Kenza eBookz

Buzu book 3 complete - Chapter 11

Buzu book 3 complete - Chapter 11

Buzu book 3 complete Chapter 11: Buzu book 3 complete Chapter 11. Mahmoudu ya jinjina kai ya ce "Ka ce mana asiri aka yi masa, da baƙin aljani, ya manta…

4,278 words

Mahmoudu ya jinjina kai ya ce "Ka ce mana asiri aka yi masa, da baƙin aljani, ya manta duk abin da ya shafe shi, ya bar garinsu ba zai iya zama a garinsu ba. Kai kuma ba zaka iya ba shi magani ba, saboda ba aljani ne da za a iya sasantawa da shi ba, sai dai a je a karya asirin da aka yi masa. Na tambaye ka ko zaka iya karya asirin? Ka ce a'a shiga al'amuran aljanin nan akwai matsala, mu koma ƙasarmu a bincika inda aka yi masa sihiri a warware shi a can"

Ya ce "Madalla"

"Uwar gijiyata, ranar da aka kawo ki gidana neman magani, Meyafaru?"

Nana ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Ka ce a je a kira buzayen da suka tafi. Aka ce maka sun tafi. Ka ce da an same su, wataƙila ga maganin nasa ciwon ko nawa"

Sarkin baka ya ce "To Alhamdillah, an zo gaɓar da nake so a zo"

"Allah ya baka nasara. Wannan ita ce rabin maganin abin da yake damunsa"

Matawalle ya ce "Kai kalle mu da kyau, kar ka kuskura ka zo nan ku na gaya mana maganar banza. Idan ma haɗa kai ku ka yi, ku ka haɗa baki domin ku raina mana hankali, wallahi muka kama ka da rashin gaskiya, sai mun yi maka mummunan hukunci" Sarkin baka ya ce "Na san dai duk azabar da zaka yi mini ba zaka saka ni a jahannama ba ko? To bayan wuta da Ubangiji zai saka ni a ciki, azaba in dai ta Duniya ce babu wadda ban sha ba, duk wadda za ta biyo baya ɗazu ce. Ban sanku ba ban taɓa ganinku ba, dan me zan yi muku ƙarya? Wani abu ne ya faru da tun a baya, na yi hasashen faruwarsa. Zan yi wani bayani amma a gaban mara lafiya da shaƙiƙansa da ya yarda da su. Idan na faɗa ban ce lallai sai kun yadda ba, amma iya gaskiyata zan gaya muku. Wannan baiwar Allah da na nuna na santa, tabbas na santa amma ni babu wanda na haɗa kai da shi domin na zo nan gurin na yi cuta ba. Saboda duk wani abun duniya da nake fatan samu, Allah ya riga ya bani shi. Ranka ya daɗe zaɓi mutum biyu zamu yi magana.

Duk suka yi zuru da ido, suna kallon Imam Hammad.

Hammad ya kalli Sultan, Sarkin baka ya yi caraf ya ce "Ɗayar, na zaɓi uwar gijiyata mutum biyu kenan. Allah ya baka yawan rai, idan babu damuwa ina so mu keɓe tare da ku"

Sultan ya ce "Babu laifi, Matawalle ko za ku bamu guri?"

Sardauna ya ce "Mai girma Sultan, ka yi a hankali kar ka bari su yi maka wasa da hankali, su faɗa maka abin da ba shikenan ba"

Sultan ya ce "Babu wani abu in sha Allah"

Bayan fitarsu gaba ɗaya, Sarkin baka ya ce "Allah ya baka yawan rai, ba dan ina tsoron hadisin da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya ce Allah yana fushi da ɗan kasuwa mai rantsuwa a kan kasuwancinsa ba, da na yi maka rantsuwa domin nima bayar da magani kasuwancina ne, amma ina baka tabbacin duk abin da zai fito daga bakina gaskiya zan gaya maka. Na san duk alkhairin da zaka yi mini ba zaka yanke mini talauci ba, sai Allah ya yanke mini. Kuma ba zaka talauta ni ba sai Allah ya talauta ni. Babu ƙarya ko haɗin baki ko yaudara a cikin abubuwan da zan yi maka. Wannan bayin Allah biyu babu wanda ba a kawo mini shi gurina neman magani ba. Asma'u ko ba ta bayar da magani ba, tsantsar tauhidinta da yarda da Allah da ta yi, zai iya sanyawa yadda yake tare da ita ya samu lafiya ko dan albarkacin addu'a. Ai Allah shi ya ce a roƙe shi zai amsa. Kafin na ce maka komai, bari na yi maka wasu tambayi m ya ka ji lokacin da ka neme shi ka rasa a ƙasar nan?"

Sultan ya ce "Na shiga tashin hankali, ba na iya cin abinci da cikakken bacci saboda rashin sanin inda yake."

"Alhamdillah, yanzu da ya dawo ya ka ke ji?"

"Murna nake yi mara misaltuwa, da jin cewa zan iya yin komai, dan na ga bai sake yin nesa da ni bax

Sarkin baka ya ce "Alhamdillah, ka yi bayani dai-dai da abin da nake son ka faɗa. Wannan yarinyar da ɗanka ba za su rayu guri daban-daban ba. Idan haka ta kasance kuma ɗaya zai rayu cikin wahala. Saboda alaƙarsu akwai tasirin soyayyar uba da ɗa a tsakaninsu"

Cikin rashin fahimta Sultan ya kalli Sarkin baka ya ce "Me ka ke nufi?"

"Aljanin da aka yi wa ɗanka asiri da shi, ɗansa ne a kanta yake ta ɗawainiya da ita saboda ta yarda ta yi masa wani aiki. Ya ɗauki tsawon shekaru ba sa tare, kwatsam da aka ba shi aiki a kan ɗanka, ya yo Nigeria da shi, suka haɗu da ita. Dan haka duk abin da zai faru, duk rashin jituwar da ke tsakaninsu, uban ba zai bari ɗansa ya ƙara nesa da shi ba. Saboda shi ne ɗa mafi soyuwa a gare shi"

Sultan ya yi shiru cike da mamaki, yana bin Nana da Hammad da kallo.

Ya ce "To yanzu babu yadda za ayi, a karya sihirin?"

"Ni ba na ƙarya dan a so ni, ban san waye ya yi masa asiri ba, ban kuma san a daidai ina aka yi ba, balle na ce kai tsaye ga gurin a je a tona ba. Kuma ba zan yi karambani ba saboda aljanin shu'umi ne zai iya halaka ni. Amma ita tun da ɗansa yana tare da ita, ban sani ba ko ya samu sassauci ko makarin abin a dalilnta ba"

Sultan ya yi shiru yana kallon su, lallai biri ya yi kama da mutum, duba da yadda lokaci guda take iya sarrafa shi, idan ciwon nan ya tashi.

Sultan ya ce "Yanzu mene ne abin yi?"

"Abin yi ɗaya, a ci gaba da addu'a, kuma ku ƙara taka tsantsan, sannan ban sani ba ko uwar gijiyata za ta nema mana alfarmar shugaba, ko akwai abin da zai iya yi a kan lamarin" Nana ta ɗan tsuke fuska tana mazewa.

"Wa za ta roƙa mana " Sultan ya yi maganar cikin damuwa.

"Ɗan nasa mana, ai hadiminta ne, kuma babu abin da za ta saka shi, ya kasa yi mata"

Sultan ya kalli Nana ya ce "To ko za ki roƙa mana ɗin, duba da mawuyacin halin da yake shiga idan ciwon ya tashi" Nana ta yi shiru ta sunkuyar da kanta.

Sarkin baka ya ce "Kar a yi gaggwa, a bi ta a sannu tukuna, ta yanke hukunci da kanta"

Sultan ya ce "Shikenan, a mayar da kai masauki, kafin na kuma nemanka"

Nana ta ce "Allah ya baka nasara, dan Allah zan yi magana da shi, idan babu matsala a hakan" Sultan ya ce "Babu damuwa"

Hammad ya haɗe rai, amma Nana ta tashi ta bi shi waje.

Ta ce "Sarkin baka, dama kana raye? Ƙaisar ya ce mini kashe ka zai yi"

"Nana Asma'u, uban duƙusa bai kashe ni ba, sai dai na ji jiki kamar ba zan rayu ba. Shi ya kawo mini magani ma, sannan ya ƙara yi mini kashedi sosai a kanki. Daga nan ma har wasu magungunan ya sanar da ni"

Ta ce "Ikon Allah, sarki ya magunguna ya marasa lafiya? Ina Salamatu da wannan aljanar taka"

Ya yi dariya ya ce "Duk su na nan ƙalau"

"To ya aka yi ka san cewa asiri aka yi wa Sayyid?"

Ya harare ta ya ce "Halinki dai yana nan uwar ɗakina. Mutum mai hankali zai yi abin da mijinki yake yi ne? Abin da nake so da ke, ki ƙara addu'a kar ki yarda da kowa, kunnuwanki da idanunki su zama a buɗe komai na iya faruwa idan Allah ya taimake ki wataƙila ya samu lafiya ta hannunki"

Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Ƙaisar ya nuna mini abubuwa da dama, sai dai ba na son gazgatawa ne, na shiga ruɗani, amma har yadda asirin yake na gani, to amma idan ya rabu da Giyaz iya samun lafiya duka?"

"Ba na ce ba, tun da ban san a kan me da me aka ba shi aikin ba. Kuma ba shi da fuskar da zan tambaye shi. Amma ina jakar da na baki?"

Kafin ta amsa, Sayyid ya fizgi hannunta da ƙarfi ya yi gaba da ita.

Bai tsaya da ita ko ina ba, sai da suka je ɗakin da yake jinya. Idanunsa jawur ya ce "Dan wulaƙanci kawai ki je ki tsaya ki na surutun banza da mutumin da ba muharraminki ba"

Ta marairaice ta ce "Haba Shugaba, wa nake da shi a nan daga ƙasarmu, yaushe rabon da na ga wani wanda na sani? Kuma Sarkin baka duk da yana wasu abubuwan da nake tantama a kansu, mutum ne da ba zan taɓa mantawa da shi ba. Bayan tafiyarka daga gidansa, abubuwa da yawa sun faru, ni a gidan nasa a ka bar ni"

"Ba na son jin koma mene ne ya faru" ya yi maganar yana tsuke fuska.

Ta ce "Haba Shugaba, kar ka manta, maganinsa ya taka muhimmiyar rawa lokacin da ka yi rashin lafiya"

Yayi mata shiru yana huci, tabbas a rayuwarsu da shi a Nigeria ta san shi da azabar kishi.

Ta kwantar da murya, tana shafa bayansa ta ce "Haba Shugaba, dama mutum zai iya fushi da rayuwarsa, tuba nake ɗan manyan mutane, kuma babban mutum" Ɗan guntun murmushi ya saki, ita ma ta yi masa murmushin.

Ya ce "Yauwwa, ki yi mini addu'a, in ajima za a sanar da Asal da iyayenta, matsayinki a gurina.

Nana ta kwaɓe baki ta ce "Na yi maka addu'a, ta mutu mana, nima ban mutu ba da kishiyata ta mayar da ni baiwa saboda tana da kuɗi, ga kuma mijina ina kallonsu tare, amma ban isa na ce komai ba".

Tsam ya miƙe, saboda ya san idan aka ci gaba da jan maganar faɗa za su yi. Ya ce "Ki shirya, idan na dawo yau komai dare, za mu je gurin kayan tarihi na Agadez, kuma zan baki labarin duk abubuwan da suka faru" Ta yi masa shiru ta cika ta yi fam, kamar za ta fashe.

Ya tausasa murya ya ce "Na san kin yi haƙuri, amma ina sake baki haƙuri, dan Allah ki saki fuskarki"

"Ni ka rabu da ni, ka je ku lallaɓa matar so, da al'adarku ta yarda da ita, ni kuma ka sake ni ku kora ni ƙasarmu" Ta yi maganar har da ƙwallar baƙin ciki.

Ya yi murmushi ya ce "Duk wata matar so a bayanki take Gimbiya Ma vie. Kin ci Agadez kin ci Nigeria" ta murguɗa masa baki, ya shammace ta ya yi kissing ɗin bakinta.

****

Asal ce a gaban Sultan, da Matawalle da Sardauna, ga kuma Tafawa sai Imam Asadullahi, da Imam Hammad sai Mahmoudu.

Matawalle ya ce "Na san za ku yi mamakin dalilin da ya sanya, muka neme ku a yammacin nan, bayan sallar magariba haka. Mun san za ku ji abin wani banbarakwai, amma mu ma haka nan ya zo mana. Duk ana kan dambarwar ɗa da Imam Hammad yake da shi, wani abu ya sake faruwa da dole mu yi muku bayani, domin babu yadda muka iya mu ma, sai dai mu na kan tunanin matakin da za mu ɗauka."

Tafawa ya ce "Mai girma Matwalle, wannan kwana-kwanar ta yi yawa, ka yi mana bayani kai tsaye."

"Kamar yadda ka yi ta bin diddigi a baya, tabbas Hammad ya yi rashin lafiya, ya kuma je Nigeria jinya. Asal na san abin da ki ka gani ya ɗaga miki hankali kina ta wasi-wasi. Ɗan da Hammad yake da shi, ba ɗan kowa ba ne face ɗan matar da ki ka kawo a matsayin kukunsa. Wannan kukun tasa matarsa ce"

AREWABOOKS

Wani irin nannauyan numfashi Asal ta ja, tana jin kamar daga shi ba zata sake jan wani numfashin ba. Gaba ɗaya sai ta kasa gane me ma ake son a yi mata bayani. Wace ce ma kukun? Take tambayar kanta. Tafawa ma sak ya yi, yana murza yatsun hannunsa, ya tsare su da idanu ɗaya bayan ɗaya, sannan ya numfasa ya ce "Ku na nufin Imam Hammad ya auri wata wadda ba ƙabilarmu ba, daga Nigeria har ta haifa masa wannan yaron da na gani?"

Sardauna ya ce "Haka ne"

Ya sake rausayar da kai ya ce "To ina fatan a wannan karon, za ku yi adalci dokar masarauta ta yi aiki a kansa, a yi masa hukunci daidai da abin da ya aikata."

Sardauna ya ce "Tukuna dai, sai mun ga abin da hali ya yi, saboda yanzu hankalinmu na kan samun lafiyarsa"

"Lafiya, wace irin rashin lafiya kenan yake fama da ita? Kuma me ya kai shi Nigeria? Kuma a kan me ya karya dokar masarauta?"

Matawalle ya ce "Wannan duk abu ne da za ka ji daga baya, amma yanzu a kan wannan gaɓar muke, zuwa gaba kaɗan za mu duba abin da ya dace a yi"

Wani irin kuka Asal ta fashe da shi ta ce "Hammad, abin da za ka yi mini kenan, ka munafunce ni? Ka cutar da ni, ka ajiye ni hoto ban haihu ba ka je ka haihu da wata. Saboda ka tozarta ni ba ma ka auri Buzuwa daidai ni ba sai wannan ƙazama mummunar yarinyar?"

Tafawa ya ce "Rufe mini baki, mutuniyar banza uban waye ya ce ki je ki kawo ta gidan sarauta, a matsayin kukun mijinki, alhalin kin san ba haka dokar masarauta take ba?"

Hammad ya kalli Asal ya ce "Ki yi haƙuri, na san na yi miki laifi mai girman gaske, amma ina mai baki haƙuri yadda al'amuran suka kasance ba wai da gangan na yi ba. Kin san babu yadda za a yi ina zaune haka kurum na ɗau jiki na tafi Nigeria na...

"Ka yi mini shiru, babu wata magana da zaka faɗa na yarda da kai, maƙaryaci...

"Hattara!" Matawalle ya yi mata tsawa.

"Ko me ya yi miki, dole ki ambace shi da girmamawa kar ki kuskura ki faɗi wani abu mummuna a kansa, ko me ya yi kuwa. Dan haka ki kiyaye harshenki"

Cikin kuka take cewa "Wallahi sai ka sake ni, ba zan zauna da kai ba, kuma na bar ka da Allah sai ka sake ni"

Sultan ya yi gyaran murya ya ce "Yarinyar kirki, na san za ki ji abin wani iri, amma babu abin da zai raba aurenki da Imam. Haryanzu mu na kan tattauna matakin da za mu ɗauka amma sai kin bamu cikakken haɗin kai kin nutsu. Haryanzu ke ce halattacciyar matar Imam da kowa ya san da zamanta."

A fusace Tafawa ya tashi ya kalli Asal, da gaba ɗaya ta rikice take kuka ya ce "Ke tashi mu tafi" Ta yinƙura ta tashi ta yanke jiki ta faɗi.

Hammad ya taso da sauri ya nufo ta, amma Tafawa ya ce "Kar ka kuskura ka taɓa mini 'ya" Ya kalli Asadullah ya ce "Zo ka ɗauke ta mu tafi"

Hammad ya ce "Ba zai yiwu ba, ba zai ɗauke ta ba. Kar ya fara taɓa mini mata"

"Ni ka ke gayawa kar ya fara taɓa maka mata?"

"Ni nake da hurumin ɗaukarta, ko na taɓa ta ban yarda ya taɓa mini mata ba" Ya yi maganar yana tsare Tafawa da ido.

Sardauna ya ce "Tafawa ko da an samu rashin fahimta, bai kamata a ce ka hana shi taɓa matarsa ba, sai ka gama wannan ɓaɓatun ita kuma ta baka kunya, ai ba a shiga tsakanin mata da miji. Bari a kira barori mata su zo su ɗauke ta, a kai ta ɓangaren Gimbiya Bilkisu"

Ya ce "Babu wanda ya isa, ba wanda zai taɓa mini 'ya"

Sultan ya ce "Umarni ne, a kaita sashen Gimbiya Bilkisu, idan ta farfaɗo ta ɗan nutsu sai a kai ta gida" Tafawa ya tsaya cak yana kallon Sultan cikin ƙunar rai. Ƙaninsa yana ba shi umarni kuma dole ya bi.

***** Wata kyakykywar matashiya ce ta shigo ɗakin, ta tarar da ita a zaune tana bawa jaririn Nono. A rikice ta ƙarasa da sauri tana faɗin "Sister kin farfaɗo Alhamdillah, Alhamdillah, Alhamdillah ala kulli halin. Barka da arziki sannu" Ta ƙarasa gaban gadon tana rungume Shukura. Shukura ma ta rungume ta, tana faɗin "Na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi"

Ta kalli Shukura ta ce "Babu komai, ni dai na gode wa Allah da ya sanya ki ka farfaɗo ki ka tashi. Sannu 'yar uwa" Ta sake maganar cikin iyayi da kulawa.

Ta kalli likktar da ta take ta ɗawainiya da Shukura, ta ce "Sannu da ƙoƙari doctor, Allah ya biya ki kema"

Doctor ta ce "Ba komai, yi wa kai ne."

"Yanzu kawo lambar wani a kira miki"

Shukura ta ɗan yi shiru sannan ta ce "To" Ta bayar da lambar Sagir, aka saka a wayar aka danna kiran wayar"

Shukura ta miƙa hannu, ta karɓi wayar. Muryar Yusra ce ta yi mata sallama, ta tsuke fuska ta ce "Ina Baban Haidar"

Wata irin rikicewa Yusra ta yi, ta ce "Shukura ke ce? Ina ki ka tafi muke ta neman bamu ganki ba? Kina ina?"

Sai Shukura ta ɗan yi saroro, jin yadda Yusra ta rikice da murna.

"Ina nan, idan yana kusa ba shi wayar"

A rikice Yusra ta sake cewa "Baya nan, ki gaya mini kina ina na zo na ɗaukko ki?"

"A'a ina nan lafiya kalau, idan ya dawo ki haɗa ni da shi"

Yusra ta ce "Baya nan, layinsa ya saka a wayata, ni ban san lokacin da zai dawo ba, ki gaya mini kina ina?"

Kamar Shukura ta share ta katse wayar, sai kuma ta gaya mata. Tana can wani Asibitin kuɗi, a can wata local government a wajen Kano. Sannan ta ɗora da cewa "Amma kar ki gaya wa kowa mun yi waya da ke"

Yusra ta ce "Har mamanki? Tana can hankalinta a tashe fa ita ma"

"Eh har ita, kar ki gaya wa kowa, idan ya dawo ki haɗa ni da shi, ina Haidar? Yana lafiya?" Ta yi maganar hawaye na cika mata ido, cike da fargabar ko shi ma ya salwanta.

"Yana makaranta, to kina lafiya cikinki ma yana nan lafiya?"

Shukura ta ce "Eh, lafiya kalau"

"To dan Allah kar ki je ko ina daga nan gurin"

"Tom" Ta faɗa a taƙaice.

Matar ta kalli Shukura ta ce " 'Yar uwakki ce?"

Ta girgiza kai ta ce "Abokiyar zamana ce"

"Allah sarki, gaskiya daga ji tana sonki sosai ji yadda ta rikice" Shukura ta yi murmushi kawai. Sai dai ta tafi tunanin ta yadda za ta fuskanci Duniya ta sanar da cewa mahaifinta shi ke da alhakin sace ta, da salwantar mata da ɗa, da kuma mummunan zaluncin da ya yi wa mahaifiyarta da wadda yake tare da ita yanzu. Ita gaba ɗaya ma ba ta san ta ina zata fara bayanin miyagun ayyukansa a idon duniya ba a matsayinsa na mahaifinta.

**** Nana tana son ta ga Sarkin Baka, akwai maganganu da dama a bakinta, amma ƙiri-ƙiri Sayyid ya hana. Ga shi ba ta da damar fita idan ba umarnin hakan a ka ba ta ba, tana son sake ganin Nene ma amma babu halin fita.

Zaman Nana a guri ɗaya, ba fita daga ci sai sha da kwanciya, ya sanya ta ƙara yin kyau, ga lafiyayyen Abinci. Sai dai haryanzu kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya ne ba ta da shi.

Tana zaune tana zancen zuci, har bacci ya fara sace ta, ta ji an taɓa ta. Ta tashi da sauri tana kallonsa. "Har kin fara bacci ba ki jira ni ba?"

"Eh, na zata a gurinta zaka kwana ai"

"Idan ma na kwana a can ɗin, ai ke ki ka ja, kin daina damuwa da ni, ko tausayina ba kya ji"

Ta kwaɓe baki ta ce "Garin tausayinka, na kwashi wani cikin na haihu ku kaɗa ni Nigeria"

Ya ɗan marairaice murya ya ce "Haba Ma vie, Sayyid ɗinki ne fa, ke ba kya kewar ɗumin jikina ne"

Nana ta kalle shi ta ce "Wane ɗumin, ai yanzu jikinka ba wani ɗumi idan ba azaba ba"

Ya rausayar da kai ya ce "Da ɗin ma akwai, kuma kina jurewa"

Ta girgiza kai ta ce "Amma bai kai na nan ba"

"To ni ki bani Sanyin dan Allah"

Ta tsuke fuska ta ce "Sayyid ka daina taɓa ni dan Allah, ni ba ƙin ka nake yi ba, amma ka tausaya mini inga yadda al'amuran za su kaya tukuna, ka san dambarwar da ake ta yi haryanzu ni tsoro nake ji kar a yi mini yadda aka yi wa Nene" Ya kwanta a gefenta ya numfasa ya ce "Ta baki labari kenan?"

Ta jinjina masa kai alamar eh.

"In sha Allah a kanmu wannan muguwar al'adar za ta zama tarihi, dan ba zan yarda na rabu da rayuwata ba"

Nana ta zumɓura baki tana kallonsa, ya ce "Da gaske nake Ma vie" Ya yi maganar sumbatar hannunta.

Ta ɗan lumshe ido tana kallonsa. Ya ce "Tashi mu je"

"Ina?"

"Zo mu je ki gani mana, ko zan cinye ki ne" Ya yi maganar daga kwnace yana ci gaba da kallonta.

Ta tashi zaune tana faɗin "Na sani, ko cinye nin zaka yi. To ka tashi mana kuma ka kwanta"

Ya yi shiru bai ce mata komai ba. Ta waiwaya ta kalle shi, ta ga yana yi mata wannan kallon yana shafa bayanta.

Ta ce "Yane? Ko in kwanciyata ne?"

Ya ce "Allah sarki Hammad bawan Allah, kowa baya so na" Ya yi maganar yana tashi zaune. Nana ta yi murmushi ta kai hannu ta shafa gashinsa ta ce "To dama wa zai so rigimamme"

"Allah sarki, Ina kewar Ma vie ɗina ta da, mai so na da tausayina, ko motsi na yi hankalinta yana kai na, Allah sarki Asmyna ta Nigeria, soyayyarta ta daban ce a cikin zuciyata"

Nana ta ce "Allah sarki Sayyid ɗina na Nigeria, da baya ganin kowa a duniyarsa sai Asmynsa kaɗai. Mai kallona da idon tausayi, wanda nake iya gano ƙaunata da tausayina a idanunsa, mai yaba duk wani motsina da ƙoƙarina. Ina kewar Sayyid ɗina na Nigeria"

Ya lumshe idanunsa ya buɗe ya ce "Wannan Imam ɗin na Agadez fa?"

Ta kalle shi ta ce "To ga shi nan dai, ban ma san inda ya dosa ba" Ta ƙarasa maganar tana murguɗa baki.

Ya yi dariya ya ce "Haka za ki ce ko? Ni ɗin ko? Sayyid ɗinki ne fa"

"Sayyid nawa, Hammad na Asal"

Ya ce "Wow, sake faɗar sunan na ji?" Ta noƙe masa kafaɗa.

Ya ce "Shikenan ma, dama Asal ta fiki iya faɗar sunan" Ta harare shi, tare da sauka daga kan gadon. Shi ma saukkowar ya yi, ya wuce gaba ta bi shi a baya. Daga bisani ya jira ta, suka tafi tare. Ƙofar nan da suke bi su fita hanyar saharar nan, suka shiga, sai dai wannan karon canza akalar hanya, zuwa wata matattakala. Tsoro ya fara kama Nana, amma ta kasa magana, sai rarraba ido kawai da take yi.

Wata ƙofa suka iso, ya ce "Kin san ina ne nan muka ɓullo?"

Ta ce "A'a"

"Gidan tarihi ne na masarautar Agadez"

Nana ta ce"Wannan dutsen da nake hangowa?"

Ya jinjina kai ya ce "Eh nan ne"

Wani takurarren tsoho suka tarar a bakin ƙofar shiga gurin, yanayin ƙofar ya bayyanar da tsufan da ta yi a Duniya. Tsohon ya miƙe jikinsa na rawa, ya risuna yana gaida Imam Hammad.

Hammad ya amsa cikin girmamawa. Nana ta ɗan tsaya ta yi shiru, tana nazarin ƙamshin turaren da ta ji a gurin, kamar ta taɓa jin sa a jikin wani, sai dai ba ta ga alamun a jikin wannan tsohon wannan ƙamshin yake tashi ba.

Ya buɗe musu ƙofar, suka shiga. Ya kunna makunni, sai ga hasken fitilun ya haske gurin.

Ya ci sunansa gidan tarihi, Nana ta faɗa a zuciyarta. Wani irin ƙaton guri ne mai kama da falo, da ƙofofi kashi-kashi a gurin.

"Wannan gurin kamar Libraryn Ƙaisar saboda tsufa" Ta ɗaga kai tana kallon tsawon gurin, jikin dutse ne aka rarake aka yi wannan ginin da ƙofofi. Kanta ne ya sara ta yi shiru tana tunanin kamar ta san gurin nan, ta taɓa ganin gurin. A take ta fara jiyo wannan ƙamshin da take ji idan ta gan su a wannan ɗakin tare da Sayyid.

Hammad ya kama hannunta ɗaya, ya buɗe ƙofa suka shiga, a take ta sske rikicewa, jikinta ya hau rawa ta kalle shi ta kalli ɗakin, ta sake kallonsa ta kalli ɗakin.

"Sayyid wannan ɗakin"

"Ɗakin da muke zuwa ko?" Ya yi maganar yana yi mata murmushi.

Ta kalli gadon, da mudubin ɗakin, komai irin na da sosai da sosai, sai dai yanayin kayan ya nuna, wanda suka yi amfani da ɗakin masu faɗa a ji ne. Ta dafe kanta da take jin wata irin ƙara a ciki, ga ƙamshin turaren nan ya cika ilahirin gurin.

"Sayyid wai ya aka yi haka ta faru a zahiri? Kar daga baya ka ce mini mafarki ne, ka fita da ni daga gurin nan kar na haukace Sayyid"

"Ba za ki haukace ba, ki tsaya na yi miki bayani"

Wani irin jiri ne ya din ga ɗibarta, ta din ga ganin wasu irin halittu na shawagi a ɗakin, ga hayaniya da suke yi cikin sauti mara daɗin ji.

Jikin Nana na tsuma ta ce "Ka fita da ni daga gurin nan, wasu abubuwa nake gani ka fita da ni"

"Babu wani abun tsoro fa a gurin nan, ki nutsu zan gaya miki komai daki-daki ciki har da abubuwan da suke shige miki duhu a kaina"

Ayshercool 08081012143

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull