Kenza eBookz

Batuol mamman complete novel - Chapter 73

Batuol mamman complete novel - Chapter 73

Batuol mamman complete novel Chapter 73: Batuol mamman complete novel Chapter 73. Shadaya saura wayar Awwab ta soma ruri ya dauka da sauri zai kashe saboda…

3,346 words

Shadaya saura wayar Awwab ta soma ruri ya dauka da sauri zai kashe saboda kada karar ta tasar masa Radhiya dake kwance akan faffadan kirjinsa. Sunan Mama ya gani babu damar kashewa kenan yayi kokarin zame jikinsa Radhiya ta kara cukwikuye shi tana zumburo baki. Murmushi ya saki ya kawar da gashinta daga kan fuskar yace "so adorable".

Wani kiran ne ya sake shigowa still dai Mama ce ya danyi gyaran murya kafin yayi mata sallama sannan ya gaisheta.

"Awwab kayi hakuri surukanka zasu wuce ne mutanen Sakkwato da Sumaila shine suke son yiwa Radhiya sallama. Sai na ga ya dace ka fara shigowa kayi musu bangajiya"

"Mama ni kadai zan shigo?" Ya ce kamar zaiyi kuka don tsakaninsa da Allah kunya yake ji ya shiga gidan.

"Ka nemi 'yan uwanka su Bilal kuyi sauri. Ina kanwar taka ina fata ta tashi ta shirya ba jimawa zasu shigo"

Shirun da yayi da guntuwar in'ina ya fahimtar da Hajiya Mama komai. Murmushi tayi mai sauti Awwab ya rasa me zaiyi sai ya ga Radhiyan ma ta farka kawai shiru tayi tana kunyar tashi.

"Bani ita Awwab" yaji Mama tace.

Dora mata wayar yayi a kunne kafin ta soma magana Mama tace "saurareni da kyau Radhiya kin tuna me nace jiya ko?"

"Uhmm" tace a hankali.

"Tau, ki shiga ruwan zafi sosai kinga gobe akwai tafiya gabanmu idan ba so kike ayi ta zancenki ba ki gyara kanki. Zan shigo anjima idan bakiyi ba zan gane kuma kinsan sauran"

Rufe kanta tayi ta mikawa Awwab wayarsa. Tana ji ya tashi ya shiga toilet bai dade ba ya fito ya yaye rufar da tayi sai da tayi masa ihun ganinsa da tawul kadai gashi ya cire mata abinda ta rufe kanta.

"Muje muyi wanka" kawai yace ya sunkuceta yana cewa ashe buhun sumunti ce bai sani ba. Duk wani zille zille da taso yi bai barta ta fita ba a haka akayi wankan. Bayan sun gama ya hada mata ruwa mai zafi a robar da ta zauna dazu wadda saboda hakan Mama ta saka musu ita.

"Kin sanni da kunne ina jin me Mama take fada" ya kashe mata ido ya fita ya barta da tulin kunya.

Lokacin da ta fito ya gama saka kaya sai wannan kamshin nasa na musamman take ji. Shadda ce ya saka mara nauyi ga hularsa a gefe.

"Ba don ina tsoron kaina ba kuma dai ana jirana da na tsaya shiryaki da kaina baby" yace lokacin da ya ajiye brush din da ya taje saisayayyen kansa.

"Na yafe fita ka tafi"

Kan gado ya fada sai lokacin ta kula ya chanja komai amma kunya ta hana tambayarsa ina ya ajiye wadanda ya cire.

"Kunyar fita nake yi kada a gane" ya tashi yana tafiya a gefenta "tayani dubawa tafiyata bata chanza ba ko"

Bubbuga kafa ta soma yi "Hammana bana so"

"Ba fa dake nake ba, nima bana so a gane ne kinsan manyan nan..."

Daga murya tayi cike da shagwaba ta ce "HAMMAAAA"

Yana kyakyata dariya ya fita. Kwandon abincin ya gani ya dauko ya dora a kan centre table sannan daga inda yake ya fada mata ta tabbatar ta ci kafin ya dawo.

Shiryawa tayi cikin wani hadadden lace tayi daurin da ya bayyana gashinta da tayi packing ta sako shi tsakiyar daurin sannan ta gaban ma ta ja dankwalin ya danyi baya. Fuskarta tasha kwalliya tayi kyau sosai. Sauri tayi ta gama saka awarwaron da ta dauko kalar kayan sannan ta fito falo ta dan karkade kura duk da babu. Turaren wuta ta saka a ko ina kamshi kuwa ya soma tashi kana tahowa bangaren za ka ji.

Fridge ta bude babu komai na kayan abinci sai ruwa da lemo kala kala. Da yake ana sanyi tunda suka zo Katsinan sau daya aka dauke wuta shima bata dade ba aka dawo da ita. Abincin da aka kawo ta bude, doya ce da aka soya da kwai a flask daya sai bread da farfesun kaza ya ji kayan kamshi. Ga kayan tea da ruwan zafi a flask. Kitchen ta kai ta ajiye don bata jin za ta iya cin komai duk yunwar da take fama da ita kuwa sai Hammanta ya dawo.

Awwab kuwa da gaske sai da Bilal yayi da gaske su ka shiga falon Mami inda iyaye da kakanni ke zaune. Ana ta tsokanarsa sai su Bilal ke ramawa shi kam baki ya mutu Schatzi kadai yake tunani. Da su ka gama fita suka yi zuwa wurin Radhiya an gama saka kayayyakinsu a motocin da zasu bi.

Duk kunya ta isheta gashi babu su Rahima an barta ita kadai da manya kowa da abinda ya ke kara mata na nasiha. Kafin su fita Awwab ya dawo ya shiga daki sai gashi da envelop guda biyu. Daya ya bawa Hajjo dayan kuma ya baiwa Gwaggonta Mubaraka kowa su raba da abokan tafiyarsu. Shi kadai ya rakasu ta biyosu zuwa bakin kofar net din suna cewa ta koma ba sai ta fito ba.

Tunda Awwab ya shigo suka ci abinci tare suke makale da juna sallah kadai ke fitar dashi. Shagwaba kala kala yana gani tana kuma burge shi sai nan nan yake da ita kamar kwai. A haka ma baya samun yadda yake so sosai saboda kunyarsa da tayi mata yawa. Abincin rana ma kawo musu akayi daga ciki wannan karon Rahima ce ta kawo Awwab ya karba. Su Zahra da Fauziyya suka kafa naci kamar bala'i sai sun je wurin Radhiya.

Mama tace "gulmammu wace acikinku bata ga wannan daren ba eyye. Zaku je ganin kwaf ku gani ko ta sauya tafiya ko..."

Mami sai da tayi dariya don ba karamar kunya suka ji ba har Fauziyyan kuwa. Zahra kamar ta kifa don sauri ta fice daga falon kafin a karasa barota. Mama kuwa sun kunnata bata iya yin shiru ba ta cigaba da sababi.

Kafin magariba ragowar tawagar Malamijo sun iso gidan saboda tafiya Nijar da safe. Salame ce akan gaba ko zama bata yi ba wai sai ta ga dakin amarya. Sakin baki tayi tana kallon kayan kudi sai da Mama taje da kanta ta yo waje da ita wai da bandaki zata shiga ta rage mara tayi alwala ko tunanin cewa bandakin daya ne kuma a cikin dakin baccinsu bata yi ba.

Sai da suka shiga ciki ne ta ga Halifa tare da Emzee da Ibrahim. Duka su ukun sun gaisheta babu yabo babu fallasa sai dai yanayin fuskar Emzee ya tsaya mata a rai fiye da zato da tsammaninta. Ganin Rahima ne ya mantar da ita komai abin mamaki ga ita kanta Rahiman Salame wani mugun tattali take yi mata kamar ta maidata ciki. Tunda Malamijo ya kirata yayi mata tas akan mutuwar idon Rahima tasha kuka kamar ba gobe.

Ba komai ya tsaya mata a kahon zuciya ba irin yawaitar lokutan da Rahima ke durkusawa a gabanta tana rokon idan laifi tayi mata ta taimaka ta yafe mata. Yarinyar bata da matsala kuma bata santa ba. Burinta daya a duniya ta ga mahaifiyarta ta sakar mata fuska ta kaunaceta kamar kowa. Ita da ta iya zuwa wurin boka ta makanta Mairama da asiri yau an wayi gari 'yar cikinta ta gamu da lalurar da indai wani abu ya sake samun dayan idon mai lafiya to ta makance kenan fa. Tana ganin abubuwa amma ba ta iya rarrabesu. Ranar duk wani guntun rashin mutumci ma nemansa tayi ta rasa. Fatanta bai wuce ta kyautatawa Rahima ba ko ta yafe mata cikin sauki. Ga Halifa fuskarsa kullum a hade idan ya ganta musamman bayan matsalar idon kanwarsa. Baccin kirki kasawa tayi da ta duba hagu da dama sai kaji tana ina Rahimata?

A bangaren su Ummi ranar su ma suka wuce Nijar da Daada. Duk wani boyonta kallo daya Mammee tayi mata ta ja ta uwar daki tana murmushi.

"Mairama ciki gareki ko?" Tace da hausarta mara fita sosai.

Ummi taji kunya sai sunkuyar da kai kasa take. Mammee kuwa tsabar murna ta fito tana shelantawa. Ummi ta rufe kanta a daki ta kasa fita saboda yadda 'yan uwa suke ta murnar wannan rantsatssen rabo. Zayyan yayi ta dariya yace maganinta kenan tunda ta damu a boye gashi anyi mata mai gabadaya. Cikin 'yan uwansa mata harda mai tambayarta wata nawa ne saboda a fara shiri. Ta ga gata muraran don ko cikin fari ne a jikinta karshen abinda zasuyi mata kenan.

**********

Da daddare bayan sun gama dinner Radhiya tana wanke kayan da suka yi amfani dashi bata ji shigowar Awwab ba sai hannuwansa da suka bullo ta gefe da gefen cikinta ya riko plate din da take daurayewa suna yi tare. Jikinta tuni ya fara rawa saboda hatta soso sai ya sarke yatsunsu sun wanke abu tare dashi.

Kiss taji a wuyanta ta kusa sakin glass cup din da suka gama daurayewa ya ce "hankali baby"

"Ai kaine"

"Ni sarkin laifi me kuma nayi"

Tsuke bakinta tayi ya cigaba da abinda yake yi yana birkita mata lissafi. A daddafe aka gama ta rufe ido kawai ta kwanto da kanta kan kirjinsa sosai na dan lokaci sai kuma ta juyo suna kallon juna "Chèri muje na hada maka kayan tafiya gobe"

"Kin hada naki ne?"

"Suna cikin akwatin da Zayyana ta kawo min dazu da ta kawo abincin dare"

Dakin su ka koma ya dauko wani akwati mai taya hudu daga kasa irin wanda duk nauyinsa mai ja baya ji saboda a tsaye yake rectangular. Na biyun karshen ya dauko ya nuna mata kayan da zaiyi amfani dasu ta fito dasu za ta zuba sai gani tayi ya zazzage nata kayan akan gado.

"Hammana ya ka juye kayan ko basu shiryu bane?"

A akwatin da take zuba nasa ya shiga jerawa "babu amfanin mu tafi da bags daban daban ne"

"Idan ba masaukinmu daya ba fa?"

Janyota yayi suka fada kan gadon yana zagaye fuskarta "nasa Yousuf ya kama mana hotel na kwana biyun da zamuyi"

Ai sai ta kasa hadiyar yawu don fargaba "duk kowa yana nan sai mu tafi hotel?"

"Yes...ta kare min Schatzi kema kin sani" ya cigaba da zana fuskarta da yatsansa "idan da nayi hakuri yanzu bazan iya ba...KEMA.KIN.SANI" ya fadesu dalla dalla kafin ya shiga nuna mata soyayyar da ko rabi rabin abinda ke ransa bai sauke mata ba.

Kayan da basu karasa hadawa ba kenan su da akwati daya da himilin kayansu dake zube a gefe suka kwana a kan gadon. Tun asuba da suka yi wanka ta karasa hada musu kayan ta gyara dakin ta wanke toilet. Basu bar komai a waje ba bedsheet din ma cirewa tayi ta dinke ta turasu cikin ledar da yake ciki da kyar saboda gudun kura.

Motoci harda wanda babu budget dasu mutane sun bi su Nijar ganin kwai da kwarkwata. Kamar kullum karamcin mutanen yana bawa Radhiya mamaki. Kudi ne dasu iyaye da kakanni amma akwai tarbiya da tsagwaron hadin kai a zuri'ar Alh Ghousman Agali. Gidan Alh Sidi Radhiya ta shiga saboda ance Umminta tana nan ta fada dakin da aka nuna mata da murnarta nan ta sami Emzee suna rigima da Mammee tana tura masa nonon rakumi ya damtse bakinsa yaki karba. Kan Ummi ta fada da murnarta Mammee ta sakarwa Emzee robar nonon ta tashi tana fada.

"Alheran yaushe zaki girma ne ni Aghaisha"

Turo baki tayi tana nanikar Ummin "me kuma nayi miki daga shigowata?"

"Dagata kada ki kassara min jika, maimakon ki tayamu tattalinta sai ki tsaya shirme?"

Ina kasa ta bude Mairama ta binne kanta. Emzee ya dago fuskarsa da nono ya watso masa ya kalleta sai wani nauyi ya bakunce shi ya dukar da kai. Radhiya kuwa ihun murna ta saki bilhakki ta sake rumgume Ummin tana murna.

"Wayyo ni, wayyo Umminmu Allah Yasa mace zaki haifa me kama dani" tace tana dariya.

Emzee ya kalli yadda take yi ya kalli Umminsu da kunyar da ta lullubeta sai ya tashi kawai yaja hannunta "Hamma Awwab yana kiranki muje na rakaki"

Zame hannunta tayi "kai Emzee yaushe kuka hadu?" Ta juya zata kuma zama "Ummi wane watttttt" keyyyy haka Emzee yayi waje da ita yaja kofar ya rufe.

Mammee tayi dariya tare da goge 'yar kwalla "sannu da kokari Mairama nasan irin halin Alheran. Haka yayata take kusan komai nata ta dauko. Zama da kishiya ne yasa tayi sanyi amma ko shi Mal. Muhammadu ai yayi fama da kiriniya tun farkon haduwarsu har auren."

Murmushi Ummi tayi tana sauraron labarin uwarmijinta da bata taba gani ba sai a hoto.

Wani falo Emzee ya kai Radhiya ya girgiza kai "ni da kin sani ni na fara fitowa yadda zan iya zaneki son rai. Sam baki kula da kunyar da Ummi take ji ba kike ta takurata da tambaya"

"Ayya Emzee ban gani ba bari naje na bata hakuri" tace innocently.

"Kin ji ki kuma, shiru ya kamata kiyi ki rinka taimaka mata idan tana son wani abu"

Gyada kai tayi sai kuma ta hau murmushi "Amma kai baka yi murna bane? Ni fa na matsu naji ranar haihuwar"

Hannunsa ya sakalo a kafadarta yana jinjina wautarta "Addata ta kaina ina tausayin Hamma nasan ya gamu da shiririta"

"Kai dalla me ka sani, Hammana yana ji dani sosai don wallahi jiyama da dadd......"

A gigice Emzee ya fara neman kofar fita daga falon yana cewa "na shiga uku don Allah kada ki fada"

Ya kai bakin kofa tace "kai wank...."

"Sai anjima" yace da sauri ya fita yana tunanin ko dai wanka za ta ce yayi mata tunda tace yana ji da ita.

Tabe baki tayi da ya fita din tace "meye don na fada maka ya tayani wanke-wanke ba abin farincikinka bane ace mijin yayarka yana sonta" wani tunani ne ya darsu a zuciyarta bata san lokacin da ta kwashe da dariya ba harda rike ciki "shege Emzee ko dai yasan me akeyi ne...tabdi gara ya nemo mata mu kaishi."

Ta nufi part din 'yan matan gidan inda su Zahra suke ta kuma ganin Emzee da tiyo yana wanke fuska ta zuci tace sumumu kasau wannan idan kayi aure matarka ta shiga dubu da soyayya. Cikin 'yan uwata ta shige tare dasu Fauziyya ana mata tsiya bakin ya kasa ramawa. Bayan isha Awwab ya kirata wai tazo su tafi ta rasa yadda zata yi. Can sai ga Tante Nasara ta kirata suka fita har wajen gate sannan ta daga waya ta kira Yousuf. Da faransanci tace masa,

"Ga kanwarka nan ka kaiwa mijinta kafin Zainab ta cinyeni"

Ya kwashe da dariya "Mam ina sonki wallah"

"Da na kyaleka ka boye matarka ko? Zamu hadu a gida ne sai ka gaya min wanda ya baka shawarar satar amarya" ta ce tana dariya.

Tare suke da Awwab a kofar gidan Alh Ghoumar ko minti biyu ba'ayi ba suka iso. Baya Awwab ya bude mata ta shiga ta gaishe da Yousuf tana tambayarsa Arifah yace wurinta zasu je.

Wani katafaren hotel ne da yake cikin jerin manya a kasar baki daya suka shiga. Hawa na bakwai Yousuf ya bude mata wani daki bayan ya kira Arifah yace tare suke sannan suka juyo shi da Awwab zasu siyo musu abinci.

Radhiya da Arifah suka rungume junansu suna murna. Arifah ke fada mata yadda daga Yousuf zai kaita gida ranar dinner suka kare a hotel.

Radhiya tayi ta dariya suka koma hirar sabuwar rayuwarsu. Arifah ta girmi Radhiya sannan ta fita wayewa musamman ta wannan fanin. Shawarwari ta shiga bata yadda zata ajiye kunya ta bawa mijinta kulawar da ta dace.

"Kinga ba mazauni bane idan ba kya kulawa dashi yanzun nan wata zata rabaki dashi"

"Dena fada Sis" tace da rawar murya bata fatan ganin wannan rana. Ko zaiyi mata kishiya bata burin ace saboda gazawarta ne sai dai hali na rayuwa.

Goma da rabi suka dawo Yousuf ya shigo yace mijinta na jiranta a waje. Tana fitowa ta fada jikinsa sai da yayi mamaki kuma ya nuna jindadinsa sosai ita kuwa sabon karatun Arifah ta dauka.

"Miss me?" Yace yana mata jagora zuwa nasu dakin.

"So much Hammana"

"Love me?"

"For as long as I live" tace tana kashe masa ido.

Bude dakin yayi dama ya ajiye musu kayansu ya rungumeta "ki rinka sassauta min babyna wannan sabon salon naki zai hanani abin arziki"

Zama yayi ta dare cinyarsa abinta tana magana cikin jan rai "wane abin arziki da za kayi?"

"Uhmm wai da yau dai na bar amarya ta huta gajiya...to amma"

Tana ganin abin zaiyi gaba ta tashi tana raba idanu "kayi hakuri Hammana ji nayi ance wai haka yana kara kauna"

Guje-guje suke a dakin taki bari ya kamata yana cewa "kaunar zan nuna miki ai wadda ta karu"

"Chèri bani da lafiya fa"

"Harda karyar ciwo kike yi?"

Ta girgiza kai tana shagwabe masa "a'a lafiyata kalau ni dai kayi hakuri"

"Na hakura janbaki kawai zaki bani..."

Daga inda take ta taho gareshi da saurinta ta hade bakinsu "ba kayi bayani bane tun dazu kasa ina wani tunanin"

"Tunanin naki ma zai tabbata kema kin sani"

**********

Washegari tun shabiyu suke tsakanin gidajen kawunan nasu ita da Arifah wadda aka kawo officially. Sai yamma aka yi wasan hawan rakuma a wani babban fili inda amare da angwaye kai harma su Ummi da Daada suka yi shigar gargajiya ta 'yan kabilar tamasheq. Yousuf da Awwab sun sha rawani buzaye sak.

Radhiya da Arifah kuma nasu kayan harda sarkoki, abin hannu, na gashi da na hanci duk an makala musu sunyi kyau sosai. Kowacce amarya angonta ya taimaka mata ta hau rakumi su na rike da akalarsa an rufe rabin fuskar amaren suka zagaya wurin dasu ana ta daukar hoto.

Salame tayi kallo ta ga abin mamaki a zuri'ar dangin mijin Mairaman da ta wulakanta. Kannen Halifa da matar Alh Salisu sun zo kai kace sun fita matsayi a wurin saboda yadda ta zubar da mutumcinta a baya.

Ana tafawa amare da angwaye ance suyi tsere akan rakuman Emzee ya kalli Addarsa da mijinta ya zauna a bayanta ya rike linzamin rakumin da suke kai ya kalli Rahima da take kallonsu itama abin yana burgeta ya ce

"nima in zo in samarwa kaina buzuwa ko ma hau rakumi da bikinmu"

A can gefe take zaune mutane duk anyi gaba kallon tsere shine ya biyota don kawai ya bata haushi.

Wani matashi kyakkyawan gaske cikin jikokin Alh Sidi ta nuna masa duk da zafin kalamanta tana murmushi "Ya Emzee to ko muma a hada namu bikin ne? Ka ga Aman yace muna komawa zai zo wurin Ummi"

Hadari ma yafi fuskar Emzee kyan gani ya ce "yazo yayi mata me?"

"Maganar aure ce don yace ba da wasa yake ba" ta yi masa wani dan banzan murmushi da ya daure masa zuciya.

"Saboda an rasa mazajen aure a Nigeria daga zuwanki kwana daya a nan za ki ce kunyi maganar aure da wani" ya ce yana huci.

Kwafa tayi a zuci tana jindadin ko ma fushin me yake da ita bai dena sonta ba "Abin ne yazo mana a bazata"

"To bari kiji in fada miki indai Aman ne yana yana shaye-shaye ah to sai ki nemi wani"

Hannuwanta ta rungume tana kallon saitin Aman din "sai inyi masa addu'a Ya Emzee yanzu ba'a gudun mutum don hali taimaka masa ake ya chanja"

Bai san ya soma fada ba yace "inji uban wa? So kike ya rinka dukanki a gida? Ke wai da wane yare ma kuka magana bayan bai iya hausa ba"

Rahima ta dake tayi murmushin da ya sake kawata fuskarta "ko babu yare mun fahimci juna...Ya Allah Ka bani...."

Kishi tuni ya rufe masa idanu yace "Shut up, wallahi kika ce Ya baki Aman sai na tattakaki a wurin nan"

Ranta ya soma suya saboda bacin rai "Sai na fada din...Allah Ka "

Hannu ya daga zai mareta Mairama cikin bacin rai duk da bata san me ya hadasu ba amma ihunsa da daga hannunsa gareta ya matukar bata haushi.

"Muhammad kana hauka ne?" Ta daka masa tsawa.

Daga bayanta Salame ce ita kuma rashin ganin sanyin idaniyarta Rahima Idris Sumaila ne ya kawota wurin. Da sauri ta je ta kama hannun Rahiman wanda idonta ko gezau sai tarin ajiyar zuciya da take saukewa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull