Kenza eBookz

Buzu book 3 complete - Chapter 16

Buzu book 3 complete - Chapter 16

Buzu book 3 complete Chapter 16: Buzu book 3 complete Chapter 16. Hammad ya zuba ido sosai, ya ga ɗan abin tsoho ne tukuf sosai da sosai. Domin kuwa…

4,322 words

Hammad ya zuba ido sosai, ya ga ɗan abin tsoho ne tukuf sosai da sosai. Domin kuwa gemunsa ƙasa yake ja.

Ya ce "Amma da idan na murza zoben ba kai nake gani ba"

Arun ya ce "Ai ba ni ka ke kira, hadiman wancan zoben daban, nima kuma daban"

"To ina zoben nawa yake?"

"Ka yi kyautarsa ga wanda ka ke matuƙar ƙauna a matsayin tukuicin soyayya"

Hammad ya ce "Soyayya kuma? Ni ɗin?

"Ƙwarai ya shugabana"

"To wa na bawa, kuma yaushe na yi soyayyar, kuma mace ce ko namiji?"

Arun ya sake cewa "Ba na son shiga hurumin da ba nawa ba, ina gudun sake rura wutar fitinar da ke tsakanin gangar jiki buyi, ruhika huɗu, alaƙa huɗu. Gangar jiki ta mutum biyu, ruhi huɗu, na mutum biyu da na aljan biyu, sai kuma alaƙar mata da miji da kuma uba da ɗa, sannu a hankali duk za ka fahimci abubuwan da nake nufi" Daga nan ya ɓace Hammad ya yi shiru yana juya maganganun da suka fi yi masa kama da shirme. Ya tashi ya fita falo, ya san lokacin kawo masa shayin dare ya yi, sai dai tun kafin ya ƙaraso cikin falon yake jiyo sautin muryarta tana waƙa. Daga nesa kaɗan ya tsaya yana kallonta, yana jin yadda zuciyarsa take bugawa da sauri.

*_ina zana ganka_* *_saƙo zana baka*_ *Hotona da naka*_ *_Ko ina zana bika*_ *_Kowa tsane ka, ni na tsane shi sanya a ranka*_ *_Zuciyata na baka duk masu ƙin ka su daina shakka*_ *_Rayuwata na baka_* *_Ni ta ya zan guje ka*_ *_Ka dawo gare ni dan zuciya ta bar kewa*_

Gaba ɗaya sai ya daskare a gurin, gumi ya din ga tsatstsafo masa, ƙwaƙwalwarsa ta shiga Kai komo, kansa kamar zai yi tsawa ya fashe. "Tabbas akwai wani abu, ya san wani abu mai kama da haka, amma yaushe? Kuma a ina?" Ya daɗe a tsaye a gurin, kafin ya saita nutsuwarsa ya shiga falon. Murmushi ta yi ta daina waƙar da ta ga ya fito ta risuna ta ce "Barka da dare" Ya jinjina mata kai.

"Sayyid ga shayinka nan, ina fatan na kammala komai, zan iya tafiya?" Ya yi shiru yana jujjuya Sayyid da take kiransa da shi.

Washegari da sassafe ya kira Mahmoudu a waya, ya sanar masa da yana son ganinsa za su yi magana. Amma Mahmoudu ya ce masa yana hanyar Maraɗi, zai kai wa Nene ziyara ne. Hammad ya yi ta mitar me yasa bai gaya masa su tafi tare, su je su gaishe ta, ya ba shi haƙuri. Sai dai tun da Mahmoudu ya je ya ga Muhsin ya rikice, ya din ga yi wa Nene tambayoyi a kan Muhsin, amma ta ƙi gaya masa haƙiƙanin gaskiyar waye Muhsin. Sai dai yanayin yadda ta ga Mahmoud ya rikice, ya sanya ta tabattar da ya ga abinda take tunani ita ma. Kwanansa ɗaya ya shirya ya nufo Agdez bayan ya faki idon Nene ya ɗauki hotunan Muhsin. Ya nufi Agadez da nufin komai zai faru sai dai ya faru. Hammad kuwa ya lallaɓa Asal ya yi mata wayo ya sanya ta dawo da Nana sashen su, ba tare da ta kawo komai a ranta ba. Amma shi a jikinsa yana jin baƙin abubuwa game da 'yar Nigeria da jikinsa bai ba shi cutar da shi za ta yi ba, amma kasancewarta daf da inda yake yana samun nutsuwa da nishaɗin kallonta. Tun da Mahmoudu ya dawo, Hammad ya lura bakinsa akwai magana, amma ya ƙi ce masa komai. "Mahmoudu na lura bakinka akwai magana, amma ka ƙi gaya mini, duk da ba ma 'yar haka da ni da kai, amma bari ni na gaya maka tawa damuwar". Mahmoud ya ce "Ni babu wani abu da zan gaya maka, amma gaya mini mene ne yake damunka?"

"Ina kukun da nake gaya maka Asal ta samo 'yar Nigeria?" Gaban Mahmoud ya faɗi amma ya dake ya ce "Eh meyafaru?" "Wasu abubuwa nake ji game da ita, da tun da nake ban taɓa ji game da wani mutum ba" Mahmoudu ya yi murmushi ya ce "Ko santa ka ke yi ne?"

"Anya kuwa, ban dai sani ba, amma ba normal mutum ba ce"

"Ka na da mata fa a Nigeriar nan"

Hammad ya kalle shi yana jiran ƙarin bayani. Mahmoudu ya ce "Da wasa nake yi, na dai ce zan aura maka 'yar maka 'yar Nigeria idan ka na so. Amma ina da wani abin al'ajabi da nake son nuna maka, amma tashi mu je ka shirya, ka ce mini za ku yi hawan raƙuma kar a yi ta jiran ka" Babu musu ya tashi suka fita. Kowanne a cikin su yana ta saƙe-saƙe a cikin zuciyarsa. Sai dai bayan an yi hawan raƙuman, da Hammad ya faɗo tare da Mahmoudu aka dawo da Hammad gida. Sai dai ya yi mutuwar tsaye, da hango ta tana leƙen mutanen da suke kaiwa da komowa a falon fuskarta ɗauke da damuwa.

A jere zuciyar Mahmoudu ta buga, addu'a ya fara yi, a kan Allah ya sanya ba mafarki yake yi ba, ko kuma tsabar saka abin a ransa ne ya sanya ta fara yi masa gizo ba.

Ayshercool 08081012143

93 93 LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KUƊIN KARATU KAFIN KI KARANTA. 08081012143

Cikin hanzari Habu ya ja rawaninsa ya nufi barin falon, yana daf da fita Nana ta waiwaya ta ga wucewarsa, sosai ta tsaya tana kallon bayansa har ya fice tana yi masa kallon sani. Washegari da safe Bayan Tafawa ya zo duba shi, ya tafi zuciyarsa a cunkushe babu daɗi, saboda kausasan kalaman da Tafawa ya yi amfani da su, har da ce masa ko shaye-shaye yake yi, shi ya sanya ya faɗo daga kan Taguwa. Wajen ƙarfe sha ɗaya, da ya ji sauƙi, ya lallaɓa ya fito, yana mamakin dalilin da ya sanya Nana hana shi hawa kan Taguwa, da ya hau kuma ya faɗo. Yana fitowa ya tarar da ita da Asal su na mujadala. Sai dai hangota kawai da ya yi, sai ya ji wani sanyi a ransa.

Nana ce take kallon Asal cikin takaici, bayan da Asal ta ce mata ta din ga sanya da hadiman gidan suke sakawa. Nana ta rasa dalilin da ya sanya Asal ke son ƙasƙantar da ita ko ta halin ƙaƙa. Nana ta dube ta ta ce "A gaskiya ba zan iya sanya kayan da hadimai suke sanyawa ba, ko ki haƙura ki kalle ni da kayan jikina, ko kuma ki sallame ni. Tun da ni ba baiwarki ba ce ba, aiki kawai ki ka ɗaukko ni na yi miki"

"Idan na so mayar da ke baiwar tawa ina da halin yin hakan, ke kin san ina da abin da ko nawa za a yi miki kuɗi zan iya bayarwa na saye ki"

"Ko da Goma ta lalace a gaban biyar take har gaban Abada Gimbiya Asal. Kuma wani garin ya fi gaban kunu. Ba ki da arzikin da za ki Asma'u a matsayin baiwarki" Nana ta ƙarasa maganar a zafafe. Hammad ya yi gyaran murya, suka tsaya Asal ta haɗiye maganganun da ta yi niyyar caɓawa Nana.

"Cherié, ba zai yiwu ki ɗaukko wadda ba hadima ba a cikin gidan nan, alhalin kin san kin taka dokar gidan mulki ba, sannan ki ce ta din ga saka kayan hadimai a nan ta fiki gaskiya."

Cikin mamaki Asal ta kalle shi za ta yi magana, amma ya ɗora yatsansa a kan laɓɓansa a dole ta yi shiru. Nana kuwa haɗa su ta yi, tai musu kallon banza ta wuce ta bar su a gurin. Sai dai kallon da ta yi musun, sai da ya kusa ɗimaucewa, ji ya yi tamkar ya bi bayanta. Wani murmushi ya saki ya nufi Asal yana lumshe ido ya ce "Ba girmanki ba ne, ki din ga sa'in sa da ma'aikatanki ai kin wuce nan".

"Amma ka na kallo a yadda take yi mini magana, kuma ka hana ni magana?" Ta yi maganar kamar za ta yi kuka. Ya kamo hannunta ya ce "Yawan musayar yawu da na ƙasa da kai, raini yake janyowa, kuma kar ki yadda ki yi fin ƙarfi a abin da ba ki da gaskiya, nan ma raini zai din ga janyo miki" Ya ƙarasa maganar yana rungume Asal, amma a zahiri hanyar da Nana ta bi, ya bi da kallo ƙamshin turarensa da ta shafa ya ci gaba da karaɗa hancinsa.

Mahmoudu kuwa bai yi bacci ba, so yake ya tabattar da abin da idanunsa suka gane masa, gaskiya ne ba gizo ba. Ya kira wayar Hammad, amma bai ɗauka ba, ga shi tsoron zuwa gidan yake domin kar su haɗu da Nana, ya san komai zai rikice ne. Ga yaron da ya gani a gurin Ummansa, ga kashedin su Matawalle, ga kuma wannan abu da ya tarar. "Anya yaron na ba ɗan Hammad ba ne?" Ya tambayi kansa. Wayewar garin Allah ya din ga kiran Hammad a waya amma bai ɗaga ba. Takaici ya ishe shi, sai can wajen Azahar sannan ya kira Mahmoudu.

"Tun jiya nake kiran ka ka ƙi ɗaga wayata"

Hammad ya ce "Ban jin daɗi ne, sai yanzu na duba wayar, ya ake ciki ne?"

Mahmoudu ya ce "A ina zamu haɗu, ina da magana da kai"

Hammad ya ce "Ina gurin Sultan, haryanzu bai sallame ni ba"

"Idan ya sallame ka, mu haɗu a saharar gidan tarihi mu sha shayi, zan nuna maka wani abu"

Hammad ya ce "To, saura na ga ba wani abin kirki ba ne, ba za ka yi mini ya jiki ba?"

Mahmoudu ya ce "To ya jiki Allah ya kiyaye gaba sai mun haɗu"

Hammad ya yi murmushi ya ajiye wayar.

Da yamma suka haɗu a sahara, lokacin rana ta yi sanyi. Hammad ya ce "Sai wani nema na ka ke yi, me za ka bani?"

Mahmoudu ya ce "Babu komai shayi kawai nake son mu sha tare."

Hammad ya yi shiru yana kallon saharar, daga inda suke su na hango gidan tarihi, kuma suna hango wani sashe na gidan sarauta. Ya na shan shayin a hankali yana son ya tuna wani abu, amma ya kasa. Mahmoudu ya ce "Ya na ji ka yi shiru?"

"Ina tunanin yarinyar nan ne"

"Wacce?"

"Wadda Asal ta kawo, a matsayin mai yi mini girki, abubu da dama su na faruwa da na kasa gane kansu" Nan ya sake gaya wa Mahmoudu yadda ta hana shi hawan taguwa, da abubuwan da yake ji game da ita" Mahmoudu ya ce "Kuma kai ba ka santa ba, baka taɓa ganinta ba ko a wani guri?" Ya ɗan yi shiru Sannan ya girgiza kai ya ce "A nan kawai na taɓa ganinta" "Baka tuna komai ba, da muka zo gurin nan?" Nan ma ya girgiza kai duk da yadda ya ji kansa ya fara ciwo. Mahmoudu ya ce "Gaskiya yakamata a ce duk yadda za mu yi, muyi bincike a kanta, mu san daga ina take, kar mu sakankance wani abin ya faru. Ka san ita kanta Gimbiya Asal ba ta yin abu babu dalili, kar mu je shirin Tafawa ne"

Hammad ya ce "Gaskiya ne, amma ta ce mini daga gidan cin abinci na Maraɗi ta ɗaukko ta a gurin su Al-Husssain"

Mahmoudu ya ciro wayarsa ya daddana, ya miƙa masa ya ce "Ka ga wani ikon Allah" Hammd ya sanya hannu ya karɓa, ya yi shiru ya zuba wa wayar ido. Jiki a sanyaye ya ɗago ya kalli Mahmoudu ya ce "Ina ka samo wannan hoton?"

"Samo shi na yi kawai na nuna maka"

Ya damƙe wayar da ƙarfi, ƙirjinsa ya yi masa nauyi ya ce "Mahmoudu kuma ka tabatta wannan ba ɗana ba ne ba? Duk wanda ya kalli wannan hoton zai yi zaton ma nine" "Ka na da wata matar ne da zata haifa maka ɗa? Ko kuma Asal ta haihu ne bamu sani ba?" Ya girgiza kai ya ce "Ko ɗaya, amma wannan yaron buzu ne, duk inda iyayensa suke ka nemo mini su a faɗin ƙasar nan"

"Me za ka yi musu?"

"Zan yi musu alkhairi ne kawai. Amma Mahmoudu kawai ji nake kamar ina da alaƙa da shi, dan Allah ka tura mini hoton nan"

Mahmoudu ya karɓi wayar ya ce "Zan tura maka" Gaba ɗaya jikinsa ya yi sanyi, ya kuma kasa shan shayin. Sule ne ya zo gurin a kan babur, ya kafe baburin, ya sauka ya gaida Hammad cikin girmamawa. Hammad dai ya amsa yana bin sa da kallo. Suka gaisa da Mahmoudu ma, ya ga sun sake sun fara hira. Mahmoudu yana ta satar kallon Hammad, ko zai ɗago ya tuna wani abin, amma ya ga babu alamar hakan. Bayan tafiyar Sule, yake gaya masa ai abokin kasuwancinsa ne na Nigeria. Kawai ya jinjina kai.

Ƙaisar ne ya bayyana a gaban Giyaz, fuskarsa babu annuri ko kaɗan. Giyaz ya ɗaga kai ya kalle shi, ya ce "Ɗan samari ya dai?"

"Zuwa yaushe zaka ci gaba da wannan mugun wasan da ka ke yi?"

Giyaz ya ce "Wanne daga ciki?"

"Kowanne ma? Ka dawowa da mutumin nan tunaninsa ya tuna da yarinyar nan, ga ɗa a tsakaninsu ko iya yanzu ka ɗauki fansar ai, ka ƙyale ta ta huta haka?"

"Yaro yaro ne. Yarinyar da kakaninta suka cutar da mu, ta zo ta ƙona ni ta sanya ni jinya, ita ka ke tunanin na ɗagawa ƙafa ma sassauta mata?" "Ba na son alaƙata da kai ta ƙara tsami, amma zan yi abin da ba ka zato, ba zan zuba ido ka ci gaba da cutar da ita har haka ba" Ƙaisar ya yi maganar cikin ƙunar rai. Giyaz ya ce "To babu laifi, ka yi abin da duk za ka yi"

Hammad kuwa da ya koma gida, ya kasa zaune ya kasa tsaye, hoton yaron nan ya din ga kaiwa da komowa a cikin kwanyarsa. Yaya za a yi a ce a samu yaro yana irin wannan kamanin da shi, ba kamanni sama-sama ba, kamanni na zahiri nesa ba kusa ba. Bayan haka yaron ya yi masa kama da wani wanda ya sani ko ya taɓa gani, amma ya manta waye, ya din ga duba wayarsa ko Mahmoudu ya turo masa hoton yaron, amma wayam bai tuta masa ba. Gefe guda ya so haɗuwa da Nana, amma bai ganta ba. Sai washegari da ta kawo masa Abincin safe ta yi masa ya jiki. Ya ce "Sai yanzu za ki yi mini ya jikin?" Ya yi maganar yana tsare ta da manyan idanunsa, saboda wani irin kyau da ta yi masa. Ga ƙamshin da take yi, har wani ƙara nutsuwa ya yi yana kallonta. "Tuba nake ranka ya daɗe" Sayyid ɗin da take kiransa da shi, ya din ga kaiwa yana komowa a cikin kwanyarsa. Haka da rana da ta yi shigar Atamfa, kamar ya sace ta ya gudu. Ta karya ɗaurin ɗan kwali, ta yi kyau. Ya ce "Amm Asma'u ko?" Ta jinjina masa kai duk da yadda ta ji Asma'un banbarakwai a bakinsa. "Cherié ta ce mini a gidan cin abinci na Maraɗi ta ɗaukko ki ko?" "Eh Sayyid" "Me ya kawo ki Niger ne? Ko takanas ki ka nemi aiki da mu, tun daga Nigeria?" Nana ta girgiza kai ta kalle shi ta ce "Abuna ne ya ɓata na zo Niger neman sa, ina son a yi mini izini, nan kusa na koma Nigeria" Ya jinjina kai kawai ba tare da ya gama fahimtar abin da take nufi ba. A daren ne kuma Nana ta jiyo kakarinsa, Asal ta fice ita kuma ta shiga ɗakin. Ƙara lafewa ya yi tamkar ya shige cikin ta, saboda daddaɗan sanyin da ya mamaye jikinsa. A hankali ya buɗe idanunsa, ya ji yadda ta ƙanƙame shi tana kuka. Ya saurara ya yi shiru ya ji ba muryar Asal ba ce. "Allah ka duba mu, ka yaye masa wannan ciwo, Allah ka yi masa maganin abin da yake damunsa. Yana jin yadda take shafa gashinsa tana ci gaba da kuka tana faɗin "Da gaske ba ka gane ni ba Sayyid, ko kuma wasa ka ke yi mini da hankali kawai. Na fara sarewa Sayyid, idan wasa ne ka tausaya mini haka, wahalar da na sha ta isa, ka duba ni ka duba makomar abin da na haifa maka dan Allah" Ta yi maganar tana ƙanƙame shi tana ci gaba da kuka. Gaba ɗaya sai ya rikice, bayan kukanta da maganganun da take yi da suka rikita masa lissafi, gangar jikinsa kuma wani saƙon take aika masa na daban, har wata tsuma ya fara yi. Sai dai Allah ya taimake shi, bai yi wani yinƙuri ba, ya ji tana magana da Ƙaisar, ta kwantar da shi a kan pillow ta koma gefe. Tunani ya din ga yi ina Asal ta tafi? Ya aka yi Nana ta shigo har turakarsa kai tsaye haka, kuma wasu irin maganganu take yi haka? Ya yi lamo kamar bacci yake yi, amma idonsa biyu. Sai gefin Asuba da ta bar ɗakin, ya tashi ya zauna, yana jin wani irin raɗaɗi a tsakiyar kansa, zuwa ƙirjinsa gaba ɗaya ji yake kamar zai fita hayyacinsa ƙwaƙwalwarsa na nema ta hargitse. Garau ya miƙe bayan sallar asuba, ya sake tuna yaron da Mahmoudu ya nuna masa, da maganganun da ya ji Nana tana yi. Ya kira Al Hussain a waya, ya ce masa lallai yana son cikakken bincike a kan Nana. Ga Sultan ya tura shi wakilicin wani ɗaurin aure, amma kusan baya cikin cikakken hayyacinsa, kansa cunkushe da lissafi kala-kala. Maganganun Nana suka din ga karafkiya a cikin kwanyarsa, da rungumar da ta yi masa ba tare da tsoron komai ba. Ko da ya dawo, har ya wuce ɗakinsa, amma kansa ya din ga wani irin ciwo, kawai ya yanke shawarar zuwa ya turke Nana, ta yi masa bayani dalla-dalla. Sai da ya bari Asal ta yi bacci, sannan ya tashi ya tafi ɗakin Nana. Sai dai da ya je ɗakin ya tarar ba ta ciki, sai wayarta da take kan katifarta a ajiye. Har zai juya ya fita, kawai ya nufi kan katifar ya sanya hannu ya ɗauki wayar. Ya jujjuya wayar, yanayin yadda screen ɗin wayar ya dusashe ya sanya ya gane wayar ta kwana biyu. Kawai ya danna madannin gefe a take hoton fuskar Nana da Muhsin ya bayyana a kan screen ɗin wayar. Mutuwar tsaye ya yi zuciyarsa ta yi wani irin mummunan bugawa da ƙarfin gaske. Alamun tahowar Nana ya ji, babu shiri ya jefa wayar kan katifar ya yi sauri ya kashe fitilar ɗakin.

AREWABOOKS

Ko da Nana ta shigo ɗakin, jikinta ya bata akwai mutum a ciki. Da ta kunna fitilar ta yi arba da shi, ta rikice ta kusa kurma ihu, sai dai duk da a tsorace yake shi ma, amma kasancewar sa Namiji ɗan gwagwarmaya ya sanya ya danne tsoronsa da tashin hankalin da yake ciki, ya yi mata duk tambayoyin da ya yi mata, sai dai bai tambaye ta haƙiƙanin abubuwan da yake son tambayarta ba. Duk amsoshin da ta ba shi, ba su gamshe shi ba, haka ya fice ya bar ta. Tun da ya bar ɗakin kusan kwanan tsaye ya yi, ya din ga kaiwa yana komowa a ɗakinsa ya dafe kansa, ya zauna ya tashi. Duk wani lissafi da ya yi sai ya ji babu mafita. Shi dai bai taɓa ganin Nana ba, amma meye haɗinta da yaron da Mahmoudu ya nuna masa? Sannan mene ne alaƙarta da shi da ta iya shiga turakarsa ta rungume shi take faɗar wannan maganganun da suke nuna da alaƙa a tsakaninsu. Har aka yi kiran sallar Asuba ko gyangyaɗi bai yi ba. Da Asuba da ya dawo daga masallaci, har zai wuce hanyar ɗakinta, ya koma ya nufi ɗakin nata. Ya jima a gurin yana kallon ƙofar. Ya buɗe ƙofar ɗakin a hankali. Ya tarar da ita tana bacci. Sai dai abin da bai sani ba, Ƙaisar ne ya ƙara wa Nana nauyin bacci, amma duk abin da yake faruwa tana gani, sai dai ba za ta iya motsi ba. Cikin sanɗa Hammad ya ɗauki wayar ya yi waje. Bai ko sake nufar ɗakinsa ba, ya fice. Gidan Mahmoudu ya tafi, ya je ya tarar da shi a zaune yana lazumi. Sai da Mahmoud ya tsorata ya ce "Lafiya na ganka da duku-dukun nan?"

"Mahmoudu wane ne yaron nan da ka nuna mini? Kuma wace ce yarinyar da Asal ta kawo a matsayin mai yi mini girki?"

Mahmoudu ya kalle shi ya kalli screen ɗin da yake nuna masa, tabbas Nana ce ba wata ba, amma zai so ya yi magana da Nana kafin gaya wa Hammad wani abu. "Ka yi magana ka tsaya ka na kallo na" Ya yi maganar cikin hasala.

Mahmoudu ya ce "To ai Asal yakamata ka tambaya ba ni ba, ni fa cin karo kawai na yi da hoton na nuna maka" Zai yi magana kansa ya sara, ya saki wayar ya fara ja da baya yana dafe kansa, ya tafi zai faɗi Mahmoudu ya yi saurin tare shi, ya kwantar da shi a hankali. Ya ɗauki wayarsa ya kira Al-Husssain. Bayan sun gaisa Mahmoudu ya ce "Imam Hammad ya yi maka magana a kan yi masa bincike a kan yarinyar da Asal ta kawo Agadez ta din ga yi masa girki ko?"

"Eh ya kira ni, ya yi mini maganar"

"To yaya ake ciki, me aka gano a kanta?"

Al Hussain ya ce "Eh ina kan yin binciken ne, amma dai wani kamfani ne, da suke samar wa mata, guraren aiki suka kawo ta. To na saka Hasna ta tuntuɓe su, dan ni gaskiya ban wani tantance ta ba, na ɗauke ta aiki, saboda ta ce daga Nigeria take. To gidan aikin sun ce, su ma wata mata ce jami'arsu ta kawo musu ita. Amma za a nemo matar yanzu haka su muke saurare" Mahmoudu ya ce "To shikenan, amma duk abin da aka ƙarasa bincikowa, ni zaka sanar, ka gaya masa tukuna" Sanin alaƙar da take tsakanin Hammad da Mahmoudu ya sanya kai tsaye ya ce masa to. Hammad kuwa yana kwnace, sai jujjuya kansa yake yi yana wani irin gumi. Giyaz yake gani yana yi masa wata irin dariya, da ƙara wadda ta cika masa kunne. Ya lallaɓa ya tashi zaune ya toshe kunnunwansa yana faɗin "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" Mahmoudu ya durƙusa a gabansa yana kiran sunansa, amma bai amsa ba ya rintse idanunsa. "Sayyid, Sayyid dan Allah da gaske ba ka tuna ni ba?" Maganganun da Nana ta din ga yi masa ya din ga ji a cikin kunnensa. "Mahmoudu" ya kira sunansa a hankali.

"Na'am Imam"

"Mene ne alaƙata da yarinyar nan?"

"Amm ban sani ba tukuna, ina jiran abin da Al Hussain zai ce ne tukuna"

"Ka kirawo ta ka tambaye ta, wane ne yaron nan? Me yasa kuma yake kama da ni?"

"Za a yi, amma ka yi shiru da bakin ka mu gano komai tukuna" Sai zuwa yamma Hammad ya ɗan samu nutsuwa, sai dai bai sake ganin Nana ba, abincinsa ma ajiye masa ta yi. Da daddare Asal ta ɗauki hankalinsa sosai, saboda yadda ta sha kwalliya cikin jajayen kayan bacci sai ɗaukar ido take yi. Yana ta ƙoƙarin kar ya shiga hakkinta, saboda damuwoyin da suka yi masa yawa. Sai dai bai iya taɓuka komai ba, hankalinsa ya fara gushewa. Wani irin haske ya din ga gani a cikin baccin nasa yana ɓullowa ta cikin wani mudubi, sama-sama ya din ga hango shi tare da Nana a ciki, cikin yanayin wata rayuwa da take nuna tsananin kusanci da kyakykywar alaƙa a tsakaninsu. Sai dai bai gama fahimtar abin cikin mudubin ba, Giyaz ya bayyana ya huro wata irin wuta a take mudubin ya tarwatse, ya ja da baya yana kare kansa. Giyaz ya gani tare da Ƙaisar, tsananin kamaninsu tsufan Giyaz ne kawai ya sanya shi ya banbance su. Farkawa ya yi jikinsa ya ɗauki wani irin zafi. Tashi ya yi yana zagaye ɗakin, amma ya ci gaba da jin zafin ya tsananta kawai ya fita ya je hanyar ɗakin Nana ya zauna. Zuciyarsa kuma sai azalzalarsa take yi a kan ya je ya samu Nana ya yi magana da ita, amma wata zuciyar ta hana shi hakan. Giyaz kuwa faɗa ne ya kacame tsakaninsa da Ƙaisar. "Ƙaisar muddin ka yi ƙoƙarin saka mutumin nan ya tuna yarinyar nan, zan iya hallakaka, ko kuma na saka shi ya haukace gaba ɗaya" Ƙaisar ya ce "Kafin ka halaka ni, ni zan halakka ka muddin za ka ci gaba da shiga abin da bai shafe ka ba"

"Ni zaka hallaka, Giyaz bin Jaddul Jinn?"

Ƙaisar ya ce "Ƙwarai kuwa, a kowane lokaci zan iya baka mamaki"

Hammad kuwa da duku-duku ya sake tafiya gurin Mahmoudu. Yana ganinsa gabansa ya faɗi.

Ya ce "Mahmoudu ka zauna mu yi magana"

Mahmoudu ya zauna yana rarraba ido"

"Ko dai ka gaya mini abin da ka ke ɓoye mini, ko kuma zan tari duk wanda nake ganin zan samu abin da nake nema, komai zai faru sai dai ya faru. Ka yi mini bayanin waye yaron nan, kuma wacece yarinyar nan"

"Matarka ce" Ya ba shi amsa kai tsaye. Zabura ya yi ya ja da baya yana kallon Mahmoudu "Yaushe kuma ta yaya?"

"An yi mini gargaɗi sosai da sosai, a kan kar na kuskura na gaya maka, duk da babu wanda ya san da wannan zancen ma. Amma ko zan rasa rayuwata na yi alƙawarin zan gaya maka iya gaskiyata. Nana matarka ce da ka aura a Nigeria. Bisa ga binciken da nake yi ta ƙarƙashin ƙasa kuma, kai ta fito nema ta zo Agadez" Jiki a sanyaye Ya ce " Mahmoudu ban fa gane me ka ke nufi ba, yaushe na je Nigeriar har na aure ta?"

"Bayanan da Matawalle ya yi maka ba haka yake ba, ka manta da komai naka, na tafi da kai Nigeria. Yanzu duk bayanin da zan yi maka ba komai zaka fahimta ba, amma Nana Asma'u matarka ce"

Hammad ya ce "Mahmoudu, anya ba haukacewa na yi ba kuwa? Ji nake yi kamar ba mutum ne ni ba. Gaskiya"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull