Kenza eBookz

Batuol mamman complete novel - Chapter 64

Batuol mamman complete novel - Chapter 64

Batuol mamman complete novel Chapter 64: Batuol mamman complete novel Chapter 64. Biki yayi biki gida ya cika da dangi abin farinciki harda wasu cikin…

3,360 words

Biki yayi biki gida ya cika da dangi abin farinciki harda wasu cikin mutanen Sakkwato banda na rugar Barkindo zuga guda. Anci an sha babu kwandalar Mairama ko ta mijinta. Malamijo ne yayi kusan komai sai kuma kannen Mairama su ma wasu katan din lemo, akwai wadda tayi zobo da ginger aka kulla a leda, cincin da meatpie kowa dai ya nuna da gaske sun gaji da zaman doya da manja zumuncin suke muradi ayi.

Amarya Radhiya sanye take da leshi mai dan karen kyau ja da adon duwatsu anyi mata dinkin buba ta daura zamin a kai. Kafarta babu lalle sai yatsu kawai haka ma hannu amma tasha ado ba kadan ba. Sarkar beads aka yi mata shirin ya kayatar matuka tana tsakiyar fili ita da Mama da 'yan uwa ana kidan kwarya. Rawa take tana juyi karaf idanunta suka gano mata shigowar Gwaggonta Salame tana tafiya tana dafa bango saboda takalminta. To da yake Allah baiyi ta mutum mai riko ba indai anyi abu ya wuce to fa ya wuce kenan a wurinta sai dai dan abinda ba'a rasa ba. Shiyasa take kaifi daya babu munafurci ayi komai a wuce wurin. Tana takun rawar a girgiza 'yan mata da masu kidan suke yi taje ta riko kafadun Salame ta kawota tsakiyar fili. Ba laifi tayi kyau atampa ce a jikinta ta sako wani takalmi da bai tsufa ba tun na lefe saboda bata sakawa sosai yayi mata tudu. Yau kuwa dole a dama da ita kowa yasan cewa bata karewa Salame ba.

Bata gama gyara tsayuwa ba Radhiya ta rinka juyi da ita ana girgiza jiki ana rawa. Salame tayi wuri wuri ta jigata 'yan uwa aka basu fili ba abin ta gudu ba ace bata son zumunci tafi kowa laifi. Wata kanwarsu ce ta leka dakin da Mairama take zaune da Rahima mai bacci tace mata ta leko tasha kallo. Daga bakin kofa ta hango rawar da suke tika harda su Hajjo amma Salame jikinta yafi na kiwa girgiza saboda Radhiya ta matsanta mata. Me Mairama zata yi kuwa banda dariyar yadda suke yi. Daidai lokacin Salame ta dago kai suka hada ido Mairama ta daure fuska kamar ba ita ke dariya ba ta shige dakin.

Kwafa Salame tayi cike da takaici a zuci take ta babatu "jimin rashin mutumci fa, tana kallo 'yarta za ta ballani maimakon ta tsawatar shine ta koma daki, yanzu kayi magana a hadaka da sojoji saboda rashin gata"

Wani kanin Mairama ne mai hoton yazo aka fara sannan fa Salame ta samu damar sabulewa. Malamijo ma yazo ansha hutuna yana rike da 'yan biyunsa. Kyautar saniya da sa ya yiwa Radhiya babbar jika yace amma a barsu a gonarsa ya cigaba da kiwata mata. Abu yayi kyau zukata sun haskaka da farinciki.

Bayan isha ne Salame ta gama shirin tafiya ta shiga neman Rahima. Haka kawai take son su tafi tare jiya taji dadi har ranta ko da bata iya nunawa ba. Tana daki wurin Mairama tana faman lallabata taci abinci. Gobe da sassafe zasu tafi saboda a kaita asibiti. Yanayin idon ya soma bata tsoro.

Daga jikin kofa Salame ta coge taki yiwa Mama da Ummi magana sai Rahiman ce tace mata "Umma inzo mu tafi ne?"

Keyar Mairama kawai take gani amma jikinta ya bata gara ta hakura kafin wani abu ya biyo baya. Duk da haka ta ga yana da kyau ta tunawa kanwarta wace tayi ciki da goyon Rahima.

"A'a yi zamanki Rahimata, gobe zan shigo da wuri kafin ku wuce mu karasa hirarmu ta dazu. Kayanki kuma zan bayar a kawo miki yanzun nan"

Dariya ce ta ciwo Ummi wai Rahimata...to dama waye yace ba tata bace? Ita kadai ta nesanta kanta da yarinyar kuma zata fi kowa farinciki idan taja ta a jiki ta sami soyayyar uwa kamar kowa. Sake maimaita kalmar tayi sai dariya tana ta kokarin dannewa amma yadda Salamen tayi magana dole mutum ya dara. Mama na ganin haka ta tace Rahima ta kawo ruwa kwarewa tayi.

Tana fita ta kalli Salame da ke tsaye har yanzu "dan bubbuga mata bayan mana Adda Salame kina tsaye tana tari"

Idanu ta zaro kamar zasu fado tace "wa? Ni....shegiya inji dan daudu. Rufa min asiri ina tabata yanzu zaki ji dirin motocin sojoji ana kiran Salame"

Kan kace kwabo ta fice abinta ko da Rahima ta dawo bata nan. Washegari sammako suka yi saboda yadda Ummi ta matsu suje asibiti kullum idon kara kumburi yake yi. Ta yiwa Malamijo zancen masu zuwa biki yace kada ta damu zai turo wasu Abujan wasu kuma su bisu Sakkwato har zuwa kai amarya Katsina sannan wasu daban suje Nijar. Hakan yayi mata kuwa sosai.

A ranar Mami itama da nata gayyar suka wuce Abuja. Abinda ya bata mamaki bai wuce biyosu da Fauziyya da Bilal suka yi ba. A take ta nunawa Fauziyya bata son yawo ta bari har sai ana gobe Bilal yace shine yake son su tafi saboda akwai abinda zasu yi da Raji da angwayen. Bata matsa son jin ko meye ba suka kama hanya.

**********

A Abuja azahar ta riskesu saboda sammakon da suka yi. Dan kwana biyun da babu Mairama Daada yaji jiki saboda har yau gani yake ko daya bisa dari na fanshe rashin matarsa baiyi ba. Yana falonsa na kasa suka iso Radhiya ta makalkale shi yana dariya. Ita kuma ta lura hakan na masa dadi sai yaji kamar bai rasa komai ba na rayuwar 'ya'yansa shiyasa take yi. Rahima na gefe tana murmushi ta gaisheshi ya sakar mata fuska fiye da yadda yake yi kwanakin baya da ta zo.

"Auta bakya laifi wannan daurin har ido na meye?"

Ummi ce tayi masa bayani Radhiya ta kwance ya ga idon ransa kuwa ya baci kamar ya ga Salame a gabansa ya saita mata fuska. Da kansa ya kira Emzee da ya bar gidan tun safe kuma saboda zuwan Rahiman ne yace yazo bayan la'asar ya kaisu asibiti. Bai ma san waye za'a kai ba amma dolensa ya amsa umarnin mahaifinsa.

Karfe hudu da rabi ya iso Ummi ta sauko sanye da riga da zani da hijab ta tura mai aiki kiran Rahima. Tamke fuska yayi bayan sun gaisa tunda yaji sunanta. Doguwar rigar atampa ce a jikinta ta dora rigar sanyi mai zip ta gaba mai dan fadi tare da hijabi fashion wanda ya zarta kafadunta da kadan. Idonta kuwa hankici tasa ta dafe shi bata son haske na ratsa shi.

"Ina wuni" tace da ta iso kusa da shi da Ummi.

Waya ya shiga dannawa baji ba gani yana a'uziyya a zuci wai kada a sake makalo shi da wani nau'in siddabarun a cikin muryarta da take masa dadi har yau.

"Baka ji ana gaisheka ne?" Ummi tace tana nufar kofa za ta fita.

Sai da ya harari Rahima mamaki ya sake kamata sannan yace "na amsa Ummi baki ji bane"

"Wai haka Rahima?"

"Ummi ya amsa" tace tana murmushi.

Emzee na ganin Ummi tayi waje ya dawo kusa da Rahima kamar gaske ya kuma daure fuska "babu kunya kike yi mata karya, ni nace ki rufa min asiri ne?"

Jikinta ne ya soma rawa saura kadan ta fashe da kuka tace kasa yayi hakuri kawai ta wuce. Da ta karasa bakin motar ma baya ya bude duka bangare biyun yana cewa wai su shiga baya tare zasu fi jindadi. Ummi bata ce komai ba tayi zamanta yaji dadin hakan saboda don bai san karyar da zaiyi mata ba idan ta tambayeshi.

Asibitin Samu Wadata su ka je inda suna zaune Ummi ta saka shi ya bada numbar katinsu aka dauko sannan suka yi zaman jiran a kira su. Basu jima ba kuwa aka kira Rahima da Ummi suka shiga wurin likitan. Bayan ya duba idon sosai yace musu wasu jijiyoyi ne suka toshe sakamakon jinin da ya daskare a ciki shi ya kawo kumburin idon. Magani ya rubuta mata na sha da digawa domin sace kumburin sannan zasu dawo bayan kwana biyar a auna lafiyar idon.

**********

Kwana biyun bayan dawowarsu an cigaba da gyara Radhiya sosai. Mama ce da aikin hadata da kayayakinsu na Sakkwatawa da kuma na wata kawarta Maman Farida. Sai kuma takunkuminta na hana Awwab ganin amarya. Tun ranar da su ka dawo daga Sumaila ta fada masa da kanta. Manufarta bai wuce samun lokaci da kyau a gyare mata 'ya ba. Sannan kuma tasan cewa idan ba haka tayi musu ba haka zaiyi ta zuwa kullum yana bata show tunda yasan matarsa ce. Idan kuwa sai da komai ya kammala ne dole ya fi ganin tasirin aikin.

Ba wani damuwa yayi sosai ba saboda shima bashi da isasshen lokaci. Tun safe suke kulle gidan Mami idan ta fita shi da Bilal, Yousuf, Raji, Emzee da Ibrahim sai wani mutum guda daya da yake zuwa sai dare ya tafi. Mama tayi juyin duniya Mami ta fada mata me suke yi taki su ma kuma kowa ya rufe bakinsa. Yau da yake neman alfarmar son ganin Radhiya lallabowa yayi yana mata magiya. Wasa yake yiwa DK da yake hannunsa yana mata magana.

"Ko awa biyu bana jin zamuyi don muma abinda yake gabanmu akwai cin lokaci"

"Na yarda amma da sharadin sai ka fada min me kuke yi kai da 'yan uwanka"

Dariya yayi don kowa yasan tana binsu daidai suna zillewa ne.

"Big surprise ne Mamanmu ni dai a taimaka kada zuciyar......"

Da sauri tace "Ahhhh dena kiran zuciya yanzu zan kira na sanar da ita."

"Allah Ya ja da ran Mama. Nagode" yace tare da ajiye DK a cikin wani abun kwanciyar yara yana murmushi.

Bayan fitarsa ta kira Ummi ta fada mata gobe zai zo daukar Radhiya zasu je yin hotuna wanda za'ayi amfani dasu a wurin dinner din. A wurin Ummi Radhiya taji zancen ta kama yi masa mitar bai fada da wuri ba yanzu wane kaya zata saka yace ita kadai yake bukata goben komai is ready.

"Hammana da ya ka shirya komai ban sani ba?" Tace cikin jindadi.

Murmushi yayi mai sauti "ke dai ki shirya around 12 zan zo. Love you...sai munyi waya anjima ana jirana"

Saroro tayi da wayar a hannu tana tunanin me yake dauke masa hankali ne yanzu bashi da lokacin hirar kirki. Da dare kuma ba wani jimawa suke ba yake kwanciya. Washegari kafin ya iso ta gama shiri tun daren jiya sunyi magana da Arifah itama Yousuf ya fada mata zasu je kuma kada ta tanadi kayan sakawa. Zahra ce ta yi mata light make up mai kyau fuskarta kamar ka dauke ka dasa ga wani irin kamshi mai rikita kwakwalwa da sanyaya ruhi. A kitchen ta yiwa Ummi sallama saboda yace bazai shigo ba sai sun dawo gudun bata lokaci.

Awwab kasa dauke ido yayi daga kanta tun fitowarta har ta iso gaban motar inda yake tsaye rike da kofa ya bude mata. Murmushi tayi tana sunkuyar da kai haka kawai wani irin nauyinsa take ji. Tana shirin zama ya duko daidai kunnenta "you look sweet"

Fadada murmushin tayi ta rufe fuska da tafukan hannayenta. Sai da ya zauna ta soma gaishe shi idanunsa a kanta kamar zai cinyeta.

"Hammana ina wuni?" Tace da karamar murya tana jin faduwar gaba.

"Lafiya kalau my baby."

Yanzu ma murmushi kawai tayi kamar ba ita ba wani salihanci ne yayi mata dabaibayi yayin da kwanakin barin iyayenta da zama cikakkiyar matar Awwab suke gabatowa. Tayar da motar yayi ya kama hannunta ya rike yana magana a hankali amma idanunsa na kan titi.

Cikin muryarsa mai tafiya da zukata wadda har yau idan Radhiya taji sai ta sanyata cikin wani irin yanayi na tsanananin son mai muryar yace "kinsan wani abu?" Kai ta girgiza ya cigaba da magana "yau inspecting dinki zanyi"

Mantawa tayi da shiru shirun ta kwace hannunta da sauri tare da zare idanu, baki na rawa tace "me...me ne?"

Kin kallonta yayi har yanzu saboda ya san sai ta saka shi dariyar da baiyi niyya ba "Inspection nace ko ban isa ba?"

Da rawar murya tace "ka isa amma ni ban taba jin anyi bane"

"To ke me kika sani game da aure dama. Kafin amarya ta tare ango yake yi domin tabbatar da cewa tana da tsafta."

Katse shi tayi da sauri "Hammana wallahi ina wanka kullum kuma ba ma sau daya ba"

"Dan kin fada da baki shikenan ni kuma sai na yarda?"

Gabanta ke matsanancin faduwa ta kwantar da murya tace "Kasan dai bazan yi maka karya ba...ka tambaya kaji"

Murmushi ya juya yayi mata sannan ya gyara muryarsa domin ta saki jiki yana dariyar yadda ta tsorata "na yarda dake Schatzi, kuma nima gaskiya da aka fada sai da naji kunya nace bazan iya ba...."

Wani irin numfashi yaji ta sauke saboda samun relief ta gyara zama harda kwantar da kanta akan seat. Murnar da ta fara bata yi dogon zango ba taji yace "..to amma kwanakin nan duk kin chanja I really miss my Alheran."

Wani abu taji har zuciyarta yana bin dukkan jikinta soyayyarsa tana karuwa a cikin ranta.

Idanu ta lumshe lokacin da ya dan kalleta yana yin kwanar gidansu Arifah domin a nan zasu dauki hotunan. Akan Radhiya ya gaskata soyayya ya kuma san dadin kasancewa da masoyi. Rabuwarsu ta shekaru ukun nan kuwa shine lokaci mafi radadi a zuciyarsa. Dawo dashi tayi daga duniyar da yake neman tafiya ya barta ta hanyar cewa "Chèri nice fa har yanzu"

Sun shiga gidan har yayi parking amma bai bude musu su fita ba ya zuba mata idanunsa "Gaskiya a'a shiyasa dole zanyi inspecting dinki na tabbarar ke din ce da gaske"

Baki ta shiga turawa kamar karamar yarinyar ya kasa hakuri sai da ya saka yatsansa yana shafar dimple dinta a sanyaye yake cewa "tawa Alheran din bata ganina ta kasa magana...I miss wannan 'yar kauyen me yawan kuka da dariya akan Hammanta, Schatzi dina da muke ci daga plate daya da spoon daya, muke shan abu mu ragewa juna. I miss 'Yar soja saboda ni ita ce wadda na kamu da sonta lokacin da na fara hada ido da ita. Idan zaki dawo min da ita yanzu I promise you babu wani inspection da zanyi....atleast for now" ya kare da kashe mata ido.

Kalamansa sun tsaya mata a rai taji kamar su dawwama a cikin wannan yanayin. Kallon da yake mata mai kashe jiki ne ta gaji dashi saboda yadda ta rasa sukuni gabadaya ta hura masa iskar bakinta daf da idonsa ya kifta idon tayi baya da sauri tana masa dariya.

"Gaskiya ta kare maka sosai Hammana"

"Na sani Alheran, daga ranar da na ganki da wannan kwal....."

Saurin fita tayi daga motar don tasan me zai ce. Ita kuwa babu lokacin da ko tuna shi idan tayi sai taji matsananciyar kunya kamar farkon haduwarsu a falon Mama. Fuskarta da alamun bacci ga kai a aske. Bayanta ya biyo yana cewa ta saurare shi ita kuwa ta ki suna dariya wata mai aiki ta kaisu falon da Yousuf da Arifah suke baje kolin soyayya suna jiransu.

Arifah rungume Radhiya tayi suna murna sannan ta ja hannunta zuwa dakinta inda wata mai kwalliya take jiransu. Jaka ce guda biyu iri daya sai dai kala da ta bambanta Arifah ta mika mata farar ita kuma ta dauki cream.

"Ga kayan da zamu saka kuma an nanata min yadda suke a jere har kasa haka zamu rinka dauka" tace tana murmushin yadda suka yi da Yousuf kafin zuwan su Awwab.

"Ina mamakin yaushe suka sayi kayan da dinki" cewar Radhiya.

"Nima tambayar da nayi kenan. Amma wurin telan nan da muka kaiwa dinkin biki suka kai. Yanzu dai tashi mu shirya"

"Muje na fara gashe da Mom tukunna"

"Tun safe ta fita maybe ta dawo kafin mu gama"

Kayan saman suka fara daukowa tare da fadawa mai kwalliyar kada tayi musu heavy make up. Atampa ce ja da zanen fulawa manya navy blue anyi musu riga da skirt fitted a cikin kayan akwai dan karamin kwalin fashion sarka da dankunne ja sai mayafansu kashka mai stones navy blue. Kowacce cikinsu ta kasa boye farincikinta suna murna kai kace yara ne. Duka kayan da mahadinsu na mayafi da sarka. Babu bata lokaci aka tsara musu kwalliya kowacce tayi kyau. Daurinsu ma iri daya ne mai hawa hawa su ka dora mayafan a kafadunsu.

Ga mamakinsu Awwab da Yousuf suna sanye da blue jeans da red shirt mai dogon hannu. Radhiya dai hawaye take neman yi saboda yadda Awwab yayi surprising dinta yayi matukar burgeta da shiga rai.

Mai hoto yace idan sun shirya shima fa ya shirya. Hotuna suka yi sosai kowanne couple sunyi su kadai sannan anyi musu tare. Kayansu na biyu shadda ce ta matan orange ta mazan kuma combination din orange da fari sun sha hula. Nan ma kamar wancan kowa yayi da matarsa sannan sunyi tare. Sai kaya na uku matan lace doguwar riga anyi aiki a gaban na mazan ma irinsa ne dinkin yarbawa harda hularsu. Wannan gudunmawar Raji ce mijin Zahra kayan sun amshi kowa aka yi hotuna ana zolayar juna. Kayan karshe abaya ce hadaddiyya kowa ya nemi kalar da matarsa tafi so amma design iri daya. Na Radhiya light green na Arifah light purple (lilac). Ango Awwab yasa yadi irin mai shara sharan nan light green amma babu hula shi kuma Yousuf lilac. Idan ka kansu kamar kada ka dauke ido. Sunyi matukar kyau aka karasa musu hotunan Yousuf ya nanatawa mai hoton zasu zo da daddare su nuna masa hotunan da su ka zaba da kuma jerin yadda suke son ayi musu slide show din.

Ko a nan kawai amaren sun san mazansu sun karramasu sun nuna musu soyayya. A daki Arifah take fadawa Radhiya abinda Dad dinta yake yawan fada mata tun bayan da aka daura auren.

"Akwai ranar da zaki ji wai me ya sameki ne kika rasa mijin aure sai wane saboda kawai ya bata miki rai. Shima watarana zaiji kamar ya rufeki da duka don takaicin wani abu da kika yi ba daidai ba. A irin wannan lokacin babu abinda ke rike igiyar aure kamar idan kuka tuna memorable moments din da kuka gina lokacin ganiyar soyayya. Saboda haka kowa ya sami dama yayi kokarin nunawa dayan cewa they are special"

Radhiya ta jinjina kai tace "Sis to mu me zamuyi musu?"

"Ki bari a gama biki yanzu dai sunyi mana one-zero."

Wayar Awwab ta katsesu Radhiya tayi hanzarin mayar da kayan da tazo dasu ta dauki jakar kayanta ta sauka. Abinci aka gabatar musu wanda Arifah tasa aka shirya amma kunya ta hanasu ci. Plate Awwab ya samu ya zuba musu shi da Radhiya ya rike hannunta su ka koma wurin wasu kujera daga can gefe guda. Yousuf yace masa ya kyauta dama bashi da niyar barin Arifah ta tashi bata ci komai ba.

Yadda suka saba kama-kama da spoon daya Awwab da Radhiya suka yi a haka aka ci abincin sannan suka tafi tare da Yousuf ya sauketa a gida.

***********

Ana saura kwana biyu fara events din Jos wanda kowa zaije banda Radhiya ance itama amarya ce. Tayi magiyar har Awwab ta roka yace tayi hakuri ba yinsa bane amma idan ta shirya ya kama musu masauki shi da ita sai su tafi tare. Da jin haka tasan hakuri ya zame mata dole ta gama rigimarta da shagwaba ta sallama. Sai gashi Zayyana da Rahima suka ce mata zasu zauna da ita su ma sun fasa zuwa. Ummi kuwa tace basu isa ba ya zama dole a karrama iyalin Excellency. To karshe dai Fauziyya ce ta fake da laulayi ta zauna tunda kwana biyu ne zasu yi kuma dai ba son tafiyar take ba. An gama wannan shawarar washegari ya kama ranar da za'a mayar da Rahima asibiti. Ido ya sace kamar bashi ba amma kuma yana ta ruwa.

Ummi ta shirya zasu tafi da Emzee da Ibrahim shiru bata sauko ba Emzee ya hau sama kiranta. A falon saman ya ganta zaune akan kujera ta dafe kai tare da runtse idanu.

"Ummi..." yace a tsorace ganin tana ta runtse ido "baki da lafiya ne?"

Hannunta ta dago masa tana son ya taimaka mata ta tashi "tun dazu nake jiran wani ya hawo, taimaka ka mayar dani daki jiri ke dibata sosai"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull