Kenza eBookz

Boyayyen mutun complete - Chapter 22

Boyayyen mutun complete - Chapter 22

Boyayyen mutun complete Chapter 22: Boyayyen mutun complete Chapter 22. Hawa kanta Abba yayi cikin gushewan hankali dawata irin maitan sha'awa yawani irin…

3,416 words

Hawa kanta Abba yayi cikin gushewan hankali dawata irin maitan sha'awa yawani irin kama kirjinta da hanunshi yana matsawa yana ihu yana mata kiss awuya. "wayyo Allah na Princess wlh kinfi Mummyn ki dadi, kinfi Mummy Zaki, Princess u are bless, Princess kinga ban mama dan Allah, kiban mama dakanki kaman irin ni jaririn ki dinan, wayyo princess ban mama mana haba princess din Abban ta, nine nadake ki to yahakuri oya ban mama" ko kadan baiji alamun anama murza handle din kofa tawaje ba hankalin shi yay nisa sosai, cikin dishewan murya yana matsasu yace "au baki hakuran ba, bazaki ban maman ba shikenan" hanunshi yakai azafafe kan pant dinta yana kokarin janshi kasa aka wani irin bugo kofan dakin aka shigo, afirgice ya tashi daga jikinta kafafunta na oc shi yana kare abinshi dake amike sambal da hannu gabanshi na faduwa dan atunaninshi ma police din daya zubane sukaji hala hayaniyan su sukazo suka balla kofan dan suga kome yafaru, wani irin kunna wutan dakin Marwan yayi haske ya gauraye dakin tun daga katon pooo da kafarshi ke gab da bugeshi yabi da kallo har zuwa kan gadon inda yaga matarshi lying down a sume, looking so helpless babu kaya jikinta sai pant, fuskarta ya kumbura sosai yay molo molo sabida punches din da Abba yamata, gefen idanunta na jini gefen bakinta ma najini, hancinta yay jajir gatanan kaman mara rai. Tun daga kafafun Abba daya ware nata na tsakiyanshi yake kallo zuciyarshi nawani irin tafarfasa data dade batayiba, da wani irin zuciya kaman zaki yay saitin gadon da sauri Abba da jikinshi ke rawa sosai idanunshi kwalale awaje heart dinshi na beating na tsoro ya tusa abin tashi datai kwanciya dole tsabagen tashin hankalin daya shiga ya maidata cikin wando, wani irin finciko shi Marwan yayi yawani irin watsamai mari Mum tana tsaye bakin kofa tana kallo dantama kasa shiga zuciyarta ya mugun tsinke, wani irin marurruka Marwan kemai kaman mahaukaci nan da nan, nan da nan a fuskar Abba, mari left right, left right kawai yakeyi mai kafin yasakin mai wani irin punch a hanci da saida kanshi ya bugu da bango jikake bum idanunshi suka fara juyawa sabida azaba da radadi, da sauri Mum ta shigo dakin ta dago Nadeera tana kuka sosai tana kallon fuskarta ta rungumeta tsamtsam ajikinta tana kiran sunanta ahankali "Princess, Nadeera" da sauri ta warware gyalen kanta ta rufa mata ajiki tasake rungumeta tsamtsam tanajin yanda Marwan ke bugun Abba.

Wani irin tadiye Abba yayi da kafa Abba yay wani irin mummunan faduwa akan tiles din dakin yana kara saiga hakorin shi biyu nagaba akasan tiles, ball ya shiga yi da Abba danji yake ya kashe shi kawai how dare he looked at his wife, ashema ba ubanta bane, mugun ball yay da Abba ya bugu da bango yadena numfashi, yazo zai kara takashi yaji karfin kukan Mum dake rungume da Nadeera yakaru sosai, hakan yasa yajuyo yawani irin kafe Nadeera dake sume da ido ahankali yawani irin tako zuwa wajen ya sauke jakar jikinshi yacire hoodie dake jikinshi, wani irin karbanta yay daga hanun Mum yanajin bakin ciki kaman ya haukace ya samata hoodie yana kallon yanda jikinta dukya baci da amai harda hancinta daya dame da ragowan amai da jini, hijabin ta daya gani akasa ya dauka ya saka mata ya goya jakanshi a zuciye abaya, yawani irin dauketa batare daya kalli ko Mum dake kuka ko Abba dake sumeba yajuya yakai bakin kofa harzai bude kofan ya tsaya chak batare daya juyoba cikin wani irin murya na wanda yay fushi sosai dake stammering i'i'na ayace "te te tel tell this g..goat" yay shiru yana numfashi tsabagen fushi cikin wani irin tsawa yace "wlh ko hanun matata yasake tabawa, warabbul ka'aba! saina kasheshi har lahira" yawani irin bude kofan yafita daga dakin bayan ya jefar da key motan momy dake hanunshi acikin dakin yawani irin sauka kasa yafita tsakar gidan ya tsallake polisawan dahar lokacin ke bacci yabude kofa yafita ya tsallake na waje yay saman layinsu da ita, ahankali yahau machine dinshi ya daurata agaba ya kulle hannayenta abayanshi yasaka hamlet dinshi yawani irin ja machine din da mugun gudun bala'i yahau kan titi. [10/17, 6:01 PM] Aishat Muhammad: *Maman Abd Shakur*

*AR*

Sosai take gudu akan keken, kutsawa cikin dajin kawai takeyi batare datasan inda ta dosaba, tai tafiya kusan na minti goma taji kafafunta sun sage da tukin keken hakan yasa ta rage gudu tana goge zufan goshinta wani dandamali keken yaci karo dashi hakan yasa da ita da keken suka wani irin juyi tadinga tumble tumble tana gangarawa dan slope din har takai wani bishiya ta wani irin buge da bishiyan ta sume awajen jini nabin kafafunta da gefen goshinta.

Yakai kusan 15min abayi sanan yafito, shirya wa yayi a closet tsaf wani black hoodie da dogon wando yasaka da talkami yasa face mask dinshi dana hannu dan akwai inda zashi, feshe kanshi yayi da turare sanan yakoma gaban bayi yadau wet dogon riganta dake kasa ya bude bayin yasa a washing machine sanan yafito ya bude kofa yafito dakin, sosai gabanshi ya fadi ganin gadon empty babu kowa akai, ahankali ya juya yabi ko ina na dakin da kallo ganin wayam babu ita yasa da sauri yay wurin kofa ya bude yafita yana waigen waige yana kwala a kaninshi kira. "Abdallah, Omari, Omari!" sauka kasa yayi da gudunshi yana kallon ko ina, yay kitchen da sauri, babu kowa a wajen yafito yana wani irin kwalama kanin nashi kira "Abdallah, Abdallah Omari!" yawani irin daka ihu azafafe "Abdallah!" da gudu Abdallah dake daure da towel yafito daga sama yace "Ya Marwan menene kasa naji tsoro wanka nake saisa ban amsaba yanzunan nadawo daga sport ya Omari tun dazu yafice" yay maganan yana saukowa daga benen, muryan shi har rawa yake yace "w..where..have you seen my wife?" girgiza mai kai yayi yace "yanzun nan nadawo wah happen?" hanyar waje yayi da sauri yace "I can't find her go and get dress" da sauri Abdallah yace "wat?" amma harya fita sama yakoma da sauri ya sako riga da wando yafito shima saida ya zagaye gidan sanan yabiyoshi waje amma harya hau kan bike dinshi yay gaba azuciye.

Lashe mata kafa dataji anayi yasa ta farka a firgice, raguna tagani kusan guda hudu da yaransu sun zagaye ta suna lashe inda ke jini a kafarta kaman tadawo abinci, wani irin ihu tayi ta ja kafar nata a tsorace tana komawa baya tana kallon su yanda suke mata "emeeee" aka, mikewa tsaye tayi da kyar tana dafa bishiyar ta arce da gudu tana kallon raguna data firgita su suma sun kwasa da gudu tasake fasa ihu, sosai take gudu da duka karfinta tana juyawa tana kara kallon saman dajin gabaki daya batasan inda zataba, karan motoci dataji yasa tawani irin kara karfin gudunta tana numfashi, bigewa tayi da bishiya taji kanta na juyawa da kyar ta koma baya sanan ta cigaba da gudu kaman tababba, yanka dajin kawai take jin karan motoci yasa tawani irin fashe da kuka takara karfin gudunta tai hanyar da kyar ta iya fita taganta akan titi mai kyau davatasan kona ina bane, fashewa tasakeyi da kuka sosai titin ma daidai motoci ke wucewa da gudun gaske, gudu tacigaba dayi duk motan dayazo tana kokarin tsayar dashi amma basa tsayawa, sosai tai gudu na kusan minti shida, hango wani Fulani man mai kiwo tayi yana kada shanun shi da raguna hakan yasa tai wajen da gudu ta ta tsaya kusa dashi cikin kuka tace "malam dan Allah ka aramin wayanka nakira mamana wani zai saceni ne" yanda take kuka yasa yace "assha yarinya garin yaya? Aiko saidai kiyi fulashin wayanta a kwadala tai aggareta" gyadamai kai tayi tana share hawayen ta da bayan hijabin ta, ya ciro wayarshi rakani toilet daga aljihu ya mika mata yana gyara rokon sandar kada shanun hanunshi, tsugunnawa tayi a gefenshi har lokacin jikinta baibar rawa ba tasaka number Mum tai dailing akashe, fashewa da kuka tayi tasaka na Ya Muhsin shima akashe sosai tafashe da kuka har dan Fulani na tambaya lafiya ta girgixa mai kai, number Ya Ahmad ta saka saida yakusa katsewa sanan aka dauka kafin ma yay magana tafashe da kuka tace "Ya Ahmad come and pick me kafin ya kamani am scared" daga tachan bangaren ya Ahmad dake tiki zaije siyo wani allura awani babban pharmacy daza ama ya Muhsin ya kalli wayar sanan ya maida a kunenshi, kukan ta dayaji yasa yace "Princess, Nadeera kece" gyadamai kai tayi bakinta narawa tace "kazo ka daukeni Ya Ahmad nine, zai kamani nagudo ne ina bakin hanya wani Fulani na ari wayanshi nakiraki Ya Ahmad kazo please baida kati call me" katse kiran yayi yakirata da sauri ta amsa yace "calm down princess yimin magana anatse, yanzu kikace kina ina kinsan wani bakin titi kike? Inane wurin?" girgiza mai kai tayi ahankali tace "I don't know" da sauri yace "bame wayan to" mikama dan filon tayi tace "gashi yayana" karba yayi tana share hawaye tana Kalle Kallen titin daga tsugunnon miko mata wayan dan filon yayi yace "gashi zai miki magana" karba tayi takara a kunne Ya Ahmad yace "kina jina princess zaisaki a mota dazai taho dake cikin Abuja zan jiraki a zuba" gyadamai kai tayi daidai nan dan filon harya tare mata mota ya kalleta yace "zokije Allah tsare gaba, sai akula akuma kiyaye" tashi tayi arude tana kallon hanya kafin taje ta shiga motar bama tamai godiya ba tsabagen rufewa, dama mutum daya ya rage a motan yacika direba yarufe motan yakoma gaba yatada yaja, sosai take kuka tajuya tana kallon baya daidai lokacin taga boyayyen mutum sanye da hoddie dinshi da face mask akan machine ya tsaya daidai bakin hanya yana waige waige, da gudu ta juyar dakai ta dukar dakai kasa tana kuka ahankali, kafe motan yayi da ido saikace yasan tana ciki yabi motan da kallo harta bacemai jikinshi na fadamai tanaciki.

Daidai lokacin Abdallah ya iso akan bike dinshi yace "kaganta kodai mukoma cikin dajin ne Ya Marwan muduba da kyau?" girgiza mai kai kawai yayi batare dayay magana ba tsabagen yanda zuciyarshi ke tafarfasa, wani irin tada machine din yayi a zuciye yadau hamlet ya kafa yajuya yakoma cikin dajin shima Abdallah yabi bayanshi.

Saida suka kai zuba aka sauketa driver yace " kawo kudinki" waige waige tafara ko zataga Ya Ahmad daidai lokacin ya sauko daga motar shi idanunshi boye cikin bakin glass yazo wajen wani irin fashewa tai da kuka tace "ya Ahmaddd" kafin tafada jikinshi ta kankameshi tana kuka, wani irin murmushi yayi mai ciwo ya ciro kudi da baima san yawan su ba ya mikama direban daya tsaya yana kallon su, karba yayi yay godiya yakoma cikin mota yatada yabar wajen ahankali Ya Ahmad ya dago fuskarta yana wani irin kallonta kafin yasa hannu ya share mata hawayen yace "stop crying" gyadamai kai tayi ya rike hanunta sukai inda yay parking, agaba ya sata yarufe kofan sanan yakoma ta mazaunin direba ya zauna yatada motar tana kallon titi dukansu sunyi shiru yana tafiya, ahankali tace "am hungry Ya Ahmad" gyadamai mata kai yayi yay parking agaban wani eatry nakan hanya ya kalleta yace "am coming" fita yayi ya shiga eatry bai wani jimaba yadawo dauke da abinci a ledan earty da drink da ruwa side dinta yabude yabata sanan ya rufe yakoma ta dayan side dinshi ya zauna ya kunna motar yana kallon yanda takecin abincin, sosai taci takoshi sanan ta rufe abincin ta ijiye akasa tasha ruwa ta ijiye kafin ta kalleshi ahankali tace "Ya Ahmad ina Mum take" batare daya kalletaba yace "hospital" da sauri tace "menene batada lpy ne?" girgiza mata kai yayi batare daya bata amsaba kaman zatai kuka tace "Ya Ahmad please wurin Mummy zaka kaini kaji" gyada mata kai yayi yanajin wani irin tausayin ta, thank God ma Abba yafita daga asibitin yana kaita wurin Mum zasusan yanda za'ayi.

Tafiyan kusan 20min sukayi sabida holdup sanan suka kai hospital din, a parking space din asibitin sukai parking ya kashe motan yafito yana kallon wurin kafin ya zagayo yabude side dinta yana kallonta, ahankali tafito tana kallon ko ina, hanunta yarike yace "muje" binshi tayi tana kallon ko ina tace "Mum batada lpy ne Ya Ahmad?" girgiza mata kai yayi yace "no ba ita bane" da sauri kaman zatai kuka tace "to waye baida lpy" ahankali yace "Ya Muhsin" tsayawa tayi chak ta kalleshi bakinta na rawa sosai tace "Ya Muhsin?" gyada mata kai yayi ahankali, fashewa tai da kuka suna tafiya tana share ido har suka kai gaban dakin, ahankali Ahmad yatura kofan dakin ido da ido tayi da Mummy ta dake zaune kan kujera tai tagumi tana facing Ya Muhsin dahar yanzu baisake farfado wa ba anamai karin ruwa, wani irin kallo Mum ke mata mata kasa magana tsabagen mamaki, wani irin rushewa tayi da kuka ta shiga dakin da gudu tafada jikin Mum tana kuka sosai tace "Mum, Mummy na I really miss you Mummy, Mummy karki kara barina ni kadai kinji" ahankali Mum dataji kuka na zuwan mata ta dage ta danne ta dagota tana kallon fuskarta yanda taga ta rame mata idanunta sunyi zuru zuru sun fada ciki, yauce rana ta farko dataji ta tsani rayuwanta, ta tsani sana'a da business datasa agaba, tafifita su sama da komi na rayuwanta amatsayin ta na matan aure, jibi matsalan data jawoma kanta yanzu, matsalan da bamata da basirar magance wanan matsalan, batada tunani da dabaran magance ta.

Ahankali ta daga hannu ta share mata hawayen fuskanta tass tace "how did you get here Princess ya akayi kikazo nan ina mijinki? Tayaya kikazo?" komawa jikin Mum tayi ta kankameta kaman zata koma cikinta tana wani irin jin natsuwa aranta data dade bata jiba uwa dabance ako ina, cikin sheshekan kuka tace "tunda naji kin dawo kina nan shine na gudo" "kika gudo?" Mum tafada cikin tsananin bacin rai, gyadama Mum kai tayi a jikinta tace "eh Mum nakira number ki akashe na Ya Muhsin ma haka shine nakira Ya Ahmad, Mum wat is wrong with Ya Muhsin?" tai maganan tana kallon Ya Muhsin daya ramemata a ido, dago kai Mum tayi tama Ya Ahmad wani irin kallo tace "ubanwa yace kaje ka daukota wen u know the problem on ground bazaka iya kirana ka sanar dani ba" cikin masifa yace "Mum kidenamin magana haka, d so called gang kikeso ta zauna dashi? And I tried calling you wayanki akashe, d problem on ground can be solved another way bamu barta ta rayu da gangster ba, yanzu on your phone ki kira kawarki Maman fauzy na kaita gidansu let her stay dere kafin Ya Muhsin ya warke musan mezamu yi" ya kalli Nadeera datai lamo ajikin Mum tana sauke ajiyan zuciya kaman wacce tai dambe da mutum dari gaban goshinta nadan jini na kurjewa yace "stand up princess muje ayi cleaning wound dinan mutafi gidan su Fauzy" da sauri ta dago kai ta kalli Mum, Mum din ma wani irin kallonta take shaidan na raya mata wasu abubuwa aranta dan yauce rana ta farko dataga kyan da Abba yake fadi, kyan data saba gani a fuskan Nadeera kyan yarta ne amma yau taga kyan da kowani da namiji zai gani yakuma yaba hakan yasa taji wani iri amma ta danne tana karantoma zuciyarta Nadeera yarta ce tadena kawomata irin abunan, ahankali ta shafa kumatun ta, tamata peck a wurin tana murmushi, harta bude baki zatayi magana aka bude kofan dakin aka shigo wani irin faduwa gabanta yayi batasan lokacin data rike rigan mum gamgamba tana zare idanu, tsabagen rudewaAbba wayan dake kunenshi salubewa yayi yafadi akasa hanunshi dake rawa sosai ya daga yay pointing Nadeera, cikin tsananin rudani da mamaki yace "Princess" da sauri ta saki Mum tareda dirowa daga jikinta takoma ta bayan kujeran datake ta tsugunna tana jan gefen rigan Mum jikinta na rawa sosai, da sauri Abba ya maida takaran dake hanunshi na test din da akama Muhsin Aljihun gaban rigan shi yakarasa shigowa dakin yana dumfaro inda suke, fashewa da kuka sosai Nadeera tayi tanajan rigan Mum tana yarfe hannu kaman taga dodo, mikewa tsaye Mum tayi cikin tsananin fushi tasha gaban Abba dake nufosu bilhakki tace "ina zaka Alhaji wai wat is this a hospital mukefa don't start with dat rubbish of yours, kagadai Princess doesn't know anything about that stuff please Alhajina respect your self kaga danmu kwance mubar shi yahuta yasami lafiya am begging you Alhajina let princess be" wani irin matsiyacin kallo Abba yama Mum ya nunata da yatsa yace "Hajara inba so kike na daddaka ki na tijaraki a hospital dinan bayau ki matsamin naduba yata cikin salama" ya nuna mata gefe da yatsa alamun ta matsa, kin matsawa Mum tayi hakan yasa ya gyada kai yaje ta gefen ta zai wuce Nadeera tawani irin fashe da kuka tanajan rigan Mum, shan gabanshi Mum tayi tarike kugu tace "Alhaji leave this girl alone ha'a wai meke damunka ne? Alhaji lafiyan ka? Kodai ammaka ne? Bakaga tsoron ka takeji ba yarinyar nan na bukatan hutu Alhaji am begging you kabarta, kabarta mana, Ahmad" ta kalli Ahmad daya jingina da bango ya runtse ido dan jiya ke kaman ya kashe mahaifin nashi daya koma bunsuru, tace "come and talk to your father o, wai wat is this Alhaji kaci maita ne kokuma haukan tsufa ce dan gaskiya you are not okay" passs! Passs! Abba ya sharara ma Mum lafiyayyun mari har biyu dayasa Nadeera wani irin zabura ta mike tsaye tana kallon Mum, Ahmad kuma yayo wajen da gudu yawani irin yo kan Abba kaman zai mareshi yana huci kaman mayunwacin zaki yanama Abba wani irin kallon tsana, wani irin kallo Abba yamai da jajayen ido kafin ya mikamai fuskarshi yana turemai kirji dakai yace "to mara kunya zaka rama matane? Nace zaka rama matane?" Yana maganan yana buga kanshi a kirjin Ahmad kafin ya dago ya nuna shi da yatsa yace "kama rama mata kaga yanda duniya zatayi dakai, yaro ya mari ubanshi yaga gayya, kuma kasan kamatudini tudan" yajuya ya kalli Princess dake tsaye tana kuka sosai tarike hanun Mum da tunda Abba ya zuba mata mari biyu kanta ke kasa tana share hawaye, wani irin fizgo hanun Nadeera yayi hakan yasa ta fashe da kuka sosai ta rike hanun Mum gamgam. "Mumm save me". janta Abba yayi yace "nace kizonan mutafi gida ko, am going to lock you up adaki, baki bafita harsai an raba dan shegiyan so called auren nan, kingama fita waje ballema ki hadu da makiyana su hure miki kunne, let's go my princess" cikin kuka sosai Mum tarike dayan hanunta tace "Alhaji dan girman Allah ka kyale yarinyar nan" wani irin tunkude Mum Abba yayi har saida Mum tafadi ta buge gefen cikinta da gado tai kara hakan yasa Ahmad yawani irin ture Abba yakusa faduwa amma bai saki hanun princes ba, cikin fushi yace "Abba wai are you mad? Wat is wrong with you please maisa kake kara zubar da girmanka a idonmu ne, look at Muhsin he's unconscious don't you have any respect for your children Abba?" wani irin kallonshi Abba yayi yana kara damke hanun Nadeera da kyau yace "Ahmad ni, ni, ni ubanka ka tura Ahmad nakusa faduwa?" yay maganan yana wani irin kallonshi irin look dinan da parent ke bama yaransu suji hankalin su yatashi, murmushi irin me ciwon nan Abba yayi yace "nika tunkude ni mahaifin ka Ahmad? Hmmm, Kaje zaka gani Allah ya tsine ma Albarka Ahmad! gaka ga uwarka kunfi sonta ai, shikenan nima bana bukatarku, bazama ku kara ganina a gidan naku ba, munbar muku kenan, lets go princess" yawani irin ja hanun Nadeera da duka karfin da Allah yamai tana ihu ana kallon su yafita da ita daga asibitin ya bude jeep dinshi baya ya jefata ya rufe ya shiga gaba yatada, da sauri Mum ta tashi ta kalli Ahmad daya dawo kaman gawa a tsaye tace "Ahmad let's follow them karya ma yarinyar nan wani abu baya hayyacinshi don't mind tsinuwarshi bazai kamakaba" hanunshi taja hakan yasa yafara tafiya kaman wanda baida jini suka fita daga asibitin amma har Abba yabar premises din, mota suka shiga Ahmad ya zauna yama kasa driving kaman tababbe tsinuwan Abba kawai ke dawomai, ganin haka yasa Mum tafito tadawo inda yake hanunshi taja tafito dashi ta kalli yanda idanunshi suka cika da kwalla sosai sunyi jajir taji kaman ta kurma ihu dan tashin hankali, ahankali tace "don't worry go and stay with your brother bari nabisu" shiga tayi ta tada motan tabar asibitin.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull