Buzu book 2 complete - Chapter 30
Buzu book 2 complete Chapter 30: Buzu book 2 complete Chapter 30. ***** Nana ta jingina da jikin gilashin motar, tana kallon tulin yashin saharar da ya…
3,371 words
***** Nana ta jingina da jikin gilashin motar, tana kallon tulin yashin saharar da ya mamaye gurin. Fili fetal hagu da dama duk yashi ne. Cikin yanayi mai kama da bacci take ganin abubuwan da ta din ga gani a bacci cikin saharar. Ko a yanzun ma su na tafe Sayyid kawai take gani a kan raƙumi yana biye da su a cikin saharar. Kamar an taɓa ta ta ɗan yi firgigit ta kalli gurin, haryanzu a titin da ya ratsa saharar suke tafiya, zuciyarta ta yi wani irin bugu da sai da ta dafe ƙirjinta. Sanyi ta fara yana ratsa ta har cikin ƙashinta, ta ɗaga ido tana ɗan waige-waige ta ga ta ina za ta gano Ƙaisar ko wata baƙuwar halittar da ba jinsin mutane ba, sai dai ba ta ga komai ba. Ta sake jingina da jikin motar tana ta karanto duk addu'ar da ta zo bakinta. A haka har suka shigo cikin gari sosai da sosai. Nana na son karanta Symbols ɗin da take gani, amma ba komai take iya fahimta ba saboda rubutun French. Babbar hanya mai ɗauke da ƙaton gate ta ciki suka wuce. Ba ƙaramar gajiya Nana ta yi ba, saboda azabar nisan tafiyar da suka shawo ba, ba su ƙarasa ba sai bayan magariba. Kewar ɗan ta ta addabi zuciyarta, tunaninta yadda za ta din ga sintirin tsakanin Agadez da Maraɗi a wannan uwar tafiyar kamar ta ya da shege.
Wasu irin gidaje ne manya-manya na alfarma da ƙasaita a cikin gurin. A ƙofar wani gida direban ya tsaya, ya cewa Nana ta fito sun zo. Haka ta saukko ƙafafuwanta duk sun yi tsami saboda azabar gajiya. Ya buɗe bayan motar ya ɗaukko ƙatuwar jakar Nana, ya rufe motar, ya yi gaba Nana ta bi shi a baya tana karanto addu'oin da suka sauwwaƙa. Cikin wani matsakaicin gida suka shiga, gidan ya ƙawatu ya yi kyau sosai da sosai. A falon gidan ya ajiye wa Nana kayanta ya ce "Ki zauna ki jira a nan"
Nana ta ce "Amma wa zan jira a nan ɗin, ban ga alamar akwai mutane a gidan nan ba"
"Za ki gan su, ni a nan aka yi mini umarnin na kawo ki kawai"
Nana ta yi shiru tana nazari, shi kuma ya juya ya fice. Nana ta din ga rarraba ido, tana son ta yi salla amma babu wanda za ta tambaya. Harabar gidan ta fita saboda ta ga famfo ta yi alwala, ta dawo falon ta yi salla. Gajiya ta yi ta koma harabar gidan da kayanta, ta zauna tana rarraba ido. Can ta ji ƙarar mota, aka buɗe ƙofar wani jami'in tsaro ya shigo ya buɗe gate ɗin, aka shigo da wata haɗaɗɗiyar mota aka yi parking ɗin ta. Aka buɗe ƙofar motar, sai ga Asal ta fito sanye cikin doguwar riga, ta ɗaura mayafin a wuyanta, kanta babu ɗankwali. Har bakin ƙofar shiga suka rakata, ta wuce Nana ta shige ciki kamar ba ta gan ta ba. Nanan ma ta yi zamanta ba ta shiga ba, ta jingina da jikin kayanta taka addu'a saboda a gajiye take matuƙa, ga uwar yunwa tana ji ga tulin damuwa. Sannu a hankali take tuna yadda ta shigo ƙasar Nijar ba ta san kowa ba, da yadda ta din ga raragefe har zuwa kan zamanta da Nene. Sai ta tsinci kanta da tattara su baki ɗaya tana yi musu addu'a, da fatan dacewa a Duniya da lahira. Ba ta san iya adadin lokacin da ta ɗauka a gurin ba, ta ji muryar Asal a kanta. "Wai ke wace irin bagidajiya ce, a Nigeria daga wani ƙauyen ki ke ne?" Nana ta ɗaga kai ta kalle ta.
"Na saka an kawo ki guri, ki shiga ki jira ni kin zauna a waje, na dawo ma kin nemi guri kin zauna ba za ki shigo ba?"
"Ta yaya zan shiga gurin da babu kowa na zauna, ni da ban san ma aikin da ki ka kawo ni na yi miki ba?"
Haushi ya kama Asal, ta ce "To idan kin ga dama ki shigo, idan kuma ba ki ga dama ba, ki yi ta zama a gurin" Ta shige ciki Nana ta bi ta da harara, kamar ba za ta tashi ba, sai kuma ta tashi ta ja kayanta, ta shiga falon ta nemi guri ta zauna a kan kujera. Asal ta saci kallon Nana, da yadda take gudanar da lamarinta cike da ƙarfin hali.
Nana ba ta kula ta ba, ita ma ba ta kula ta ba, Nana ta gaji da zama, ta saukko ƙasa ta miƙe ta kwanta. Can Asal ta ce mata "Ga kitchen can, akwai abinci" Daga haka ta tashi ta bar falon. Nana ta tashi ta shiga kitchen ɗin, ta tarar da Abinci, ta ɗauka ta ci sannan ta ɗan dawo hayyacinta. A nan falon Nana ta kwana, da Asuba ta yi alwala a harabar gidan, ta koma falon ta yi salla. Duk wannan abin zuciyarta a cike da zullumin aikin da za ta yi wa Asal. Da gari ya yi haske, Asal ta fito Nana ta gaishe ta, amma ta yi kamar ba ta ji ba, ta fice ta bar gidan ta bar Nana. Nana tana nan zaune, aka zo aka ƙwanƙwasa ƙofar falon, ta tashi a ɗan tsorace ta buɗe, wani mutum ya miƙo mata takeaway ya ce "Ga shi nan, aka ce a kawo miki" daga haka ya juya ya tafi. Nana ba ta sake ganin Asal ba sai dare, ba ta saurari Nana ba still. Ta cika gidan ita da ƙawayenta, suka hau saman bene, suka kunna kaɗe-kaɗe har kusan ɗaya na dare su na abu ɗaya, suka hana Nana bacci. Sai gefin Asuba suka daina wannan shirirtar, Nana ta din ga mamakin ita Asal zaman kanta take yi ne, ba ta da magabata ko kuwa? Sai washegari sannan ta saukko ƙasa, a lokacin ƙawayen nata duk sun tafi. Ta kalli Nana ta ce "Daga yau kar ki ƙara kwanar mini a falo, ga ɗaki can kusa da kitchen, a nan za ki din ga kwana. Na kawo ki ne duk da ba yanzu ne za ki yi aikin naki gaba ɗaya ba, amma za ki din ga yi mini girkin Abinci da ni da ƙawayena, da sauran aikace-aikacen gida. Abu na farko dalilin da ya sanya na ɗaukko ki, ke ba ƙabilarmu ba ce ba, ba na son saka ido, ba na son surutu Duk wani abu da za ki ga na yi, ko ina yi babu ruwanki, aikin duk da na saka ki shikaɗai za ki yi mini" Nana ta yi shiru tana tunani, dama duk wannan abin ba wani branch ɗin za a kai ta aiki ba, wannan zuƙaƙƙiyar za ta yi wa bauta, shi ne har da ci mata mutuncin cewa an yi amfani da kuɗi sai ta yi abin da ake so. Kuma me yasa ba ta zaɓi kowa ba sai ita?. "Ba kya ji na ne?"
"Na ji"
"Ban gane kin ji ba? Haka zan din ga yi miki magana ki na amsa mini, ke ni fa ba Hasna ba ce ba, dole ki yi mini biyayya ki yi duk abin da nake so".
Nana ji ta yi tamkar ta yi tsaki, ta ce "Amma yanzu fisabilillahi duk faɗin ƙasar nan ki rasa wanda za ki ɗaukko ya yi miki aikatau sai ni. Ni harkar dafa abinci nake yi, amma kin kawo ni nan in din ga yi miki girki da boyi-boyi ba tare da an yi mini bayanin haka ba, ni gaskiya ba a kyauta mini ba"
"Da hakan ki ka dace ai, ko kina ganin kin cancanci wani abin bayan bauta? Idan ba za ki zauna ba ga hanya nan za ki iya tafiya" Ta yi maganar tana miƙewa tsaye. Har ta yi gaba sai kuma ta tsaya ta ce "Duk wani abu da za ki buƙata akwai shi a kitchen, kina iya dubawa, wanda babu kuma ki sanar mini, shi ma idan ba ki ga dama ba kar ki yi aikin" ta yi gaba ta bar Nana da ta gama ƙulewa.
*****
Gaba ɗaya Shukura ta burkicewa Sagir, ba ɗaga masa hankali ta yi da rigima ba, tattara shi ta yi ta watsar gaja ɗaya take harkokinta, da gaske take ƙoƙarin gano abin da mahaifinta yake ɓoyewa tsawon wannan lokacin da har ya hana Hajiya Amina bincike a kan lafiyarta. Ga shirin tariyar Yusra Sagir na yi, ga damuwar rashin sakin jiki da shi da Shukura ta yi, ta tattara shi ta watsar. Ɓangarensa ya saka aka gyarawa Yusra, dama ba amfani yake yi da shi ba, aka ƙara gyara shi, aka haɗa gidan gaba ɗaya aka sake yi masa fenti. Daga gaya mata batun dawo da Yusra zuwa gyaran gidan da kawo kayanta, ba a yi sati guda ba, gida ya ɗau harama. Duk yadda ya so ya lallaɓa Shukura, ta saukko ta din ga saurararsa ta yi burus da shi.
Nana ta shafe sati guda tana gidan Asal, tana yi mata hidima, ta hantare ta ta kyare ta, dandazon ƙawayen da take tarawa ma, su hana ta sukuni da aiki. Nana ta din ga iya ƙoƙarinta, gurin kai zuciyarta nesa, amma abin ya fara isarta. Tana tsaka da nazarin yadda za ta ɓullowa lamarin, da safe Asal za ta fita ta kalli Nana ta ce "Ki shirya nan da sati ɗaya zamu bar nan, zamu je asalin inda na ɗauke ki ki yi mini aiki a gurin"
Nana ta ce "Ina kenan? Kuma aikin me?
"Idan mun je za ki gani" Ta ba wa Nana amsar a taƙaice.
***** Jamila tana kwance tana chatting da Abba, bikinsa saura sati biyu. Hajiya Sa'a tana ta zaginsa da yi masa bala'i, a kan yadda yarinyar take ta ƙorafin ba ya kula ta, waya ma sai dai ita ta kira shi, babu abin da ya yi masa zafi da ita. Yanzun ma kamar ya yi wa Jamila kuka. Ita take ta rarrashinsa tana nuna masa babu komai ya yi aurensa kawai.
"Ƙanwata ko na yi aure hankalina ba zai kwanta ba, kar ki manta da ɓarnar da ta faru tsakanina da ke, ya zan yi da shi"
Ta ce "Na san kai mutumin kirki ne yayana, hakan ne ya sanya ka ke jin damuwa a kan abin da ya faru, amma ka yi haƙuri ka yi aurenka kawai, ina roƙon Ubangiji Allah ya kawo mini wani mijin"
"A'a ki daina faɗa mini haka, zuciyata tana sosuwa, baki da wani miji sai ni in sha Allah" haka suka kasance tana ƙarfafa masa gwiwa, shi kuma yana rarrashinta. Ta gama wayar ta ajiye, ta ga Suwaiba ta ƙuro mata ido tamkar ba ta taɓa ganinta ba.
"Meye ki ke kallona, lafiya?" Suwaiba ta yi shiru ba ta bata amsa ba, kuma ba ta yi magana ba.
Jamila ta ja tsaki, tana ƙoƙarin kwanciya, Suwaiba ta ce "Jamila"
"Na'am mene ne?"
"Ki ɗauki saƙonki mana"
Cikin rashin fahimta ta ce "Wane saƙon?"
"Na cikin jakarki"
"Cikin jakata kuma? Mene ne a jakar tawa? Wato bincike ki ke yi mini a jakar ko?"
"A'a ni tuni kawai nake yi miki da saƙonki na cikin jakar"
Jamila ta tashi zaune ta ce "Wai wani saƙon? Miƙo mini jakar dai na gani"
Suwaiba ta ce "A'a ba zan taɓa miki jaka ba"
Jamila ta janyo jakar ta fara buɗewa ta ga abin da Suwaibabta dame ta a kai. Cin karo ta yi da wannan 'yar tsanar da ta riga ta jefar. Saura ƙiris ta kurma ihu, ta rikice gaba ɗaya jikinta ya hau rawa, a tunaninta tun da ta yar shikenan ta rabu da ita. Suwaiba kuwa ta tuntsure da wata irin mahaukaciyar dariya, ta din ga yi tana ƙyaƙyatawa tana kallon Jamila. Gaba ɗaya Jamila ta kiɗime ta rasa abin da yake yi mata daɗi, gaba ɗaya jikinta ya hau rawa tamkar ta kurma ihu, sannu a hankali kanta ya fara juyawa ta fara gani dishi-dishi, dole ta rufe jakar ta nemi guri ta kwanta.
*****
Alhaji Zailani ya kwana biyu bai je gidan Alhaji Fatuhu ba sai yau. Sai dai ya sha mamakin ganinsa a harabar gidan da sanda yana dogarawa yana tattakawa a hankali, yana tsaye a kan ƙafafuwansa yana kallon yadda Muhsin yake ta gudu a harabar gidan. Sai da ya aro jarumta sannan ya iya danne abin da ya ji ya taso masa na tashin hankali da mummunan baƙin ciki. Da ƙyar ya iya washe baki ya ce "Ikon Allah, Abokina kai ne haka nake gani?"
Alhaji Fatuhu ya yi murmushi ya ce "Ka ga ikon Allah ko? Sannu da zuwa Bismillah" ya yi maganar yana nuna masa ɗaya daga kujerun da ke ajiye a gurin. Alhaji Zailani ya zauna suka ƙara gaisawa
"Bani labari, ya aka yi sauƙi ya samu haka, wani Asibitin ka je ne?"
Alhaji Fatuhu ya ce "A'a na ga an yi na Asibitin ne babu wani ci gaba, Fadila ta zauna ta din ga yi mini bayani, na amince muka fara gwada na islamic, cikin ikon Allah sannu a hankali wannan ɗaurewa da nake ji a jikina ya yi mini sauƙi, wannan gigicewar da nake na ji kamar zan yi hauka shi ma Alhamdillah ina daɗewa ban ji ba, wannan warin ma da nake ji ya ragux
"Amma Fatuhu ya za a yi ka biye wa mace da shirmen ta, ga na Asibiti ana yi kawai ta saka ka fara wani na shirme, sai ka je ka yi abin da za ka kauce wa hanya tukuna?"
"A'a nima na jaddada mata, ta kuma tabattar mini da babu kauce hanya a ciki, kuma nima shaida ne, shi ya sanya ma nake amfani da magungunan kuma ana samun ci gaba"
Alhaji Zailani ya miƙe ya ce "Haka ne, to bari na je dama ina da gurin da zan je na biyo, sauri nake yi"
"Ba zaka tsaya ku gaisa da mutanen gidan ba?"
"Sauri nake yi zan sake dawowa"ya yi maganar yana yin gaba cikin ƙunar rai, ji yake yi tamkar ya kashe Alhaji Fatuhu ya huta, dan shi bai taɓa zaton zai kawo yanzu bai mutu ba.
*****
Al Hussain ne a tsaye ya tsare Hasna da ido, yana yi mata faɗa cikin matsanancin ɓacin rai. "A kan me za ki yi haka? Dan me za ku yi mata dole, ai ba ɗaukar ta aiki muka yi saboda buƙatar mutum guda ba. Abin da yake cikin yarjejeniya shi ne ta yi wa gidan Abincinmu aiki, idan ma canza gurin aikin ne, wani reshen zamu mayar da ita, amma dan me za ku haɗa kai ku yi mata haka wannan wulaƙanci ne da cin zarafi, kuma ga shi bama 'yar ƙasarmu ba"
"Ni fa Al Hussain na kasa gane maka, ko son yarinyar nan ka ke yi ne? To bari na tuna maka kai Buzu ne, buzun ma farin buzu ka san abin da nake nufi ai, kuma matar aure ce ko bazawara dan ta ce mana tana da ɗa ma" "Ni ba wannan na tambaye ki ba, dan me Asal za ta yi amfani da ƙarfi da kuɗi ta tursasa mata yin abin da ba ta so, ai ba haka ake rayuwa ba"
"Ai na san za a yi haka, babu bayanin da ban yi mata ba taƙi yadda, ga shi ni yanzu ka zo ka saka ni a gaba da jaraba, sai ka je ka dawo da ita ni ba zan iya ba"
"Ke dai da ki ka yi hakan ki je ki dawo da ita, idan ba haka ba daga ke har ita na rubuta masa abin da ku ka aikata, daida yake da ku"
Ta kwaɓe baki ta ce "Wa ya san ma inda yake, mutumin da ake tunanin ya ɓata babu wanda ya san ma yana raye ko yana mace?"
"Hakan ya baku damar cin karenku babu babbaka daga ke har Asal ko? Yayi muku kyau" Hasna ta fice tana jin haushin masifar da Al Hussain yake ta yi mata, duk yadda ta yi ƙoƙarin hana Asal ɗaukar Nana.
*****
Ana gobe su Nana za su bar wannan gidan, Asal ta sanar da Nana ta shirya washegari za su bar nan. Ita dai Nana ta sanya wa sarautar Allah ido, rayuwarta ta zama tamkar tamaula daga nan zuwa can, ba ma ta da 'yancin tambayar ko sanin inda za a kaita sai dai inda ta tsinci kanta kawai. Ta sha aiki ta gama, ta ɗan zauna a falo tana hutawa, sai ga ɗaya daga gayyar ƙawayen Asal ta saukko ta kalli Nana ta ce "Dan Allah ina son shayi" Nana ta ce "Akwai a kayan Abincin da na girka" "Shayin kanumfari kawai nake so bana son Shan na girfa"
"Ga gurin dafawar can, idan ki ka je akwai komai, ki dafa ki sha idan kin matsu"
"Ke, kin san wace ce ni ki ke gaya mini haka?"
"Ban san wace ce ke ba, kuma ba na buƙatar sani"
Asal ta saukko tana tambayar lafiya.
Ta gaya mata abin da ya faru, ta kalli Nana ta ce "Wai ke me yasa ba ki da mutunci, ban gaya miki dole ki girmama baƙina ba, mene ne a cikin dafa shayi mintinan nawa ne kin yi kin gama?"
Ta kalli Asal ta ce "Ki yi haƙuri, wallahi ko cokali ba zan iya sake ɗauka ba, yau na bautu a gidan nan ke kin sani, kuma ban taɓa yi miki ƙorafi ba, amma yanzu dai na gaji gaskiya"
Suka juya yare suka yi magana, ba ta san me suka ce ba, ta ga sun koma kan bene.
Washegari da wuri suka ɗau hanya, sai dai ga mammakin Nana, har da rakiyar jami'an tsaro, kuma a wannan karon shigar Shadda Asal ta yi, an yi wa shaddar aiki tun daga sama har ƙasa. Mota ɗaya suka hau, ta ce Nana ta hau gaba, ita kuma ta hau baya. Sai da aka kuma wata tafiyar mai nisa, sannan ta ga sun tunkari wani irin ginin ƙasa tamkar ginin ganuwar Kano. Ginin ya ƙayatar da Nana sosai da sosai. Jami'an tsaro ne suke gadin ƙatuwar ƙofar gurin, da wasu Buzaye farare tas sanye da rawani. Nana kamar ta ce a tsaya, ta duba buzayen nan ɗaya bayan ɗaya ko za ta ga Sayyid ɗin ta cikinsu. Sai da motar su ta tsaya, suka sauke glass ɗin motar. Da Hausa suka gaisa, suka yi mata sannu da zuwa, ɗaya daga cikin su ya kalli Nana ya ce "Wannan fa?"
"Baƙuwata ce" ta ba shi amsa, ya jinjina kai motar ta shige. Su na shiga Nana ta ga ai gari ne guda a cikin ganuwar nan. Sun ɗan yi tafiya kafin su shiga wani ƙaton gida. Nana ta tsaya tana ganin yadda aka yi wa ginin ƙasa wani irin ado mai ƙayatarwa. Tun da suka doshi shiga gidan, ake gaida Asal cikin girmamawa, ita kuma ta yi fuska sai taku take cike da ƙasaita, kamar ba ita ce suke rashin hankali da ƙawayenta a wancan gidan ba. Wannan gidan saɓanin wancan da mutane a ciki, kuma da alama duk a ƙarƙashin Asal suke. "Wace ce ita?" Nana ta tambayi kanta. Sai da suka ƙarasa wani falo, sannan ta yi wa wata dattijuwar magana da yaren su. Matar ta kalli Nana ta ce "Bahaushiya ce ke ko? Zo mu je na kai ki masauki" Babu musu Nana ta bi ta, matar ta kai ta wani daki ta ce nan ne ɗakinta. Sai da Nana ta kwana biyu a gidan, ba ta sake ganin Asal ba, ba kuma ta aikin fari ba ta na baƙi kawai tana zaune, sai dai za a kawo mata Abincin safe, rana da dare sau uku a rana. Sai dai babban abin da ya dame ta, tun da ta shigo gidan, network ɗin wayar ya sauka gaba daya, ko ta kira Nene ba ta shiga sam.
A kwana na huɗu, da daddare dattijuwar matar nan ta zo ta kira Nana. Babu musu Nana ta tashi ta bi bayanta. Sun yi 'yar tafiya su na ratsa faluka masu kyau da ado, sannan suka bi wata ƙofa. Sanyin A.C ya daki Nana, ga wani irin haɗaɗɗan ƙamshi. Asal ta hahakimce a kan kujera kaɗa ƙafa. Ta kalli dattijuwar ta ce ta jira a waje. Daga ƙasa wata matar ce a zauna a kan carfet, ta gurfana kamar tana jiran Asal ɗin ta gafarta mata.