Kenza eBookz

Batuol mamman complete novel - Chapter 63

Batuol mamman complete novel - Chapter 63

Batuol mamman complete novel Chapter 63: Batuol mamman complete novel Chapter 63. Yana zaune a dakin Jume kan tabarma yana cin abincin da ta dafa masa da…

3,346 words

Yana zaune a dakin Jume kan tabarma yana cin abincin da ta dafa masa da kanta suna hira. Abin mamakin da ya gani bai wuce sabon fenti ba ciki da wajen gidan ana ta gyare gyare wanda yawanci jikokin gidan samari keyi.

"Wai ni wannan gyaran Jume waye zaiyi amarya ne?" Zayyan ya tambayeta yana dariya.

" 'Yan uwanka ne suke son yin gyara saboda bikin Alheran mana. Ita ce fa jikar farko ta bangaren namiji a gidan nan ka ga kuwa mune da biki"

Dadi yaji sosai "Allah Ya saka da alkhairi Jume nagode"

Dan harararsa tayi "meye haka kamar wanda aka yiwa wani abu. Kai dai ka gama ci ga 'ya kayayyaki can da suka hadawa amarya."

"Harda wata wahala kuma?"

"Ashe ba 'yarsu bace indai abinda suka yi sunansa wahala"

Saurin bata hakuri yayi ya gama cin abincin sannan ya mika mata wata leda mai kauri. Budewa yayi ya dauko kullin kudi guda uku kowanne dubu dari biyar biyar yace gashi nan ta bawa yayunsa Badaru, Rayyan da Maikudi. Sannan ya dauko kananun kullin su kuma dubu dari bibbiyu ne yace na matan ne su ma su uku. Wannan duk cikin kudin da aka bashi ne wanda yake ganin idan bai nemi lada ya raya zumunci dasu ba yayi asara kuma bai godewa Allah da ya dawo dashi gida lafiya ba.

Jume sai kwalla tasa zani ta goge "Zayyanu da wane bakin zanyi maka godiya kuma in cigaba da rokon yafiya akan zaluncin da nayi maka?"

Baya son tana yi masa haka domin uwa ya dauketa "kisa min albarka kawai Jume abar maganar. In Allah Ya yarda ke kuma hajjin wannan shekarar zamu je dake da Mairama"

"Ayya...ayya Zayyanu...Allah Ya jikan Innarka da Malam. Na cutar da baiwar Allahn nan ashe nice da moriyar danta" tace tana kuka sosai. Cikin wanda ta ya fara bata na dubu dari biyar din ta dauko ta mika masa kuma tana sane saboda ta gano Maikudi ya taho dakin amma ya tsaya daga waje saboda ya hango Zayyan.

"Wannan ka rike kayanka Zayyanu don wallahi ko kwabo bazan baiwa Maikudi ba."

Da sauri Zayyan yake dubanta "haba Jume me yayi zafi haka?"

"Komai ma. Zayyanu komai da komai yayi zafi daga lokacin da Maikudi ya danne dukiyar marayu sannan saboda bakin hali da tsantsar mugunta ya aika da sakon mutuwarsu har Nijar ya dakile masu tallafa musu"

Maikudi yana daga waje yaji kamar ya rafka ihu. Shigowa yayi ya rakube a gefe ya durkusa amma ya kasa cewa Jume da kanin nasa komai. Ita kuwa kallon banza take masa saboda irin abubuwan da yayi da irin yadda itama ya rainata.

"Saboda kaji ana zancen kudi shine ka taho ko? Ka gani..." tace tana dorawa Zayyan kudinsa "to na bashi kayansa ban kuma lamunce ya baka ba ko da a bayan idona ba. Yau ba don dawowar abokansa ba ina da yakinin haka za ka yi ta gina kanka da dukiyarsu batare da nadama ba"

Zayyan kama bakinsa yayi tunda ita da danta sunfi kusa. Ba don zumunci domin Allah ake yinsa ba ko inuwar Maikudi bazai sake kallo ba. Mutumin da baiji tausayin matar da akace mijinta ya rasu ba ga danyen jego. Mutumin da yayi amfani da emotional sentiment din Mairama yasa ta hakura da takardun gidan mijinta akan wasikar da ya bar mata kafin ya tafi. Zumunci akwai dadi akwai wahala sai mutum ya daure ya kai zuciyarsa nesa.

Wayarsa yaji tana vibrating ya dauko sai lokacin ya kula da missed call din Radhiya da na Emzee. Tashi yayi ya saka kudinsa a aljihu yace da Jume yana zuwa. Wurin dakin Innarsa yaje ya tsaya zai kirasu Maikudi ya biyo shi da sauri. Dukar da kai yayi saboda mugun kwarjinin da Zayyan yayi masa.

"Yaya akayi?" Zayyan yace da dakakkiyar murya.

Kamar wanda aka tsuma a cikin ruwa don kunya Maikudi ya dago kai yana hada hannuwa "Zayyan ka duba girman zumunci..."

"Wannan ka biyo kenan Maikudi..." ya zura hannu ya dauko kudin ya mika masa "gashi na riga nayi niyya dama"

Ja baya Maikudi yayi "ba kudinka nake so ba Zayyan. Nasan akwai kunya in kalli idanunka ko na iyalinka in roki gafara amma ku taimaka don Allah. Kawu Aminu yace dama akwai ranar da zanji kunya gashi ko shekara baiyi a kasa ba lokacin yazo"

Zayyan yaji wayarsa ta sake vibrating kallo daya ya yiwa Maikudi yace " 'ya'yana suna bukata ta zamuyi magana anjima"

Bai jira cewarsa ba ya daga wayar gabansa ya fadi saboda jin muryar Radhiya tana kuka.

"Daada" tace lokaci guda tana kara sautin kukanta.

Faduwar gaba yaji sosai da sauri ya rinka watsa mata tambayoyi "Alheran menene? Ina Umminku? Me ya faru?"

Salame na jin ta ce Daada hankalinta ya sake tashi don Zayyan ne mutum na karshe da zata so yasan wannan abu. Jikinta ya hau bari musamman da idanunta su ka sauka akan Alhaji Indararo da Maman Danmama. Radhiya ko a jikinta sai ma kara kwantar da murya da tayi.

"Ummi tana gidan Malamijo"

"Ke kuma kina ina?"

"Gidan Gwaggo Salame" ta fada tare da kara sautin kukan kamar lokacin ma dukanta ake yi.

Cikin fada yace "Can nace kije ko nan mijinki ya tura ki?"

"Kiji tsoron Allah Radhiya me nayi miki kike kara kuka haka" Salame tayi maganar tana komawa kalar tausayi sosai.

Shi kuwa Zayyan kukan 'yarsa har kokon ransa yake jinsa. Lallabata ya koma yi don yaji me ya faru "Alheran dena kukan ko waye ya taba min ke ba kyalewa zanyi ba"

Ba kunya ta sakarwa Salame murmushi sannan tasa speaker ta kure volume din wayar "Daada dukana tayi da wayar rediyo fatar bayana ta cire..."

"Laaaaahhhh kuji min yarinya...ba Rahima nazo duka ba kika tare? Ni ina ruwana da 'ya'yan gidanku me zai kaini dukanku...." idanunta har sun fara tara kwalla saboda wani sauyin numfashi da take iya jiyowa na Zayyan ransa ya soma baci.

"Wai don na gane ashe tana sonka kuma ita ta makanta Ummi don ta auri Alha...."

Salame kasa hakuri tayi tasa hannu ta toshe bakin Radhiya saboda yadda Zayyan yace "ME???" da karfi.

Alh Indararo yana jin haka shi kuma ya wawurota ji kake tas-tas ya tsittsinka mata mari. Zayyan da ya zata tasa 'yar ake duka a kidime ya kashe wayar ya kira Mairama.

Baiwar Allah bata san me ake yi ba tana tare dasu Innawuro ana hira ta dauka. Abinda bata taba ji ba wato Zayyan ya daga mata murya taji a yau. Zai iya hakuri da komai banda taba masa 'ya'ya ba kuma wai don bashi da kara ba sai don yasan wacece Salame a da lokacin da bata ji kunyar kai masa kokon barar soyayya ba alhali yana neman kanwarta. Abu na biyu kuwa bai wuce shekarun da ya kwasa cike da tsananin kewar iyalinsa. Yanzu da ya sami dama ta biyu ba zaiyi wasa da ita yana ji yana gani 'ya'yansa suna zubar da hawaye ba. Bashi da uwa ba uba sai mata sai su. Baya fata amma ya sani ana chanja mata amma jininsa bazai iya taba chanja shi ba.

"Kije gidan yayarki Salame ki dauko min Alheran sannan gobe zanzo na dauketa mu koma gida"

Tashi tayi ta matsa daga cikin mutane hankali a tashe "Sojana ban fahimceka ba"

"Nima ban fahimta ba Fillo.."yace cike da damuwa "Alheran ta kirani yanzu wai Salame tana dukanta da wayar rediyo...."

Ko karshen zancen bata tsaya ji ba ta koma ciki da sauri danunta sun kada sunyi ja. Nanatawa take yi yau ko ita ko Salame...ta gaji da wannan halayya da take nuna mata. Rahima ma a yanzu ba bari zata yi ta tabata ba bare kuma Radhiyanta. Wani dauke kai da take yi akanta ba shine yake nufin bata son abarta ba. Bata hada son 'ya'yanta da komai sai dai sanin rayuwa da kyaun hali yasa bata sangartasu da soyayya ba.

"Mairama ina zaki haka lokaci guda kin fita hayyacinki" cewar Yadikko tana tasowa ta riketa.

"Gidan Salame zani Yadikko. Kuzo muje kuyi shaida ayi min tsakani da ita domin na rantse zan nuna mata duk abinda nake yi ba wai rashin sanin ciwon kai bane. Idan zumunci dani ne bata so a yau ni da kaina zansa wuka na datse shi uban kowa ma ya huta"

Mama cire DK tayi da take shayarwa ta mikawa Laila ta dafa Mairama "kiyi hakuri ki fadi me tayi miki"

Kowa ya ga Mairama yasan tana cikin bacin rai dama ga ta da zuciya. Hakurinta da yawan kau da kai shine yake sawa a ga kamar bata da fushi.

"Babansu Karami ya kirani yanzu wai Salame tana dukan wannan yarinya da wayar rediyo"

"Me kika ce?" Malamijo yace da sauri yana nufosu. Hayaniya yake ji har soro shine ya fito.

Cikin kankanin lokaci Malamijo, Nene Marka, Yadikko da Hajjo su ka hadu da Mairama zasu tafi gidan Salame kowa ya kasa gane me yake faruwa. Mairama ta kira Radhiya amma tana dauka kuka kawai ta rinka yi bata ce komai ba. Zasu fita ta ga Mama Zainab a tsaye bata da niyar binsu.

"Yanzun nan in fada miki ana dukan 'yarki amma ki tsaya a nan Zainab" cewar Mairama.

Gani tayi abin ya shafi danginsu bai dace ta tura kai ba "Kuje ku dawo Ummin Awwab"

Fushin nata kan Mama ya nemi komawa tana ta kumburi tace "kada kije din...kuma sai na fadawa Mami" fuuuu tayi gaba tana sababin da babu wanda ya santa dashi.

Nene Marka tace "maza Zainabu dauko mayafinki wannan 'yar uwar taki bata iya fushi ba ko kadan"

Duk da babu nisa motar Mairama suka shiga sabo mutane dreba ya ja su.

**********

Bayan marin da Alh Indararo ya rinka saukewa Salame zuciyarsa a sama har yana haki ya nuna ta yatsa "naji komai kuma nasan komai. Sai yau na fahimci yaya akayi na aureki Salame"

Radhiya gefe ta koma abinta bayanta na zugi tana jiran isowar su Ummi saboda Daada yace ta jira gasu nan zuwa.

Kuka yaki zuwar wa Salame sai kumatunta duka biyun da ta rike zugi da radadi na shigarta.

Cigaba yayi da fadansa sa'arsu daya babu yara a gidan kamar anyi shara. Dama na Salame ne masu zama su ma yau Radhiya tayi musu jan ido babu ko daya.

"Lallai biri yayi kama da mutum. Salame ko ina shan giya me zai kaini aurenki bayan tun kina gidan Idris na sanki. Sau nawa nake bawa matana labarin yadda yake zuwa wurina neman bashi saboda ya auri hatsabibiyar mata mai bani-bani wadda ta raina shi. Kinsan talaka ne amma kike amfani da son da yake miki kika tatike shi. Ranar da zaki haifi Rahima ma idan baki sani ba ni na bashi aron mota aka kaiki asibiti. Sannan ragon suna da kika matsanta masa shima bashi ya nema a wurina sai da ya shekara uku ya iya hada min kudin ragon."

"Alhaji me ya kawo wannan tone-tonen? Kada kace ka yarda da zancen yarinyar..."

Mugun kallon da ya jefa mata yasa ta koma tayi lakwas "Salame kyan dan maciji asirinki ya tonu" ya nuna Maman Danmama "ga uwargidana nan ki tambayeta ko da Mairama ta makance nan nazo na fada musu matar da zan aura ta sami matsalar ido kuma tana da marayu. Idan ta tare duk wadda ta cutar da ita a bakin aurenta. Amma duk wannan abu lokaci guda naji zan iya rabuwa da kowa a kanki Salame. To albishirinki aikin boka yayi ci da kyau domin ke da gidan nan sai dai kiyi min takaba ko a fitar da gawarki. Kinzo kenan 'yar kundun uba"

Wayar da ta gama dukan su Rahima da ita ya dauko daga kan kujera ya daga kawai ya shiga lafta mata. Saukar farko Salame ta zabura za tayi rawar 'yan bori. Ashe ba dadi ta sa matar da ya saki karshe sai da yayi mata dukan kawo wuka kawai saboda ta dakar mata 'ya. Dukan da yake mata ya soma firgita Radhiya da uwargidansa duk haushinta da suke ji Radhiya sai ta sami kanta da janyo Salame bayanta yayin da Maman Danmama ta rike hannun Alhajin yana ta kumfar baka yana masifa kamar ya ari baki.

Numfarfashi Salame take saukewa su ka ji sallama daga waje wadda mai yinta ko ba'a fada ba yana cikin bacin rai ne da fushi. Ba'a dena sallamar ba cikin daga murya tare da dukan kofar gidan a fusace.

Alh Indararo shima cikin bacin rai ya fita yaci karo da Idris rungume da 'yarsa Rahima idonta daya ya kumbura ga shatin waya yayi bororo a rabin fuskarta har wurin idon da samansa.

Mutum mai hakuri ba sawa ba fitarwa irin Baffan Rahima yau shima an kure shi karshe ko gaisawa basuyi ba ya soma fada "Billahillazi huwar Rahmanu Alhaji ka gargadi matarka idan ba haka ba zan tube rigar mutumci in shiga har cikin gidan nan inci mutumcinta. Dubi wannan diban albarka da ta yiwa Rahima. Yau yarinyar nan ko zaman kishi suka yi da uwarta a yanzu da babu aure a tsakaninmu bata cancanci wannan abu ba bare kuma 'yar cikinta."

Saukowa Alh Indararo yayi saboda yadda yarinyar ta bashi tausayi "dakata muyi magana Baban Rahima"

"Wace irin dakatawa zanyi? Kullum da fargaba da komai ni ko Iya muke matsanta mata tazo gidannan saboda uwa uwace komai lalacewarta. Babu ranar da Rahima bazata dawo min gida da hawaye ba amma yau ka duba ka gani don Allah. Dubi yadda fuskarta ta koma daga zuwanta"

Motar su Mairama ce ta tsaya suka firfito gabadayansu. Kafin su karaso Rahima ta kwasa a guje ta rungumeta tana kuka mai ban tausayi. Hajjo ce ta fara ganin fuskar ta dago kanta da sauri. Mairama ma ta gani a tsorace tace "meye wannan Rahima?"

"Umma ce ta dakeni"

Mairama cije lebenta kawai tayi ta damki hannun Rahima ko Alh Indararo da Baffan Rahiman bata tsaya yiwa kwakkwaran kallo ba ta shige cikin gidan tana cewa "SALAME kina ina?". [5/22, 11:03 PM] Sis Ruky: Tare suka yi girkin amma Rahima ce karfin aikin. Yaran gidan sai binta suke da kallo ita dai kanta na kasa har suka kammala. Baffanta ne ya kira Ummi ya sanar da ita inda zata kwana kada suji shiru. Addu'a ta rinka yi Allah Yasa kada wani abu mara dadi ya biyo baya.

Lura Salame tayi da yadda Rahima take tsakurar abincinta. Tuwon masara ne da miyar karkashi sai tashin daddawa take yi ga sukunbiya an saka saboda ita. A cikin kwanon silva ta zubawa Rahima ta kwarara miyar a kai.

Sai da ta gama lashe hannunta ta bi irin abin miyar nan da ya kan makale a tsakanin hakora da harshe tana sakato shi sai ji kake tana tsk-tskk da baki ta kora da ruwan rijiya sannan ta tabe baki.

"Abincin namu bai kai na 'Yan Abuja dadi bane naga kina ta yafita kamar bakya so?"

Kafin ta kai karshen maganarta Rahima ta zunduma wata katuwar loma wadda ta kasa hadiyewa saboda bata kaunar karkashi ko kadan. Da gudu taje bakin rariya ta zubar ta dawo tana jiran Salame ta soma fada sai taji tayi mata magana babu wannan fadan.

"Ba kya cin tuwo ne?"

"Miyar...miyar ce dama...dama karkashi ne....bana sha"

"Yo maimakon ki fada nayi miki hadin mai da yaji sai ki cuci kanki? In kin fada min ai ba dukanki zanyi ba" tace da ita amma idan kaji yadda muryarta ke fita sai ka dan tsorata. Takaicin yadda yarinyar ke zabura duk motsinta ne yake damunta. Kwanon ta dauka ta mikawa sauran yaranta da gudu suka far masa dama sun cinye nasu ita kuma taje kitchen ta dibar mata wani cikin sauran da zasuyi dumame dashi da safe. Mai kwantirola ta yaryada mata da gishiri ta dauko yaji da rabin maggi a dakinta ta saka sannan ta bata. Ko kadan wannan hadi bai yiwa Rahima dadi ba saboda man danye ne sai karni ke tashi amma kyautatawar da mahaifiyarta ta gwada mata karon farko tun wayonta yasata yin kwalla ta janyo farantin ta cinye shi duka.

Basu wani jima da gamawa ba Alh Indararo ya dawo gida Salame ta kai masa nasa abincin. Kayan jikinta tun na jiya ne babu zancen wanka a ajandarta duk kuwa da cewa da murhu tayi girki ga kauri ga datti. Tunda ta shiga banda harara da habaici babu abinda yake mata ya gama cin abincin yace ta fita kada ta sake zuwa turakarsa da sunan kwana sai idan da kansa ya nemeta. Abu na biyu kuma ya bata lokaci kankani ta san yadda zata yi su daidaita da Mairama a basu ko da mutum biyu ne cikin yaran shi ma a rage masa nauyi.

Kallon raini ta bishi dashi "wannan shi ake kira karfin hali barawo da sallama."

Hannu ya kawo da sauri zai sauke mata ta fita ba shiri yana ta fada kuma wai kashin tsiya gareta kada ya kuma ganin kafarta a dakin. Dama waye ya aiketa bayan jiya ya mata dukan nan jiki yayi tsami. Dakinta ta koma aka yiwa yara shimfida Khadi tana gado tace da Rahima.

"Kwaba lallen kizo ki yayyaba min dashi zan kwana saboda ya kamu sosai"

"Kada ya cabe ko ba mai ado kike so ba?"

"Ado kai 'yan nan. Kada ki damu zan iya kwana dashi."

Duk yadda idonta yake damunta bata nuna ba ta kwaba lallen nan ta zauna. Wayarta ta soka a gaban dankwalinta bayan ta kunna torchlight saboda rashin wuta sannan ta kamo kafar. Dandakuwa sunan wani abu. Ga datti da wani maiko maiko ga yalwataccen kaushi yabi ko ina a cikin kafar babu inda babu. Kamar ta ce mata ko zata wanke kafar amma babu fuska sai uwar hamma da Salamen take yi. Ba yadda ta iya haka tasa kasan zaninta ta goge kafar sosai sannan ta baje basira ta soma zane. Goma ta wuce ta gama Salame tace mata ta kwanta a daya gefen ya zamana Khadi na tsakiyarsu. Da kyar ta iya bacci saboda rashin sakewa da sabo. Asubar fari kuwa ta mike ciwon ido yayi sallama ya kara nauyi tana ruwa. Alwala ta dauro ta zo ta tashi Salame ta kwashe mata lallen ta goge hannuwan da kafafu sannan itama tayi alwalar. Tun a lokacin tana iya ganin yadda lallen nata ya fito radau yayi kyau musamman hannuwanta. A sannu sannu gurbin da ta danne Rahima a zuciyarta ya fara neman nuna kansa ga duniya. Sai take jin wani takaici da haushin kanta na kin sakarwa yarinyarta tun farko.

Sunyi sallah Rahima ta gaisheta ta amsa tare da cewa ta bude idon da ta rufe mana. Ai kuwa tana ganin yadda ya kuma hadewa gabanta ya fadi. Hakuri ne tun jiya ta kasa bawa Rahima sai yanzu take sake ganin rashin hankalinta. Ruwan kunu taje ta dora da ya tafasa ta debi wani a bokiti tazo ta gasa mata wurin. Babu wani sauki da taji amma abubuwan kyautatawar da Ummanta ke yi mata kadai sun isheta farinciki.

Kafin ta dawo daga dama kunun Rahima ta soma janyo kayayyakin da suke soke a lungu da sakon dakin babu wadatar isa ga zarni da wari duk ya hada. Gari guda ta hada wanki sannan ta soma shara Salame ta shigo. Tunda take dan cikinta bai taba yi mata shara ba. Na gabanta banda cin tsiya da fitsara basu san komai ba. Halifa namiji ne, macen da zata yi kuma ta dauki karan tsana ta dora mata. Bata ce mata komai ba Rahima ta aikatu sai wuraren shabiyu ta gama gyara dakin. Wankin kuwa Salame tace zata yi da kanta.

"Lokaci na kurewa shirya ki tafi gidan Malamijo zan taho anjima ki bar min wankin"

Wanka taje yi bandakin babu kanta sai kawai ta shafa ruwa a fuska da kafa ta fito sauran ta wanke musu bandakin. Da sauri ta shirya suka yi sallama ta fito. Sai yanzu ta saki ajiyar zuciya ta sami nutsuwa saboda duk a tsorace take.

Da zuwanta gidan tayi sa'ar samun bandakin da babu kowa ta nemi ruwan zafi tayi wanka. Ido suntum ta shiga daki wurin Ummi hankalinta ya sake tashi. Abinci ta sa ta ci suka tafi asibiti a cikin garin. Sai bayan azahar suka dawo anyi mata allurai tasha magani ta kwanta bacci.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull