Kenza eBookz

Buzu book 2 complete - Chapter 29

Buzu book 2 complete - Chapter 29

Buzu book 2 complete Chapter 29: Buzu book 2 complete Chapter 29. Ta tashi tana kallon yadda suka din ga ci da wuta, ta bar gurin. Kai tsaye ta tari abin…

3,208 words

Ta tashi tana kallon yadda suka din ga ci da wuta, ta bar gurin. Kai tsaye ta tari abin hawa ta tafi gidan Hajiya Sa'a. Hajiyar ta yi iya ƙoƙarinta gurin ɓoye jin haushin Jamila da take yi, ta karɓe ta hannu bibbiyu har ta taya ta lissafin kuɗin kasuwancinta da kuma kayan da take da su a ƙasa. Bayan sun kammala ta ce "Ni kuwa Jamila, yaya batun ƙungiya wa za ki bayar ne?" Jiki a sanyaye ta ce "Haryanzu ban gama tunani ba ne ba"

"Tsoron dai ki ke ji haryanzun ko?"

"A'a na rage ji"

"To ki yi ki hanzarta ki yi abin da yakamata amma kin tsaya. Ni kalli nawa nan na shirya komai aiwatar wa kawai ya rage mini, sai na je gidan zan yi, na sake bayar da ɗan Fatuhu"

Jamila ta kalli drower da Hajjya Sa'a ta janyo, tana nuna mata 'yar tsanar nan.

Jamila ta ce "To idan ban kai kowa ba, akwai wani abu da zai faru ne?"

Ta ce "Au da kara zube za ki zauna ki ƙi bin umarnin ƙungiya? To idan ba ki kai kowa ba, jininki aljanin zan shanye ki mutu" Cikin Jamila ya yi wata irin ƙara bayan tuna ta ƙona kayan. A tunaninta shikenan ta huta sun rabu. A ranta ta ce "Wannan wane irin bala'i ne na jefa kaina a ciki, Ubangiji Allah ka kawo mini agaji na rabu da wannan masifar.

***** Fafur Nana ta ƙi yadda zuciyarta ta amince abin da ya faru gaskiya ne ba mafarki ba, saboda ta riga ta saba da irin wannan cazan kan da Ƙaisar ya kan yi mata wasu lokutan, har ta gaza banbance abin da yake zahiri da kuma mafarki.

Su na ɗakin girki su na ta ɗorawa da saukewa, ta kalli shugabar su ta ce "Dan Allah a gidan nan, babu yadda zan yi na samu waya, ina son na kira gida ne, na ji halin da yarona yake ciki"

Balaraba ba ta bata amsa ba, ta ji Muryar Asal ta ce "Babu wannan damar, sai dai idan kina buƙata ki zo gurina ki karɓi wayar ki kira" Nana ta ɗan yi shiru sai kuma ta girgiza kai ta ce "A'a ki bar shi na gode"

"Me yasa ki ka ce haka? Kina tunanin wani abu a ranki ne?"

"Bana tunanin komai, kawai dai na fasa ne"

Ta yi murmushi ta ce "Shikenan, ga saƙo can daga gidan Sultan, tukuicin aikin da ku ka yi na girki"

Balaraba ta risuna tana yi wa Asal magana da yarensu, Nana kuma ta cigaba da aikinta, tana sane ta cewa Asal ba ta so, dan ba ta gama gane ina Asal ɗin ta saka gaba ba, da kuma cikakkiyar manufarta a kanta ba. Tana tsoron ta yi amfani da wata dama da za ta samu ta cutar da ita.

Dogwayen riguna na alfarma Nana ta samu, guda uku da kuɗi. Ta yi murna sosai da kayan, saboda rigunan na alfarma ne.

Katafaren ɗakin bacci ne, mai ɗauke da kayan alatun more rayuwa irin na masu mulki. Duhun dare ne, sai dai hasken fitilun ɗakin ya gauraye ko ina, kai ba ka ce dare ne ba. Yana zaune a gefen gadon, tare da dattijon. Cikin kamala dattijon ya ce "Imam, ina ƙara yi maka gargaɗi da jan kunne a kan ka ƙara kula da kan ka. Kar ka ɗauka kowane murmushi ne na soyayya, wani murmushin na babu yadda aka iya da kai ne. Kar ka kuskura ka faɗi wani abu da zai rusa shirinmu, mun ɓoye abubuwa da dama a game da kai, duk abin da baka fahimta ba, ka tambaye ni, kar ka wani ya buƙaci sanin wani abu daga gare ka, ka sanar masa kawai jinya ka yi tsawon wannan lokacin.

"Abii"

"Na'am abin ƙaunata" Imam Hammad ya yi murmushi ya ce "Me ka ke ɓoye mini ne, akwai abubuwan da suka hargitse a rayuwata, tsawon wani lokaci na ɗauka ina jinya ba a hayyacina ba?"

"Ka na ji na? Haryanzu ba ka warke ba, ka na buƙatar hutu mussaman a ƙwaƙwalwarka, kar ka takurawa kanka da tunanin abubuwan da suka faru. Jita-jitar da ake yaɗawa a kan ka, da surutai daban-daban shi ne dalilin da ya sanya muka dawo da kai ƙasar nan, a shaida dai kana raye, cikin ƙoshin lafiya"

"Mahaukaci ne ni kenan? Tun da ina iya tuna yadda ciwon nawa ya fara, amma ban san yaya ya ƙare ba"

Sultan ya tsuke fuska ya ce "Ya ishe ka haka. Kar ka kuskura na ji labarin nan ya fita, waye ya ce kai mahaukaci ne? Larurar zuciya ce take damun ka, babu daɗi babu ƙari daga haka. Babu wata larurar hauka a tattare da kai".

"Amma Sultan ko zaka saka na ɓoye wa duniya, yakamata na san matsayin lafiyata...

"Hammad!" Tilas ya ja bakinsa ya yi shiru, ganin yadda ya fusata Sultan ɗin.

*****

Tun da garin Allah ya waye, Nana take jin faɗuwar gaba da matsananciyar fargaba, ga sanyin da take jin yana ratasa ta, ta san ba na lafiya ne kawai ba. Dan haka ta ɗaura alwala take ta addu'a. Bayan fitowarta ta cika da mamakin ganin yadda ma'aikatan gidan, suke ta aiki tuƙuru suke gyara gidan duk da ko ina a gyare yake. Ko ta ina ƙamshin turaruka ne ke tashi daban-daban. Har sun so su yi yawa ma. Ɓangaren da take aiki, sai azalzalarsu ake yi, ta fahimci dai wani baƙo ne mai muhimmanci zai sauka a gidan. Har mamaki take yi yadda suke ba wa abinci muhimmanci, baƙo ɗaya sai a saka a yi masa abinci biyar, kuma duk da an san ba iya cinyewa zai yi ba.

Ta fito kenan ta ci karo da Asal, ta sanya zani da doguwar riga na shadda baƙar shadda, kanta babu ɗan kwali, hannayenta da yatsunta duk zobunan gwal ne, uwa uba wata irin sarƙa da ta saka ta zinari tun daga wuyanta har cikinta. Gashinta ya sha ado, ta sake shi har kafaɗarta, shi ma ta sanya masa wata siririyar sarƙa da ta kwanto har goshinta. Duk hassadar mai hassada babu yadda za a yi ka kalle ta ka kushe ta, jawur da ita a cikin baƙar shaddar sai ta haska shaddar.

Ita dai Nana tun da ta zo gidan, ba ta taɓa ganin Asal da miji ko 'yan uwa ba, sai tarkacen ƙawayenta, su ma a wancan gidan ne, wannan gidan ba sa biyo ta su zo. Kuma duk abin nan Nana ba ta taɓa bin diddigi ta ji wace ce Asal ba, me yasa kuma take rayuwa a gidan daga ita sai masu yi mata hidima ba.

Da daddare Nana ta ji su Balaraba su na yare, su na faɗin sunan Imam, lokaci lokaci su na haɗa wa da Hausa, sai dai ta manta a inda ta taɓa jin Imam ɗin.

Babban abin da ya ɗaurewa Imam kai, bai wuce yadda a faransa yake jin sa garau, ba shi da wata damuwa ko wani ciwo da yake ji ba. Amma tun da ya sanya ƙafarsa a Agadez tsawon kwanaki huɗu, ko sau ɗaya zuciyarsa ba ta saurara da bugun da take yi cikin sauri babu ƙaƙƙautawa ba.

Nana na ta kai komo a kitchen, ta kammala duk wani aiki da ya shafe ta, tana shirin tafiya ta je ta kwanta. Balaraba ta ce "Saurin me ki ke yi ne Nana?"

"Ina son na je na yi wanka na kwanta ne"

"Ki je ki yi wankan, nan da mintuna talatin za ki kai wa Gimbiya Asal bunu da madara sashinta"

Har Nana za ta yi magana, dan ba ta shiga sashin Asal sai sau ɗaya, ta taɓa zuwa idan sun yi girki akwai waɗanda suke kaɗai suke iya zuwa sashen su kai. Ta fasa maganar ta ce "To"

A gurguje Nana ta kintsa, ta koma ta ɗauki kayan za ta yi gaba, Balaraba ta ce "Ai ba sashinta za a kai ba, Ramata raka ta"

Ramata ta kalli Nana ta yi mata kallon banza, ta ɗan kwaɓe baki sannan ta yi gaba Nana ta bi bayanta. Duk yadda Nana ta so sarrafa kanta ta kasa, ta ɗaga kai ta din ga kallon ƙawataccen gurin tare da jinjina yadda masu gidan suka ƙware a iya almubazzaranci. Dan ba za ta kira shi ado ba kawai sai dai almubazzaranci.

Tana saka ƙafarta a cikin falon, ta ji tamkar an jona mata shocking, saboda rawar da jikinta ya yi, sai da farantin hannunta ma ya girgiza tamkar zai ɓare. Ramata ta kalle ta, ta yi tsaki kawai. Nana ta ajiye kayan a hankali a kan carfet ɗin ɗakin. Bayan ta ajiye ta yi taku huɗu zuwa biyar, ta ji yadda adadin sanyin da take ji yana ƙara yawa. Ta sauke idanunta a kan ƙaton frame da hotonsa a jiki. Danƙarewa ta yi a guri ɗaya, ta kasa motsa ko da ƙafarta. Taku ta fara ji a bayanta, ana tahowa, muryar Asal ta ji tana magana da faransanci cikin shagwaɓa. Ɗan ja ya yi ya tsaya, jin yadda jikinsa ya yi wata girgiza.

"Lafiya dai ko?"

Ya jinjina mata kai alamar eh.

"Amm me ku ke yi a tsaye a gurin nan ne?"

Ramata ta ce "Abinci muka kawo"

"Waye ya yi?"

Ta nuna Nana da ba ta juyo ba.

"Zo" ta kira Nana sai dai Nanan ta ƙame ba ta juyo ba. A wulaƙance Ramata ta taɓa ta ta ce "Ana yi miki magana" "Tana ji na rainin hankalin za ta yi mini" Sannu a hankali Nana ta juyo, idonsa na kan wayar hannunsa. Yanzu ta tabattar da mafarki ta yi ba, Sayyid ta gani, sai dai ganinsa bai razana ta ya kiɗimata ba, kamar yadda alamu suka nuna Asal matarsa ce ba. Ta sunkuyar da kanta ƙasa, tana jan ƙafafuwanta a hankali.

"Me ya same ki ne?"

Ta girgiza kai alamar ba komai.

"Ki yi mini magana kina girgiza kai kawai"

"Ba ni da lafiya"

Asal ta ja tsaki ta ce "Je ki kar ki ɓata mini rai"

Ta zuba masa shayin a kofi, ta zuba masa madara, ya ɗauka a hankali ya kai bakinsa yana sha.

Nana kuwa a ɗakinta, gaba ɗaya ta burkice, tamkar za ta yi hauka ta ce "Dama abin da ka ke gargaɗina a kai kenan Ƙaisar? Sayyid me yasa za ka yi mini haka, dama ka na da wata matar ka aure ni? Yanzu ka na nufin ka manta ni, Sayyid anya alƙawari ya ce haka? Na haƙura zan ɗauki ɗa na na koma gida, ganinka da wata kawai ya isa ya yi ajalina. Wataƙila alhakin iyayena ne ma da na taho ba da izininsu ba. Yadda ka ke a cikin daular nan, yaya za a yi na ce ina da alaƙa da kai ma a yarda da ni?" Ka ce Ruhina da naka su na rayuwa a tare, kowannenmu yana ɗauke da ruhin ɗan uwansa, ni na yi dakon soyayyarka ashe ka na da matar da ta fi ni komai" Ta yi maganar cikin matsanancin kuka tamkar za ta fita daga hayyacinta.

Yana tsaye yana jin yadda ruwan yake ratsa shi daga cikin gashin kansa zuwa jikinsa. Wani irin zafi yake ji a cikin ƙwaƙwalwarsa, tamkar kansa zai tarwatse. Karo biyu yana jin jikinsa ya yi girgiza. Ya yi wankan ya lulluɓo jikinsa da towel. Asal ta sha kwalliya cikin baƙaƙen kaya na bacci. Ta nufo shi tana rangwaɗa, ta cire towel ɗin da ya lulluɓa da shi. Ya ɗan lumshe idanunsa saboda ƙamshin turaren da Asal take yi mai jan hankali. Ta shige jikinsa ta rungume shi, ta ce "Na yi kewarka sosai Imam" "Nima ina jin kewar abin da ban san mene ba, bayan kewarki da na yi"

"Akwai abin da ya fi ni muhimmanci dama, da har ka ke kewarsa fiye da ni?"

"A'a ban ma san mene ba, kawai dai ina jin akwai wani abu da ba daidai ba"

Ya yi maganar yana shafa gefen wuyanta, yana son tambayarta wace ce yarinyar nan, amma ya haɗiye ya fasa. Ya fara ƙoƙarin sumbatar ta, sai dai ya ja da baya da sauri yana dafe kansa, da yake jin wani sauti mara daɗin ji a cikin sa.

"Imam jikin ne dai?"

Bai yi magana ba, ya hau kan gadon ya kwanta ya lumshe idanunsa.

Washegari da safe, idanun Nana sun kumbura suntum, saboda ba ta rintsa ba ko kaɗan. Ta saba da wuri take tashi, ta fara gudanar da aikinta, amma sai da aka zo aka kira ta, ta ce ba za ta yi aikin ba.

Bayan mintuna talatin sai ga Asal a ɗakin, ta kalli Nana a wulaƙance cikin isa da gadara ta ce "Ki ka ce ba za ki yi aiki ba yau? Saboda gidanki ne ko zaman kan ki ki ke yi a gidan? An kai wa Imam shayi ya ƙi sha ya ce ba irin na jiya ba ne"

"Eh ba zan yi girki ba, kuma barin gidan nan zan yi, na gaji da wannan aikin, zan je na ga yarona"

Asal ta yi dariya ta ce "Ai kuma ƙarya ki ke yi. Na ɗaukko ki gidan nan saboda nesanta mijin da waɗanann munafukan hadiman, na kawo bare da baki san komai a kan harkar gidan mulki ba. Kuma ba kya cikin kalar matan da za su iya ɗaukar hankalinsa. Dan haka na kawo ki ne dan ki din ga kula da abin da Imam zai ci aikin da ki ka zo yi gidan nan kenan. Nana ta yi wa Asal wani irin kallo mai cike da tsana, ji take tamkar ta kama Asal ta yi ta jibgarta har sai ta ji ta huce.

"Gimbiya Asal, ai an bar kari tun ran tubani. Ba zan yi girki ba sai dai yunwa ta kashe Imam ɗin, ke da yake aure idan ba za ki girka masa ba, to kar Allah ya sa ci, sai na bar gidan nan ba zan zauna ba" Ta yi maganar cikin ɗaga murya da zazzaro ido.

Asal ta yi taku biyu, ta hankaɗa Nana baya ta ce "Ki kiyaye harshenki a kan abin da zai din ga fitowa daga bakinki, a kan mijina. Biyan buƙatata ce kawai ta sanya nake ƙyale ki, ki daina ƙoƙarin ƙetare iyaka. Tafiya kuma ga hanya nan maza ki tafi mu gani, idan kina tunanin da ka na kawo ki gidan nan na ajiye"

Ayshercool 08081012143 Littafin kuɗi ne, 1k ne via 0069685771 Aisha Adam stanbic bank ku tura mini hakkina kan ku karanta. 72

Sai da Nene ta tabattar Nana ta ɗan nutsu, sannan suka kwanta.

Washegari Nene ta fita, ta bar Nana a gidan tare da Muhsin. Bayan ta dawo daga gurin sama'arta ta cewa Nana, yakamata ta je ta ɗan sai abubuwan da za ta buƙata saboda tafiyar da za ta yi da nisa, kuma ba su san yaya tsarin aikin can ɗin yake ba. Nana ta ce "Ni babu abin da nake buƙata, ki bani wani abin na riƙe a hannuna, sauran kuɗin kuma ki riƙe saboda kula da Muhsin na s...

"Biyana za ki yi kenan dan na riƙe miki Muhsin?" Nene ta katse ta.

"Allah ya baki haƙuri, ba haka nake nufi na, na ga dole ɗan abubuwan buƙatunsa duk ke ki ke yi masa Nene, tun da ga kuɗi sun"

"Kuɗinki ba su isa su saka na riƙe miki ɗa ba ko?"

Nana ta ce "Na sani, ai shi ya sanya na ce ki yi haƙuri.

Nene ta ce "Ba zan yi haƙurin ba sai na gama, kin iya kunna ni da na fara faɗa ki hau bani haƙuri, wato in ci kaina to sai na idar" Nana ta yi mata shiru ta yi faɗanta ta gama. Washegari Nene ta saka Nana a gaba suka je kasuwa, ta sata ta yi sayayyar kayan sakawa da na ɗan shafe-shafe, ta yi wa Muhsin sayayyar kayan sakawa da pampers. Babu yadda ba ta yi da Nene ba ta ɗauki wani abin ta ce ba za ta ɗauka na. Nana ta haɗe rai ta ce "Eh dama ba ki ɗauke ni 'yarki ba, shi ya sanya duk abin da zan yi miki ba kya karɓa"

"Ni za ki yi wa wayo, na ji ban ɗauke ki 'yar ba, ni ga ɗana nan" tayi maganar tana shafo Muhsin da ke bayanta. Da ƙyar sai da suka kai ruwan rana Sannan Nene ta karɓi abin da Nana ta saya mata. Sai dai kan su bar kasuwar har sun shirya. Nana ta ce "Nene kin ce mini ki na da ɗa, amma ban taɓa ganinsa ya zo ba, ba ya zuwa ya gan ki ne?"

Nene ta ce "Kamar ban damu da shi ba ko?"

"A'a kawai dai tambaya na yi "

"Yana can Nigeria"

"To me yake yi a Nigeria ba ya zuwa inda ki ke?"

"Sana'a yake yi, ai ya zo ki na can gurin aiki" Duk da Nana ba ta gamsu da amsoshin da Nene ta ba ta ba, amma ta basar ta ce "Allah sarki, Allah bai yi zamu haɗu ba".

Haka suka ci gaba da hira suka koma gida, Nana ji take yi tamkar ta ɗauke ɗanta ta tafi da shi.

Gidansu Ashura Nana ta je, ta samu keke ta ɗiɗɗinka kayan da ta sayo, ta sake haɗa jakarta ta ɗauki muhimman abubuwa a kayanta. Duk da a ɗaki Nene take rufe mata su, ba ta taɓa ganin alamar Nenen tana yi bincike a cikin kayan ba.

***** Ko da Jamila suka dawo Kano, fakar ido ta yi ta jefar da wannan tarkacen da aka ba ta aka ce da su za ta kai jini. Gaba ɗaya da ta tuna abin tsigar jikinta take tashi, ta ji ciwon kanta da zazzaɓi ya ƙaru. Gefe guda kuma hankalinta yana kan yadda ta ji Hajiya Sa'a tana faɗin za ta sake bayar da ɗan Alhaji Fatuhu. Ta jinjina rashin imaninta mutumin da yake fama da karayar arziki ga ciwo, ya rasa wancan ɗan kuma a sake bayar da wannan kamar ba a yi masa adalci ba. Sai dai gaba ɗaya ba ta san ta ina za ta fara ba, tana jin a ranta kamar yakamata ta tseratar da yaron. A gida ta tarar da Gaddafi, ta sha jinin jikinta da irin mugun kallon da ya yi mata, amma bai ce mata uffan ba. Suwaiba ma ƙura mata ido ta yi tana bin ta da kallo. Ta tsuke fuska ta harsri Suwaiba, sai dai Suwaiba ta tuntsure da dariya, kamar za ta shiɗe. Jamila ta yi tsaki ta shige ɗakinsu. Ba ta tarar da Mama a gida ba, haka ma Baba.

*****

Shiru Alhaji Zailani ya yi yana kallon Doctor Sharif yana sauraren shi, har ya gama karanta masa abin da Shukura ta je ta same shi ta yi masa. Ya ja numfashi ya ce "Shikenan, aikinka ya yi kyau Sharif, na kuma gode sosai da sosai da ka ke sanar da ni wannan abubuwan, Allah ya saka maka da mafificin alkhairi. Ka je za ka ga saƙo" Sharif ya yinƙura ya tashi ya tafi.

Alhaji Zailani ya numfasa a fili ya ce "Duk da kasancewar ki 'ya mafi soyuwa a cikin zuciyata, an zo gaɓar da ki ka ƙetare layin da bai kamata ki ƙetare ba, kina ƙoƙarin tono abin da zai wargaza zaman lafiya da kwanciyar hankali, dan haka ki yi haƙuri da duk matakin da zan ɗauka a kan ki.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull