Bibiyata akeyi complete novel - Chapter 25
Bibiyata akeyi complete novel Chapter 25: Bibiyata akeyi complete novel Chapter 25. * Saida taga hankalinsu ya d'an kwanta sannan ta nufii nata shashin,…
3,144 words
* Saida taga hankalinsu ya d'an kwanta sannan ta nufii nata shashin, sai 5 hameeda tazota sunyi hira sosai, hameeda sai tsokanar *hanna* takeyi, ganin *hanna* tak'i kulata yasata tunanin MG ya kashe bakinne, Itakuwa *hanna* tausayin ay'annan bayin Allah ne yacika ta," Dariya hameeda ta kyalkyale tace Wai, su *hanna* anjii maza baki yayi shiru, aini band'auka akwai abunda zai kashe bakinnan ba," Tsaki *hanna* taja tace da'allah malama ni kindameni, idan bazakiyi shiruba Allah saina bar miki falon," Dariya hameeda ta gimtse tace," yi hakurii bani nakar Zoman ba rataya akabanii." Tsaki *hanna* tak'araja sannan ta juya mata baya. " Duk wata zolayqrta da hameeda takeyi bata kulata ba, dan tasan ba Hakan bane." Kiran sqllar magrib ne yasa hameeda tashi da niyyar tafiya, ruk'ota *hanna* tayi tace hava Sis, gaskiya bazakitafii yanzuba, kibari yadawo sai mutafii tare," Bud'e baki hameeda tayi tace, kina amaryar zaki fitafita?." Murgud'a baki *hanna* tayi tace to sai me? " D'azuma munfita, Allah yashiryeki hameeda tace sannan tace nifa tafiya zanyii," Sama *hanna* tahaura t ebo mata turaruka kayan kwalliya, da abubuwa kala-kala." Har bakin k'ofa tarakota, tana shirin fita hameeda tace kinga ki koma baki tambayi mijinki ba." Hararanta *hanna* tayi kawai, tad'an rakata tace beb samun abun hawafa zaimiki wuya a, Allah kinga dare yayi." Suna tsaye saiga captain Ahmad yazo dasauri zaije masallaci," Ganin *hanna* atsaye yasashi nufan wajan, tmbyanta yayi mai sukeyi, nan tashaida masa cewa hameeda ce zata tafii, " Kollon hameeda yayi yad'an basar, yana gyara hannun rigarsa yace," tajira nayi sallah nakaita. " Yana fad'in haka ya juya yqtafii." . Gidan suka koma Ana idarda sallah, yazo yayiwa *hanna* Magana tarakatq Har gaban mootar, sannan suka tafii tanajin kewar y'ar uwartata," Bata dad'e da tafiya ba labba tashigo,, da harara *hanna* tabita tace, " wato akawoni gidanku a ajiyenii, Amma ko leqe, dama bukatarku tabiya nashigo ko?" Kama kinnuwanta tayi tace afuwan, wallhy tun 12 nakeso nashigo ummii tahanani Wai ba'a Zuwa gidan amare," Wallhy bbu yanda banyiba tahanani yanzu ma sulalewa nayi bata sanii ba." Dariya *hanna* tayi tace dan Allah kaji ummii menene agidanmun da ba za'a zoba? " Uhmmm kawai labba tace dan batasaon taja maganar." Hira sukayi sosai *hanna* tajii dad'iin zuwanta sosai, " MG nafita daga masallaci shashin ummii yawuce, zaunawa yayi akusa da ita bayan ya gaisheta ta amsa." Cikin sakin fuska tana tambayarsa ya *hanna* sosa kayi yayi sannan yace ummii tun kafin la'asar nafita sai yanzu zan koma, fad'a ummii tabishi dashi sosai tana cewa yad'auko yar mutane zai tafii yabarta ita kad'ai," Hak'uri yabata sannan yasanar da ita rasuwar minister dakuma tafiyar data taso jibi," Addu'a tamasa Amma Har cikin ranta bataso tafiyar ba." Amma dai zaka tafii da ita ko?" D'ago kansa yayi dakekan cinyarta, yace ummii zantafii da ita bansan lokacin da tafiyar zata d'auka ba." Addu'a ummii tamusu sannan tarinqa masa nasiha akan yarigeta da amana. " D'aurawa tayi da cewa nasan kana sonta so mai tsanani Amma hakan bashi zaisa nadaina maka nasihar riqeta da amana ba." Nasan cewa zuciya batada k'ashi, Kuma dole wataran duk dad'ii akan samuu sa6ani, k'arqmar yarinya ce, dole saikayi hakurii harda irin furucinta, sannan abuu na biyu, kaji tsoron Allah kasan yana ganinka, kada ka zalumcii yarinyar mutane." Nasiha sosai ummii tamasa mai ratsa jiki, " Sannan tace yatashi yatafii yabarta ita kadai." Tashi yayi yafita," Baiwuce gidaba sannin cewa tana tare dasu karima, yasa yawuce shaidawa mai martaba." Tashi labba tayi tace kada ummii tanemeta tamata sallama tafita," Tashi tayi ta nufii shashin su karima, sanda ta tabbatar ta basu komai dazasu buk'ata sannan tajuya zata tafii, muryar karima ne takatseta, mungode Allah yasaka muku da mafificin alkhairinsa, murmushi kawai hanna tayi afili acikin ranta Kuma tace ameen, Juyawa tayi ta futa." Nasu shahsin tashiga, kawai ganin mutum tayi harta tsorata, sai zuciyarta ta hasko mata taga fuskan awajen diner d'insu, da fara'a tqk'arasa tana mata sannu da zuwa, daqyar ta amsa, gaisheta *hanna* tayi nan ma intisar kamar mai ciwon baki tace lpy." Ganin haka dake *hanna* ita kanta miskilar kantane, yasa ta ebeta ta watsar." Sunfii 10 minute bbu Wanda yacewa wani k'ala *hanna* na danne-danne awayrta, Itakuwa tad'aura d'aya kan d'aya taunar chwengum kawai takeyi." K'as K'as ne ya ishi *hanna* yasa tad'anja tsaki, d'agowa intisar tayi tace, owh srry baki sanni bako, ni cousine d'in sace, owh namanta Kuma budurwarsa, gaban *hanna* ne yayi masifar fad'uwa, lokacii d' aya qirjinta yafara bugun taratara, har wani dushi-dushi take kallo," Srry baikamata kisani yanzu ba, Amma gani nayi bbu yanda na iya yakamta ace kinsan wata na shigowa kada ki bararraje," Kinsan fa duk nisan jifa k'asa zai dawo," Sannan kada kiyi tunani ko wasa nake miki, ki rubuta ki ajiye Har indai inadarai, ya yareema kamar na aureshi angama." Ta bud'e baki zata k'arayin magana, sqiga sallamar MG, kawarda kai *hanna* tayi azuciyar tana cewa munafuki azzalumii kawai, saurin tuba tayi tana agtasfirulla tunowa da tayi cewa, ma mijinta take fad'awa way'annan kalamai koda azuciyarsane." Kallon *hanna* yayi yaga yanda ta kawarda kai kamar batajii shigowarsa b, Kuma yanada tabbacin tasan shigowarsa, aransane yace kowa yata6omin yar fitinar tawa, ko rshin dawowata da wurii ne yasa," Zuwa dabb da ita yayi sannan yace, sweety wayo ta6ominke?" Yitayi kamar batajishi ba danko Juyawa batayiba." Muryar intisar ce takatseshi, na cewa sannu da Zuwa ya yareema, Juyawa yayi ya kalleta, wata irin kunyace takamashi matarsa takasa yi masa sannu Amma wata tamasa, murmushi yayi yace yawwa habeebty yaushe kika shigo?" Gaban *hanna* ne yayi masifar fad'uwa jinda sunan daya karata wato ya tabbata cewa, ita budurwarshi ce." Wani irin zafii zuciyarta tafarayi mata," Kwallah yacika idanuwanta taff," Wannan wani irin ciin fuska ne agabanta yana kiran wata habeebty, lallai dama abunda take gudu kenan tasan cewa MG ba tsaran ta bane, dole zai nemi kyakkyawa da ajee kamarsa, " Shikuwa MG anasa wajen habeebty daya ambata al'adansu ne tun suna yara aka taso dasu da fad'in wannan kalmar ma y'an uwansu," Dan kowa yatashi dason kowa acikin zuciyarsa." Kok'ad'an dayasan wannan kalma zata k'ona rana *hanna* dabai fad'a ba." Cikin kissaa da kisisina intisar tace habeeby dear inkawo maka ruwane? " Kallon *hanna* yayi Wanda kanta ke gefe ganin ba tasan da halittarsa awajan ba sai jikinsa yayi sanyii sosai." K'ara cewa tayi nagaa amaryar tamu najiin kunya ne." Shiru yayi sannan yace ok tom, Danshi MG arayiwarsa bai iya baonsa mutumba, " Tashi tayi tafii hanyar falon data hango frigde aciki tanayi tana karairaya." Shikuwa Wanda takeyi dominsa baima saniva dan hankalinsa nakan sweetynsa, tashi yayi yazo wajanta, yana tambayarta maiyafaru Amma firr tak'ii magana, bayanda beyiba hankalinsa ne yatashi, baisandai menene ba Amma ya lura kamar Zaman intisar ne ya6ata mata rai, idankuwa hakanne mai take nufii kenan?" batason yan uwansa kome? " Dawowa tayi da robar fayrouz ahannun ta dakuma na swan, tana Zuwa ta ajiye." Kallonsu ahaka ya sosa mata rai amma tadake tace ya habeeby dear gashi nakawo maka, tashi yayi da toh, ya isa wajan, intisar hadda kissaa ma Amma asali tafii ki ransa da yaa yareema,ganin yanzu tanayi baya gwaleta ne yasata zak'ewa." Fayrouz ta Zuba masa acup yak'arba yana Sha, nanne Kuma hakurin *hanna* yak'are ganin cewa dazasucii abinciin rana tad'auko masa fayrouz yace ta canja Amma yanzu ya k'arba, lallai yanzu tayarda namiji dakalin majina ne ka haushi ka sule," Shikuwa MG ganin ita matarshine yanadakyau tasan abunda yakeso da Wanda bayaso yasa yace ta canja Itakuwa intisar da saninta da rashin sa bbu amfanii." Tashii tayi da gudu tayi sama tana Zuwa ta kwanta akan gado tacii gaba da kuka." Shikuwa MG yayi niyyar binta amma intisar ta tsareshi da sururtu ba ita tasakeshiba sai 10, a lokacin *hanna* tayi kuka Har k'arfinta yak'are tayi samada 2hour's tana kuka." Banda nishi da ajiyar zuciya bbu abunda take iyawa." Bayan ya kulle k'ofa d'akinta yfara nufa, ayanayin daya ganta yai, bala'in birkitashi." Dasauri yak'arsa yad'agota yasata ajikinsa hannu biyu tasa tana dukansa tana tureshi, " Amma bai kyaleta ba, sanda ya manna ta dajikinsa yacii gaba da lallashi." Sai kusan 10 tukun tabar dukansa tafara ajiyan zuciya, ganin yak'ii saketa yasata dallara masa cizo ak'irjii, runtse ido yayi yajii zafiin Amma zafin kukanda takeyi yafii k'onashi. " Ahaka Har bacci yqd'uketa, Jin saukar numfashinta ya tabatrs masa sannu hakan." Tunanii kala-kala yarunga yi arnsa, sannan shima ahaka bacci yad'aukeshi. "
To be continued
Ur's *Z33iiyyb3rw3r*
*BIBIYATA AKEYI*
_Bismillahirrahmanirrahim_
Writing by © _Zaynab Bawa_ ( _z33iiyyb3rw3r_ )
_Like my page on Facebook :::Zaynab BAWA novels_
Followed me on instagram ::::mhiz_z33iiyyb3rw3r
Ka/ki zamo mai yawan karanta, ```Allahumma ajirni fi musibati, wa'aklifli khairan minha``` aduk lokacin ka/ki ke cikin wata musiba."
Ka/ki kasance mai karanta ```Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla, wa'anta taji'alul amra iza shi'itah sahla``` aduk lokacinda wani abuu yashige maki/ka duhu, kukoma kanajin wuyar aikata abun."
*Ka/ki kasance mai karanta,* *```Allahumma antassalamuwaminkal salam tabarak ta ya zul jalalu wal'ikram``` *aduk sallah bayan ka/kin idar."*
*Shawara ce*
================
Page 66 * Ahaka har kiran sallan farko." Bud'e idanuwanta tayi ahqnkali da suka mata nauyi, har sund'an kumbura." Jinta ajikin mutum yasata d'agowa tana dubansa, bacci yakeyi azaune, ita kumbura tana jikinsa gabaki d'aya, tausayinsa ne yakamata tatsaya tana kallon sa yana sauke numfashi ahankalii." Bud'e hannunshi tayi tasauk'a da niyyar zuwa toilet tad'auro alwala dinyin sallar raka'atanil fijr." Har tafara tafiya ya ruqota, gabantane yahau fad'uwa dan batayi tunanin ya farkaba, abunda tamasa jiyane yadawo mata, harda cizon data masa, wata irin kunyar sace ta lullu6eta." tashi yayi yazo dabb da ita, itakuna ta sunkuyarda kai k'asa yace ina zakije." alwala zanyi tabashi amsa, sanyi yajii aransa, jinyadda ta amsa masa that means tadaina fushin kenan, murmushi yayi sannan yace, kiyi hak'uri kinjii, kiyi hakuri if i hurt u knwnly or u knwnly, wallhy bansan ganin hawayenki, zafii nakeji acikin raina," Hawaye ya sulalo afuskarta dasaurii ta sa hannu da niyyar gogewa, yayisaurin riqe hannun yace," Sweety akawai abunda namiki plz kisanar dani." Shiru tayi yajawota jikinsa, lafewa tayi ak'rjinsa, amma tayi shiru, jijjiaga yayi yace plz say ur mind dear, cikin son yin kuka tace bakai bane kace mata habeebty, gabansane yayi mugun fad'uwa, yaja hannunta suka zauna akan gado yace, Sweety duk family d'inmu haka muke kiran juna, ko bakiji haka nake kiran labba bane, turo baki *hanna* tayi tace, shine itama hadda wani cemaka habeeby dear, ita kuma labba aibabu aure atsakaninku, tafad'a hawaye na gangarowa fuskarta, babban yatsansa yasa ya goge mata hawayen, yace," Kiyi hakuri daga yau nabarii." Gyada kai tayi tace shine ka kar6i fayrouz ahannunta kasha nikuma kace nacanja maka." Dear ainii banga amfanin cewa ta canjaminba." Kinga ke matatace dole kisan abunda nakeso da wanda banso, itakuwa banga amfanin saninta ba." Murmushi tayi tace najii amma Allah kadena kallonta, nadena sarkin kishii, sanda yafad'ii kalmar kishii saikuma kunya takamata." Gyaran murya yayi sannan yace, haryanzu fa tunanin yanda za'akaisu nakeyi, suwa?" *hanna* tatambaya saikuma tace owh srry natuna way'annan yaran, sake baki MG yayi yace babbar cikinsufa tabaki samada shekara biyu amma kike kiransu yara." Aidai ita yarinyace tunda nayi aure itakuma batayiba." Bud'e baki MG yayi yace wani aure?" Aurenta haryanzu bbu tabbacin yinsa," Idan kinaso asan kinyi aure kibarii nakafa miki shaida," Dan haryanzu baki cika farillan aurenva." Yi tayi kamar batajii maiyaceba, takawar da zancen da cewa." To maiyasa bazamu zauna dasuba?" Dazamu naima musu wajen zama, cikin hikima yace tafiyace tatasomin dole ana buk'atana a russia so bansan lokacinda tafiyar zata d'aukeni ba shiyasa, cikin damuwa tace to kabarnii mana." Girgiza kai yayi yace bzan iyaba, banyi miki k'aryaba, jikintane yayi sanyi tace, kana ganii to mezai hana, akaisu bauchii wajan mama, nasan zata kula dasu, jijjiga kai yayi yace, kina ganin zata yarda, zanirata tace, " Kokuma muje kaga saimu mata sallma," harara yawulla mata yace bazakace ba, kwata - kwata kwananki ukune da barin gidan yana fad'in haka ya taashii yashige toilet." Dasafe kamar jiya yauma tare sukayi breakfast, bayan sungama tad'auki kulolin takai musu, tayi musu sallama sannan suka d'auki hanyar bauchii, tana futowa dakinta tanufa ta dauko sannan ta sauko tazo dai-daishi ta zumbula hijabinta sannan tace muje." Tashi yayi suka nufii shashin kilishi, afalo suka samii intisar na zaune, ganinsu yasa, gqban intisar fad'uwa badai harta sauko ba daga fushin datayi jiya," Indai hakane zatasha wahala da ita kenan tunda, tanada saurin sakkowa." Da harara tabi *hanna* itakuwa *hanna* tasake mata wani malalcin murmushi mai ma'ana dayawa,, k'ulewa tayi da murmushin, yasa tatashi tayi d'aki fuu, *hanna* ta d'aga murya yanda zata jita inkinahiga kikira mana umma, Tsayawa tayi cakk da bak'in ciki wai ita take aika, bata iya juyowaba tafice, shikuwa MG juyawa yayi ya kalli *hanna* yace bata girmeki bane kike aikanta?" D'aga kafad'a yayi yace idanma tagirmeni ai yayanta nake aure, kaga dole ta girmamani, " D'aga kai yayi yace wato kin iya kiran aurannan abaki, shigowar kilishi ne yakatse musu hirarsu, gaisheta sukayi had'eda yimata sallamar tafiyar, bataji dad'in tafiyar ba dan intisar tabata labarin yanda sukayi jiya." Adaddafe ta musu addu'a sukuma suka fice, MG kuwa abinda ke ransa dabanne shiyasa baison sakewa yara fuska, gashi jiya d'an sakewa intisar dayayi haryau taganshi tak'ii kulashi, anyi nafarko dana k'arshe yace acikin ransa, azaune suka samii ummii gaisheta sukayi ta amsa da fara'a d'an hira suka ta6a sannan ummii tace sai zuwa jimawa zaku tafii kenan?" Ina fa? " yatambayi ummii, sallama da mahaifanta mana, au ummii sai munje?" Auda haka zaka d'auki yarinya Ka tafii da ita batareda ta ga iyayenta ba." Zuwa jimawa kubi flight kakaita sannan Idan kundawo kuje Gidan abbanta, kasan sassafe zaku wuce." Dan haka katashi kuje kayi muku booking." Amsawa yayi ta to, itakuwa *hanna* farinciki yacikata, hakanne yasa tasacii kallonsa ta gefen ido, ga mamakinta taga damuwa sai taga fuskarsa asake," Suna had'a ido yasake mata murmushi sannan yayiwa ummii sallama yafita." Tashi tayi tanufii d'akin labba, hira sukayi sosai ba ita ta, fitaba sanda yasanar da ita akan tafito sutafii." Basu dad'e da isa ba su karima suka isoh." Tayiwa baba, mama da Ammah bqyanii sun fahimceta sannan sanyi alk'awarin riqesu kamar y'ay'ansu harzuwa dawowansu." Dakyar *hanna* tabar gida harda d'an kukanta MG yasha aikin lallashi Bayan zuhr kad'an suka dawo, sunyi la'asar sannan suka nufii gidan umma, tayi murnar ganinsu, sosai nan da nan tashiga hidima dasu, MG kuwa yasake da ita bakamar yanda yakejin kunyar mama ba." Kunun aya takawo musu da zobo dayasha cocumber, yasha MG yakeyi yana santii ya kalli *hanna* ya d'aga mata zo6on yace," inafatan kin iya? " Murgud'a baki tayi tace," Ko na iyama bazanyiba, auhaka kikace? " eh tabashi amsa atakaice, ok zamu ganii, suna tashi tace, umm.... Nace dan Allah muje gidan anty afeeya mana." Kallonta yayi yace, idanbaki fad'ii sunana ba, ba yanda zamuje, marairaicewa tayi tace yaa yareema muje gidan anty afeeya plz." Murmushi yayi maikyau wanda sanda gefen kumatunsa yalotsa," yatsa tasa ta danna dai-dai kan dimpull d'in, sanda yatsanta yad'an shiga ciki, murmushi yak'arayi ya lumshe idonsa yanajin sonta cikin jikinsa." Sun isa gidan anty afeeya sai murna take da ganinsu tunda take da yayan nata bai ta6a zuwa gidanba saiyau ta dalilin matarsa, dan tasan bayin kansa bane." amma tayi farinciki sosai, Basu dad'e ba suka tashi tafiya, leda guda tabawa *hanna* wanda nikaina bansan na menene ba." Har gaban motocinsu tarakosu, yaronta namusu byebye." Sai gidan samha, nan ma basu dad'e ba, sun d'auki hanyar gida, *hanna* tace bazamuje mugaida moddibbo bane?" Nishi yad'anyi kad'an yace kin tunomin ma, banje masa sallama ba, yayi murna da ganin su sosai, Addu'a yayita musu, daga k'arshe yake tambayar *hanna* inadai tana Addu'a eh ta amsa masa," To Allah yamiki albarka ta amsa da amin." Sai dabb magrib suka yiyo gida, masallaci itakuma ta shiga yiwa ummii sallama saida tayi sallan magrib da isha acan sannan MG yashigo suka koma tare." K'arfe takwas dai-dai suna falon saiga intisar Ko sallama bbu tayi kawalliya kamar mai zuwa gasar kyau." Alokacin. MG nakwance acinyar *hanna* tana wasa da gashinsa." Ranta ya6aci ganin su haka amma tashare dan kilishi tashaida masa cewa har Indai zata ringa zuciya toh bazatacii nasara ba." Da karai raya iso tazauna ta gaishsahi karaf *hanna* ta amshe tace lpy klau knawarmu yagajiya?" Takaicine yakamata lallai *hanna* taraina ta itance zata gaidata." Murmushin dole tayi ganin idon MG abud'e, can *hanna* tace plz habeebty dan d'aukomin ruwa afridge, kinjii tafad'a tana dariyar shu'umancii." Intisar Yi tayi kamar batajii ba, kawai tsinkayan muryan MG tayi yana cewa, kihad'omin da fresh milk, bayadda ta iya haka tatashi tanufii fridge fresh milk kawai tadauko da cup takawo, masa ganin bbu ruwan yasa yace ina ruwan yake? " Mikomin kikoma kidauko mata, bak'in ciki ne yacikata, dazata miqa masa sanda tad'an rusuna saman boobs d'inta yafito." mistakely idon MG yakai wajan rintsa idanuwansa kawai yayi atake tsikar jikinsa yazuba." Rintse idanuwansa yayi *hanna* ta cafke gorar tace plz d'aukomin ishirwa nakejii." Sanda ta galla mata harara sannan ta nufii fridge tad'auko ta dangwara mata." Aranta tace ohowdai kind'auko." Tana zaunawa baifii da 5minute ba *hanna* tace dan wanke mun plate dinda mukaacii abincii, guda biyu ne bbu yawa, bak'in ciki kamar yakasheta hararar datakeyiwa *hanna* kuwa kamar idanuwanta su fad'o." kenan 2 minute bata kulava, yace bakiji mai tace miki bane?" Tana k'unk'uni tatashi tad'auraye, ita arayuwarta ba wanke wanke takeyiba." Tana gamawa tafito tasamu *hanna* itakad'ai MG yashiga d'aki." Kallon *hanna* tayi tace bani kikayiwa wulakancii ba? " Hmm ayanzu bazaki gane matsayinki ba harsai nashigo gidan tana fad'in haka tajuya tafice." Kulle k'ofa *hanna* tayi, tahaura stairs d'akinta taje tayi wanka tafito sa wata y'ar ficiciyan sleeping dress tayi." Sannan tayi light off ta kwanta, tasan bbu amfanin rufe k'ofan dan yanada key d'in." Cikin bacci taji kamar ana kiranta, Bud'e ido tayi sannan ta kunna bedside lamp, MG ne tsaye idanuwansa sun canja kala kamar maijin bacci." Zama yayi kusa da ita sannan yajawota jikinsa, tana shirin yin magana yahad'e bakinsu waje d'aya." Taso hanashi amma hakan yafaskara," shin yana mata wasu abubuwa masu wuyar fad'a yasata fara tureshi," Yakai hannuwansa cikin rigarta tayi saurin riqe hannun tana kuka, ganin kukanta ya tsananta yasashi saketa yana bata hakuri." Ahaka bacci yad'auketa." Da asuba sanda MG yayi wanka kafinnan yayi sallah itakuma tayi sallah, sannan suka wuce aminu kano airport, K'arfe bakwai jirginsu yad'aga zuwa airport."
To be continued
Ur's *Z33iiyyb3rw3r*
*BIBIYATA AKEYI*
_Bismillahirrahmanirrahim_
Writing by © _Zaynab Bawa_ ( _z33iiyyb3rw3r_ )
_Like my page on Facebook :::Zaynab BAWA novels_
Followed me on instagram ::::mhiz_z33iiyyb3rw3r
*Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace, duk wanda yayi sallah yaban ya idar ya karanta Ayatul kursiyu, bayan kowacce sallah, bazai mutu cikin wannan dareba face Allah yagafarta masa duk zunubansa."*
*Manzon Allah zira da amincin Allah sutabbata agareshi yace, duk wanda yakaranta suratul iklas sau koma arana, bazai gushe ba harsai angina masa gida acikin aljanna."*
===============
Page 67