Kenza eBookz

Buzu book 3 complete - Chapter 18

Buzu book 3 complete - Chapter 18

Buzu book 3 complete Chapter 18: Buzu book 3 complete Chapter 18. "Hammad ba na son jin komai daga gare ka, ka tashi ka tafi ka bani guri. Macuci ma ci…

4,303 words

"Hammad ba na son jin komai daga gare ka, ka tashi ka tafi ka bani guri. Macuci ma ci amana, ba ka ji daɗin halinka ba"

Ya ce "Na ji na kuma yadda, duk abin da za ki kira ni da shi na karɓa, na san kina cikin fushi ne, amma ina mai roƙonki kar wani ya ziga ki ko ya tayar miki da hankali aurenmu ya samu matsala"

"Ka riga ka haifar da matsala a cikin aurenmu da kanka, matsalar da ba ta da magani. Har ka yi aure ka haihu ko Hammad, ba ruwanka da matsala ta kanka kawai ka sani. Ka tashi ta fita ka bani guri. Kuma wallahi ina mai yi mka rantsuwa da Allah, sai na yi mata mummunar illar da ba zata moru ba, sannan in saka a hallakata sai ta san ta jangwalo rigima mafi girman da ba zata iya tare ta ba a rayuwarta. Wallahi Hammad kai nawa ne nikaɗai ni Asal ba zan yi tarayya da ƙasƙantaciyar mace a koma mene ne ba" Ya yi murmushi ya ce "Ni dai ina roƙonki ki kwantar da hankalinki, kar ki biye wa zuciyarki dan kaf cika da batsewar Agadez ke Niger gaba ɗaya babu mahalukin da zai raba ni da matata da ɗana. Dan gara na bar muku Agadez ɗin da mulkinku na bi farin ciki da kwanciyar hankalina. Ba zan taɓa wulaƙantaki ko na yarda a wulaƙantaki ba, saboda matata ce ke kuma 'yar uwata. Amma wallahil azim duk abin da ya samu Asma'u ba zan ɗaga wa kowane mahaluki ƙafa ba, a kanta komai kusancina da shi kuwa, dan Asma'u rayuwata ce, dole kuwa na bawa rayuwata dukkan wata kariya dan babu gangar jikin da take fatan rabuwa da ruhi" Wani irin kukan kura ta yi, ta din ga kai masa duka ko ta ina, tana gaya masa maganganu masu zafi, amma ko gezau kawai ya tsaya yana kallonta. Gimbiya Bilkisu ce ta shigo da gudu tana tambayar ko lafiya saboda jin ihun Asal da ta yi. Ta ƙaraso ta rirriƙe Asal ta ce "Imam me ka yi mata?"

Ya ce "Babu abin da na yi mata"

Asal cikin gunjin kuka ta ce "Ammi ya cuce ni, ya bar gida tsawon lokaci ya je ya yi aurensa a ɓoye ya haihu ban sani ba, sai dai na ji zance sama taka, kuma yarinyar da na kawo a matsayin kukunsa. Wataƙila ma shirya komai suka yi, an cuce ni am zalunce ni, wallahi Ammi ba zan zauna da wata ba. Ya aka yi na fara son shi na bari son Hammad ya yi mini illa. Ni yake gaya wa kaf Agadez babu mai raba shi da waccan ƙasƙantaciyar halittar wallahi sai na kashe ta" Gimbiya Bilkisu ta rungume Asal ta ce "Yi shiru ki daina magana, ki daina faɗar wannan maganar. Ki kwantar da hankalinki" "Ammi zuciyata ciwo take yi mini, ko ganinsa ba na son yi, ya tashi ya tafi ya bani guri"

Gimbiya Bilkisu ta numfasa ta ce "Imam, ina ga kamar yadda ta buƙata ka tashi ka tafi kawai, ka bata lokaci ta samu nutsuwa. Domin magna ta domin Allah ba ka kyautawa Asal ba, dole ta shiga damuwa da tashin hankali"

Hammad ya ce "Allah ya taimake ki, kar ki zaɓi Asal saboda 'ya take a gurinki, a zamana da ita har zuwa abin da ya faru ban zalunce ta ba. Cikin ƙaraji Asal ta ce "Ammi kin ji ko? Kina jin abin da yake faɗa" "Imam ka tashi ka je kawai" Ya miƙe tsam ya fice daga ɗakin, Asal kuma ta ci gaba da kuka.

Fita ya yi, ya nufi wani sashi na gidan, ya yi umarnin a je a zo masa da Sarkin baka. Yana nan zaune hadimai biyu suka shigo, tare da Sarkin baka, ya tarar da Hammad fuskar nan a ɗaure tamau babu annuri. Sarki ya ce "Barka da wannan lokaci"

Hammad ya amsa da yauwwa barka.

Ya ɗora da cewa "Ammm duk da zan iya cewa baƙon Sultan ne kai, amma saboda ni aka kawo ka gurin nan, kuma ina tunanin ina da damar yin magana da yanke wa kaina hukunci" Sarkin baka ya ce "Wannan gaskiya ne"

"Ina ganin tun da babu wani abu da ya yi saura, ka ce ba zaka iya yi mini magani ba, yakamata ka yi magana da Sultan a sallame ka ka tafi"

"Saboda ba ka son na kula matarka ko?" Hammad ya yi shiru yana kallon Sarkin baka. Sarki ya yi murmushi ya ce "Ai duk taka tsantsan ɗinka ina da yaƙinin Nana ta fika, kuma ko da take yi mini kallon ba a kan daidai nake ba, ta san ni ba mutumin banza ba ne. Wannan gidan naku ba zan taɓa tafiya na bar Nana a cikinsa ba saboda balahirar da na gani a gidan"

Ya kalli Sarkin baka ya ce "A matsayinka na wa?"

"A matsayina na ɗan uwanta, ba ka san ina da alaƙa da ita ba? Duk da na san zaka kalli alaƙar ba wata ta kusa ba, amma a yadda ba ta da kowa a cikinku daga ahalinta ina ga zan wakilci ahalinta a nan. Ina da dangantaka ta kakannin kakannin da ita. Ka kwantar da hankalinka ni ba zan cutar da kowa ba, ko na shiga tsakaninku ba amma dole zata buƙace ni, idan kuma ka bari na tafi wallahi ba zan dawo ba bar abada kuma hakan ka iya zame muku matsala. Kuma ya zama dole ka bata duk wata dama ta ganawa da ni a duk lokacin da ta buƙaci hakan, ta nan ne za a iya samun warwarar abubuwan da suka baibaye ka. Ba na son a ji daga bakina ne, kuma ina son ta fahimci akwai abin da idan yana cikin ƙaddararka ba ya nufin ka saɓa wa Allah, amma Allah na iya amfani da kai ya kawo wa wani bawan nasa mafita" Hammad ya yi shiru yana jujjuya maganganun Sarkin baka, duk da ba komai ya gane ba. Amma ya numfasa ya ce a mayar da Sarkin baka masaukinsa.

Ya tashi ya fita, ya ɗauki mota ya bar gidan. Ya yi tafiya mai nisa aƙalla ta awa guda sannan ya iso wani makeken katafaren gida. Bayan ya shiga da motar ya ajiye, sai gaishe shi hadiman suke yi yana amsa musu cikin girmamawa. Ya shiga cikin gidan ya bi wata hanya ya hau kan bene. Ya ƙwanƙwasa wata ƙofa, sannan ya saka kansa ya shiga da sallama. Yana zaune ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya, yana cin inibi tare da wasu ƙanan yara su uku, jikin bangon ɗakin kuma ƙatuwar TV ce take yi, ana shirin cartoon. Cikin nishaɗi yaran ke ta cin inibin su na zubarwa, ɗaya daga cikinsu kuma yana jikin mutumin yana tana jagwalgwala nasa inibin cikin nutsuwa. Sallamar da ya yi ne ya sanya su waiwayawa, Muhsin ya jefar da inibin hannunsa, ya nufi Mahafinsa da gudu. Hammad ya ɗaga shi yana murmushi ya ƙarasa shiga cikin falon sauran yaran maza su ma suka nufi Hammad. Ya rungume su yana murmushi ya kalli Imam Zahradeen ya ce "Kai ne ka ke wasan da su da sassafen nan?" Zahradeen ya yi murmushi ya ce "To ya na iya, su wannan biyun sun hana mamansu sakat da rigima, shi ma Muhsin sai kuka yake yi yau, yana kiran Umma, duk sun rikitata, shiyasa na kwaso su muka dawo nan" Hammad ya yi murmushi ya ce "Ina godiya sosai da sosai" Zahradeen ya tsuke fuska ya ce "Da aka yi me?" Hammad ya sake yin murmushi ya ce "Tuba nake baban Muhsin" Imam Zahradeen ya zauna sosai ya ce "Yaya ake ciki ne? Sultan bai kuma ce maka komai ba haryanzu?" Hammad ya girgiza kai ya ce "Ina dai jiran abin da zai ce, kawai dai yana yawan ce mini, sai abin da aka yanke na shawara"

"Ka ga Imam, ka tsaya ka nutsu da kyau ka duba makomarka da makomar wannan jaririn yaron naka. Yaron nan na buƙatar mahaifiyarsa, kuma ina ganin ka dawo da mahaifiyar Mahmoudu gidan nan, su zauna kafin komai ya daidaita, na ga ya saba da ita sosai. Ka san ba abu ne mai sauƙi su bari ka fito da ita daga gidan nan ba. Saboda ina tsoron shawarwarin da Matawalle da kum Sardauna za su yanke a kan matsalar nan. Ba dan kar na yi musu ƙazafi ba, da na ce sun fi mutunta Al'adar Agadez sama da addininsu."

Hammad ya ce "To ina nan dai ina sauraren su, na ji hukuncin da za su yanke ɗin"

Imam Zahradeen ya ce "To, Allah ya sanya mu ji alkhairi"

Imam ya amsa da Amin.

**** Jikin Shukura ne yake tsuma, tana kallon Yusra a inda suke ɓoye, ga ta rungume da jariri da yake ta ƙoƙarin farkawa ya tsala ihu. Yusra na riƙe da jaririn tana yi wa Shukura alama da ta kwantar da hankalinta. Ɗaya bayan ɗaya mutanen suka fita daga cikin ɗakin, ɗayan ya kira wayar Alhaji Zailani. Yana ɗagawa ya ce "Yaya kun same ta?"

"Alhaji mun caje Asibitin nan kaf bamu ganta ba, ga shi sun yi mana barazanar kira mana jami'an tsaro kar su kama mu"

"An bani tabbacin ta na cikin Asibitin nan, a yadda binciken nan ya nuna, dole ku nemo ta ba sai na ganta ba ku kashe ta kawai, dan ba za ta tona mini Asiri ba" Jaririn hannun Yusra ne ya tsala uban ihu, hankalin mutanen ya dawo kan ɗakin, ɗaya daga cikin su ya juya da sauri ya nufi ɗakin.

*****

Nana tana tsaye a gaban mudubi, ta saka riga ta alfarma, gaba ɗaya jin ta take kamar a cikin tarko, ta gaji da zaman guri ɗayan nan, hankalinta na kan a ƙarƙare abin da za a yi, a bata ɗanta ta koma Nigeria. Gefe guda kuma zuciyarta na ci gaba da wasi-wasi da son lallai sai ta ga mene ne a rufe a wannan ɗakin na gidan tarihin Agadez. Asal ce ta bankaɗo ƙofar ɗakin da ƙarfin gaske sai da Nana ta tsorata. Ta kalli Nana cikin doguwar riga mai maɗauri, ko 'yar uwatta mace zata sarawa kyawun dirin da Allah ya bata, balle ɗa namiji. Wani abu ɗacin gaske ya taso wa Asal, Gimbiya Bilkisu ce ta biyo bayan Asal. Nana dai ta tsaya ƙyam tana kallon su.

AREWABOOKS

Da sauri ya dawo, ya buɗe ɗakin jin kukan jariri, kawai ya tarar da Yusra a zaune a kan gado, tana jijjiga jariri. Cikin tsawa ya ce "Ke, me ki ke yi a nan wace ce ke?"

Yusra ta ce "Kamar yaya? Nice a ɗakin nan, lafiya suwaye ku?"

"Ya aka yi da muka shigo ɗakin nan bamu ganki ba?"

Yusra ta ce "Ku na tsaye a bakin ƙofa na zo na wuce ku, na je na karɓo jaririna daga ɗakin jarirai ne, an sallamo shi daga can"

Ɗayan ya ce "Ke ƙarya ki ke yi, mene ne sunanki?"

Yusra ta ce "Ban gane mene ne sunana ba, suwaye ku tukuna me kuma ku ke nema a gurina ni ban sanku ba" Ɗayan ya dubi hoton cikin wayarsa, ya kalli Yusra ya ga sam babu haɗi. Ya tunkaro Yusra ya ce "Ki gaya mana mene ne sunanki?" "Yusra, sai kuma me?" "Na ke ce wata mata ta tsinto, ta kawo Asibitin nan ba?" "A ka tsinto kuma kamar wata kuɗi? Ni ban san zancen ba, mijina tare muka je na ɗaukko jaririna. Yanzun nan yayata kuma za ta dawo da take zaune tare da ni. Amma mene ne dalilinku na zuwa ku ritsa ni kuna tuhuma ta." Ta yi maganar cikin dakiya tana tsare mutumin da ido. Ƙasam zuciyarta fata take yi, Ubangiji Allah ya sa kar Shukura ta ce za ta fito ta tona musu asiri. Ɗayan ya ce "Ba fa ita ba ce ba, mu koma mu gaya masa ba ta Asibitin nan, ba a ba shi bayanin daidai ba" Suka ƙara ƙare wa Yusra kallo sannan suka fice. Abin da ya faru kuwa, Shukura babu yadda ba ta yi da Yusra ta tafi ba, amma ta ce babu inda za ta je ƙafarta ƙafarta, ba za ta tafi ta bar ta ba. Ga shi ta uzzura mata da tambayoyin yaya aka yi ta ɓata aka neme ta aka rasa. Alamu ya nuna mata haryanzu Yusra da saura kan babu daɗi dan haka ta ce mata sace ta aka yi, ta kuɓuta da ƙyar shi ne wata mata ta tsinto ta ta kawo ta Asibiti. Yusra ta ce "Lallai kin auna arziki tashi mu tafi to" Shukura ta ce "Ai ba a sallame ni ba, ba zai yiwu mu tafi ba, ba ni da cikakkiyar lafiya fa" "To ba sai mu koma Asibiti a can cikin gari ba, kin ga yadda mamanki ma hankalinta yake a tashe, idan muka je da Baban Haidar ta yi ta kuka"

Wata Nurse ce ta yi sallama, suka gaisa da su Shukura, ta yi wa Shukura allurai. Wata ce ta sake shigowa da sauri, ta kalli Shukura ta ce "Ke ce Shukura ko?" Ta jinjina kai. "Wasu mutane ne suka zo, wai 'yar uwassu ce ke dubiya suka zo, amma yanayinsu kamar marasa gaskiya, mun ce babu mai wannan sunan, saboda mun san case ɗinki, amma ga shi can ana ta faɗa da su sun ce sai sun caje Asibitin nan, 'yar uwassu ce ke dole su ganki" Tsoro ne ya bayyana ƙarara a fuskar Shukura. Nurse ɗin ta ce "Ki kwantar da hankalinki, ai an kore su ma, kar ki damu" Bayan sun fita a rikice ta kalli Yusra ta ce "Ina ga wanda suka sace ni ne suka biyo ni nan, dan Allah ki tashi mu tafi "

Yusra ta ce "Ai da tuni mun tafi ki ka dage, yanzu bamu san suwaye ba, idan muka fita ai sai a samu matsala. Dole mu jira zuwa anjima sannan mu saci jiki mu gudu." Da ƙyar Shukura ta amince sai dai da aka jima suna tsaka da shirin guduwa, suka ji muryar mutanen a waje, Shukura ta rikice, Yusra ta yi dabarar janta su ɓuya.

*****

Bin su da kallo Nana take yi , Asal ta ƙaraso gaban Nana cikin huci da zafin rai, tana kallonta kamar ta kai mata duka. "Munafuka, muguwa, na jawo ki jikina ashe haɗa baki aka yi da ke a cuce ni? Kin auri mijina kin haihu da shi ban sani ba, kuma da yake ke munafuka ce, ba ki taɓa gaya mini saboda ba kya tsoron Allah. Wallahi idan ba ki rabu da shi ba, sai na kashe ki, na kashe ɗan naki dole ki koma inda ki ka fito a yau ba sai gobe ba, 'yar matsaiyata ƙasƙantacciyar halitta"

Nana ta dubi Asal ta ce "Subhanallah, ai Allah kaɗai ya san ƙasƙantaciyar halitta ba ke abar halitta ba. Kuma ɗan ja da baya, numfashinki yana takura mini a fuskata, sai na baki amsar maganganun"

Asal ta rikice ta kalli Gimbiya Bilkisu ta kalli Nana, ita kanta Gimbiya ganin Nana da ta yi ta ɗauka sokuwa ce ba ta magana. Nana ba ta jira me za su yanke ba ta matsa daga gaban Asal ta ce "Wannan abubuwan da ki ke faɗa, duk ba ni za ki gaya wa ba, Sayyid za ki gaya wa domin igiyar aurena a hannunsa take. Sai ki ji amsar da zai baki. Kuma ni Allah ya bani haƙuri da na zauna ina kallonki da mijina ban nuna miki komai ba, na biki a yadda ki ke so zuwa lokacin da ya dawo hayyacinsa ya gane ni. Dan haka yanzu da ki ka san komai, ni ba baiwarki ba ce, kuma ba kukun mijinki ba ce, matarsa ce wato kishiyarki"

Asal cikin ƙaraji ta hankaɗa Nana ta ce "Wallahi na fi ƙarfin na yi kishi da ke 'yar matsiyata ƙazama, baƙa mummuna. Wallahi sai na kashe ki na kashe abin da ki ka haifa." Gimbiya Bilkisu na ƙoƙarin riƙe ta, amma sai fizge-fizge take yi tana ihu.

"To Bismillah Asal, ki kashe ni idan har hakan zai sanya ki huce. Ba za ki taɓa canzawa tuwo suna ba, Hammad mijina ne, wanda na fiki ƙaunarsa"

"Ke ya ishe ki malama, dan kin ga na yi shiru saboda ba ki da kunya da mutunci sai ki tsaya kina gaya mata maganganun banza? To bari ki ji na gaya miki, sai kin bar gidan nan a yau ba sai gobe ba. Sai kin bar gidan nan buzayen jinin sarauta ba sa raɓar talaka, balle su aure su su rayu da su. Sai kin bar gidan a wulaƙance cikin ƙasƙanci kuma sai an hukunta Hammad kan laifn da ya aikata"

Nana ta ƙare wa Gimbiya Bilkisu kallo ta ce "Haba Mama, ke da ba da ke nake kishin ba? Nifa kamata ya yi a sara mini akan haƙurin da na yi. Kuma ko ba komai, dole sunan 'yar matsiyata ya shiga kundin tarihin Agadez, mace ta farko da ta karya tarihi bayan ɗaruruwan shekaru. Ku daina zagina dan ban yi muku komai ba, abin da na sani kawai na fi Asal son Hammad har Duniya ta naɗe, haka zalika ba ni da tsara a zuciyarsa ki yi haƙuri"

"Ƙarya ki ke yi, yadda na yi amfani da kuɗi na mallake ki ta ƙarfin tsiya, haka zan yi amfani da su na yi maganinki mummunan a bar ƙyanƙyami"

Nana ta ji zafin maganganun Asal, amma ta yi murmushi ta ce "Ke kin ga alamar muni a tare da ni, kalli da kyau Gimbiya Asal. Kodayake ba wannan ba ma; kar ki manta kina magana da matar da ki kai gidan da ki ke kwana kina shaye-shaye da kaɗe-kaɗe da ƙawaye a lokacin da ba ta san halin da mijinta yake ciki ba, kar kuma ki manta matar da ki ke bawa magani ta zuba a shayin Imam Hammad, haka zalika matar da ta san kina ajiye masa takarda mai hoton ƙwarangwal da yake ci da wuta, wanda shi ne yake burkita masa hankali da lafiyar jiki; wannan matar ita ce matar mijinki kuma baƙa mummunar da ki ke ta kushewa ki ke iƙirarin kashewa"

Dummm ƙirjin Asal ya buga da ƙarfi, ta ƙwalalo ido tana kallon Nana.

Nana ta ci gaba da cewa "Ni ba karabutin mutanen da ki ka saba wulaƙanwatawa ba ne, kasancewar Hammad mijina ya sanya na bar idanuna a buɗe ta kowace kusurwa a kansa, tunda na haihu da shi, har abada ba zan bari wani abu mummuna ya same shi ba"

Asal ta tattaro jarumta ta yi murmushin ƙarfin hali, bayan da mararata ta cika taf da uban fitsarin tsoro.

"Ƙarya ki ke yi, ba ki da abin da za ki kawo ƙarshena a masarautar Agadez, saboda ba ki za hujja a kan wannan soki burutsun da ki ke yi" Ta yi maganar tana tsare Nana da ido. Nana ta ce "Kwantar da hankalinki, ba na buƙatar wata hujja ko wani abu, dan har gaban Abada ba zan taɓa tona miki asiri ba. Ai Hammad yana sonki kuma ko ba komai 'yar uwassa ce ke, dan haka ki kwantar da hankalinki, amma daga yau da rana mai kamar irin ta yau, muddin ina tare da Hammad da ke da duk wani abu da yake kawowa rayuwarsa wani tarnaƙi"

Gimbiya Bilkisu ba ta bari Asal ta sake magana ba, ta kama hannunta suka yi waje. Nana ta ja numfashi tana bin bayansu da kallo, kafin tsunduma tunani. Gimbiya Bilkisu ta kalli Asal ta ce "Ke, kina wani wawanci har ki ka bari ta san kina wannan abubuwan? Asal kina da hankali kuwa?"

Cikin kuka ta ce "Ammi yaya zan yi, wallahi ban san da wata alaƙa a tsakaninsu ba, ban sani ba. Kuma ban san za ta kawo wani abu ba. Na shiga uku ba zan iya rayuwa babu Hammad ba wallahi Ammi ina son mijina, kuma ba zan iya buɗe ido na gan shi da wata ba ki taimake ni" "Nutsu ki kwantar da hankalinki, bari na yi wa babanki magana a san abin yi a yau ba sai gobe ba, dole a san yadda za a yi da yarinyar nan ki daina kuka" Da kyar ta din ga rarrashin Asal.

Nana na zaune na zaman jiran dawowar Hammad,furucin Asal ya tsorata ta, ta fuskanci da gaske kowa na iya aikata duk abin da yake so, a wannan gidan domin cimma burinsa. Ita ba ta kanta take yi ba, ta ɗan jaririn ɗanta da ba ta san inda yake ba ta shi take yi. Ta ƙudurce a ranta, idan Hammad ya dawo, bori za ta yi masa sai ya fitar da ita daga gidansa komai zai faru, amma ƙasan zuciyarta yana ta azalzalarta a kan son a buɗe wannan dakin na gidan tarihin. Bayan azahar ya shigo, sai dai yanayinsa ya nuna mata a cikin damuwa yake. Ya nemi guri ya kwantar da kansa a kan cinyarta. Nana ta shafa kan a hankali ta ce "Lafiya kuwa?" Ya jinjina mata kai kawai. "Ka ci abinci ne?" "Na ci" ya amsa a hankali. "To meyafaru?" Ya ce "Babu komai"

Nana ta numfasa ta ce "To dan Allah ina son ka dawo mini da Muhsin, kuma nifa na damu na koma gida, Sayyid hankalina a tashe yake wallahi, na san iyayena sun gaji da nema na" "Asmy kar ki ƙara mini damuwa dan Allah, ina sane da komai, a tsare nake yin komai in sha Allah zai wuce" Cikin damuwa ta ce "Zai wuce yaushe? Shekera ta uku nake shirin yi a ƙasar nan, nima ina da ahali bai kamata na tare a nan ba" Ya tashi zaune cikin damuwa, ya kalle ta zai yi magana, amma bai yi ba ya ciro wayarsa da take vibrating" Da to kawai ya amsa ya tashi ya fita. Nana ta koma ta nemi guri ta zauna cikin damuwa. Da sallama ya shiga ɗakin, ya tarar da Asal ga Sultan, ga Matawalle ga Tafawa da Sardauna sai Gimbiya Bilkisu da take ta ƙoƙarin rarrashin Asal. Gefe ga Imam Asadullahi ga kuma Imam Zahradeen rungume da Muhsin. Asal ji take kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu ganin Muhsin, dan babu abin da ya banbanta shi da Hammad. Yayi mamakin yaushe aka yi masa wannan gangamin har haka? Bayan bai jima da barin gidan Imam Zahradeen ba ya tsaya a gurin Mahmoudu. Sardauna ya ce "Ka je ka zo da babar yaron nan" Babu kara ya karɓi ɗansa a hannun Yayansa Imam Zahradeen, ya tafi inda Nana take. Ya kai mintuna sha biyar, sannan suka dawo tare. Nana suka yi ido huɗu da Asal da idonta ya kumbura, Nana ta sakar mata murmushi ta kawar da kanta gefe. Guri ya tsit sai Muhsin da yake ta hawa jikin Nana yana yi mata surutunsa na yara.

Zahradeen ya ce "Imam Muhsin, ka yi shiru"

Sardauna ya yi murmushi ya ce "Har ya zama Imam shi ma?"

Zahradeen ya ce "Eh mana Allah ya taimake ka. Ɗan Imam ai Imam ne" Suka yi murmushi.

Tafawa ya ce "Yakamata mu yi abin da ya tara mu, ba tare da ɓata lokaci ba."

Sardauna ya ce "Haka ne kam, Imam Hammad" Hammad ya ɗaga kai ya kalli Sardauna. "Duk da mun san aurenka da ita wannan 'yar Nigeria, ƙaddara ne daga Allah, Amma ina fatan ka sanar da ita matar taka, sharaɗin ƙasar Agadez na rashin auren bare?". Gaban Hammad ya faɗi, Nana kuma ta kalle shi suka yi ido huɗu. Sardauna ya dubi Nana ya ce "Ina fatan ya yi miki bayani?" Nana cikin girmamawa ta ce "Eh ranka ya daɗe. Ya yi mini na sani" Sororo ya bi Nana da kallo. Tafawa ya yi caraf da zancen, ganin ana neman a ɓata masa lokaci. "Amm dama na nemi a yi wannan zaman ne, domin na san mene ne makomar 'yata, sannan wane hukunci za a ɗauka a kan Hammad, bisa karya dokar Agadez" Hammad ya numfasa ya ce "Ai ni ba ni da wata matsala da Asal, ban sake ta ban kuma yi wani abu da...

"Kai dalla rufe wa mutane baki, ai na san baka saketan ba, amma mene ne matsayinta? Zaka zauna da ita ne? Ka saki waccan yarinyar ko kuma mene ne?" Hammad ya tsuke fuska ya yi shiru. Matawalle ya ce "Amma mai girma Tafawa, bai kamata a je ga wannan maganar ba. Kana neman sanin matsayar Asal ne?" Tafawa ya ce "Ka bari mu yi magana da shi ka daina saka mini baki" Hammad ya ce "Makomar aurena da Asal, yana daga gare ta, idan tana son zama da ni, ba wani abu dama ni ban ce ba zan rayu da ita ba. Amma ina mai neman afuwarku ina shirye na ɗauki duk wani hukunci da za ku yi mini, amma sau ɗaya a rayuwata, nima ina neman ku yi mini alfarmar nan, ba zan iya sakin Nana ba, mussaman da rabo ya shiga tsakanina da ita. Ba zan iya sakinta ba". Sak suka yi su na bin Hammad da kallo. Sultan ya numfasa ya ce "Hammad, ba kai ka ke da ikon yanke wannan hukuncin ba, sai abin da muka yanke maka. Mai girma Tafawa muna mai baka haƙuri, Hammad ya tabattar da cewa aurensu yana nan daram, dan haka yakamata ta kwantar da hankalinta." "Babu batun kwanciyar hankali a nan, sai zuwa yaushe zamu san matsayarta, yarinyata tana wuni ta kwana babu bacci. Kuma da haka ku ke shashantar da duk wani laifi da zai aikata ba tare da an hukunta shi ba. A wannan karon dole a bar doka ta yi aiki a kansa, kuma a zartar da duk wani hukunci da yakamata a kansa. Ya saki matar nan a yanzu ya bata ɗanta ta tafi inda ta fito shi kuma a hukunta shi" Hammad ya girgiza kai ya ce "Zan karɓi kowane irin hukunci, amma ba zan rama sharri da alkhairi ba" Asal ta rushe da kuka tana rirriƙe Gimbiya Bilkisu. 95 1k ne via 0069685771 Aisha Adam stanbic 08081012143

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull