Boyayyen mutun complete - Chapter 30
Boyayyen mutun complete Chapter 30: Boyayyen mutun complete Chapter 30. *** Dan shiru tayi tai dan murmushi kadan ta dauke kai batare datace komiba tadan…
3,225 words
*** Dan shiru tayi tai dan murmushi kadan ta dauke kai batare datace komiba tadan matsa gefe sabida yanda suke kusa kusa da Marwan daketa daddanna system abinshi kamshin shi na fizganta, dan dago kai tayi karaf suka hada ido da Abdallah daketa kallonta hoping zatace wani abu again, dan hararan shi tayi tana wasa da yatsun ta tana turo baki tana kukkuni kasa kasa tace "ni banason ana kallona fa" "lalalala" Abdallah yafada yana saukar da kafanshi kasa, da sauri ta kallai murmushi yay escaping bakinta, ta wutsiyar ido Marwan keta kallonta, Abdallah ya kalli Ya Marwan yace "Ya Marwan wlh kama amaryan ka magana ba kaga tanamin kukkuni ba" murmushi sosai tayi, hakanan batasan mesa she always find the guy funny ba, kamanYa Ahmad haka yake mata, ahankali Marwan ya janye system din yana wani irin kallon ta kaman yahadiyeta yakasa magana, turo baki Abdallah yayi kaman zaiyi kuka yace "Ya Marwan bakace komiba kagama dariya takemini" murmushi tayi sosai harda daura hanunta akan fuskarta, daidai lokacin aka bude kofa Omari ya shigo dakin dauke da sallama shima idanunshi akan kanwar tasu da sauri Abdallah ya kalleshi kaman zaiyi kuka yace "Ya Omari kaga amaryan Ya Marwan na tsokanana ko, wlh this nurse ko she's so tsokanacious" fashewa tai da dariya hartana bige kafan ya Marwan, dukansu tsayawa sukayi suna kallonta barin ma Ya Marwan dake gefenta dayakeji kaman ya tsaga jinin shi ya sata ciki, Ahankali Omari daya kasa dena kallonta ya shigo dakin ya zauna gefen Abdallah gani yayi dariyanta kaman na Momma su, da kyar tai shiru tana murmushin data dade batai irinshi ba dimples dinta nawani irin lotsawa, dukan cinyan Omari Abdallah yayi yace "ehen nurse zokiga Ya Omari yaji ciwo a hannu dama dazu yabige da table ko Ya Omari?" kallon Abdallah Omari yayi, Abdallah ya kannemai ido hakan yasa Omari ya kalleta suka hada ido yace "y..y..uhm" da sauri Abdallah ya fizge hanunshi yaja hanun riganshi sama yace "zoki gani nurse" make kafada tayi ahankali tana leken hanun nashi daga inda take zaune tace "aini banga ciwo a hanunba, in bigewa ne jamai kawai za'ayi zai dena zafi, kajamai" da sauri Abdallah ya kwalalo ido yace "ni? Wai bakiga katon hanun Ya Omari bane kaman na Ya Marwan" murmushi yayi ya kalli hanun ya Marwan din dayay kaman baya jinsu nanko kunenshi nakan duk abinda suke cewa, juyowa yayi ya kalli Nadeera itama shitake kallo ya nuna mata hanun Ya Marwan yana cemata look yana nuna mata manyan muscles dinshi Yana nuna mata ta kalla, makemai kafada tayi taki kallo, turo mata baki Abdallah yayi hakan yasa kaman daga sama tace "wlh kacika shagwaba" hararanta yayi shima harsaida tai murmushi yace "nakai ki?" da sauri tace "ni? Ni ai banda shagwaba" tabe baki yayi yace "wai talle kema audi gori" kama baki tayi tace "wai a ina kaji hausa? You don't look like a hausa man" murmushi yayi yace "kema u don't look like a hausa girl shagwababbiya kawai" makemai kafada tayi ta kalli Omari daketa kallon su kaman yasami film yanajin son kanin nashi aranshi tace "dan Allah waini shagwababbiya ce?" girgiza mata kai yayi ya tallabe keyan Abdallah yace "don't mind him lil sis keba shagwababbiya bace" dan murmushi tayi tana komawa jikin kujera dudda she found yanda yakirata da lil sis a little bit weird amma saita basar tajingina da kujeran tareda lumshe ido kaman mai shirin yin bacci, wani irin faduwa gabanta yayi harsaida taidan ihu tareda bude ido a firgice tana numfashi da sauri da sauri, kallo dukansu suka bita dashi, ahankali Marwan dake gefenta yataso ya matso kusa da ita yana kallon fuskarta murya chan kasa yace "menene?" baki ta tabe tana wani irin nishi tana kallonshi tana shirin yimai kuka, girgiza mata kai yayi tareda daura yatsan shi akan lips dinta yana wani irin kallon ta murya chan kasa danko su Abdallah bazasu iyajin abinda yace ba yace "don't cry for me, menene?" yay maganan yana janye yatsan daga kan lips dinta yamata wani irin kallon ban amsa, ahankali hawaye nacika idanunta ta dafa zuciyarta tace "My heart" ahankali ya kalli kirjin nata kaman mai nazarin abu kafin ya mika hanunshi ya janye nata ya daura nashi akai koshi yaji yanda yake bugu fast fast, fashemai tayi da kuka sosai tace "please kiramin Mum, zanyi magana da ita something is wrong" tafara wani irin nishi bakinta ya bushe sosai, dan juyo da kai yayi ya kalli Abdallah dake kallonsu yace "get me water Abdallah" dasauri Abdallah yatashi yana waigenta yaje kitchen ya dauko bottle water yadawo ya mikamai, budewa yayi ya kai bakinta da kyar ta sha tana fashemai da kuka tace "dan Allah Mummy na" yanda take kukan tana wani irin nishi yasa yajata jikinshi ya rungumeta yana buga bayanta hanunshi daya kuma yana kokarin ciro wayarshi dake bayan wando ya ciro yadawo dashi ta gaba ya bude wayan yay dailing number Mum.
Mum dake zaune cukin mota kuka take sosai ko mutum daya takasa kira saima kallon wayar nata da Abba yaciro daga purse dinta yasamata a hannu take, shidai Abba sai kiran mutane yake da limamai, ringing wayan Mum din tayi tabi wayar da kallo dudda tagane number Marwan ne amma takasa picking, sai uban kuka take akaro na uku sanan Abba yace "amsa mana Hajara hakuri zakiyi kinji" da kyar ta iya tai picking call din ta kara akunenta tana kuka sosai takasa magana, daga tachan bangaren saida gaban Marwan yafadi a yanda yaji Mum na kuka da sauri Nadeera dake jikinshi ta dago kai tafashe dawani kukan tana kallonshi, cikin kuka tace "Mummy na ta dauka?" jin maganan Nadeera yasa Mum ta katse wayar da sauri tarushe da kuka sosai, sakinta yay ahankali ya mike tsaye dan jikinshi yabashi wani abu matsawa yayi chan bangaren dining ya tsaya yay dailing number da kyar Mum ta iya picking call din ahankali Marwan yace "why are you crying Mum? Did dat man hurt you?" cikin wani irin murya raunanniya Mum tace "d'ana Muhsin dake kwance a asibiti ya rasu yanzun nan" sosai maganan ta dakai harsaida kirjinshi ya buga yadago kai ya kalli Nadeera dake zaune akan kujeran daya barta tana goge kwalla tana kallonshi jira kawai take taji mezaice, dan murmushi yamata danya kwabtar mata da hankali, kafin ya kalli wayar ahankali yace "may his soul rest in peace, and may Allah forgive his short comings" ahankali cikin kuka Mum tace "Ameen" tareda katse wayan, ahankali ya shigo falon yana kallon su Abdallah da sun riga sun karanci something is wrong daga fuskan shi, kafin ma yakaraso cikin dakin ta tashi da sauri ta karaso tana numfashi sama sama ta rike mai hannu tace "uhmm meya sami Mummy na? Metace? Wlh inaji ajikina something is wrong, please kafadamin gaskiya kaji please" ta karashe maganan tana fashemai da kuka, hanunta ya rike ahankali ya kakalo murmushi yace "come" stairs yay da ita tana kuka sosai ya shiga dakinsu da ita, fashewa tai da kuka sosai tana sake kallon fuskanshi tace "kafadamin dan Allah meya sami Mummy na" rungumeta yayi very tight tanamai kuka sosai kafin ahankali ya cirota daga jikinshi ya jata ya bude kofa suka suka tsaya agaban closet wani doguwan fine rigan abaya yaciro mata sai binshi da kallo take tafashe dawani irin kuka tace "ina zamu?" ahankali ya zage zip din bayan riganta batare daya bata amsaba yacire mata rigan tana kallon fuskanshi tana kuka, ajiye rigan yayi yana kallon fuskarta itama asanyaye, cikin kuka ta dafa hanunshi tace "ina zamu meya sami Mummy na?" yana zage zip din bayan skirt dinta yace "nothing, Mum is fine wife" jan skirt din yayi kasa tsabagen rudewa bama tadamu ba yabi santala santala cinyoyin ta da kallo, doguwan rigan ya dauka ya samata da hijabi. Cikin kuka sosai tace "I.. I want to change" gyada mata kai yayi ahankali yasaketa tadau pad dinta ta shiga bayi da gudu tana kuka, wayarshi ya ciro yatura ma su Omari text su shirya d'an Mum na hospital ya rasu yanzun nan, shiryawa yayi shima yasaka wani light blue yadi mai taushi dayamai bala'in kyau ya fesa turare yana jiran tafito, fitowa tayi tana hawaye sosai ta karaso gabanshi tace "am ready" takalmin ta ya nuna mata ta zura flat shoe jikinta na rawa yarike hanunta suka fito daga dakin, akasa suka samu Omari da Abdallah sunci manyan kaya suma sunyi kyau kaman zasuje gasan kyau sai kallonta suke duk suka fice suka shiga babban jeep din Marwan, Omari na mazaunin driver Abdallah na gefe sai shi da ita abaya suka rufo sanan Omari yatada motar yaja suka fita daga gidan, ahankali ya kwanto da ita jikinshi, dago kai tayi ta kalleshi bakinta na rawa sosai cikin kuka tace "are you sure my Mummy is fine?" gyada mata kai yayi tareda lumshe mata ido yana sake kwanto da ita tai lamo ajikinshi tana sauke ajiyan zuciya.
Akofar gida da already mutane sun cika Abba yasa mai taxi yay parking, fitowa yayi yabiya kudi ya zagayo ta bangaren Mum yabude mata ya riko hanunta tafito daga motan da kyar mutane suka karaso wajen yan anguwa anata musu gaisuwa ana tambayan karfe nawane jana'izar dan ga magrib ta kusa yau za'a kaishi ko sai gobe?" Eh yace musu yace "da isha'i za'ai jana'izar" yamusu godiya yaja hanun Mum dake binshi luu suka shiga cikin gidan, kawayen ta tagani yan kwararu agaban barander su, da sauri Maman fauzy da Abba ya kira ma Mum ta tashi tafito ta rungume Mum tana lallashin Mum data fashe dawani irin kuka Abba kuma yawuce shashin su Muhsin, Mum Fauzy tace "ki daure, ki daure Hajiya, nasan abin da ciwo, I know how painful it's to lose a Son, ki daure kinji, kici wanan jarabawan, ubangiji Allah yafimu son Muhsin, yaro mai kirki, shiru shiru, mara hayaniya, baida magana ga kunya, ga kyauta ga yawan sadaka da kyautatama mabukata, me kuma kike nema? Share hawayen ki" tashare ma Mum hawaye, ahankali Mum tace "ina Muhsin ina Ahmad?" shashin su Muhsin ta nuna mata tace "chan aka tafi dashi anje yanko likafani sai amai wanka" gyadamata kai Mum tayi tace "kaini wajen bana gani sosai" gyadama Mum kai Maman fauzy tayi taja hanun Mum ta kaita shashin su Muhsin ta tura kofan suka shiga da sallama ta kurama gawan Muhsin ido ga Ahmad zaune agefe idanun nan sunyi jajir yana kallon gawan shima, sai Abba dake gefen Ahmad kadan shima yana kallon gawan, ahankali Mum tawani irin zube agaban Muhsin tana wani irin kuka tahade hannayenta biyu alamun roko tana kuka tama kasa fadin abinda takeso tace, tai nadama tai nadama tai nadama biyema Abba, maima yasameta? Ya akayi tabari shaidan yaci galaba akanta? Itace ke dambe da namiji? Meya sameta? sosai Ahmad yaji tawani irin bashi tausayi dan yanda take kuka tana nishi saika zata suma zatayi, ahankali ya mike tsaye yaje inda take ya dagata murya chan kasa yace "Mummy is okay, kidena kuka haka is not good for your health, addu'a zakimai" rungume Ahmad tayi tana kuka shima hawaye ya goge da sauri batare daya rabata da jikinshi ba yajata yakoma chan gefe ya zaunar da ita man dogon kujeran falon su ya dago ta ya cirota daga jikinshi, hannunshi yasa ya goge mata hawayen datake yi dasuka kasa dena zuba, Abba da jikinshi yay sanyi sosai sai wani irin kallonsu yake, murya chan kasa Ahmad yace "Mum kinfada ma Nadeera? Yakamata ta sani, yakamata tazo taga Yayanta tamai addu'a kafin akaishi, kin kirata? Because I know kinada masaniyar inda take? Yanzu rasuwa akayi mu manta komi, kin kirata?" da kyar ta iya girgiza kai cikin kuka in a low tone tace "nafada ma mijinta Muhsin ya rasu" ahankali yasake kai hanunshi kan fuskarta yana goge mata hawayen yace "nace kidena kuka be strong, don't break my heart Mum" gyadamai kai tayi tana wani irin kuka, ahankali yamata kiss a goshi yace "is okay Mum" gyadamai kai tasake yi murya chan kasa yace "give me your phone ban number mijin nata lemme call him nace yakawota" gyadamai kai tasake yi tana kuka sosai ta ciro wayar tabude tabashi number, karba yayi yace "stay here am coming" fita yayi daga dakin yafita waje jiri na dibanshi daurewa kawai yake yakira wayar ringing daya Marwan dake mota rungume da Nadeera dayasamu bacci ya fizgeta yay picking ganin number Mum, ahankali Ahmad yace "this is Ahmad yayan Nadeera I hope ina magana da mijin tane?" ahankali Marwan yace "yea" Ahmad da muryanshi tadan fara rawa yace "please i have a request Yayan mu Muhsin yarasu, dan Allah ka kawo Nadeera let her bid farewell to Ya Muhsin please" shiru Marwan yayi hakanan yaji yana relating to the guy's pain yasan ciwon mutuwan your love one, yasan zafin da dacin abin, baka taba gane ya mutuwa take sai wani naka ya mutu, dan ajiyan zuciya yayi yace "we are on our way mun kusa isowa ma" da sauri Ahmad yace "thank you" yay maza ya share hawayen daya zubomai jiyake kaman ya kurma ihu but he's sure ya Muhsin bazai so hakaba, he has to be strong for him, share fuskanshi yayi daidai lokacin Bello ya shigo gidan dasu likafani da sauran su aleda karba yayi suka koma shashin nasu tare.
Parking sukayi ata gefen anguwan sabida mutane da maza dasuka cikashi fam, ana parking tabude ido rass tafashe da sabon kuka tana kallon anguwan nasu, kashe motar Omari yayi suka bude suka fito tana kallon mutane ta kalli Marwan tace "na shiga uku maiya faru?" shiru yayi ta kalli Omari da Abdallah dasuka fito daga motar tace "dan Allah kufadamin meya faru maiya sami Mummy na eh?" hanunta yarike suka fara tafiya suna sallama da mutane sai kallon su ake anga larabawa har zuwa gaban gate din gidan, yanayin yanda take yasa yabude kofan gate din suka shiga ciki tana kallon mazan dake compound din duk yan office din Ya Muhsin da Ahmad ne mata na bangaren Mum, gaban shashin su suka tsaya daidai lokacin fauzy tafito itama idanunta sunyi jajir rike da buta ahanunta zata bama baban su dake tsaye cikin wani irin kuka tace "ina Mummy na Fauzy?" kallonta fauzy tayi cike da mamaki kafin ahankali tai pointing shashin su Ya Muhsin, wani irin fizge hanunta tayi daga na Marwan taruga dawani irin gudu tana kuka tafada babban falon nasu ta tsaya chak tanabin kowa da kallo tana kuka, da Abba tafara hada ido daya kafeta da ido kaman yau yafara ganinta kafin ta kalli Mum daketa uban kuka kanta akasa sai Ya Ahmad zaune kusa da Mum da shima kallonta yake da idanunshi dasukai jajir kafin ta sauke idanunta akan gawan data gani akasa a lullube, bakinta har rawa yake kirjinta nawani irin bugawa, ta daura hanunta akan kirjinta dake wani irin gudu, miyan bakinta ya kafe, da kyar ta iya bude lebbanta dataji sun wani irin manne kaman ansa gum tace "Y..Ya..M..Ya..Muh...Muhsin?" baya tayi luuuu asume wani irin ihu Abba yayi yazabura yamike yace "My Princess!". [10/17, 6:01 PM] Aishat Muhammad: *karki karanta in baki biyaba, kisani idan kin karanta ina binki bashi*
*Zaki iya samin access to karanta labarin nan akan kudi naira Dari 300 kacal*
*3107021073 first bank aisha Muhammad* *07012181461 watsapp min tanan for any enquiry*
*BOYAYYEN MUTUN*
*A6*
Da kyar Abba ya mike tsaye yana dan dingishi yana nishin azaba sosai dan wani irin tafarfasa kwanyarshi takemai yana wani irin kallon hanun nashi yace "wayyo Allah na shiga uku ya kashe ni, Princess please ki dawo gareni" da kyar ya iya yafita daga dakin yana kwalama Adamu driver kira awahale. "Adamu, Adamu, wayyo Allah na Adamu zoka kaini asibiti hakika yau bakar rana ce agareni" arude Adamu yafito daga dakinsu yana salati ganin yanda hanun Abba yayi kafin yay magana ma Abba yace "kaini asibiti kai, kaini asibiti kafin narasa hannuna" jan kafadar Abba yayi yabude mota ya sakashi ya shiga gaba da gudu ya rufe yaja da sauri suka fita daga gidan, private asibitin daya bari dazu ya koma yana zuwa suka karbeshi da gudu.
Direct bedroom dinta Mum ta shiga tana share kwalla tabude wardrobe taciro manyan manyan akwatinan ta tana kwaso kayanta tana hadawa ciki tana hawaye sosai, wani irin bakin ciki takeji sama dana kullun, ahankali Muhsin yatura kofan dakin ya shigo Ahmad biye dashi duk suka tsaya suna kallon yanda Mum ke kuka tana hada kaya inka ganta saika tausaya mata kaman wacce take fama da wata cuta, ahankali Muhsin yataka yakaraso gaban wardrobe inda take yasa hannu ya karbi kayan dake hanunta ya ijiye akan gado kafin yabata wani irin hug yana bubbuga bayanta, fashewa tai da wani irin kuka da tuntuni takeso tayi irinshi takasa, sosai take kukan tana shesheka tace "am sorry Muhsin, am sorry, Muhsin kaya kuri okay" ahankali Ahmad ya shigo shima ya rungumeta tabaya suka sata atsakiya suka rungumeta tsamtsam, sosai take kuka tana rokon su gafara, tace "am sorry, kuyafemin, kuyafemin, komi daya faru ayau laifina ne, nice silan komi, ninaja komi, Abban ku batun yau yake nunamin bayason tafiye tafiye naba, nazauna a Nigeria nai business bazai hananiba amma bayison tafiye tafiye, nai kunen uwar shegu, nakiji, gani nake tunda ya yarda tun kafin muyi aure da business dina baida right akaina, baida right yacemin ga yanda zanyi game zanyi, gashinan yau naga illan hakan, na tarwatsa family na dakaina, nabata komi, yakuma sakeni, am sorry Muhsin and Ahmad kuyafemin dan Allah, is all my fault, am the root to all that's happening, kunsha kirana bana dauka, baban ku ma haka ya kira ya kira bazan sami time din dauka ba, princess ma haka, wlh duk laifina ne, ninaja komi, kuyafemin dan Allah" tahade hannayenta biyu tana wani irin kuka mai taba rai, ahankali Muhsin ya saketa ya sanya hannu ya saukar da hanunta kasa yasa hannu ya goge mata fuskan da hawaye yagama wankewa yace "is okay Mum, stop crying, sit" ya zaunar da ita abakin gado ahankali ya kalli Ahmad dake tsaye yana kallon Mum cikin tausayawa yace "jeka mana parking kayanmu Ahmad, lemme park Mum's own" gyadamai kai Ahmad yayi yajuya yafita daga dakin shikuma yacigaba da kwashe na Mum kayan yana zubawa a box, daurewa kawai yake daga Mum har Ahmad need him, so he has to be strong for them, Nadeera is not his and yay accepting dis faith, yariga yaga yanda guy din yake sonta, so koma wanene shi he don't care, Alhamdulillah tunda tasamu wanda ke sonta haka, Allah ubangiji yacire min sonta araina yabani wata tagari and make me strong enough nasamu na kula da mahaifiyata da kanina, tass yahada ma Mum kayanta ya zage jakan yana dagasu tsaye yaja ya fitar dasu waje ya ijiye gaban motan shi sanan yadawo ciki yafito da Mum dake tafiya ahankali yabude bayan mota yasata yarufe daidai lokacin Ahmad yafito daga shashin su yana gunguro akwatinan su, a boot duka yahada yasa sanan yabama Ahmad key dan bazai iya driving ba ya shiga baya ya zauna kusa da Mum dahar lokacin ke kuka yana sharemata hawaye suka fita daga gidan, saida suka tsaya a hanya sukai magrib da isha'i kafin suje wani babban hotel suyi lodging, yabiya musu kudin komi suka kai Mum dakinta suka zauna a wurin dan suyi keeping dinta company sai wuraren 12 sanan suka fito suka tafi nasu dakin dan bacci dan gobe da safe sukeso subar garin.