Buzu book 2 complete - Chapter 8
Buzu book 2 complete Chapter 8: Buzu book 2 complete Chapter 8. Jiki a sanyaye Nana ta ce "Nima haka, amma ni dai na san ban taɓa zuwa gurin nan ba, amma…
3,373 words
Jiki a sanyaye Nana ta ce "Nima haka, amma ni dai na san ban taɓa zuwa gurin nan ba, amma ina jin kamar na san gurin, amma dai... Sai kuma ta yi shiru bayan da gurin ya gauraye da duhu aka yi wata irin walƙiyya, haske ya mamaye gurin. Tsohon nan ta gani a tsaye, riƙe da sandarsa ya zubo wa Nana idanunsa marasa kyan gani. Jikinta ne ya ɗau kyarma, ta ƙara rikicewa bayan ganin a hankali wasu halittu da take kyautata zaton ire-iren su Ƙaisar ne su na bayyana a bayansa. Tsohon ya kalle ta, ya buɗe baki ya fara magana. "Ina sake yi miki barka da zuwa, garin da kakanin kakaninki su ka durƙusa suka haifo matsalar da har abada ba za ta daina bibiyar zuriyar su ba. Zan ci gaba da azabtar da rayuwarki, za ki ci gaba da biyan bashin nan, ko bayan ranki, muddin aka ci gaba da samun haihuwar masu irin tauraronki."
Yana rufe bakinsa, ɗaya daga cikinsu da Nana take kyautata zaton jininsin mace ce, saboda yanayin wani irin tsohon mayafi da ta yafa a kanta. Ta tunkaro Nana gadan-gadan. Tana zuwa matar, ta hankaɗa Nana ƙasa, sauran suka rufu a kan Nana, su na zira hannunsu a mararta, su na ciro gudan jini.
"Ya hayyu ya ƙayyum ya Allah. Allah ka kawo mini ɗauki, Sayyid, Sayyid, Sayyid ka tashi" Ta yi maganar tana jijjiga Sayyid da yake kwance a gefen ta yana bacci.
Ya ja jikinsa ya tashi ya ce "Ma viee lafiya kuwa?"
"Sayyid marata ciwo take yi. Sayyid marata. Sayyid babyna. Ba na son na rasa jaririna a wannan karon, Dan Allah ka taimake ni"
Cikin rashin fahimta ya ce "Meyafaru ne?"
"Marata ce take ciwo, Sayyid ba na son cikina ya zube, ina son jaririna Sayyid ciwo marata take yi sosai" Ta yi maganar tana zubar da hawaye. Ya saka hannunsa a mararta, ta saka hannayenta ya dafe hannunsa tamkar hakan ne zai hana cikin zubewa.
Ya ce "Ki yi Addu'a" Kawai ta jinjina kai, amma Addu'a kam, ko ɗaya ba ta zo kanta ba, dan ta manta komai daga cikin kanta.
Cikin rauni Nana ta ce "Sayyid fitsari nake ji, ya matse ni"
Ya ce "To mu je ki yi"
Ta girgiza kai ta ce "A'a ba na son na je na ga jini ya zubo, cikin ne zai zube"
Ya ce "A'a ba za ki gani ba" . Ta miƙe ya kama hannunta, ya haska fitila har banɗaki, su na zuwa a tsorace ta yi fitsarin, sai dai tana yi sai ga jini. Wani irin kuka ta fashewa da Sayyid. Ta miƙe jikinta yana rawa.
Ya rungume ta ya ce "Ki yi haƙuri, kin ga dare ne, ki daina kuka. Kuma idan za ki yi ɓari, jinin da ki ke zubarwa ya fi wannan kin manta?"
"A'a idan jini ya fara zuba, shikenan ciki zai zube"
Ya ce "A'a, ba haka ba ne, ai bai zuba da yawa ba" Ya lallaɓa ta da ƙyar, ta gyara jikinta, ta ɗauraye jikinta, da banɗakin su ka koma ɗaki.
Karatun Alkur'ani ya kunna a waya, ya ajiye a gefen katifar da suke kai, kamar yadda ya ga tana yi, a duk lokacin da su ka shiga yanayi na tsoro.
Suka kwanta yana ɗan shafa ta, cikin sigar rarrashi.
A hankali ta ce "Sayyid"
"Na'am"
"Da gaske mun fita ɗazu ko?"
"Eh mun fita"
"Mun je can bayan gari, har ka ce mini kamar ka san gurin?"
"Eh haka aka yi, mun je"
Ta sake cewa "To daga nan meyafaru?"
"Faɗuwa ki ka yi, na riƙe ki muka dawo gida. Tun da muka dawo kuma ki ke bacci"
Ta yi shiru ba ta sake cewa komai ba, ta ƙara lafewa a jikinsa cikin tsoro. Yau ma kwana suka yi, tana gane-gane da jin abubuwa daban-daban masu razanarwa. Wannan bafulatanar matar ce, ta ƙara zuwa ta tsaya a saitin tagat Nana tana kiran ta, a kan lallai sai ta fito ta ga yadda suke gudanar da bikin girka. Nana ta ƙara rintse idanunta tare da ƙanƙame Sayyid.
Da safe ta tashi da wani irin nauyin jiki, ga sanyi da ta kasa daina ji. Ta duba ta ga ba ta kuma ganin jinin nan ba. Ta yi wanka ta rama sallolinta, sai dai Sayyid bai tashi ba. Da ƙyar ta samu ya yi alwala ya yi salla.
Ta gaishe shi, amma bai yi magana ba sai kallonta da yake yi. Hakan ya sanya ta fuskanci maganar ta ɗauke. Ta tambaye shi za ta fita, amma bai ko ɗaga kai ya kalle ta ba. Ta saka hijjabi ta fita ta bi 'yan matan gidan Uwani gona roron gyaɗa a gona.
Allah ya taimake ta, ta samo da yawa ta zo tsakar gida ta baje ta domin ta sha iska.
Ta ɗora musu Abinci, ta kammala ta fara dafa masa maganinsa, kawai ta ga ya fito daga cikin ɗakin. A zaton ta, ko banɗaki zai shiga, ta tashi da nufin kai masa ruwa, kawai ta ga ya nufi fita waje.
Da sauri ta bi shi tana faɗin "Sayyid ina za ka je ne haka?" Ya yi mata shiru yana ƙoƙarin buɗe ƙofar. Ta riƙo hannunsa, amma ya waiwayo fuskarsa a ɗaura kamar bai taɓa dariya ba, saka hannu ya hankaɗe ta, ta faɗi a gurin, ya saka kai ya fice daga gidan. Da gudu ta shiga ɗaki, ta ɗaukko hijjabi, ko takalmi ba ta saka ba, ta bi bayan sa. Ga yamma ta yi liƙis, hanya babu kowa, ta ga ya nufi hanyar inda wannan bishiyar ta kuka take.
"Sayyid dan Allah, dan Allah kar ka koma gurin nan. Me za ka je ka yi?" Sai dai tamkar ba mara lafiya ba, saboda yadda yake sauri.
Sai da ta ɗan haɗa da gudu, Saboda saurin da yake yi, amma ta ji gefen mararta ya ƙulle. Ta daure ta cim masa.
Babu tsammani ta furta "Bismillah wa hifzan min kulli shaiɗanin marid." Aya ta bakwai cikin suratul saffat, kamar yadda Malam Auwal ya taɓa cewa ta yawaita nanata ayar. Gaba ɗaya ta shafe a cikin kanta, sai da ta faɗo mata yanzu. Tana karanta ayar, ta riƙe hannunsa ya ja ya tsaya ya yi shiru ya sunkuyar da kai.
"Mu koma gida" ta yi maganar tana jan hannunsa, tamkar raƙumi da akala, ya bi ta suka koma gida. Allah ya taimake ta, babu wanda ya gan su har su ka isa gida. Ta rufe ƙofar.
Su ka shiga ɗaki, ta kunna fitila ta kalli Sayyid cikin damuwa ta ce "Sayyid me yasa ka fita? Me za ka je ka yi a wajen da?" Ya yi shiru ya sunkuyar da kansa ƙasa fuskarsa babu annuri a ciki.
Ba ta sake ce masa komai ba, ta fita banɗaki ta yi alwala, ta dawo ta yi salla, amma ta ga ba shi da niyyar tashi ya yi.
"Sayyid, ba ka yi salla ba fa" Nan ma bai kula ta ba, dan haka ba ta sake magana ba, ta zubo masa Abinci ta zo gaban sa ta ajiye. Ta tashi ta ninke hijjabinta, tana waiwayowa, ta ga ya kifar da Abincin ya tarwatse a tsakar ɗakin, yana wani irin huci.
"Sayyid wai meye haka ne? Idan ba ka cin abincin sai ka zubar mini a ƙasa?" Sai dai tana rufe baki, ya wulwula kwanon ya yi jifa da shi guri ɗaya. Ya miƙe ya fara fatali da kayan ɗakin. Take Nana ta fuskanci ba lafiya ba. Jiki a sanyaye ta rakuɓe tana kallon sa. Tana tunanin yanzu kuma abin har ya kai ga haka? Ba ta yi yinƙurin hana shi ba, ya yi kaca-kaca da ɗakin, ya fita tsakar gida ya nemi guri ya kwanta a dandaryar ƙasa. Inda ta yi wa Allah godiya ba su da maƙwabta, da kowa sai ya san abin da ya faru. Haka ta durƙusa ta hau aikin gyaran ɗakin, ta kintsa abin da za ta iya kintsawa. Ta dawo tsakar gida inda yake kwance. Ta durƙusa a kan sa, ta dafa shi ta ce "Tashi mu je ka kwanta a ɗaki, nan akwai sauro kuma ƙwari za su cije ka"
Da ƙyar ya tashi, suka koma ɗaki, ya nemi guri ya kwanta a ƙasa. Kawai Nana ta zauna ta zura masa ido, cikin matsananciyar damuwa, duba da yadda take maganin ƙaba amma kai na daɗa kumbura. A haka dare ya tsala, ta gaji ta kwanta a gefen sa, zuciyarta fal da damuwa. Bacci na ƙoƙarin ɗaukar ta, ta ji tasowar guguwa ta buɗe idonta, ta gan su kwance a cikin sahara, ga yashin saharar na wani irin hanƙoro iska za ta mamaye su. Ta saka hannu ta rungume shi saboda guguwar saharar. Sautin tsohon nan ta ji yana wata irin dariya. Ji ta yi an hankaɗa ta, sai da ta wuntsula ɗakin gauraye da duhu, amma ta ga alamun Sayyid ne zaune a kan katifa shi ne ya hankaɗa ta. Ya tashi ya koma bakin ƙofa ya yi zamansa. Da kyar ta sake lallaɓa shi, ya koma ya kwanta. Ita ba ta sake komawa bacci ba, ta yi alwala ta zauna tana tasbihi har aka yi sallar asuba. Sai dai fafur ya yi salla ya ƙi yi. Ya nemi guri ya zauna ƙyam yana kallon ta.
Ta dama masa kunu, ta soya fanke, ta zo ɗaki ta zauna a gaban sa. Ta ce "Ga kunu ka sha, amma dan Allah kar ka zubar Sayyid ka ji?" Ta yi maganar tana miƙa masa kofin kunun. Sai ya miƙo hannun hagu zai karɓa. Ta janye kofin ta ce "Hannun dama dai, wannan hannun za ka bani" Ta yi maganar tana nuna hannun damansa, amma bai miƙo mata ba, ya zura mata ido.
Ta kai hannu ta janyo hannun nasa, dan ta damƙa masa kofin kunun, amma ta ji hannun a ƙame ƙam. Ta sake ƙoƙarin janyowa, amma ta ji tamkar tana jan itace.
Ta kalli hannun sosai, sai ta ga shanyewa ya yi.
Gabanta ya yi wata irin mummunar faɗuwa, ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Sayyid me ya same ka haka? Me ya samu hannunka? Ya Allah!" Ta yi maganar tana kuma ƙoƙarin ganin ta miƙar da hannun nasa, amma hannun yana maƙale, kamar an tsotse shi.
Ya sunkuyar da kai ya yi shiru, fuskarsa ɗauke da damuwa. Ta aro jarumta, ta matsa daf da shi, ta ɗebo kunun ta kai bakinsa. Amma ya tsaya yana kallonta, bai buɗe bakinsa ba.
"Buɗe baninka na baka" Ta yi maganar tana ƙoƙarin danne hawayen da ke ƙoƙarin ƙwace mata.
A hankali ya buɗe bakin, sai ta ga shi ma bakin ya karkace, yawu na ƙoƙarin zubowa. Kawai ya rufe bakin hawaye ya fara gangarowa daga cikin idanunsa. Ta ajiye kofin kunun ta rasa abin yi. Kawai rungume shi, ta fashe da matsanancin kuka, sai da ta yi iya yin ta. Sannan ta cika shi, ta share masa hawayensa. Ta fara ƙoƙarin ba shi kunun, sai dai tana ba shi, ya haɗiye wani kuma ya zubo. Ta na yi tana goge masa wanda yake zubowa, ta gama ba shi, ta kama hannunsa su ka je waje, ta taimaka masa ya yi alwala. Ya dawo ya rama sallolin da ta gaya masa ana bin sa. Sai dai ba magana ga hannu a maƙale, da ta kalle shi sai ta ji hawaye ya cika mata ido. Ganin yana gyangyaɗi a zaune, ya sanya ta saka masa pillow ya kwanta, ta saka hijjabi ta fita.
Tafiya mai nisa ta yi, ta je ta samu wani chemist, bayan sun gaisa ta ce "Dan Allah malam, idan babu damuwa, Bp nake son mu je ka gwadawa mijina a gida"
Ya kalle ta ya ce "A ina ne?"
"Cikin Budu ne, nan unguwar maharba"
"Taɓ gaskiya da nisa gurin nan ba kaɗan ba, ba zan iya zuwa ba sai dai ki je ku zo tare a yi masa"
"Wallahi da zai yiwu, da ba zan zo na roƙe ka ba, yana kwance babu lafiya ka taimaka mini dan Allah"
Ya ce "Gaskiya kin san cajin zuwa gida ma ka yi wa mutum abu daban yake, sai dai idan za ki ba ni dubu biyu"
Nana ta ce "Eh na yarda mu je zan baka in sha Allah" Ya rufe chemist ɗin ya bi Nana.
Su na zuwa gidan, Nana ta shiga ta tarar da shi a zaune ya tashi, ta ce "Sayyid kar ka ga na fita ban gaya maka ba. Na je na samo wani ma'aikaci ne, ya zo ya duba jininka a gani, idan jinin ne ya hau ya sanya hannunka ya shanye, mu tafi Asibiti. Idan kuma ba shi ba ne, sai mu san abin yi." Bai ce komai ba, ta yi wa mai chemist magana, ya shigo ya gwada jininsa. Ya gwada ya kalli Nana ya ce "Jininsa bai wani hau sosai ba, 140/90 ne" Ajiyar zuciya Nana ta yi. Ta ce "A ganinka wannan hawan zai iya sanya masa shanyewar hannu?. Ya girgiza kai ya ce "Gaskiya ba na tunanin haka, amma ban tabattar ba tun da ni ba likita ba ne ba. Amma a shekarunaa bana tunanin jinin 140 zai shanye masa wata gaɓa a jikinsa, amma dai ku je Asibiti a ƙara bincikawa" Nana ta ba shi kuɗin sa, ta yi tai masa godiya. Ta koma ɗaki ta zauna ta yi shiru, tana tunanin ko Uwani za ta tambaya, idan akwai wani mai magani, ta raka su, sai dai ta fasa saboda akwai sauran ɓurɓushin jahilci a tattare su, ba ta son surutu kuma tana tsoron a kai su gurin da ba shikenan ba.
****
Alhaji Fatuhu kuwa kamar yadda ya matsa, sai da aka sallame shi ya koma gida. Gidan nasa ma wani abokin kasuwancinsa ne ya saya, ya bar shi a ciki ya zauna ya bar masa aro.
Sagir yana kwance a kan gadonsa, yana kaɗa ƙafa ya ƙura wa screen ɗin wayarsa ido. Yusra ce zaune sanye da doguwar rigar material, kanta ko ɗan kwali babu, dogon gashin kanta ya sha gyara. Tana ta zuba masa surutu. Har mamaki yake yi, yadda Yusra ta zama mai ɗan karen surutun tsiya, wanda da ba haka take ba.
"Ya ka yi shiru ne?" Ya wani lumshe ido ya ce "Ina jin ki ai".
"So talk, ka yi magana mana" ta yi maganar tana cika bakinta da guggurun hannunta.
"Ina ga zan shigo Abuja mu haɗu very soon in sha Allah" wata irin zabura ta yi ta ce "Are You serious, dan Allah da gaske?"
"Da gaske nake, zan zo na ganki, amma ki na ganin babu matsala a zuwan nawa? Kar a yi miki faɗa fa, ba zan ji daɗi hakan ba"
Yusra ta ce "Babu wata matsala, ba za a yi mini faɗa ba, ai ba na tare da su Mami, ina gidan Anty Sumayya. Dan Allah ka zo"
Sagir ya yi murmushi ya ce "Kin yi missing ɗina ne?"
Ta gyaɗa masa kai tana murmushi.
"Shikenan, i miss you too, ban taɓa tunanin ma za ki neme ni ba, na za ta ki na jin haushina haryanzu, amma in sha Allah zan shigo, zan sanar miki lokacin da zan shigo na zo na ganki" ya yi maganar yana kashe mata ido.
Shukura ce ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, a burkice ya kif wayar yana kallon ta. Ƙarara yanayinsa ya nuna alamun rashin gaskiya, amma ta share shi, ta haye kan gadon ta ja bargo ta lulluɓe jikinta. Ya matsa kusa da ita yana ɗan shafa ta ya ce "Sweetheart, ya na gan ki kamar a fusace ne? Lafiya dai ko?"
"Lafiya ƙalau" ta amsa a taƙaice. Ɗan shiru ya yi yana tunanin ko dai ji wayar da yake yi ne? Amma a yadda ya santa da azababben kishi, da zargi da ta ji sai ta yi masa magana. Sai dai ya bar abin a haka bai matsa mata da tambayoyi ba gudun kar su yi faɗa.
Tana ankare da take-taken Sagir, na rashin gaskiya. Sai dai ita yanzu ba wannan ne a gabanta ba, bin diddigin mutuwar ɗanta take son yi. Dan haryanzu zuciyarta ta kasa amincewa da natural mutuwa ya yi. Domin haryanzu tana mafarke-mafarke marasa daɗi da mahaifinta da kuma Doctor Sharif.
**** Aka shiga sati na biyu, Sayyid yana cikin wannan yanayi na rashin lafiya, kuma hannunsa bai saki ba, yana nan a maƙale. Ga hauka da yake yi tuburan wasu lokutan, wasu lokutan idan ya burkice sai ya shaƙe ta, ko ya hankaɗe ta ƙasa, sai dai ta yi ƙoƙarin kare cikinta. Ko kuma Ya ya ta watsi da duk abin da ya ci karo da shi, a ɗaki ko a tsakar gida. Wasu lokutan ma katangar ɗakin yake duka da kansa. Ya ƙi cin abinci ya ƙi shan magani, ba salla, komai sai dai ta yi masa cikin rarrashi da ban haƙuri. Tun tana jin tsoron ya yi mata wani abin, har ta daina ji, ta zuba wa sarautar Allah ido. Sannu a hankali ta rage yawan amai, sai dai zazzaɓi da rashin son cin abinci da take yi, hakan ya sanya ta tabattar da cikin jikinta bai fita ba haryanzu. Sai dai ba ma ta cikin nutsuwar da za ta nemi inda Asibiti yake ta je, ta tabattar da halin da suke ciki ita da jaririn saboda tashin hankalin da take ciki. Yanayin yadda uwani ta lura kamar Nana na ɓoye wani abu, ya sanya ta daina zuwa gidan,ta rage aika yara ma. Sai dai lokaci lokaci, ta kan aika mata da Abinci. Haka sauran 'yan uwansu na garin ma, su kan aiko mata da sha tara ta arziki saboda su na tausayin Nana, sun san mijinta a kwance yake babu lafiya. Yawon roro a gona kuwa yanzu Nana ta ƙware, ranar kasuwa ta je ta sayar da abin ta. Kasancewar ranar Asbar kasuwar garin take ci, sai ta tashi ta yi fanke da sassafe, jikan Uwani Haladu, ya kai mata kasuwa. Ko ta dafa masa zoɓo ta ƙuƙƙula ya tafi da shi. Idan ta gama komai kuma, ta bi yara gona roro.
Dare ya tsala, amma Nana tana zaune tunkurkur, wuni Sayyid ya yi yana wani irin nishi, ga wannan azababben zafin jiki da yake fama da dhi. Tana zaune tana tunani, tana jin yadda mararta take motsi, cikin jikinta yake motsawa. Ba ta da sauran wanda za ta kai kukanta bayan Ubangiji. Ta fara tunanin ƙoƙarin tara musu kuɗin mota, su tafi Nijar, neman danginsa, sai dai idan sun je Nijar ɗin ina za su nufa? Babu tsammani ta ji Sayyid ɗin ya laluba cinyarta, ya kwantar da kansa. Ta shafa gashinsa ta ce "Sayyid" bai amsa ba, sai dai ya riƙe hannunta. Hakan ya tabattar mata da ya dawo hayyacinsa ne. Haka ta tashi a cikin daren ta tsiyayo ruwan zafi, ta ba shi shayi ta yi masa wanka suka kwanta, ta lulluɓe su da bargo. Sheshsheƙar kukansa ta ji, duk da yadda ta san ya daɗe yana dauriya, da son ɓoye gazawarsa, sai dai ta ga hakan a idanunsa.
"Sayyid idan ka na kuka, ni kuma ya zan yi kenan? Dan Allah ka daina" ta yi maganar muryarta na rawa. Ta din ga shafa bayansa a hankali, har ya yi shiru, bacci ya ɗauke shi. Sai dai tun daga wannan, haka aka sake shafe kwanaki biyu, bai sha ko ruwa ba. Dama rashin maganarsa ya daina damunta. Ga shi yau abin ya tashi sosai, haukan yake yi da gaske. Ta rufe shi a gidan, ta je ta samo gasara a gidan Uwani, ta dawo ta dama masa kunu. Ta nufi ɗakin cike da fargaba tare da fatan ya samu ya sha ko kaɗan ne. Sai dai ta ji wata irin guguwa ta taso mai ƙarfi.
Jin yadda guguwar ta taso da ƙarfinta, take fatali da duk abin da ta ci karo da shi a tsakar gida, ya sanya ta tashi da azama, ta fara ƙoƙarin rufe ƙofar katakon da take ɗakin. Sai dai tana danna ƙofar guguwar ma na danno ƙofar.
A take ta fara karanto "A'uzubillah, Allahumma inni as'aluka khairiha wa a'uzubika min sharriha. Allahumma inni as'aluka khairiha wa khairi ma fihi, wa khairi ma ursulat bihi, wa a'uzubika min sharriha wa sharri ma fiha, wa sharri ma urisilat biha" take ta ji nauyin da ƙofar ta yi ya ragu, ta samu ta rufe ta, ta juya da sauri ta nufin gurin da yake.