Batuol mamman complete novel - Chapter 53
Batuol mamman complete novel Chapter 53: Batuol mamman complete novel Chapter 53. "Nasan kinji abinda naji yanzu kafin ki koma kallon titi haka ne?" Baiyi…
3,371 words
"Nasan kinji abinda naji yanzu kafin ki koma kallon titi haka ne?" Baiyi tsammanin jin amsarta ba ya cigaba da kallon gabansa "my feelings are true idan na sami karbuwa ina fatan kare rayuwata Zayyana Mustapha tana tale min baki idan tana jin shagwaba. Abu daya ne bana so....dena yi min magana da kike yi"
Cusa kanta tayi kawai a tsakanin cinyoyinta gabanta na tsananta bugu ba ita ta sake dagowa ba har aka bude gate din gidan suka shiga.
A raunane Ibrahim ya dakatar da ita da zata fita "please Zayyana kice wani abu". Saboda yadda yake jinta a ransa idan taki amincewa bai san ina zai saka kansa ba.
A guje ta fice batare da tayi magana ba. Tana shiga gidan tayi sama da gudu dakin Radhiya ta kankameta tana murna. Lokacin ko awa daya basuyi da isowa ba Rahima tana wanka.
"Kalau kike kuwa?"
Dariya tayi "Ras ras Adda" yau anya ma zata iya bacci kuwa take kissimawa a ranta. Gani take kamar ba gaske ba. Wai sai da yayi maganar take ji a ranta tamkar ta shekara da soyayyarsa sai yanzu ta farga. Wayarta ce tayi kara ta kasa dauka da ta ga shine sai rawa da jikinta yake yi ta saka a silent ta fice daga dakin zuwa wurin Ummi. A can tayi zamanta daga baya suka sauka kasa tare Ummi na son dora girki kafin Daada ya dawo tunda bata da mai aiki yanzu dai suke neman ko da mai shara ce ita zata cigaba da girkinta.
Ibrahim suka tarar a falon ya kunna tv amma hankalinsa baya wurin. Kamar ta koma Ummi ta gama amsa gaisuwarta ta turata kitchen ta samo masa abin sha. Tana tafiya Radhiya da Rahima suka sauko daidai fitowarta daga kitchen Radhiya tana dariyar shakiyanci ta mika mata wayarta.
"Gashi nan kin barta a daki wani Khaleel yana ta kira"
Da sauri ta karbe tayi sama sauran kadan ta fadi Ummi ta bita da kallon tuhuma. Ibrahim ne ya hade rai ya cika yayi fam wato tana da wani Khaleel shine taki amsa masa dazu. Ummi ce tace ya hau sama dakinta su gaisa da Innuwuro don tace ita da saukowa sai da safe saboda ba ta kaunar hawa bene.
Saman ya hau ya sami Zayyana a falo tana ta kai kawo da waya a hannu. Karbe wayar yayi ran nan a bace ya ga akwai lock ya mika mata.
"Bude min"
Budewar tayi ya sake karba da sauri ya nemo sunan Khaleel din ya kira a fusace yana jira a dauka ya fara fada sai wayarsa ta soma ringing. Guntun tsaki yayi saboda Khaleel din yaki dauka ga wayarsa ta dame shi da ruri.
"Ana yi maka waya" Zayyana tace tana kallonsa a kunyace
"Babu ruwanki....shi Khaleel din baya daukar waya ne?"
"Nima ban sani ba"
Kira yayi na uku can ba'a dauka ba tasa wayar kuma anki hakura. Yana zaro ta daga aljihu Zayyana ta karbe da sauri ta daga tasa a kunne idanunta a kansa.
"Ya Khaleel ya akayi ne?"
Kallonta yayi ya ciro wayarta dake kunnensa ya tabbatar muryarta ce a ciki yaji. Wani kayataccen murmushi ya saki idonsa yana yawo tsakanin wayar da fuskarta.
"Ni Ibrahim Khaleel din?"
"Bani wayata ni" ta shagwabe masa.
Biye mata yayi batare da ya sani ba shima tasa fuskar yanayin yadda tayi...tale bakin nan da baya so.
"Kin tayar min da hankali Zayyana. Its not fair sauran kadan zuciyata ta tsaya"
Dariya take a hankali tana sadda kai shi kuwa tamkar ya hadiyeta ya fada tsundum baya fatan fitowa. Wayar ya mika mata da yaji kamar ana hawowa saman ya motsa bakinsa kadan "nagode"
Dakin Ummin da yake a bude ya tafi wurin Innawuro ita koma ta koma kasa inda Radhiya ta hadata da Rahima. Kafin dare su biyun sun dinke tamkar sun jima da sanin juna.
Sai wurin tara Zayyan ya dawo. Sallamarsa kawai Radhiya taji ta tashi a guje kamar yarinya taje ta rungume shi suka sa dariya. Rahima ya kalla da ta gaishe shi a ladabce tare da Zayyana.
Ya saki fuska "Rahima ko? Yaya mutanen gida?"
"Lafiya kalau, mun sameku lafiya?"
"Alhamdulillah" ya amsa mata sannan ya bi bayan Ummi ya hau sama.
***********
A kwanakin da suka gabata Innawuro ta dage wurin wanke jikarta da ruwan lalle mai kyau wanda babu wani hadi cikinsa sai zallan garin da take jikawa ta hada mata da ruwan turare wanda matar Baffa Gide ta hada mata da wasu itatuwa. Ranar da zata nuna mata yadda zata yi sai ga Radhiya ta fito daga toilet a guje fuska sharbe da hawaye tana cewa ita bazata yi wanka dashi ba.
Innawuro ta rasa yadda zata yi da ita saboda kukan gaske take sai ta Ummi ta shiga tsakani. Tana faman hawaye da jan hanci daure da tawul tace "Ummi so take kawai jikina yayi faci faci da jan lalle a ce min dodo ranar bikin. Kinga fa haka ta taba yi min aski yanzu kuma ruwan lalle...ja take so na koma?"
Zayyan yana jiyo su don ranar asabar ce babu inda yaje hankalinsa yayi dakin kunyar Innawuro ta hana shi shiga amma da tuni ya fito da 'yarsa. Ummi tun tana fada sai ta koma lallabata karshe dai ita tayi wanka da ruwan tace ta jira ta gani ko nata jikin zaiyi ja. Ai kuwa ta jira sai gashi Umminta ta fito jikinta yana wani irin santsi ga kamshi mai dadi.
Washegari da kanta tace Innawuro ta hada mata tace taki suka gama dramarsu sannan aka fara gyaran jikin jika. Rigima ta biyu tana wannan baccin nata kamar wadda aka saukewa buhun siminti Innawuro ta daura mata lalle dungulmi har kusan rabin kafa. Kafa daya akayi ta farka a gigice zata cire Innawuro tasa Zayyana da Rahima suka danneta. Babu abinda Radhiya bata ce zata yi musu ba idan ta tashi ko a jikinsu sai da aka gama Innawuro tayi mata jan ido sosai.
"Wallahi idan kika cire sai na saba miki. Wannan lallen dumama miki jiki zaiyi ana miki gata kina shirme"
Hawaye ne ya digo mata "to sai ki min tsohuwa ta fada kwata ina laifin ma kice a siyo salatif ayi na gayu"
Dun jgure mata kai Innawuro tayi "nasan damuwar taki bata wuce kada azo na biki wannan bai fita ba ko. To kisha kuruminki kina da akalla kwana ashirin dole zai fita kuma bayi miki zanyi a hannu ba"
Baki ta zumburo "kuma safa zan rinka sakawa kullum"
"Da kuwa kin burgeni domin so nake ki rabu da taka wannan tayil din naku duk ba gata bane a jikin mace sanyi na ratsa ta"
Ta dai kwana da lalle amma da safe Rahima da Zayyana sai da tasa suka gudu daga gidan suka koma gidan Mami don cewa tayi balotelli zata yi musu. Tun suna dariya sai gata da almakashi tuni Zayyana ta tsure saboda ta tuna da.
Akan lallen Awwab kansa yasha mita kamar shi ya kulla mata sai hakuri yake bata. Shima suna ta nasu shirin da Yousuf saboda ba wasu abokan kirki garesu ba. Awwab idan ka cire mazajen kannensa da Yousuf din a yanzu da suka yi muguwar shakuwa bashi da abokai a Nigeria sai na wurin aiki. Shiyasa kayan da zai yi amfani dasu na daurin aure iyayensa ya barwa ragama. Baba Hadir kaninsa ya turawa kudi da wasu kayan Awwab din domin ayi masa daidai jikinsa.
A bangaren mata kuwa Mama tuni ta warke don bata zama. Duk abinda za'ayi ita ce gaba Mami da Ummi 'yan kallo. Siyayya suke yi sosai zuwan Mama Kano sau biyu. Zayyan dai ya saki bakin aljihu ne hankali kwance wannan arziki da Allah Yayi masa na ganin auren 'yarsa ba karamin abu bane. Duk wani abu da ake bukata na auren 'yar gata ya yiwa Alheran. Ana haka sai ga dankareren gado da setin kujeru 'yan Italy masu dan karen kyau da tsada Alh Mousa mahaifin Yousuf wato mijin Tante Nasara ya aiko dasu banda kudi masu yawa da ya tura ta account dinta yace kada ta tambayi Zayyan komai idan tana bukatar kari ta neme shi. [5/22, 11:03 PM] Sis Ruky: Sake kiranta akayi taji cikinta yayi wata irin murdawa. Ina ita ina yin magana kuma wai a gaban wadannan mutane harda shugaban kasa, gwamnoni, sanatoci da 'yan majalisu. Kan Awwab taji a daidai kunnenta saboda kamshin turarensa ta gane shine cikin rada yace.
"Get up baby" taji tsigar jikinta ta tashi.
A sanyaye ta mike ya rike hannunta suna tafiya cikin burgewa ana daukarsu hotuna sai da ya kaita bakin steps din da zata hau ya tsaya yace mata "go on zan jira ki".
Har ta haye yana jin taushi da dumin hannunta a cikin tafin hannunsa. Tsayuwa ta gyara ta kalli iyayenta taji wani kwarin gwiwa ta soma magana a nutse. Ta yabawa sojoji akan rayuwar da ba kowa yake da zuciyar yinta ba ta kara da rokon a dube su domin sun cancanci kulawar al'ummar da suke yiwa bauta.
"Soja shi kadai ne yake mayar da kowane dan kasarsa dan uwansa a lokacin tashin hankali. Kowa zaiyi kokarin ceton nasa amma soja zai tsaya ya kai ceto ga wanda kila har ya gama taimakon ko kwakkwaran kallo bazai sami damar yi masa ba bare ace akwai wata alaka. Soja babu ruwansa da bambancin al'ada ko addini. Yare daya yake fahimta shine SAVE, HELP AND PROTECT EVERYONE." Daada ta kalla tace "Ina rokon afuwar babban bakonmu domin zan saci kalmominsa long live Nigeria, God bless my country"
Haka aka rinka tafawa Radhiya sai da tazo step din karshe Awwab ya mika mata hannu ta rike ya kaita har gaban seat dinta sannan ya koma ya zauna.
Taro ya burge matuka Zayyan ya sami alkhairi fiye da zato da tsammani. Supervisor din Radhiya tazo ta rungumeta su ma sunji dadi domin kuwa a take wani da minister of information ya tura musu ya bukaci su cigaba da bata duk wani training da zai taimaka mata domin su tababbatar da bunkasar wannan shiri.
Sun fito tafiya Arifah tayi gefe ashe mukullin motarta zata karba da tasa dreba ya kawo mata. Yousuf yazo ya shige ya zauna bayan ya radawa Awwab cewa gida kawai zai rakata sai ya dawo.
"Kuma an fada maka zan yarda da wannan zancen ne" yace yana dariya.
Yousuf ya rage murya yana dariya shima "ni dai ko yaya sai na tabbatarwa Arifah ni mijinta ne yau...kada ka rufe min kofa rakiya ce kawai zanyi"
Kusan kowa ya fito ana ta shiga mota. Awwab na kallon Radhiya ta shige motar da suka zo. Wadda ya tuko ya shiga kai tsaye gidan Daada yabi bayansu Bilal yana tambayarsa ina zasu je kuma yace "rakiya zanyi na dawo". Daga bakin gate ya cillawa Bilal key din motar yace shima kada a rufe masa kofa sai ya dawo.
Raji dariya kamar me sun dago angwayen hakurinsu ya kare ne. To su din ma ciki suka shige kowanne ya kira matarsa.
Tana hawa bene a gajiye taji wayar Awwab saboda kidansa daban ne. Da sauri ta dauka ga kuma kunyarsa da take ji.
"Kina ina?"
"Yanzu muka shigo gida"
"Yunwa nake ji Schatzi" taji yace harda marairaicewa.
"Ka karasa gida ne?"
"Na biyo matata ta bani"
Saukowa tayi da sauri tana fita suna karo ya riko hannunta ya ja ta gefe sai da ya gama dube dubensa ya turata wani karamin falo wanda kujeru ne kadai a ciki sai tutar Nigeria a tsaye. Faduwa gabanta yayi da ya tura kofar da kafarsa ya rinka taku a hankali zuwa gabanta. Kasa dago kai tayi sai dai ba shiri ta daga din sakamakon daukan da Awwab yayi mata.
Dagota yayi ta hanyar saka hannuwa daga kasanta yayi sama da ita dole ta saka hannuwanta ta riko wuyansa domin kada ta fadi. Idanunsu cikin na juna ya soma juyi da ita yana dariya itama sai da tayi saboda yadda yake yi mata.
"Nice to meet you Mrs Awwab" yace lokacin da ya direta a gabansa.
Kunyar ce ta motsa saboda yadda ya tsareta da idanu ta kasa magana sai ma juyawa da taso yi ta fita. Hannunta kawai ya janyo ta fado jikinsa ya rungumeta sosai. A tare suke sauke numfashi da ajiyar zuciya yau burinsu ya cika. Kanta yana kirjinsa ya saka hannuwa a bayanta ita kuma nata suna ta wurin cikinsa ya soma magana cikin wani irin salo da shaukin soyayya.
"Alheran don Allah kada mu taba bari fushi ko wata zugar mutane su shiga tsakaninmu. Nasan ni dake are not perfect but we complete each other. Kece zabin Awwab tun kin baby har ranar da zai dena numfashi in sha Allah"
Kalamansa sun kara masa matsayi da kima a idanunta. Batare da ta dago kanta ba ta yi magana don tsokana "har lokacin da aka yi min aski?"
Murmushi yayi "tashinki daga baccin nan da kallon da kika yi min shine lokacin da Awwab ya fara yiwa Alheran soyayyar da yake fatan ta kare a aure"
Murmushin da tayi ne ya janyo shigewar dimple dinta ciki sosai. Abinda Awwab ya dade yana jiran damar yi sai ji tayi ya dora lips dinsa a wurin yayi kissing dinta. Kunya har sai da taji cikinta yana wata irin yamutsewa shi kuwa bai tsaya ba sai pin din da tayi rolling dashi yabi ya zaresu ya zame mayafin. Kansa ya kai gaban goshinta yana shafa gashinta da yake kulle cikin ribbon tayi packing dinsa a tsakiyar kanta ya kuma bata wani kiss din.
Da wata irin murya yace "rufe idanunki"
Ki tayi sai dai suna hada ido ta runtse nata da sauri saboda bata da kuzarin cigaba da kallon idanunsa. Tana ji yana dan motsi amma bata bude ba taji ya saka hannu ya zame mata ribbon ya cusa yatsunsa cikin gashinta ya sake matso da ita. Bakinsa ya hade da nata a nutse ya jefa mata sweet din bakinsa irin wadda suka taba sha a soron Malamijo. Bata san lokacin da ta bude idanuwanta ba saboda ta gane dandanon alawar. A haka suka sha ta kusa rabi sannan ya bar mata a bakinta ya sake janyota jikinsa.
"Ina jindadi idan muna sharing abu...nafi son ko me naci babyna ma taci. I hope daga yau haka zamu koma yi...it is better than daya ya ragewa daya"
Duk da bakon yanayin da take ji sai da ta tsokane shi "harda abinci ko?"
"Ewww ke fa kazama ce" yana bata fuska da tunanin a tauna abinci daga baki.
Dariya tasa "kaga tuwo zaiyi dadi...."
"Fita, fita ki tafi dirty girl" yace yana nuna mata kofa tare da dora mata mayafinta a ka.
Turjewa tayi "nama fa?"
"Out" ya kuma cewa yana bata fuska ya dago hannu ya biyota ta kara gaba da sauri. Tana bude kofar ya janyota ya rungumeta ta baya kansa na kafadarta "babu abinda zai fito daga bakinki na kyamace shi Schatzi. Idan kin ga dama har kunu musha a haka"
Ita ya bari da bata fuska "shhhh please Hammana dena fada"
"Ko kosai shima zaiyi dadi"
Yatsunta tasa ta toshe kunnuwanta ya sake matseta "juyo kiji last one din"
Kafada ta noke ya juyo da ita da kansa "I love yo baby"
A hankali ta dago kai ta kalle shi idanunta sun kara girma da haske tace "I love you Chèri" tare da shammatarsa ta fice da sauri. [5/22, 11:03 PM] Sis Ruky: Ita da Arifah suma nasu shirin suka fara inda da sahalewar angwayen nasu suka amince a hada dinner a Abuja bayan kowacce anyi mata nata bikin na gida. Arifah a Jos za'ayi wasu events din bikin 'yar gwamna guda daya tilo ita kuma Radhiya sai da aka yi ta tunanin inda yafi dacewa karshe Mama tace ayi a Abuja amma yini a Sakkwato za'ayi kamar yadda za'ayiwa Arifah a Jos. Ranar kai amarya kowacce a daukota daga garin mahaifinta washegari suyi dinner dinsu. Daga nan kuma tsugunne bata kare ba domin Tante tana can Nijar da sauran 'yan uwa ana shirin bikin 'ya'yanta Yousuf da Radhiya saboda haka ana wannan dinner din can zasu wuce ayi sabon biki sannan amaren su tare. Dama kuma Tante din ta riga ta sanar dasu Ummi kada a dauko wata mai gyaran jiki zata taho da kawarta tun suna 'yan mata idan sun zo taron Zayyan zata barta a nan. Arifah daga Nijar zasu wuce France shi kuma Awwab ya riga yasa an fara nemawa Radhiya visar Germany can zai tafi da ita suyi sati biyu su dawo Nigeria.
Tun yanzu kowa jiki ya fara fada masa saboda shirye shirye. Ana ta kai dinkunan biki na amarya , 'yan uwanta da iyaye. Zahra da Raji sun dawo daga Katsina sai hutu ya kara daga wurin aiki amma fa idan ya koma shekarar kaf bashi da hutu. Fauziyya itama sauki ya samu sun koma Katsina sai daurin auren Bilal zai taho da ita.
SANNU SANNU BATA HANA ZUWA
Saura kwana uku daurin auren Arifah hakan na nufi kwanaki hudu ya rage na Radhiya amma har yanzu Awwab bai dawo ba sai bata hakuri yake yi al'amura sun zo ba yadda yayi zato ba. Radhiya tun tana daurewa sai da tayi masa kuka da daddare akan bata fatan a daura auren baya nan. Hakuri ya bata domin wani training aka saka yake jagoranta. Ainihi bashi bane da tuni ma ya dawo gida sai matar wanda zaiyi ta haihu sati biyar kafin ainihin lokacin haihuwarta. Abu yazo da tangarda dole ya dauki hutu. Gashi daga shi sai Awwab ne suka yi wannan course din a Ukraine. Tunda sunsan aure zaiyi shine aka daga masa kafa zai taho ana gobe daurin auren Yousuf.
Ga abu ya dame shi ga fushin Alheran dinsa sannan Mami da Daddy sun kira shi a lokuta mabambanta kowanne baisan dayan ya kira ba suna jaddada masa idan ya bari aka daura aure babu shi zai ga fushinsu.
Ya gama shirinsa tsaf ranar da zai taho ana gobe daurin auren su Arifah yayi ta kiran Radhiya taki dauka tana ta kunkuni. Text yayi mata mai dauke da dadadan kalamai ya sanar da ita yana hanya zai sauka shadayan dare. Bata yi masa reply ba sai sai kowa ya ga sauyi da walwalarta da ta karu. Tante ta fadawa ya taho tace to maza ta tanadar masa abinci a kai gidan Mami. Yousuf da suka zo da sauran mutanen Nijar shi acan yayi masauki dakin Awwab tare da Raji. Gidan Major General Zayyan kuwa babu masaka tsinke saboda 'yan uwansa na Nijar iyaye su Alh Sidi da Alh Ghoumar. Alh Mousa dai da mijin Mammee da sauran tawagarsu hotel aka kama musu. 'Yan uwa ne aka taru ko ta ina. Emzee ma ya da safe ya iso sai dai gidan Mama ya wuce kai tsaye ga mamakinsa Halifa ma ya riga shi zuwa suna tare da Ibrahim. Sakin fuska yayi kamar babu komai a ransa ya rungumi dan uwansa sai dai har ransa yana jin babu dadi da kuma hangen me zai faru idan gaskiya tayi halinta.
Sai bayan magariba Radhiya ta dora girkin da Tante tace tayiwa Awwab Emzee da Ibrahim suka zo dauka. Farar shinkafa ta dafa masa tayi shar da ita sai dai baifi minti biyu ya rage ta kwashe ba ta juye mata alayyahu madaidaici a ciki. Gyareshi tayi amma bata yayyanka ba a haka tayi amfani dashi bayan ta cire shi. Ba kuma tsigar nan ta ganye kawai ba, ta hada ne harda itacen inda yayi karfi da yawa kadai take yankewa. Yau dai tayi kamar na mutum biyar ne tunda tasan su Yousuf na gidan. Miyar kuwa farfesun kaza ne da ta barshi ya danyi kauri an yanka dankali amma da girmansa a ciki da caras shima da dan girma sai koren wake. Rahima, Zayyana da Hibbah suna makale wurin koyon girki tayi ta gama. Sai da ta dibar musu suka sama mata lafiya. Ibrahim ne ya fara zuwa kitchen din yace Zayyana tazo ta bashi labarin Khaleel.
Radhiya da bata gano komai ba tace "ashe dai zatona ya zama gaske da nake tunanin ko saurayinta ne kusan kullum sai ya kirata sai ta gudu don kada muji me ake cewa"
Kashewa Zayyana ido yayi da take ta jin kunya Hibbah da Rahima sun san komai shiru kawai suke yi "zan binciko mana shi Adda Amarya muna zuwa"