Kenza eBookz

Batuol mamman complete novel - Chapter 54

Batuol mamman complete novel - Chapter 54

Batuol mamman complete novel Chapter 54: Batuol mamman complete novel Chapter 54. Bai yarda ya fita ba sai da ya sakata a gaba. Rahima ce take ta yiwa…

3,374 words

Bai yarda ya fita ba sai da ya sakata a gaba. Rahima ce take ta yiwa Radhiya tambayoyi suna tsaye ita da Hibbah ita kuma tana wanke kwanukan da ta bata Emzee ya shigo. Bata ganshi ba sai alama ya yiwa Rahima da suyi shiru. Ido ya rufe mata ta baya sai dai jini baya buya tuni ta gano rabin jikinta ne Zayyan dan Zayyan. Rungume juna suka yi tana ihun murna don har ta fitar da ran zai zo saboda tasan tsananin makarantarsu.

Ya wani kara budewa ya kereta tsaho sosai yana mata dariya ya dan duku kansa "ashe nayi missing dinki Addata yau gaskiya kwanan hira zamuyi kafin Hamma ya daukeki, na fasa bin Ibrahim ma"

"Ka manta ko an daura ina gida har sati biyu?"

"Eh to idan ya bani damar hirar kenan. Muje dakina kiga wani abu"

Suna juyawa Hibba tace "Ya Emzee ina wuni"

"Lafiya kalau mai tale baki number two"

Dariya tayi za ta fita taji Rahima tayi mata wani irin riko tabi bayanta da sauri. Radhiya tayi saurin cewa Emzee ga Rahima tana dakatar da ita su gaisa.

Haba Rahima idanu tuni sun raina fata ashe tunda ya shigo ta tabbatar shine sojan taji cikinta ya kulle saboda girmansa da ta gani. Sai yanzu ya kula da ita a zatonsa 'yar uwar Hibbah ce ko wata dai cikin bakin biki ya saki fuska zai amsa gaisuwar da tayi masa a tsorace suka hada ido. Wani irin yanayi ne da bai taba zato ko tsammani ba ya fizge shi a take a lokacin ya fadada murmushinsa gareta yanayin idanunta tamkar wani maganadisu ya zame masa.

"Kinyi kama da matsorata, yaya sunanki?" Ya tambayeta a kasalance.

Yawu ta hadiya tace "Rahima"

"Rahima zaki zama kawar soja?" ya sami kansa da cewa babu wani tunani.

Duka Radhiya ta kai masa a baya ganin idanun Rahiman sun kara girma duk ta firgice "kada ka tsorata min kanwa dama har yanzu bata sakewa idan Daada ya shigo."

Tana ganin Radhiya ta dauke masa hankali ta fita da sauri ta riga Hibbah zuwa daki. Sai da ta rufe kofa ta soma sauke numfashi da sauri da sauri. Tunda take bata taba ji ko ganin wani abu da ya kwashe mata nutsuwa kamar wannan bawan Allah ba. Danganta abin tayi da tsoron sojoji da take yi ta kai hannunta kirji tana jin yadda zuciyarta ke bugawa.

A kasa kuwa kafin su bar kitchen din Ibrahim ya shigo yana kiran Emzee dreban da zai dauko Awwab motar ta lalace a hanya Raji kuma da yake gida bai san gari ba shine Ummi tace suje su dauko shi. Shi dai Emzee so yayi ya zauna a kira masa yarinyar nan mai idanu bai gaji da kallonta ba.

Da abincin da Radhiya tayi a motar suka je dauko shi. Ibrahim kasa hakuri yayi sai da yace masa yayi jiki saboda aikin nasa yafi yawa a zaune gashi babu inda yake zuwa daga gidan da ake basu kamar hostel idan baka da ra'ayin kama wani ko kana da naka sai office din nasu. Murmushi kawai yake yi yana jin kewar Radhiya amma dare yayi ana neman shabiyu gashi jirgin safe zasu bi zuwa Jos saboda karfe biyu ne auren kuma suna tare da ango. Wanka kawai yayi da sallah yaci abincin nan sosai tare dasu Raji suka kwanta a gajiye bayan ya tura mata text din godiya tunda taki daukar wayar tasa. Ya dena damuwa don ya ma fi son haduwarsu ta gaba da amsa sunan matar Awwab.

Da safe kuwa ba a nutse suke ba anata shiri. Duka kayan da zasu saka na daurin auren a jaka suka saka su. Suka wuce airport mota mota sai Jos. Karfe biyu da 'yan mintuna bayan sallar azahar Major General Zayyan Tureta ya karbi sadakin Arifah daga hannun kanin Alh Mousa naira dubu dari da dalleliyar mota. Nan da nan jama'a suka shaida auren Yousuf da Arifa abinda wata uku da suka wuce ko sanin juna basuyi ba bare suyi tunanin wannan rana. His Excellency the Executive Governor of Plateau state Rtd Col. Nasiruddeen Aliyu ya tara jama'a sosai 'yan siyasa manya a wannan taro mai dumbin tarihi. Ansha hotuna a ranar biyar na yamma suka sake dagewa sai Birnin Shehu. Ga gajiya an dauko ga wata za'a sake dauka gobe.

Hotel da wani guest inn Zayyan yasa yayunsa kama dakuna da dama saboda yayi mamakin jama'ar da suka zo wannan aure. Da wuri ya biya kudin masaukin saboda haka basu sami wata matsala ba. Mutanen Katsina gayya guda sai kayi mamaki kamar ba su bane masu cewa dole Awwab ya auri 'yar uwarsa don duka kakanin Awwab sunzo su ukun. Malamijo da 'ya'yansa maza kananun ne kadai babu amma ya dauko kowa ga kannensa suma motoci suka ciko da mijin Nene. Ga jama'a guda daga Nijar wadanda suka halarci auren Yousuf jiya. Daga Rugar Barkindo Ardo, Baffa Gide, Baffa Habubakari da su Zakari kusan kowa yazo shaida auren 'yar soja. Mutanen Tureta da su Alh Salisu da duk wanda ya kamata sun zo. Chibuzor dashi aka daura na Arifah kuma yau ma yana tare da babansa Zayyan shima zai shaida. Karfe goma na safe aka saka saboda masu komawa a ranar su iya tafiya. Kusan ma dai kowa juyawa zaiyi suna sa ran da an daura anci abinci a fara tafiya.

Zuwa lokacin Zayyan ya ciko sosai don Mairamansa ba da wasa ta tasarma fito da mijin nata ba. A babban masallacin juma'ar unguwarsu da yake bakin titi za'a daura auren. Wata hadaddiyar mota ce ta tsaya a harabar masallacin sojoji suka yi dafifin kare shugabansu. Mutum uku ne suka fito daga motar wata shadda suka saka iri daya ruwan zuma mai dan karen tsada. Dinkinsu da komai hatta hula da takalmi basu bambanta ba. Suna fitowa aka fara daukarsu a hotuna tun kafin su karasa ciki. Uban gayya ne Major General Zayyanun dan mutan Sakkwato yana ta murmushi kamar shine angon. Har yau da yake shirin aurar da 'ya bai dena tafiya da hankulan mata ba. Daga gabansa rike da wata sanda mai kyau domin samun balance din jiki Daddy Rtd Major Mustapha ne mutumin Katsinan Dikko kunya gareku ba tsoro ba. Kamilin mutum msi tafiyar da komai cikin tsari da haiba. A bangaren damansa kuwa aminin kwarai ne wanda abotarsu ta zame musu 'yan uwantaka Rtd Lt Hadir gaisuwarsa daban take jinjina ga dan mutan Kanon Dabo mai dutsen Dala da Gwauron dutse, Kano ko da me kazo an fika. Hadir Murtala abokin da Zayyan Tureta wadanda sukayi zamani a matsayin zaratan jaruman samari kyawawa. Su ukun nan tarihin rayuwarsu abin duba ne domin kada duniya ta manta da soyayyarsu da sadaukarwa domin kasarsu domin abotarsu. Taku suke maza 'yan uwansu na waigensu domin sun isa a dube su din. Cikin masallacin suka shige ana ta gaisawa da 'yan uwa da abokan arziki.

Daga waje mintuna kadan bayan shigewarsu wata motar ta iso Awwab ya fito rike da waya a hannunsa yana sanye da shadda fara kal wadda aka yiwa aiki da zare ruwan toka msi duhu. Hula da takalminsa kalarsu daya da zaren sai agogo da links din hannun rigar duka silver masu kyau. Saboda kurewar lokaci ranar da zai taho yayi aski saisaye aka yi masa wani irin gyaran fuska da ya fito da gajeren kwata miliyon dinsa. Matashi ne ajin farko mai tattare da nutsuwa da kamala. Kallo daya za ka yi masa kasan cewa yau din ta dabance a wurinsa ranar aurensa da Alheran dinsa. A gefensa angon jiya ne Yousuf bayansu kuma Emzee da Ibrahim sanye da wani ubansun yadi da Mama ta dinka musu. Su dinma kamar iyayensu daga sama wato hula har takalmi babu ta inda su ka bambanta komai. A tare dasu Halifa ne shima ya fito fiye da zato.

A cikin masallacin kuwa wakilan ango da amarya aka nema Hadir da Zayyan su ka matso gaban limanin suka zauna a kusa dashi. Yadda yake a tsarin musulunci haka aka gabatar da komai inda Hadir waliyin amarya ya karbi sadakinta naira dubu dari daga hannun Zayyan waliyin ango. Addu'a aka yi aka shafa Captain Muhammad Awwab Mustapha ya zama mijin Alheran Radhiya Zayyan Tureta.

Hamdala ya rinka yi babu tsayawa a lokacin da yaji kammaluwar komai Schatzi dinsa ta zama tasa halak malak. Hotuna ake ta yi da gaishe gaishe na 'yan uwa da abokan iyayensu. Malamijo da tawagarsa kadai sun isa gayya. Gidansu Zayyan aka wuce ya sakarwa 'yan uwansa da matansu Badaru ragamar girkin da za'a ciyar da mutane kafin su tafi. Da farko Mairama yaso su zo su kwana a garin domin yin abincin ita kuma tace dama ce ta nuna musu yana kaunarsu kuma ya yarda dasu. Ai kuwa basu bashi kunya ba domin kowa yaci ya sha anyi abu cikin girma. Kuma sai da Baban Arifah ya samu yazo shima duk da mutanen da ya baro a gida. Maikudi ne dai idan akwai namijin mujiya to shi ne a wannan taron. Yana ta rakubewa a gefe Zayyan sai ya dauke kansa kawai. Daga baya ya ga bai da amfani nunawa duniya akwai baraka tsakaninsu shiyasa ya koma sako shi cikin al'amuran. Da yace Maikudi kuwa sai ka ganshi da mugun sauri ya taho.

Ba su suka sami saukin kebewa daga mutane ba sai lokacin da ya idar da sallar la'asar. Yana zaune da 'yar cikinsa ya ajiye babbar rigar da hula can gefe. Bayan doguwar addu'a ya dauko wayarsa ya turawa Radhiya text din da yake ta son yi tun bayan an daura auren.

(Ina hukuncin matar da bata daukar wayar mijinta? Ki fada mata Awwab ya zama na Alheran kuma ta shirya karbar punishment dinta na share shi).

Hira suke yi da Fauziyya da Zahra rabi suna tsokanarta rabi kuma shawarwari ne suke bata tunda yanzu itama girma yazo. Ita dai jiki yayi sanyi kamar ba ita ba. Wani abin tayi dariya wani kuwa sai dai taji kunya idan sun fada amma ta kasa magana. Duk da ba bikin bane ya taso amma gidan ya rude don ma anyi sa'ar kawowa Ummi masu aiki biyu 'yar dattijuwa da kuma mai sauran kuruciya.

Sakon Awwab ta karanta suka ga murmushin nata ya koma na daban.

Fauziyya ta dago wuya zata leka wayar "Ango ya miko gausuwa kenan...mu gani me yace"

Janyota Zahra tayi "ina ruwanki, idan kin matsu kiji me yace nemi naki mijin tunda suna tare kema yayi miki text din. Radhiya tashi ki koma daki kiyi magana da mijinki kinji"

Kasa mikewa tayi Fauziyya ta cigaba da zolayarta sai da Zahra tayi da gaske don ta kula jikin kanwar tasu mai sabon mukamin matar yaya yayi mugun sanyi. Tana tafiya Fauziyya ta tallabe kanta da hannu biyu.

"Jikin ta kanwa yayi la'asar fa Sis. Duk surutunta kinga fa bakin ya mutu. Allah sarki irin matsoratan amaren nan za'ayi"

"Tausayinta kike ji ko tsokana?"

"Tausayin dai...hmmm kazo kayi ciki ka rasa inda za ka tsoma ranka kaji dadi"

Tuntsirewa da dariya Zahra tayi ta gano Fauziyya laulayi ne yasa ta a gaba shine za ta saka mutane itama.

Bayan Radhiya ta koma dakin babu kowa. Gefen da tayi sallah ta kalla ta tuna nasihar da Mama tayi mata a wurin bayan ta umarceta da tayi nafila ta godewa Allah bayan an daura auren. Wata irin soyayyar Awwab take ji tana kara shigarta sosai ta lumshe idanu ta kwanta sannan ta kira shi.

Sautin numfashinsa ne ya sanar da ita ya dauka amma yaki yi mata magana shima nata hawa da saukar numfashin kadai yake sauraro wanda ya kara masa gudun bugawar zuciyarsa.

Ita ta fara kartse shirun nasu ta hanyar gaishe shi da tattausar murya "Hammana ina wuni"

Da kyar ya iya hada kuzarin amsawa yana jin kamar yau ya fara son ta "Matsoraciya yaya kike?"

"Tsoron me nake yi?"

"Daga kinji nace zaki karbi punishment shine kika dawo daga strike din yi min magana mana"

Kamar yana gabanta ta tura baki "to ba kaine ba"

Katseta yayi don yasan fushin har yanzu na menene "Ko ba ni zan aureki ba kinsan bazan yi missing aurenki ba bare kuma Alheran din ta Awwab ce"

Kunya taji sosai yayi murmushi ganin yau ita ce babu baki "wai ni tun yanzu ina bakin naki ya koma ne? Anya zamu shirya da wannan amaryar kuwa wata bebeya nan da ita"

Ibrahim ne yayi masa alama da hannu motocin da zasu kwashesu sun iso. Ba yadda ya iya sallama yayi mata yace tayi musu addu'a gasu nan fitowa zasu taho. Kafin su iso anyi abinci sosai jiran isowarsu kawai akeyi. Kowa yaci ya koshi kuwa sai son barka aure ya yi albarka sai fatan zaman lafiya ga sababbin ma'auratan.

A gajiye su ka dawo ana sallar isha kowa sai bacci. Angwayen biyu, Raji da Bilal suna gidan Mami. Ibrahim da Emzee kuwa gidan Mama. Daya ga wata ta matso babu lokacin zama babban taron da ake ta jira ne Allah Ya kawo shi. A haka ma da ba su ne suka shirya ba basu da zama balle kuma na washegarin da yake nasu.

Dadin abin ma kuma domin tallata shirin Radhiya Baban Arifah ya samu yace a saka wani bangare nashi a wurin taron tunda shugaban kasa zai je. Ita kuma sai ta gaggauta sanar da Supervisor dinta domin ta nema mata izini. Kwana biyu a tsakani matar ta fada mata cewa su uku an wakiltasu zuwa su gani sannan su tayata murnar dawowar mahaifinta. Ranar kwanan murna tayi sai gashi ana gobe taron sun iso. Duk wannan lokacin angon nata yayi wuyar gani suyi nan suyi can saboda ganin sun kammala komai bisa tsari yadda suke so.

Malamijo da kansa ya hada mutum biyar cikin masu zuwa taron daga gidansa a yara sai kuma Yadikko da Hajjo. Shatar mota yayi musu ana shirin tafiya sai ga Salame niki niki da kaya ita da yaranta wai itama zata je. Ba wani abu bane ya tunzurota kuwa sai labarin da ta samu na cewa Rahima ashe ta bi Mairama. Zuwa zata yi har gidan taci mutumcin yarinyar tunda tana son nunawa makiyanta cewa bata isa ba. Abu na biyu kuma so take taje ta ganewa idanunta wace irin rayuwa Mairama da Zayyan suke yi da akaje daurin auren 'yarsu a Sakkwato aka dawo ana zuzuta taron da angon da Radhiya ta dace da shi. Malamijo bai hanata zuwa ba amma da karamar 'yarta kadai ya yarda taje sauran ya turasu cikin gidansa.

Tunda aka shigo garin Abuja bakin Salame yaki rufuwa tana ta kalle kalle. A tasha dreban ya tsaya aka tura wani dreban daga gidan yaje ya taho dasu. Nan fa cikin Salame ya duri ruwa ganin sojoji da bindiga tun daga bakin gate din wani irin katon gida mai kyau. Jikinta yayi sanyi kalau ba ta fatan ace wannan ne gidan Mairama. Bata gama tunanin ba kuwa aka wangale gate din gidan. Wani bacin rai taji ya tuko ta da fa yanzu gidan nan nata ne ba don bakincikin da Mairama tayi mata ba. Suna shiga Ummi da kanta ta fito tarbarsu da murnarta tare da Rahima wadda tun safe da tace mata Malamijo yace da Salame za'a taho jikinta yayi sanyi. Ummi tana kula da duk motsin yarinyar kuzarinta ya ragu sai kayi mata magana bata ji ba saboda zulumi.

Ashe kuwa ba a banza ba don suna saukowa daga mota da ta tafi da murnarta saboda tana son Umman nata taje ta durkusa har kasa tana gaisheta. Kusan hambareta Salame tayi kafin ta dangwara mata yarinyar da ta kai shekara uku tana wani irin wari.

"Ki wuce da ita ki gyara mata jiki tayi kashi sannan ki bata abinci "

Jiki na rawa Rahima ta karbi yarinyar da kafarta da komai amma dole ta dauketa ta wuce Ummi ta shiga ciki. Itama Ummin ba ta niyar koyawa Rahima rashin kunya dole ta bi umarnin mahaifiyarta. Sakin fuska tayi tana musu maraba. Salame tana ta wani basarwa ita bata ga abin burgewa ba har suka shiga ciki. Tun daga katon falon zaka san gida ne na wanda ya isa duniya take damawa dashi. Dakunan da zasu zauna ta nuna musu da kanta su Radhiya suka zo gaishesu ita da Zayyana da Hibbah wadda tayiwa gidansu kaura duk da cewa Maman tasu tana gari. Duj inda 'yan mata suka hadu sunfi jindadin kasancewa tare musamman idan tasu tazo daya.

Rahima wanka ta shiga yiwa kanwarta Khadi yarinyar tana ta yi mata rashin kunya

"Ki dena tabani"

"Kin kona ni"

"Sai na fadawa Umma"

"Ni ki bani sabulun da kaina dan wanke"

Radhiya tuni ta hasala ta fada bandakin tace Rahima ta fita ta karbo mata kaya. Wani irin kallo ta yiwa Khadi yarinya ta bare baki za tayi kuka ta daure fuska "kina yi min kuka zan cillaki ta taga kowa ya huta mara kunyar kawai"

Yadda bata ga alamun wasa a fuskar Radhiya ba sai ta hadiya kukan dama na samun wuri ne tayi mata wanka kamar tayi amai ace yarinya kamar wannan tana kashi a wando ga wani kai a daddage babu gyara anyi kitson roba da yawa sun warware. Zuge sauran tayi ta zuba mata shampoo akan ta soma kukan sai ta fadawa Umma saboda bata yarda a taba mata kai ko Salamen sai tayi ta lallabata tunda tana ji da ita. Radhiya bata sake bi ta kan rarrashi ba sai da ta wanke kan nan tayi mata wankan.

A kasa kuma Rahima dakin da suke taje a gaban Salame ta durkusa tace a bata kayan Khadi.

"Kin wanke wadancan ko kuwa ni zaki kawowa na wanke?"

"Yanzu zan wanke Umma"

Hajjo tuni ta fara zuwa wuya a kufule tace "Salame idan kinsan zuwa kikayi ki tsangwami yarinyar nan ina mai tabbatar miki yanzu zan kira Malamijo a mayar dake gida. Shashancin banza da hofi kai. Rahima ga jakarta can bude ki dauka"

Ummi tana wurin ita abin na Salame yanzu tausayi ne take bata saboda ta hana kanta sakewa ta hana wasu. Rahima da ta duba kayan ashe na babbar Salame ta dauko garin haushin an hanata zuwa da dukkansu. Rigunan sunyi girma haka dai ta dauki wata riga zata saka mata ga pants din duk na babbar. A kanta Salame ta huce haushin rashin dauko kayan daidai tana ta yi mata fada saboda bata san yadda zata yi ba.

Ummi ta kada kai "Rahima anjima bayan magariba kizo na aikeki dasu Zayyana"

"To Ummi" tace a sanyaye ta fita.

Tana cikin hawa benen Emzee na saukowa a gurguje yake tafiya suka kusa karo tayi saurin matsawa gefe. Idanun nan nata ne suka sauka a kan fuskarsa wadda a take murmushi ya maye gurbin bacin ran da ya sauko dashi saboda ganin Salame da yayi a cikin tawagar 'yan Sumaila.

"Kawar Soja daga ina?"

"Ni dai ba kawarka bace"

Murmushi yayi ya nade hannuwansa a kirgi ya tsare hanyar wucewarta "nima ba kawancen kawai nake so ba harda...."

Da sauri ta dago gabanta na faduwa "harda me?"

Kansa ya dukar daidai fuskarta "harda idanun Rahima...zan samu?"

Rikicewa tayi ta samu ya dan matsa ta kwasa a guje yana ta cewa tayi a hankali kada ta fadi. Sai da ya ga ta bace masa ya dan rankwashi kansa "Muhammad Zayyan kalau kake kuwa?" Ya tambayi kansa don ya rasa yadda akayi idan ya ganta daga bugun zuciya sai kasa controlling kansa da bakinsa da yake yi. Kai ya girgiza ya sauka ya dauki mota ya fita.

Bayan magariba kuwa Ummi ta bawa Zayyana dubu ashirin da biyar tunda ita ce babba tace dreba na jiransu su siyowa Khadi kayan sawa kuma kada su manta da takalmi, pants da brush. Sahad ya kaisu suka kwaso kayan da ya dace. Rahima tana da wata dubu daya cikin kudin da Ummi ta basu rannan suka siyo kayan kwalliya ta sayawa Khadi packet din ribbons na dari shida za ta yi mata kitso sai ta saka mata. Gida suka wuce da murnarta bayan sun nunawa Ummi tasa musu albarka ta wuce ta kaiwa Salame. Ba karamin dadi Salame taji ba don bata da komai sai dari uku amma dayake ta saka hassada da kyashi a zuci sai ta kyabe baki.

"Ki fada mata ina komawa gida zan turo mata kudinta don nafi karfin cin arzikinta yanzu ma don na manto jakar ne kuma a ciki kudina yake"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull