Buzu book 1 complete - Chapter 42
Buzu book 1 complete Chapter 42: Buzu book 1 complete Chapter 42. Tun da Nana ta koma ɗakin, ya ƙura mata ido, amma ta basar ta ce "Sannu Sayyid" kawai ya…
4,497 words
Tun da Nana ta koma ɗakin, ya ƙura mata ido, amma ta basar ta ce "Sannu Sayyid" kawai ya kawar da kansa ya lumshe idanunsa.
**** Cikin damuwa Fadila take yi wa Hajiya Suwaiba magana, duk da yanayin fuskarta cikin ko in kula take amsa mata.
"Ni gani nake kamar za mu ɗora wa Alhaji Zailani ɗawainiya a ce mu koma Asibitin da yake da file, ya ɗauki nauyin Daddy. Kin ga haryanzu kashe kuɗi ake yi, ba ma a gano me yake damunsa ba. Amma shi Alhaji Zailani ya dage, kina ganin babu matsala?"
"To da da matsala zai ce, a kai shi ne? Tun da mun kasa affording nan Asibitin, kuɗinmu ya ƙare, idan muka koma na gwamnati, ai dariya za a yi masa. Gara mu koma can ɗin".
Raudah da a baya, take biyewa mahaifiyarta ita da ƙannenta, suke zabga wa Fadila rashin kunya son ransu, yanzu gaba ɗaya ta saduda. Musamman ganin yadda Fadila ba ta da nutsuwa duk ta rame, saboda damuwa saɓanin da da suke tunanin, kuɗin mahaifinsu ne kawai ya sanya ta aure shi, kamar yadda mamansu ke nanata musu.
Ta ce "Mummu Anty fa gaskiya ta faɗa, nima gani nake yi, tamkar ɗora wa Daddyn su Shukura nauyi ne, ba fa mu san ranar barin Asibiti ba"
"Na saka baki da ke ne?" Rauda ta girgiza kai tare da yin shiru.
Fadila ta sake cewa "Ni kuwa ya maganar kuɗaɗen kuwa? An gama biya ko haryanzu da saura?"
"Da an gama biyan ai za ki ji"
Fadila ba ta haƙura ta sake cewa "Dama gidan da Umma take ciki ne, shi ne ya bata, mun yi magana da ita, a sayar da shi za ta koma gidan Yaya da zama. Sai kuma gwala-gwalaina na aure, duk su na nan. A sake rage bashin, a kuma biya kuɗin makarantar su Hibba. Jiya da ya ɗan farfaɗo sai da ya yi maganar su. Ƙuri Hajiya Suwaiba ta yi mata da ido, domin ta tabattar da gaske take yi, ko kuma makirci ne kawai da iya Duniya. "Fadila" ya kira sunanta da ƙarfi.
Gaba ɗaya suka nufe shi, saboda tun jiya bacci kawai yake yi, kamar sumamme.
"Kar ki sayar da gidan Umma, ba ta na yi. Ni Allah zai kawo mini ɗauki" Ya yi maganar tamkar yana magana da kurame, saboda yadda yake ɗaga murya.
Fadila ta ce "To, ba sayarwa za a yi ba"
"Kin haihu ne?"
Ta ce "A'a"
"To Allah ya raba lafiya. Dan Allah ku cewa likitan nan, ya zo ya cire mini robar fitsarin nan, ta dame ni wallahi"
Rauda da idanunta suka cika da hawaye ta ce "Daddy ka yi haƙuri, ka ga ba iya tashi ka ke yi ba, zuwanka banɗaki zai baka wahala. Ka yi haƙuri ka bar robar fitsarin nan "
Ya jinjina kai ya ce "Shikenan Raudana, na gode"
"Sannu Daddy" ta yi maganar idanunta na zubar da hawaye.
A ranar Alhaji Zailani ya aiko da mota, aka mayar da Alhaji Fatuhu Asibitin su Doctor Sharif.
A gaban iyalan Alhji Fatuhu, ya din ga jaddadawa Doctor Sharif, a kula da amininsa, duk abin da ya kama a yi masa, shi zai din ga biya. Suka yi ta godiya. Daga bisani ya bi bayan Doctor Sharif, suka fita.
"Ka na ji na Sharif?"
"Eh Alhaji"
"Wannan mutumin ko me za a yi masa, ba zai taɓa warkewa ba. Kawai dai ku din ga yi masa abin da ya sauwwaƙa da duk wani abu da zai ƙara rikita masa jiki. Ka sanya ido sosai a kansa, zan din ga kiran ka, ina jin halin da yake ciki. Zan tafi umara ne."
"Ba ka da matsala Alhaji"
"Shikenan, za ka ga saƙo in sha Allah"
****
Nana kuwa tun tana kiran lambar Habu, tana sanya ran za ta same shi, zai ɗauka har ta sare.
Ga jikin Sayyid sai godiyar Allah, babu wani ƙarfi a tattare da shi. Sai dai akwai ƙarfin hali, a haka wasu lokutan yake fita buɗe gate.
Jiki a sanyaye take kallon shi, ta ce "Sayyid, gobe in Allah ya kaimu, Litinin za mu je gwaje-gwajen da aka bamu, ga shi haryanzu ban samu Habu a waya ba. Ko gidan zan je na duba ko lafiya?" Ya girgiza kai ya ce "A'a" ta yi shiru tana kallonsa, dabara ta faɗo mata, ta ɗauki wayarta ta fara duba lambar Hajiya Amina. Amma ko sama ko ƙasa ta nemi lambar a wayar ta rasa. Ta duba iya in da za ta iya dubawa amma ba ta samu lambar ba. Ta ɗaga kai ta kalle shi, ta ga ya lumshe idanunsa, jikinta ya ba ta shi ne ya goge lambar ba wani ba.
Ta koma gefe ta yi shiru, ta rasa abin da yake yi mata daɗi a ranta, gaba ɗaya a tsorace take da ciwon nan nasa. Cikin dare ba ta iya bacci, da ta fara bacci, sai ta tashi, ta duba ta ga ni ko yana numfashi, ta ɗora hannunta a kan ƙirjinsa, ta ji ko zuciyarsa na bugawa, gaba ɗaya ba a nutse take ba.
Daren ranar Lahadi, Nana ta tafi cikin gidan, domin sanar da Hajiya Halima, batun komawa Asibiti da za su yi da safe.
Siyama ta tarar a falo, tana kallo tana ciye-ciye.
Nana ta ce "Dan Allah gurin Hajiya na zo" ko inda Nana take ba ta kalla ba, ta ci gaba da kallon Tv. Ganin Siyama ba ta da niyyar kula ta, ya sanya ta nemi guri ta zauna, ta fara zaman jira. Aƙalla Nana ta shafe awa ɗaya da rabi, ƙarshe ma Siyama ta tashi ta bar mata falon. Har Nana ta yanke tsammanni, sai ga Hajiya Halima ta saukko daga kan bene.
Nana ta yinƙura ta ce "Hajiya ina wuni"
"Lafiya ƙalau" ta nemi guri ta zauna.
Ya kalli Nana ta ce "Ya aka yi?"
"Dama Hajiya zuwa na yi na gaya miki dan Allah gobe in Allah ya kaimu, za mu yi sammako, mu je Asibiti ne an bamu gwaje-gwaje, shi ne na ce bari na zo na gaya miki kar mu yi laifi".
Kamar Hajiya Halima ba za ta yi magana ba, sai kuma ta kalli Nana ta ce "Shi kuma gadin, da buɗe gate ɗin ni zan je na zauna na yi?"
Nana ba ta yi tsammanin jin haka daga bakin Hajiya Halima ba, amma ta dake ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri Hajiya, in sha Allah ba zamu jima ba, ki yi haƙuri"
"Ni fa kin ga Nana, idan abin nan ba zai yiwu ba, a haƙura kawai. Na nemi wani, ku je ku nemi lafiya babu yadda za a yi ga aiki, sai dai ku bar mini ƙofa ku na can yawon Asibiti, ba fa zai yiwu ba"
Nana ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri, na sani amma in sha Allah zai samu lafiya ya ci gaba da aikin, ki yi haƙuri"
Hajiya Halima dai, ba ta cewa Nana su je ko kar su je ba, Nana ta tashi ta koma ɗakinsu, duk jikinta a sanyaye.
Wayewar garin Litinin, Nana ta kammala komai da wuri, ta tafi cikin gidan, domin sake gaya wa Hajiya Halima, amma ta tarar ba su ma tashi daga bacci ba.
Ta ga idan ta tsaya jira, za su iya makara, dan haka ta fice, ta samu abin hawa suka tafi.
Nana ta ɗauka abin mai sauƙi ne, amma wuni suka yi yawo, daga nan zuwa nan, wasu gwaje-gwajen, aka ce ma ba za su fito a ranar ba, sai bayan kwanaki biyu. Ga shi duk kuɗin hannunta suka ƙare. Ƙarshe ba su samu ganin likita ba, da tasa tasan da suke hannunsu ba, saboda sai bayan la'asar liƙis sannan suka samu teses ɗin.
Su na komawa Nana, ta ɗora girki, zuciyarta ta yi ta raya mata, ta je ta gurin Hajiya Halima dai, ta ƙara ba ta haƙuri, amma ta fasa saboda ba ta san me za ta tarar ba, kar ta yi mata wulaƙanci.
Nana ta ci gaba da bashi magungunansa, tana kula shi, zuwa kwanaki biyun da aka ɗibar musu, komawa karɓar sakamako. Idan ana buƙatar buɗe gate, ita take zuwa ta buɗe, idan kuma ya ji jikin nasa da sauƙi, sai ya je ya buɗe da kansa.
Nana ta sake zuwa ta sanar da Hajiya Halima za su koma Asibiti, nan ma ta din ga ƙanan maganganu, Nana dai ta yi ta ba ta haƙuri. Ta fito suka fita da Sayyid.
Suka fara zuwa, suka karɓo gwaje-gwajen, suka koma Asibiti. Sai dai wani likitan suka gani daban. Likitan ya ce ba za su iya kula da case ɗin sa a nan ba, saboda akwai matsala a zuciyarsa, dan haka aka tura su Asibitin gaba. Can ma da suka je, aka yi masa hoton ƙirji, aka yi masa ECG, shi ma da ƙyar suka samu, dan sai da Nana ta bayar da cin hanci, sannan aka yi cuku-cuku, aka ba su result ɗin a ranar, sai dai shi ma da suka koma likitan da zai duba su, ya tafi. Nana tamkar ta ɗora hannu a ka ta fasa ihu, gaba ɗaya ma ta rasa abin yi, ga shi dakiya kawai take yi, ba ta son ta yi kuka ya gani, ta san yana yin kuka, za ta ɗaga masa hankali. Kawai ta zauna ta yi shiru ta rasa abin da yake yi mata daɗi.
"Mu tafi gida"
"Sayyid ba mu ga likitan ba zamu koma?"
"Eh mu tafi" jiki a sanyaye Nana ta tashi, suka nemi abin hawa suka koma gida.
Sai dai su na zuwa gidan, suka din ga bugu, amma gate ɗin a rufe. Tun Nana tana sanya ran za a buɗe har ta sare. Ta zauna a kan ɗan dakalin da Sayyid ya zauna, ta rasa abin da yake yi mata daɗi.
Ta sake jarraba kiran wayar Habu, amma still ba ta shiga, ta damu sosai da rashin jin ɗuriyar su Habu. Ta samo ruwa suka yi salla a ƙofar gida, tana ta tunanin mene ne abun yi? Har magariba ta yi, sauro ya fara bin su, Nana tana bugun gate ɗin, amma shiru.
"Sayyid yanzu mene ne abin yi?" Bai yi magana ba, sai ga motar Hajiya ta dawo, tare da Siyama. Nana ta yi ajiyar zuciya, ta tashi ta nufe su fuskarta ɗauke da murmushi ta ce "Hajiya ashe fita ku ka yi, kawo mukullin a buɗe" ta miƙa wa Nana mukullin, ta buɗe musu gate ɗin. Wani abu mai ɗaci ya ɗar su a zuciyar Sayyid, ganin yadda Nana ke kokawa da ƙaton gate ɗin da ya fi ƙarfinta. Ba su damu da tambayar Nana ya mai jiki ba, amma Siyama ta ƙura masa ido, tamkar idonta zai faɗo.
Suka wuce da mota, Nana kuma su ka tafi ɗakinsu. Wasu lokutan jikin nasa, sai ya ɗan samu afuwa, lokaci ɗaya kuma sai jiki ya burkice ya kasa komai.
Sai ranar Juma'a, sannan suka samu su ka ga Likita. Likitan ya duba gwaje-gwajen da aka yi masa, da hoton zuciyarsa sannan ya kalle su ya ce "Maganar gaskiya Hajiya, zuciyar mijin ki akwai matsala. Yana fama da Av block stage 2"
"Ni dan Allah ba sai ka yi mini bayani ba, dan Allah ya za mu yi. Mun sha wahala kafin mu ganka Doctor "
Ya ce "Ki yi haƙuri, zan ɗora shi a kan magunguna, zamu din ga yi mu na monitoring zuciyarsa. Zan rubuta muku allurar da za a yi masa, saboda a kiyaye zuciyarsa daga shiga stage 3. Idan ya tafi stage 3 to 4, to sai dai a yi masa aiki, a saka na'urar da za ta din ga taimakawa bugun zuciyarsa."
Sayyid dai ya yi shiru, ya sunkuyar da kansa.
Cikin rawar murya Nana ta ce "Doctor,ni yanzu duk ba na gane wannan bayanin naka, meye abin yi? Me za a yi masa yanzu?"
"Zamu yi masa allura ne, amma sai under ECG machine, to kuma gaskiya a Asibitin nan, zaku iya kaiwa wata biyu ba a yi masa ba."
Cikin matsanancin tashin hankali, Nana ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Dan Allah babu yadda za a yi, a taimaka mana, yana shan wahala wallahi. Wasu lokutan ba ya iya bacci, saboda numfashinsa."
Likitan ya ɗan kalli Nana sannan ya ce "Idan da kuɗi a gurinku, sai na kwatanta muku, wani Asibiti, da za ku je a yi muku"
Cikin azarɓaɓi ta ce "Likita ina ne?"
"Can wani Asibiti ne a by pass, za a yi masa allurar tsawon watanni ukku, duk wata za a din ga yi masa allurar, bayan an yi zai yi kwanaki uku a Asibitin, kafin ya tafi gida. Naira dubu ɗari biyu da hamsin ce, duk yi ɗaya".
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un" Nana ta furta a hankali jikinta a matuƙar sanyaye.
Sayyid ya kamo hannunta, ta kalle shi murya ƙasa-ƙasa ya ce "Mu tafi gida"
"A'a Sayyid, ba shi ne mafita ba" ta mayar da hankalinta kan likitan ta ce "Dan babu wani abin yin sai wannan?"
"Gaskiya wannan ne kawai abin yi, sai dai idan ba ku da hali, ku bi layin na nan Asibitin, shi kuma dubu ɗari da Ashirin ne. Kuma idan aka bari ba a yi ba, ya ci gaba sai dai a yi masa aiki, a saka masa na'ura naira Million huɗi, kuma shi ma aikin sai a Lagos ake yin sa. Yanzu zan rubuta muku magunguna, wanda zai din ga amfani da su, zuwa lokacin da ku ka yanke shawarar abin da za a yi. Nana ji take kamar ta ɗora hannu a ka, ta rusa ihu, saboda kaf abubuwan da likitan ya lissafa babu ɗaya da take tunanin zai yiwu. Ya rubuta musu magunguna, suka tafi gida.
Da wuri suka koma gida, sai dai tun da suka koma, babu wanda ya iya yi wa wani magana, tamkar kurame, haka suke zaune a ɗakin. Ta lallaɓa shi da ƙyar ya ɗan ci Abinci, ya koma gefe ya zauna ya yi shiru, babu tsammani Nana ta ga Siyama ta ɗage musu labule. Nana ta kalle ta, shi kuma ko motsi bai yi ba, balle ya buɗe idonsa.
"Mami na neman ki" ta yi maganar tana satar kallon Sayyid, da yake zaune babu rawani"
"Ina zuwa" Nana ta faɗa a hankali.
"Shugaba, bari na je kiran da ake yi mini na dawo"ya jinjina mata kai ta tashi ta fita.
Bayan mintuna kusan talatin, ta dawo ɗakin, ba ta ce masa komai ba, ta ci gaba da harkokinta.
Sai da aka yi sallar la'asar, sannan ta dube shi cikin tausasa murya ta ce "Dan Allah Sayyid ka bari na je na sanar da Habu halin da ake ciki. Mu na buƙatar sa da gaggawa, abubuwan sun yi mana yawa mussaman yanzu da... "Ta kore mu ko?" Ya tari numfashin Nana.
Ras! Gabanta ya faɗi. Ta buɗe baki za ta yi magana, amma ta kasa, sai ma hawayen da take ta maƙalewa, da suka samu damar zirarowa tamkar an kwance famfo.
Ayshercool 08081012143 49
Ta sunkuyar da kanta, zuciyarta na yi mata wani irin zafi da raɗaɗi.
Tun da Siyama ta zo ta kira ta, zuciyarta take dukan uku-uku, har ta shiga falon, ta samu Hajiya Halima. Ta durƙusa ta gaishe ta, ta amsa mata sama, sannan ta dube ta ta ce "Amm dama, na kira ki ne, a kan tun da mijinki babu lafiya. Kin ga ba zai yiwu yana kwance babu lafiya, ku ku na yawon Asibiti, a din ga bar mini gida haka ba. Na zata abin na ƙare ne, to ban ga alamar zai samu lafiya nan kusa ya ci gaba da aikin ba. Saboda haka nake mai baki haƙuri, ga haƙƙinsa na wannan watan, dubu saba'in na ƙara muku dubu talatin, na sallame ku. Ina fatan Allah ya ba shi lafiya ya sanya kaffara ne. Na saka an nemo mini wani mai gadin ma, jibi in sha Allah zai zo ya fara aiki, sai ku kwashe kayan ku. Duk ba wani daɗewa za mu ci gaba da yi a gidan ba, mu ma zamu koma can inda mijina yake a Abuja. Mijin Hajiya Amina, da ta haɗa ni da ku ya sai gidan nan, mu ma Abuja zamu koma"
Duk yadda ƙirjin Nana ya buga da ƙarfi, amma ta yi iya ƙoƙarinta, tattara nutsuwarta da nanata Innalillahi wa Innalillahi raji'un a zuciyarta.
A zahiri kuma, ta sanya hannu biyu, ta karɓi kuɗin daga hannun Hajiya Halima, tare da sakin murmushi mai ɗauke da ma'anonin da zuciya ce kawai za ta iya shaida su. Ta ce "Mun gode sosai da sosai da wannan damar da aka bamu Hajiya. Ina fatan a zamanmu da ku tsawon watanni biyar zuwa shidda, ba mu yi wani abu da zai ɓata muku rai ba. Idan ma mun yi mu na neman afuwarku a yafe mana dan Allah. Idan kun je Abuja dan Allah a gaida ƙawata, a ce ina yi mata fatan alkhairi sosai da sosai."
Hajiya Halima ta ce "Ba komai, Allah ya ba shi lafiya" Nana ta miƙe jiki a sanyaye ta fita.
Nana na fita Hajiya Halima ta murza goshinta ta ce "Kai, na yi abu zai dame ni, yarinyar nan ta bani tausayi sosai da sosai. Ban so na sallame su yanzu ba, yanayin idon mijin da yadda na tarar da shi a kwance da muka dawo, ya tabattar mini da yana jin jiki. Ni ban san dalilin da ya sanya Alhaji Zailani ɗaukar wannan matakin ba, kuma ya ce kar na kuskura na gaya wa Hajiya Amina"
Siyama ta kwaɓe baki, ba ta ji ta damu da korar su ba, saboda ta tsani Nana, amma tana jin kewar daina ganinsa da za ta yi.
Sayyid ya ƙura mata ido, yadda take ta rusa kuka, ya saka hannu ya share mata hawayenta, ya ce "Ki daina kuka, ki je ki nemo Habu, da zan iya da kaina zan je. Amma da na fara tafiya nake jin haki" Ta jinjina masa kai, ta share hawayenta, ta shiga banɗaki ta wanke fuskarta.
Ta fito ta mayar da hijjabinta, ta ce "Bari na je, ko ka na da buƙatar wani abu, kafin na fita?"
Ya girgiza kai ya ce "Sai dai ki kula da kan ki, ki dawo mini lafiya Rayuwata" wasu hawayen ne su ka cika mata ido, ta ƙaƙalo murmushi ta ce "In sha Allah shugaba" ta fice daga ɗakin cikin matsananciyar damuwa.
Haka kurum ta din ga jin gabanta yana faɗuwa, jikinta a matuƙar sanyaye, amma ta danganta hakan, da halin da suke ciki.
Sai dai duk da yamma ce, layin gidan Alhaji Zailani shiru, ba ta hango dandazon buzayen a zaune, su na shan shayi ba. Kamar yadda suka saba. Da ƙyar take jan kafarta, ta ƙarasa cikin layin. Ta je ƙofar gidan Alhaji Zailani ta fara bubbugawa. Sai da ta buga sau uku, sannan wani matashin dattijo ya buɗe. Nana ta ɗan yi turus sannan ta ce "Ina wuni?"
"Lafiya ƙalau yaya aka yi?"
"Amm dama, gurin Habu na zo, ko Sule masu gadi a gidan nan"
Ya ɗan ware ido sannan ya ce "Buzaye ko? Ai yau kwanaki huɗu da suka wuce, aka zo da wata doguwar mota, duk aka kame Buzayen layin nan kaf, aka tafi da su, babu wanda ya san inda aka kai su"
Cikin matasanancin mamaki, Nana ta ce "Baba su waye suka tafi da su? Laifin me suka yi?"
Ya ce "Allah masani 'ya ta. Doguwar mota ce dai baƙa ƙirin, ke motocin uku ne ma, biyu a farkon layi, duk su ka kame su, ɗaya motar dai rubutun fransanci ne a jiki, babu wanda suka yi wa bayani, suka tafi da su".
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ta maimaita cikin matsanancin tashin hankali ta ce "To dan Allah Hajiya Amina tana nan?"
"A'a, sun tafi Umara, tun washegarin faruwar abin"
Nana ta sake cewa "To dan Allah bawan Allah, babu wani wanda zan samu wani bayani daga bakinsa a layin nan" Gaskiya ban sani ba, sai dai ki zagaya ki tambaya. Ya koma cikin gida ya rufe gate ɗin. Nana ta ji ƙafafuwanta na wata irin rawa, har suna neman gaza ɗaukar ta. Da ƙyar ta din ga ɗaga su, tana tafiya ba tare da ta san inda ta dosa ba. Ta yi shiru tana tuna maganganun Hajiya Halima, da ta ce mijin Hajiya Amina ne ya sai gidan da suke ciki. Wato yana sane ya yi abin da ya yi kenan. Ta koma tunanin suwaye suka ɗauke buzayen layin gaba ɗaya, lokaci ɗaya ko dai wata ɓarnar suke aikatawa, akwai abin da suke ɓoye mata? Tunanin ma ta rasa wanne yakamata ta yi.
Har ta je titi, ba ta tsaya da tafiya ba, ba kuma ta daina tunani ba. Idonta ya sauka a kan mai sayar da gurji da ƙuli-ƙuli. Kawai ta ji ranta ya biya, duk da damuwar da take ciki. Ta miƙa masa ɗari biyu ya bata, ta samu abin hawa, ta gaya masa inda zai kai ta. Tun a napep ɗin, ta cinye gurjin tas. Tana zuwa gida aka fara kiraye-kirayen sallar magariba. Ta shiga gidan jikinta duk a sanyaye, sai dai da ta duba ɗakinsu, ba ta tarar da shi ba. Gabanta ya sake faɗuwa, ta fara tunanin ko an zo shi ma an tafi da shi, ba ta sani ba.
Ba ta gama yanke hukunci ba, ta ji cikinta na hautsunawa, ta faɗa banɗaki da gudu, ta din ga sheƙa amai. Sai da ta amayar da gurjin da ta ci kaf. Tun tana yinƙuri, abu na fitowa har komai ya daina fitowa. Da ƙyar ya tsaya, ta wanke gurin, ta duba kantar abin sabulu na banɗakin, ta ɗaukko abin gwajin ciki, ta yi fitsari ta tsoma a ciki. Layi biyu ya fito raɗa-raɗa. Jikinta ya hau rawa, wani irin kuka ya kufce mata.
Wani aman ne ya sake taso mata, ta din ga yinƙuri, amma babu abin da ya yi saura a cikin nata, sai kakari da yawu mai yauƙi da yake fita daga bakinta. Ji ta yi ya dafa ta, ya kunna famfon banɗakin, ya din ga taro ruwan a hannunsa, yana kai wa bakinta, tana kuskurewa.ya zuba ruwa ya wanke gurin. Ya kalli tsinken gwajin da ta yi, ya kama ta,ta tashi tsaye, jiri na kwasarta, fararen idanunta sun rine zuwa launin ja. Ya taimaka mata ta yi alawala.
Suka fito daga banɗakin, sai a zaune ta yi salla, saboda yadda iya aman da ta yi ta wahala. Duk sauran cikin da suka din ga zubewa ba ta amai, amma wannan ta ji abin babu sauƙi.
Bayan ta idar da sallar, ya kalle ta ya ce "Ina Habun?" Ta yi shiru tana kallonsa cikin tausayawa, ta ma rasa ta ina za ta faro masa bayanin.
"Yi magana"
Ta ɗan motsa bakinta, sai kuma ta yi shiru. Ya ƙara tsare ta da ido. Ta ɗan ja numfashi ta ce "Na je, wai kwana huɗu da suka wuce, an je da wata mota layin, duk an tafi da Buzayen layin, har da su babu wanda ya san inda aka kai su" sak ya yi yana bin ta da ido, tamkar bai gane me take nufi ba. Ta yi shiru tana tsoron kar abin da ta faɗa, ya ta'azzara ciwonsa.
"Ba sa nan kenan? Babu wanda ya san ina suka tafi?"
"Eh abin da aka ce mini kenan, kuma da alama kama su aka yi"
"Hsbunallahu wa ni'imal wakil" ya furta tare da sunkuyar da kansa ya yi shiru.
"Dan Allah Sayyid ka kwantar da hankalinka, ka ga baka da lafiya, ina son ka warke. In sha Allah, Allah yana tare da mu. Dan Allah kar ka ɗaga hankalinka. Sonake na nutsu na ga yadda zan yi na haɗa kuɗin da za a yi maka allurar nan, ko guda ɗaya ce"
Ya kalle ta cikin damuwa ya ce "A'a dan Allah kar ki damu, kar ki takura wa kan ki. Iya ɗawainiyar da na saka ki ma, ta isa. Mutuwa ce dai na sani, Allah ya sa na cika da imani, kuma ki yi mini addu'a, t... Bai rufe bakinsa ba, ta dunƙule hannunta ta dake shi a ƙirjinsa da ƙarfinta cikin kuka tamkar za ta fita daga hayyacinta.
"Ba ka tausayina, na san dole kowa zai mutu, amma me yasa kalaman ka ba za su zama na ƙarfafa gwiwa a gare ni ba, sai dai ka kashe mini zuciya da sanya mini tsoro da razani. Ga ɗanka a cikina, ga ka babu lafiya, nan a kore mu, ga shi 'yan uwanka ba a gan su ba, kuma ka saka ni a gaba, kana gaya mini wannan maganganun. Har ka manta ka ce kowannenmu ruhin ɗayanmu ne a jikinsa? Dama faɗa ka ke yi dan jin daɗin bakinka ba ka so na, ba ka tausayina" Yanayin yadda take kukan, ya sanya ya fahimci tsagwaron damuwa ce, ta rasa yadda za ta yi, shi ne ta yi amfani da wannan damar take hucewa. Ya yi shiru ya sunkuyar da kai. Ta ci gaba da kuka tana surutu, ganin ya yi mata banza ya sanya ta haɗa hannunta, ta hankaɗe shi daga gabanta ta tashi ta fita daga ɗakin. Ƙofar ɗakin ta fita, ta samu guri ta zauna ta yi shiru. Sauro ya baibayeta da cizo amma sam, ba ta jin zafin cizon sauron, sai tunanin mene ne mafita a wannan halin da suke ciki.
Ya fito daga ɗakin, kawai ya danƙi hannunta, ya mayar da ita cikin ɗakin. Ta fizge hannunta, ta koma gefe ta ja ta tsaya a tsaye. Sai ya ƙyale ta, ya tayar da sallar isha'i, ya idar ya yi kwanciyar sa. Ita ma sallar Isha'in ta yi, sai dai kuma amai ya saka ta a gaba, ta kasa sukuni. Da ta zauna sai amai, haka za ta tashi ta tafi banɗaki.
Ta duba cikin kayan da take dafa masa tea, ta samu kanumfari ta saka a bakinta. Ta yi zamanta a ƙasa ta ƙi hawa katifar ma, ta kwanta a ƙasa. Sai dai bacci ya gagari idonta, tunaninta kawai mene ne mafita? Ina za su koma? Yaya za ta yi da rashin lafiyar sa. Ta kalli inda yake, idonsa a lumshe. Gani ta yi kamar ba ya numfashi. Ta yi wata irin zabura, ta nufe shi ta kara hannunta a hancinsa. Ta ji ba ya numfashi, wata irin rikicewa ta yi za ta yi ihu, ya janyo ta ta faɗo kan katifar, ya zagaye ta da hannayensa, yana numfashi sama-sama, yanayin fitar numfashin nasa, ya sanya ta ƙara tsorata, saboda ba a daidai yake fita ba.
"Ka daina tsorata ni, kuma ka cika ni"
"A'a ki dain fushi"
"Ya zan yi na daina, bayan ba ka tausayina"
"Ina yi, na daina ba zan sake ba" daga haka bacci ya ɗauke shi. Amma Nana ta kasa bacci, ko baccin ya fara ɗaukar ta, sai ta buɗe ido a rikice, ta duba ta ga yana numfashi. Sai daf da Asuba, nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita.
Da safe Nana ta fita ta sayo ƙosai, ta dawo ta tarar ya yi wanka da kansa. Cikin damuwa ta ce "Sayyid me yasa ba ka bari na dawo na yi maka ba, kar ka wahala"