Buzu book 1 complete - Chapter 43
Buzu book 1 complete Chapter 43: Buzu book 1 complete Chapter 43. "Ni jariri ne?" Ya yi maganar cikin haki.
4,434 words
"Ni jariri ne?" Ya yi maganar cikin haki.
Idonta ya cika da hawaye ta ce "Ina jinka a jikina, fiye da jaririna"
Ya yi murmushi ya ce "Rayuwata Husnah" yadda ta ga Abincin ma ya gagara ci, abin ya ƙara razana ta, ita dama kasa ci ta yi. Saboda ƙamshin ƙosan ma amai ya saka ta. Saboda ta ga yana so ne sosai ya sanya ta je ta sayo masa.
Ta ba shi magungunansa ya sha, ya kwanta a kan katifa ta din ga danne hawayenta.
Ta ɗaukko ƙatuwar bagco, ta fara kwashe kayansa na wardrobe, ta zuba a ciki, ta ɗebo nata kayan ta zuba. Ta ɗaga kai suka yi ido huɗu tana kwashe kayan,ya yi sauri ya lumshe idanunsa. Ta share hawayenta ta ce "Sayyid, bari na je na ƙaro bagco, wannan ba za ta isa mu kwashe kayanmu ba"
"Ina zamu koma?"
"Zan laluba mana, in sha Allah ba zai gagara ba".
Cikin damuwa ya ce "Haƙƙina ne, ni yakamata na yi, ki yi haƙuri"
"Shugaba, ba na son Irin wannan maganar da ka ke yi wallahi. Bari na je na dawo" ta ɗauki kuɗi ta fice.
Ba ta zame ko ina ba, sai can gidan su.Ta sha mamaki ganin yadda gidan su ya ɗauki gyara, ko ina shar kamar ba gidan ba. Sai dai hakan ba shi ne a gaban ta ba, ta yi sallama ta shiga gidan. Cikin matsananciyar sa'a, ta tarar da Baba a gidan.
Mama ma tana nan, su na ta hira a tsakar gida.
Suka amsa mata sallama, Baba ya ce "Too Nana yau a gari? Ai na zata dangin uwa taki, ko Imrana sun tafi da ke?"
Nana ta yi murmushi ta ce "Baba su kai ni ina? Ina wuni Baba."
"Lafiya ƙalau" Ta kalli Mama ma ta gaishe ta, ta amsa cike da za zaƙuwar son jin abin da ya kawo Nana, ganin fuskarta ɗauke da alamun damuwa, duk da murmushin da take yi. Suwaiba ta fito daga ɗakinsu, jin muryar Nana, Nana ta kalle ta, ganin yadda wata jibgegiyar kaza baƙa ƙirin, da bataliyar 'ya'yanta aƙalla, sun kai ɗari, su ma baƙaƙe ƙirin, su na ta fitowa daga cikin ɗakin, su na biyo Suwaiba.
"Suwaiba kina nan dama, ina Jamila?" Ta kalli Nana, ba ta ce mata komai ba, ta nufi banɗaki ta shiga, kajin nan suka bi ta ciki suma.
Nana ta dawo da hankalinta kan Baba, sai dai ta kasa magana.
Ya ce "Nana ya aka yi ne?"
"Amm Baba dama, an sallame mu ne, daga gidan da Sayyid yake gadi"
Baba ya waro ido, Mama ta ce "Ikon Allah, laifin me ku ka yi?" Nana ta yi shiru. Baba ya ce "Magana ake yi miki fa.
Ta haɗiye wani yawu mai ɗaci ta ce "Ba mu yi laifin komai ba, ba shi da lafiya ne, ba ya iya aikin"
Baba ya ce "Subhanallah, zazzaɓi ko zawo?"
Kawai kuka ya zo wa Nana ta ce "Ciwon zuciya" Sai da Baba ya zabura, Mama ta ce "Too ciwon zuciya kuma? Ciwon zuciya ai na masu kuɗi ne, ina talaka ina ciwon zuciya?"
Baba ya ce "To yanzu yaya aka yi?"
"Baba na rasa yadda zan yi, yana kwance babu lafiya, allurar dubu ɗari biyu da hamsin za a din ga yi masa wata, ko a saka masa na'ura a zuciya ga shi kuma an sallame mu"
Baba ya ce "Danƙari to ni Nana ina na ga wannan uban kuɗin har haka? Ina 'yan uwansa?"
"Ba a san inda suke ba" ta yi maganar tana share hawayenta da gefen hijjabinta.
Baba ya yi shiru sannan ya ce "Ina 'yan uwansa suke a Nijar ɗin?"
"Baba ban sani ba, shi ma kansa bai san su ba"
"A'a wane irin shirmen banza ne wannan? Tsawon wata shidan bai kai ki, kin gano 'yan uwansa ba?" Nana ta yi shiru, saboda takaicin da tambayar tasa ta bata.
"To kin ga dai ɗakin Gaddafi, kayansa ne a ciki, kuma ya kulle abin sa, ya koma Ikko. Nan cikin gida kuma... Mama ta yi caraf ta ce "Ba zai ma yiwu ba, ya za a kawo mana gardi cikin gida, ga yara mata har da 'yan mata a cikin gida a ajiye, ba zai ma yiwu ba wallahi, ku nemi dai wata mafitar"
Baba ya ce "To faɗi wace mafitar za a nema?"
"A'a wannan kuma ku za ku nema, amma ba zai yiwu a kawo ƙato da ba muharraminmu ba, a yi mana jinya. Ciwon da ba warkewa ake yi ba, sai dai mutum ya gama wahala ya mutu, tun da dai babu kuɗin kula da shi."
Wani irin kuka da dana sani, ya ƙwacewa Nana. Baba ya ce "Ya isa haka, yanzu ki koma can gidan, ki ɗan roƙe su, su ɗan ƙara muku lokaci, kafin a san abin yi"
Nana ta yinƙura, Baba ya ci gaba da magana, har da gaya mata yadda za ta marairaicewa wanda suke yi wa aikin, da nuna musu tsagwaron talaucin da suke ciki, yadda za su ƙara ɗaga musu ƙafa. Tuni Nana ta daina gane abin da yake faɗa.
Haka ta koma gidan, ba tare da samo mafita ba. A ƙofar ɗakinsu, ta tarar da shi yana zaune, tun daga shigowar ta, tana iya hango yadda yake haki. Ta ƙarasa da sauri, ta ajiye ledar hannunta ta ce "Sayyid ka gaji da jira na ko? Sannu ya jikin naka?"
"Na samu sauƙi Alhamdillah" ta janyo ledar, ta fito da kankana fal, ta ce "Ka na son kankana, za ka iya sha?" Ya jinjina kai alamar eh. Ta din ga ɗauka tana saka masa a baki, Allah ya taimake ta, ya sha sosai.
Sai dai gaba ɗaya ta rasa a ina yakamata ta ajiye tunaninta, duk lissafi ya ƙwace mata.
Ummi ce ta faɗo mata a rai, amma ta kasa kiranta, saboda tana ganin Ummi mace ce, za ta iya ɗora mata ɗawainiya, amma kasancewar ba ta da wata mafita,ya sanya dole ta kira ta.
"Hello Nana"
"Na'am Ummi"
"Ya na ji muryarki a sanyaye? Ko an gamu ne?"
"A'a Ummi, an kore mu ne daga gidan da muke gadi" Ummi ta ware murya ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, saboda me?"
"Ba shi da lafiya ne? Ciwon zuciya yake fama, kuma gobe in Allah ya kaimu, aka bamu mu tashi, sabon mai gadi zai fara aiki. Na je na gaya wa Baba, amma ya ce na koma na ba wa masu gidan haƙuri su ƙara ɗaga mana ƙafa. Kuma sun yi mana ƙoƙari na san ba za su sake bamu dama ba".
Ummi ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, yi haƙuri Nana, ki kwantar da hankalinki, ni da kin bi ta tawa ma, ba za ki gaya wa Baba ba, dan babu abin da zai yi miki. Yanzu za a samu kuɗi a hannun ki? A duba muku ko ɗaki ɗaya ne a nan unguwar, ku kama haya, kafin a samu yadda za a yi"
Wata irin ajiyar zuciya Nana ta yi ta ce "Eh, idan aka samu mai arha, zamu iya kamawa in sha Allah"
"To shikenan, ki saurareni zuwa da safe in sha Allah, a daren nan zan bayar da cigiya, na san za a samu, mu nan Kurna ɗaki ba ya wahala"
Cikin farin ciki ta ce "Allah ya saka da alkhairi Ummi, na gode sosai da sosai " ba ta tsaya katse wayar ba, cikin farin ciki ta koma ɗakin su da sauri ta ce "Sayyid, Ummi za ta saka a sama mana ɗaki, sai mu kama mu koma. Dama unguwar fuskar jama'a ce, zan iya fara sana'a ma na tara kuɗin allurar ka" Ya din ga bin ƙwayar idon Nana da kallo, cikin tausayawa da karaya.
A saɓule ta ce "Ya na ga ba ka murna?"
"Ina yi rayuwata, ina jin tausayinki ne, sab...
"Za ka fara ko?"
Ya girgiza kai alamar a'a. Haka ta tattare musu kayan su. Ƙarfe tara na dare, Ummi ta kira ta. Ta ɗaga cikin murna "Nana an samu gida na dubu ɗari da hamsin shekara, sai kuma ɗaki, amma shi wata shida dubu talatin, kuma da mutane a gidan"
Nana ta ɗan yi shiru ta ce "A bamu na wata shidan tukuna, kar na ƙarar kuɗin hannuna. Kin ga zamu din ga komawa ganin likita, ga harkar abinci da magani, ko kuwa ya ki ka ce?"
Ummi ta ce "Nima na yi tunanin hakan, turo kuɗin a cikin opay ɗina, na tura musu"
"To Ummi, na gode sosai bari na turo miki" Nana jiki na rawa ta tura wa Ummi kuɗin, ta je ta samu Sayyid tana gaya masa.
"Sannu Allah ya yi miki albarka " ya furta jiki a sanyaye.
"Amin shugaba"
"Ina jin yunwa" cikin murna ta ce "Za ka ci abinci? Na dafa maka? Me za ka ci?"
"Ke ce ba ki ci abinci ba, nake jin yunwa" ta tura baki ta ce "Ba na jin yunwa, idan na ci amai zan yi"
Ya sake cewa "Rashin lafiyata za ta ƙaru, ki ci kaɗan"
"Dan Allah ka yi haƙuri. Kar ciwon nan ya ƙaru, na sha shayi ai idan na ci amai zan yi" ta tsallake shi ta kwanta.
"Ki ci ko kaɗan ne"
Cikin shagwaɓa ta ce "A'a na ƙoshi"
"Allah ya sa wannan karon babyn ya zauna"
"Amin, ya kuma baka lafiya ingantacciya"
"Amin"
Nana ta ce "Wallahi sai daɗi nake ji, da muka samu hayar ɗakin nan, ka ga ma zauna, na yi wata sana'ar ma, mu tara kuɗin yi maka allura".
Ya kwanta a jikinta ya ce "Ba sai kin yi haka ba, ba na son duk wani abu da zai sanya ki sha wahala, gaba ɗaya ji nake na zame miki wani nauyi".
"Ni ka daina faɗa ba na so."
"Tom"
"Rayuwata"
"Na'am Shugaba Sayyid"
"Ina mamakin inda su Habu suka tafi suka bar mu, na san ko ba komai da kin sami rangwamen wata ɗawainiyar, amma da yardar Allah idan na samu sauƙi, zan nemi abin...
"Sai da safe" ta kaste shi.
Ya ɗan yi murmushi ya ce "Ai na daina, kar ki yi fushi"
Ta ce "Ai ba fushi ba, kuka ka ke son saka ni"
"To na daina, kar ki yi fushi, kuma kar ki yi kuka, nima zan yi" yayi maganar yana yawo da hannunsa a jikinta.
Sakin jiki Nana ta yi, saboda yadda ta yi kewarsa, sai dai a wannan karon ma, ya ji shi ba daidai ba, ya kasa komai.
Yana jin yadda Nana ta yi bacci, amma shi bacci ya ƙauracewa idanunsa. Tunani daban-daban ya cunkushe masa zuciya. Ji yake da yana da gurin zuwa, da ya tafi ya bar ta, saboda wahalar da take ta yi da shi. Sai dai ko alama bai ji zai iya aikata hakan ba, kamar yadda yake faɗa, a cikin jikinsa yake jin ta. Ba zai iya matsawa ko ina daga gare ta ba. Ya kumna fitilar waya, ya haska ta ya kalli yadda take bacci cikin aminci, ba tare da damuwa ba. Fuskarta ta faɗa. Wani irin tausayinta yake ji, yadda yake ganin ya zame mata alaƙaƙai. Ya jima a zaune, kafin ya kwanta bacci. Shi ma sai da ya haɗa fululluka, ya tada bayansa da shi, kamar yadda likita ya nuna musu, sannan ya samu bacci ya ɗauke shi.
Fitsari ya tashi Nana an fara kiraye-kirayen sallar Asuba, sai da ta fara dubawa, ta ga yana numfashi, sannan ta shiga banɗaki ta yi alwala. Ta fito ta ɗauki ruwa leda biyu ta shanye, wani irin daɗi ruwan ya yi mata, dama ga cikinta babu abinci, sai ta ji ta ƙoshi. Ta tayar da sallar Nafila, ta yi ruku'u, ta fara yinƙurin amai, ta hanci ta baki.
Kakarinta ne ya tashe shi daga bacci, ya yinƙura ya bi bayan ta. A bakin ƙofa ya tsaya cikin tausayawa. Sannu kawai yake iya mata, abin duniya duk ya dame shi.
Tare suka yi sallar asuba, ta kwanta saboda yadda jikinta duk ya saki.
"Asmy" ya kira sunanta yana shafa bayanta.
"Me za ki ci?" Ta girgiza masa kai alamar babu.
"Mu je Asibiti to"
"A'a Sayyid, zan ware in sha Allah, bari na yi bacci" Abin da yake bata mamaki, a kwanakin nan gaba ɗaya ta daina ganin Ƙaisar, ya daina zuwar mata, ko a bacci ko a zahiri.
Ta ji daɗin baccin da ta yi, amma yanayin jikinta, babu daɗi zazzaɓi ne yake son kama ta.
A hankali ta ji ana matsa tafukan hannayenta. Ta buɗe idonta, suka yi ido huɗu yana ta matsa mata hannu a hankali.
"Sayyid ba ka da lafiya ka na wahalar da kan ka"
"Ki zo ki ci Abinci, kin ga za ki ci ko?" Ya yi maganar yana nuna mata buredi, da soyayyen ƙwai da ya fita ya sayo mata. Ta yi zuru da ido tana kallonsa, har yanzu yana haki idan yana magana. Ya fara ƙoƙarin ɗago ta. Ta yinƙura ta tashi, ya zubo mata shayin da ya dafa.
Ta kafa kai duk da zafin shayin nan, amma ya yi mata daɗi, ta buɗe maƙogwaro ta din ga sha. Ta cakali buredi da ƙwan kaɗan, shi ma dan kar ya ji babu daɗi, ta ci. Ta tashi ta ci gaba da tattare musu kayan su. Har cikin zuciyarsa yake jin zafin barin gidan da za su yi.
Ɗan abin da ta ci, ko mintuna talatin ba a yi ba, shi ma sai da ta amayar. Cikin matsananciyar damuwa yake kallon Nana, idanunsa suka yi jawur, ƙirjinsa ɗauke da magana, amma ya gaza furta komai, sai zafi da raɗaɗi da zuciyarsa take yi.
Ayshercool 08081012143 50
Ji suka yi an buɗe ƙofar gate, an yi sallama. Ya nufi bakin ƙofar su, ya leƙa ta taga, ya juyo ya kalli Nana ya ce "Yayarki ce"
Ta waro ido ta ce "Wacce?"
Ta taso tana leƙawa ta ga Ummi, wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta. Ta ɗaga labule tana wani irin murmushi mai cike da nuna zallar farin ciki.
Nana ta ce "Ƙaraso baƙuwar Safe"
"To na koma ne?"
"A'a ni na isa, shigo"
Ummi na shiga, ta tarar da Sayyid, ya ɗora mayafin rawaninsa a kansa.
Ummi ta ce "Sannu ina kwana"
"Lafiya kalau Alhamdillah"
"Ya jiki kuma, ta ce ba ka ji daɗi ba"
"A'a na ji sauƙi Alhamdillah"
"Allah ya ƙara afuwa" ya amsa da Amin.
Ta mayar da idonta kan Nana ta ce "Dama zuwa na yi, na gani idan ba ki haɗa kaya ba, na taya ki, na biya mai 'yar ƙurƙura za su zo, tare da Nasiru a kwashe kayan. Ai dama Hajiyar da ki ke yi wa aiki ce, ta saya muku ko?" Nana jinjina mata kai.
"To duk a kwashe su, na je na ga ɗakin, babu laifi, babba ne da banɗaki a ciki. Sai kuma akwai mutane biyu a gidan, duk masu aure ne."
Nana ta ce "Ni dai tun da mun samu gurin zama, Alhamdillah Allah ya saka da alkhairi Ummi"
Sayyid ya ce "Ma vie, bari na jira ku a waje"
Ummi ta ce "Yi haƙuri. Na zo na takura muku ko?"
Ya ce "A'a mun gode sosai da sosai da kulawa". Ya fita waje ya samu guri ya zauna.
Ummi ta ce "Yau ma mijinki ya yi magana Nana"
Nana ta yi dariya ta ce "Ai dama yana yi fa"
"Gaskiya yana jin jiki Nana, na ji yana haki, ina 'yan uwan nasa ne?"
Nana da kamar ta yi shiru, sai dai ta warware wa Ummi komai da komai, duk da ta ɓoye mata wasu abubuwan. Jiki a sanyaye Ummi take maimaita "Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Nana Baba bai yi miki adalci ba, duk da mahaifinmu ne. Yanzu shikenan ba a san inda wannan 'yan uwan nasa suke ba, bayan taɓin hankali ba ma shi da asali, bai san daga ina yake ba?"
"Ki yi a hankali kar ya ji, ba zai ji daɗi ba" ta yi maganar idonta na cika da hawaye.
Ummi ta jinjina kai ta ce "Ki yi haƙuri Nana, komai tsanani akwai sauƙi in sha Allah, ki daina kuka"
"Ummi ba kukan aurena da Sayyid nake yi ba, tausaya masa nake yi. Ga larura ban sani ba ma, ko guduwa suka yi suka bar shi. Amma dai na kasa yadda da hakan, da za su gudu su bar shi, da ba su tsaya masa zuwa yanzu ba. Tun da muka yi aure, musamman Habu shi ne yake ɗawainiya da mu. In sha Allah zan kula da shi, iya yi na"
"Allah sarki Nana, kaf cikinmu babu mai ƙarfin tawakallinki da kuma haƙurin ki, Ubangiji Allah ya ƙarfafe ki, kar ki sare ba ki san a inda Allah zai ji ƙan ki ba. Idan ki ka lissafa yadda aurenku ya kasance, ke kin san akwai hikimar Ubangiji a cikin hakan, ki yi haƙuri."
Ta yi murmushi ta ce "Ba wani abu in sha Allah, na gode sosai da sosai Ummi, da yadda ki ke ɗawainiya da ni, ba tare da kin gaza ba"
"Matsa ko na mare ki, wace ɗawainiyar na yi miki?. Matsa ni" Nana ta matsa tana murmushi.
Yana zaune yana tasbihi da yatsunsa, Siyama ta fito daga cikin gidansu, ta nufi gurin ajiye motoci, sam ba ta lura da shi ba, sai da ta fito da mota, ta gan shi a zaune, babu rawani sai mayafin da ya ɗora a kansa. Tun da suka yi ido huɗu, gabanta ya faɗi. Sai dai ta dake, ta ɗaukko wayar ta tana yi masa hoto, ba tare da ya sani ba.
Ta ƙaraso da motar, ta fara horn, ko ɗaga kai bai yi ba, balle ta sanya ran zai buɗe mata gate ɗin. Kawai ta rufe motar ta tunkare shi.
"Amm sannu, ina ta horn zan fita ne" ta yi maganar tana ƙara yaba kyawun da Allah ya yi masa.
"Magana fa nake yi" Bai kalle ta ba, ya tashi ya nufi gate ɗin. Ummi ta ce "Nana wai me ki ke yi a jikin tagar nan?" Nana ba ta amsa mata ba, ta ɗora mayafi a kan rigarta ta fita.
"Me yasa za ki saka shi buɗe gate, ina tunanin aikinmu da ku ya ƙare, tun da yau za mu bar gidan nan, kuma ba cikakkiyar lafiya ce da shi ba."
"Na kasa da ke ne? Tun da ba ku bar gidan ba, dole ya yi aiki, ko da aka ba ki kuɗi kin rage wani abu, saboda ba ku yi mana aiki ba?"
"Ban rage ba kuma ba zan rage ba. A yau za mu bar gidan nan, idan ki ka ƙetare layi za ki sha mamaki."
"Me za ki yi?"
Ya nufo Nana, da jikinta ya fara tsuma ya ce "Ki yi haƙuri mu rabu lafiya"
"Ka rabu da ni Sayyid" Murmushi ya yi,ya saka hannu ya riƙe Nana, da ranta gaba ɗaya ya ɓaci, har take tsuma.
Ummi ta fito tana tambayar ko lafiya.
Siyama ta ce "Ni kuma zan ga ƙaryar hauka da rashin hankali, ku zauna a ƙarƙshinmu, ku ci arzikinmu, kuma ki tsaya za ki yi mini rashin kunya?"
Ummi ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri baiwar Allah, kin san zuciya. Ki yi haƙuri dan Allah ba ta kyauta ba" Nana tuni ta fita daga hayyacinta a hannun Sayyid, jikinta ya saki idanunta a lumshe sai hawaye da yake fita ta gefen idonta. Ummi ta tafi lallaɓa Siyama, Sayyid ya kai Nana ɗaki ya kwantar da ita. Jikinta ne ya fara karkarwa tamkar ana girgizata. Ummi ta dawo ɗakin, ta ga yadda ya rungume Nana a jikinsa, cikin damuwa take kallon Nana, tana mamakin dama haryanzu ba ta daina iskoki ba, ta ga wasu idan an yi musu aure abin yana lafawa, da ta ji Nana shiru bayan auren, ta ɗauka ta daina.
Cikin damuwa ta ce masa "Dama tana yin haka haryanzu?"
Ya ce "Ba kullum ba, sai ta yi fushi"
Sosai Nana take kuka tana karkarwa dama Ummi matsoraciya ce, ko kafin ta yi aure, idan Nana tana yi tsoro take ji. Ya kai bakinsa kunnenta murya ƙasa-ƙasa ya ce "Ki yi addu'a Husnah, ko ba za ta fito a bakinki ba, ki yi a zuciyar ki, ki daina kuka, ki yi haƙuri. Yi addu'a sosai ki daina kuka" A sama kamar cikin mafarki take jiyo muryarsa kawai, amma ba ta ganinsa, sai ita kaɗai a cikin sahara. Ta dage iya ƙarfinta tana Addu'a cikin ɗaga murya, amma a zahiri ba ta iya furtawa a kan harshenta, sai dai a cikin zuciyarta kawai. Tana zaune a cikin saharar, sai ga Yusra ta nufo ta. Nana ta yi shiru tana kallon ta.
"Ƙawata"
Nana ta ce "Yusra ko Haula?"
"Haular dai. Ashe tashi za ku yi kuma?"
"Eh, ina Yusra, ina fatan ba kya cutar da ita?"
Ta yi murmushi ta ce "Bayan kin gaya mata abubuwan da za ta hana ni sukuni, zama take yi da alwala, ta daina tsorata ko na tsorata ta, hankalina ma dai ba a kanta yake ba sosai, ina can fafutukar neman soyayyar Ƙaisar"
Nana ta yi shiru tana mamakin, yaya aka yi ita, ko ta yi alwalar ta yi addu'a, Ƙaisar ba ya fasa cutar da ita.
"Da kin sani kin bar ni da matar nan, na ci gaba da wahalar da ita, yadda babarta za ta ƙara ɗanɗanar takaici, ba ta da mutunci shi yasa ma aka sakar mata 'yar ta"
Nana ta ce "Ai ke ki ka saka a ka sakar mata 'yar, kuma Yusra ba bu wani abu da ta yi miki na laifi. Kuma ita kanta Hajiyar, tana da gaskiya mijina ba shi da lafiya ba ta yi ba dai-dai ba".
"Ai shikenan, yanzu haka za ki tafi na daina jin ƙamshin girkinki mai daɗi"
"Haula, dan Allah ko ke kin san waye Sayyid, daga ina kuma yake?"
Haula ta waro ido ta ce "Taɓ, so ki ke dattijo ya kashe ni? Ko kuma ya azabtar da rayuwata. Yo bai bar ɗansa ba balle ni. Babu ruwana"
Nana ta marairaice ta ce "Dan Allah ki gaya mini, babu abin da zai yi miki "
"A'a ba ruwana. Ai Ƙaisar ya gaya miki, shigen Asirin da aka yi wa Alhaji Fatuhu, aka yi wa mijinki, amma ke ni babu ruwana a wannan lamarin naku"
Nana ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Da gaske, abin da Ƙaisar ya nuna mini a mafarki ya faru? Alhaji Zailani ya yi wa Alhaji Fatuhu Asiri da ɗan Shukura?"
"Sosai da gaske ne, ba ƙarya ya yi miki ba. Da zai ci gaba da buɗe miki ido, ki cigaba da ganin ɓarnar da bil'adama ku ke yi wa junanku, sai kin haukace. Alhaji Zailani yana gadon Asibitin, da aka ɗauke wa kishiyar Yusra ɗa"
"Wace Yusran?"
"Ƙawar ki mana, ita ce matar Sagir ta farko. Kin ga tafiyata kar na yi laifi, garin ɓare-ɓare na faɗi abin da za a hukunta ni" Nana ta zabura ta damƙi hannun Yusra da sauri, domin sake tambayar ta. Amma ta ji jikinta ya yi sanyi ƙalau, ta buɗe idonta, ta kalli Sayyid, da ta riƙe masa hannu gam.
Ta yinƙura ta tashi zaune, yanayin yadda ta ji jikinta, ta gane abin da ya faru.
Ummi ta ce "Nana kin tashi? Ki wanke fuskar ki, masu ƙurƙurar sun kusa ƙarasowa.Ta tashi ta wanko fuskarta.
Tana fitowa kuwa, masu motar suka ƙaraso.
Aka kwashe kayan su Nana tsaf, sosai Nana take jin kewar barin ɗakin nasu. Ummi ta raka ta, suka shiga gurin Hajiy Halima, suka yi mata sallama.
Tar Nana take jin hirar da suka yi da Haula a bacci, tana dawo mata kanta, ba tare da ta manta komai daga hirar ta su ba. Sai dai ta ƙi yarda zuciyarta ta gazagata komai a cikin maganganun Haula, ta dage wa zuciyarta da cewa shirmen mafarki ne, saboda tana yawan tunanin Yusra da take yi. Duk da tana jin kamar wani abu makamancin haka ya faru, wani abu mai kama da Alhaji Zailani ya yi wa Alhaji Fatuhu asiri, da kuma maganar jariri, amma ta kasa tuna komai.
Ummi ta fita waje, domin tabattar da an shirya komai, a kan motar.
Nana ta tarar da Sayyid a cikin ɗakin, yana ƙare wa ɗakin kallo.
"Shugabana" ya waiwayo a hankali yana kallon ta.
"An tafi samo abin hawa, za mu tafi, na ga ka zo ka tsaya a nan"
"Nana"
"Na'am Sayyid"
"Ina kewar rayuwar da muka yi a ɗakin nan tare da ni da ke, ban san ya zan misalta miki ba. Ga ki dai a tare da ni, amma ina kewar ɗakin sosai. Sai na ji kamar ba zamu sake Rayuwa mai daɗin da muka yi a cikin sa ba"
Ta girgiza kai ta ce "In sha Allah, sai mun yi wadda ta fita komai da komai, da yardar Ubangijin talikai. Taho mu tafi" Da ƙyar ta riƙo hannunsa, suka fito idanunsa jawur.
A adaidaita sahu suka tafi, da shi da ita da Ummi, sai dai ya ƙura wa gidan ido, tamkar ya ce a tsaya ya koma. Nana ta riƙo hannunsa cikin nata ta ce "Mu kyautatawa Allah zato, ina da yaƙinin rayuwar da zamu ci gaba, ta fi wadda ka ke kewa daɗi"
"Ina fatan haka Rayuwata"
Ummi ji ta yi tamkar ta yi tsuntsuwa, ta fita, ba ta san lokacin da Nana ta fitsare haka ba. Ta yi ta biye masa su na abu a gaban mutane, idan shi ba bahaushe ba ne, ai ita bahaushiya ce.
Sun ɗan yi doguwar tafiya, daga Tudun yola, zuwa Kurna.
Babban abin da ya soki zuciyar Sayyid, bai wuce ganin gidan akwai maza ba, duk da masu aure ne, amma har cikin zuciyarsa hakan bai yi masa tsari ba. Amma babu yadda ya iya, tun da ba shi da wata mafitar. Ɗakin nasu bai kai wanda suka baro girma ba. Cif ya ɗauke kayan su, sai dai babu sauran space ɗin kirki a ɗakin. Ga zafi saboda wata 'yar ƙaramar taga ce a ɗakin, kamar ɗakin tattabara.
Abin takaicin bai wuce yadda yaran layin suka cika gidan ba, saboda ganin ana sauke kaya ana shiga da su cikin gidan.
Sai da Ummi ta din ga korar yara, suka saka Sayyid a gaba da kallo, saboda ya yi shigar buzaye da rawani. Abin takaici har matan layin, wasu suka din ga leƙowa, masu son ganin ƙwal uwar daka kuwa, gidan suka din ga shigowa, da sunan sun zo gurin sauran matan da suke gidan, amma a zahiri, zuwa suka yi su ga suwaye kuma suka tare a gidan.
Ummi tana tare da su Nana, har aka gama shirya ɗakin tsaf, duk da Nana su na da sauran kayan Abinci, amma ta yi waya aka kawo mata kayan abinci daga gidanta, ta girka wa Nana. Kasancewar Nana ba ita ta dafa ba, sai ta samu ta ci sosai.