Kenza eBookz

Batuol mamman complete novel - Chapter 66

Batuol mamman complete novel - Chapter 66

Batuol mamman complete novel Chapter 66: Batuol mamman complete novel Chapter 66. Kafin shigarsu iyayen taro suka taho. Kayansu saka iri daya bakin lace na…

3,325 words

Kafin shigarsu iyayen taro suka taho. Kayansu saka iri daya bakin lace na Ummi da sky blue irin shaddar Daada, Mami Caramel irin shaddar Daddy, Mama light yellow irin ta Baba Hadir, Tante Brown irin na Alh Moussa sai kuma na Mom light green irin na Excellency. Idan ka cire iyayen Yousuf sauran hudun zaratan maza ne da suka dandani me ake kira bautar kasa da jiki da lafiya tare da matansu jarumai wurin hakuri da juriya. Taku suke ana daukarau hoto a cikin kayataccen hall din har zuwa mazauninsu. Bayan sun zauna be aka kira angwaye da amare abin gwanin ban sha'awa da burgewa.

Taro ne na manyan mutane komai cikin nutsuwa da hankali ake gabatar dashi. Bayan an bude shi da addu'a aka gabatar da takaitaccen tarihin angwayen da amarensu.

Wani abin burgewa shine kiran Emzee da da MC Kdm yayi a matsayin babban abokin amarya saboda babu wanda yasan Alheran Radhiya Zayyan Tureta sama da shakikinta Muhammad Zayyan Tureta. Zahra ce ya bada tarihin Awwab sai kuma wani abokin Yousuf da kawar Arifah 'yar kanin babanta suka bada nasu.

Can cikin taro akwai 'yan gidansu Zayyan da su Hussaina harda Mummy Gambo da yaranta. Ghazalatu ta shiga wani yanayi na tashin hankali ganin yadda Awwab ya fito yayi masifar kyau. Kallonsa take bata ko kiftawa saboda yadda take jinsa a ranta.

Ana tsaka da taron ne su ka ji wani dummm sai wanda ya sanya Awwab da Yousuf tashi lokaci guda kuma hall din yayi duhu sai haske ya koma bakin kofar shigowa. Radhiya dai taji Awwab ya matse mata hannu kadan sannan a daidai kunnenta yace mata yana zuwa. Idanu fa sai suka koma bakin kofa bayan kamar minti daya da rabi sai ga Yousuf da Awwab sun bullo ta katuwar kofar shigowa. Dukkansu sun cire coat dinsu sai ta cikin mai maballai ta gaba wadda suka dora akan farar shirt din mai dogon hannu sannan sun cire necktie sun bude maballai biyu na gaban shirts dinsu. Sanye suke da homburg hats kalar wandunansu an dan turo ta gaba a karkace.

Yousuf ne ya fara magana da mic a hannunsa daga can gefen amaren ta sama aka fara slide show inda hoton Arifah ya bayyana tana zaune cikin fulawoyi tana murmushi.

Sannu a hankali yake takowa zuwa gareta yana magana cikin harshen turanci duk da dai faransanci yafi zama sosai a bakinsa.

("Thank you Arifah Nasiruddeen for being a part of life. Thank you for accepting me to be the man in your life. You are my Queen the most beautiful woman I have ever seen. To the special you I say I love you")

Ba Arifah ba hatta Mom dinta sai da taji wata kwallar farinciki. Hannunta ya kamo zuwa tsakiyar filin idanunsu cikin na juna a lokacin da Awwab ya soma taku daidai zuwa wurin zaman Radhiya.

("Once upon a time an adorable Angel was born") hoton Radhiya ne ya bayyana ranar sunanta wanda aka daukesu tana hannun Awwab yana murmushi ya dan juyo da fuskarta yadda zata fito a camera ("You and I were always meant to be. I love you with all my heart...just so you know, it has always been Alheran Radhiya. The fearless 'Yar soja, my one and only")

Wannan karon Ummi ce da hawayen ta sunkunyar da kai Daada ya matsa mata hannu yana cewa suyi kusu addu'ar fatan zaman lafiya.

Awwab ma riko hannun matarsa yayi zuwa tsakiyar filin kusa da Arifah sannan ya yi mata murmushi shi da Yousuf suka ja baya. Kidan wakar da matasan wurin da dama suka sani ta Umar M Shareef JININ JIKINA ce ta karade wurin hasken wurin ta koma kan Awwab, Yousuf, Emzee, Ibrahim, Bilal da Raji duka sun ajiye coats dinsu kowa ya tsaya a inda ya dace suka fara takun wakar yayin da baitin farko ya cika wurin.

(Da ganinki sai na kamu.. gashi kin zamo jinin jikinaaaa)

Ba tare da kuskuren taku ko tangarda ba domin sun sha wahalar rehearsal da mai koyar da rawar da suka dauko suke miming wakar suna rawar da ko wadanda suka hau ta a film din bazasu nuna musu komai ba. Mamaki tukuru.a fuskar Radhiya da Arifah yayin da jama'a suke kallon wannan abin burgewa ana ta murmushi da dariyar farinciki.

Can gefen slideshow ake yi na hotunam da suka dauka rannan kowa yana bin baiti ana nuna amaryarsa. Saboda basu taba zato da tsammani ba shiyasa mamakinsu da farinciki yayi musu yawa.

Radhiya sai da taji kamar a wurin ta rungume Awwab ta kwana tana fada masa cewa shi kadai ne farincikinta a rayuwa.

Sai da wakar ta kare a daidai imda suke rawa a tsugunne suna kada hannuwansu su ma su Awwab hakan suka yi wuri kuwa ya kaure da tafi kamar zasu tsaga hall din. Gashi duk yadda manyan nan suka so yin liki an saka wani abu kamar ribbon alamun babu wucewa. Suna gamawa fita suka yi haske ya mamaye wurin MC yace za'a fara cin abinci. Ana ta hayaniya da zancen yadda abu ya kayatar Fauziyya tazo ta ja amaren zuwa dakin da zasu canja kaya. Lace suka saka coffee color da gold head da sauran accessories aka gyara musu kwalliya. Ana tambayarsu yaya suka ji game da babban surprise din su Awwab sai murmushi an rasa me cewa wani abu. To su ce me bayan amgwayen sun gama musu komai.

A wurin shiga suka hadu dasu Awwab da Radhiya na gaba su Arifah na bayansu. Wannan karon shadda suka saka golden babbar riga da hula. Sun shiga kafin su zauna aka canja waka zuwa ta Nura M Inuwa wato 'Yar amanar da Radhiya ke matukar so. Wannan karon kam iyayensu mata sai da suka fito Awwab da Yousuf basu bar komai na irin takun Zango da ya hau wakar ba suna faman baza babbar riga. Liki akeyi kamar ba'asan ciwon kudi ba Awwab ya makale matarsa a gefe ganin wurin babu masaka tsinke.

Taron ya tashi sa misalin shadaya da rabi na dare anyi hotuna anci an sha rayuka sun faranta. Ghazalatu kamar ta hadiyi tabarya haka bakinciki ya tsaya ya tokare mata wuya. Tana ta bin Awwab da ido bata san ta ina ba sai jin Nura tayi a bayanta ya rungumota a waje da suka fito ana tafiya gida. A fusace ta juyo tace masa bata son wulakanci meye haka zai tabata.

"Dazun nan na mayar dake Ghazy" yace yana shafa keya.

Ashar ta dankaro masa saboda tsabar bacin rai. Tana hangen yadda zatayi ta sami Awwab shine don rashin mutumci ya mayar da ita. Ko sauraronta baiyi ba ya jefata a motar da yazo da ita yace mata yau zasu fara angwanci.

Wuri ya watse saura mutane kadan Awwab ya karbi mota a wurin drebansu wadda yada ya kawo masa ya budewa Radhiya. Yau duk ya kashe mata baki da abubuwan mamaki. Babbar rigar ya cire da hula ya dora mata akan cinya kamshin turarensa ya mamaye hancinta ya shiga mazaunin dreba ya tada mota.

Shiru ta kasa magana sai murmushi ya kalleta yace "tunanin me kike yi Schatzi?"

Kafin ta bada amsa ya zame mata gwaggwaronta da ya zauna das a kanta ta ja mayafin da ta ce a saka mata a jakar kayan ta rufe kanta.

"Ke nake sauraro?"

Ido ta runtse ta soma magana a hankali "Hammana bani da wani buri da ya wuce faranta maka. Abinda kayi min tun farkon haduwarmu har zuwa yau bazan taba mantawa ba. I love you with all i've got. Alheran is never complete without Awwab. Nagode, nagode, nagode" ta daga hannunta mai zoben da ya saka mata ta sumbata.

Hannunta kawai ya kamo ya rike a haka ya kaisu gida suna kallon juna suyi murmushi. Ita kuwa harda sunkuyar da kai.

Kusan kowa ya dawo ga motoci nan birjik a ciki ya samu wuri yayi parking.

Rigarsa da hular ya dauke daga cinyarta ya jefa baya inda ya cilla mata gwaggwaro sannan ya juyo da jikinsa yana fuskantarta ya jinginar da kansa gefe.

"Baby" taji yace a hankali sai da tsigar jikinta ta tashi.

"Uhmm"

"Na gaji sosai"

"Ai dole ka gasa jiki ko ka kasa tashi gobe" ta fada gabanta na faduwa.

Hannunsa ya mika mata duk lokacin yana kallonta tana jin idanuwansa a jikinta ta dukar da kai tana wasa da yatsunta da suka sha lalle. Sai da ta sake jin sabuwar faduwar gaba ta mika masa hannun damanta.

Tayi zaton rikewa kawai zaiyi ashe hanya ya nema ya janyota gabadaya jikinsa tana kan cinyarsa. Rungumeta yayi sosai yana sauke numfashi ta soma mutsu mutsun son tashi.

"Kinga" yace yana jan wani dan compartment a gaban motar tayi arba da mukullai "na gidanmu ne, ko dai ki nutsu ko na juya kan motar a biyoki da kayanki gobe"

Da sauri tace "Kai Hammana"

"I am serious baby na gaji sosai...mun kusa wata da aure da yanzu kin fara amai da tashin zuciya...."

Salati ta soma yi kunya kamar ta nutse a wurin "ni dai babu ruwana"

"Da nawa ni kam please ki bani janbakin nan na goge miki ko kuma mu tafi gidan"

A tsorace tace "idan wani ya ganmu fa?"

"Baki ji nace janbaki zan goge ba...haka zamu fada musu ai" ya sake yi mata wani irin riko.

"Wannan fa wayo ne"

"Ki bari nayi miki wayon mana" ya kyabe fuska shi a dole zaiyi mata shagwaba.

Dariyar da ta soma yi ya datse da bakinsa tun tana jin tsoro har ta biye masa suka manta a cikin gidan Daada suke. [5/22, 11:03 PM] Sis Ruky: Cikin Salame kullewa yayi da ta ji muryar Mairama. Yau ko ba'a fada ba ta sani cewa kashinta ya bushe ta kure kanwarta ta. Radhiya kuwa da sauri ta iso bakin kofar dakin idanu sunyi ja sun kankance.

Ummi na ganinta a haka taji hankalinta ya sake tashi yau 'yar kunyar ma babu ta janyota jikinta za ta dubata ta saki siririyar kara saboda bayanta da aka taba.

Ai kuwa da sauri Ummi ta zaro idanu ta juya Radhiyan ta dage rigarta. Ga farar fata ga gyaran da take sha jiki yayi mugun laushi shiyasa wayar tayi mata wani dogon layi da yake tsartuwar jini daga tsakiya. Ruwan bala'i da masifa yau sun tarar wa Mairama ta kama hannun Radhiya ta hada da ba Rahima.

"Kama kanwarki kuje Lucas yana mota ya kaiku MHC"

Mama kallo daya ta yi a kofar dakin ta hango Salame kamar kaya jibge a kasa tayi saurin jan hannun Rahima saboda duk lalacewa baza su so ta ga mahaifiyarta a wannan halin ba. Da taimakonta suka kama Rahiman saboda ta fi Radhiya jin jiki suka fice. Itama bata son ayi a gabanta gara yau dai suyita ta kare a gaban mahaifinsu.

Dama jiran fitarsu Ummi take yi tausayin Rahima ya dakatar da ita. Dakin ta banka kai ciki a fusace Salame ta mike da kyar.

Cike da bacin rai da masifa Ummi tace "zuwa nayi mu saukewa juna iskokan dake kanmu Salame saboda na dade da fuskantar cewa kanki yana da matsala"

Wai saboda karfin hali tana kallon kowa a tsaye ta kumburo baki "saboda na daki 'yar gwal shine kuka yo min taron dangi..." waje tayi sai ta tsaya turus gani ashe harda Malamijo da Nene, ga su Yadikko da Hajjo. A zatonta Mairama ce kadai da Baffan Rahima da ta gano tare da Alh Indararo shima tana jin ramawa tasa 'yar yazo yi. Bude baki tayi za ta sake yin magana Malamijo ya kai mata wani wawan marin da bazaka taba kawowa a ranka dan hannunsa zai iya ba. Hannu ne na tsohon kashi ya sake bata a kumatun hagu. Wasawasa sai da yayi mata yafi biyar wani tukukin bakinciki yasa ta kasa kuka.

"Ke mahaukaciyar ina ce Salame? Na fuskanci burinki bakincikinki ya kaini lahira to amma baki isa ba. Ko Amiru da yake yawon jagaliya bai samin bakincikin da kike kunsa min ba"

"Duk wannan abin akan Radhiya ne saboda ita kuna kaunar uwarta tunda babanta yana da kudi ko"

"Rufewa mutane baki mutuniyar banza" cewar Nene tana jin kamar ta maketa.

Jan bakinta tayi ta tsuke kowa a tsakar gidan ita yake yiwa kallon da take fassara shi da tsana.

Mairama ta dubi iyayen nasu "Malamijo yau gani ga ka ga kuma babbar 'yarka. Ban san me nayi mata ba tsayin shekarun nan tun farkon aurenmu amma wallahi na gaji. Daga yau sai yau idan ta kuskura ta sake taba min yara zan dauki matakin da mu duka nan sai ran kowa in yayi dubu ya baci." Ta mayar da idanu ga Salame "Wai da nake ta taraki ki sani ba tsoro bane kawai ina yi ne da sa ran wata rana zaki ajiye makaman yakinki mu zauna lafiya. Amma tunda kince ba haka ba mu zuba nida ke shege ka fasa. Duk wani zafin rai da kike takama dashi kin kwana da sanin Mairama tana da dubunsa a ajiye"

"Kinga malama ni dai ba da niya na taba Radhiya ba. Rahima zan daka ta tare wayar ta sauka a bayanta ko ba haka ba?" Ta tambayi iska tunda babu mai bata amsa jikinta yana kadawa kada a cigaba da maganar nan allura ta tono garma.

Malamijo zaiyi magana Mairama ta riga shi "assha 'yar uwa, kada kiyi tunanin dukan Alheran kadai ya kawoni ko daya. Gobe kafin wannan lokacin zaki baiwa ubanta bayanin dalilin dukan masa 'ya, kuma kada ki manta matar aure ce ban san me zai faru ba idan mijinta ya ji. Wannan diban albarka da kike yiwa Rahima kadai ya isheni. Don ta ni kin dade baki yi min rashin mutumci ba. Ranar da duk na gaji na fyatoki ba ganuwa zakiyi ba"

Dariyar Alh Indararo ce ta katse Mairama "wai ke nan duk masifar akan dukan da tayiwa Rahima ne dama? To ni tunda na auri Salame ban taba ganin yarinyar nan ta shigo gidan nan ta fita babu kwalla a idonta ba. Wannan kuma kadan ne cikin abubuwan da tayi miki"

"Me kake nufi Alhaji? Wai me kika dauki Rahima ne Salame?" Baffan Rahima ya tambaye shi a zatonsa ta yiwa 'yar tasa abinda yafi wanda ya gani "yanzu ashe alkhairi zai iya zama sharri, sharrin ma ka rasa wanda zaka yiwa sai dan cikinka. Kudine dubu dari da 'yan kai Rahima ta kawo tace min a Habuja tayi lalle ta samu. Shine aka raba kudin ni talatin itama uwar aka ce ta kawo mata talatin sauran kuwa zamu fara yi mata tanadin aure. Shikenan daga zuwanta ta dawo min gida da fuska a kumbure" ya kare zuciyarsa a karye saboda shi ba ma'abocin fada bane. Mutum ne mai kyaun hali da matukar hakuri. Kaddararsa daya bata wuce soyayyar Salame da tayi masa mugun kamu ba ashe rabon haihuwa ne yasa ya aureta.

Maganganunsa ba karamin shigar Salame tayi ba sai lokacin ta sake kallon ledar da Rahimar ta yar saboda marukan da ta sha. Kenan Mairama sake bawa Rahima wani kudin tayi a madadin wanda ta karbe? Wani abu taji yana neman danne mata zuciya sai dai bata yi nisa ba ta tsinkayi muryar Alh Indararo yana cewa "wanda bashi da kashin arziki ko a cikin rijiyar kudi zaka tsoma shi bazai taba yi ba. Nan ta dawo da kudi dubu dari tana yi mana burga wai 'yarta ta fara sana'a. Ci banza ci hofi bana jin akwai sauransu yanzu ma."

Kallon banza Mairama ta watsa mata saboda da gani babu abin tsinta a jikin Salame bayan tsiya tsagwaronta. Juyawa tayi da zummar fita daga gidan Alh Indararo ya ga idan yayi shiru ai wasa ya kare bayan ko rabin tanadin da ya yiwa Salame na bakinciki bai idar ba. Fada sosai Malamijo da su Nene suke yiwa Salame shi kuwa yayi saurin tsayar da ita.

"Mairama ince ko kina da masaniyar cewa duk wannan rashin hankalin da Salame take yi miki tana yi ne saboda son mijinki da take yi"

Cak Mairama ta tsaya ta juyo a hankali ta koma gaban Salame ta rike hannayenta duka biyu ta soma yi mata fada tamkar 'yar cikinta "da gaske baki da hankali ne Adda? Ta yaya za'ayi ki bari duniya tasan cewa kina son mijin kanwarki? A lokacin da ake zaton babansu Karami ya rasu babu kunya kika dubi idanuna ina zaman kunci da zafin rabuwa kika fada min kinso shi na hakura ban taba daga zancen ba. Adda Salame a lokacin har tausayinki na ji saboda soyayya bata taba yiwa mutum uzuri sai nake ganin ba laifinki bane." Hawaye ne mai zafi ya ke fito mata saboda rashin sanin wace irin mutum yayarta ta zama "idan kika kuskura kika bari su Halifa suka san wannan abin nayi miki rantsuwa abinda ya rage na kimarki da darajar uwa a zukatansu sai ya tsiyaye ya bi rariya."

Baki na rawa Salame ta iya hada kalmomin "sharri...sharri ne. Sharri yake min"

Tsawa Malamijo ya daka mata "Ki rufe min baki shashashar banza wadda bata san ciwon kanta ba...ko kinsan ko sati biyu bamu rufa ba da nasa Halifa ya hadani da babansa kuma ya tabbatar min dalilinsa na sakinki kenan. Har yaushe zaki cigaba da karar da rayuwarki akan hangen ta wani"

Mairama gani tayi idan ta cigaba da tsayuwa ba mamaki a kwashi Salame a baro saboda ji take yau da ita ce ta haifeta sai tayi mata dukan kawo wuka ko za'ayi sa'a kanta ya dawo daidai.

Abinda Nene Marka take ta gudun fitowarsa Alh Indararo yace "ke kuwa wace irin zuciya gareki Mairama? Ta so mijinki kin sani baki dauki mataki ba sannan ta makanta ki tsahon shekaru shima duk taci bulus kenan? To idan ke kin hakura ni bazan yafe ha'incin da tayi min ba na asirin aurenta ba tare da son raina ba"

Suman tsaye Mairama tayi jikinta yana bari kamar wadda aka kwara wa ruwan sanyi wani irin kallo take yiwa Salame ita kuwa sai girgiza kai take yi tana hawaye tare da yarfe hannuwa. Bata taba jin tsoron batawa wani mahaluki rai ba sai yau da take jin ta tsani kanta saboda sabanin kallon tsana ko fushi sai ta ga kallon tausayi sosai Mairama take yi mata. Idanu Mairama ta rufe hawaye suka zubo tasa bayan hannunta share sannan tayi murmushin kafi kuka ciwo. Muryarta tayi mugun sanyi ta dafa kafadar Salame tace

"A kaina saboda ba kya kaunar ganin murmushi a saman fuskata kika yi shirka Adda? Shin Adda kina tunanin zaki iya rayuwar da nayi ne har kika zabi neman yadda zaki mayar da rayuwata taki? Kin taba tsawaita tunani kice Mairama shekararta ashirin da hudu da aure amma har yau bata taba zaman shekara uku tare da mijinta ba har girma ya soma zuwa garesu. Ban san kiyayyar da kike yi min ta kai haka ba amma ina rokonki da ta tsaya a kaina ni kadai kada ki kuma bari ta shafi 'ya'ya. Daga yau kuma nayi miki alkawarin idan har ba bisa lalura ba ko ke kika nema da kanki bazaki kara ganin fuskar Mairama ba bare ta sanya miki bacin rai." Tafiya ta soma yi cikin wani irin kunci mara misaltuwa su Malamijo suka bi bayanta tunda babu wani amfanin jan magana kuma.

Bacin rai sosai Mairama take ji a wannan lokacin. Ita kam bata taba nufin kowa da sharri ba amma ga wadda tafi so duk duniya tun kafin tasan kanta tana neman ganin bayanta. Wanda zai makantaka ko na kwana guda ne ai babban makiyi ne bare wannan shekaru haka cikin kwanciyar hankali.

Da sauri Salame cikin rashin sanin madafa ta bi bayansu ta sha gaban Mairama. Kuka ta ga kanwarta tana yi sosai fuskarta tayi ja.

"Me kuma ya rage, raina kike nema?" Mairama tace da kaushin murya. Da sauri Salame ta girgiza kai "to bani hanya in wuce don ni da kike gani na haufu cikin uwa da uba bana amai na lashe. Tunda nace kin dena ganin fuskar da kika tsana to kin daina da gaske ba wasa ba" tace tana rabewa ta gefenta ta fita daga gidan.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull