Batuol mamman complete novel - Chapter 74
Batuol mamman complete novel Chapter 74: Batuol mamman complete novel Chapter 74. Ummi ta damki hannun Emzee saboda bata taba ganinsa haka ba dayake filin…
3,367 words
Ummi ta damki hannun Emzee saboda bata taba ganinsa haka ba dayake filin a gefen gidan Alh Ghoumar ne tattaki kadan suka shiga gidan. Dakin uwargidansa ta wuce dashi suna zuwa ta rufe kofar ta juyo a fusace.
"Karami baka taba yi min abinda ya sosa min rai kwatankwacin na yau ba saboda haka kafin nayi maka hukunci ka bude baki ka fada min me ya hadaka da Rahima har kake tunanin idan ka mareta zamu wanye lafiya"
Salame lokacin tana rike da hannun Rahima ta kama hannun kofar za ta bude Rahima ta hanata tana girgiza kai. Itama ta gaji so take ta san me tayi masa. Wannan wahalar soyayya har ina kullum yana azabtar mata da zuciya.
Ga mamakin Ummi sai kawai Emzee ya saka mata kuka ya dora kansa a kafadarta. Rahima na jin sautin kukansa itama ta fara nata yayin da jikin Salame yayi sanyi.
Sai da yayi mai isarsa yana cije lebe yace "Ummi I love her so much, wallahi Ummi Rahima nake son aure kamar zanyi hauka saboda son da nake mata"
Salame ta yiwa Rahima kallon tambaya wanda ita kuma taji furucinsa a bazata duba da yadda yake kyararta yanzu. Dariyar Ummin suka ji.
Fuskarta tana nuni da zallar farinciki ta dora hannu akan fuskarsa "Allah sarki Zayyan Turetana ya girma, to waye ya fada maka ana dukan mace idan ana sonta? Ko tace bata son karamin sojan Mairama ne?"
Takaici ya kama shi "Ummi yaya kike dariya this is not funny at all. Rahima fa nake nufi. Rahiman Gwaggo Salame wadda ta makantaki tsahon shekara goma"
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Rahima da Salame suka fada a tare jikinsu na rawa. Salame bata son Rahima taji zancen nan da wuri sannan a yau a yanzu taji wata katuwar nadama ta lullubeta a gaban 'yar cikinta.
Emzee ya soma ruwan hawaye "Ummi ni bansan 'yar Gwaggo Salame bace da bazan fara sonta ba, bakiji zuciyata ba Ummi ki rinka yi min addu'a Allah Ya yaye min. Ta yaya zan so 'yar wadda bata son mahaifiyata kullum burinta kiyi kuka"
Mairama ma sai ta fashe da kuka Emzee ya rungume mahaifiyarsa yana jin dacin zuciya da rashin adalcinta na son Rahima.
Hawaye na kwaranya a idanun Mairama tana share masa nasa ta ce "Karami idan kana son kanwarka nayi maka izini ka manta da komai ka nemi soyayyarta"
"A'a" ya shiga girgiza kai.
Kuka take sosai tace "Lallai ashe baka da wayo ban sani ba. Abinda Adda Salame tayi min ALKHAIRI NE babba a gareni. Yau da banyi wannan makantar ba maimakon murna Karami zan shiga rudani mara misaltuwa ne akan dawowar mahaifinku. Ko kasan cewa ko banyi auren soyayya ba dole zan nemi mijin aure saboda inganta rayuwarka da ta yayarka? Da yanzu ina da 'ya'ya da wani mutumin ba Zayyan Tureta ba fa Karami. Kana tsammanin duk wanda na aura ga zuri'a tsakaninmu zan iya barinshi kai tsaye saboda naku mahaifin ne? Kasan girman dake tattare da aure irin wannan kuwa. Ga mijin da nake so ya dawo amma wani yayi mana shamaki. Kila Allah Ya jarabceni da son sa fiye da babanku"
Ta sake fashewa da kuka " nayi imani da yanzu mahaifinku yana cikin kuncin rayuwa duk da tarin arzikin da ya samu. Ciki ne dani Karami da ta ina kake tunanin Umminka zata sami wani rabon ta rabu da wani mijin da yara ta dawowa tsohon mijinta...ka duba girman wannan alkhairi da Allah Ya bamu ka gode Masa domin ni wannan kadai ya isheni dalilin da na yafewa Addata"
Bai taba tunani makamancin wannan ba amma duk abinda ta fada masa gaskiya ne. Kukansu suka yi sosai sannan yace "duk da haka Ummina bazan iya ba. Ki yi min addu'a zan sami wata in kawo miki"
Salame da Rahima sunji komai haka Radhiya wadda fitsari ya koro tun tsayuwar su Rahima a wurin take bayansu tana jin komai. Ganinta kawai suka yi ta wucesu ya bude kofar dakin ta shige tsakanin Ummi da Karami suna hawaye.
Rahima kuwa da sauri ta matsa yadda babu mai hangosu daga cikin dakin ta shiga na kusa dashi da bata san ko na waye ba tana fitar da numfashi da kyar ta rike kirjinta tana dannawa. Salame ta gigice ta dafata "Rahimata yaya? Me ya sameki"
A matukar raunane ta kalli Salamen idonta babu hawaye ta ce "Umma, don Allah nima ki soni kamar yadda Ummi ke son su Adda Radhiya. Wallahi Umma idan kika soni ko...uhmm nayi miki alkawarin zan zama 'ya tagari a wurinki ko banyi kudi ba zanyi miki biyayya."
Magana take kamar zautacciya saboda tsananin tashin hankali ace mahaifiyarta, hasken rayuwarta, inuwar jindadinta ta aikata mummunan abu irin wannan.
Salame sai hawayen mai cikea nadama sosai taji Rahiman ta kama hannunta "Umma nima kiyi min addu'a don wallahi ina son Ya Emzee...kinji kirjina Umma yana min zafi saboda na rabu da shi. Bazan iya zama da shi ba har abada saboda zaiyi ta kallonmu da laifin da muka yiwa Ummi"
Kukan Salame ya dadu ta rungume Rahima sosai a jikinta "ba ke kika yi laifin ba nice nayi kuma zan je na nemi yafiyarta."
"Duk abinda kika yi nima na dauka Umma. Shi baya gudun Ummi sai ni zan gujeki....Allah Ya kiyaye"
Salame ta dago kan Rahima ta ce "kiyi kuka Rahimata kiji sanyi a ranki. Idan Mairama tace sai na kwanta na bata hakuri sannan zata yarda Karami ya aureki zanyi...Rahimata kiyi hakuri kullum kuka nake sakaki akan son zuciyata"
Mikewa Rahima tayi harda karfin halin murmushi "ba kuka nake ba Umma kizo muje ana tsere mu cigaba da kallo"
Kafin Salame ta ankara Rahima ta fita daga dakin ta durkushe a wurin ita kuwa tana kuka mai tsananin taba zuciya...waye ya aiketa kuma me ya rudeta ta rinka lalata rayuwarta da ta iyalinta da hannunta. [5/23, 9:43 PM] +234 703 075 7917: Kasa zama Salame tayi ta tashi bin bayan Rahima sai ganin Mairama tayi tana dube dube. Ita take nema saboda Radhiya ta fada mata cewa sun ji komai. Daurewa tayi ta saki fuska ta nunawa Salamen kofar dakin tana so ta shiga su yi magana. Ita yanzu neman sulhu take yi saboda yadda damuwar Rahima ta zame mata kamar an ajiye mata dutsen dala a zuciya.
Su na shiga kuwa ta juyo tana hada hannuwa ga idanunta sunyi ja sosai ta ce "Mairama nayi miki ba daidai ba nima na sani. Ba ke kadai ba duk wanda ya rabeni na cutar dashi na cuci kaina kuma, amma ki yiwa Allah da ManzonSa kada Rahimata ta biya bashin da ba ita taci ba"
Mairama tana iya ganin gaskiyar maganganun Salame. Idan ma ba ta tuba bane don girman laifinta kallo daya za ka yi mata kasan cewa she is desperate, ta kai kololuwar bukatuwa da neman agaji a wurin wadda ta dade tana farautar farincikinta.
"Adda Salame nan ba muhallin wannan maganae bane ki bari mu koma gida" ta ce mata tare da mikewa za ta fita.
Da sauri Salame ta tashi ita ma "babu damuwa Abujan zan biki wallahi"
Murmushi Mairama tayi ganin cikin lokaci kalilan Salame ta sauya. Za ta bude kofa kenan ta ga hannunta ta riko nata hannun da dan saurinta.
"Tsaya dai mu yita da wajewa Mairama kinga a nan wurin...." ta fita ta tsaya daga kofar dakin inda suka tsaya dazu da Rahima "naji komai lokacin da kike fadawa Karami cewa kin yafe min. Kinga an rufe wannan shaftar kada sai mun tafi kice ba haka ba, ni kuma nasan naji da kunnuwana"
Guntun tsaki Mairama tayi da dariya, mai hali baya fasa halinsa "tun kafin ki ce komai na riga na yafe miki Adda"
Wani abu taji ya sauka daga makoshinta ta saki murmushi korayen hakoran nan su ka bayyana. A take zuciyar Mairama ta soma tashi ta danyu baya.
Cikin sigar rainin wayo wadda za ta nuna Salame har kullum Salame ce sai ana mata uzuri ta ce "sai naji kuna zancen ciki kuma? Ina ke ina sake haihuwa an fara girma ga 'ya'ya suna tafiya gidan miji"
Idan ta biye mata ba fa shiryawa zasuyi ba sai ma dai a karawa rigimar fetur. Amma ko yaya sai ta dan rama za ta ji dadi.
"Soyayyar kenan Adda, ba dare ba rana kullum miji yana dokinka. Indau kuma batun auren Radhiya ne kada wannan ya dameki ni nan harda matar Karami sai mun kara haihuwa" tana fada a zuciyarta tana cewa (Allah Kada ka nuna min wannan bakar rana)
Ta sake tabawa Salame inda yake mata kaikayi ta ce "zaki sha aiki kuwa don indai Rahimata ni ta biyo za ki kwatsa 'ya'ya kamar dabino. Za dai kiyi masa maganar ko? Ba yabon kai ba ni ban taba ganin 'ya mai ladabi da biyayyarta ba. Nake fada miki halin Sahabbai ta gado"
Ran ta yana baci da maganganun farkon gashi na karshen suna bata dariya shiyasa kawai ta fita tana murmushi da rokawa 'yar uwarta shiriya.
**********
Emzee dakin da suka yi masauki ya tafi ya kwanta yana ta juyi ya rasa shawarar da ya kamata ya dauka cikin dimbin shawarwarin da zuciyarsa take bashi akan Rahima. Bari dai su koma gida yayi magana da Daada. A haka gani yake soyayya bata yi masa adalci ba ta kaishi inda baya son zuwa kuma babu alamun za ta fiddo shi nan kusa.
Radhiya kuwa da ta fito janyeta akayi za'a cigaba da hotuna jikinta duk babu kwari. Awwab ya kula da yadda tayi zuru-zuru kwalliyar ta goge saboda cabewar da tayi da hawaye sai ta goge kawai shiyasa ganinta haka ya shiga damuwa saboda bata da walwala. Samu yayi ya faki ido saboda yamma da tayi hankalin iyaye yayi nesa dasu ya fitar da ita daga wurin. Rawaninsa ya cire ya nemar musu taxi ko Yousuf bai nema ba suka koma hotel dinsu.
A hanya bai ce mata komai ba sai da suka shiga dakinsu ya rage mata kayan jikinta da danginsu sarkoki da sauran kayan adon ya zaunar da ita a gefen gado sannan ya zauna a kasa a gabanta ya dora kafafunta akan cinyarsa yana matsawa a hankali.
"Me ya sameki Alheran?"
Dama kiris take jira kawai ta fashe masa da kuka. Hankalinsa a tashe ya tashi ya zauna a gefenta ya rungumeta tayi kukan ta gaji. Sai da ya lura numfashinta ya soma dawowa daidai ya sake tambayarta.
Da kyar ta iya fada masa abinda ya riga yaji daga wurin Daada lokacin da suka je Sumaila bayan Salame ta daketa. Sai dai yayi matukar kaduwa game da dalilin makantar Ummi da kuma karshen bayanin Radhiyan wanda shine musabbabin kukanta a yanzu.
"Hammana ka tuna lokacin da aka ce na hakura da kai saboda kada na bata zumunci?"
Ya gyada kai yana tuna lokaci mai daci da ya shude a rayuwarsa. Ya azabtu da rashin cikar burinsa ya kuma ji haushin amincewarta a lokacin taki goya masa baya. Siririyar muryarta da ta dashe saboda kuka ce ta katse shi yaji ta ce,
"It was so painful Chèri sai lokacin ma na fara sonka sosai. Yanzu yaya Emzee zai ji? Yana son Rahima ashe kuma yana gudunta saboda Ummi. Emzeee yana da sa abu a rai nasan da wahala yau ya iya bacci"
Awwab sakin baki yayi yana kallon ikon Allah. Radhiya ta cigaba da fadin halin da kaninta zai shiga cike da tausayawa.
Hade bakin nasa yayi ya ce "yanzu duk wannan hawayen na Emzee ne ba ma Ummi ba?"
Tsakaninta da Allah tace "Ummi ai ta yafe nasu ya wuce. Emzee nake maka magana yanzu. He is so hurt yana ganin laifin Rahima a tunaninsa yaudararsa tayi taki fada masa wace mamanta"
Jinjina kai ya rinka yi "indai zaki yiwa Emzee wannan kukan ni kuma me zaki yi min idan na kamu da son wata aka rabamu?"
"Kace me?" Ta jefa masa tambayar idanunta sun wani kankance tana huci.
Dariya ya soma yi mata "cewa nayi fa...ke dai banyi magana ba"
"Ya dai fiye maka idan ba haka ba kuma yau babu bacci a dakin nan" ta juya masa keya.
Kwanto ta yayi jikinsa "wasa nake yi miki Schatzi don ki saki ranki. Ina jindadi idan naga 'yan uwa suna son juna domin Allah. Keep it up my baby amma fa kada kowa ya kamo matsayina"
Sunkuyar da kai tayi tana jin kunya "kowa matsayinsa daban...KAIMA.KA.SANI"
"Wanne ne matsayin Awwab?"
"The only man in my life"
Rungume ta yayi suna shakar kamshin juna daga baya ya tasheta daga kan gadon "muyi wanka idan nayi sallar magrib zan koma wurinsa muyi magana man-to-man. Amma ki sani tun wuri sai na rankwashe shi. Haka kawai ya janyo min dan janbakin da naci burin gogewa idan mun dawo ya bi hawaye ya gudu"
Da sauri ta tashi ba shiri ta koma ta zauna. Abu goma da ashirin ke damunta, dama jikin lallaba shi take ga kuma hawa rakumi da tayi dazu ta rinka jin kanta kamar akan kaya. Runtse idanu kawai take yi Awwab dama ya san matsalar yana mata sannu suka yi wanka ta gasa jiki sosai. Ana kiran magrib yace mata za'a kawo abinci takwas da rabi idan ta ci ta yi isha ta kwanta kafin ya dawo. Da kyar ta tsakuri abincin tana idar da sallah bacci mai nauyi ya kwasheta saboda irin gajiya da ciwon jikin da yayi mata rubdugu lokaci guda.
Tare da su Daada Awwab yayi sallah ya nemi Ibrahim ya kira masa Emzee. Dawowa yayi yace yana kwance kamar bashi da lafiya kuma yaki bari ya fada a cikin gidan.
"Kyale shi muje dakin"
Ibrahim sauri yake yaje wurin Zayyana bai shiga dakin ba. Awwab na shiga ya same shi ya hada kai da gwiwa zaune a kasa. Kusa dashi yaje ya zauna yayi irin zaman da yayi suna zaune kusan minti biyar sannan Emzee yace "yaya zanyi Hamma?"
Ya tabbatar dole zai ji daga bakin Radhiya kuma abinda ya kawo shi kenan.
"Rahima tana sonka?"
"A da ba! Ni yanzu ban ma san me ta daukeni ba" ya amsa cikin kunar rai.
"Bana jin wannan yarinyar mai nutsuwa da hankali ga karancin shekaru za ta iya amince maka saboda wani mugun nufi. Emzee open your heart and listen to its voice. Me kake so?"
Baiyi wani tunani ba yace "Rahima"
"Shekarun baya dangina sun rabani da Radhiya a tunaninsu sunyi domin karfafa zumunci sai gashi ya lalace fiye da zato da tsammanin kowa. Idan kana tunanin za ka gujewa Rahima saboda zumunci ne you are making a grave mistake. Emzee aurenka da ita shine abinda zai fi komai saurin gyara abinda yake tsakanin Ummi da yayarta."
Da sauri ya dago kai "Allah Hamma?"
"Talking from experience" yace da murmushi "da ace tun wancan lokacin na auri Ghazalatu da Radhiya zumuncin iyayenmu da yafi karfi iyaka mata suyi kishi a junansu. Amma da hakan bata samu ba sai da akayi shekara uku su ukun suna jin haushin juna ana rigima mara tushe. Babu wanda nake fadawa amma I hate myself da na zama dalilin faruwar hakan so if you can avoid it please do so"
A raunane Emzee yace "ina jin ni fa yanzu ta dena sona ta sami wani"
Awwab ya ce "So da wahala yake komawa ki. Kai dai kada kayi wasa da damarka at the same time ka tuna cewa kaima yaro ne ko karatu baka karasa ba. Zanfi so ka gama karatun ka fito da karfinka ka yaki zuciyar Rahima har sai ta amince maka."
"To yanzu dai in kyaleta?"
"Da zancen soyayya kam ka rabu da ita ka gama karatu itama ta gama secondary. Amma try your best ka tabbatar ka mamaye rayuwarta..."
Chuckling Emzee yayi yau fa yana daukar darasi sosai "how?"
"Kada ka bari wasu mazan su sami dama. Keep her close, babu zancen soyayya amma ka bata kulawar da ko wani yazo a bayan idonka zata rufe ido ta kore shi batare da ka sani ba ma"
Haba Emzee ya rike "Allah Sarki Addata, Hamma ka rinka yi mata a hankali kada son ka yayi mata yawa"
Keyarsa Awwab ya talle yana dariya "kai kace ita, iya tace kai ni mai bada shawarar kuma baku damu dani ba"
"Daga fadan gaskiya" ya turo baki.
"Ladan kukan da ka saka min mata ne...bari na koma na barta ita kadai karshenta ta kasa....."
Kofa Emzee ya bude masa da sauri "Allah Ya bamu alkhairi ba sai kace komai ba" ya kara da toshe kunnensa kada ya jiyowa kansa.
Awwab ya fita yana dariya sosai ya ce masa "ni dai ka daure ko P.O.P ne kayi sai mu aurar da kai....ga Rahima 'yar karama da ita har ta bani tausayi"
Kamar zaiyi kuka ya ce "wayyo Hamma ya na neman fassara ni"
"Me kaji nace? Daga cewa 'yar karama to ba karamar bace?" Ya kuma yin dariya.
"Wallahi zama da Adda ya fara nunawa a jikinka ni dai sai da safe" Emzee ya bata rai ya rakoshi waje.
Tare da su Yousuf suka tafi. Yana zuwa shima kwanciya yayi yana rungume da Radhiyansa. Washegari akayi gagarumar dinner da daddare inda ma'auratan suka yi shigar buzaye su da iyayensu. Da safe kuwa kowa ya kama gabansa. Yousuf da Arifah Hawaii suka wuce honeymoon daga can kuma zasu tafi France inda gidansa yake kusa da na iyayensa.
Su Awwab ma a ranar da suka koma washegari bakwai na safe suka tashi zuwa Athens babban birnin Greece zasuyi kwana goma kafin ya koma aiki.
Duk wannan abu da akeyi babu wata alama ko kadan da Rahima ke nunawa ta damuwa sai dare yayi ta kwana tana kuka. Sabanin Halifa da yake namiji ita abin ya tsaya mata a rai fiye da kima. Da ciwo matuka ace mahaifiyarka ta cutar da wani, wanin ma kanwarta ta hanyar asiri har tayi shekaru goma babu ido. Ita nata daya ne yanzu baya bambance mata abubuwa amma yaya take ji bare wanda zai ga tsananin duhu na tsayin lokaci. Abu na biyu bai wuce mahaukacin so da tausayin Emzee da take yi ba. Ko kadan bata ganin laifinsa don ya kyamaceta. Uwa tafi karfin wasa. Ita ma bata guji Salame ba duk munin halinta ta yaya shi ba zai tsayawa tasa mahaifiyar ba..mace kamar Ummi mai kyauta da kyautatawa. Bayan dogon tunani da koke koke a boye ta yankewa kanta shawarar hakura dashi har abada. Emzee ba sa'an aurenta bane da kunya ta iya hada ido dashi bayan abinda Ummanta tayi musu. Sai yanzu ma take dada godiya ga Allah da ita ta samu a ido da wayar ba Radhiya ba. Da zasu barta ta koma Sumaila da tafi jindadi ma. A zahirin mu'amalarta da mutanen gidan duk karancin shekarunta ta iya daurewa ta nunawa Ummi bata da matsala. Har daki Ummin ta kirata akan maganar Emzee ta ce mata ko yana sonta bai taba fada ba. Shi kuma yana makaranta bare ya karyata.
Satinsu guda da gama biki har an kai Rahima sabuwar makarantarsu anyi sa'a sun barta a SS3 amma Daada yasa an dauko mata lesson teacher wuni suke suna karatu saboda ta ci WAEC tunda bata yi rejistar NECO ba kuma an riga an makara. Ummi ma ta soma zuwa Baze tana kuma samun kulawa sosai daga maigida ran gida Zayyan Tureta. Cikinta mai laulayi ne shiyasa daga makaranta sai daki saboda rashin son kamshin gidan.
A yau ana sauran kwanaki hudu su Radhiya su dawo Emzee yayi magana da Awwab wanda yace kada ya manta shawarar da ya bashi game da Rahima. Bayan sun gama hirarsu ne ya tura mata text.
Zaune take tana kokarin solving din wani aiki da lesson teacher din ya bata a physics text din ya shigo. Duk a zatonta irin na layin wayan nan ne shiyasa zuciyarta tayi wani irin bugu da ta ga sunan Emzee. Jikinta wata irin rawa ya kama yi ta bude da sauri.
(Kanwata kwana biyu boko ya boyeki. Ina fata babu wata matsala a sch din taku. All the best Rahima, Allah Ya bada sa'a. Yayanki)
Ta karanta wannan gajeren text yafi sau shurin masaki. Dama malamin nata ya tafi aikin ta zauna yi sai kuma ta kasa fahimtar komai dole ta tashi ta shiga ciki. Wayarta a hannu lokaci lokaci sai ta duba ta kuma karantawa duk da tana kwabar zuciyarta da take jinya har yanzu.