Kenza eBookz

Batuol mamman complete novel - Chapter 72

Batuol mamman complete novel - Chapter 72

Batuol mamman complete novel Chapter 72: Batuol mamman complete novel Chapter 72. Kafin ya kai karshe ta yiwa hijabin masauki akan wata kujerar yaji…

3,350 words

Kafin ya kai karshe ta yiwa hijabin masauki akan wata kujerar yaji numfashinsa ya tsaya na yan dakiku saboda kyaun da tayi masa. Gashin ta ta kama ya zare ribon din ya zuba a bayanta da kafadu. Wannan lallen da tayi yasa kan yayi kyau sosai inda kalar ta fito ya zura yatsunsa a ciki yana rufe idanu.

"I love this Alheran" ya janyota kusa dashi sosai yana yamutsa mata gashin.

A gefen jikinsa ya rabata ya shiga bata naman yana ci shima. A haka suka koshi yace tayi zamanta ya kwashe komai zuwa kitchen. Sauran ya saka fridge ya wanko hannunsa ya dawo. Miko mata hannu yayi yana son ya taso ta kyabe fuska "ai ba'a gama film din ba"

"Brush kawai zamuyi mu dawo"

"To kaje ka fara yi kaine babba"

Dariya ta bashi wai nan wayo zata yi masa ya wuce dakin yayi ya dawo "saura ke"

"Kada ka kashe tv din Hammana yanzu film din ya fara kyau" tace tana tashi bayan bata fuskantar komai a ciki. Ko wuka za'a saka mata bata san me akeyi ba.

"Zama zanyi na gane miki inda kika tashi" ya zauna ta tafi.

Tana rufe kofa ya kashe tv din da fitila sannan ya shiga daki ya rufe kofa.

Ai tana jin motsin shigowarsa jiki ya soma rawa ta gama brush din ta kasa fitowa. Sai da tayi minti biyar ta yanke shawarar ce masa ita fa kallo zata yi kawai. Da kwarin gwiwa ta fito yana waya cikin harshen jamus yaki kallonta. Zaune yake akan gado ya mike kafafunsa ya jingina da pillow. Kofar dakin taje ta murda taji a rufe. Ta sami wuri ta tsaya tana jiran ya gama.

Sallamar mutumin yayi ya taso yana tahowa gabanta na kara faduwa. A tsakiyar dakin ya tsaya ya ware mata hannuwansa yana murmushi tare da yi mata nuni da ka. Babu yadda ta iya ta saki hannun kofar ta taka da sauri ta fada kan kirjinsa. Sun dauki kusan minti biyu a haka kowa da nasa tunanin da yake tattare da soyayyar dayan.

Da yatsunsa ya dago kyakyawar fuskarta a tausashe yace "Babyna guduna kike yi kuma?"

"Film din...." sai kuma tayi murmushi ta kasa karasawa.

"Kema kin san baki da gaskiya gashi kinyi shiru. Muje ni inyi miki tausar tunda kin kasa cika alkawari"

"Zanyi maka"

"Fara saka kayan bacci"

Akwatin nata ya bude babu ko daya na lefenta kuma suna Sakkwato za'a wuce dasu Abuja. Wardrobe ya bude inda ya zuba nasa kayan ya dauko mata t-shirt dinsa tana ta kamshi.

"In saka miki?" Yace yana dariya don yasan bazata yarda ba.

Harararsa tayi "da kayana zan kwanta"

"Schatzi" yace hannuwansa na jindadin yamutsa mata gashi ya rasa dalili ita kuwa da kyar take iya bude idanu saboda yadda take ji.

"Naam" ta amsa a raunane.

"Saka riga ko Ango yayi abinda yayi niyya"

Sakinta yayi ba don yaso ba tana ture turen baki ya fita daga dakin don ta shirya a tsanake. Cikin sauri take komai tana yi tana kallon kofa gashi key din ta waje yake. Rigar ko cinyarta bata gama rufewa ba. Tana fesa turare ya turo kofar jikinta ya soma rawa shi kuwa Awwab rufe kofar yayi ya jingina da bayanta tare da harde hannuwansa a kirji yana kallon Alheran a matsayin matarsa abar so da kaunarsa.

Turaren da ta dauka ta ajiye jikinta yayi matukar sanyi tana kallon gadon tana son zuwa ta kwanta ta rufe jikinta amma bata son yin kwakkwaran motsi a gabansa. Tahowa yayi gabanta yasa hannu a waist dinta ya matso da ita jikinsa da dayan hannun kuma turaren da ta ajiye ya dauka ya feshe mata jiki dashi sannan ya saka hannuwansa duka ta bayanta ya dagota jikinsa ya soma juyi da ita a dakin tuni ta kankame shi tana dariya.

"Please, please, pleeeeaaass ka ajiyeni" tace tana zagaye hannuwanta a wuyansa.

"Sai na cire miki wannan tsoron da yake hanaki sakewa"

"Zan sake....Chéri na sake ma.....Hammanaa"

Ajiyeta yayi a hankali tana jin kamar har yanzu juyin suke yi ta kankameshi tana sauke numfashi. Hannuwansa ta sake ji ta bayanta ya tura yatsunsa cikin gashinta da ya mayar abin wasa yana magana can kasan makoshi "na yafe miki tausar nan fa"

Zare jikinta take neman yi ta kasa saboda rikon da yayi mata a hankali tace "nagode"

Dago kanta yayi yana bin bakinta da kallo idanu a lumshe "gani nayi ko da tausa ko babu bazai hanani abinda nayi niyya ba"

Tsoron ya soma dawowa tace "Wai me kayi niyya ne?"

Wani irin kallo mai kashe jiki yake binta dashi yace "Spending the whole night loving you my baby. Ki taimaka ki bani dama saboda ko kinki bazai hana Awwab abinda yayi niyya ba, bani da hakuri indai akan sonki ne Alheran" kasa yayi da kansa ya soma kissing dinta tamkar ranar ya fara samun wannan damar. Radhiya bata iya sake komai ba sai abinda Awwab ya koya mata. Kamar yadda yace ya nuna mata soyayyar da bazata taba hadata da komai ba a rayuwarta. Bacci kuwa sai can cikin dare ya rungumeta tsam a jikinsa ta soma yinsa a wahale tana ajiyar zuciya hawaye har cikin bacci yana jin digarsu a kirjinsa.

"I am sorry my love" yace yana kara karfin rikon da yayi mata. "I love you so much" duk da yasan ta dade da soma bacci ba zata ji ba. Hannunsa na dama ya sarke da nata yana shafa kanta a zuciyarsa yana addu'ar Allah Ya basu zaman lafiya da albarka a zaman aurensu kuma Ya basu hakuri da juna. Soyayyar gudan jinin Tureta da ita ya girma yana rainon abarsa a zuci tun kafin su sake haduwa. Idan da akwai abinda yafi love at first sight kuwa to shi ya fada head over heels akanta. Ita ce duniyarsa, farincikinsa, cikar burinsa.

[5/23, 9:43 PM] ‪+234 703 075 7917‬: Bai jira cewarta ba ya saketa ya kama rigarsa zai cire. Da sauri ta bar dakin ta rufe masa kofa tana haki ita dai yau ta shiga dari. Awwab kuwa dariya yayi ya wuce yayi wanka shima yayi duk wani abu da ya saba na shiri bacci.

Tana zaune tsuru kamar wadda ta yiwa sarki karya ya bude kofar dakin ta dago kai da sauri suka hada ido. Kayan bacci ne a jikinsa na cotton riga mai gajeren hannu da dogon wando. Wannan kamshin da yake janta gareshi ta soma shaka ta lumshe ido a hankali. Kusa da ita ya zauna ya bude ledar kazar da take da zafi har yanzu sai kuma ya mike ya dauko robar maltina daya a fridge ya dawo.

"Cire hijabin kici abinci"

"Ni dashi zan ci"

"To babu laifi shi ma bazai hana ango abinda yayi niyya ba" yace yana kashe mata ido.

Turo baki tayi cikin shagwaba "ni wallahi tsoro kake bani Hammana. Me kayi niyya"

Mischieviously yayi murmushi "nothing...ahhh bude baki" ya mika mata naman.

Kasa karba tayi ta sunkuyar da kai. Ya kula dai yau da rigima a tare da ita sai ya dauko remote ya danna tunda an jona komai na tv din ya shiga neman channel din da zai bari a nilesat. MBC 2 ya kai ana wani film ya tambayeta ko tana son gani tace eh da sauri.

"Zan barki ki gani amma da sharadin zaki cire wannan hijab din muci naman nan if not yanzu zamu shige daki..."

Kafin ya kai karshe ta yiwa hijabin masauki akan wata kujerar yaji numfashinsa ya tsaya na yan dakiku saboda kyaun da tayi masa. Gashin ta ta kama ya zare ribon din ya zuba a bayanta da kafadu. Wannan lallen da tayi yasa kan yayi kyau sosai inda kalar ta fito ya zura yatsunsa a ciki yana rufe idanu.

"I love this Alheran" ya janyota kusa dashi sosai yana yamutsa mata gashin.

A gefen jikinsa ya rabata ya shiga bata naman yana ci shima. A haka suka koshi yace tayi zamanta ya kwashe komai zuwa kitchen. Sauran ya saka fridge ya wanko hannunsa ya dawo. Miko mata hannu yayi yana son ya taso ta kyabe fuska "ai ba'a gama film din ba"

"Brush kawai zamuyi mu dawo"

"To kaje ka fara yi kaine babba"

Dariya ta bashi wai nan wayo zata yi masa ya wuce dakin yayi ya dawo "saura ke"

"Kada ka kashe tv din Hammana yanzu film din ya fara kyau" tace tana tashi bayan bata fuskantar komai a ciki. Ko wuka za'a saka mata bata san me akeyi ba.

"Zama zanyi na gane miki inda kika tashi" ya zauna ta tafi.

Tana rufe kofa ya kashe tv din da fitila sannan ya shiga daki ya rufe kofa.

Ai tana jin motsin shigowarsa jiki ya soma rawa ta gama brush din ta kasa fitowa. Sai da tayi minti biyar ta yanke shawarar ce masa ita fa kallo zata yi kawai. Da kwarin gwiwa ta fito yana waya cikin harshen jamus yaki kallonta. Zaune yake akan gado ya mike kafafunsa ya jingina da pillow. Kofar dakin taje ta murda taji a rufe. Ta sami wuri ta tsaya tana jiran ya gama.

Sallamar mutumin yayi ya taso yana tahowa gabanta na kara faduwa. A tsakiyar dakin ya tsaya ya ware mata hannuwansa yana murmushi tare da yi mata nuni da ka. Babu yadda ta iya ta saki hannun kofar ta taka da sauri ta fada kan kirjinsa. Sun dauki kusan minti biyu a haka kowa da nasa tunanin da yake tattare da soyayyar dayan.

Da yatsunsa ya dago kyakyawar fuskarta a tausashe yace "Babyna guduna kike yi kuma?"

"Film din...." sai kuma tayi murmushi ta kasa karasawa.

"Kema kin san baki da gaskiya gashi kinyi shiru. Muje ni inyi miki tausar tunda kin kasa cika alkawari"

"Zanyi maka"

"Fara saka kayan bacci"

Akwatin nata ya bude babu ko daya na lefenta kuma suna Sakkwato za'a wuce dasu Abuja. Wardrobe ya bude inda ya zuba nasa kayan ya dauko mata t-shirt dinsa tana ta kamshi.

"In saka miki?" Yace yana dariya don yasan bazata yarda ba.

Harararsa tayi "da kayana zan kwanta"

"Schatzi" yace hannuwansa na jindadin yamutsa mata gashi ya rasa dalili ita kuwa da kyar take iya bude idanu saboda yadda take ji.

"Naam" ta amsa a raunane.

"Saka riga ko Ango yayi abinda yayi niyya"

Sakinta yayi ba don yaso ba tana ture turen baki ya fita daga dakin don ta shirya a tsanake. Cikin sauri take komai tana yi tana kallon kofa gashi key din ta waje yake. Rigar ko cinyarta bata gama rufewa ba. Tana fesa turare ya turo kofar jikinta ya soma rawa shi kuwa Awwab rufe kofar yayi ya jingina da bayanta tare da harde hannuwansa a kirji yana kallon Alheran a matsayin matarsa abar so da kaunarsa.

Turaren da ta dauka ta ajiye jikinta yayi matukar sanyi tana kallon gadon tana son zuwa ta kwanta ta rufe jikinta amma bata son yin kwakkwaran motsi a gabansa. Tahowa yayi gabanta yasa hannu a waist dinta ya matso da ita jikinsa da dayan hannun kuma turaren da ta ajiye ya dauka ya feshe mata jiki dashi sannan ya saka hannuwansa duka ta bayanta ya dagota jikinsa ya soma juyi da ita a dakin tuni ta kankame shi tana dariya.

"Please, please, pleeeeaaass ka ajiyeni" tace tana zagaye hannuwanta a wuyansa.

"Sai na cire miki wannan tsoron da yake hanaki sakewa"

"Zan sake....Chéri na sake ma.....Hammanaa"

Ajiyeta yayi a hankali tana jin kamar har yanzu juyin suke yi ta kankameshi tana sauke numfashi. Hannuwansa ta sake ji ta bayanta ya tura yatsunsa cikin gashinta da ya mayar abin wasa yana magana can kasan makoshi "na yafe miki tausar nan fa"

Zare jikinta take neman yi ta kasa saboda rikon da yayi mata a hankali tace "nagode"

Dago kanta yayi yana bin bakinta da kallo idanu a lumshe "gani nayi ko da tausa ko babu bazai hanani abinda nayi niyya ba"

Tsoron ya soma dawowa tace "Wai me kayi niyya ne?"

Wani irin kallo mai kashe jiki yake binta dashi yace "Spending the whole night loving you my baby. Ki taimaka ki bani dama saboda ko kinki bazai hana Awwab abinda yayi niyya ba, bani da hakuri indai akan sonki ne Alheran" kasa yayi da kansa ya soma kissing dinta tamkar ranar ya fara samun wannan damar. Radhiya bata iya sake komai ba sai abinda Awwab ya koya mata. Kamar yadda yace ya nuna mata soyayyar da bazata taba hadata da komai ba a rayuwarta. Bacci kuwa sai can cikin dare ya rungumeta tsam a jikinsa ta soma yinsa a wahale tana ajiyar zuciya hawaye har cikin bacci yana jin digarsu a kirjinsa.

"I am sorry my love" yace yana kara karfin rikon da yayi mata. "I love you so much" duk da yasan ta dade da soma bacci ba zata ji ba. Hannunsa na dama ya sarke da nata yana shafa kanta a zuciyarsa yana addu'ar Allah Ya basu zaman lafiya da albarka a zaman aurensu kuma Ya basu hakuri da juna. Soyayyar gudan jinin Tureta da ita ya girma yana rainon abarsa a zuci tun kafin su sake haduwa. Idan da akwai abinda yafi love at first sight kuwa to shi ya fada head over heels akanta. Ita ce duniyarsa, farincikinsa, cikar burinsa. [5/23, 9:43 PM] ‪+234 703 075 7917‬: Kiran assalatu na farko ya farkar da Awwab ya tashi da sauri yayi wanka saboda kada ya makara. A hankali yake komai saboda kada ya tasheta. Da ya gama ya sa dogon wando jeans ya dora rigar sanyi akan shirt din ciki don tun dare garin yake a lumshe ga iskar nan ta tsananin sanyin arewacin Nigeria da asuba. Zama yayi a gefen gadon yana shafa fuskar Radhiya a cikin duhun dakin sai haske kadan da yake fitowa daga toilet da ya bar fitila a kunne. Tashinta yayi yace asuba tayi. Sannu a hankali ta dago kan ta daga pillon ta bude nannauyan idanunta da fitowar hawaye.

Yatsansa ya dora akan lebenta "Shhhh haba babyna kinyi bacci da kuka kin tashi dashi bai kamata ba. Idan bazaki iya tashi ba ki jirani na dawo daga masallaci"

Hannunta na dama ta dunkule ta kai masa duka a kirjinsa tana kara narkewa cike da shagwaba da hawaye "bana bukata tunda ba ka sona"

Awwab yayi murmushi tare da mikewa yana son tayar da ita sosai "zan baki amsa idan na dawo"

Kunyarsa na tare da ita tayi saurin boye fuskarta cikin lallausan duvet din "Allah Ya tsare"

"Amin Alheran"

Yasa kai ya fita sannan ta tashi tana cije lebe don ma ya fita da ya ga raki da shagwaba mai lasisi. Duk abinta bata so ya dawo ya sameta a kwance saboda tana jin kunyarsa kada yace zai taimaka mata ba yarda zata yi ba. Shawarwarin Mama Zainab da Innawuro tsohuwar kakarta da tun farko ta fara gyara mata jiki da lalle tayi amfani dasu wurin cire son jiki ta gasa kanta da ruwan zafi sosai. Tunda akwai sanyin gari sai ta kara jindadin hakan. Bata bata lokaci sosai ba saboda gudun kada ya dawo ya sameta ta shafa mai mai kamshi da body spray sannan ta mayar da t-shirt dinsa da ya bata kafin su kwanta da dogon skirt dinta. Hijabinta ta dauko a falo tazo ta tayar da sallah tana faman runtse ido.

Lokacin da Awwab ya fito a bakin gate ya hadu da Daddy. Kunya kamar ya nutse a wurin ya ji kamar ya koma saboda wani nauyin mahaifin nasa da yake ji. Samun kansa yayi da durkusawa har kasa yana tambayar Daddy din "an tashi lafiya? Yaya baki su ka kwana?"

Sakin fuska yayi saboda ya fuskanci Awwab din a takure yake da kunya ya ce "Lafiya kalau Captain yaya kwanan diyata?"

Kara masa kunyar yayi ya kasa amsawa sai kai da ya sunkuyar yana sosa keya. Daddy yayi murmushin manya yana musu addu'ar zaman lafiya.

Da aka idar da sallah a masallacin ya so yayi saurin tafiya gida amma idon Daddy ya zaunar dashi. Tsohon sojan ba wuya ya gano bakin zaren shiyasa yayi kokarin katse wani makocinsu da yake neman jansa da hirar zaben da ya kusanto ya tashi su ka dawo.

Gyangyadi Radhiya take yi akan abin sallah ta jingina bayanta da gadon ta ji ana rufe kofa. Cikin sauri ta cire hijabin ta hada da abin sallar ta ninke ta koma gadon ta rufa har ka. Sauran rufar ma a idon Awwab tayi saboda bude kofar dakin da yayi da sallama. A zuci ta amsa masa a zuwan bacci take yi. Yana kallon yadda take ta gyara kwanciya irin na masu baccin karya ya kyaleta sai da ya cire kayansa don yasan ba dadin kwanciya dasu zaiji ba ya saka jallabiya.

Zagayawa yayi gefen gadon bangaren da fuskarta ke kallo ya durkusa. Da sauri da sauri take fitar da numfashi saboda tsabar kaduwa ga hawayen tausayin kanta tana yi. Hannun Awwab ta ji ya janye rufar da tayi ya bude fuskarta. Cikin gashinta da ya bazu akan pillow din ya sarke yatsunsa yana jin yadda ta soma rawar jiki.

Idanunsa yake lumshewa yana budewa a kanta cike da kasala ya ce "Da kinyi soja yau da nayi musu dariya saboda kin basu kunya karshe. Abu kadan sai kuka jikinki yayi ta rawa."

Bakinta ta turo "to ba kaine ba..."

Ya karyar da kai idanunsa a kan bakinta "Saboda kin fini baki Schatzi, nima fa kukan nan ya kamata nayi tunda jiya aka kawoni"

Dariyar da bata shiryawa bace ta kama ta. Yadda take dariyar ma baiki ya koma gareta ba saboda tamkar wanda aka sakawa magnet haka yake jin kansa. Sai dai yana tausayinta don yasan taji jiki...Allah Ya taimake shi an ware musu wuri ba a cikin gidan aka basu daki ba da an tafka abin kunya yadda ta rinka kiraye kirayen mutane.

"Yaya jikin naki my amazing wife?"

Juyawa take son yi daya barin saboda kunyar tambayar da yayi mata ya rike mata hannu yana girgiza kai.

"Ko zaki juya ki bari na fada miki abinda nayi niyya kafin kiyi bacci jiya" kasa kunnuwa tayi saboda ko me Awwab zai fada mata abin so ne a gareta. Ba tun yau ba ya kware wajen fada mata kalmomin da kan sa ta kwana tana murmushi ita kadai. Idonsa sarke da juna suna aikawa juna sakonni da fahimtarsu sai su din ya soma magana da muryar nan mai tsuma zuciyar Alheran Radhiya.

"Na karbi amanarki kuma na baki tawa. Matsayinki bana jin akwai wadda za ta taba samu a zuciyata. A kanki nasan mecece soyayya kuma nasan amfanin shakuwa. Baby kin faranta min rai sosai jiya duk da kin so cika min kunne da kuka...." murmushi tayi ta kawar da kanta shi kuwa tafin hannuwanta ya bi ya sumbata. Kafin ya cigaba da cewa,

"You have my love" ta dago kai kadan ta dube shi.

"You have my trust" ya matse hannunta yadda ba zata ji zafi ba.

"And you have my respect" ya duka tare da kissing goshinta.

Zai dago Radhiya ta zura duka hannuwanta ta rungumeshi a jikinta. Suna shakar kamshin jikin juna a haka ya dawo kusa da ita ya kwanta karatun nasu ya tattara ya koma na sababbin auren da suke matukar so da kaunar juna. Radhiya tayi dauriyar kin yi masa kuka amma ta kasa daga karshe. Kuka ne da tasan ba na wahala bane kawai harda wata irin soyayyar Awwab mara misaltuwa. Shi ma yana namiji yaya mamakin ganin yana tayata hawaye a lokacin da sabuwar soyayyarta take huda kowane bari na jikinsa tana sake samun mazauni. A take a wannan lokacin jikinsa yake fada masa cewa da wahala matuka wata mace ta sake samun gurbi irin na Alheran....son ta a jinin jikinsa yake. It has always been Radhiyan Hamma Awwab.

Bacci suka koma irin wanda da wuya in sun taba yin irinsa mai tattare da nutsuwa da kwanciyar hankali. Basu san lokacin da Zayyana tazo wurin goma ba tayi ta doka sallama da breakfast dinsu har ta gaji. Kofar net da aka zagaye karamar barandar da ke gaban katuwar golden kofar gidansu mai kyau ta bude ta ajiye kwandon tunda a rufe komai yake da wani kyalle mai kyau. Komawa tayi ta fadawa Mama ita fa taji shiru.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull