Kenza eBookz

Buzu book 2 complete - Chapter 9

Buzu book 2 complete - Chapter 9

Buzu book 2 complete Chapter 9: Buzu book 2 complete Chapter 9. Da fari yana zaune a guri ɗaya ne, amma yanzu Jifa yake da kayan ɗakin da hannu ɗaya, da…

3,349 words

Da fari yana zaune a guri ɗaya ne, amma yanzu Jifa yake da kayan ɗakin da hannu ɗaya, da sauri ta fara bi tana tattarewa, cike da damuwa. Cikin siriryar muryarta ta ce "Sayyid za ka ji wa kan ka ciwo, ka saurara ka saurari muryar matarka, ni ce a gare ka, ni ce fa, Husnan ka ce fa" Ta ƙarasa maganar a raunane, duk yadda take ƙoƙarin tare shi ta kasa, domin ta gama firgita da lamarinsa. Tun safe take fama da shi, ya ƙi cin komai, kuma ta kasa sarrafa shi duk rarrashin da ta yi a banza. Cikin matsananciyar damuwa, hawaye na bin kuncinta ta ce "Ubangiji ka dubi mijin Nana, ka cire masa zafi da raɗaɗin da yake ji, ka saita masa tunani da ƙwaƙwalwarsa, ya yi rayuwa mai cike da nutsuwa da farin ciki irin na sauran mutane" sai kuma ya tsaya cak, ya juyo yana kallonta. Ta ƙarasa gurinsa, ba tare da fargaba ba ta riƙo hannunsa cikin nata jikinsa zafi sosai. Ta kalli cikin idanunsa sai taga yana birkice mata yana rikiɗewa kamar ba Sayyid ɗin ta ba, idanunsa har wani hayaƙi yake fitarwa, gaba ɗaya kaminsa sun sauya. Ta lallaɓa ta zaunar da shi, Ta yunƙura zata tashi, domin ta ɗaukko kununsa ta sake jarraba ba shi, ta ji ya cafko ta yana wani irin sambatu bakinsa na kumfa da dalalar da yawu, da alama magana yake son ya yi mata. Rashin ƙarfin jiki ya sanya ta faɗa jikinsa. Ya ƙanƙame ta sosai, saboda zafin da yake ji, ita kuma jikinta sanyi ƙalau. Ita ma jikinta ya ɗauki rawa, ta lafe a jikinsa ta kwantar da kanta a ƙirjinsa tsawon mintuna, jin ya ɗan nutsu jikinsa ya rage zafin ya sanya ta zare jikinta a hankali.

Ta ɗaukko kofin kunun da cokali, sai wani ɗan ƙaramin tsumma, ta zauna a gabansa ta ɗebo kunun a cokali ta kai bakinsa, sai dai ya tsaya yana bin ta da ido, kamar ya ga baƙuwar halitta, ta buɗe nata bakin, ya kalleta shi ma ya buɗe nasa. Ta fara zuba kunun a bakinta ta haɗiye, sannan ta zuba masa a bakinsa shi ma. Ya haɗiye sai dai wani na biyo gefen bakinsa, bai haɗiye duka ba. Tana bashi tana goge masa wanda yake zubowa. Sai da ta tabattar ya ƙoshi, sannan ta goge masa bakinsa. Ta ɗauki kofin ta nufi ƙofa ta buɗe a hankali ta ga an daina iskar, ta fita da kofin ta ajiye, ta tattara abin da guguwar ta watsa sannan ta dawo ɗakin.

Jiki a sanyaye, ta zauna a gabansa tana ƙare wa kyakyawar fuskarsa kallo. Da ƙyar yake jan numfashi yana saukewa. Ta sanya hannayenta biyu, ta gyara masa gashinsa, da ya rufe masa gefen idonsa, ta saka idonta a cikin nasa, cikin rauni da karaya, idanunta na zubar da hawaye ta motsa bakinta, ta fara magana

"Sayyid, dan Allah ka yi magana ko na ji daɗi, wannan karon ka daɗe ba ka ce mini komai ba. Da na sanya ran ka fara samun lafiya, amma kullum lamarin nan gaba yake yi. Ka gaya mini wane ne kai? Daga ina ka ke? Ina zan samu danginka da 'yan uwanka, wataƙila kai naka dangin ba za su guje mu ba, za su karɓe mu, tare da sarƙar da ta haɗa ƙaddarorinmu wuri guda, duk da ban kasance ɗaya daga cikinku ba, ni fatana a nema maka magani ka samu lafiya, ba na son ganin ka cikin wannan mummunan yanayin, idan na ci gaba da ganain ka a haka, zuciyata za ta iya bugawa. Dan Allah ka yi magana" Ta yi maganar wasu hawayen na zirarowa daga cikin idanunta.

Ayshercool 08081012143

58 Ya haɗiye wani irin yawu, da yake yi masa zafi a ƙirjinsa, yayi ƙoƙarin ɗago hannunsa na dama, sai ya tuna ya riga ya shanye, ba ya iya komai da shi. Ya buɗe baki da nufin ya kira sunanta, saboda tasiri da kuma ciwon da kukanta yake yi masa a zuciyarsa, amma ya gaza bakin ya karkace yawu ya fara zubowa daga bakin nasa, maimakon kiran sunanta da ya yi yinƙurin yi. Tana kuka, ta sanya tsumman da tayi amfani da shi wurin ba shi abinci, ta goge masa bakinsa. Ba shi da zaɓin da ya wuce, ba wa hawayen da yake maƙale a cikin idanunsa damar zubowa, ko shi ma ya samu sassauci abin da yake ji. A hankali ya hura mata iskar bakinsa a fuskarta, a take ta silale ta faɗi a jikinsa. Ya sanya hannunsa mai lafiya, ya rungume ta, ya ci gaba da kuka. Jikinta gaba ɗaya ya saki.

Ƙaisar ta gani a gurin haɗe-haɗen magungunan sa, yana ta haɗa wani abu a cikin kwalba. Zuciyarta ce take ta azalzalarta, da ƙoƙarin ingizata, sai dai ba ta yi magana ba.

Babu tsammanni, ta ji ya fara magana "Zaɓi ɗaya ya rage miki, a halin yanzu, ko dai ki yadda da abin da na zo miki da shi, ki rungumi ƙaddararki, ko ki na kallo Buzun nan zai mutu, domin ba zai taɓa tuna waye shi ba har abada, muddin Giyaz yana tare da shi. Dan ba na tunanin akwai wanda zai iya raba shi da shi. Idan har bai iya tuna waye shi ba, shikenan kin ga ba ki da wata makoma. Abu ɗaya zai sanya a wannan karon na bar miki abin da yake cikinki, duk da ba ni da tabbacin zai zama mai cikakkiyar lafiya ko akasin haka, Giyaz da muƙarrabansa sun riga sun fara taɓa shi a cikin ki. Kin san meyasa ban ƙarasa lalata wannan cikin ba?" Bai jira ta ba shi amsa ba ya ce "Saboda zan so na ga yadda za ki yi, a lokacin da ɗan zai amsa sunan shege, kuma ba za ki iya hanawa ba, domin ba ki da hujjar kare kanki. Idan Buzun nan ya rayu bai san waye shi ba, ga kuma nakasa. Idan kuma ya mutu suwaye dangin baban ɗan ki? Daga ina yake? Suwaye ahalinsa? Kin san ku a jinsinku na bil'adam da uba ake ado ba riga ba. Babu wanda zai damu da wacece ta haifi mutum, amma za a damu da waye ubansa meye nasabarsa? Tun da ki ka zo garin nan, zuriyarmu suke alwashin yadda fansar su za ta kasance a kan ki. Kafin zuwa wannan ƙadamin babu abin da ban gaya miki ba, na gargaɗi. Dan haka dabara ta rage ga mai shiga rijiya"

Cikin kuka Nana ta hau girgiza kai ta ce "Ba zan yi bori ba Ƙaisar, ba zan yi shirka da Allah ba. Babu tsanani ko wahalar da za ta sanya na rabu da imanina. Amma na rasa gaba na rasa baya, ba dan ina neman taimakon ka ba, ko ka kawo mini ɗauki ba. Na san Ubangiji Allah shi zai taimake ni. Amma dan zatin Allah idan ka na da hannu a ciwon Sayyid, ka yi mini rai ka rabu da shi, shi ne kaɗai duniyata. Ina matuƙar tausayin sa, ban damu da jinya da nake yi ba, wahalar da yake sha ta isa haka. Idan kuma laifikan zuriyarmu ne suke shafar sa, dan Allah ku yi haƙuri ki ƙyale shi haka"

Cikin sautin muryarsa mai ban tsoro, da ya kan yi amfani da ita, idan ya so razana ta, ko yi mata magana mai muhimmanci ya ce "Na sha gaya miki na maimaita miki, daga lokacin da ki ka fara bani umarni, kin yadda kin amince da buƙata ta ne. Ba ni da hannu a ciwon mijinki, kuma bai ya cikin zuriyar ku, sai dai ƙaddara mai ƙarfin gaske, ta haɗa ku tarayya guri guda. Amma muddin ki na son ya warke daga wannan rashin lafiya, ba ma iya haka ba, ya tuna waye shi, sai kin karɓi ƙaddararki.".

Nana ta sake marairaicewa ta ce "Ba zan iya shirka ba, ba zan iya zama 'yar bori ba. Zan jure jarrabawata komai zafinta amma ba zan yadda rasa imanina ba"

Ƙaisar ya ce "A cikin biyu dole abu ɗaya ya faru, tunda kakaninki su suka ƙyanƙyashi wannan matsalar. Na yi iya ƙoƙarina gurin dakatar da ita a wancan lokacin, amma ta sake tasowa a wannan karon. Dole a cikinku ɗaya zai warke ya rayu ɗaya ya mutu a haka, dan babu alamar Giyaz zai sassauta wannan mummunan ƙudirin nasa a kan zuriyar ku. Gefe ga aikin da ya karɓa yake yi a akan mijinki, ko dai ki ci gaba da rayuwa da shi, laifukan ku na shafar sa, ko kuma ki yarda ki karɓe ni a matsayin hadiminki ki yi abin da nake so, ni kuma na san yadda zan yi da Giyaz, na baki maganin da mijinki zai warke"

"Ta yaya? Me yasa sai ni? Me yasa ni zan biya zunubin da lokacin da aka aikata shi ba na nan, zunubin da zamanin da aka aikata shi, ya yi nisa da nawa zamanin? Me ya sa kakannina suka zaɓi zama 'yan bori? Suka gada mini wahala da masifa take ta bibiyar rayuwata. Na zama mujiya a cikin mutane, duk inda na tsuguna sai wata masifa ta afku, da za a jefa mini zargi, kasantuwata ni ba mutum ba ni ba wani jinsi daban ba? Me yasa zan girbe baƙar shukar da ban san a lokacin da aka dasa ta ba? Ina son mijina duk da daga ni har shi, ba mu san waye shi ba. Duk da Nijar ba ɗaki ɗaya bane ba, ba kuma ƙaramar alƙarya ba ce ba, ƙasa guda ce, na gwammace zagaye ta neman ahalinsa na damƙa shi a gare su, da na ci gaba da zama da shi, mummunar ƙaddarata tana shafarsa, ko kuma na zama 'yar bori na ci gaba da gadar da wahala da masifa ga zuriyarmu, gara ko ma mene ne ya ƙare a kaina." Ta ƙarasa maganar cikin ƙaraji, tana kuka mai bayyanar da tsantsar baƙin cikin da yake binne a cikin zuciyarta.

*****

A hankali yake driving cikin nutsuwa, yana sauraren Jamila, da ke bin waƙar da ke tashi a cikin motar ƙasa-ƙasa, sai kuma ta yi shiru.

"Ya ki ka yi shiru kuma?" Ta ce "Au wai ka na ji na?" Abba ya ce "Eh mana, har kin fi masu waƙar ma iyawa" Dariya ta yi ta ce "Ka ji ziga, muryar ta su da aka tace, aka goge tawa kuma a haka, ka ke cewa na fi su iyawa"

"Au ba ki yarda ba? To shikenan ni dai na san kin fi iyawa" ya yi maganar yana parking ɗin motar a harabar gurin shan ice-cream ɗin. Abba bai taɓa soyayya ba, duk wannan abubuwan da yake yi wa Jamila, bai taɓa furta mata cewar yana sonta ba. Sai dai ita sarai ta gane sonta yake yi, so kuma ba na wasa ba. Sai dai tana mamakin yadda duk wannan abin da yake yi mata, ba ya iya nuna wa a gaban Hajiya Sa'a, hakan ya sanya ta fara tunanin ko dai yana da wata manufa a kanta ne. Sai dai ta lura halaye da ɗabi'unsa, sun sha banban da na Hajiya Sa'a, shi Abba akwai tsantseni, da gudun saɓa wa Allah. Dan duk da son da yake yi mata, sai da ya yi mata faɗa a kan shigar banza da ta kan yi wasu lokutan.

Ice cream su ka sha, yana ba ta labarin yadda ya yi karatu, da irin ƙalubalen da ya fuskanta na rayuwa. Su ka gama ya ɗauke ta ya mayar da ita gida.

Bayan ta shiga gida, Mama ta ce "Yauwwa ke nake jira dama, gas ya ƙare na kira wayar ki kuma ba ki ɗaga ba"

"Ina hanya ne, ga ATM ɗina, a bawa Nasiru ya je ya ɗuro. Har za ta shiga ɗaki sai ta fasa ta ce "Ni kuwa jama'a ina Nana ne? Wayarta ba ta shiga, shekaranjiya waccan ma na biya gidan da mijinta yake gadi, na ga kamar babu kowa a gidan"

Mama ta taɓe baki ta ce "Au ke ba ki san abin da yake faruwa ba dama?"

Ta tsaya tana kallon Mama ta ce "Mene ne yake faruwar?"

"Ai tuni aka kore su daga wannan gida. Ke ba zama ki ke yi ba ne shi yasa, suka koma unguwar su Ummi, to kin santa duk inda ta zauna bala'i ne yake bibiyar gurin, hatsaniya ta haɗa ta da matan gidan da suke, suka ce mayya ce aka tashe su. Ai nan Babanku ya je aka yi ta fafatawa, da ta kwaso jiki ta taho nan, wai za ta dawo mijinta babu lafiya, na ce bani da gurin jinya a gidan nan. Allah ya raba ni da masifa, ba za ta dawo mini ba, to ƙarshe dai wai yanzu tana ƙauye, can gurin Uwani a can take jinyar mijin nata"

Jamila ta yi sak, ta ce "Mama Nana tana ƙauye fa ki ka ce?"

"Eh mana, to idan ba ƙauyen ba ina za ta je? Tana can"

"To waye yake ba ta Abinci?"

Mama ta ce "Oho ina na sani?"

"Amma ya aka yi tsawon wannan lokacin ban sani ba? Yanzu ba kamar da ba ne, ban ji daɗin abin da ki ka yi ba Mama, bai kamata a kore ta ba a ce ta koma ƙauye da zama ba. Da ina nan ko na sani, da na kama musu wani gidan, gaskiya sai ta baro ƙauye"

"To ke ina ruwanki? Mene ne naki a ciki uwar Iya? Kina kallon irin baƙar azabar da na sha, a kan zamana da ita a gidan nan. Na meye za ki kuma jajubo mana ita. Gara ki bani kuɗin da za ki kama mata hayar na bawa ɗanLadi, ɗan autanmu ya tafi kasuwa da zaman banzae da yake yi, na yi masa aure tun da Allah ya sanya kuttun arziki ya fashe mana, ba ki kai kuɗi inda babu amfani ba"

Jamila ta dubi Mama ta ce "Wannan ɗan uwanki ne, sai ki nemi kuɗinki ki yi masa, nima 'yar uwata nake tunani. Haba Mama, ko wani Nana ta kashe miki ƙiyayyar ta isa haka ai. Ai yakamata a tausaya mata, miji babu lafiya ga zaman ƙauye, ita Uwanin za ta ɗauki nauyin Abincinsu ne? Tun da muka tashi a wahala muke a gidan nan, amma ita nata ya fi na kowa ma" Jamila ta ƙarasa maganar cikin damuwa, ta shige ɗaki, ta bar Mama da buɗaɗɗen baki.

***** Kallonsa Nana take yi, suna zaune sun yi juguum daga ita har shi. Bayan ta gama yi masa kitson zanen hannu guda takwas, ta yanke masa faratansa na hannu da na ƙafa. Kamar wadda aka mintsina ta tashi tsaye, ta kalle shi ta ce "Sayyid, bari na je na dawo" ya bi bayanta da kallo har ta fice.

Sai dai a ƙalla ta kai awanni biyu kafin ta dawo, ko da ta dawo ta tarar da shi ya haɗe fuska, ta yi shiru ba ta kula shi ba, ta koma tsakar gida. Ta laluba kayanta, ta ɗaukko wata takarda mai ɗauke da ayoyin ruƙiyya da na karya sihiri, sannan ta hura wuta a cikin murhu. Ta dawo tsakar gida ta zauna, ta fara da Bismillah da karanta Suratul fatiha, sai Suratul falaƙi da nasi. Ta karanta ayoyi biyar ɗin farko na Suratul Baƙara, ta fara karanta Suratul mulk, a hankali sai ta fara gani dishi-dishi, ta fara daina ganewa. Ta busa ayoyin a cikin ruwan, Sai ta ajiye takardar. Ta ɗauki wata leda da ta zo da ita, ta fito da man habbatussauda da jan Almiski. Saboda wauta sai ta buɗe miskin, ta kai hancinta, da sauri ta dungurar da shi a gurin, ta ja da baya, dan tuni ta ji jikinta ya fara tsuma. Sai da ta ɗan samu nutsuwa, sannan ta zazzaga tazargaɗe a cikin bokitin, ta kawo ganyen magarya guda bakwai, ta saka a leda ta ɗan bubbuga musu muciya, ta haɗa a cikin ruwan. Ta yi shiru tana tunani a ranta ta ce "Allah ya sa ba mai magani na zama ba, Ƙaisar bai mayar da ni 'yar bori mai bayar da magani ba, larurar Sayyid ta saka na fara koyi da magungunan sarkin baka." "Amma ai ayoyin Alkur'ani ki ka karanta, shi ma kuma Sarkin Bakar yana amfani da Alkur'ani" wata zuciyar ta tunatar da ita. Haka dai ta ci gaba da wasi-wasi. Can yamma, bayan ta tabbatar da ganyen magarya da tazargaden sun tsumu, ta ɗumama ruwa ta tsiyayi ruwan tofin ta tace ta haɗa da ruwan ɗumin, ta kawo man habbatussauda ta tsiyaya a ciki, ta kawo jan miskin nan da ta saka kwalbar a ruwan ɗumi, ya narke ta tsiyaya a ciki, ta ɗebo garwashi a kasko ta shiga ɗakin. Yana ganin Nana ya tashi zaune yana kallon ta, ya ga ta samu ƙyalle ta ɗaure hancinta da bakinta. Ta nufo shi ya ga ta hau tuɓe masa kaya, ya din ga bin ta da ido, ta bar shi daga shi sai gajeren wando. Hannunsa da yake maƙale take kallo cikin damuwa, ta shafa hannun. Sai kuma ta yi Bismillah ta fara shafa masa wannan ruwan. Tun daga cikin kansa. Girgiza kai ya fara yi, yana ture ta da lafiyayyen hannunsa, yana toshe hancinsa. Ya din ga girgiza kai jikinsa yana karkarwa bakinsa yana rawa, ya din ga wani irin gunji yana miƙa. Amma sai da Nana ta jiƙe shi da ruwan nan tsaf. Ta kunna kiran salla a wayarta. Ta kawo tazargade, da habbatussauda da ganyen magarya ta zuba su a kan garwashin nan, hayaƙin ya turnuƙe ɗakin, ta ajiye shi a nesa da shi kaɗan. Ta fice daga ɗakin ta kulle shi a ciki. Ta tafi ta din ga wanke hannunta. Wani irin jiri ya din ga ɗaukar ta, ga matsanancin ciwon kai, ɓari ɗaya da ya sanya take jin, tamkar kan zai yi bindiga ya rabe. Ta samu guri ta zauna a tsakar gida, ta dafe saitin zuciyarta da yake ta bugawa da sauri.

Bayan wasu mintuna, ta tashi ta je ta leƙa ta window, ta hango shi a kwance a ƙasa. A tsorace ta buɗe shi, ta nufe shi da sauri tana kiran sunansa. Gaba ɗaya ƙwayar idonsa baƙar ta ɗauke sai farar, ta durƙusa a kansa kawai ya miƙo hannu zai shaƙe ta, amma ta riƙe hannunsa. Hannun ya din ga rawa, ya sauke shi a hankali.

"Sayyid" tana ambatar sunansa, ƙwayar idonsa ta dawo ya kalle ta.

"Sannu Shugaba" hararta ya yi ya juya mata baya. Dariya ta fara yi ƙasa-ƙasa.

Ta ce "Haba Shugaba, ya ka juya mini baya, juyo ka kalle ni" ya ƙi juyowa. Ta tashi ta buɗe labule saboda yadda warin ita ma ya fara damunta. Ta ɗaukko tsumma, ta hau goge masa jikinsa, saboda ya daina warin miskin nan ita ma ba ta so. Ya tashi zaune, tana goge masa. Ta ce "Ko a yi wanka?" Ya ɗaga idonsa yana hararta, jikinsa ya koma jawur kamar wanda ya ƙone. Ta din ga ɓoye dariyarta, ta yi masa wanka, ya din ga sinsuna jikinsa yana yamutsa fuska. Ya shafa fuskarsa ta ce "Ka yi haƙuri, magani ne, ina son ran Ubangiji Allah ya kawo mana afuwa" Ya ture ta daga jikinsa. Amma ta manne masa ta hau cinyarsa ta zauna tana dariya.

Ta juyo da fuskarsa suna kallon juna, ta lumshe ido ta buɗe ta ce "Sannu shugaba" Ya jinjina mata kai. "In zubo Abinci ne?" Ya girgiza kai.

"Sai an yi salla?" Ya gyaɗa mata kai.

Ya yi sallar magariba da isha'i, ta zubo masa Abinci.

Washegari ma da sassafe, ta kuma rutsa shi tana shafa masa ruwan nan. Yau ma ture ta ya din ga yi yana girgiza mata kai. Ta kunna masa hayaƙi, ta gudu ta rufe shi a ɗakin. Haka ta sake tarar da shi, ya koma ja ya haɗa uban gumi. Ta yi masa wanka. Ta ba shi Abinci ya karya. Allah ya dafa wa Nana, ba su taɓa rasa abin da za su ci ba. Kuma haka take ta jujjuya kuɗin.

Sai da ta gama yi masa duk abin da zai buƙata, sannan ta tashi za ta yi wanka, tana tsaye daga ita sai bra da zani a ƙugunta, sai cika bakinta take da aya mai gishiri, ga cikinta ya ɗaga sosai. Ta waiwayo suka haɗa ido. "Ya ake kallona haka?"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull