Kenza eBookz

Buzu book 1 complete - Chapter 16

Buzu book 1 complete - Chapter 16

Buzu book 1 complete Chapter 16: Buzu book 1 complete Chapter 16. Nana ta ce "Ka jahilci ma'anar aure idan haka ne, maganganu ka ba sa nuna komai sai…

4,449 words

Nana ta ce "Ka jahilci ma'anar aure idan haka ne, maganganu ka ba sa nuna komai sai zunzurutun wauta da rashin sanin ciwon kai"

Ya ce "Ba komai na ji na yadda" yayi maganar ba tare da jin zafin maganganun Nana ba.

Tsaki ta yi, ta juya za ta koma cikin gida, kafin baƙin ciki ya saka ta wanka masa mari, ko ta ci masa mutunci. Kawai ya riƙo hijjabinta yana "Haba Nanasko, haka za ki tafi babu sallama irin ta masoya, ko na lalata ki fa ni ne zan aure ki, ba kuma zan guje ki ba, rungume ki kawai nake so na yi, na ji ƙirjinki a jikina"

"To sannu tsinanne, sakar mini hijjabi, kafin na ci zarafin ka"

Ƙara matsawa ya yi yana ƙoƙarin haɗeta da bango, ta tattaro ƙarfinta, ta hankaɗa shi ƙasa, ta juya da saurin gaske ta shiga gida, cikin tsananin ɓacin rai da damuwa.

"Ke Nana har kin dawo? Ya tafi ne?"

"Eh" ta faɗa a taƙaice ta shiga ɗaki.

Ta cire hijjabinta ta riƙe a hannunta, zuciyarta na wani irin tafasa yanzu shikenan wannan shi zai zama mijinta, uban 'ya'yanta? Ta san duk bayanin da za ta yi wa Baba, ba zai yadda ba, ba ma zai fahimce ta ba, saboda idonsa ya rufe burinsa kawai ta yi aure ta yi gaba, mussaman yanzu da Mama ke ta yi masa barazanar zube masa yaransa ta tafi.

Muryar Baba ta ji a ƙofar ɗakin cikin faɗa ya ce "Ina magana kin yo gaba, bai ce miki komai ba game da shirye shiryen?"

"Baba bai ce mini ba, ni wallahi Baba ba na son sa, ko ƙaunar ganinsa ba na yi, bai cancanci a ba shi aure ko ya zama uban da zaka zaɓawa 'ya'yanka ba, dan Allah Baba a fasa auren nan" ta yi magana cikin magiya, hawaye na zirarowa daga idanunta. Tsaki kawai ya ja ba tare da ya ce mata uffan ba, ya yi gaba abin sa.

*****

Yanayin damuwar da Nana take ciki, bai hana ta yin murmushi da ta ga Haidar ba.

Shi ma murmushin ya yi, ya saukko daga kan kujera ya nufo ta.

"Ba ka ce ba"

Ya durƙusa a ƙasa, cikin gwarancin yara ya ce "Anty ina kwana" kamar yadda Nana ta koyar da shi.

Ta ce "Lafiya ƙalau, sai ɗayan"

"Good morning"

"Mornin my boy, how are you?"

"I am fine, thank you" ya faɗa yana tashi tsaye, haɗe da yin tsalle.

Ita dai tana son yara sosai da sosai, ko ma tana da rabon yin auren oho. Ta tambayi kanta ta bawa kanta amsa.

Ƙamshin turaren Hajiya ne ya karaɗe falon.

"Nana har kin zo?"

Cikin girmamawa Nana ta ce "Eh, ina kwana Hajiya"

"Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya ɗan naki?"

Nana ta kalli Haidat ta ce "Haidar, ka manta?"

Ya kalli Mummy, ya durƙusa ya ce "Mummy ina kwana, good morning"

Baki buɗe Hajiya take kallon Nana da Haidar. "Ikon Allah, Haidar ne da gaisuwa yau? Nana ke ki ka koya masa?" Ita dai murmushi kawai ta yi, idan ba a fara koya masa abubuwa yanzu ba sai yaushe?.

Bakinta ya kasa rufuwa, cikin matsanancin farin ciki, saboda duk son da suke yi wa yaron, azabar kukansa ya sanya suke ƙyale shi.

Shukura ta fito tsaf za ta tafi makaranta, Haidar yana kallonta, amma bai je gurinta ba.

Mummy ta ce "Shukura, Haidar fa iya gaisuwa, ka gaishe da mamin ka" Noƙe kafaɗa ya yi yaƙi ko kallonta.

Nana ta ce "To ɗaga ni, mun ɓata kuma yau ba zan karanta maka littafin ba"

Daga kwance ya ce "Mami ina kwana"

Ɗan kwaɓe baki ta yi, ta amsa ta fice.

Da yamma da Nana ta tafi, ganin da sauran lokaci, ya sanya ta hau abin hawa ta tafi gidan Ummi.

Ummi na ganinta ta ce "Alhamdilillah, da gidan zan tafi ai, na kira Baba na gaya masa, ya ce ba kya nan ki na gurin aiki"

Nana ta ce "Me ya faru?"

"Dama game da maganar shirye-shirye ne, kuma kwatsam jiya Saleh kwana ya yi da ciwon ciki a asibiti ya kwana, ɗazun nan na dawo na ce dama yakamata ki zo mu je mu duba shi"

A hankali Nana ta furta "Ƙaisar"

Ummi ta ce "Me ki ka ce?"

"A'a ba komai"

"A'a bari na kaɗa miya, mu je ki duba shi, yana jin jiki sosai wallahi, jiya wai har da dafara ya din ga fitarwa"

"Allah ya ba shi lafiya, amma ba zan je ba"

"Nana, ba za ki je ba kuma? Wanda za ki aura ɗin?"

"Wallahi Ummi ba na ƙaunar sa, na danne zuciyata ne na amince na aure shi, domin farantawa Baba, amma na ga alamar garin faranta masa, zan shigar da rayuwata da yarana cikin madauwamiyar nadama ne. Ummi ke kan ki kin san Saleh ba mutumin kirki ba ne na, kawai dan ku na son na yi auren nan ne"

Da fari Ummi ta hasala, amma sai ya danne ta ce "Nana, ana duba miki yanayin rayuwa ne. Ko ba mutumin kirki ba ne ba, idan ya shiryu sanadin ki, sai ki samu lada. Ba da ke muka karanta littafin ƙarfe a wuta ba a gidan nan, da Jauhar ta yi juriya ba ki ga yadda ta canza mijinta ba..

"A'a fa Ummi, littafi ba gaskiya ba ne, kuma shi Vipern ai ba ɗan iska bane ba, koma ba haka ba, kin san ina da juriyar da zan iya kamanta abin da Jauhar ta yi, amma wannan misalin da wancan da ki ke bayarwa gaba ɗaya ba iri ɗaya bane ba. Ina mamakin ace a aurawa namiji mace ta gari zai shiryu, lalatacciya kuma kowa gudunta yake yi. Ke ba ki san abin da ya yi mini ba, gaskiya ba zan iya auren sa ba wallahi"

"Nana, ki tsaya ki saurare ni.."

Banza Nana ta yi mata, ta ɗauki ledarta, ta fice daga gidan.

Washegari Nana ta koma gidan rainon yaronta. Ta riga ta saba, ko ba ta tarar da kowa a falon ba, ɗakinsa take tafiya, ko ta tafi kitchen gurin Jummai, ta taya ta aikin girki. Sai dai ta tarar Haidar baya ɗakinsa, ta dawo Falo sai ga Mummy.

Suka gaisa, ta ce "Nana ba ki ga ɗan naki ba ko? Yana gurin kakansa, yau sai da Haidar ya gaida kowa, har fatiha ya fara iyawa. Kin yi ƙoƙari sosai mun gode"

Nana ta ce "Bakomai"

"Babansa ma da aka yi waya da shi, yana ta murna, yanzu ma kakansa ya ce ki je, yana son ganinki. Amma kafin nan akwai 'yan kayana da na Shukura da muka yi kwalema, ki duba idan da wanda za su yi miki, wannan da ki ke sakawa duk sun mutu" Nana ta ce "To"

Mummy ta yi wa Nana jagora, har ɗakinta, ta ɗebo mata kayan fal, ga uban dogwayen riguna, kaya masu tsada, ba su yi komai ba wai ba a so.

"Idan ki na so, kafin ki tafi, duk ki ɗiba ki tafi da su, ki canza wannan na jikin ki, ki je ɗakin Haidar sai ki saka"

Nana ta karɓi doguwar rigar da Hajiya ta bata, ta tafi ɗakin Haidar.

Ita kanta ta yaba kyawun da ta yi a cikin kayan, ta daɗe tana burin sanya ire-iren waɗannan rigunan, amma Allah bai bata dama ba.

Ko da ta koma gurin Mummy, ta yi ta koɗa mata irin kyan da ta yi a cikin kayan.

"Ma sha Allah, Nana haka ki ke tubarkallah mai kyau, kin ga diri ma sha Allah. Mu je Alhaji yana ta murna yadda ki ke kula masa da jikansa".

Nana ji ta yi tamkar ta ce ba zata je ba, amma ba ta da wani zaɓi da ya wuce rufa wa Hajiya Amina baya, suka tafi sashin Alhaji Zailani.

Haidar na ta tsalle-tsallensa a falon, yana kaiwa yana komowa. A hankali ya ɗaga kai ya kalli hanyar da suke shigowa.

"Alhaji ga ta"

Sai dai ya ƙare wa Nana kallo sannan ya ce "Ma sha Allah, zuwan ki gidan nan kin zo da kyakyawan alkhairi fa, na ji daɗi sosai da sosai, yadda ki ke kula da jikana, na yi mamakin yadda yake yadda da mutane yanzu har ya iya gaishe ni" Nana ta sunkuyar da kai, tana wasa da yatsunta ko kallon Alhaji Zailani ba ta son yi. Ita dai ba ta taɓa ganinsa ba, amma ta rasa ya aka yi take yi masa kallon sani, ta tsane shi har haka.

Ya kalli Mummy ya ce "Amina, ina ga a ɗakin ki fa na bar glass ɗi na, ina ta son tura kuɗi, amma ba na gani sosai"

"Ok bari na ɗaukko maka" ta yi maganar tana tashi. Tana fita ya dawo da idanunsa kan Nana, yana ƙare mata kallo yadda zai samu riba biyu a tattare da ita. Ga kyakyawar ƙirar jikin da Allah ya yi mata ga kuma taurarin ta.

"Matso daga nan mana mu yi magana" yayi maganar yana nuna mata gefen ƙafarsa.

Ta ce "A'a nan ma ya isa"

Ya numfasa ya ce "Na ji daɗin irin kulawar da ki ke bawa Haidar. Amma nima ina da wata buƙata da nake neman agajin ki"

Cikin mamaki Nana ta ce "Ni kuma? Ƙwarai kuwa" ya yi maganar muryarsa na rawa.

Ayshercool 08081012143 Page 20

Dawowar Mummy ce, ta sanya shi yin shiru.

"Ba a ɗakina fa ka bar shi ba, na duba baya nan" cewar Hajiya Amina tare da ƙoƙarin zama a kusa da shi.

Ya ce "Too, ikon Allah ko ina na yar da shi Allah masani. Nana ko?" Ya ƙarasa maganar yana kallon Nana.

Ta jinjina masa kai. "Ɗauki yaron ki, ku tafi zan bayar da saƙo a kawo miki, mu na godiya sosai da sosai"

Nana ta miƙe, ta kamo hannun Haidar suka fita. Duk da rigar ta ɗan yi mata yawa, saboda ta Hajiya Amina ce, amma hakan bai hana bayyanar da yadda ƙugunta yake juyawa ba.

Bayan ta gama duk abin da za ta yi wa Haidar, ta tafi kitchen tana taya Jummai aiki, su na ɗan taɓa hira.

Sai dai ƙasan zuciyarta tana mamakin, me mutum kamar Alhaji Zailani yake nema a gurinta? Duk da zuciyarta tana ƙoƙarin kawo mata ko wata muguwar ɗabi'ar zai nuna mata, amma sai ta kawar da wannan tunanin.

Jummai ta ce "Nana dan Allah miƙa wa buzayen nan abinci, Shukura zan dafawa nata abincin, kafin ta dawo ta yi ta bala'i"

Nana ta ce "To"

Ta ɗauki ƙatuwar cooler abincin, tana tafe Haidar na biye da ita.

Habu ta tarar ta ba shi, ya karɓa tare da yin godiya. Maimakon su koma cikin gidan, sai ta ƙyale Haidar ya yi ta wasa yana tsalle-tsallensa, tana gefe tana kallonsa, tana jin daɗin ganin yadda yake wasa cikin nishaɗi. Muhsin ne ya faɗo mata, take ta nemi annurin fuskarta ya ɗauke. Jikinta ya yi sanyi, tana matuƙar son ta san halin da yake ciki. Tashi ta yi daga inda take, ta kama hannun Haidar, da nufin su koma cikin gida, amma ya ce shi ba zai koma ba, haɗe rai ta yi ta kalle shi, ba tare da ta ce masa komai ba, a take ya nutsu ya bita suka koma.

Bayan la'asar ta gama abin da take yi, ta ɗaukko kayan da Hajiya Amina ta bata, ta yi musu sallama ta fito.

Da fari shayi yake sha, yana zaune a kan benci, yana facing ɗin ƙofar falon, tana fitowa ya ja rawaninsa ya mayar, ya rufe fuskarsa.

A hankali take tafiya, tana ɗan rarraba ido, ko ƙifta idanunsa ba ya yi, har ta farga kallonta yake yi, suka yi ido huɗu da shi. Sai dai wannan karon ba ta ji faɗuwar gaba ba.

Ta yi saurin ɗauke nata idon, ta sake ɗaga ido, ta ga still ita yake kallo, ga shi shi, ba a ganin fuskarsa sai idanunsa kawai. Murguɗa masa baki ta yi, ta harare shi, amma tamkar maye ya ci gaba da kallonta. Sai kuma tsoro ya kama ta, ta haɗa da sauri, ta ƙarasa gate ɗin, ta fara ƙoƙarin buɗewa, amma ta gan shi a rufe. Tayi-tayi amma ta ga ashe key aka saka ta ciki aka rufe gate ɗin.

"Dan Allah buɗe mini ƙofa, zan tafi gida" ta yi maganar da sigar magiya. Sai dai kamar an gina shi, ko motsi bai yi ba, balle ta sanya ran zai amsa mata.

"Bawan Allah dan Allah ka buɗe mini, zan tafi gida ne na tashi" ko kallonta bai yi ba, ya ci gaba da kaɗa ƙafarsa a hankali.

Ajiye kayan hannunta ta yi, ta ɗan ƙara matsawa daf da shi, ta ce "Malam magana nake yi, ko baka jin hausa?" Takaici ya kama Nana, ko kurma ne ai yakamata ace ya na jin sauti, kuma tun da ya ganta a gurin ai ya san tafiya za ta yi.

Sule ne ya nufo ta, hannunsa riƙe da kwanon abincin kare, ya ce "Malama kin fito?"

Nana ta ce "Eh, ina ta yi wa wannan ɗan uwan naku magana, ya yi mini banza"

Sule ya kalle shi ya ce "Banza ya ce miki?"

"A'a ya yi mini shiru"

Ya ce "Auu shiru bai yi magana ba? Ba shi da lafiya ne, ki yi haƙuri"

Ta ce "Kurma ne?"

Sule ya ce "A'a yana ji, magana ce ba ya yi"

Maimakon ta tafi, sai ta ce "Bebe ne kenan?"

Sule ya ce "Bebe me kenan?"

"Ba komai, buɗe mini na tafi"

Ya ajiye kwanon hannunsa ya buɗe mata, ta ɗauki kayan har za ta fita, sai ta waiwaya aikuwa karaf idanunta a cikin nasa.

Ta ja kayanta ta fice ta tafi gida.

*****

Cikin damuwa Mama take kallon su Jamila, Suwaiba jiki ya ɗan yi kyau kwana biyu. "Jamila, wai haka za mu ci gaba da zama babu wani ci gaba? Kun san da an aurar da yarinyar nan kanku zai juyo, kuma haryanzu kuma babu wani tsayayye na kirki, duk sai takarce"

Jamila ta ce "Taɓ, ai wallahi babu wanda ya isa ya yi mini abin da ake yi wa Nana, wallahi bujirewa zan yi"

"Ke dalla rufe mini baki, kafin a kai ga hakan ba sai a samu mafita ba, na gaji da kashe kuɗi a gurin malamai, babu wani saurayin kirki mai kuɗi, duk sai gayyar tsiya".

Jamila ta ce "Ni fa auren nan ko na yi shi, ko kar na yi shi bai dame ni ba, ni damuwata na samu mai kashe mini kuɗi, nima na ɗana rayuwar jin daɗin nan, wannan baƙin talaucin nan na gidan nan, idan ka biye masa, haka rayuwar ka za ta ƙare, ka je kuma auri talaka irin Baba ka ci gaba da gyangyaɗa rayuwa, jin daɗi sai dai ka ga wasu suna yi"

Suwaiba ta ce "A ina za a samu mai kuɗin, mu ba wani shegen kyau ba"

Jamila ta ce "Kanti za mu shiga wallahi, dan ni ina ganin allura ma zan yi"

Suna cikin maganar, Nana ta shigo da sallama, kasa amsa sallamar suka yi, sai bin ta da kallo, ganin kayan da suke jikinta, ga hannunta ta jakar kaya.

Nana ba wani shahararren kyau ne da ita ba, sai kyakyawan diri, domin jikinta shi ne babban rashin tsaronta. Idan ta taho ta gaba duk hijjabin da ta saka, baya ɓoye ƙirƙirar ƙirjinta. Baƙa ce mai matsakaicin tsayi.

Ta fito tsakar gida ta ɗebi ruwa ta yi wanka, ta yi alwala.

Jamila ta kasa jurewa ta ce "Nana ina ki ka samu wannan rigar? Ta yi miki kyau sosai" Nana ji ta yi tamkar ta share ta, saboda yadda suka haɗa kai da babarsu, su ka wulaƙanta ta, suka ɗauki gaba da ita.

Amma ta yi yaƙi da zuciyarta ta ce "Da gaske?"

"Wallahi ta yi miki kyau sosai"

"Na gode" ta faɗa a taƙaice.

"Waye ya baki?"

Nana ta ce "Gidan da nake aiki ne suka bani"

"Zan zo a din ga bani aro"

Ta jinjina kai ta ce "Idan ma so ki ke sai na baki"

"A'a aron dai" Nana na shiga ɗaki, Mama ta ce "Mara zuciya, me take da shi da za ta baki? Ba ga uwar ɗakinki nan tana baki kaya ba"

Nana na saka ƙafarta a ɗakinsu, ta ganta a libraryn Ƙaisar.

"Meye haka kuma? Salla fa zan yi" ta yi magana tana waiwayen ganin ta ina za ta gan shi.

A kan kujera ta hange shi, yana rubutu a cikin wani littafi, ba tare da ya kalle ta ba ya ce "Ai ba a kira sallar ba ko?"

"To me ka kawo ni nan na yi maka, a yanzu? So nake na yi azkar kafin a kira sallar" Nana ta faɗa a hasale.

"Wanda za ki aura ba shi da lafiya, an ce ki je ki duba shi kin ƙi, me ki ke zato?"

Ɗan shiru ta yi, sannan ta kalle shi ta ce "Kai ka saka shi ciwon ciki kenan?"

Ya ajiye alƙalamin, ya rufe littafin, ya tashi ya ce "A'a, ba ni ba ne ba, miyagun ƙwayoyin da yake sha ne kawai suke tambayarsa, duk ba wannan ba, haryanzu ba ki shirya barin gidan nan ba."

"Wai in bar gidan na je ina?"

Ya tura littafin hannunsa, tsakiyar wasu littattafai ya ce "Yanzu ba wannan ba tukuna, kin ga da kin yadda da sharaɗinmu, da kin ceci ɗan yaron nan da yake ta ƙaunar ki"

A razane Nana ta ce "Wane yaron? Ba dai Haidar ba"

Ya harɗe hannayensa a ƙirjinsa ya ce "A'a ba shi ba, kalli mudubi da kin yarda ki na da halin ceton yaron nan, amma baƙin taurin kan ki ya sanya zai rasa rayuwarsa"

A gigice Nana ta ce "Wai wani yaron?" Da idonsa ya nuna mata mudubin. Muhsin ne a kwance, babu inda yake motsi a jikinsa, ga robar abinci, ga oxygen a hancinsa. Gefe mamansa ce, idanunta jawur saboda kuka. Ga kuma yar mahaifinsa Hajiya Sa'a a gefe.

Nana ta gigice ta ce "Muhsin"

"Eh, kin makara, an riga an bayar da jininsa ga wani aljani, mutuwa zai yi yaron"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, meyasa ba ka yi komai a kai ba?" Ta yi magana cikin kuka.

"Ina cikin aljanu masu son zaman lafiya, dama da zan yi wani abu a kai, sai dai ta hanyar ki, kuma farkawar sa ta ƙarshe ma sunan ki yake ta kira. Kash Allah sarki, dama sunan uwarsa ya kira da take zaune kusa da shi, tna lissafa dukkanin numfashin da yake fitarwa, cike da ƙauna da kuma fatan ya ci gaba da rayuwa, ba ke ba da ba ki sam ciwon sa ba" yayi maganar yana hura iska a jikin mudubin, a take komai ya ɗauke.

Nana ta rikice cikin kuka, ta rasa abun yi gaba ɗaya.

"Ƙanwar babansa ce ta bayar da jininsa, aka yi mata domin ci gaban samun duniyarta. Wadda dai ta bayar da turare a kawo miki. Shikenan mun gama je ki yi sallar ki"

"Nana" ta ji Baba ya kira sunanta da ƙarfi. Ta ɗago kai ta kalle shi, tana zaune a cikin ɗaki ta haɗa kai da gwiwa tana ta kuka.

"Me aka yi miki? Ko wani ne ya mutu?" Ta girgiza kai alamar a'a.

"To gidan aikin ne suka yi miki wani abu?" Ta girgiza kai alamar a'a.

Baba ya sake cewa "To kukan me ki ke yi, an ce tun da ki ka dawo ki ke abu ɗaya ko jikin ne?"

"Baba babu fa komai" ta yi magana tana tashi tsaye. Ta kalli gari ya yi duhu sosai, da alama isha ta wuce. Ta yi shiru ta tuna abin da ya sakata kuka, amma ta kasa tuna komai.

Ta yi alwala ta yi sallar magariba da isha'i, tana jin wata irin matsananciyar damuwa da tashin hankali a cikin zuciyarta, amma ta kasa tuna ko a kan mene ne. Abincin da ta zo da shi ta kasa ci, ta kira Nasiru ta bashi, ya karɓa ya gudu waje kar Mama ta hana shi ci.

Sai dai tun da sanya haƙarƙarinta a ƙasa take addu'a, amma bacci ya gagara, ta yi juyi, ta kuma amma ko alamar bacci babu a idonta, har aka yi kiran sallar farko, a kunnenta ta tashi ta yi alwala, ta yi nafilfili ta zauna har aka yi sallar asuba.

Har gari ya yi shaa, tana zaune. Ta tashi zata fara shirin fita, kawai idanunta suka sauka a kan jakar da ta dawo da ita, daga gidan sarkin baka. Ta ɗaukko jakar ta hau buɗewa. Sai dai ta zazzage jakar kaf babu komai a ciki. Ta yi guntun tsaki, ta ajiyeta, sai dai ta yi shiru tana tuno abubuwan da suka faru a gidan sarkin baka. Ko ba komai ya karrama ta, ya mutunta ta, tana matuƙar son sanin halin da yake ciki a yanzu.

Ta gama shirinta, ta yi wa Baba sallama ta tafi gidan aikinta.

A ɗaki ta iske Haidar bai ko tashi ba, kasancewar ba ta samu bacci daren jiya ba, ya sanya ta nemi guri ta kwanta a ƙasa, bacci mai nauyin gaske ya ɗauke ta.

Ji ta yi tamkar wani abu ba dai-dai yake ba, ga baccin tana yi, amma ba ya mata daɗi sam. A hankali ta buɗe idonta, kawai ta ga Alhaji Zailani a cikin ɗakin. A mugun sukwane ta tashi, ta ja da baya ta kalle shi ta ce "Lafiya, me ya kawo ka nan?"

"Gidana ne" ya bata amsa.

"Eh na san gidan naka ne, amma a cikin gidan naka akwai inda shari'a ta yi maka iyaka, tun da ba duka mutanen gidan ne iyalinka ba"

Ba tare da ya amsa maganar da ta yi ba ya ce "Mun fara magana ba mu ƙarasa ba, na zo mu ƙarƙare ta yau"

Cikin takaici Nana ta ce "Wace maganar?"

Ya nuna mata gefen gadon Haidar ya ce "Zauna mu yi magana"

"Ni ba zan zauna ba, ka gaya mini ko ma mene ne a haka"

Ya nemi guri shi ya zauna, a gefen gafon Haidar yana tsareta da idanunsa.

"Buƙata ce da ni a gare ki, wadda idan ki ka amince ke ma za ki samu biyan buƙatun ki"

Ta ce "Ni na ce maka ina da buƙatar wani abu ne?"

Alhaji Zailani ya ƙara tattara hankalinsa a kanta ya ce "Ko ba ki faɗa ba, na san ki na da buƙata kema. Kasuwancina ne ya fara yin baya, an ce mini muddin na yi tarayya da mace irin ki, taurarin ki za su haska nawa." Galala Nana take bin sa da kallo, yadda ya zauna babu kunya babu tsoron Allah, yana gaya mata maganganun banzar da babu komai a cikinsu sai jahilci da hauka.

Ko a jikinsa da kallon da take yi masa, ya ci gaba da magana. "Idan ki ka amince, zan baki kuɗi, kuɗaɗe ba ƙanan kuɗaɗe ba, kuɗin da sai kin rasa yadda za ki yi da su"

Cike da takaici Nana ta ce "Kai yanzu bawan Allah, ka na da kuɗin da zaka bani wanda sai na rasa yadda zan yi da su, me za ka yi da wasu kuma? Ai ina tunanin idan ka haɗa ka riƙe sun wadace ka"

Ya miƙe tsaye ya ce "Ai ba a daina neman kuɗi, ki amincewa buƙatata, zan baki kalar rayuwar da ba ki taɓa tsammani ba a rayuwar ki"

Nana ta ja da baya ta ce "Ba na buƙatar kuɗin ka, ko zan koma ga Allah a talauce ba zan abin da ka ke so ba, ko zan yi wannan mummunar ɗabi'ar ba zan yi da mushriki irin ka ba, Allah ya tsare ni daga sharrin ka"

Alhaji Zailani ya ce "A'a ba ki da wani zaɓi fa, tunda aka kasa riƙe budurwa kamar ki a gidanku, aka bar ki, ki ka fito yawon rainon yaro. Kuma na san tunanin ki bai wuce budurcin ki ba, babu lallai wani abu ya shafi nan gurin ma. Budurcinki ba zai taɓu ba, kuma idan ki ka samu kuɗi, za ki iya rayuwar ki ba tare da wani ɗa namiji ba. Ki yi tunani a kai" ya nufi hanyar fita ya fice daga ɗakin.

Jikin Nana ne yake wata irin tsuma, cike da tsoro da razani, ta dafe saitin zuciyarta da yake wani irin bugu tamkar ta fasa ƙirjinta, ta fito.

Ta kalli Haidar da yake ta baccinsa hankali kwance. Jiki a sanyaye ta tashi Haidar, ta yi masa wanka ta fita da shi falo tana ba shi Abinci.

"Ke me ki ke bawa ɗa na haka?" Ta ji muryar Shukura cikin ɗaga murya.

Nana ta kalle ta ta ce "Ƙosai ne da kunun gyaɗa"

"Ƙosai? Ki ke ba shi, a gidan uban wa ki ka samo wannan tarkacen ki ke bawa yarona?"

"Kunun a nan na dama, ƙosan kuma daga gida na taho da shi, shayi ba abincin yaro ba ne" Nana ta faɗa kanta tsaye.

"Shut up malama, ki kwaso jagwalgwalo daga waje ki kawo shi kina bawa yarona kashe shi za ki yi? Na san wani concoction aka haɗa a ciki ki ke ba shi, dan samun guri?" Nana kamar ta yaɓa mata magana, mussaman da take cike da takaici, da mamakin abin da babanta ya yi mata, amma ta yi shiru, ta haɗiye.

Haidar dai hankali kwance, yaka ta ɗaɗɗakar kunu a cikin feeder, ta tafi a fusace za ta fizge kwanon ƙosan ta yi jifa da shi. A zuciye Haidar ya buga mata feeder hannun sa, yana ihu.

Nana ta haɗe rai ta kalle shi, sai ya nutsu.

"Ɗaukko kwanon da ƙosan, ka zo ka bata haƙuri, ko kuma yau na saka a kwano a kai wa kare ya cinye ka, sai wataran za a sake haifo ka"

A ruɗe ya tashi ya ɗaukko kwanon ya kawowa Nana, yana cewa "Sorry Anty"

"Ba ni zaka bawa haƙuri ba, maminka za ka bawa haƙuri"

Mummy da take kallon duk abin da ya faru ta ce "Lallai tsakanin Haidar da Nana sai Allah. Sannan ke Shukura ban da abin ki, soyayya ce ta sanya har ta ɗauki abin ta ta bawa ɗanki. Sati biyun nan wallahi har ya yi kumari, ba nan ki ke complain na ramar sa ba? Malama ki wuce ki tafi makarantar ki, sannu da ƙoƙari Nana"

"Yauwwa Mummy ina kwana?"

"Lafiya kalau Nana, ya ɗan naki?"

"Yana nan lafiya ƙalau"

Kasancewar a fusace yake, bai gai da Mummy ba, sai da Nana ta yi magana. Nana tana ganin mutuncin Hajiya Amina, tana da kirki sosai da sosai, Nana ta din ga mamakin yadda take zaune da Alhaji Zailani da wannan mummunar ɗabi'ar da yake aitawa. Kodayake wata ƙila ba ta san yana yi ba. Wata zuciyar ta bata amsa.

Abin ya din ga damunta a zuciyarta, amma ta rasa wa za ta gayawa. Tare suka yi girki da Jummai. Har na dare suka yi bayan sun kammala yau ma Jumman ta roƙe ta, ta ajiyewa masu gadi Abinci kafin ta wuce gida.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull