Kenza eBookz

Buzu book 3 complete - Chapter 17

Buzu book 3 complete - Chapter 17

Buzu book 3 complete Chapter 17: Buzu book 3 complete Chapter 17. Ya dafa kafaɗar Hammad ya ce "Mutum ne kai, wasu abubuwa ne dai kawai suke faruwa amma ka…

4,492 words

Ya dafa kafaɗar Hammad ya ce "Mutum ne kai, wasu abubuwa ne dai kawai suke faruwa amma ka nutsu, ka yi addu'a. Dan muddin ba ka tuna komai ba, ba zamu iya tunkarar kowa da maganar nan ba. Mutumin da ya zo muna tare a sahara, tare aka kamo ni da su, tare muka yi aikin gadi da su a Nigeria. Hammad ban san yaya zan yi maka bayanin jajircewa da sadaukarwar da yarinyar nan ta yi saboda kai ba." Nan Mahmoudu ya din ga yi masa bayanin wasu abubuwan da ya sani. Ya yi shiru ya rasa gazgatawa zai yi ko ƙaryatawa, idan ya yi duba da wasu abubuwan sai ya ga yakamata ya gazgata batun, dan Mahmoudu ba zai masa ƙarya ba. Amma ya din ga jin sa kamar ba mutum ba, ko kuma a wata Duniyar yake ta daban. Da daddare yana tare da Asal, tana danna waya, Nana ta kawo Abincin dare. Kamar ya yi mata magana ya fasa, sai dai ƙasan zuciyarsa ya din ga fatan Allah ya sanya gaske ne, Nana matarsa ce, ta kowacce fuska ta yi masa. Tun kan ya ji kan wannan burkitaccen labarin yake jin wani abu na sukan zuciyarsa a game da ita. Babban abin da yake ƙara burge shi da ita, sanin mutuncin kanta da ba ta yadda Asal ta taka ta ba. Saɓanin waɗanda suke kwantar da kai Asal ɗin ta taka su saboda abin Duniya. Ya gaza manta rungumar da ta yi masa a turakarsa. Ta ɗago kai suka yi ido huɗu da shi, amma bai sauke idanunsa ba ya ci gaba da kallon ta. A ɗan diririce ta ce "Na gama zan iya tafiya. Bai amsa mata ba ya tuna yadda take ba shi Nonon raƙumi da habbatussauda, ga abinciccikan da yake matuƙar da take gwangwaje shi da su. Asal ta ce "Za ki iya tafiya" Sai da Nana ta je tsakiyar falon sanan ya ce yana buƙatar lemon kankana da shayin citta da kanumfari kawai, ba zai sha na kimba ba. Nana ta yi shiru ta ci gaba da tafiya, Asal ta ce "Kin ji ai"

A hankali Nana ta ce "Na ce miki ba ni da kunne ne, da ba zaki iya tsinana wa mijinki uban komai ba"

"Ke ba magana nake yi miki ba" Nana ta waiwaya ta ce "Ai na amsa na ce to"

Shi kuwa ya yi haka ne, dan ta sake dawowa ya ci gaba da kallon ta ko Allah zai sanya ya iya tuna wani abin. Amma har ta kawo masa shayin tayi tafiyarta bai tuna komai ba.

Sosai faɗa ya ɓarke a tsakanin Giyaz da Ƙaisar a kan Nana, Giyaz ya din ga ɗaga Ƙaisar yana bu ga shi da ƙasa. Karfin Ƙaisar da na Giyaz ba ɗaya ba ne ba, duk da Giyaz ya kwana biyu a duniya amma yana da matuƙar ƙarfi. Ƙaisar ya baje a gurin, bayan buga shi da jikin dutsen gidan tarihin Agadez,da Giyaz ya yi, ga ƙona shi da ya din ga yi da wuta. Sai dai ganin Ƙaisar ya baje ko motsi ba ya yi, ya sanya ya nufe shi da sauri yana kiran sunansa, ya ɗago Ƙaisar, amma ya shammaci Giyaz, ya fito da jakar gurin Sarkin Baka daga cikin rigarsa, ya naɗe masa wuya da hannun jakar. Wata irin kururuwa Giyaz ya din ga yi, yana tumami a gurin yana burgima. Ihun nasa sai da ya razana da yawa daga cikin halittun da suke cikin gidan tarihin. Ƙaisar ya miƙe da kyar ya tunkari wani ɗaki, aljanun da suke ƙofar ɗakin su ka dare suka ba shi guri. Ya zura hannunsa a ya ɗaukko kwalbar da Giyaz ya ce tunanin Imam Hammad ne a cikinta. Ya ajiye ta a nesa kaɗan ya ja da baya ya din ga hura iskar bakinsa a jikin kwalbar. A take kwalbar ta yi wata irin ƙara ta tarwatse, a take ɗan hayaƙin da yake cikin kwalbar yana zagayawa a cikin wani ruwa ya bar cikin ta. Ƙaisar ya koma kan Giyaz da ya suma a gurin, ya ɗauke jakar da ya shaƙe shi da hannunta, ya ɓace daga gurin.

A hankali yake juyi, ya buɗe bakinsa domin ya jarraba yin magana, ya ji ko maganar ta dawo ya ce "Ma vie" sai dai ya ji shiru. Shi ma shirun ya yi yana ji wani raɗaɗi tun daga cikin kansa har idanunsa. Ya yi juyi ya ji taushin abin da yake kai ya banbanta da nasu. Ya buɗe idanun da suke yi masa raɗaɗi da kyar yana kallon ɗakin. Asal ce ta shigo ya kalle ta, ta ce "Amour ta gama abinci, ka taso ka karya" Ya jinjina mata kansa da ya yi masa wani irin nauyi mara misaltuwa. Tabbas ya san Asal matarsa ce, amma ina Nana. Sai ya yi shiru sannu a hankali ƙwaƙwalwarsa ta tariyo masa yadda aka fita da shi daga gidansu na Buda yana fizge-fizge yana kiran matarsa Nana. Ya rintse idanunsa tare da damƙar gashin kansa yana girgiza kan, saboda yadda ƙwaƙwalwar tasa ta hargiste, tunanin ma ya rasa wanne zai yi. "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ya din ga maimaitawa babu ƙaƙƙautawa. Asal ta sake shigowa ta ce "Amour wai yane? Baccin ne bai ishe ka ba? Sha biyu saura fa na rana, ba ka ko karya ba" Ya yi mata nuni da hannunsa alamun yana zuwa.

"Ok, ni zan je gida, Abbu yana jira na" Ya jinjina mata kai"

Sannu a hankali ya fara samun nutsuwa, ya miƙe tsaye a hankali, ya shiga banɗaki ya watsa ruwa, sai dai jiri ya din ga ɗibarsa. Ya fito ya zura rigarsa ya fita, ya hau kan doguwar kujera ya kwanta. Ya lumshe idanunsa, abubuwan da suka faru a Nigeria suka din ga dawo masa saɗara-saɗara, zuwa dawo da shi Niger da aka yi. To ya ya aka yi ya manta da ita komai nasa ya shafe da ya baro Nigeria, kuma yaya aka yi ya manta da komai nasa da yaje Nigeria. "Anya babu wata maƙarƙashiya ko wani abu da ban sani ba, game da rayuwata ba?"

Bakinta ɗauke da sallama ta shigo ɗakin, hannunta riƙe da kwandon kwanukan Abinci. Wata irin karaya ta ziyarce shi, zuciyarsa ta din ga azalzalarsa ya tashi ya rungume ta, Asmynsa ce, amma zuciyarsa ta din ga gargaɗinsa kar a samu matsala, dan ya san dokar Agadez.

"Barka da wannan lokaci Sayyid, ga abincinka, na ga na safe ma baka ci ba, ko ba shi ka ke so ba ne?" Hannu kawai ya ɗaga mata, ya lumshe idanunsa, mamaki ya cika ta, ganin ba shi da niyyar magana, ya sanya ta tashi ta fita cike da damuwa. Tana fita ya haɗe tafukan hannayensa, ya dafe fuskarsa ya fashe da kuka, da wace fuskar zai kalle ta? Me zai ce mata? Ta ina za ta yarda da shi cewar ba yana sane ya ƙi kula ta ba. A hankali ya ci gaba da tuna tsantsar juriya da sadaukarwar da ta yi saboda shi. Ba ta haƙura ba ta taho nemansa, sun haɗu kuma bai gane ta ba.

Ya so fita ya je ya samu Habu, amma ba zai iya ba, saboda ji yake yi tamkar an sauya masa gangar jikinsa. Wayarsa da ya bari tun daren jiya a falon tana caji, ya ɗauka ya duba ya ga Mahmudu ne yake kiransa. Ya ɗaga wayar bai yi magana ba, Mahmoudu ya ce "Hammad ina tunanin yaron nan fa ɗan gurin Nana ne, kuma..

"Nana matata ce, ina iya tuna komai yanzu" Mahmoudu a rikice ya ce "Ina fatan ba ka gaya mata ba?" "Babu wanda na gayawa" "Alhamdillah, kar ka ce mata komai, sai mun tabattar da abin da muke bincike, ka zo mu je Maraɗin gurin Umma, na san za ta saurareks fiye da ni. Amma ya aka yi ka tuna komai?"

"Maganar ma da kyar nake yi Mahmoudu, ba zan iya fitowa ba. Mu yi magana anjima" Ya ajiye wayar hawaye na ci gaba da zuba daga idanunsa.

Haka ya wuni ba tare da ya ci komai ba, jikinsa kuma gaba ɗaya babu ƙwari, kamar wanda aka zarewa laka. Babu abin da yake yi banda tuna rayuwar da suka yi da Nana, da girmama yadda aka yi ya manta da ita, ya kasa tuna ta. Sai dare sannan ya iya samu ya sha shayi kawai. Sai dai zuciyarsa babu daɗi a cunkushe. Ya lallaɓa jikinsa da yake a mace, ya nufi hanyar ɗakin Nana, sai dai ya tsaya a bakin ƙofa yana lissafin me zai ce mata? A hankali ya ɗago hannayensa, ya kalli yatsunsa, ya tuna yadda ya yi mata kyautar zoben, a lokacin da yake tsakiyar jin shauƙin ƙaunarta. A hankali ya murza tagullar hannunsa, sai ga Arun ya bayyana. Ya ce "Na amsa kira ya shugabana" "Ka duba mini; me yarinyar cikin ɗakin nan take yi?"

Arun ya risuna ya ce "Tana ninkin kaya ne ya shugabana, amma alamu sun nuna a gajiye take sosai da sosai, kuma akwai damuwa a tare da ita, sai kuma bacci da take ji. Gajiyar da ta yi da damuwar da take ciki ya haifar mata da kasala sosai. Kuma ta yi kuka mai yawa awanni kaɗan da suka gabata". "Ya isa haka, ina son ta yi bacci yanzun nan" Arun ya ce "Shiga kanka tsaye mai gidana, an riga an gama." Hammad ya numfasa ya buɗe ƙofar ɗakin ya shiga, ya mayar da ƙofar ya rufe. Ɗakin sai ƙamshin turaren wuta yake yi. Tana kwance a ƙasa ga kayan ninkin nata a gefe. Daga ita sai zani da ta ɗaura a ƙirjinta, saboda daga wanka ta fito ta zazzage kayan ta hau ninkewa ko za ta ga wayarta da ta nema ta rasa. Jikinsa har rawa yake yi, ya ƙarasa gabanta, bai yi wata-wata ba ya ɗago ta yana kallon kyakykyawar fuskarta. Wata irin karaya da matsanancin tausayinta ya ratsa zuciyarsa. Ya ƙanƙameta a jikinsa yana wani irin kuka zuciyarsa na yi masa zafi da ƙuna.

"Ki yi haƙuri Asmyna, ki yi haƙuri ki yafe mini, ni kaina ban san abin da ya same ni ba, ban san yaya aka yi na gaza tunawa da ke ba. Ban yi miki adalci ba amma kk yi haƙuri rayuwata" Ya din ga yi mata surutai ba tare da ta san yana yi ba, saboda wani irin nannauyan bacci da take yi. Duk da yadda burki ya so ƙwace masa, kasancewarsa da Nana a wannan yanayi, da ya din ga tariyo masa irin rayuwar da suka yi ta tsantsar soyayya da ƙauna. Ya yi iya ƙoƙarinsa gurin sarrafa kansa da kyar gurin ganin bai aiwatar da wani abu ba. A ganinsa yin hakan tamkar rashin adalci ne kai tsaye a gare ta. Kamar wani zai ƙwace ta, haka ya matse ta a jikinsa, yana zubar da hawaye, yana sake jin wani abu na ratsa lungu da saƙo na gangar jiki da kuma ruhinsa a game da ita. A duniya ba ya jin yana da wani abu da zai iya aikata wa Nana ya yi ko kwatankwacin saka mata a kan abin da ta yi masa. Har gefin Asuba yana rungume da ita, hawaye kuma bai bar kwarara daga idanunsa ba, lissafi yake yi ko za ta yarda da shi, ta sake ba shi dama ta biyu. Ko kaɗan, tunaninsa da hankalinsa ba sa lissafa masa kalubalen da yake gabansa, na auren wata ƙabila baƙar fata da buzuwa ba. Da kyar ya iya raba jikinsa da ita, ya ɗan yafa mata zaninta, ya gyara mata kwanciyarta, ya durƙusa ya sumbace ta, ya ci gaba da kallonta, daga bisani ya tashi da kyar ya fice ya bar ɗakin. Ko da Nana ta farka ta sha mamakin yadda ta ga jikinta, ita dai ta san ta yi mafarkin tana tare da Sayyid, amma da ta farka ta ga alamun kamar an taɓa ta. Ga shi a iya saninta ninkin kaya take yi, amma ta farka ta ganta rabin tsirara, ta yi tunanin ko Ƙaisar ne, amma cikin hanzari ta kawar da wannan tunanin daga ranta da take jin tamkar saɓo ta aikata, dan ta san Ƙaisar bai taɓa yi mata yawo da hankali a abu makamancin wannan ba. Ta yi iya ƙoƙarinta ta kawar da tunanin komai daga ranta, ta shiga banɗaki ta yi wanka, ta yi alwala ta dawo ta yi sallar asuba tana ta istigfari saboda yadda ta makara. Gari yana yin haske, ya shirya ya tafi gidan Mahmoudu, duk da yadda jikinsa yake a mace. Kallo ɗaya Mahmoudu ya yi masa, ya gane a rikice uban gidan nasa yake. "Mahmoudu, wallahi na gane ta, na tuna ta Nana ce matata ce, to amma yaya aka yi komai ya shafe a cikin kaina na manta da ita?" Mahmoudu ya ce "Ka nutsu ka kwantar da hankalinka, yanzu aiki ne ya ganmu jawur, sai dai ba wannan ba dole mu tsananta bincike a kan abubuwan da suke faruwa da kai." "Ni kaina abubuwan sun ɗaure mini kai Mahmoudu, ji na nake yi wani iri, kamar an ƙwance wani nannauyan dutse daga kaina. Yanzu ta ina zamu fara, ni fa duk abin da za a yi ko Agadez za ta tashi, ba zan rabu da matata ba" Mahmoudu ya ce "Ban gane Agdez ta tashi ba, a'a gaskiya sai dai ku ku tashi kai da ita" Hammad ya ce "Mahmoudu ka daina wasa mana" "Na daina wasa shugabana, amma yanzu ka tuna su Sule?" "Na tuna shi, yanzu ina iya tuna komai fa a cikin ƙwaƙwalwata." "To ma sha Allah, albishirinka" "Mene ne?" "Wallahi sai ka saya, ba zan faɗa a sadaka ba" "Faɗi ko me ka ke so, wallahi zan baka" Mahmoudu ya yi murmushi ya ce "Zan yi tunanin me nake so, amm yanzu yi sujudar godiya ga Allah tukuna" "Zan yi amma fara gaya mini" "Ta tabatta yaron nan, ɗan Nana ne, kuma a bincikena, da Gimbiya ta zo Niger, a hannun Ummana ta sauka. Al-Husssain ya turo mini komai nata, kamar yadda ka sanya shi bincike. A zahirin gaskiya da naje Maraɗi na gano yaron nan a gurin Ummana, shiyasa na damu da matsa bincike. Na kira Umma mun yi magana ta tabattar mini da ɗan Nana ne, kuma ɗanka ne yana daga dalilin da ya sanya ta turo ta Maraɗi aiki gidan cin abincinku, kuma ta ƙarfafeta ta taho Agadez ɗin" A rikice ya damƙi hannayen Mahmoudu a gigice ya ce "Dan Allah da gaske ɗana ne? Ina da ɗa? Mahmoudu? Mahmoudu dama zan haihu zan ga ɗana a Duniya. Subhanallahi wa bi hamdihi subhanallahil Azim. Allahumma lakal hamdu wa laka shukur. Mahmoudu dan Allah da gaske ka ke?" Cikin tausayawa Hammad, mussaman sanin irin ƙalubalen da ya fuskanta na rashin haihuwa da jarabtar da Allah ya yi masa na son 'ya'ya, aka hana shi ƙara aure, kuma Tafawa ya din ga ƙalubalantarsa da hakan yana nemana a sauke shi. Mahmoudu ya dube shi ya ce "Nutsu ka kwantar da hankalinka, ka san ka na da matsalar zuciya kar ciwonka ya tashi, amma ka san ba zan yi maka ƙarya da abin da ka daɗe kana nema ba. Ina da tabbaci a kan abin da na gaya maka, dan sai da na gama bincike na tabattar sannan na gaya maka. Hammad ya saki Mahmoudu, ya yi sujuda yana yi wa Allah godiya, sannan ya tashi fuskarsa sharkaf da hawaye ya ce "Yanzu mene ne abin yi? Ko ka zo mu je ka yi mata bayani, ban yi burus da ita ina sane ba" "A'a kar mu kuskura mu sanar mata komai yanzu, sai mun gama daidaita komai da shirya yadda zamu tunkari jama'ar Agadez da wannan babban al'amari" Ya share hawayensa ya ce "To tashi mu je Maraɗi na ga yarona" "Mu bari sai gobe in Allah ya kaimu" Hammad ya ce "Ba zan iya jira ba, kuma kar wani abu ya same shi, dole na dawo da shi kusa da ni, ko na ajiye su a wani guri keɓantacce, idan yana hannuna sai ta fi tsayawa ta saurare ni. Na san halinta akwai sauƙin kai amma akwai kafiya ba za ta saurare ni ta daɗin rai ba" Mahmoudu ya yi murmushi ya ce "To shikenan, amma ka jira kaɗan Sule ya zo, ku gaisa sai mu je Maraɗin tare da shi" Haka kuwa aka yi, ba a jima ba Sule ya shigo, ya risuna yana kwasar gaisuwa gurin Hammad. Ya rungume Sule tare da yi masa godiya, a kan ɗawainiya da kuma gudunmuwar da suka ba shi a lokacin yana Nigeria. Suka shirya suka tafi Maraɗi gidan Nene, ko da Hammad ya ga Muhsin, ya kasa zaune ya kasa tsaye, ya rungume shi yana kuka, da gode wa Allah da ya sanya yana da rabon haihuwa a Duniya. Duk da sun kai ruwa rana da Nene, ta ce ba zata ba su Muhsin ba, dan ba su yi haka da Nana ba. Hammad ya ce ba ɗaukar Muhsin zai yi ba yana son ya nesanta su da gurin da suke na ɗan wani lokaci, kamar yadda Hammad ma ya yi tunani haka ita ma Nene ta tabattar masa da muddin ya jewa Nana kai tsaye babu abin da zai hana Nana zuwa ta ɗauki Muhsin ta gudu, dan ta san halinta dole ya bi komai a hankali.

A hankali Hammad ya ɗago Nana daga jikinsa ya ce "Asmy bacci ki ka yi?".

"Idona biyu" Ta ba shi amsa.

"Kin yi shiru, Asmy ba da gangan na ganki na ƙi kula ki ba, kin san muddin ina cikin hayyacina babu yadda za a yi na share ki. A lokacin ina ta shirye-shiryen yadda zamu ɓullowa lamarin, Tafawa kuma ya sanya ni a gaba da da haƙilon ba zan yi mulki ba, ni juya ne, ga rashin lafiya ga hauka ga babu zobe. Ya daɗe yana jifana da kalmar juya, abin yana yi mini zafi da ciwo shiyasa na fallasa komai a lokacin da shirin duk abin da zai faru ya faru."

Nana ta yi ajiyar zuciya ta ce "Yakamata mu tashi, an kira sallar Asuba".

Hammad ya ce "Haka ne, amma ba ki ce komai ba" Ta ce "Zan ce ne, ina jin bacci ne sosai ka ga kwana muka yi ba mu yi bacci ba" Ya ce haka ne. Suka tashi suka koma ɗakin nan zai rufe amma ya tsaya ganin Nana na ƙara kallon ɗakin. Ya ce "Wannan ɗakin tun zamanin Sultan Azhar yake, duk Sultan ɗin da ya zo a nan ɗakin ne turakarsa. Kowane zamani akwai canji da kuma yadda ake ƙawata ɗakin. Kafin daga bisani a daina amfani da gidan gaba ɗaya."

Nana ta jinjina kai ta ce "Ni yanzu abu ɗaya nake son ka gaya mini, ina da ciki ko ba ni da shi?" Ta yi maganar a ɗan shagwaɓa tana marairaice fuska. Ya yi murmushi ya ce "A cikin labarin kin ji inda wani abu ya faru ne?"

"Eh mana, tun da kana zuwar mini ɗaki ba tare da sanina ba"

Ya jinjina kai ya ce "Sosai kuwa, dan tun da na gano ke matata ce, kusan kullum tare muke kwana, ya yi maganar yana rufe ɗakin. Ya damƙi hannunta suka yi gaba, ja ta yi ta tsaya tayi shiru sannan ta ce "Sayyid ba ka nuna mini mene ne a cikin ɗakin can ba" Ya kalli ɗakin ya ce "Hanyar tsohuwar prison ce, inda daga baya ake aikin sarrafa gold a ciki, amma yanzu babu abin da ake yi da gurin"

"Ina son ganin mene ne a ciki" Ya ce "To shikenan" Ya ja hannunta zuwa ƙofar gurin, amma suka tarar da ƙaton kwaɗo a jikin ƙofar. Ya ce "To ai gurin a rufe yake ma"

"Ya aka yi sauran ƙofofin ba a saka mukulli ba sai wannan? A tambayi mai tsaron gidan ya buɗe mini zan gani"

Hammad ya ce "To ai lokacin salla ya yi"

Ta ce "Na sani gani kawai zan yi mu tafi"

Ya tsaya yana kallon Nana da rikicin tsiya, ya ce "Zo mu je sai mu yi wa mai gadin magana, ya zo ya buɗe mana" ta bi shi a hankali jikinta cike da kasala ga kuma bacci da take ji.

Ko da Hammad ya tambayi tsohon nan mai tsaron ƙofar, sai cewa ya yi "Allah ya taimake ka, ban san wanda ya rufe ɗakin nan ba, ya kwana biyu a rufe"

Hammad ya ce "Wataƙila ko masu yawon buɗe ido su na ɓarna a gurin, shiyasa aka rufe"

Nana ta ce "Waye yake da alhakin rufewar?".

"Ma vie, wai lafiya kuwa?"

"Hammd sai an buɗe gurin nan kafin na bar Agadez"

"Shikenan na ji, za a buɗe amma muje mu yi salla tukuna" Da kyar ya lallaɓa ta suka bar gurin, saboda yadda take nema ta burkice masa gaba ɗaya.

***** Shukura na zaune a kan gadon Asibiti, ta zuba ido tana kallon ɗan jaririnta, ƙato da shi mai matuƙar kama da Sagir, ta din ga tuno da jaririnta da aka ce ya mutu da haryanzu zuciyarta ta kasa amincewa da hakan. Ji ta yi an turo ƙofar ɗakin ta ɗago da sauri, gabanta ne ya faɗi ta yi turus tana kallon mai shigowar.

Ayshercool 08081012143

94 LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KAFIN KI KARANTA. 0069685771 AISHA ADAM STANBIC

Yusra ce ta shigo ɗakin, Shukura ta yi tsuru da ido tana kallonta. Yusra ta ƙarasa gaban gadon Shukura cikin damuwa ta ce "Meyasa ki ka taho nan, ki ka saka ake ta neman ki, duk hankalin mutane ya tashi?" Maimakon Shukura ta bata amsa sai cewa ta yi "Ke kaɗai, ki ka yi driving ki ka zo nan? Ina Baban Haidar ɗin?"

"Wayarsa ce lalace, ya saka layin a wayata, yana can gurin meeting, kafin ya dawo kawai na ce bari na zo na ɗauke ki. Wannan ɗan da ki ka haifa ne?" Ta yi maganar tana karɓar jaririn hannun Shukura. Shukura ta jinjina kai jiki a sanyaye. Yausra ta ƙura wa jaririn ido tana kallonsa, tana ɗan murmushi ta mayar da hankali kan Shukura ta ce "Wai meyasa ki ka zo nan gurin ki ka zauna?" "Ba komai" "A'a da komai, kowa kin saka hankalinsa ya tashi sosai, ga ki da tsohon ciki, ki tashi mu tafi gida idan ya dawo kawai sai dai ya ganki. Abbanki har yana cewa zai ɗaure shi, shi ne ya saka ki ka ɓata, ai ba dan ya dawo da ni ki ka tafi ba ko?" Ta yi maganar jikinta a sanyaye tana kallon Shukura. Da mamaki Shukura ta ce "Daddyn ne ya ce zai ɗaure Sagir saboda ɓata na?" Yusra ta jinjina kai ta ce "Wallahi haka ya ce" Ta yi shiru tana zunzurutun ɓarna da zaluncin da ya gaya mata ya aikata. Ta numfasa ta ce "Amma ina fatan ba ki gaya wa kowa ina nan ba?" "Babu wanda na gayawa, ai kin ce kar na faɗa, ga abinci can ma na ɗaukko a mota, da 'yansanda zan gayawa amma na fasa" Shukura ta yi ajiyar zuciya ta ce "Yauwwa gara da ba ki faɗa ba" Yusra ta ce "To ki taso mu tafi" "A'a ai sai an sallame ni tukuna, kuma yakamata ki koma gida saboda ki sanar masa inda nake" "Babu inda zan koma, salon in tafi ki sake guduwa" Ta yi maganar tana ƙara lulluɓe jaririn Shukura da yake hannunta.

***** Cikin damuwa Alhaji Fatuhu yake kallon Hajiya Sa'a, yadda take zubar da yawu tana wani irin ihu, da gurnani duk ta yi najasa a jikinta. Ga ƙafafuwanta sun shanye, ba ta gane kowa sai wannan gurnanin da take yi. Likitoci sai dai su ta mata allurar bacci. Ranar da Fadila ta je duba ta, duk da ba ta magana amma tana ganinta tare da Muhsin ta din ga ihu tana tsine masa tana faɗin "Da tuni wannan shegen ɗan ne zai mutu ba Abbana ba, Allah ya isa ba zan yafe ba" Alhaji Fatuhu yana gurin, ya yi mamakin jin irin wannan maganganun da take yi, amma sai ya bar hakan a sakamakon taɓuwa da aka ce ƙwaƙwalwarta ta yi. Likitan da ya kammala rubutu a kan takarda, ya miƙa wa Alhaji Fatuhu. Alhaji Fatuhu ya karɓa tare da kallon Likitan ya ce "Doctor haryanzu ba a gano takamaiman abin da yake damunta ba?" "To, duk wani abu da yakamata mu duba mun duba, jininta lafiya kalau ba ta da hawan jini. Babu alamar strock a tare da ita. Sai dai idan sakamakon gwaje-gwajenta ya kammala bamu ga komai ba, zamu tura ku ɓangaren ƙwaƙwalwa dama mu nan mun riƙe ta ne domin mu gano maƙasudin shanyewar limbs ɗinta, to haryanzu ba a gano komai ba, zuwa ranar Litinin zamu fara tura ku physiotherapy ko Allah zai sanya a dace" Alhaji Fatuhu ya jinjina kai cike da karaya, tabbas da lokacin da yake da kuɗinsa ne, da kansa zai fitar da ita waje a duba ta. Ko a yanzu ba ya jin daɗin yadda da kuɗinta ake nema mata magani. Haka ya tafi gida jikina a sanyaye. Alhamdillah jikinsa ya yi kyau sosai, duk da haryanzu da sanda yake yawo bai gama warewa ba, amma yana iya fita shikaɗai. 'yarsa Rauda ya samu a gida yake ta yi wa faɗan rashin zuwa duba Hajiya Sa'a da ba son yi. "A ƙa'ida kamata ya yi a ce ke ce a gurinta Raudah, kina kallo lokacin da nake kwance kullum tana tafe" Rauda ta ce "Daddy ni wallahi tsoron ganinta nake yi, kuma duk lokacin da muka je da Maman Muhsin, sai ta yi ta ihu tana tsine masa tana da tuni shi ya mutu ba ɗanta ba, ta yi ta ihu tsoro take bani" "To Raudah ai larura ce, ni da Allah ya jarabbe ni, ba har wari na din ga yi lokacin da nake kan fama da larura ba. Jarrabwa ce Allah ya jarabce mu, kuma ku da ku ke kusa da mu, ku ne zaku ƙarfafa mana gwiwa. Ku din ga haƙuri". Ta jinjina masa kai kawai ta ce "To"

**** Nana bayan sun idar da sallar asuba, ta ɓungire ta hau bacci, saboda yadda suka kwana jiya babu bacci. Ya zauna a gabanta ya zuba mata idanunsa, yana jin tamkar ya haɗiyeta ya din ga jinta a cikin jikinsa. Me zai yi wa wannan halitta domin nuna mata ɗumbin godiyarsa da farincikin kasancewa da ita. Ƙarshe ya ɓuge da sumbatarta yana shafa fuskarta, daga bisani ya tashi ya fita. Sashen Gimbiya Bilkisu ya wuce, ya tarar ba ta fito ba, ya wuce ɗakin da yake kyautata zaton Asal tana ciki. Aikuwa tana ciki ɗin fuskarta ta kumbura suntum ta yi jawur, idanunta sun yi wani irin kumburi mai ban tsoro. Jikinsa a sanyaye ya ƙarasa gabanta ya zauna ya zuba mata ido, ta kawar da kanta gefe ta yi shiru, ji take kamar ta shaƙe shi ya mutu ta huta. "Asal" Ya kira sunanta. Ta ɗago ta kalle shi a ƙule. "Ina roƙon ki da kar ki ɗauki damuwa da tashin hankalin lamarin nan ki saka a cikin ranki. Duk abin da ya faru a cikin rayuwarmu abu ne da Allah ya riga ya ƙaddara"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull