko daga dakinta tana sauraronsu. Haka take so taji ko wani nata yaji a kai mata rahoto.

"Kada ka damu naman nan ba mune zamu ci ba. Wadanda za'ayiwa yankan kuma danye suke so"

Idanu Malamijo ya zaro "Hajiyayye zaki yiwa yanka?"

Sai da ta kula kowa ita yake sauraro ta dare kan turmi ta zauna "Bakina dai da zasu zo. Jiya da na ga yadda gidan nan ya koma shine na kira Sarkin mayun Faransa...can inda nake karatu. Dayake muna mutumci da 'ya'yansa sai ya daukeni kamar 'yar cikinsa. To shine nayi masa maganarka na cewa ka auro mayya. Yayi ta mamaki tunda yasan ni ba mayyar bace. Shine fa yau da sassafe ya kirani wai ya kai maganar can ofishin majalisar dinkin duniya akan harkar mayu sun ce zasu turo wakilai azo ayi bincike ke"

Idanun Malamijo tuni suka raina fata ya hau rawar jiki "ni nace kiyi zancena da wasu ne? Haba Radhiya ashe baki da hankali ban sani ba. Mayun Najeriya basu cinyeni ba sai na Faransa"

Yadikko tana ji tasan sharrin Radhiya ne amma yadda idanun Malamijo suka kada suka yi ja sai ta kyale ko banza ta rinka tunawa tana dariya.

Cikinsu Ibrahim ne ya iya daure dariyarsa yace "Turawan mayu inajin kince basa cin mutane sai mayu 'yan uwansu ko"

"Eh mana, matsalar dai bincike zasu zo yi. Wai ashe daga last year aka haramtawa duk wanda ba maye ba auren maye saboda gudun rigingimu da suke tasowa." Ta yi kamar ta rage murya za ta yi rada bayan ta san sarai kowa yana ji "yace zasu kama duka mayun gidannan ne a tafi dasu. Hukuncin take dokar shine kisa ta hanyar babbakaraisin din mayun a baiwa oganninsu su ci da bredi"

Tsuuuu zawo ya nemi saukowa daga jikin Hajiyayye cikinta na murdawa tana matse shi da kyar saboda tsabar kaduwa. Babban yaron da tazo dashi gidan ashe shima yaji ko takalmi bai saka ba ya fito daga dakin nata a guje Radhiya tana a kamo shi. Dayake ba niyar kama shi da gaske suka yi ba da gangan suka bari ya gudu. Ragowar yaran nata ta kalla tace kowa ya tashi tana uban gumi kamar wadda tayi tsere. Muryar Radhiya taji tana magana da yaren da bata ganewa.

Wayar karya ta gama da French ta juya ta kalli Halifa da yake jindadin wannan drama yayi ta dariya kamar cikinsa zai kulle "ka rufe kofar nan. Yanzu suka kirani wai ashe sun ga fitar daya kuma sauran ma sun gama shiri yace idan wani ya sake fita daga gidannan harda mu za'a ci da bredin"

Hajiyayye da gudu ta saki mayafinta hankalinta gabadaya ya tashi. Ta ma rasa da me zata ji. Talle da yaki daukar wayarta tun safe taji ya ake ciki game da shannun ko kuwa wakilan majalisar mayu da za'a turo su kama ta. Acinyeki da bredi wata zuciyar ta tuna mata. Harda guntun hawaye sai da tayi bata ankara ba kafin ta daure ta fito inda suke.

"Uhmm nace Malamijo yau me za'a dafa da rana ne? Naga ana ta hira shine baku kirawoni ba" wai ita nan za ta bagarar kamar bata san me suke yi ba. Daga nan ta samu ta arce. Ofishin 'yan sanda zata je ta shigar da kara kafin turawan mayun su iso azo a fitar mata da yaranta.

To shima ba wai yana cikin hayyacinsa bane duk ya gama tsorata ya fara danasanin kiran Radhiya. Yarinyar nan da ya gama sanin halinta me ya kaishi kiranta da kansa. Wayarta ce tayi kara a lokacin taken wakar Celine Dion ta film din Titanic wanda ta sanyawa Awwab. A wurinta wakar bata tsufa sai ma nishadin da take saka ta idan ta tuna masoyinta.

Idanun Malamijo da na Hajiyayye basu da na biyun kwatance a lokacin. Tsoro ne karara ya bayyana ita kuwa tana dauka da turance tace masa "Chèri please follow my lead i'll explain everything later. Say something in German" (ka biyewa duk yadda kaji nayi, zanyi maka bayani daga baya. Ka yi magana da yaren Jamus)

Yana cikin office dinsu a lokacin ya kirata. Abinda tace kawai ya isa ya saka shi gane cewa akwai abinda take yi. Alheran dinsa bata ji, sai dai kuma idan ta canja daga yadda take ta tashi daga yarinyar da ya fara so daga haduwar farko kenan. Fitinanniyar dai ita ce tashi mai sanya shi nishadi a kowane lokaci.

Speaker ta sanya kowa na ji ya rinka yi mata kalaman soyayyar da yasan cewa ba fahimta take yi ba ita ma.

"Amaryar Malamijo kin dai ji me yace. Wai ku jeru a daki ke da yaran naki yanzu zasu shigo. Idan anyi binciken sun ware mayu a cikinku sai su saki sauran"

"Inji uban wa akace mu mayu ne? Garin nan waye bai san gidan iyayena ba? Malamijo kace wani abu mana" ta fada a raunane hawaye na zuba.

"Ince me? Na auro mayya tayi sanadin da majalisar dinkin duniya ta mayu zata zo gidana" ya ce gumi na karyo masa. Gidan gabadaya yayi masa zafi dari bisa dari ya yarda da zancen Radhiya.

Wayar ta dan kara a bakinta "ranka ya dade ko za ka danyi mata hausa ta fahimta. Mayyar da ta auri kakan nawa ce ta fito" ta kalle su "shine wakilinsu da yake kula da hausawan mayu"

"Bata wayar" Awwab yace dariya na ciwo shi. Wace mai tsautsayin ce wannan ta shiga tarkon Alheran?

Ai Hajiyayye na jin haka ta zube a kasa ta fashe da kuka. Tsoro yayi mata yawa zawon ya fara tsartuwa daga ma'ajiyarsa saboda tsoro. Muryar Awwab dama irin wannan deep voice din ce mai tahowa daga kirji. Mata da yawa suna fadawa soyayyarsa a kanta yayin da take razana marasa gaskiya irin Hajiyayye.

"Kayi min rai ranka ya dade aradun Allah karya nake ni ba mayya bace. Mutum ce kamar kowa kuma indai aurene ko bai sakeni ba ni na saki kaina yanzu zan tafi ba sai kun zo ba"

Dariya yake neman yi Radhiya tace da sauri "ranka ya dade bari na tayaku binciken kafin ku iso zan tabbatar da gaskiyarta" kashe wayar tayi ta ga kowa ya fara ja da baya saboda zawon Hajiyayye. Wari ya isheta amma haka ta daure bata matsa ba.

"Me kike cewa?"

"Nace ba, aurena da Malamijo wallahi duk shiri ne tsakanina da Talle. Rabonmu kawai muka zo yaga mu tafi amma bani da alaka da mayu. Kuyi hakuri yarana akwai marayu a ciki. Waye zai kula dasu?"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull