Buzu book 1 complete - Chapter 17
Buzu book 1 complete Chapter 17: Buzu book 1 complete Chapter 17. Tun da ta tafi hanya take saƙawa tana warwarewa, idan ta ajiye aikin nan ba ta da wata…
4,461 words
Tun da ta tafi hanya take saƙawa tana warwarewa, idan ta ajiye aikin nan ba ta da wata makoma, yanzu Allah ya rufa mata asiri, ba ta da fargabar abinci ko kaɗan, dama abinci shi ne babbar damuwarta, ga kuma albashi mai tsoka da take sanya ran fara karɓa. Sai dai ga ƙoshi ga kwanan yunwa, ko dai ta ci gaba da zuwa tana fuskantar barazana daga mai gidan, ko kuma ta koma zaman gida ba ta da abin yi, yunwa ma kaɗai ta ishe ta.
Duk da akwai 'yar tazara kaɗan daga gidan aikinta, zuwa gidansu, amma har ta je gida tunani take yi.
Tun a ƙofar gida ta haɗu da Nasiru, ya ce "Nana kin dawo? Me muka samu yau?"
Ta yi murmushi ta ce "Ba komai"
"Bayan ga leda nan a hannun ki"
"Shinkafa ce, ka bari sai mu ci da daddare, ko an yi girkin dare ne?"
Nasiru ya ce "Tuwo ne, kuma tun da ga shinkafa ba zan ci tuwo ba, yauwwa ni na manta ma, ɗazu Baba ya yi wasu baƙi, yana ta shiga yana fita yana faɗa, ke yake jira ki dawo"
Ta yi sak, ta ce "Ni kuma?"
"Eh"
A ɗan marairaice ta ce "To me kuma na yi?"
Ya ɗan ɗage kafaɗarsa ya ce "Wallahi nima ban sani ba"
Ta kalli gidan ta ji gabanta ya faɗi, sai ta ji sam ba ta ƙaunar shiga gidan ma.
Ta daure a hankali, tana takawa da ƙyar, cike da fargabar rashin sanin abin da za ta tarar.
Ta yi sallama babu kowa a tsakar gidan, ta shiga ɗaki ta ajiye ledar abincin hannunta.
Gaba ɗaya ta rasa abin da yake yi mata daɗi, a zullumi take kawai Baba ya zo ya gaya mata me kuma ta yi a wannan karon.
"Laa Nana kin dawo?" Ta ɗan zabura, ta kalli Jamila dan ba ta san ta shigo ɗakin ba. Ta ce "Eh ya gidan?"
Jamila ta ce "Lafiya ƙalau, ga kunun aya can da na ajiye miki a jug, a gidan maman khairat muka yi, na san ki na son shi, shiyasa na ce bari na ajiye miki"
Nana ta yi murmushin ƙarfin hali, ta ce "Amma kuwa na gode sosai da sosai, bari na yi sallar magariba na haɗa da abinci"
Jamila ta ce "To shikenan, ga shi can ma an yi kira"
Nana ta ce "Amm yauwwa Jamila, Nasiru ya ce mini Baba yana nemana, dan Allah ko kin san abin da na yi yake nema na?"
"A'a, ai ban daɗe da dawowa ba nima"
"Ok to na gode" haka dai a ɗarare ta yi sallar magariba, duk da tulin damuwar da take ciki, ta ɗauki jug ɗin kunun ayar nan, domin ta ɗan sha ta bawa Nasir sauran, dan ko sha'awar abinci ba ta yi. Shi ma dan kar Jamila ta ji haushi ne, tun da ta ga neman shiri take yi da ita.
Ta buɗe jug ɗin ta kai bakinta, ta ji an ce "Kar ki sha"
Ta waiwaya ba ta ga kowa ba, ta sake kaiwa bakin ta aka sake cewa "Kar ki sha" kawai ta ɗauki fitila ta haska jug ɗin.
Jini ne a ciki yake ta tafasa, tamkar akan wuta. A razane ta saki jug ɗin kunun ayar ya zube. Ta din ga sauke numfashi, ta yi maza ta janyo zani ta goge gurin, dan kar Jamila ta zo ta tarar da abin da ya faru. Ba ta gama wannan taradaddin ba, Baba ya kwaɗa sallama muryarsa a sama kamar tashin hankali.
Wani fitsarin tsoro ne ya kama Nana, tun kafin ta san abin da ta aikata.
"Nana ta dawo ne?"
Jamila ta ce "Eh tana ɗaki"
Cikin hargowa ya ce "Ki na ina fito ki zo nan, magajiyar tsiya da jaraba"
Dumm ƙirjinta ya sake bugawa, a karo na babu adadi, jikinta ya din ga rawa yana neman gaza ɗaukarta, ta fito jiki a sanyaye tana jiran ji abin da Baba zai ce.
"Ashe kin je gidan Ummi, ta ce miki ku je ku duba yaron nan, ki ka ce ba zaki ba, ki ka ƙara nanata mata ba kya son sa. To ƙanin babansa ya zo nan ɗazu, sun ce a tattara duk wani abu da ya san ya yi miki a mayar masa. Kuɗin aurensa dubu saba'in, kuɗin da ya bayar aka kai ki gurin mai magani, da kayan shafe-shafe da ya kawo, ki na gidan mai magani aka yi amfani da su a gida, kusan lissafin dubu ɗari da sittin, sun ce a mayar musu, kuma ni ban san inda zan je na nemo wannan kuɗin ba, dan haka sai ki shiga ki fita ki san yadda za ki yi a nemi kuɗinsu a ba su."
Ayshercool 08081012143 Page 21
Idan da sabo, Nana saba da ire-iren waɗannan ɗabi'un na Baba, amma na wannan lokacin sun ɗaure mata kai fiye da yadda take tunani. Duk cikin kuɗin nan, babu wanda take tunanin ta ci, hana rantsuwa sai wanda aka ce an kai ta gurin mai magani da su, hatta kuɗin auren nata ba ta san nawa aka kawo ba, kayan toshin da ya kawo kuma, bayan tafiyar ta gidan mai magani, da ta dawo ma ba ta tarar da su ba, dan tun da aka kawo su ba ta taɓa ba. Ba ta tunanin ko a tukunya, an girka kuɗin nan ta ci, amma ya haƙiƙance a kan sai ta nemo kuɗi ta biya, to a ina za ta samo wannan maƙudan kuɗaɗen har haka?.
"Ina magana kin yi sukuri da kai, kamar makauniyar akuya. Nan da rana i ta yau suka ce za su dawo su karɓi kuɗinsu, ni kuma ba ni da su, kin ga kin yi wa kanki Asma'u. Babu rarrashi da ban bakin da ban yi miki a kan ki yi haƙuri, ki auri yaron nan ba, amma ki ka ƙi, sai ki ci gaba da zama a gidan ki ci uwar da ta sanya ba za ki yi aure ba. Ni wallahi na fara yadda da maganganun da mutane suke yi, shi wancan da aka fasa aurenku, duk da Rabi ta taka muhimmiyar rawa, amma matarsa ta din ga rashin lafiya sai da aka fasa, shi wancan daga fasa aure, an kashe shi har lahira, shi kuma wannan ya zo lafiya ƙalau daga komawa gida sai ciwon ciki. Nana babu irin murna da ban yi ba lokacin da aka haife ki, duk da ina da tarin 'ya'ya na gatanta ki na nuna miki so, ina yi miki kallon wadda za ta ji ƙaina, amma babu wanda yake azabtar da ni a cikin yarana sai ke Asma'u shikenan duniya ce ki je ki yi."
Cikin kuka Nana ta ce "Baba baki za ka yi mini? Haba Baba ba laifina bane ba ya zan yi. Ni a ba su haƙuri ko gobe a ɗaura auren, ko ina ne ma ya kai ni, muddin hankalinka zai kwanta"
"Kya ji da shi" Baba ya faɗa a ƙufule.
Mama ta cafe zancen da cewa "Ahaaf a juri zuwa rafi da tulu, wallahi wataran sai ya fashe, idan an faɗa ka din ga jin haushi, gara da ka gane annobar da take tattare da ita ai, ina ƙara gaya maka muddin wa'adin da na ɗibar maka ya cika tana gidan nan, wallahi sai na tafi"
"Dalla gafara rufe mini baki, ki fi ruwa gudu mana, ki bar ni da abin da ya dame ni"
Nana garin komawa ɗaki, ta yanke hannu da ƙofar ƙarfen ɗakinsu, sai dai sam hakan bai dame ta ba, ta fashe da kuka, ta rasa me ma yakamata ta yi. Da gaske ita annoba ce? Anya babu ƙamshin gaskiya a kan abin da ake faɗar a kanta?.
"Ƙaisar ne kai ne! Kai ka ke janyo komai, duk saboda son zuciyarka Allah ya shiga tsakanina da kai" ta yi maganar cikin ƙaraji. A library ɗin sa ta ganta. Ba ta damu ba, ta rintse ido ta ci gaba da faɗin "Ka rabu da ni, ka ƙyale ni na yi rayuwata, ka bi kakanin nawa kabari ku ƙarata, ni meye nawa da zaka din ga cutar da mutanen da suke tare da ni, ina ruwanka da rayuwata? Sai dai shiru, bai bayyana ba, kuma ba ta ji sanyi yana ratsata da yake alamta mata yana guri ba.
Watso litattafan gurin ta fara ƙoƙarin yi, cikin damuwa da kuka, amma suka ƙi faɗowa, tamkar gina su aka yi a gurin. Sai ma ƙara jin ciwo da ta yi a hannunta. Babu tsammani, wani littafi guda ɗaya tal ya faɗo ƙasa. Ta ƙurawa littafin ido, sai kuma cikin azama ta ƙarasa ta ɗauki littafin, na kwanaki ne da ta fara karantawa Ƙaisarya ƙwace.
Sai dai ta buɗe littafin, ta ga sai farar takarda babu komai a ciki, ta zazzage shi ta sake buɗewa amma babu komai a jiki.
Sai kuma a hankali ta lura da gurin da jininta ya taɓa, rubutu ya fara bayyana a jiki.
A hankali rubutu ya ci gaba da bayyana, tun yana dishi-dishi har ya yi clear.
Ko da ta fara karanta wannan shafin, sai ta ga tamkar ba ci gabn gurin da ta tsaya ne, a wancan karon ba, amma saboda tsananin son jin ƙwaƙwaf, da gudun kar ya kuma ƙwace littafin, kawai ta ci gaba da karantawa a haka.
Shekaru masu yawa da suka gabata, ƙauyen Buda da ke cikin ƙaramar hukumar Garkon jihar Kano. Sannu a hankali mutane sun raya gurin, su na gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali, da su da dabbobin su, ba tare da wata damuwa ba. Bayan shafe tsawon shekaru, ba tare da zuriyar wannan aljani sun kuma waiwayar mutanen gurin, domin ɗaukar fansa ba, kwatsam! Rana ɗaya mutanen garin suka tashi da fari. An yi noma ana jiran ayi girbi, kawai suka je gonakin su, suka tarar da shukokin su sun ƙone ƙurmus. Su ka shiga tashin hankali mara misaltuwa, domin noma yana ɗaya daga cikin abin da suka dogara da shi, domin rayuwa. Ba su gama wannan alhinin ba, dabbobin su suka din ga kamuwa da ciwo, ga yunwa da rashin wadattacen abinci. Tsuntsayen su, suka din ga kamuwa da mura su na mutuwa su ma. Hankalinsu ya yi mummunan tashi, suka rasa menene mafita, sai mutumin da yake jagorantar wannan ƙauye, ya yi tafiya domin bincikawa, ko za a samu magani, da kuma neman maƙwabtan ƙauyuka, su tallafa musu saboda abin da ya same su. A ɗaya daga maƙwabtan ƙauyukan, ake gaya masa sun yi sake, da suka zauna haka babu wani boka, da zai iya yi musu binciken abin da ka iya faruwa, da kuma gaya musu maganin matsalolinsu. A nan take aka haɗo shi da wani boka, suka taho garin tare.
Bokan ya ce a ba shi kwanaki uku, zai dawo musu da bayani. Ya tafi kan wani dutse da jakar kayansa, sai bayan kwanaki uku, ya saukko ya koma gurin mai gari.
"Ba ni labari, me yake faruwa da wannan gari, muke ta afkawa cikin bala'i a jejjere haka?"
Bokan ya dube shi ya ce "Ba komai ya haddasa wannan abubuwan ba, face ɗaukar fansar da wasu daga cikin aljanu zuriyar Dirsham suke yi, a kan abin da ainihin wanda suka fara zama a cikin ƙauyen nan suka yi musu." Nan ya ba su labarin abin da ya faru, duk da dama wani sun sani.
"To yanzu mene ne abin yi?"
"Zan yi muku aiki, amma na ɗan lokaci ne, domin kuwa za su kuma dawowa dan ba sa yafiya, abu ɗaya za ku yi wanda nake ganin shi ne mafita"
Cikin zaƙuwa mai gari ya ce "Mene ne wannan abin?"
"Yauwwa, za ku bada mutum ɗaya, ko biyu da za a yi wa girkar aljani, yadda zai din ga yi muku bayanin abin da ka iya faruwa wanda ba ku sani ba, sai dai za ku din ga yi wa aljanin hidima, da yi masa duk abin da yake so, shi kuma abu kafin ya faru ya sanar muku. Idan da wani mataki da za a ɗauka, duk zai din ga gaya muku".
Mai gari ya ɗan yi shiru sannan ya ce "To wai mene ne girkar?"
Bokan ya gyara zamansa, ya ƙara tattara hankalinsa a kan mai gari ya ce "Girka na nufin a zaunar da aljani ko kuma aljanu a jikin mutum, ta yadda za su iya zuwa kansa a duk lokacin da ya kira su. Idan aka yi haka za ku iya magana da su ma ta bakin wanda aka yi wa girkar, idan ma wani bayanin ne su yi muku"
Mai gari ya ce "Taɓɗijan, Aljanu kuma? Ba na tunanin akwai wanda zai amince ya yarda ayi masa wannan abun, mu dai ka yi abin da ya kamata ka taimake mu"
Ya ce "To shikenan, babu laifi sai dai maganin ba mai ɗorewa ba ne ba, ku sake bani kwana biyu kafin hudowar alfijir na ranar Alhamis zan yi aikin"
Haka kuwa aka yi, bayan kwana biyu, kafin hudowar alfijir, boka ya kawo wani ƙaho, da aka naɗe shi da farin zare, aka rataya masa wasu layoyi ya ce a za a binne a tsakiyar garin.
Ya saka aka gina wata ƙatuwar tukunya, aka haƙa rami aka sakata, ya zuba tarkacen tsaface-tsaface da lauyoyi, da wannan ƙahon aka binne ta a tsakiyar garin.
Sun yi imani, kuma sun yarda da wannan abu da boka ya yi musu, dan haka suka zauna lafiya a garin. Sai dai ɗaya daga makusantan mai gari, ya ce masa ya dace a tara mutane a samu ko mutum ɗaya, a yi masa girka saboda gudun abin da ka iya faruwa a gaba.
Ya amince da wannan shawarar, aka tara mutane aka yi musu bayani. sarkin aska ya yi farat ya ce shi ya yarda ya amince a yi masa girkar, saboda wani abu da ya ƙulle a ransa.
Haka aka yi shiri, aka haɗa shi da 'yan rakiya, zuwa ɗaya ƙauyen gurin bokan nan domin yi masa girkar Aljanu.
Sai dai da boka ya bashi zaɓin kalar aljanun da yake so ayi masa girkar da su, sai ya zaɓi baƙaƙen aljanu! Maimakon farare.
Aka yi masa girka, ya koma Buda, su na murna za su ƙara samun afuwa da kariya daga sharrin zuriyar aljani Dirsham Jaddul jinn, sai dai kash! Rashin sani ya fi dare duhu, Sarkin aska ya yi amfani da wannan damar gurin mayar da mutanen garin tamkar bayinsa, babu wanda yake ja da shi, abin da ya faɗa tilas ayi ko ba a so saboda kar aljani ya hukunta mutum. Ya sanya wa mutane tsananin tsoronsa, hatta mai gari sai abin da sarkin aska yake so shi ake yi. Kullum mutanen garin, cikin sintirin kai dabbobinsu suke yi, domin sadaukarwa aljani duna da aka yi masa girka da shi, domin ya kare su ya kare ƙauyen daga bala'i. Ya din ga janyo wasu daga cikin aljanun da mutanen Buda suka yi wa laifi, yana canza tsarin jinsinsu, ta hanyar sadaukar musu da jini, da yi musu alkawarin taimaka musu, gurin ɗaukar fansa a kan mutanen garin.
Sarkin baka na garin Buda, ya kasance cikin mutanen da suke bayar da magani, idan mutum ba shi da lafiya. 'yar sa guda ɗaya tal a duniya mai suna Lanti, duk in da za shi yawonsa da ita yake tafiya. Sarkin aska abokinsa ne, amma tun da aka yi masa girka ya canza halaye suka raba hanya.
Kwatsam! Sarin aska ya ce Aljani duna ya ce kar wanda ya sake bayar da magani a garin, idan ba shi ba, kuma garin babu wani wanda yake bayarwa dama bayan sarkin baka.
Sarkin baka ya ce Uban dunan ma ya yi kaɗan, balle shi kansa dunan, babu wanda ya isa ya hana shi bayar da magani.
Sarkin aska ya ce akwai gagarumin bala'i, muddin ya ci gaba da bayar da magani, sarkin baka ya ce bala'in ya daɗe bai afku ba.
Nan rashin jituwa ya ɓarke a tsakaninsu.
Mutanen gari, duk da su na jin tsoron sarkin aska, amma sai aka rabu biyu, wasu suna bayan sarkin baka, wasu kuma sarkin aska.
Kwatsam! Aka tsinci gawar sarkin baka a daji, jikinsa babu ko ƙwarzane balle a ce dabbobin daji ne suka kashe shi.
Lanti ta shiga tashin hankali, ta yi kuka sosai da sosai, dan daga ita sai kakaninta sai shi ta sani, babarta ta daɗe da rasuwa, shi ne yake yi mata komai.
Sarkin aska ya samu dama ya ci gaba da tsula tsiyarsa, sai da ya talauta da yawa jama'ar garin, saboda tsoron sa da ya sanya musu.
Bayan wasu shekaru, Lanti ta yi aure har ta haifi 'ya mace, mutsnen Buda suka sake tashi da wata annobar, a lokacin sarkin aska ya yi bulaguro da shi da yaronsa.
Aka wayi gari ƙafafuwan yaran garin yana shanyewa, ga wani irin tari da ƙuraje da suka din ga fesowa mutane.
Aka rasa yadda za ayi, ga Sarkin aska baya nan, tun da mahaifin lanti ya mutu, ba ta yi gigin cigaba da sana'ar sa ba, amma ganin halin da mutane suke ciki, ya sanya ta fara ba su ɗan abin da ta sani na magani, a matsayin taimakon gaggawa. Saboda alaƙar su da sarkin aska ta ƙara yin tsami, bayan da ɗansa ya nuna ya na son ta taƙi amincewa.
Ko da sarkin aska ya dawo ya tarar da abin da yake faruwa, ya yi ta bala'i a kan dan me Lanti ta bayar da magani, idan ba ta yi wasa ba Duna ya yi fushi da ita, abin da ya samu babanta ne zai same ta. Abin ya tsayewa Lanti, ta daɗe da tunanin sarkin aska yana da sanya hannu a cikin mutuwar mahaifinta. Mijinta ya ce ta yi haƙuri kar ta tanka. Kawai aka wayi gari, 'yar gurin Lanti ba ta iya tafiya ƙafafuwanta sun shanye, ita ma ta kamu da wannan larurar"
Nana ta juya shafin gaba, amma ta ga wayam babu rubutun komai. Ta dudduba duk rubutun ya goge, har na baya da ta karanta. Raunin hannunta take ƙoƙarin matso jini ta kuma shafawa a kai, ta ci gaba da karantawa, ta ji wata iska mai ƙarfi na ƙoƙarin ƙwace littafin daga hannunta.
Iya ƙarfinta ta saka, ta riƙe littafin, amma iskar ta haɗa da ita, ta yi sama ta fizge littafin ya shiga inda ya faɗo, Nana kuma ta dawo ƙasa tim!
"Wash!" Ta faɗa jin yadda ta ji ƙashin bayanta tamkar ya buɗe.
Guguwar ta rikiɗe ƙaisar ya bayyana.
"Idan ba ki yi wasa ba, taurin kai zai yi ajalinki kamar yadda ya yi na kakannin kakaninki, kodayake idan ba ki yi haka ba ai ba za a ce daga zuriyar su ki ka fito ba. Saboda ke na ɓatar da rubutun jikin littafi, amma saboda baƙar jaraba, ki ka gano jinin ki ne zai bayyana rubutun. Sai kuwa kin yi jinyar jinin ki da ki ka yi amfani da shi ki ka buɗe rubutun".
"To waye ya ce ka kirawo ni ina zaman zamana?"
"Ai kuma na fasa faɗar abin da ya sanya na kirawo ki, fita ki ban guri"
Nana ta ce "Ta ina zan bi?"
"Ta kaina"
Tsaki Nana ta ja ta ce "Ai ba ni na kawo kaina ba" ta yi maganar tana juyi.
"Wash Allah!" Ta faɗa cikin marairaicewa saboda ciwon da bayanta yake yi.
"Nana, an yi salla fa"
Tashi ta yi zaune tana kallo Nasiru, da yake a tsaye a bakin ƙofa, ta ɗan yamutsa fuska ta ce "Na gode Nasiru"
Ta yi juyi ta ji bayanta ya ƙara riƙewa, da ƙyar ta iya tashi ta lallaɓa ta fita ta yi alwala, ta dawo ta yi salla.
A wannan karon tiryan-tiryan abin da ta karanta a littafin Ƙaisar ya din ga dawowa kanta, ba ta manta komai ba, saɓanin sauran mafarkan da take manta komai.
"Sarkin baka, sarkin aska, Garba ga baka ga aska, kenan sarkin baka yana da alaƙa da labarin mutanen ƙauyen Buda?' 'A'a ba zai yiwu ba kawai dai labari ne ya zo a haka. Amma ya Lanti ta yi da 'yar ta mai ciwo, kuma za ta yarda sarkin aska ya ba su magani. Mtsew ƙaisar bai yi ba. Amma da nake danganta sarkin baka da wannan labarin, wataƙila ƙaryarsa ce kawai yake rubutawa ba wai faruwa ya yi a gaske ba.
Ba ta yi aune ba, ta ga lokaci ya kusa ƙure mata, ta tashi ta fara shiri a gaggauce, ta jiyo hargowar Baba, yana ta bala'i tare da jaddada ta nemo kuɗin da za a mayar wa su Saleh kafin sati ɗaya.
Ita dai ba ta ce uffan ba, ta gama kintsawa ta nufi gidan aikinta. Ba ta tashi tuna abin da ya faru ba jiya sai yanzu da ta nufi gidan. Gaba ɗaya pressure Baba ta sanya ta manta da abin da ya faru jiya a gidan Alhaji Zailani.
Yau gidan a buɗe yake, tana zuwa tura ƙofar kawai ta yi ta shiga. Yana kallonta har ta wuce ta shiga cikin gidan.
Shukura ta tarar a falo, ta gaisheta ta amsa mata a yatsine ta ce "Yau Hajiya ba ta nan, sun fita da Jummai tun sassafe, Haidar yana gurin Daddy, idan da wani abu ki shiga kitchen ki duba ki dafa muku, ni na tafi"
Saroro ta yi jin ta ce wai Haidar yana sashen mai gidan, Shukura ba ta jira me Nana za ta ce ba kawai ta fice ta tafi.
Nana ta shiga kitchen, ta dafa abin da za ta bawa Haidar, da wanda za ta samu ta ci ita ma, sai dai shiru babu Haidar babu alamarsa.
Ta din ga kallon agogo, ta ga yakamata ace zuwa yanzu an wanke masa baki, an yi masa wanka ya karya amma bai fito daga sashen Alhaji Zailani ba, duk da ma bai fiye yin dogon bacci ba idan gari ya waye.
Abu kamar wasa har ƙarfe sha ɗaya da mintuna na rana, Haidar ɗin bai fito ba, sai ta ji ta damu ƙwarai da gaske. Ta nemi guri ta zauna, tana tunanin ko tarko ya yi mata, amma wata zuciyar ta ce ya za ayi ya haɗa baki da 'yar sa ya yi miki tarko? Tun da dama yana wasa da Haidar sosai.
Kamar a cikin tunani, ta din ga jin kukan Haidar, yana ce mata yunwa yake ji.
Firgigit ta tashi, kamar wadda aka mintsina, ta nufi sashin Alhaji Zailani.
A ƙofar falonsa ta din ga kwaɗa sallama amma shiru, ba a amsa ba. Ta zira kai ta shiga falon amma babu kowa a falon. Sai kuma jiri ya fara ɗibarta garin ya din ga jujjuya mata. Ƙaton frame ɗin da yake ɗauke da hoton Alhaji Zailani, a hankali ya juye Alhaji Fatuhu ya bayyana a jiki, idanunsa na zubar da hawayen jini.
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, Innalillahi wa innalillahi raji'un" Nana ta din ga maimaitawa.
Fitilun ɗakin ne suka ɗauke, wata iska ta din ga buga tagogin da ƙarfi.
Muryar Alhaji Fatuhu ta ci gaba da ji yana sheshsheƙar kuka, sai kuma ta fara jin muryar Muhsin yana kiranta "Anty Nana, Anty Nana" sautun muryar Haidar ma ya fara amsa kuwwa a kunnenta "Anty yunwa nake ji"
"Ƙaisar wai meye haka ne? Dole sai ka tozarta ni a gaban mutane, meye haka ka ke yi mini?" Nana ta yi maganar cikin ɗaga murya.
A take ta ga komai ya koma yadda yake, sai Alhaji Zailani a gabanta.
"Lafiya dai?" Ya yi maganar yana mata kallon tuhuma. Duk ta haɗa gumi sai ajiyar zuciya take yi.
"Haidar zan ɗauka na ba shi abinci, lokacin cin abincin safen sa ya wuce"
Alhaji Zailani ya yi murmushi ya ce "Kin damu da ba ɗan da ke ki ka haife shi ba a kan kuɗi ƙalilan, ni a kan kuɗi masu yawa nake buƙatar ki ara mini dama, amma kin ƙi. Kuɗi zan baki ba ƙanana wanda ke da talauci har abada".
"Ka ce "Har abada? Kai wa ya baka wannan tabbacin? Dan Allah kar ka sake tunkarata da wannan maganar, ka rabu da ni ba na so".
"Daɗina da ɗan talaka girman kai, ke ga talauci ga girman kai"
"Na ji, dan Allah ka bani yaron nan na ba shi abinci"
Ya yi dariya ya ce "A tunaninki, zan zuba miki ido ne, na rasa damata wallahi ko za ki mutu sai na yi amfani da ke na cimma muradina, ba zan sake lallaɓa ki ba, ta ƙarfin tsiya sai na samu abin da nake so"
Jikin Nana ya hau rawa, sai ta marairaice "Dan zatin Allah ka yi haƙuri, ka rufa mini asiri bayan Allah da manzonsa mutuncina ne kawai ya rage mini dan Allah ka yi haƙuri"
Shima ya kwantar da murya ya ce "A'a Asma'u, mutuncinka kuɗinka, idan kina da kuɗi miji sai wanda ki ka zaɓa. Auren ma bai zama dole ki yi ba, na ishe ki komai. Kin ga yau ne ranar sa'ar aikin nan, dan Allah ki kwantar da hankalinki, ba dogon lokaci za a ɗauka ba"
Dif! Dif! Dif haka zuciyarta ta ƙara ƙaimin bugawa, maimakon tsoro ya shigeta sai wata irin rawa da jikinta yake yi.
"Ka bani hanya na wuce, idan ba haka ba wallahi sai na kashe ka, ka je a duba maka taurarin Shukura, wataƙila na ta sun fi nawa haske. Ka bani hanya kafin na yi ajalinka"
Ganin ya ƙame kamar gunki yana kallonta, ya sanya ta hankaɗe shi, ta buɗe ƙofa ta fita. Tana fita daga ɗakin ta ƙara jin ta burkice, kamar hankalinta zai gushe.
Biyo bayanta ya yi, tana gaba yana bin ta a baya yana kiran sunanta.
Tun kafin ta ƙarasa gate, ta gan shi zaune a kan benci shikaɗai, addu'a ta din ga yi Allah ya sa a buɗe gate ɗin yake ta fice, domin in dai wannan ne ba kulata zai yi ba ya buɗe ƙofar. Kullum fuskarsa cikin rawani.
Sai da Alhaji Zailani ya yi mamaki, domin hatta masu gadi ya aike su, duk da ga babban yaronsa mai zuwa aike a gidan.
Ga mamakin Nana, kafin ta ƙaraso gurin gate ɗin, ya miƙe tsaye ya nufo su, taku biyar ya yi ya tsaya ya kafe Alhaji Zailani da ido. Ji ya yi tamkar an yi masa wani irin mugun dabaibayi ya kasa ɗaga ƙafarsa.
A hankali ya juya ya nufi Nana da take ta jijjiga gate ɗin, tana neman hanyar fita.
Bai ce mata uffan ba, ya buɗe mata gate ɗin ta fita ko takalmi babu a ƙafarta.
Ayshercool 08081012143 P22
A hankali Alhaji Zailani ya buɗe idanunsa, ya gan shi a kan gadonsa a kwance. Shiru ya yi yana ƙoƙarin tariyo abin da ya faru. Fes komai ya dawo kansa, amma daga iya lokacin da ya biyo Nana, suka yi ido huɗu da wannan Buzun, ya kasa tuna komai.
Ya tashi zaune yana ƙoƙarin saukkowa daga kan gadon, sai ga Hajiya Amina ta shigo ɗakin, hannunta ɗauke da kofin tea.
"Sannu Alhaji ka tashi?"
"Yaushe ki ka dawo?"