Buzu book 2 complete - Chapter 6
Buzu book 2 complete Chapter 6: Buzu book 2 complete Chapter 6. Ta yi ƙasa da murya ta cewa Nana "Dan ubanki, ki din ga ɓoye mijinki, kar ki bari 'yan mata…
3,255 words
Ta yi ƙasa da murya ta cewa Nana "Dan ubanki, ki din ga ɓoye mijinki, kar ki bari 'yan mata su din ga zuwa su na kallon sa." Uwani ita iya rage muryarta kenan, amma Sayyid na jin ta. Nana ta ɗaga kai suka yi ido huɗu, ya yi murmushi yana sunkuyar da kai.
*****
Alhaji Fatuhu, farin cikinsa ya kasa ɓuya, duk da halin rashin lafiya da yake ciki, idan aka zo duba shi, sai ya yashe haƙoransa da sukaɗai suka rage farare a jikinsa. Alhaji Zailani ya ƙura wa jaririn ido, ya kalli Alhaji Fatuhu da yake ta yashe baki.
Hajiya Sa'a ta ce "Kai Fatuhu. Sai ka ce ba a taɓa yi maka haihuwa ba, ji yadda ka ke washe baki, kana fama da kan ka"
Hajiya Suwaiba ta kwaɓe baki ta ce "Abin da na gani kenan"
Alhaji Zailani ya ce "A'a ku bar shi ya yi, ɗan mutum fa, kyauta ce Allah ya ba shi, da duk Duniya babu mai ba shi. Ni ba gani ba 'ya'yan duk babu sai biyu ne suka tsaya." Ya yi maganar yana zuba wa jaririn ido, yana tuna na Shukura. Tun da yake harkar ƙungiya, bai taɓa bayar da jinin da ya tsaya masa ya kasa mantawa ba, sai na Shukura. Mussaman idan yana tuna irin baƙar wahalar da ta sha. Ya kalli Fadila, da take ɗakin a zaune, ga jego tana yi, amma ta tare a Asibiti da ɗanyen jaririn da ko suna ba a yi ba.
Ya yi ajiyar zuciya ya ce "Wane sunan za ka saka masa?"
"Muhsin ɗina zan mayar" ya yi maganar muryarsa ɗauke da rauni.
Hajiya Sa'a ta ce "Wai an din ga saka Muhsin ɗin kenan?"
"Sunan mahaifin Fadila ne, shi za a mayar mu ci gaba da kiransa Muhsin, ni na yi mata alƙawari shi yasa. Na so Muhsin ɗina da ya rasu sosai da sosai. Na ji zafin rashin sa, sai dai ina tausayawa wannan Muhsin ɗin. Ya zo lokacin da mahaifinsa ba shi da komai, ba zan iya ɗaukar nauyinsa na kula da shi ba. Wataƙila ma kafin ya yi wayon sani na na rasu. Ga shi ko hakika ba zan iya yi masa ba" ya yi maganar hawaye na zubowa daga idanunsa.
"Haba Fatuhu, ya haka? Dan dai Hakikar da za ayi wa jaririn nan, ka san ba za ta gagara ba, amma ya za ka zauna kana kuka kamar ƙaramin yaro, a gaban iyalinka da 'yan uwanka hakan bai kyautu ba ai".
Alhaji Fatuhu ya ɗago idanunsa da suka yi jawur ya ce "Zailani. Ka san me nake ji kuwa? Gidaje da motocin hawa nake da, ina kyautar maƙudan kuɗaɗe ba tare da na ji komai ba, da abu ya dame ni, zan sai ticket na tafi umara. Ina da shaguna dukiya Allah ya yarje mini, bayan gwagwarmaya da na sha ta rayuwa. Astagfirillah ba ƙarar Allah nake kawowa ba, ko rashin imani da ƙaddara ba, ina jinjina girman lamarin Ubangiji, kuma ina jin babu daɗi ɗa na na cikina, ba zan iya saya masa ko wando ba"
Fadila ta ce "Dan Allah Daddy ka yi haƙuri. Mu na murna sauƙi yana samuwa, ga shi ka na ta magana sosai da sosai, kukan nan karya mana zuciya yake yi. Kuma da ka yi mana a baya, yanzu kuma da Allah ya kawo jarrabawa shikenan sai a yi haƙuri"
Su na nan zaune, sai ga ƙanin Baban Fadila, ya zo duba Alhaji Fatuhu ya kuma jaririn Fadila, wanda shi ne waliyyin Fadila. Sai dai shi ma ya tsorata da ganin Alhaji Fatuhu.
"Alhaji haka jiki ya zama? Subhanallah Allah ya baka lafiya"
"Amin kawu, amma jiki ya yi kyau Alhamdillah, tun da ina ta magana"
"Haka ne, amma menene takamaiman abin da aka ce ya same ka ne?"
Fadila ta ce "Haryanzu ba a gano takamaiman mene ne ba, yau a ce ƙodarsa ta kumbura, gobe a ce ko cancer ce, an yi gwaji ba ita ba ce. An yi gwajin zuciya shi ma lafiya ƙalau"
Cikin damuwa ya ce "Amma Fatuhu ana haɗa maka da na addini kuwa? Ka san muna da ido ne ba na ganin gari ba. Mussaman ku da ku ke shahararrun mutane da Allah ya ba wa wadata. Yakamata a yi na sihiri da shaiɗanu"
Alhaji Zailani ya ce "A'a ga likitoci su na kula da shi, ya za a yi a ce kuma a kawo wani abu daban? Magungunan gargajiyar nan kashe mutane suke yi ai, tun da ba auna su ake yi ba".
Alhaji Fatuhu ma ya ce "A'a ba wannan ba ne, wa ya damu da ni da zai yi mini sihiri. Larura ce kawai kuma likitoci na kula da ni"
"Kai, kalle ni da kyau. Duk bokon ka, nima ɗan boko ne, kuma na san ilimin addini, amma sihiri da shaiɗanu gaskiya ne. Tun da aka yi Annabi Sallallahu alaihi Wasallam sihiri, duk duniya ban ga wanda ba za a yi wa ba. Ciwo ya ƙi ci ya ƙi cinye wa ai akwai alamar tambaya, ga lalacewar dukiya lokaci guda. A dai tsananta addu'a. Ya gama bambaminsa ya fita. Alhaji Zailani ya din ga ziga Alhaji Fatuhu, tare da kushe magungunan gargajiya. Ba tare da jin nauyin Fadila da take gurin ba.
Ya gama soki burutsunsa, ya tashi ya yi musu sallama, tare da cewa zai aiko da abin hakika.
Har ya kusa ƙarasa wajen motarsa, ya waiwaya ya ga Hajiya Sa'a ta nufo shi, ya tsaya ta ƙarasa.
Ya ce "Ya dai?" Ya yi maganar yana kallonta.
"Zailani"
"Na'am "An sauke ɗan uwana daga shugabancin 'yan kasuwa an ɗora ka, ka saka an dawo da shi Asibitin nan, ƙarƙashin kulawarka, an ce a yi masa maganin gargajiya ka haƙiƙance kana kushewa. Kar ka kuskura na tarar da sanya hannunka, a cikin wannan abubuwan da suke faruwa da ɗan uwana"
Ya gyara tsayuwarsa ya yi murmushi ya ce "Babu sanya hannuna a ciki. Ina ƙoƙarin zama aboki mai halacci ne kawai. Sannan ki daina mazewa kamar ke ɗin mai ƙaunarsa ce, bayan sadaukar da 'ya'yansa maza da ki ke yi"
"Duk da haka, munin abin da na yi bai kai wanda ka ke aikatawa ba, ka fi ni sanin kai da me da me ka sadaukar, dan haka ka kiyaye ni". Ta juya ta koma. Bin bayanta ya yi da kallo, ya ji wani abu ya tsirga masa, tabbas idan Hajiya Sa'a ta ci gaba da wannan gigin, zai ɗauki matakin da ya dace a kanta."
*****
Cikin bacci, take jin hayaniya a bayan ɗakin, tamkar ana cin kasuwa. Ga wata irin sukuwa da take ji a roofing ɗakin, tamkar ta dawakai. Tun da ta farka sai juyi take yi, bacci ya gagari idanunta, ayatul kursiyyu ce ta zo bakinta ta din ga maimaitawa, har ta samu nutsuwa daga razanin da take ciki. Ta ruge idanunta, sai dai a maimakon ta yi bacci, sai wata irin kewar Sayyid take addabar ta. Ta rasa dallin da ya sanya, ba ya kula ta yanzu. Duk da ba shi da lafiya tana yi masa wannan uzurin, amma duk da haka da ya kan yi attempting sai ya ƙyale ta, yanzu kuma gaba ɗaya ya daina yinƙurin aikata komai ma. Wanda da idan ya sako ta gaba, har takura take yi.
Ta tashi zaune ta gyara maganin sauro, ta taka a hankali ta ɗaga labulen ɗakin, saboda zafi. Ta dawo ta ɗauki fitilar wayarta ta kunna. Ta haska shi ta ga idanunsa a lumshe, yana bacci. Ta zuba masa ido, ta fara tunanin ko ita ce mai matsala gaya mata ne bai yi ba, ko ma sharrin Ƙaisar ne?. Ta yi ajiyar zuciya, ta kashe fitilar, ta kwanta a gefen sa tana wasa da gashin ƙirjinsa. Zuwa na fuskarsa. Ta sake matsawa a hankali, tana sumbatar leɓansa, tamkar mara gaskiya. Gaba ɗaya a tunaninta bacci yake yi, sai da ta ji ya sanya hannayen sa, ya zagaye ta, tare da ba ta damar sumbatar bakin nasa. Nana za ta iya cewa, tun da Allah ya sa ta buɗi ido a duniya, ba ta taɓa jin kunya irin ta yau ba, cikin sauri ta fara ƙoƙarin rabuwa da jikinsa ta matsa, amma ya mirgina ya rungume ta gam a jikinsa yana numfashi a hankali.
Ayshercool 08081012143 56
Yana jin yadda jikinta yake tsuma, tamkar wadda aka kama tana aikata wani abin ashsha! Ko kuma wadda ake kaɗawa mazari. Magana yake son yi mata, amma abu ya gagara, duk ƙoƙarin da ya yi amma abu ya ci tura. Ya ƙara ƙanƙame ta tamkar wani zai ƙwace ta, ya din ga murza hannunta har ta fara jin zafin riƙon da ya yi mata. Yanayin ya ƙara ninka mata halin da take ciki, ta rintse idanunta. A hankali ta ji yana hura mata iska a cikin kunnenta, tamkar yana zuba mata wani sindari, haka ta ji wani irin nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita.
Ƙamshin nan ta ji yana ratsa hancinta, ta buɗe idonta a hankali, kamar yadda ta yi tsammani, a wannan ɗakin ta gan su. Ta hau waige-waige. Ta wata ƙofa ta ga ya fito, ƙugunsa ɗaure da wani abu kamar zani, ya zauna a kusa da ita yana kashe mata ido.
"Sayyid ka warke?"
"Eh mana"
"Ka daina jin duk abin da ka ke ji?" Ya jinjina kai yana murmushi. "To ka yi mini magana mana"
"Ma vieee" ya faɗa yana ɗan jan maganar yana kwanciya a gefen ta. "Har na ji daɗi da ka samu lafiya, Allah ya ɗorar maka da sauƙin nan Sayyid"
"Amin rayuwata, matso ki kwanta mu yi bacci"
Ta noƙe kafaɗa ta ce "A'a"ya saki murmushi yana kama hannunta. Duhu ne ya gauraye ɗakin. Dariya ta fara jin Sayyid ɗin yana yi mata cakulkuli. Ta kasance da shi cikin wani yanayi mai tsayawa a zukata.
Ba ta iya tantance a wani hali take, ta daina ganinta a ɗakin, sai a libraryn Ƙaisar. Ta tsaya tana kallon gurin, tana tunanin yaushe rabon da ta zo gurin nan.
Ƙaisar ta hanga, a tsaye yana gyara litattafan sa.
"Ƙaisar ka warke kenan?"
Yayi shiru yana goge wani littafi, ya gama ya ajiye littafin sannan ya ce "Eh, na warke. Waye ya ce ki je ƙauyen nan?"
"Ban gane waye ya ce na je ba? Zan kwana a titi ne? Ga mara lafiya ina da shi"
"Gaskiya ne, bai kamata ki kwana a titi ba. Wannan dalilin ya sanya tun a farkon auren nan, na din ga haska miki matsalolin da za ki iya fuskanta, amma gani ki ke yi kamar ƙarya nake yi, to yanzu sai ki san yadda za ki yi, ki rayu da ke da wannan lanjararren mijin naki, da duk larurar duniya ta ƙare a kansa".
A ƙule Nana ta ce "Larura Allah ne ya ɗora masa, kuma kun taka muhimmiyar rawa a larurarsa. Kuma ka daina ganin laifina. Zan tsallake shi ne a wannan yanayin da yake ciki, na bar shi? Mu bil adama mu na da bambanci da ku, mu na da tausayi da kuma nuna kulawa ga waɗanda muke ƙauna"
"A'a kar ki tsallake ki bar shi, amma ki yi ɗamara fiye da ta baya, garin Buda ki ka zo za ki zauna, ban sani ba ko kin fahimci abin da nake faɗa ko ba ki fahimta ba. Idan ma ba ki fahimta ba, za ki gane daga baya. Bil adama ku na tausayi da nuna kulawa ga wanda ku ke ƙauna, ku ke iya ɗaukar jinin makusantanku ku bayar, a yi muku tsafi ko? Da kyau matsala kuma ki sani, ba ki ga komai ba" Daga haka ya ɓace ɓat. Ta buɗe idonta a hankali.
Tana buɗe idonta, ta ji ana kaɗa kacakaura, da garaya a tsakar gidan su. Ana ta hayaniya tamkar ana cin kasuwa a tsakar gidan. Sanyi ta fara ji yana ratsa ta, bugun zuciyarta ya ƙaru, fiye da da, waiwaya ta yi tana son ganin ta inda za ta ga Ƙaisar, ko makamancin hakan amma ba ta ga kowa ba.
Wata irin guɗa ta ji an rangaɗa da wata irin murya, mai sauti, sai kuma aka ce "Yeeee barka da zuwa wakilin rafi, ku matsa ku bayar da hanya ga ango mairamu ya iso" ta ji wata murya na faɗa, ana ci gaba da shewa da kaɗe-kaɗen garaya. "Ku kawo Nono da suga, a kirawo 'yar Mairo ga mijinta ya iso. Ga farin goro ƙwarya dubu biyu ta rafi ta ce a bawa mamman wakilin rafi, gaisuwar iyaye" sai kuma aka saka shewa. Ba yau Nana ta fara ire-iren wannan jiye-jiyen ba, amma ta tsorata da wannan sosai da sosai. Ta rirriƙe Sayyid, ga sanyin da take ji ya fara damunta. Cas cas cas, ta fara jin sautin kaɗawar wani abu mai kama da abin ado na mata. Ta kalli tsakar gidan ta hango wata irin zanƙaleliyar mata, mai tsawon gaske ƙafafuwanta duk sarƙoƙi, ta yi shigar Fulani, sai dai ita ma ba a iya ganin sawayenta tamkar a kan iska take tafiya. Ta ɗan ƙara buɗe idonta, ta ga rana ce tarwai a tsakar gidan, ga dandazon mutane ana ta hada-hada. Sai dai shigar mutanen irin na zamanin da ne can baya sosai, kamar dai taron wani abu ake yi. Wata mata ta hango sanye da kayan saƙi farare tas, ƙugunta sanye da wuri, kanta babu ɗan kwali duk ta yi wa tulin gashinta adon wurin, hannunta riƙe da sandar dargaza, tana kaɗa ta tana juyi.
Wannan bafulatanar ce ta tsaya a bakin ƙofar ɗakin Nana ta ce "Baƙuwarmu, bikin girka ake yi, ko za ki taso ki ga yadda muke gudanar da al'adun bikin girka?" ta yi maganar tana zuro zanƙalelen hannunta cikin ɗakin Nana".
"La'ilahaillalah, Sayyid, Sayyid wayyo Baba" ta tashi a gigice, rirriƙe ta ya yi, ya janyo wayarta, ya haska ta. Fuskar sa cike da mamaki yake kallon ta, yanayin fuskarsa ke bayyanar da alamar tambaya.
"Sayyid wata mata ce, wata mata ce take ziro hannunta, tsoro nake ji, wasu mutane ne a tsakar gidan nan" ya haska ɗakin ta ga babu komai, haka tsakar gidan ma dare nesai hasken farin wata, babu komai. Sai a lokacin ta fahimci mafarki take yi. Ya ji jikinta ya yi sanyi ƙalau, amma bai ga Ƙaisar a gurin ba, bai kuma ga wata alama da take nuna yana gurin ba. Gaba ɗaya ta nemi ko addu'a ɗaya, ta rasa a cikin kanta. Ta kaɗa ta raya amma babu abin da ya zo da kanta. Tana so ta karɓi wayarta ta kunna karatun Alƙur'ani, amma ko ƙwaƙƙwaran motsi ba ta son yi, saboda tsoron da take ji. Da ƙyar wani baccin ya ƙara sace ta.
Babu babban abin da ya ba shi mamaki, irin yadda da safe take komawa normal, babu ma alamar akwai wani abu da yake ba ta tsoro cikin daren. Haka ta ci gaba da sabgoginta. Sai dai gaba ɗaya a kunyace take, ko idonsa ba ta iya kallo, saboda abin da ta aikata ya kama ta cikin dare. Shi ga tausayin kan su, ga kuma dariya ta ba shi.
***** Baba yana zaune yana shan koko da ƙosai a tsakar gida, sai ga kiran wayar Uwani.
Ya kalli wayar tasa ya ce "Tofa! Wannan jarababbar tsohuwar ko me za ta ce mini, take kira na da safiyar nan oho.
Ya ɗaga kiran ya saka a kunnensa. Sai dai ba ya jin ta sosai saboda rashin network. Ba ta haƙura ba ta din ga kira har sai da ransa ya fara ɓaci.
"Uwani ko a haƙura da wayar ne, kin ga babu network ne"
"A'a ina jin ka yanzu. Amm dama kiran ka na yi, na tambaye ka ina Nana kuwa?"
"Nana, tana gidan mijinta"
"Gidan mijinta wanne?"
"Mijinta dai na aure"
Uwani ta ce "Eh a ina gidan yake?"
"Amm can wajen gidan Ummi ne"
"Rufe mini baki, mutumin banza da na wofi. Ai kwana uku kenan ina neman layinka, amma bana samu saboda garin nan bamu da natiyok ake cewa ko me?"
"Uwani wai me ya faru ne?"
"Ai ba za ka san meyafaru ba, tun da ka bar yarinya tana ragaita ita kaɗai ranta ga miji mai larura,an kore su daga gidan haya, ba su san ma inda za su je ba, kana zaune hankalinka kwance. Ai ko 'yar riƙo ce Nana ka duba lamarinta"
Ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba, ta wanke shi ta tas, ta ƙare masa zagi da cin mutunci, ta ce kuma za ta kira Yaya Atine ma, sai ta ci ubanta.
Ran Baba ya yi mummunan ɓaci, kenan Ummi da Nana haɗa kai suka yi, suka kai ƙararsa gurin Uwani. Ya kira Ummi ita ma ya fara sauke mata kwandon tijara. Ranta ya ɓaci ta ce "Ni fa Baba ban kai ƙarar ka gurin kowa ba, Uwani ce ta kira waya, mu na tsaka da alhinin halin da Nana ne ciki, na gaya mata komai, kuma ni na faɗa ba Nana ba. Shi ne ta ce Nana su koma Ƙauye can gurin ta".
Sai kuma Baba ya yi sak. "Ƙauye kuma? Ta yi me a ƙauye?"
"To Baba zaman nan ɗin ya ƙi, kai kuma ka ƙi taimakawa, babu yadda muka iya Nana tana Buda"
"Ke Ummi ki na ji na, duk yadda za ki yi, ki nemi kuɗin mota, ki je Buda ki taho mini da 'ya ta. Lallai ya sakar mini 'ya ku taho tare, ya je Allah ya ba shi lafiya"
"Baba ya sake ta, 'yan uwansa ma ba a sa inda suke ba, wa za ta bar wa shi a can?" Yana cikin bambami kuɗin wayar suka ƙare. Dama Mama na tsaye tana jiran ya gama wayar, yana gamawa ta dube shi ta ce "Wato Nana ta kaso aurenta ta dawo ko? To wallahi ta dawo gidan nan ba ta da gurin zama, wai har ka manta irin zaman azabar da muka yi da yarinyar nan a cikin gidan nan? Babu bacci kullum bala'i da tashin hankalin iskokai, ba zai yiwu ba wallahi"
Sai dai kafin Baba ya ba ta amsa, suka ji Suwaiba ta ƙyaƙyace da wata irin dariya mara daɗin ji tana faɗin "Asma'u a ƙauyen Buda, tushiya masomar dawa, kowa ya bar gida gida ya bar shi" ta yi maganar tana ci gaba da ƙyaƙyata dariya kamar ba mace ba.
"Ke Suwaiba meye haka, wannan wace irin dariya ce? Ban hana ki irin wannan dariyar ba kamar ba mace ba?"
Suwaiba ta ce "Ina ruwan ki da dariyata"
Baba kawai ya gyaɗa kai, ya gyara hularsa ya fice ya bar gidan gaba ɗaya.
**** Rashin maganar nan ta Sayyid, ba ƙaramin damun Nana take yi ba, abin ya yi yawa sosai.
A wannan karon ta yi sa'a, ya bar ta ta je gurin Uwani, daga nan kuma ta je ta yo musu sayayya. Ta tafi ta bar shi da wayarta, domin ta ɗebe masa kewa.
*****
Alhaji Zailani ya saka sabon layin da ya sayo a cikin waya, ya kira lambar Nana. Sayyid yana kwance yana jin yadda wayar take ta vibrating, amma ya yi banza. Saboda ko ya ɗaga ba iya magana zai yi ba. Jin mai kiran ba shi da niyyar daina kiran, ya sanya ya ɗauki wayar zai kashe. Sai dai ya fasa kawai ya ɗaga kiran ya kara a kunnensa.
"A tunanki dan kin yi blocking ɗin lambata, zai sanya na kasa cimma burina a kan ki ne? Yanzu hankalina ya dawo gare ki, na saka an kori mijinki daga gurin aiki. Kuma zan nemo ki duk inda ki ka shiga sai na cika burika a kanki" wani irin jiri Sayyid ya ji ya fara ɗibar sa.