Buzu book 2 complete - Chapter 7
Buzu book 2 complete Chapter 7: Buzu book 2 complete Chapter 7. "Ba za ki yi magana ba?" Alhaji Zailani ya yi maganar yana kallon wayarsa. Wani irin haske…
3,243 words
"Ba za ki yi magana ba?" Alhaji Zailani ya yi maganar yana kallon wayarsa. Wani irin haske ya ga wayar tana yi, tana fafar fafar za ta ɗauke. Mamaki ya kama shi, dan wayar ba ta taɓa yin haka ba. Fitilun ɗakin suka ɗauke, duhu ya gauraye ɗakin nasa. Sai ya rikice ya tashi tsaye yana waige-waige. "Karo na biyu, ka sake shigowa hanyata, duk da gargaɗin da na yi maka, cewar mallakina ce, ina sake yi maka gargaɗi, kafin na tona maka asiri." Alhaji Zailani ya toshe kunnensa, saboda wani irin sauti da yake ji mara daɗi, ga ɗakin yana ta jujjuya masa. Can ya ji shiru ya daina jin sautin, ya buɗe idanunsa a hankali. Sai dai ya ga Shukura a tsaye a gabansa, jini yana bin ƙafafuwanta, ga wuƙa a hannunta, tsirara ta.
Ya miƙe cike da razani, ya fara ja da baya.
"Daddy ina jaririna? Ka bani jaririna Daddy" Ya ci gaba da ja da baya. Da gudu ta bi shi, da wuƙar tsirararta. Ya fita da gudu yana ihu.
"Alhaji lafiya kuwa? Anya hawan jinin nan bai fara taɓa maka ƙwaƙwalwa ba, ya ya zaka din ga ihu haka?" Hajiya Amina ta yi maganar cikin mamaki tana kallonsa. Ya kalli gurin ya gan shi a kan gado, a ɗakinsa. Yana son yi wa Hajiya Amina tambayoyi, amma abu ya gagara saboda tsabar razani da tashin hankalin da yake ciki.
AREWABOOKS
*****
Uwani ta din ga yawo da Nana a cikin ƙauyen nan, tana nuna ta a dangi, tana gaya musu 'yar gurin Isa ce. Dan galibi ba su santa ba. Nana gaba ɗaya hankalinta yana kan Sayyid da ta baro a gida, shikaɗai tana gudun kar ta je yana buƙatar wani abin. Ganin gantalin ya yi yawa, ga duk inda suka je sai Uwani ta tsuguna ta surutu kamar babu gobe. Tun Nana tana jurewa, har ta gaji ta ce "Uwani, na bar mara lafiya a gida, ko za mu je inda zan yi sayayyar, na koma kar na je yana buƙatar wani abin.
Uwani ta ce "Kuma fa haka ne, to mu je na raka ki. Na so ma sai ranar kasuwa za ki je sayayyar, an fi samun rahusa. Ai tun da Allah ya sa ki ka zo garin nan, za ki yi ta ganin 'yan uwa da dangi, za a yi ta zuwa duba mijin naki ma"
Ita dai Nana ta yi shiru, dan duk surutunta, Uwani sai da ta saka ta gaji, ga azabar tafiyar ƙafa da suka sha.
Ta rakata inda ta yo musu 'yan sayayyar kayan abinci, gaba ɗaya tsoron taɓa kuɗin take yi. Gani take yi kamar ƙarewa za su yi.
Uwani ta raka ta har gida, sannan ita ma ta zagaya, ta koma nata gidan.
Nana ta shiga ɗakin da Sallama, tana faɗin "Sayyid, ka ganni sai yanzu ko, ka yi haƙuri Uwani ce ta din ga ja na, ƙafafuwana kamar su karye" Sak dai ta yi shiru ganin wata irin kwanciya da ya yi a kife a kan cikinsa, hannunsa a lanƙwashe, kuma ba kamar mai ruf da ciki ba. Ga shi a tsakiyar ɗakin, ba inda ta tafi ta bar shi ba.
Ta zube kayan ta nufe shi jikint a sanyaye, gabanta na bugawa saboda fargaba da tsoron ko mutuwa ya yi. Aikuwa tana juya shi ta ɗan ja da baya a tsorace tana sauke numfashi.
Wayarta ta gani a ƙarƙashin inda ya kifa, idanunsa a kakkafe, babu baƙar ƙwayar idon, sai farar. Ga jikin zafi rauuu tamkar wuta. Ajiyar zuciya ta yi cike da damuwa, ta matsa kusa da shi ta yi Bismillah ta fara rage masa kayan jikinsa. Ta ɗebo ruwa ta din ga shashshafa masa tana sake nanata Bismillah. Ta je ta rufe ƙofar gidan, ta dawo ta cire rigar jikinta, ta kwanta a jikinsa, tana rintse idanunta saboda raɗaɗin da take ji a fatarta. Wani irin nishi yake, tamkar zai yi gurnani, yana miƙa jikinsa yana ƙara sandarewa. A hankali ta ji tamkar hankalinta yana gushewa, ita ba a farke be, kuma ita ba mai bacci ba. Ta ɗan ɗaga idonta, ta ga Ƙaisar tsaye a jikin ƙofar ɗakin yana kallon su. Ta yi shiru ba ta yi motsi ba, kuma ba ta yi magana ba, fatanta Sayyid ya samu sassauci daga azabar raɗaɗin da yake ji. "Ko dai ki bi a hankali, ko wannan ɗan tayin na cikinki ya yo waje saboda zafin jikinsa. Ko kuma Giyaz ya yi masa mummunar illa." Nana ta ɗaga kai ta kalli inda Ƙaisar yake, jikinta ya yi mata wani irin nauyi, ba ta ko iya motsa ɗan yatsanta.
"Babu irin kashedin da ban yi miki ba tun da fari, ki ka yi burus da ni, gani ki ke kawai cutar da ke ne kaɗai abin da nake yi. Amma tun da jimirnki taurin kai, wahala sai ranar da Allah ya yanke miki, tukuna ma." A hankali ta lumshe idanunta har ta daina jin muryar Ƙaisar.
****
Cikin damuwa Maijidda take kallon Saude ta ce "Yaya Saude haryanzu lambar Nanan ba ta shiga ko? Gaba ɗaya na kasa nutsuwa duk ji nake hankalina a tashe".
Saude ta ce "Dan Allah ki daina damun kan ki, in sha Allah tana cikin ƙoshin lafiya, kin san sharrin wayoyin nan, da rashin network, amma zan ci gaba da kiran ta, da na same ta zan sanar miki, kuma zan sake zuwa har gida na haɗa ki da ita."
"To Allah ya sa dai lafiya, kin ga na yi, na yi, na kaɗa na raya, Baban su Walida ya ƙi ba ni wayata, tsawon wannan lokaci haka nake zaune babu waya. Kuma duk wasu dabaru da zan yi na samu dama na je Kano na samu na ga yaran nan, abu ya ci tura sai ka ce ba Muslimi ba, ba ya jin magiya ba ya jin rarrashi".
"A'a kul Maijidda, uban 'ya'yan naki ki ke cewa kamar ba musulmi ba, kar ki sake. Ki rabu da shi da halinsa. Duk da Nana tana cewa za ta zo ita da mijinta, idan ma ba su zo ba, ni zan sake komawa na gano miki ita in Allah ya yarda. Iliyasu kuma ki rabu da shi ku lallaɓa kar ki fusata shi ya yi wani abin da ba a fata"
Maijidda ta yi ajiyar zuciya, ta jinjina kai kawai, amma gaba ɗaya ba ta cikin nutsuwarta.
****
Abu kamar wasa, aka shafe kwanaki biyar, Sayyid yana cikin wannan yanayin, sai dai Nana ta juya shi, ta goge masa jikinsa, ta yi masa ƙanin wanka a ɗaki, ta shafa masa turare ta saka masa kaya. Ga shi juya shi kawai aiki ne, saboda yadda ya yi mata nauyi, ga jikinta babu ƙwari saboda azabar laulayi. Juriyarta ce kawai ta sanya ba a gane mawuyacin halin da take ciki, dan ba ta taɓa yarda ta kwanta. Ga shi jikinsa duk ya kumbura, mussaman ƙafafuwansa. Tana zaune ta yi shiru tana kallonsa, kawai tamkar an yaye mata wani abu daga kanta, sarkin baka ya faɗo mata. Sai da ta ɗan zabura ta tafi tunanin ko yana wani hali yanzu?. "Ko dai can zan kai ka Sayyid?" Ta yi maganar tana kallonsa.
"To ni da ban ma san a ina yake ba, ta yaya zan kai ka?"
"Kul mene ne sahihancin magungunan da yake bayarwa? Mene ne halacci ko haramcin abin da yake yi, da za ki je neman magani gurinsa?" Wata zuciyar ta gargaɗe ta. Sai kuma ta yi shiru, tana tuna irin wahalhalun da ta sha, da faɗi tashin gurin masu magani, ita dai tana da yaƙinin har gurin bokaye da 'yan tsubbu an kai ta, domin a nema mata magani. Domin wasu ƙarara ayyukansu da abubuwan da suke faɗa, ne nuni da kaucewa hanyar gaskiya.
"Allah na tuba, Allah ya sanya ba wannan ne dalilan da ya sanya nake ta shan wannan wahalar ba. Allah ka yafe mini, ba da son raina aka din ga kai ni wasu guraren ba. Allah ka bamu lafiya da ni da mijina, Ubangiji Allah ka yaye masa wannan larurar, ka dawo masa da tunaninsa. Allah ban yanke tsammanni da daga falalarka da ni'imamominka ba"
Ta juyo a hankali ta dubi gurin da yake, ta ga idanunsa sun dawo daidai yana kallon ta. A rikice ta ce "Sayyid"
"Ma vie"
Cikin tsananin murna ta ce "Alhamdillah, ka tashi?" Ya jinjina kai yana lumshe idanunsa da suka yi masa nauyi. Ya ja jikinsa ya tashi zaune da kyar. Sai dai jikin nan duk a kumbure,ga kuma haki da ya farfaɗo da shi. Haka yau ma ta taimaka masa ya yi wanka ya ci Abinci ya fara rama sallolinsa a zaune.
Kallonsa take yi cikin damuwa, yakamata a ce sun koma Asibiti. Amma kafin a nemo mota a saka shi, su yi sammako su koma Asibiti, aiki ne. Mussaman da babu wadattacen kuɗi a hannun ta. A take ta tuna da maganin da sarkin baka yake haɗawa masu hawan jini, da wanda ɓarin jikinsu ya shanye a sakamakon hawan jini da matsalar zuciya.
Ba ta jira ya idar ba, ta zari hijjabi ta yi waje. Ta din ga tuhumar kanta da yadda aka yi tuntuni ba ta tuna ba, sai yanzu. Tun da su magunguna ne da yake haɗa s da saiwoyi ba wani surkullen ya yi ba.
Ta dawo ta tarar ya dawo bakin ƙofa ya zauna yana kallon hanya.
Tafiya mai nisa ta yi sosai da ta fita, ta samo ɓawon kwakwa da sassaƙen zogale, sai kuma farin zoɓo. Ta hura wuta ta wanke su, duk ta zuba a tukunya ta zuba ruwa, ta kawo ɗan kanumfari ta zuba a ciki. Sai da ta kammala sannan ta koma gurinsa, ta ce "Ka yi haƙuri, magunguna na je samo maka, na fita ka na salla"
"To na gode"
"Allah ya baka lafiya shugabana, Allah ya sanya ya wuce kamar ba a yi ba"
"Amin. Ke ma Allah ya baki lada, ya saka mini ke a aljanna. Ya sanya ki maƙwabci Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam a aljanna" waro ido ta yi ta gigice gaba ɗaya hawaye ya fara zirarowa daga idanunta ta ce "Sayyid ba ni da aikin da zai kai ni wannan matsayin. Amma ban san matsayinka a gurin Allah ba. Ban sani ba ko Allah ya karɓi addu'ar da ka yi mini. Amma a ce na maƙwabci Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam. Innalillahi wa Innalillahi raji'un Sayyid na rasa me zan ce. Baiwa ce mai tarin zunubai kuma mai tarin rauni. Amma Allah kai mai yawan rahama ne da falala, Allah ka amsa wannan addu'a da ya yi mini shi ma ka ba shi abin da ya roƙa mini"
Ya yi murmushi ya ce "Amin rayuwata"
"Sayyid, anya an taɓa yi mini addu'a da ta tsuma ni kamar wannan? Subhanallah, subhanallah. Na ji daɗi wallahi" Shima idanunsa ne ya cika da hawayen, ya ci gaba da bin ta da idanunsa. Kawai sai Nana ta ji ta manta kaso mafi yawa na damuwarta. Da ta tuna Addu'ar da ya yi mata sai murmushi ya kasa barin fuskarta.
Maganinta ya daɗe yana dahuwa, ta sauke ta mayar da ruwan girki. Ta tsiyaya masa a kofi, ta je ta zauna a gaban sa.
"Sayyid ga magani na dafa maka, mu jarraba, bamu sani ba, ko Allah zai sanya a dace" ya kalli kofin ya kawar da kansa gefe, yana ɓata rai.
Ta marairaice ta ce "Dan Allah ka sha, babu ɗaci ko bauri fa"
"Ba na son magungunan nan, babu yadda na iya ne nake shan na Asibitin ma, ni wahalar da ni suke yi"
"To ai wannan ba na Asibiti ne ba, dan Allah ka daure ka taimaka, ba dan ni ba"
Da ƙyar ya yarda ya karɓa, ya ɗanɗana ya ji babu ɗaci, sannan ya ci gaba da sha, sai ma ya ji ɗumin maganin ya yi masa daɗi. Bayan ya shanye, ta dafa masa shayi kuma, ya ɗora dan duk wahalar ciwon da yake ciki, ba ya iya haƙura da shan shayi.
Nana ta dage da bawa Sayyid, wannan ruwan maganin, tana addu'ar Ubangiji Allah ya taimake su, ya sanya ya karɓe shi. Cikin ikon Allah, sai kumburin da ya yi, ya fara sacewa a hankali, har yana iya cin Abinci sosai. Nana kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha. Nana ta din ga murna, ganin ana samun ci gaba a yanayin jikinsa. Har banɗaki yana iya zuwa, ba tare da ta kama shi ba, yana tafiya a hankali a hankali da kansa yana iya yi wa kansa Wasu abubuwan.
Yana zaune tsakar gida, yana shan shayi ta ce "Ashe maganin Sarkin baka yana yi"
Ya kalle ta, ta ce "Ka san Sarkin baka?" Ya ɗan yi shiru yana kallon ta.
"Ranar da aka kai ni, kai na an kai ka, zaku tafi lokacin, ni kuma a lokacin na ji na fita daga hayyacina. Kai mun fa daɗe muna haɗuwa da kai."
Ya yi murmushi ya ce "Ruhina ne ya addabe ki, sai da ki ka nemo ni, ki ka aure ni ki ka nutsu"
Ta ɓata fuska ta ce "Ba wani nan, kai ne ka din ga bi na dai, har ka aure ni".
Ya ɗan sake zuƙa shayin hannunsa ya ce "A'a. Har gidan da nake ki ka bi ni fa"
"Ni ba bin ka na yi ba, kuma ai kai ka ce a biya maka sadakin aurena"
Ya maze ya ce "Ai gani na yi kin liƙe mini, har cikin ɗakinmu na gadi ki ka bi ni, na ce kai yarinyar nan idan ban aureta ba, akwai matsala haka za ta yi ta bina saboda ruhinta da yake jikina. Kina ganina kuma ki ka rikice"
"Ni ba ina sane na shiga ɗakinku ba, Jummai ce ta ce na ajiye muku Abinci, kawai na ji ana kirana a cikin ɗakin, ban ma na san na shiga ba. Kuma ni da na shiga wannan tsohon na gani. Kuma ai kai ma idan ka ganni kallona ka ke yi"
"A'a faɗi gaskiya dai, ni ki ka leƙo ki gani, ranar ba ki ganni ba, sh... Kawai ya ga tana hawaye. A diririce ya ajiye kofin hannunsa ya ce "Mene ne?" Ta yi masa shiru.
"Laifi na yi miki? Wasa fa nake yi" ta yi masa shiru, tana matse ƙwalla. Ba wai wasan da yake yi mata ne ya sanya ta kuka ba. Tuna yadda aka yi auren abin da Baba ya din ga faɗa da wanda Mama ta din ga yamaɗiɗi da ita, abin ne kawai ya dawo mata. Ji ta yi yana goge mata hawaye, fuskarsa ɗauke da damuwa, ya ce "Ba zan sake ba" Kwaɓe baki ta yi cikin shagwaɓa, wasu hawayen na ziraro mata.
"Na ce na daina fa, ki bari ƙirjina ya fara nauyi" da sauri ta saka bayan hannunta, tana goge hawayen fuskarta.
"Yauwwa dama ina so mu yi wata magana, mai muhimmanci da ke"
Ta tattara hankalinta, gabanta na dukan uku-uku cike da wasi-wasin wace maganar zai yi da ita haka?.
Ayshercool 08081012143
57
Ya yi mata alama da hannunsa, a kan ta nutsu ta kwantar da hankalinta. Ta jinjina masa kai, duk da gabanta na ci gaba da faɗuwa.
"Amm na san kina haƙuri a kan abubuwan da suke faruwa, duk da kin ce mini ba kya so na din ga irin wannan maganganun, amma sun zama dole na yi. Ina ƙara yi miki godiya da nema miki yardar Allah, na san ba ni da abin da zan biya ki da shi a wannan Duniyar. Ke ce komai nawa da ki ka rage Asmy. Sannan ɓangaren abin da ya shafi auratayyarmu, shi ma na san...
Ta katse sh6ta hanyar cewa "Amm ni dai a bar wannan zancen, bari na je na ɗora wakena"
"A'a ki tsaya mu yi magana"
"A'a ba sai mun yi ba"
"To kar na sake jin kin bi dare ki na taɓa ni" Kamar ta yi tsuntuwa ta ɓace, saboda azabar kunya, ita a zatonta ma ya manta gaba ɗaya. Cikin azama ta miƙe ta ɗauki robar wakenta, ta nufi inda take girki. Tana tashi ya kashingiɗa yana dariya.
Nana tana ta fifita wuta, yana daga zaune yana kallonta. Wani irin abu ne yake yi masa yawo a jikinsa, a game da ita. Yana jin zai iya yin komai, dan tabattar da ci gaba da zamanta mallakinsa, shikaɗai. Juriyarta, sadaukarwa da kuma tsananin tausayinta, ya sanya yake jin ina ma yana da wani abu da zai iya kamanta faranta mata rai, kamar yadda take ta wannan ɗawainiyar da shi. Ya san in dai a wannan Duniyar ne ba shi da abin da zai biya ta. Duk da matsananciyar damuwar da ya kan shiga, da jin cewa ya zama silar nakasta rayuwarta, ta zama tana rayuwa ba tare da tunanin wani abu da take so ta cimma ba. Kullum tunaninta a kan sa ne kawai. Tana ɗagowa suka haɗa ido, ta murguɗa masa baki, ta ci gaba da fifitar wutar gabanta. Ya tako zuwa gaban murhun ya tsuguna.
"Dan Allah ka tashi, saboda numfashinka fa"
"Kawo na yanka miki salak ɗin"
"A'a kar ka yanke hannu"
Ya ce "Ki kawo zan iya" Ta tsuke fuska ta kalle shi ta ce "Saboda sauƙi ya samu, kana iya fitowa da kanka yanzu, shi ne za ka din ga damuna ko?"
Ya yi murmushi, ya zauna a gefe yana kallon ta, da ta ɗaga ido, sai su yi ido huɗu da shi, sai ya yi mata murmushi.
Su na cikin cin abinci, ya ce "Ki na kiran Ummi?"
"Ba na samun ta, ita ma ta kira ni wayar ba na ji. Uwani ta ce haka garin nan yake babu network, sai a yi kira fiye da sau goma ba ka samu mutum ba.
"Idan na ƙara jin sauƙi, zamu je mu gaishe ta, mu yi mata godiya"
Ta ce "Alhamdillah, lallai sauƙi ya samu."
Ya ce "Eh, ina jin hakan a jikina nima. Mu je waje na ɗan tattaka na ga gari"
Nana ta faɗaɗa murmushinta ta ce "Allah abin godiya, wallahi Sayyid da har na fara fitar da rai da kai, na karaya sosai wallahi" Cikin murna ta saka hijjabinta, suka fita. Su na tafe a hankali ta kalle shi ta ce "Gaskiya na yi mamaki, ashe da gaske magungunan sarkin Baka yana yi"
Ya tsuke fuska ya ce "Na gaji da jin zancen Sarkin Bakar nan"
Nana ma ta yamutsa fuska ta ce "Sayyid ka yi haƙuri, amma na yi farin cikin yadda maganin da na gani a gurinsa ya yi maka aiki. Ina yi masa fatan idan a kan daidai yake, Ubangiji Allah ya ƙarfefe shi ya dafa masa, ko dan saboda yadda yake taimakon mutane. Idan kuma a kan kuskure yake Ubangiji Allah ya ganar da shi, ya ba shi ikon tuba kafin lokaci ya ƙure masa."
Sayyid ya yi mata banza, suka ci gaba da takawa a hankali su na zagayawa.
Wani irin sanyi ne ya fara ratsa Nana, ganin Sayyid ya durfafi wata hanya, ta kuma kasa ce masa uffan, balle ta hana shi. Su na tunkarar gurin, ƙirjinta na bugawa da sauri da sauri.
Wata irin narkekiyar bishiyar kuka suka tarar a gurin mai ban tsoro. Yanayin yadda take ɗauke da wasu irin murɗaɗɗun rassa, da yadda murtuka-murtukan jijiyoyinta suka huda ƙasa suka mamaye gurin. Ga wani irin ƙaton kogo a jikinta, hakan ya nuna daɗewar da bishiyar ta yi da wanzuwa a gurin.
"Asma'u" ya kira sunanta kai tsaye. Ta kalle shi cikin matsanancin mamakin yadda ya kira sunanta na yanka kai tsaye. "Ji nake yi kamar na san gurin nan"