Kenza eBookz

Boyayyen mutun complete - Chapter 31

Boyayyen mutun complete - Chapter 31

Boyayyen mutun complete Chapter 31: Boyayyen mutun complete Chapter 31. ** Dawani irin gudu Marwan ke tuki har kaman mahaukaci har saida ta kankame kanta…

3,807 words

** Dawani irin gudu Marwan ke tuki har kaman mahaukaci har saida ta kankame kanta cikin tsananin tsoro tana kuka sosai, tsayawa dataji anyi yasa tadago kai ahankali tasa hannu tana share kwalla dake zubo mata daga ido, wani irin kashe motan yayi yabude kofa yafita batare daya kallesu ba, fashewa tayi da kuka sosai tana goge kwallan da bayan hijabi, ahankali Omari da Abdallah suka bude kofa suka fito zagayo wa ta bangaren ta Abdallah yayi yabude side dinta ahankali ya mika mata hannu cike da tausayin ta dan yanda take kuka na mugun tabashi yace "come" gyadamai kai tayi cikin kuka kafin ta mikamai hanunta dake rawa sosai ya rike, da taimakon shi tafito daga motar dan kafafunta sun mata wani irin sanyi sosai, rufe kofan Abdallah yayi yana rike da ita Omari a gefenta sukai shashin nasu suka bude kofa babu kowa a falo sukai hanyar stairs tirjewa tayi Abdallah yajuyo ya kalleta yace "menene?" girgiza mai kai tayi cikin kuka sosai tace "am afraid of him, zai dakeni" takarasa fizge hanunta ta koma ahankali ta zauna cikin daya daga cikin kujerun falon tana goge kwallan dasuka kasa dena zuba da bakin hijabin ta, ahankali yake saukowa daga stairs fuskarshi da danshi ruwa alamun alwala yayo yana tattare hanun riganshi yana tafiya ko daya daga cikin su bai kalla ba yawuce yabude kofa yafita daga falon yay masallaci.

Omari ne yadawo inda take yace "let's go, bazai miki komiba, kinga yama tafi mosque" tashi tayi ahankali tabi bayansu tana waigen kofan suka kaita dakin ta zauna abakin gado ahankali, Abdallah ya kalleta yace "are you hungry? Meza kici" ahankali tace "I want yogurt zansha maganina" "alright yanzu zan kawo miki da abinci but stop crying okay" hannu tasa tana goge kwalla, ahankali Omari ya zauna kusa da ita yakama hanunta yarike batare dayace mata komiba yana kallon fuskarta, he just wanna hug his little sis, ya lallasheta, he want to shower her with love, ahankali yace "Rahma, my little sister" ahankali ta dago kai ta kalleshi hawaye sun cika idanunta shima haka hawaye suka cika idanunshi gam, ahankali yana kara matse hanunta yace "baki yarda, we are your brothers ba ko? ranan da Momma ta haifeki aranan ta rasu, we've went through hell in this life but munyi enduring sabida ke muke nema, don't worry bit by bit I will tell you everything, I will show you our file and your file kigani, but for now kidena kuka okay, we will always protect you, we really need you in our lives, I love you so much Rahma" wani irin fadawa jikinshi tayi tafashe da kuka sosai hakanan all maganganun dayake mata tana feeling dinsu har cikin ranta, and tunba yauba barin ma Abdallah dataji she feels so connected to the guy tun ranan dasuka fara haduwa a super market saisa ma bata manta da fuskan shi ba, dan idan normal person ne da tuni ta manta dashi, bude kofan Abdallah yayi ya shigo dauke da tray dake dauke da abinci chicken rice dakuma farm fresh yogurt da cup da spoon, ganin yanda ta rungume Omari tana kuka yana bubbuga bayanta shima hawaye na zuba daga idanunshi yasa yaji kukan shima yazo mai, da kyar ya ijiye tray a gefe ya zauna agefen su yanadan murmushi, ahankali Omari ya saketa ta juyo ta kalli Abdallah daya kafeta da idanu dasuka chanza kala, murmushi tayi hawaye na bulbulowa daga ido kafin tawani irin bashi emotional hug tace "Ya Abdallah" kankameshi tayi shima haka yana kuka yace "My shagwababbiya Sister" makemai kafada tayi tace "uhm uhm" cirota yayi daga jikinshi yanaji kaman ya cinye ta yamata kiss a forehead yakara rungumeta very tight da kyar ya iya sakinta shida Omari suka sata a tsakiya hakanan taji tamanta da duk wani bakin cikinta, wani irin farin ciki da batasan daga ina yakeba taji yawani irin lallubeta, duk sukai shiru sun tasata agaba sunata kallonta, Omari ne yay breaking silence din yace "zokici abincin ki, muje muyi salla Abdallah" kaman zaiyi kuka Abdallah yatashi suka fita daga dakin yana mata bye itama haka tanata kallon su kafin taja tray din chicken rice dayakawo mata da yogurt da spoon, hada maganin da Mum takawo mata tunda dama safe da dare ne tasha da kyar sanan taci abincin da sauri sabida yanda yabata mata baki taci kusan rabin abincin sanan taji ya isheta tasha tsimin da acewanta shiyafi dadi tasha sosai sanan ta maida tray kasa ta jingina da gado tareda lumshe ido tai shiru tana tunanin komi da kowa na rayuwata, barin ma Abba da agabanta Marwan ya ballamai hannu, wasu hawaye masu zafi ta share. Takusan bata one hour ahaka sanan ta tashi da kyar ta shiga bayi tayo wanka da brush ta shirya ta saka wani cotton rigan bacci white iya guwiwa tafito ta zauna akan gado tai tagumi tana kallon kofa ita kanta batasan metake jira ba takai kusan 30min tana kallon kofan kafin bacci yay nasaran awon gaba da ita.

** Abba kam hanunshi a machine din hoto aka fara sawa kafin aciro amai dauri, bakaramin wuya yasha ba, ihu babu kalan wanda baiyiba, kai karaya da zafi, take wani mugun zazzabi ya turke shi akai admitting dinshi aka samai ruwa, da kyar bacci yay awon gaba dashi yana kiran sunan Princess ahankali ahankali yana nishi kaman zai mutu yay baccin.

** 5:30 na safe tama su Mum da Muhsin da Ahmad a airport, basu wani bata lokaci ba suka biya wani extra kudi akan kudin tickets din flight dinsu dasukai missing na jiya aka basu New tickets, karfe bakwai jirgin su ya daga sukai bye bye da Nigeria.

*** Knocking mata kofa da akayi yasa tabude ido ahankali taga rana tayi gari yay haske sosai, ga kanta dataji yana mata wani irin ciwo, daga tachan waje Abdallah ya daga murya yace "hope kin tashi babysis? Good morning, oya stand up and get ready we are going to New house, yeeee excited right?" yay wani irin kara, murmushi tayi ahankali ta sauko daga kan gadon tana kallon dakin ganin ko alamunshi bata ganiba, tashi tayi ta shiga bayi tai brush tayo wanka tsaf tafito ta shirya cikin wani skinny Jean dayabi shape din jikinta sosai black, dawani yellow t-shirt daya kamata shima, wani black kimono ta dauko cikin kayan da Mum ta kawo mata ta daura akai ta yane kanta da gyalen kimonon kafin ta fesa turarenta da Mum ta kawo mata twilly, dudda babu makeup a fuskarta but tai wani irin inviting kyau ta zira flat shoe dinta tafito.

Kaman wata matsoraciya tabude kofan dakin tafito kirjinta na faduwa daidai lokacin shima ya bude kofan dakin Omari yafito yana sanye da white shirt daya kamashi da fadadden kirjinshi yafito sosai sai dogon Jean sai baki, yasaka wani black Prada sandal daya kara haska farin kafarshi yay kyau ciki, sai kamshi yake kallo daya yamata ya dauke kai yacigaba da tafiya abinshi yay kasa, wani irin mummuna faduwa gabanta yayi takasa koda motsin kirki balle tai tafiya, Omari ne yafito daga dakin nasu yana gunguro wani babban hadadden akwati yana ganinta ya sakin mata murmushi, murmushi itama ta sakin mai tace "ina kwana" hanunta ya kama yarike yace "how was your night Kinga yanda kikai kyau kuwa, muje Ahmad zaizo ya dauko jakan ki" gyadamai kai kawai tayi tabishi suka sauka gabanta na faduwa har zuwa compound din, tsaye tahango shi dawani tsoho baban Kamal yana magana yana dan murmushi wurin motan Omari ya kaita ya bude baya ya sata kafin yabude boot yasaka jakan shi aciki yakoma cikin gida, yakai kusan 2min yana magana da baban kamal sanan ya juyo ya dawo motan yanadan Satan kallonta yanda kanta ke kasa tana wasa da yatsun ta, bude gaban motan yayi ya zauna a mazaunin driver, ahankali ta dago kai tadan saci kallonshi miyan bakinta nawani irin bushewa da kyar ta daddage kaman zatai kuka tace "good morning" ko alamun amsawa baiyiba balle tasaran zai amsa, sake mayarda da kanta kasa tayi daidai lokacin kuma Omari da Abdallah suka karaso wajen jakunkunan su da nata suka zuba a boot din suka rufe sanan suka bude motan Abdallah ya bude baya ya shiga yana daura mata file din adoption dinta a cinya na wurin Mum yana rufo kofa shikuma Omari ya shiga gaba ya rufo kofan. Kunna motan yayi suka fita daga gidan Abdallah yace "shagwabatu open it and see" gyadamai kai tayi duk jinta wani irin take takeji, tabude ahankali tafara karantawa na wurin, hoton ta natun tana jaririya tafara cin karo dashi dan Mum ta nuna mata hoton dama saikuma sunan ta data gani baby R, saikuma motherless home din da akai adopting dinta dagashi a Egypt, sanan saiga hoton su Mum da Abba da Muhsin ranan da akai adopting dinta, hawaye ta goge da sauri ashe da gaske ne! Dama ita ba yar su Mum bace, mikama Abdallah file din tayi yamiko mata dayan yace "ga namu" karba tayi tabude shima tabishi tana karantawa yara hudu Marwan, Omari Abdallah dakuma jaririya Rahma da hotunan su duka ke kai da date din ranan da suka zo, fashewa tayi da kuka tawani irin ture file din tafada jikin Abdallah, bubbuga mata baya yayi yace "is okay, komi yariga yawuce okay" gyadamai kai tayi tana hawaye ahaka suka karaso gidan wani anguwan ne babban gaske awani estate, saida security ma suka duba boot dinsu sanan aka bari suka shiga estate din, hadadden estate very quite kaman ba mutane ciki, agaban wani babban gida yadan tsaya yadau wani remote ya danna gate din yabudu suka shiga bakaramin haduwa gidan yayi ba, gidan bangare biyu ne manya manyan gaske kuma da dan tazara tsakanin su ga flowers a compound din sosai masu colors sunyi sharshar dasu, parking yayi Abdallah yabude yafita ya zagayo ta side dinta yabude mata tafito ahankali, boot yabude mata ya janyo baban jakanta yace "muje kinji na kaiki dakin ki shagwabatu" murguda mai baki tayi tana share idanunta tabishi suka fara tafiya kafin ahankali tadan waigo ta kalli gaban motan wajen mazaunin driver hada ido sukayi da sauri ta dauke kai tacigaba da bin Abdallah kafafunta na hardewa suka shiga shashin dayake nata, hadadden duplex ne gidan kaman gidan turai, anyi fenti off white saikuma cottons din blue kujerun ma haka gawani babban TV na bango sai kallon komi take dan gani take nan yamafi dayan gidan dajin kyau sau dari, sukai sama wani daki ya bude mata yaja jakanta cikin dakin da yay wani irin fitinannen kyau gawani makeken gado aciki, Abdallah ya juyo ya kalleta yace "sit and relax, incase you need anything akwai kitchen akasa, zamuje muyi takeaway sai muyi breakfast kinji" gyadamai kai tayi yace "idan nadawo zanzo na dauke ki muje shashin mu because dole zamu cike time dinan da mukayi bamu tare, I will tell you about everything that happen to us" gyadamai kai tayi tana murmushi, murmushi ya mata yana mika mata wayarshi kirar iPhone daya ciro daga aljihu yace "gashi play with it kafin mudawo, banda kiran kowa, u know I trust you ko" gyadamai kai tayi tana kallon wayan, kumatun ta yaja yace "tell me okay jor" ahankali tace "okay" murmushi yamata yace "good gurl bye" bye ta mishi yajuya yafice daga dakin da dan gudu sanin Ya Marwan na jiran shi. [10/17, 6:01 PM] Aishat Muhammad: *masu posting novel waje, kuda Allah* *karki karanta in baki biyaba* *in kinason littafin nan Zaki tura 300 3107021073 first bank aisha Muhammad, saikimin magana a watsapp 07012181461*

*BOYAYYEN MUTUN*

*A5*

Wani irin bubbuga kafa Marwan yafara akasa kirjinshi na tafarfasa, yanamai suya kaman an hura wuta aciki, cikin fushi Abba yace "au bazaka kuyi magana ba ko, nace Marwan yamike tsaye mu bama hammata iska" cikin fushi Mum da batai niyyan magana ba tace "Alhaji!" afusace Abba yawani irin juyo ya kalleta yana nunata da hannu, yace "karki sake ki kira sunana makirar mata, annamimiya, wato kinyi iyakan bakin kokarin ki ki rabani da Princess kicire sonta a raina, amma kikaga sonta kainuwa ne araina dashin Allah, kikaga son princess zanen dutse ne araina, shine zaki sirfafo wanan karyan ki narka, kika bullo ta wanan hanyan kicemin wayanan yan daban yayyin princess dina ne? Yan uwanta ne bla bla bla, to sannu makira, kinji ko nace sannu makirar, mai bakin hali me princess ta tsare miki dakike kishi da ita? To bari kiji Allah ubangiji daya dauramin son Princess araina shi kadai ne zai ciremin shi daga raina, kuma wlh yau koma uban waye Marwan cikin su saiya sakin mini y'a, saiya saki baby girl dita, bazan kiwanci yarinya kimanin shekara ashirin da biyu babu wata uku ba, tai lumu lumu haka da ita, yarinya yar duddurma pakutu kaman kataba jini yafito wani yazo ya auremin ba, ai abunda bazata sabu bane wai taba nonon sirika, ya mori kiwona, kiwon danayi? Ina! " wani irin tashi Omari yayi cikin fushi ya kalli Abdallah yace "Abdallah get the check book from d car" ya kalli Abba dayawani gyara tsayuwa yana tale kafa yace "name your price Malam nawa ka kashe arainon kanwata? 100 million? 200 million? 500 million? How much just name it?" wani irin tashi Marwan da idanunshi sunyi jajir, jijiyoyin kanshi sunfito yayi ya kalli Abba yace "zan baka 50billion naira for rainonta, inma yafi haka name your price zan biyaka instantly" cikin fushi Abdallah ma yamike yarike hanun Ya Marwan dan yaga yanda hanunshi ke rawa and inhar yarike Abba zai iya kasheshi cikin fushi yace "Ya Marwan please mutafi, wlh baza'aba tsohon nan kosisi ba" wani irin ihu Abba yayi yawani irin kaima Marwan naushi a kirji amma ko gezau, yace "dama kaine Marwan? Dama kaine matsiyacin dibabbe wanda aka haifeshi babu cibiya shaidani, zo dan uwatata mubama hammata iska" wani irin jumping Ahmad yayi daga kan kujera yay wani irin ihu. "tirrrrrrr, yauwa Marwan dan Allah give him d beating of his life, karkai sparing tsohon nan, go Marwan" wani irin tunzura Abba maganan Ahmad yayi yay wani irin tsalle yadane jikin Marwan da zuciyarshi kewani irin zafi tsabagen fushi kanshi har wani irin rawa rawa yake, Abba yawani irin gannamai cizo a kirji yana nushin shi a ko'ina kafin ya dira kasa kuma yana nishi, fashewa da kuka sosai Nadeera tayi ta kalli Ya Muhsin da idanunshi kekan Abba da a yanzu jiya ke kaman yatashi ya kasheshi dan bakin ciki da tsanan halinshi, cikin kuka taja hanun Ya Muhsin tace "Ya Muhsin Abba yana dukanshi" ahankali Ya Muhsin ya kalleta yama kasa magana baida karfi ko kadan, da rarrafe taje wajen Mum tarike hanun Mum tace "Mum say something, Abba is beating him" kallon kwayar idonta Mum tayi tai shiru danhar cikin ranta sotake su uku suma Abba shegen duka dako tashi bazai iyayi ba, karan saukan Mari yasa da sauri suka daga kai, Abba ne ya kwashe Marwan dawani irin shegiyan mari, kawad dakai gefe Marwan yayi jikinshi nawani irin rawa ahankali yafara wani irin dunkule hannu da sauri Omari ya rike hanun koba komi darajan yayan shi da suma basa murna dahalin baban nasu, da kuma Mum dake son Nadeera tsakani ga Allah bai kamata ya daki Abba agabansu ba, wani irin shako kwalanshi Abba yayi cikin fushi yana jijjiga shi yana nishi yace "nace ka sakin min Y'ata, ka saketa, fight me now, tsoro na kakeji, fight me back Marwan, look me in d eyes, ka kasa kallona, ka kalleni muhada ido and fight me back like a Man, mu dambata, princess tasan wayafi chanchanta da ita, ka sakenmin yarinya ta inkana neman zaman lafiya" yakara marinshi tawani side din, da sauri Nadeera ta saki hannun Mum tazo wajen da gudu tana kuka, juyowa Abba yayi ya kalleta ya washe mata baki yana nishi kaman wanda yaje yaki yace "matsa baya my princess karna sameki garin dukanshi, kije ki zauna basai kin shigan min ba, I can take them down wlh, bakiga yanda natsuwa yasoma shigan shi ba, stop crying my baby girl, bazai iya dukan Abban kiba, he's to small for me, don't be scared okay" wani irin gyara tsayuwa yayi yana ware kafa ya daddage ya hambari Marwan akafa saida kafan Abba yay kara yay baya kaman zai fadi yay kara tareda yin baya da sauri ya kalli fuskan Nadeera dake kuka sosai ya daddage ya tsaya yana nishi sosai yace "am fine, am fine princess, stop crying, zan bashi kashine yau" yakara komawa yanadan dingishi dan kafan dayay hambari dashi tamai tsami, chakumo wuyan Marwan din da idanunshi ke kasa har lokacin yawani irin yi ya jijjiga shi yace "nace ka sakenmin my princess, ka saketa nace, bata saki" ya kaimai mari, fashewa da kuka Nadeera tayi tazo wajen da gudu tana kuka sosai tana wani irin yarfe hannu, tasa hannu ta janye hanun Abba daga kwalan Ya Marwan da idanunshi ke kasa har lokacin tace "stop beating him Abba, Abba mesa kake haka, ni I don't like you, bazan taba auren ka ba, koma abinda sukace gaskiya ne koma ba gaskiya bane u will always be my Abba, and ni babu aure tsakanina da Abba na, kaine wanda nasani amatsayin uba and u will always be dat, Abba please stop all dis, wlh bazan taba auren kaba, koka raba auren mu bazan taba auren kaba, tayaya ma zan auri babana? I don't like you Abba, I don't like you, I don't like yo... " wani irin wawan Mari Abba ya dauketa dashi yana huci, da sauri Marwan yadago jajayen idanunshi ya kalli Abban dawani irin idanu masu firgita mutum, da sauri Ya Muhsin da baida karfi ko daya yaji wani irin karfi yazomai ya mike tsaye yana dan dingishi yazo wajen ya tsaya a gefen Nadeera Marwan na dayan gefenta suna ma Abba wani irin kallon, wani kallo Abba yabisu dashi kirjinshi namai zafi kaman zai tarwatse kafin ya maida idanunshi kan Nadeera data fashe da kuka hanunta akan inda yamara ya nunata da yatsa yana dafa kirjinshi sabida yanda maganganun ta yamai wani irin shegen ciwo yace "P...Pr..Princess ni kika gayama magana haka? Ni Abban ki? Ni kike cema baki sona? Princess ni? Wat is my fault in loving you? Kinsan tun yaushe nake sonki? Princess ni" hawaye ya zubo daga idanunshi tsabagen yanda abin kemai ciwo, da sauri Nadeera ta ware ido gabanta na faduwa ganin Abba na kuka akanta, ahankali tace "Abbaa" hannu Abba yadaga mata yana girgiza mata yace "karki ce min komi, baniso naji komi, baniso naji me zakice, princess I fought the whole World for you, I stood by you through thick and thin, am always there to keep you company lokacin da maman ki ke abandoning naki tayi tafiyar ta kasashe, Princess I adopting you wen u were 3months old, u were this small" yanuna dan karamin yatsanshi yana share hawayen dayake yi, yace "I took you to the hospital aka miki check up, nakawo ki gidana nahadaki da family na, namiki suna, every sort of baby toy dat u could think of aduniyan nan nasai miki shi dakudina dakina yarinya, nasaki a one of the best schools da Nigeria keji dashi, I clothed you, hired one of the best nani, na kaiki Montessori kika fara tun daga creche har zuwa primary school, where turawa oyinbo ke koyar dake, kikai girma you told me bakison BSc Nursing normal school of nursing kikeso I took you there, d best damuke dashi agarin nan, St. Edward school of nursing and midwifery, nasai miki laptop, nai fentin dakin ki to your dream color baby pink, Princess I've always given you wat you wanted kafin na tai coughing dinshi out, I've always been there for you my baby girl, I know nai couple of mistakes but am human Ain't I?" yasake goge kwalla yana jan majina yace "and human make mistake, I wanted to wait for you kigama school of nursing dinki nafada miki everything sai muyi auren mu mutafi spain, but rashin Mum dinki shiya kaini namiki nai pushing dina har nai abinda nayi but it was never my intention" yafashe da kuka sosai yana goge idanunshi da hanun rigan shaddan jikinshi, yace "takan ki an zubarmin da hakora, wanan mutumin hit me badly, he injured me, he kidnapped you from me ya auremin ki, walls din stomach dina as am talking to you right now is very very weak princess, but dudda haka bantaba giving up ba on u, I've suffered alot because of you amma ko kadan sonki bai ragu a..a..rai..na..ba" yafashe da kuka sosai da sauri Nadeera data fashe da kuka dan maganganun Abba sun mugun tabata ta matsa zata kama hanunshi cikin wani irin kuka da tausayi Marwan yawani irin fizgota yace "let's go" yajata dawani irin force yay hanyar fita daga dakin da ita, wani irin ihu Abba yayi cikin kuka yarike Marwan gamgam yana kuka yana kallon Nadeera dake kuka sosai tana kallon shi ya mika mata hannu yana kuka harda majina yace "Princess don't leave me, don't leave me dan Allah, zan wulakanta, zan tozarta, My Princess karki bari yaraba ki da Abban ki, wayyo Allah princess kinaso Abban ki yamutu?" wani irin runtse ido Marwan yayi dan Abba yafara kaishi karshe zai kasheshi faa, ihu Ahmad yayi ya rike hanun Ya Muhsin da hawaye ya gangaro mai yace "na rantse da Allah Abba ya haukace, ko kaffara bazan yiba, kalli Abba fa yanda ya makalkale Marwan kaman dan biri alalo alalo, wlh Abba deserve to be examine and admitted in the asylum kai! The old Man head don loose noti fa" Nadeera kuka Abba kuka ya makalkale Marwan gam gam, ahankali Marwan yamika ma Omari Nadeera da hannu yace "take her away" wani irin ihu Abba yayi yay wani irin jumping ya rungume Nadeera tsam tsam yace "Princess karki bari arabani dake I will just die, I will die wlh, Princess dan kaunar dakike ma Manzo sallalahu alaihi wa sallama karki bari arabani dake, Nadeera! My baby girl, I need you, my princess, karki bari arabani dake" wani irin fizgo Abba Marwan yayi yawani irin bankare shi mercilessly kaman roba kafin yawani irin murde wutsiyar hanun Abba a zuciye jijiyoyin kanshi kaman zasu bullo tsabagen fushi jikake kakar kakar kasssas ya balle ma Abba wutsiyar hanunshi duka biyun Abba yay wani irin ihun azaba, wani irin ture Abba yayi yafada a tsakiyar dakin ya nuna shi da yatsa yace "never in your come close to my wife or touch my wife mugaffal" yawani irin ja hanun Nadeera dake kuka kaman zata mutu tana kallon yanda Abba ke kallon hanunshi da tana iya ganin yanda fatane kawai yarage tsakanin wutsiyar hanunshi da tsintsiyar hanun dan Marwan yakarya kashin tass, Abba nawani irin kuka yana kallon hanun yafita da ita daga gidan su Omari biye dashi yawani irin jefata cikin mota ya karbi key a hanun Omari suka shiga yawani irin ja motan da mugun gudu.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull