Buzu book 1 complete - Chapter 45
Buzu book 1 complete Chapter 45: Buzu book 1 complete Chapter 45. Ta ci gaba da jan ƙafafuwanta, jiki babu ƙwari ta nufi ɗakin da Hajiya Amina ta kwatanta…
1,986 words
Ta ci gaba da jan ƙafafuwanta, jiki babu ƙwari ta nufi ɗakin da Hajiya Amina ta kwatanta mata. Sai da ta yi knocking sannan ta tura ƙofar ta shiga. Fadila na zaune a gefen gadon kusa da Alhaji Fatuhu, ga cikinta ya yi wani irin girma, tamkar tana yinƙurawa ɗa zai faɗo. Sai dai gaban Shukura ya yi mummunar faɗuwa, ganin yadda Alhaji Fatuhu ya koma. Dogon mutum mai jiki, mai hasken fata, ya koma baƙi ƙirin ya yi wata irin mahaukaciyar rama, jikinsa tamkar fata kawai aka yafa wa ƙashi. Ta ji kanta ya sara, wani irin abu ya soki zuciyarta. Wani irin wari ɗakin yake yi, tamkar na mushe, ga shi dai babu ƙazanta a jikinsa, ga ɗakin a share a goge yana ƙamshin turaren wuta, amma ita warin mushe ta din ga ji, da ba ta san daga ina yake fitowa ba
Fadila tana yi mata sannu da zuwa, amma ba ta kula ba, ta ƙarasa kan gadon, ta zaune. Yana daga zaune, ya kalle ta ya yi murmushi tamkar mai raɗa ya ce "Shukura"
"Daddy, haka jikinka ya koma?" Ta yi maganar cikin matsanancin tashin hankali, da tuni hawaye ya wanke mata fuska.
Ya ce "Alhamdillah, ai na ji sauƙi ko Maman Muhsin?" Fadila ta jinjina kai hawaye na zubo wa daga idonta ita ma.
"An ce mini kin haihu ɗan ya rasu, ban zo na duba ki ba, na haɗu da wannan larurar"
Cikin kuka ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri ban zo na duba ka a kan lokaci ba. Ban zaci abin ya kai har haka ba"
Ya yi murmushi yana jinjina kai, aka turo ƙofar ɗakin,gaba ɗaya suka waiwaya Doctor Sharif ne ya shigo, tare da wata nurse.
Yana ganin Shukura ya yi murmushi ya ce "Hajjaju kwana da yawa, ni da na yi zaton zuwa yanzu ma, kin dawo mana awo? Ya gida ya mai gidan?"
"Lafiya kalau" daga haka ta ja baki ta tsuke. Sai da ya sha jinin jikinsa, da irin amsawar da ta yi masa.
Ya kalli Fadila ya ce "Uwar biyu, ya mai jikin?"
Fadila ta ce "Alhamdillah mun gode Allah"
"Ma sha Allah. Na ce ki je a duba ki, idan inducing ɗin ki za a yi, idan ma tiyata ya kamata a yi miki to. Amma kin ƙi"
"Kar ki soma yarda, a kashe miki ɗa, gara ki je wani Asibitin" tsit suka yi baki ɗaya, suka waiwayo su na kallon ta.
Jikinsa ne ya yi wani irin sanyi, wani irin tsoro ya ziyarci zuciyarsa. Cikin damuwa ya ce "A kashe mata ɗa kuma Shukura"
"Nawa ba a hannunku ya rasu ba?"
"Kuma ai ba kya ce za a kashe mata ɗa ba, nakin ma, Allah ne ya kawo ajalinsa"
Shukura ta ce "Ba zan dai sake zuwa Asibitin nan na haihu ba. Daddy Allah ya ƙara afuwa. Maman Muhsin sai anjima Allah ya raba lafiya"
Fadila ta ce "Amin, mun gode sosai da sosai Shukura, ki gaida gida. Mummy ma an ce ta tafi Umara ko?"
"Eh wallahi. Allah ya raba lafiya" har Shukura ta fice, jikin Doctor Sharif tsuma yake yi, amma ya dake tare da ɓoye hakan.
*****
Jamila na tsaka da bacci, ta ji ana tashin ta. Ta buɗe idonta ta ga Hajiya Sa'a a tsaye amma fitilar ɗakin a kashe.
"Hajiya lafiya kuwa?"
"Lafiya ƙalau, tashi ki saka wannan rigar mu tafi"
Cikin mamaki ta ce "Ina?"
"Ki saka sai mu je ki gani. Ki cire komai na jikinki ki saka ta"
Bakinta fal tambayoyi, amma babu damar yi. A duhun ta karɓi rigar ta saka, kanta babu ko ɗan kwali, Hajiya Sa'a ta kama hannunta suka fice. Sun yi doguwar tafiya sosai, su na ratsa guri-guri, sai dai duk a cikin duhu ne. Jamila ba ta san ina suke bi ba, da kuma inda za su je ba.
Aka buɗe musu wata ƙofa suka shiga, ta ja ta tsaya. Yanayin gurin babba ne yana da girma sosai. Sai dai da mutane a ciki, galibinsu maza ne. An kunna kyandira a gurin. A haka ta lura kayan jikinsu jajaye ne da baƙaƙe. Sun kewaye wata ƙatuwar tukunya a tsakiyar ɗakin, fuskokin su a rurrufe. Hajiya Sa'a ta ja ta suka samu guri suka zauna. Wani irin gurnani mutanen ɗakin suke yi, su na wasu irin maganganun da ba ta fahimtar abin da suke faɗa. Da alama ɗaya daga cikin su ne yake jagorantar abin da suke yi, mai kama da ibadar bautar wani abin.
"Mun yi baƙuwa a gurin nan" cewar mutumin da yake zagaye tukunyar, yana faɗar abin da yake faɗa suna yi masa amshi.
Hajiya Sa'a ta ce "Eh, baƙuwar mu ce, da na sanar da zuwan ta wannan bugiren"
"Ita ce aka kasa samo jinin 'yar uwatta, uwar gijiyar uban duƙusa?"
"Eh ita ce"
"Mu na yi mata maraba da zuwa ƙungiya, za ta samu abin da take so. Idan duniya ce kun same ta kun gama. Babu wani abu da zai gagare ku. Can kuma wannan matsalar ku ce, ku neme ta ku rasa nan, ko ku nemi nan can kuma sai abin da hali ya yi. Mu na yi wa wanda ba su bayar da sadaukarwar su ta wannan shekarar ba, idan lokaci ya yi za su ga abin da ba su zata ba. Wanda suka riga su ka yi, mu na taya su murna da ƙara tabattar musu sun samu duniya, su taka wanda suka so, babu mai ganin bayansu, masu neman ɗaukaka za su samu, masu neman ilimi za su dace. Masu neman kuɗi sun samu, haka ma masu neman madafun iko. Mu na sake jaddada muku dokokin ƙungiyarmu, babu fita bayan an shiga. Babu tona asirin ƙungiya. Duk wanda ƙungiya ta buƙata za ka bayar, babu jayayya babu musu. Akasin haka jininka ya zama mallakin dodon ƙungiya".
"Mun yarda, mun yi mubayi'a, mun bi dodon ƙungiya, mun bi sarkin ƙungiya, ranmu da jukkunanmu fansa ne a gare ku, muna son duniya, mu na son tabattuwar duniyarmu" suka haɗa baki su na maimaitawa. Jamila bin su kawai take yi da kallo, jin abin take yi tamkar a mafarki, kuma kamar wani film. Wani irin sauti mara daɗin ji ya karaɗe ilahirin gurin. Miƙewa mutanen suka yi, suka risuna tamkar za su yi sujuda. Su na ci gaba da karanto wasu irin abubuwa. Wani abu mai kama da guguwa, ya kashe kyanduran gurin. Ƙarar sautin abin, da surutun da suke yi ya karaɗe gurin, baka iya gane komai. Can bayan wani lokaci kuma, sai gurin ya yi tsit hasken kyanduran ya dawo. Suka ɓarke da wata irin shewa. Hasken ya haska gurin sosai da sosai, sai dai ba ta iya gane suwaye a gurin, kuma ta nemi Hajiya Sa'a ta rasa a gurin. Sai daga baya ta fahimci ashe akwai mata a gurin ba wai maza ne kawai ba. Aka din ga raba wani abu a cikin kofi, aka zo kanta a ka ba ta, ta karɓa ta sinsuna ta ji wani irin ƙarni mara daɗin ji ya daki hancin ta. Ta kawar da kanta yawu na taruwa a cikin bakinta. Ji ta yi an damƙi hannunta, an nufi wata ƙofa da ita. Tana ta ƙoƙarin gane waye, amma abu ya faskara ta kasa gane waye. Su na shiga ƙofar ta ga duhu ya ƙara gaurayewa, amma ta ji sanyin AC na ratsa ta. Ta ji an shaƙe mata wuya, an toshe mata hanci, ta fara kiciniyar ƙwacewa amma abu ya gagara, ta buɗe bakinta za ta yi numfashi ta ji an zuba mata wani abu, da ya fi ruwa kauri kaɗan, mara ɗanɗano. Tana gama haɗiyewa ta ji wannan ƙarnin ya mamaye mata hancinta da bakinta. Take ta yi yinƙuri ta fara amai, sai dai ba ta gama aman ba, ta ji jiri ya kwashe ta.
****
Bangaren Nana kuwa, aka shiga kwana biyu, ba tare da ko ruwa Sayyid ya saka a cikin sa ba. Balle Abinci, ba wanka babu salla balle ya sha magungunan sa na matsalar zuciya. Ga shi kuma bai daina haki ba. Idanunsa sun yi jawur tamkar gauta. Laɓɓansa sun yi wata irin bushewa. Ga gashin nan butsu-butsu a hargitse babu gyara, ya koma mahaukaci sosai da sosai. Ga shi da ta tunkaro inda yake, ko ya hankaɗe ta, ko ya shaƙe ta. Ko kallonsa ta fiye yi, sai ya hau huci yana zabure-zabure tamkar zai kai mata duka. Ta yi iya ƙoƙarin ta, babu wanda yake shigar mata ɗaki. Ga laulayin ciki ya saka ta a gaba, ita kanta lallaɓawa kawai take yi. Ba ta yi da yawa ba a rana ta yi amai sau goma, tun cikin dare take farawa. Tun tana sha'awar ta ci wani abu har ta daina. Daga shayi sai ruwa, ko juice ɗin lemon tsami. Idan ta ga jikinta ya bushe ne, sai ta aika a sayo mata ruwan gishiri ta haɗa ta sha. Ga ranar da za su koma follow up, na Asibiti ya yi amma yana cikin wannan yanayin, a dole ta rabu da shi, ta ci gaba da addu'a. Sai dai yau gaba ɗaya Jamila ce take ta kaiwa tana komowa a ranta. Sannan ƙasan zuciyarta kuma haka kurum, take tunanin abin da ya sanya ta daina ganin Ƙaisar kwana biyu.
"Allah ya sa dai lafiya" ta furta a fili, sai kuma ta yi saroro bayan wata zuciyar ta ce "Ina ruwan ki da lafiya ko ma babu, abin da ki ke neman maraba da shi?"
Sayyid take kallo, zuciyarta na raya mata, ta matsa kusa da shi, ta jarraba yi masa karatu, amma tsoro ya kama ta, saboda gudun kar ya cutar da ita, ga ƙaramin ciki a jikinta, da take ta lallaɓawa tana fatan Allah ya bar mata.
****
A hankali Jamila ta buɗe idonta, ta ganta a ɗakin da suka sauka da Hajiya Sa'a. Ta yinƙura za ta yaye bargon da take lulluɓe da shi, amma ta ji jikinta na yi mata wani irin ciwo mai tsanani. Ga wani irin raɗaɗi da azaba da ta ji a ƙasanta zuwa gurin bayan gidanta, tamkar an sanya abu mai kaifi an haɗe guraren biyu.
Ta yaye bargon ta ganta a tsirara, jikinta duk an yi mata zane da jini, ta ɗaga ƙafarta ɗaya tana ƙoƙarin tashi zaune, amma ta ji ba za ta iya ba, saboda azabar raɗaɗi da zafin da take ji.
"Wayyo Allah Mama, na shiga uku mene ne ya same ni haka? Nana, Suwaiba dan Allah ku taimake ni na shiga uku"
Hajiya Sa'a ce ta shigo da sauri, tana faɗin "Daughter kin tashi?"
"Mene ne ya same ni, me ya faru da ni?"
"Yi shiru, ki kwantar da hankalinki, zan yi miki bayani. Amma ki daina wannan kukan. Taso mu je, ki yi wanka ki gasa jikin ki, ki karya tukuna. Cikin kuka ta ce "Ba na so, ki yi mini bayanin mene ne ya same ni? Ina ne nan? Me yasa nake jin wannan zafin, kuma me ye wannan rubutun a jikina?"
Hajiya Sa'a ta ce "Ke ba na son hauka. A lokacin da Safiyya ta haɗa ni da ke. Nake kashe miki kuɗaɗe a banza zan yi miki ne, ba tare da na amfani komai a tattare da ke ba? Kin gaza kawo mini jinin 'yar uwakki, kin ƙi shiga cikin harkar mata yadda nake so, kuma ga burinki na son abin Duniya, dan haka tallafawa burinki kawai na yi cicciɓa ki"
Hawaye na kwarara daga idonta cikin sanyin murya ta ce "Yanzu me ya same ni?"
"Taronmu na ƙungiya ki ka zo, kuma na nema miki sassauci ta hanyar ki bayar da budurcinki, ga sarki da kuma dodon ƙungiya maimakon a ce ki kawo jini tashin farko. Aljanin da ke da alhakin bamu kuɗaɗe,da jagorantar ƙungiyar, shi ne ya shiga jikin sarkin ƙungiya ya kwanta da ke, a matsayin barka da zuwa na ƙungiya kuma da sadaukarwar ki ta shekara!!!
(Alhamdillah, da haka muka kawo ƙarshen book 1, sai mun haɗe a kashi na biyu).
Ayshercool 08081012143