Kenza eBookz

Buzu book 3 complete - Chapter 2

Buzu book 3 complete - Chapter 2

Buzu book 3 complete Chapter 2: Buzu book 3 complete Chapter 2. Sardauna ya yi gyaran murya ya ce "Imam Hammad, kamar yadda Tafawa ya buƙata da shi da wasu…

4,458 words

Sardauna ya yi gyaran murya ya ce "Imam Hammad, kamar yadda Tafawa ya buƙata da shi da wasu daga cikin 'yan majalissar Sultan. Lallai mu na buƙatar jin gamsashshiyar amsar ina zobenka na tambarin Imam yake? Gamsashshiyar amsa mai cike da hujja muke so, na wai-wai ko kame-kame ba, dan ka san muhimmancin zoben idan babu shi dole za ka sauka daga kan muƙamin da ka ke kai. Abu na gaba, mu na buƙatar sakamakon rahoton lafiyarka, na tsawon lokacin da a ka ce ka shafe a faransa kana jinya. Kuma hakan baya nufin za a canza umarnin da Sultan ya yi? Zuwanka faransa wakiltar Agadez wajibi ne bisa ga sahalewar Sultan. Kai kuma Tafawa, duk da uba ne kai ga Imam Hammad, kuma uba a Agadez za a hukuntaka bisa ɗaga murya da yin jayayya da hukuncin da Sultan ya aiwatar, kamar yadda kwamitin ladabtarwa da sulhu ya yanke. Zaka kawo mana cikakkiyar shaida da hujja, ba wai-wai ko kame-kame ba, a kan Imam Hammad yana ɗauke da larurar ƙwaƙwalwa, akasin haka za'a yanka maka tara mai yawan gaske ka biya shi. Haka zalika an hukuntaka bisa amfani da kausasan laffuza a kan Imam Hammad, wanda yake shugaba ne da yake jagorantar Imam, da ake sanya ran zaman su sarakan gobe. Dan haka an dakatar da kai tsawon watanni shida, har sai ka gabatar da abin da aka nema daga gare ka"

Cikin fusata ya miƙe ya ce "Ai dama na sani, wata maƙarƙashiyar da manaƙisar ake ƙulla mini, saboda ba a ƙaunata. Amma shi Jalaludeen ya musa cewar ɗansa mahaukaci ne mana. Ciwon hauka ya yi suka kai shi suka ɓoye amma aka ce jinya ya yi a ƙasar waje. Ba ku burge ni ba da ba sauke ni kuka yi daga muƙamina ba har abada ai. Kuma na faɗa na maimaita, Hammad ba zai taɓa zama Sultan a Agadez ba, ba shi da lafiyar zuciya, ba shi da ta ƙwaƙwalwa kuma ba shi da magaji juya ne, dan haka mai baƙin baya ba zai yi mulki a Agadez ba"

Wani irin duka Hammad ya yi wa teburin gabansa da ya bayar da wani irin sauti. Ya kalli Tafawa ya ce "'yar ka zaka tuhuma ya aka yi ba ta haihuwa? Ni mahaukaci ne ka zagaye Agadez kana maimaita hakan, kuma ba ni da lafiyar zuciya shi ma ban damu ba, na yi sarauta ko kar na yi bai dame ni ba, duk abu dai ka san kujerar Sultan ta fi ƙarfinka. Duk abin da za ka faɗa a kaina ka faɗa amma kar ka sake kira na da Juya mai baƙin baya, Asal ita ce juya ita zaka bincika dan ni ina da ɗa, na haihu ba baƙin baya ne da ni ba! Zobe kuma ya ɓata ban san inda yake ba" Ɗif gurin ya yi, tamkar an yi ruwa an shanye, ko kuma babu mai sauran numfashi a gurin, saboda yadda maganganun nasa suke buƙatar fashin baƙi gwari-gwari.

*****

Hajiya Amina cikin damuwa da nuna rashin jin daɗinta take duban Alhaji Zailani ta ce "Alhaji ban ji daɗin yadda ka yi wa yaron nan mijin Shukura ba. Tare da mu da shi ake ta faɗi tashin neman Shukura, bai kamata a ce gaya masa maganganun da suke nuni da cewar wai zarginsa ka ke yi da sace Shukura ba"

Ya dube ta ya ce "To dan yana mijinta kar na zarge shi? Duniyar nan fa babu abin da ba zai iya faruwa ba, ni bincikena ba zai bar kowa ba, ya zama dole a binciki kowa, kuma ki rabu da ni da abin da yake damuna, ki ƙyale ni da maganar sani mijin Shukura"

Ta ce "Shikenan, ni ina gudun kar daga baya a zo a ji kunya ne" Ya ɗan ɗago da sauri ya ce "Me ki ke nufi?"

"Ahh a zo a ganta a gano ba shi da hannu a ciki, su ci gaba da zama da matarsa kai ka zo ka na jin kunya"

Ya yi guntun tsaki, yana sake miƙe ƙafafuwansa a kan gadon.

***** Jamila ce a kwance dare ya tsala, amma ta yi ƙurii tana kallon roofing ɗakin. Tun da Abba ya koma ga Allah, bacci ya ƙaurace wa idanunta. Idan kuwa bacci ɓarawo ya yi awon gaba da ita, to tabbas mafarkin Abba za ta yi ta yi, tana ganin sun yi aure ga yara ta haifa masa. Sannu a hankali ta tafi tunanin abin da ya faru. Bayan da Hajiya Sa'a ta yi mata bayanin yadda za ta sadaukar da ɗan gidan Alhaji Fatuhu ƙaninta. Abin ya dame ta, ga shi ta san idan ta je ta sanar wa su Alhaji Fatuhu, asiri ne zai tonu har ita, kuma ma mene ne shaidarta, dan ta san tsaf Hajiya Sa'a za ta zame ta bar ta a ciki. Ta yi tunanin ko ta sace 'yar tsanar, amma ta fasa, saboda yadda ta rabu da ta ta da ƙyar. Bayan fitar Hajiya Sa'a, Jamila na kwance a falo bacci ya ɗauke ta, ta yi mafarkin 'yar tsanar nan a ƙone ta yi baƙi ta biyo ta tana ƙoƙari shige mata cikin riga tana wani irin kuka tsiii-tsiii. Cikin ihu ta tashi a razane. Lokacin Abba ya shigo ɗakin, kawai ta cakume shi tana ihu.

"Ƙanwata lafiya kuwa?" Ya yi maganar yana kallonta, a hankali ta cika shi, ta nemi guri ta zauna ta ce masa tsorata ta yi a bacci. Ya zauna yana yi mata nasihar mafarki ba gaskiya ba ne, kuma ta din ga addu'a, idan ba haka shaiɗanu za su iya shiga jikinta saboda wannan tsoron da take ji. Sai dai har ta tafi gida, a tsorace take kuma tunani take yi, yaya za ta yi ta tseratar da ɗan Alhaji Fatuhu. Ta rasa abin da yake yi mata daɗi, ga 'yar tsana ta sako ta a gaba a mafarki, yanzu bin ta take yi da sata sharɓeɓiyar wuƙa a mafarkin za ta kashe ta. Kawai ta yanke wata shawara a ranta, wajen ƙarfe sha ɗaya ta je gidan Hajiya Sa'a, lokacin bata nan ta fita gantalinta, cikin sa'a ta duba inda ta ajiye 'yar tsanar da tarkacen kayan tsafin ta ga su na nan. Ta kira Abba a waya, bayan sun gaisa ta tambaye shi yana ina, ya ce mata ya tafi kasuwa ta ce masa ya zo tana gidansu tana son ganinsa. Ba a yi awa ɗaya ba sai ga shi ya dawo, har da tsaraba ya sayo mata, cike da murnar ganinta, dan kwana biyu ta ɗauke ƙafa da zuwa gidan. Yanayin walwalar da ta gani a fuskarsa sai ta ji dana sanin kiransa da ta yi. Sai dai ya takura mata a kan lallai sai ta gaya masa abin da ya sanya ta kirawo shi. Ta ɗebo tarkacen nan na kayan tsafin Hajiya Sa'a, ta Zazzage masa a gabansa.

Cikin mamaki ya dube ta ya ce "Mene ne wannan haka?"

Ayshercool 08081012143

79 Tabbas ba ka san ko mene ne ba, kuma na san za ka yi mamakin mene ne wannan ɗin, amma ina mai baka haƙurin abin da zai fito daga bakina, ba ni da wani zaɓi ne nima, ina son yin ceton rai, na rasa wanda zan gayawa ya fahimce ni ya sama mini mafita ya rufa mini Asiri sai kai" Ta yi maganar cikin kuka.

Cikin damuwa da ƙaguwa ya ce "Babu komai, ko mene ne gaya mini. Wallahi Jamila ina jin ki a raina fiye da yadda ki ke zato, ki gaya mini dan Allah" Ba ta tsallake masa komai ba, tun daga tariyar Maman Khairat a unguwar su, da fara zuwa gidanta zuwa haɗuwa da Hajiya Sa'a, ta gangaro har kan neman jinin Nana yadda suka saka ta a ƙungiyar asiri abin da aka yi mata, hatta labaran da Hajiya Sa'a ta ba ta na yadda ta shiga ƙungiyar sai da ta gaya masa.

Jamila za ta iya cewa tun da take, ba ta taɓa ganin idanun ɗan Adam sun yi jan da na Abba suka yi ba. Ya ƙame a guri ɗaya tamkar babu rai a jikinsa.

Cikin rikicewa ta ce "Dan Allah Yaya Abba ka yi haƙuri ka yafe mini, ban gaya maka dan na haɗa ka da mahaifiyarka ba ko makamancin haka, ceton rai nake fatan mu yi, bawan Allah nan da yake rashin lafiya kar ya kuma rasa ɗan sa. Kuma dama ni na san mutuwa zan yi, dan ba zan iya bayar da kowa ba ga barazana kuma da ake ta yi mini a mafarki. Dan Allah ka yafe mini ban faɗa dan na haɗa ka da mahaifiyarka ba.

Idanunsa suka fara tsiyayar da hawaye, yayi kuka, ya yi kuka, Jamila kuma ta kasa rarrashinsa, can ya ce "Tabbas! Biri ya yi kama da mutum, yanayin facakar da Mummy take yi da kuɗi tamkar ba ta san zafin neman su ba abin yana ɗaure mini kai. Ina kula da harkokin kasuwancinta, amma na san abin da take kashewa ya ninka abin da muke samu. Kuma duk yadda zan bi na gano wani abu sai ta toshe. Jamila na ji daɗi sosai da sosai, da ba ki gaya wa wani abin da take aikatawa ba, kuma na ji daɗin ƙoƙarin kare kisan ɗan ɗan uwanta. Amma na yi mamakin yadda ta iya bayar da mahaifinmu saboda abin Duniya. Ita ma idan ba ta sadaukar da kowa ba mutuwa za ta yi ko?"

Jamila ta jinjina masa kai tana kuka. Ya ce "Shikenan, babu komai, ki daina kuka, daga ke har ita ba zaku mutu ba, zan zama abin sadaukarwar ku, sai dai daga ni ina fatan duk yadda za ki yi ki fita daga cikin kungiyar nan. A razane Jamila ta ce "A'a ba zai yiwu ba, ban gaya maka dan ka ɗau wannan ɗanyen hukuncin ba, mafita zaka nemo"

Abba ya ce "Wace mafitar Jamila? Na nuna wa Mummy na san abin da take yi? Ko na bari ke ko ita wani ya rasa ransa? Ko kuma ɗan Kawu Fatuhu da bai ji ba bai gani ba? Dan Allah Jamila duk yadda za ki yi kar ki yadda ki bayar da jinin wani, ki kuma bar kungiyar nan. Wallahi Jamila kuɗi ba su ne kwanciyar hankali da nutsuwar ɗan Adam ba." "Yaya Abba to me zaka yi?"

"Ni zan zama abin sadaukarwar taku?"

Ta girgiza kai ta ce "Ba zai yiwu ba gaskiya, na bayar da jininka kenan, ai gara ni na bayar da jinina ba zai yiwu ba"

Ya ce "Ba ke za ki bayar ba, ni zan bayar da kaina, ina fatan hakan ya zame wa Mummy darasi, ya kuma yi silar fitarta daga abin da take aikatawa"

Cikin kuka Jamila ta riƙe hannunsa ta ce "Idan ka yi haka ka kashe kanka fa kenan?"

"Jamila wa zan tunkara ya lalata Wannan abun asirin Mahaifiyata ya tonu tana Kungiyar asiri? Wane kallo ɗan uwanta zai yi mata? Ke idan aka ce ki na kungiyar asiri wane kallo al'umma za su yi miki ko bayan kin tuba? Ina roƙonki dan Allah ki rufa mata asiri kar ki gaya wa kowa wannan maganar" Ya ƙarasa maganar yana tashi tsaye, ya hau tattare kayan. Rikicewa ta yi tana ƙoƙarin hana shi, amma ya ture ta ya ɗebe, ta riga ta yi masa bayanin duka yadda ake amfani da kayan. Dan haka ya buɗe alawoyin da ta yi niyyar zuwa ta ba wa Muhsin, ya saka a bakinsa.

Ya nufi hanyar fita ya dakata ya ce "Idan na rayu shikenan, idan kuma an yi amfani da jinin nawa, ki tabattar wa Mummy ni ne sadaukarwata na shekara, kuma ki roƙa mini ita gafara, da kuma na zama ni ne mutum na ƙarshe da zai rasa ransa a dalilin nan duniyarta, ta tuna inda na tafi ita ma za ta tafi" Jamila ta yi kuka da dana sanin gaya wa Abba maganar nan.

Yana zuwa ɗakinsa ya ɗau biro da takarda ya yi rubutu, ya caka alluran nan a jikin 'yar tsanar, kawai ya ga ta ɓace daga hannunsa. Bai razana ba, ya saka hankicin a ƙasan fulonsa. Bai yadda ya haɗu da Hajiya Sa'a ba, har dare ya yi yana ƙule a ɗaki, ya kwana a kan fulon da jan ƙyallen, wanda shi ma ya ɓace daga baya. Jamila ta yi kuka tamkar ranta zai fita, dan faɗiwar gaban da ta ji ce ta tabbatar mata da cewa Abba ya aikata abin da ya ce, kuma ƙungiya sun shanye masa jini.

*****

Da ƙyar Abduou matawalle ya yi gyaran murya ya dubi Hammad ya ce "Yanzu Hammad har wuyanka ya yi kaurin da zaka din ga sa in sa da mu? Bamu san ka da haka ba, wannan ba halinka ba ne ba. Kuma ya zama dole a ladabtar da kai bisa nuna rashin ɗa'ar da ka nuna."

"Da na ce mahaukaci ne ai ba a yarda ba, yanzu ga haukan nan yana yi " Tafawa ya yi maganar a harzuƙe.

Cikin nutsuwa Imam ya ce "A cikin hayyacina nake, ina da ɗa, ka gaya wa ko a ciki da wajen Agadez "

Sardauna ya dakatar da taron ya sallami kowa banda Imam Hammad, da Abdou matawalle sai kuma Sultan.

Sardauna ya ce "Na san maganganun Tafawa ne suka yi maka zafi ka ke wannan iƙirarin, amma wannan soki burutsun naka, babu abin da zai haifar sai ƙarawa wuta fetur. Kaf faɗin Agadez Asal ce matarka, kuma tun da ku ka yi aure ba ku haihu ba, ko ka na da saɗaka ne bamu sani ba".

"Allah ya taimaki Sardaunan Agadez, ni fa ba ƙarya nake yi ba, kuma ba soki burutsu nake yi ba. Ina da ɗa"

Matawalle ya ce "Wai wani irin ɗa a na zaune ƙalau? Yaushe Asal ɗin ta haihu ba mu sani ba?"

Ya girgiza kai ya ce "Asal ba ta haihu ba, ɗa na kuma ba shi da alaƙa da kowace mace a Agadez a ma Nijar gaba ɗaya"

Sultan da ya fara harzuƙa ya ce "Kai ba na son shashanci fa, zan ci maka mutunci yanzun nan, wane irin shirme ne haka? Ko sai ka gazgata maganar Tafawa cewa baka da hankali"

Cikin girmamawa ya ce "Tuba nake ranka ya daɗe, amma idan an bani dama zan yi bayanin komai".

Abduou matawalle ya ce "Mu na sauraren ka".

Ya ciro wayarsa a aljihunsa, ya daddana.

"Ga Balaraba can tana jiran ki, ana neman ki a gidan Sultan" Nana ta ajiye tukunyar da take wankewa, ta kalli Asal ta ce ana nema na kuma a gidan Sultan? Laifi na yi?"

"Idan kin je kya ji. Nima ban san me ki ka yi ba, Imam ne ya ce a kai ki"

Gaba ɗaya sai jikin Nana ya yi sanyi, ta kammala abin da take yi a gurguje, ta shirya ta bi Balaraba.

Su na tafe ta ce "Mama Balaraba, ko kin san abin da na yi ake nema na?"

"A'a nifa Gimbiya ce kawai ta ce na raka ki? Amma idan kin san babu abin da ki ka yi, bai kamata ki ɗaga hankalinki ba, wataƙila Imam Hammad ne kawai yake neman ki"

Cikin sanyin jiki Nana ta ce "Kuma a gidan Sultan?"

"Eh wataƙila alkhairi ne, ko kuma girkin za ki yi" Duk da wannan kalaman na ƙwarin gwiwa, da Balaraba ta faɗa wa Nana, ita dai Nana ta ji ba ta gamsu da kiran ba. Tun daga nesa aka dakatar da Balaraba, aka turo wani ya shiga da Nana.

Nana ta yi turus, bayan ganin manyan mutane har da Sultan a wajen, gabanta ya yi wata mummunar faɗuwa, suka yi mata wani irin kwarjini ta ja ta tsaya a bakin ƙofar tana rarraba idanu.

Su ma duk suka zura mata idanu, su na mamakin ita wannan da aka kirawo, me ya kawo ta nan.

"Ƙaraso mana" Sayyid ya yi maganar yana kallonta. Sai ta diririce ta kasa gaba ta kasa baya.

Da kansa ya fara takawa, yana tunkarar inda take, yana zuwa ya kamo hannunta, yana tafe tana bin sa a baya har zuwa tsakiyar gurin. Bai saki hannunta ba ya kalli idanunta ya ce "Ma Vie" Gabanta ne ya yi wata irin mummunar faɗuwa, tsigar jikinta ta tashi, numfashinta ya fara fita sama-sama, jin abin da ya fito daga bakinsa tamkar almara.

"Ki shaida musu ni ba juya ba ne, ina da yaro"

Ƙoƙarin ja da baya ta fara yi, tare da son fizge hannunta tana girgiza masa kai.

Sardauna ya ce "Imam, wace ce wannan ɗin? Me ka ke ƙoƙarin yi ne haka?"

"Matata ce, ita ta haifa mini yaro" Ya ba shi amsar yana kallon Nana da idonta ya yi ja, ya cika da hawaye.

Cikin rashin fahimta Matawalle ya ce "Ta yaya, wace ce wannan ɗin daga ina take?"

Hammad ya yi shiru bai ce komai ba, shi kuwa Sultan tuni ya karaya, bayan ganin asirin Hammad ya tonu na taɓin hankali sa saboda soki burutsun da yake yi.

Sardauna ya ce "Wai Imam kan ka ɗaya kuwa? Ita wannan ɗin daga ina ka samo ta, ta ina ta zama matarka?"

Matawalle ya dubi Nana ya ce "Ke Baiwar Allah, daga ina? Kuma mene ne alaƙarki da shi?"

Cikin ruɗewa da hawaye Nana ta ce "Ni babu wata alaƙa tsakanina da shi, aiki kawai Gimbiya Asal ta ɗaukko ni na yi mata, ni ban san shi ba"

Hammad ya girgiza kai ya ce "A'a Husnah, kar ki ji tsoro, ina tare da ke. Kar ki yi mini haka dan Allah"

"Dan Allah ka yi haƙuri ni ban san ka ba" Ta yi maganar kuka mai ƙarfi na ƙwace mata.

"Cika ta tafi" Sardauna ya yi maganar cikin bayar da umarni. A hankali ya saki hannunta, ta juya da sauri ta fice.

"Hammad, anya maganar Tafawa babu ƙamshin gaskiya a cikin ta, na ga baƙa ce kamar ma ba 'yar ƙasar nan ba ce? Meye haɗin ka da ita?"

Ya yi shiru ya sunkuyar da kai ya ƙi magana.

Sultan ya yi gyaran murya ya ce "Ina ga a bari zan yi magana da shi"

Nana kuwa tun da ta fita take kuka, tana zuwa babu kowa a falon, ta wuce ɗakinta ta tattare kayanta cif ta yi waje. Sauri take zumbuɗawa tamkar za ta tashi sama, tana tafe tana fatan Allah ya bata nasarar ficewa daga gidan, ba tare da dakarun Asal sun ganta ba su hana ta fita, kamar yadda suka taɓa yi mata aka hana ta fita daga gidan. Sai dai ba ƙaramar tafiya ba ce ba, daga sashen da gidan Imam Hammad yake a cikin gidan zuwa shi kansa gidan. Ta sha doguwar tafiya kafin fita babban gate.

Masu gadin ƙofar suka ƙare mata kallo ɗayan ya ce "Maraɗi za ki tafi ko? Ga mota can Imam ya ce a kai ki" Ta girgiza cikin mamaki ta ce "Ba zan hau ba, ni ba can zan je ba"

"Idan ba za ki hau ba, ga wannan ya ce a baki" Aka miƙa mata envelope. Ba ta duba meye a ciki ba, ta karɓa suka buɗe mata ƙofa ta fice. Tana tafe tana waiwaye tana fatan kar a biyo ta a mayar da ita gidan nan. Ta ƙudurce a ranta, tana zuwa gidan Nene za ta ɗauke Muhsin ta yi Nigeria.

Sai dai tana tafe tana kuka zuciyarta cike da takaici, yanzu dama duk tsawon wannan lokacin Sayyid ya gane ta. Amma ya bari take ta wahala saboda shi, ya ci amanarta bai yi mata adalci ba. Ba ƙaramin gudu motar da ta hau take yi ba, amma gani take kamar ba a sauri. Ta buɗe envelope ɗin da aka ba ta kuɗi sabbi kar a ciki. Sai wata takarda. "Dan Allah ki samu nutsuwa, za mu yi magana Asmy, kar ki yanke mini hukunci a yanayin da ki ke" Wani uban tsaki ta ja a fili. Tana furta "Ba ka yi mini adalci ba, ka cutar da ni" Ta yi maganar kaɗan-kaɗan.

Sun sha tafiya ba kaɗan ba a hanya, kafin su isa Maraɗi. Daga nan Nana ta nemi abin hawa zuwa garin da suke da Nene. Sai dai tana zuwa ta tarar da gidan a rufe, ga babu waya a hannunta. Cikin matsananciyar damuwa ta shiga gidan su Ashura. Ashura na ganinta ta hau tsalle ta rungume ta, Nana ta maze suka gaisa cikin yaƙe. Suka din ga yi wa Nana maraba da zuwa, mutan gidan su na ta yaba yadda Nanan ta yi haske ta ƙara ƙiba. Nana da gabanta ke tsananta faɗuwa ta ce "Nene fa, ko ta tafi gurin sayar da Abinci?"

"A'a Nene kusan kwana huɗu ba ta nan"

Gaban Nana ya faɗi, ta ce "Ba ta nan ina ta tafi?"

"Gaskiya ba na tunanin akwai wanda ta yi wa sallama, kawai dai gani muka yi ba ta nan"

"Babar Ashura, dan Allah ku bani aron waya na kira ta" Ta yi maganar cikin tashin hankali, muryarta na rawa.

Aka ba wa Nana waya, ta saka lambar Nene, wayar ta shiga, amma ba ta ɗauka ba. Nana ta kasa zaune ta kasa tsaye, ji take yi tamkar ta kurma ihu, gaba ɗaya ta rikice, ta ji numfashinta yana fita sama-sama. Da kyar ta iya daidaita nutsuwarta ta gabatar da sallolin da suke kanta. Su ka kawo mata abinci, amma ta ƙi ci, ta yi musu sallama ta ɗauki kayanta ta fice. Gidan Hajara ta nufa, inda suka kawo ta gidan Nene. Hajara ta din ga murna ganin Nana, suka rungume juna cikin farin ciki, duk da Nana cikin tashin hankali take.

Hajara ta kawo mata Abinci, ta din ga jan ta da hira. Nana ta numfasa ta ce "Na je gida gurin Nene, na tarar ba ta nan, ga babu waya a hannuna, ko za ki kira mini ita a wayarki?"

Hajara ta ce "Bari na kira ta"

Sai da aka kira sau biyu, sannan Nene ta ɗaga.

Cike da rawar jiki Nana ta ce "Nene"

"Na'am Nana, ki na lafiya?"

Nana ba ta amsa ba ta ce "Nene na zo ba kya nan, na kira wayarki ba kya ɗagawa ina ku ka tafi?"

Nene ta numfasa ta ce "Nana ina mai baki haƙuri, baban ɗan ya zo ya karɓi ɗan sa"

Cikin matsanancin tashin hankali Nana ta tashi tsaye ta ce "Nene waye baban ɗan? Nene wa ki ka ba wa ɗa na? Haka muka yi da ke Nene?"

"Dan Allah Nana ki yi haƙuri, nima fin ƙarfina aka yi, babu yadda na iya, masu garin ne"

"Nene ba ki kyauta mini ba, bamu yi haka da ke ba, dan zatin Allah Nene ki gaya mini inda ɗa na yake, dan Allah Nene, ki yi mini rai ki bani ɗa na"

Nene ta ce "Nana da zan cutar da ke, da ban zauna da ke tsawon wannan lokacin ba, yadda muka yi a rubuce, haka ya karɓi ɗan sa a rubuce da hukuma, idan na hana su matsala zan shiga"

Cikin rauni da hawaye Nana ta ce "Nene waye ya karɓe shi?"

"Imam Hammad Jalaludeen Agadez "

"Na shiga uku" Nana ta furta cikin matsanancin kuka da tashin hankali.

AREWABOOKS

Cikin tausayawa Hajara ta ce "Dan Allah Nana ki yi haƙuri ki daina kukan nan haka? Kuma wai me yake faruwa ne?"

Nana ba ta saurari Hajara ba, ta ci gaba da kuka, tare da lissafa yadda za ta ninka ta koma Agadez, ta ƙudurce a ranta gara ajalinta ya riske ta, a yi duk wadda za a yi ta karɓi ɗan ta, ko hakan zai yi silar tarwatsewar Agadez gaba ɗaya.', a kan ta tafi ta bar ɗan ta, a wannan gidan. Bugun ƙofar gidan aka din ga yi da ƙarfi ana sallama. Hajara ta tashi ta fita, ba a jima ba ta dawo, ta dubi Nana ta ce "Ki na da baƙi a waje"

Nana ta ɗago jajayen idanunta da suka kumbura saboda kuka ta ce "Suwaye?"

"Ki je ki gani, baƙinki ne dai"

Nana ta yinƙura ta tashi ta fita, tana jan ƙafafuwanta, mutum biyu ta gani cikin kaaki, sai ɗaya da rawani, ya rufe fuskarsa sinkif, ba ta ganin komai sai idanunsa, duk da hakan bai hana ta yi masa kallon sani ba. Ba ta tsaya takura wa kanta ina ta san shi ba, saboda matsananciyar damuwa da tashin hankalin da take ciki. Cikin girmamawa ya ce mata "Barka da wannan lokaci" "Yauwwa sannu" Ta furta da dasashshiyar muryarta.

"Imam Hammad ne ya aiko mu, ya ce mu tafi da ke"

Ta yi wa mai maganar wani irin mugun kallo ta ce "Ya aiko ku ku tafi da ni ku kai ni ina? Ba zan bi ku ba, babu in da zan je"

"Gurin yaronki za a kai ki" Sai kuma ta yi turus tana kallon su.

"Tafiyar da ɗan nisa, ki ɗaukko kayanki, inda yaronki yake ya ce mu kai ki" Ba ta tsaya ta zurfafa tunani ba, ta shiga cikin gidan. Hajara ta ce "Nana yaya?"

"Tafiya zan yi"

"Ki je ina? Wai ni, me ya haɗa ki da Buzayen nan ma? An ce mini daga gidan Sultan ɗin Agadez aka zo gurinki, me yake faruwa ne?"

"Zan yi miki bayani daga baya, bari na je tukuna" Ta ja jakarta, ta yi waje. Wata irin haɗaɗɗiyar mota ce, ta haɗu ga kyau ga wani daddaɗan sanyi da take fitarwa. Sai dai Nana ba ta tsaya tantance kyan motar ba, lissafinta kawai Muhsin ya zo hannunta, ta gudu. Dan ko me za a yi ba za ta bayar da ɗan ta ba, kuma ba za ta bar Nijar ba sai Sayyid ya sake ta. Sun sha tafiya, kafin su isa wani irin ƙaton gida, sai da ta ga an shiga gidan, ta waiwaya ta ga an rufe jibgegen gate ɗin gidan, sai kuma tsoro ya fara kama ta, dan ta san barin wannan gidan ba abu ne da zai yi sauƙi ba. Sai dai hanakalinta baki ɗaya ya fi karkata, ga ta yi tozali da ɗanta, ta san a halin da yake ciki. Ta sauka daga motar ta tsaya tana rarraba ido, mai rawanin ya yi mata jagora zuwa katafaren falon gidan.

Ya sauke rawanin fuskarsa ya ce "Akwai banɗaki, da abinci, ki yi salla ki ci abinci kafin Imam ya zo" Wata irin muguwar razana Nana ta yi, ta ce "Sule? Kai ne dama? Me yasa..? Ta rasa wace tambayar ma yakamata ta ƙarasa. "Ki yi haƙuri, ba ni da damar ce miki komai, ki yi salla tukuna" Nana ta ƙara rikicewa kanta ya kulle. Da kyar ta samu ta yi sallolin. Jikinta sai ciwo yake yi saboda azabar zirga-zirgar tafiya ga cikinta babu komai. Gaba ɗaya rarraba ido kawai take yi, tana tunanin ta ina za ta ga Muhsin, ga fafur Sule ya ƙi tsayawa ya yi tafiyarsa ya bar ta sai itakaɗai, balle ya yi mata wani gamsashshen bayani. Jin ana turo ƙofar falon, ya sanya ta miƙe tana ƙara leƙawa ko za ta ga Muhsin.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull