Buzu book 3 complete - Chapter 10
Buzu book 3 complete Chapter 10: Buzu book 3 complete Chapter 10. "Ni ka mayar da ni gurin Nene, tun da ka samu lafiya"
4,492 words
"Ni ka mayar da ni gurin Nene, tun da ka samu lafiya"
"Yaushe na samu lafiyar? Ni ban samu lafiya ba tukuna, ba ki san me nake ji a jikin nan nawa ba" Yayi maganar yana ci gaba da shafa ta a hankali.
Cikin kulawa ya ce "Ba ki da lafiya rayuwata, jikinki da zafi. Ga shi haushina ki ke ji kin ƙi yadda da ni, balle na ce ko Muhsin ne zai samu ƙani"
Nana ta ci gaba da kuka, da ita kanta ta kasa tantance kukan me take yi. Ya yi murmushi ya ce "Yanzu kishin ne ya saka miki zazzaɓi ma viee?" Ture hannunsa ta yi tana kuka. Ya rungume ta a jikinsa ya ce "Da wasa nake miki, ban je ko ina ba fa da na bar ɗakin nan, a ƙofar ɗakin nan nake kwana, saboda idan mu na tare guri ɗaya akwai matsala ne. Ba kuma na son ɓata miki rai" Kwanciya ta yi sosai a jikinsa, ta saka hannu ta zagaye bayansa ita ma, ta yi shiru tana mayar da numfashi. Ya din ga murmushi yana shafa bayanta ya ce "Ki yi haƙuri, ba na ƙaunar na din ga aikata duk wani abu da zai sanya mini ke fushi da damuwa. Je vous aime ina son ki rayuwata".
Nana ta ɗago tana kallon ƙwayar idonsa, idanunta fal hawaye.
Ya jinjina kai ya ce "Da gaske nake Asmy, ina yi miki so mai tsananin gaske. A jinina nake jinki ba iya zuciyata ba"
"Sayyid"
"Na'am rayuwata"
"Kar na sakankance da kai, 'yan uwanka su ce ba zaka zauna da ni ba, ban san ya zan yi ba Sayyid. Ba gudunka nake dan na daina sonka ba, tsoro nake ji. Na azabtu ko a iya haka a tsaya, ina son na samu nutsuwar ƙwaƙwawa da zuciya. Na kasance da abubuwan da za su sanya ni farinciki" Ta yi maganar a raunane.
"Ke jaruma ce Asmy, kar wani abu ya baki tsoro, kai da fata komai zai faru ina tare da ke, zan zaɓe ki da ɗana a kan komai, babu butulci tsakanina da ke, ai na san babu wani abu da zan yi miki da zai sanya na biya ki ko na kamanta abin da ki ka yi wa rayuwata ba. Kuma ina fatan a wannan karon za ki ba ni dama ki saurari uzurina, inda na yi miki kuskure kuma ki yafe mini. Ki bani dama mu ɗora ginin rayuwarmu rayuwa mai kyau da aminci"
"Ni ba biyana za ka yi ba, ban yi dan ka biya ni ba, ni kawai su bar mini kai, kuma su dawo mini da Muhsin mu rayu tare" Ta yi maganar tana kuka.
Ya yi murmushi idanunsa na cika da hawaye, ya ce "An bar miki ni, halak malak. Hammad naki ne rayuwata" Ya yi maganar yana haɗe bakinsa da Nana.
Babu tsammani aka banko ƙofar ɗakin, Nana ta yi wata irin zabura, shi kuwa cikin nutsuwa ya waiwaya ya ga waye wannan ya shigo musu babu neman izni. Da Asal ya yi tozali, jikinta na wata irin tsuma take bin su da kallo. Ta nuna Nana da yatsanta bakinta yana wata irin rawa, jikinta ma karkarwa kawai yake yi, tamkar ana kaɗa mata gangi. Ba ta taɓa tsammanin abin da za ta gani ba kenan, ko a hasashe da tsammani ba ta taɓa hasko ganin Nana tare da mijinta ba. Kasamcewarta baƙar fata da ba ƙabilarsu ba. "Ham..Ha.ha...Hammad!" Ta faɗa cikin wani irin ƙaraji mai razanarwa.
Bakin Asal ne ya ci gaba da rawa, dan da fari ma kanta gaba ɗaya kullewa ya yi, ta manta wace ce ma Nana. Ita da ta zo tambayarsa ba'asin ina ya samu ɗa, sai ta riski abin da ya fi maganar da ta zo da ita tashin hankali. Hankali kwance Nana ta gyara rigarta, ba tare da abin da ya faru ya ɗaga mata hankali ba. Ja da baya Asal ta fara yi, numfashinta na fita da kyar, jikinta na wata irin kyarma. A sukwane Imam Hammad ya diro daga kan gadon ya nufe ta, cikin tashin hankali bai so Asal ta san alaƙarsa da Nana ta wannan sigar ba. Amma ya san babanta shi ne ya lalata komai.
"Kar ka taɓa ni, kar ka ƙaraso inda nake Hammad. Ka yaudare ni ka zalunce ni, dama rashin lafiyar da ka ke yi ƙarya ka ke yi? Ka haɗa kai da mahaifinka ne dan ku yaudare ni ku cutar da ni? Lalata da wannan ƙasƙantacciyar ƙazamar matar? Na zaɓo ta a matsayin kukunka dan kawar da kanka daga kalle-kallen wasu matan, ashe yaudarata ka ke yi? Tun tsawon lokacin da ta gudu na neme ta na rasa, a she a nan ka ɓoye ta ku ke lalata."
Cikin azama Hammad, ya danƙo hannun Asal, da take ta fizge-fizge ya danna ƙofar ya datse ta. Ya kalli Asal ya ce "Ki nutsu cherié zan yi miki bayani, ni ba lalata nake yi da Asmy ba" Cike da baƙin ciki take kokowar fizgewa cikin ƙaraji ta ce "Idan ba lalata ku ke yi ba, me ku ke yi? Tsawon wannan lokacin da ba ta nan, ashe ku na tare ka ji kunya ba ka ji daɗin halinka ba. Ke kuma 'yar iska mazinaciya wallahi sai na ƙasaƙantar da ke, sai na saka an kashe mini ke a kashe banza"
Nana ta ce "Point of correction my dear, ba da kukun mijinki ki ke magana ba a yanzu, kuma ni ba mazinaciya ba ce ba. Ki dai nemi wani sunan ki kira ni da shi" Ya kalli Nana da ta tsuke fuska ya ce "Ma vie dan Allah ki yi shiru, mu warware matsalar nan a hankali"
AREWABOOKS
Daskarewa Asal ta yi jin sunan da ya kira Nana da shi, wanda shi gaba ɗaya ya manta, saboda yadda sunan ya shiga bakinsa ya zauna.
"Hammad gaskiya ne abin kunnuwana suke jiye mini? A gabana? Hammad" Ta furta tana ajiyar zuciya mai ɗauke da nannauyan baƙin ciki da tashin hankali. Damƙar hannun Asal ya yi, ya buɗe ƙofar suka fita tare.
Kokowa ya shiga yi da Asal, yadda take kai masa duka, tana fizge-fizge.
"Asal, ki tsaya ki saurare ni, kar ki ji wa kan ki ciwo mana"
"Ba zan saurare ka ba, ba na buƙatar duk wasu kalaman yaudara da ƙarya da za su fito daga bakinka. Me ya rage bayan abin da na gani? Da girmanka da mutuncinka ka ɓoye kukunka a sashen mahaifinka kana zina da ita, ba ka ji daɗin halinka ba" Kalaman Asal sun yi wa Hammad zafi nesa ba kusa ba, da kyar ya haɗiye wani yawu mai zafi ya ce "Ni ba zina nake yi ba, idan ba ki tsaya kin saurare ni ba, ki ka fita ki ka yayata abin da ba shikenan ba za ki cutar da ni dan kin yi mini ƙazafi"
Kallonsa take yi, tana jinjina girman yadda ya ƙware a iya wasa da hankali, ta ci gaba da ƙoƙarin fizgewa, amma ya riƙe ta gam.
"Hammad ka gama raina mini hankali, dama ga batun ɗa ana yi, an ce ka na da ɗa da a ƙalla ya shekara biyu, yanzu kuma na kama ka da wata, amma kana iƙrarin zan cutar da kai? Da ni da kai waye ya cutar da wani? Wadda ka yi wa ciki ba ta ishe ka ba, ka ɗauki kukunka ka sanya a sashen Sultan ka ke lalata da ita"
"Ban taɓa cutar da ke ba Asal, a shekara goma sha biyu da muka yi da ke, idan zan iya aikata abin da ki ka faɗa kin sani, idan akasin hakan ne ma kin sani. Amma mu je gurin Sultan ɗin ki ji komai daga bakinsa.
Nana kuwa guntun tsaki ta yi bayan fitarsu, ta tashi ta shiga banɗakin ta yi wanka, ta yi alwala. Ta ƙura wa kanta ido a mudubin banɗakin, tana tunanin yadda Asal ta din ga yi mata kallon ƙasƙanci, da bautar da ita ta ƙarfi da yaji, saboda tana da kuɗi da mulki, a matsayinta na kishiyarta, kuma ta daure ta haɗiye. Ta ci gaba da tunanin daga bisani ta fito da niyyar ta canza kaya, amma ta kasa, ta nemi guri ta zauna ta yi shiru. A zuciyarta take addu'a ta ce "Allah ga Nana, bakwarka ce ni mai raunin gaske, ga ɗan jaririn ɗa na da nake fatan ya samu kyakykywar rayuwa ya tashi a tsakanin uwa da uba. Ubangiji Allah ka na ji ka na gani, ka ga wahalar da na sha a baya, ga shi na zo wani bugire da nake sanya ran samun afuwa, sai dai alamu sun nuna an fi ƙarfina. Allah idan sun fi ƙarfina ba su fi ƙarfinka ba, da ni da su duk bayinka ne. Ubangiji Allah ka sassauta mini ka kawo mini ɗauki. Ubangiji Allah ka yaye mini wannan kishin da nake ji, ka sanya su bar ni na rayu da mijina da ɗa na. Ubangiji Allah ka ba wa mijina ingantacciyar lafiya ka yaye masa abin da yake damunsa, Allah ka ba kare mini ɗana daga dukkanin sharrin da ido ka iya gani, da wanda ma baya gani. Ƙaisar ma bawanka ne, Allah ka ba shi lafiya. Allah ka ga wahalar da na sha a baya, yanzu idan na koma suka raba ni da ɗa na, wata wahalar zan shiga, Allah ka kawo mini agaji" Sai kuma ta yi shiru tana nazari, duk abin da take faɗa ai Allahan yana ji yana gani. 'Idan ba ubangijina ba, wa nake da shi da zan kaiwa kukana kai tsaye ya share mini. Na san ya sani amma ƙara gaya masan, yana sama mini nutsuwa da kwanciyar hankali, ko da ina cikin damuwa. Ta ba wa kanta amsa.
Asal ce a gaban Sultan, tana ta uban kuka, fuskar nan ta yi jawurr, idanunta sun kumbura sosai da sosai.
Sultan ya yi shiru, saboda yadda abubuwan shi kansa suka kulle masa kai. Gaba ɗaya bai yi tunanin abubuwan za su damalmale har haka ba, ya ma rasa ta ina zai fara. Ya ce "Ki na ji na Asal. Wannan maganar abu ne mai faɗin gaske, da ko ba ki gano ba, dole za a yi miki bayani. Amma wannan bayanin ba ke kaɗai yakamata mu yi wa ba, a gaban mahafinki yakamata mu yi shi. Tabbas da gaske Imam Hammad ba shi da lafiya, kuma ke ma shaida ce, saboda kin zo kin gan shi a halin da yake ciki. Sai dai ita wannan yarinyar tana da alaƙa da samun sauƙinsa. Yanzu bayanin da zan yi miki ba za ki gane ba, ina son sai mun zauna gaba ɗaya za mu yi miki bayani. Amma ki samu nutsuwa ki kwantar da hankalinki. Gaba ɗaya Asal ba ta fahimci abin da Sultan yake gaya mata ba, gani take kawai yana ƙoƙarin goyon bayan ɗansa ne. Muryarsa ta sake tsinkayowa yana faɗin "Kar ki bari kowa ya ji maganar nan, sai mun zauna an yi miki bayani tukuna dan Allah." Ya dubi Imam Hammad ya ce masa ya kai Asal gida, ya rarrashe ta, ta samu nutsuwa kafin a yi mata bayanin komai.
Nana kuwa kajin gurin Nene ta samu ta ci, saboda taga alamun idan ta biye ta kishin nan, yunwa ce za ta kar ta a banza, duk da yanzu naman duk ya ishe ta, abinci take so ta ci sosai. Ga shi ta yi zaton ko zai dawo mata da Muhsin, amma bai dawo mata da shi ba.
Ba ta sake ganin Hammad ba, sai bayan sha ɗaya na dare. Idanunsa jawur da alama yana cikin damuwa kuma ko abinci ba ta tunanin ya ci. Sau ɗaya ta kalle shi ta basar, ba ta ko kula shi ba.
Gani ta yi ya cire rigar jiknsa ya yar a ƙasa, ya hau kan gadon ya kwanta, ba ta motsa ba ta ci gaba da zamanta, dan haushinsa ne ma ya kama ta. Jin ya fara numfarfashi ya sanya ta tashi tsaye. Ta kalle shi ta ga ya fara komawa ja. Sai kuma jikinta ya yi sanyi, abin da ta lura da shi kamar ciwon ya fi tsananta masa a Niger. Ta fara ƙoƙarin ninke masa rigar, kawai wannan takardar ta faɗo daga aljihun rigar. Ta ɗauki takardar ta yi shiru tana kallon takardar. Ta hau kan gadon ta juya shi da kyar, taga yana ta taune leɓensa yana jujjuya kansa.
"Ki yi mini addu'a, zan mutu" ya furta da kyar kamar numfasihinsa zai ɗauke. Suratul Fatiha ta din ga karantawa da Bismillah tana tofa masa. Fizge-fizge ya fara yana girgiza kai ya ce "Tashi mu tafi"
Cikin rashin fahimta ta ce "mu je Ina?"
"Ki tashi nu tafi, kafin na rasa raina" Ya ƙarasa maganar yana dafe kansa da yake jin kamar zai yi bindiga. Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin aka yi. Amma ba damar Nana ta tashi, saboda yadda ya rirriƙeta. Ga shi ta san ko ta ce a shigo babu lallai a jiyota daga waje.
Mai bugun ne ya gaji da bugawa, ya turo ƙofar, Sultan ne tare da wata babbar mace fara solnda ita. Sai kuma Mahmoudu. A rikice suka ƙarasa gaban gadon, cikin tashin hankali Sultan ya ce "Jikin ne?"
"Ki tashi mu tafi, zan rasa raina, ƙwaƙwalwata za ta tarwatse. Ki yi mini addu'a"
Tuni Nana ta fara kuka, ta ce "Ina yi maka, kai ma ka din ga yi ko a zuciyarka ne. In sha Allah babu abin da zai same ka"
Matar ta ce "Wannan ce matar tasa?"
Sultan ya jinjina kai ya ce "Ita ce"
Ta ce "Ikon Allah, lallai Allah gwani ne"
Mahmoud kuwa jiki a sanyaye ya ce "Sannu Imam"
"Hamud, dan Allah ka ɗauke ni ka sake tafiya da ni, ba na son zaman garin nan, ba ku san me nake ji ba."
Mahmoudu ya kalli Sultan ya ce "Ranka ya daɗe, a irin wannan yanayin fiye ma da wannan, na bar Niger da shi a wancan lokacin. To kuma na ga alamar jikin na neman sake dawowa.
A hankali ya fara fita hayyacinsa, ya fara lanƙwasa Nana, ta rintse idanunta Sultan ya ƙarasa da sauri yana faɗin "Kai kar ka yi wa 'yar mutane illa, Hammad" Mahmoudu rasa abin yi ya yi, dan ya san ganganci mafi girma da zai aikata shi ne ya taɓa jikin Nana garin ƙoƙarin ɓanɓare shi daga jikinta.
Sai kuma Sultan ya ja ya tsaya shi ma ya rasa abin yi.
"Ke kin san me nake ji ai" ya sake futawa cikin ƙarfin hali.
"Na sani, shi ya sanya nake yi maka addu'a"
Sultan ya ce "Hammad, kar ka ji mata ciwo fa"
A hankali Nana ta ce "Ba zai ji mini ba in sha Allah"
Addu'a ta ci gaba da yi masa, tana tofa masa. Sultan kam kasa jurewa ya yi, saboda ba ƙaramin tashin hankali yake shiga ba, idan ya ga ɗan nasa a cikin wannan yanayin.
Sai kusan ƙarfe biyu na dare sannan ya dawo hayyacinsa gaba ɗaya. Ya yinƙura ya tashi zaune yana kallon Nana.
Ta ce "Sannu. Ka daina jin abin da ka ke ji ɗin?"
Ba ta yi zaton zai iya magana ba ta ji ya yi, ya ce "Ina ji amma ya lafa mini"
Ta ce "To Allah ya baka lafiya ingantacciya. Amm ka yi haƙuri kana cikin yanayin larura zan tambaye ka abu" ya yi shiru yana kallon ta.
Ta ɗago masa wannan takardar ta ce "A cikin rigarka na ganta, waye ya saka maka ita?" Ya girgiza kai ya ce "Nima ban sani ba"
Ta sake cewa "Shekaranjiya wani abu mai kama da mafarki ya faru, har muka fita ta wata ƙofa, gaske ne ko kuma mafarki nake yi?"
"Gaske ne" Ya bata amsa kai tsaye.
"Ina buƙatar fahimtar wasu abubuwan, dan ka na yin abubuwan da ba kowane ɗan Adam ne zai iya ba. Tun mu na Nigeria ka ke yin wasu abubuwan. Kuma ina buƙatar na ji abubuwan da suka faru wanda ban sani ba" Ya numfasa ya ce "Zo ki raka ni shan iska tukuna" Suka sauka daga kan gadon. Ya zira rigarsa ya buɗe ƙofar nan, suka ƙara ratsa duhu suka fita wannan corridor.
Yau ma saharar ta gani, gurin ya ɗauki sanyi sosai da sosai. Ta kalli Wannan tsaunin dake gefen saharar ta ce.
"Wai mene ne a cikin dutsen can, shi nake son sani"
Ya kalli gurin ya ce "Nan ne ainihin inda kakanninmu suka fara mulki, dan haka duk wani kayan tarihi, a ciki a ke adana su"
Nana ta ce "To ka gaya mini abin da na tambaye ka, kuma ina son ka kai ni na ga abubuwan tarihin garin naku"
"Zan kai ki, kuma zan yi miki bayanin amma yanzu ba na jin daɗi"
Ta ɗan shafa bayansa ta ce "Sannu" ya jinjina mata kai. Ya matsa kusa da ita, ya rungume ta, sanyin gurin ya din ga ratsa su a tare.
Ta ɗaga kai tana kallon wannan tsaunin, da ya ce mata gidan tarihi ne, tana jin kwaɗaituwa da son sanin abin da gidan ƙunsa.
Tana jin kewar Ƙaisar, ta damu sosai ta san ya jikinsa, amma ko sama ko ƙasa ta daina ganinsa.
Ta lumshe idanunta ta buɗe, kewar gida kuma na sake bijiro mata, tana cikin matuƙar fargaba a kan irin karɓar da za a yi mata idan ta koma.
"Ma viee"
"Na'am Shugabana"
"Ina da wani kyakykywan albishir da zan baki, amma ba yanzu ba"
Ta yi murmushi ta ce "Sai yaushe?"
"Sai an wa Muhsin ƙani"
Ta ce "Babu rana kenan"
"Akwai mana nan kusa" yayi maganar yana ƙara ƙanƙameta.
Asal kuwa yadda ta ga rana haka ta ga dare, dan faɗa suka yi kaca-kaca da Hammad, duk da rarrashin da Sultan ya yi mata. Ta kira Hasna a waya, Hasna ta ɗaga tana "Faɗin Gimbiya Asal, kwana biyu"
Cikin kuka ta ce "Hasna, kin san abin da Hammad ya yi mini kuwa?" Gaban Asal ya faɗi ta ce "Meyafaru?"
"Hasna wai Hammad yana da ɗa"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ɗa kuma kamar yaya?"
Cikin kuka ta ce"Ɗa dai ya haihu da wata, Tafawa kuma ya tabattar mini da hakan, kin san ba zai yi mini ƙarya ba. Kuma ba na ce miki yarinyar nan ta gudu ba, mai yi masa girki ba, har nake ce miki duk inda ta gudu zan saka a nemo ta"
Hasna ta ce "Eh haka ne"
"Na je na kama shi da ita, a can cikin sashen Sultan, duk tsawon lokacin da aka shafe ba ta nan, suna tare su na lalacewa, na shiga uku Hasna, ji nake kamar na kashe kaina na huta. Na tsani Hammad na tsane shi, ban taɓa cin karo da abin da ya gigita ni ba, kamar abin da na gani yau ba. Kuma Sultan goyon bayansa yake yi, wai in bari za a yi mini bayani, bayanin me za a yi mini an cuce ni Hasna" Ta yi maganar tana ƙara rushewa da kuka, kamar wadda aka nuna wa ranar mutuwarta.
Hasna ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Asal, ki yi haƙuri ki nutsu, ki tattara hankalinki guri ɗaya kar ki yi ganganci da rayuwarki. Amma ni kwanaki na ji Al Hussain yana cewa ya kira shi ya ce ya yi masa bincike a kanta, a nemo kamfanin da suka kawo ta. To ni ban kawo komai a raina ba, na ɗauka da saninki, amma zan tambaye shi ko ya san wani abu. Amma dan Allah ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki"
"Ba ki san me nake ji ba, hankalina ba zai taɓa kwnaciya ba" Haka Asal ta kwana ido biyu, babu abin da take hangowa sai abin da idanunta suka gane mata a tsakanin mijinta da wannan baƙar yarinyar.
Bangaren su Nana da safe, da Mahmoudu ya kai musu abinci, ya sanar musu da cewa Sultan ya ce su zo gaba ɗayansu, mai maganin ya ƙaraso.
Hammad ya ce "Waye mai maganin?"
Ya ce "Ban san waye ba, kawai dai saƙon da ya bani kenan"
"Ni fa ba na buƙatar wani mai magani, ga maganina nan a gefe na" Ya yi maganar yana kashewa Nana ido.
Ta basar da shi, ta ɗan yi murmushi. Ya karya sannan suka rankaya suka fita tare. Tun da aka kawo Nana, sai a lokacin ta samu damar sake fitowa daga ɗakin da suke. Sai dai wani surƙuƙin ɗakin suka shiga. Abin har mamaki yake ba wa Nana, yadda ake ɗakuna a lunguna da saƙo na gidan, kamar marasa gaskiya, inda ba ka yi zato ba ma, sai ka ga ɗaki ne.
Da Asal ta yi tozali a ɗakin, idanunta jawur, tana ganin Nana ta sake tsuke fuska, kamar ta tashi ta kashe ta ta huta. Suka je gaban Sultan suka gaishe shi, Nana ta basar ko kallon inda Asal take ba ta yi ba.
Sultan ya ce "Asal, na saka an kira ki ne, saboda a yi komai a gaban idonki, a ji me mai maganin zai ce, saboda kina da hakki ki sani kar ki ga ana ci gaba da rufe ki a kan abubuwa, tun da mijinki ne" Ta yi shiru, saboda shi kansa Sultan ɗin haushin sa take ji.
Sallamar da aka yi ne ya sanya Sultan yin shiru, Nana kuma ta miƙe tana faɗin "Kaii Sarki, dama ka na nan?"
Ya yi dariya ya ce "Tuba nake uwar gijiyata, tuba nake uwar ɗakina"
Bakin Nana ya ƙi rufuwa, tamkar ta ga wani ɗan uwanta na jini.
Cikin murmushi ta sake cewa "Sarki mai baka mai aska, kai ne mai maganin da zaka duba Sayyid?"
Ya ce "Ni ne uwar gijiyata, an yi mini lamuni, ko kuwa na koma ba a bani dama ba?.
Ayshercool 08081012143
88 1K NE VIA 0069685771 AISHA ADAM STANBIC IBTC BANK 08081012143
Nana ta kalli Sarkin baka ta yi murmushi ta ce "Wane mutum! Dama zan sake ganinka?"
Ya yi murmushi, hadimin da ya rako Sarkin baka, ya ankarar da shi Sultan. Cikin girmamawa Sarkin baka ya risuna ya kwashi gaisuwa a gaban Sultan.
Sultan ya ce "Na ga kamar ka santa ko?"
Ya jinjina kai ya ce "Ƙwarai uwar gijiyata ce" Sai kuma ya sauke idanunsa a kan Sayyid, ya yi murmushi ya kalli Mahmoudu ya ce "Kamar ba ka gane ni ba ko?" Mahmoudu ya ce "Ina dai yi maka kallon sani"
Ya matsa gaban Hammad, ya zuba masa ido ya ce "Ka tuna ni?" Hammad ya yi shiru sannan daga bisani ya ce "Na tuna ka"
"Waye ni?"
"Ba zan iya cewa ga waye kai ba, amma mun je gurinka a Nigeria"
Sarkin baka ya yi murmushi ya ce "Yanzu tunaninka kaf na zamanka a Nigeria ya dawo kana tuna komai?" Ya jinjina masa kai alamar eh.
Ya dubi Nana ya ce "Kin ga batutuwan duk da na gaya miki sun dawo ko? Kin yarda ko haryanzu kina da ja?"
Nana ta girgiza kai ta ce "Ba ta sauya zani ba, ina nan a kan bakana"
Ya ce "Babu laifi, amma an bani dama ko kuma na bar lamarin tun da na manya ne?"
Matawalle ya ce "Bawan Allah, ina ganin ka yi abin da aka kawo ka ka yi mana. Idan ma wani abu ne a tsakaninku, kwa tattauna daga baya. Nan ba gurin wasa ba ne"
Sarkin Baka ya tsuke fuska ya kalli Matawalle ya ce "Duk cikin aikina ne, kai ka san wacece wannan kuwa? Ku na da maganin matsalarku a tare da ku, amma ba ku sani ba" Gaba ɗaya suka kalli Nana, ita ma ta yi sororo cikin mamaki.
Sarkin baka ya ce "Allah ne ya taƙaita masa, ba domin tana tare da shi ba, da sai ya zare ko ya mutu" Sultan da Mahmoudu suka haɗa ido.
Sarkin Baka ya ce "Ni yanzu abu ɗaya zuwa biyu zan ce, sauran magana ce tsakanina da ni da shi da Nana Asma'u Uwar ɗakina ba Allah ya taya miki" Ya yi maganar cikin girmamawa da jinjina wa Nana. Nana ta sunkuyar da kai tana murmushi.
Mahmoudu ya ce "Bawan Allah, nan fa a gaban Sarki ka ke, in yi maka da yaren da zaka fi ganewa"
Sarkin Baka ya ce "Nima Sarki ne, dan haka a bari ni na gudanar da aikina. Kai ka manta Garba ga Baka ga Aska da ku ka kai mini wannan ɗan uwan naku can Nigeria" Mahmoudu ya yi sak ya ce "To ai na ga kamaninka sun canza?"
"Eh, ba kamannina ne suka canza ba, dan baka ganni cikin kayan aikina ba ne ba."
Sultan ya ce "Asal tashi ki je, duk abin da aka tattauna za a gaya miki"
Asal ta ce "Allah ya baka nasara, dan Allah ina roƙon alfarma, a yi komai a gabana, ina son sanin halin da yake ciki nima". Sardauna ya ce "Ke Asal! Ki nutsu ki saurara tukuna, ki tsaya mu ji kan rashin lafiyar tasa, sannan a yi miki bayani daga baya"
Asal ta tashi jiki a sanyaye, tana kallon inda Nana take da kuma Hammad ta fice.
Sarkin baka ya kalli Nana ya ce "Nana Asma'u, mene ne labari? Meyafaru bayan tafiyarki ne? Kuma yaya aka yi na ganki a birnin Agadez?"
Nana ta yi murmushi ta ce "Komai ma ya faru Sarki, amma dogon labari ne, mai tsayin gaske"
Ya murmusa, ya ƙare wa mutanen gurin kallo, sannan ya sake kallon Nana ya ce "Uwar ɗakina, me ya kawo ki Agadez ne?"
Nana ta nuna masa Sayyid. Mahmoudu ya yi murmushi ganin abin da Nana ta yi. Ya ce "Uwar gijiyata, kina nan me yasa aka neme ni, kin karɓi aikin gurin uban duƙusa ne?".
Nana ta girgiza kai. Ya ce "To bani labari meyafaru?"
Sultan ya ce "Bawan Allah, ban fahimta ba me yake faruwa ne?"
"Allah ya baka yawan rai, duk cikin aikina ne. Idan babu damuwa ina son na san matsayin kowa a nan"
Mahmoudu ya ce "Ga Sultan kana gabansa, shi ne mahaifin Imam Hammad, sarkin Agadez, ga Matawalle da Sardauna, su ma iyaye ne a gare shi, kuma manya ne a Agadez. Sai Gimbiya Asal matarsa da ta fita. Sai kuma" Sai ya yi shiru yana bin su da kallo yana tsoron ya faɗi matsayin Nana ya yi laifi.
Sarkin baka ya ce "Ba ka gaya mini matsayin uwar gijiyata ba"
Sayyid ya ce "Matata ce"
Sarkin baka ya sake yin murmushi ya ce "Na san a rina, an saci zanin mahaukaciya jikina ya bani tun a lokacin da na ganku. Allah ya baka yawan rai, in dai yana tare da Nana Asma'u zai samu sassaucin matsalarsa. Tana ɗaya daga cikin dalilan da ya sanya yake zaune lafiya a Agadez, bai sake ɓallewa ya bar ƙasar nan ba"
Sarkin baka ya sake maimaita musu, Nana tana da alaƙa da maganin Hammad.
Matawalle ya ce "Me ka ke nufi? Ko dai wani haɗin bakin ne, ku ke son ku yi mana" Sardauna ya yi maganar yana kallon Sarkin baka.
Sarkin baka ya ce "Ɗan tsahirta mini tukuna, a kan aikina nake"
Ya sake kallon Mahmoudu, ya ce "Ɗan uwana ko za ka iya tuna abin da na gaya muku, lokacin da ku ka je gurina?"