Buzu book 3 complete - Chapter 25
Buzu book 3 complete Chapter 25: Buzu book 3 complete Chapter 25. "Dan Allah Hammad ka yi haƙuri ka yafe mini, na san laifukana ba za su ƙirgu ba, sai a…
3,349 words
"Dan Allah Hammad ka yi haƙuri ka yafe mini, na san laifukana ba za su ƙirgu ba, sai a wannan karon Allah ya tona asirina"
Yayi murmushi ya ce "Ba zan yi miki dole ki zauna da ni ba, muddin kin san zuciyarki haryanzu tana son Omar" Wata irin ɗagowa Asal ta yi a razane jin abin da ya ce. "Hmm Asal kenan, duk tsawon zaman da na yi da ke, babu abin da ban sani ba, kar ma ki yi zaton ko wani ne ya gaya mini. Saka mini magani da duk wani nau'i na ƙoƙarin illata ni da ki ke yi, duk na sani, kuma ina kallonki. Ba domin babu yadda zan yi da ke ba, sai domin ina jin tausayinki, kuma ke ƙanwata ce" Zamowa ta yi ƙasa cikin kuka ta riƙe rigarsa ta ce "Wallahi na yi nadama Hammad, na san ko ba ka ce mini komai ba, Hakkinka ba zai bar ni ba. Amma ba laifina ba ne ba, ka sani dan Allah ka yi haƙuri ka yafe mini, kar ka sake ni. Wallahi ina sonka" "Dama ai ban ce zan sake ki ba, mahaifinki ne ya nemi hakan, kuma nima na so aikatawa amma na duba idan na yi haka, ba ki da wata kyakykywar makoma, bayan gama lalata rayuwarki da aka yi. Kuma ba na son asirinki ya ci gaba da tonuwa a idon Duniya. Uwa uba Nana tana ta yi mini magiyar kar na rabu da ke. Na so samarwa kaina cikakkiyar nutsuwa da rayuwa da wadda bata harin komai daga gare ni sai alkhairi, amma ban san me Allah zai yi mini a sanadin yafe miki ba. Asal zaki koma ɗakinki bisa sharaɗi, dan ta ni ko yanzu ki ci gaba da duk abin da ki ke yi mini, bai dame ni ba; amma muddin ki ka yi wani na yinƙurin cutar mini da matata ko ɗana, wallahi sai na ɗaure ki, ɗaurin rai da rai ma kuwa. Ba zan taɓa yin wasa da duk wani abu da ya shafe su ba, dan haka zaki amince da babu ruwanki da duk wani abu da ya shafe su, balle a zo ga batun cutarwa" Wani abu raɗaɗi ya tsirga wa Asal, wai ita ake gindaya wa sharaɗi a kan Nana. Sai dai babu yadda ta iya ta jinjina masa kai ta ce "Na amince"
Ya ce "Ki yi tunani da kyau, kar ki saɓa abin da ki ka ce daga baya, na ɗauki mataki ki ji haushina"
"Na tabattar da na amince"
Ya ce "To shikenan, tashi" Sai dai ƙafafuwanta suka yi mata nauyi, ta kasa tashi, saboda haryanzu tana jin nauyinsa, kenan har soyayyar da suka yi da Omar ya sani, amma ya ƙyale ta a gidansa. Babu tsammani ta ji ya saka hannu ya ɗago ta tsaye. Ya ce "Na saka an ɗan yi mana gyara a gida, zan canza miki komai. Har cikin zuciyata na yafe miki, na san wasu abubuwan ba laifinki ba ne, kuma ko dan kusanto da Nana gare ni da ki ke yi yakamata na yafe miki. Allah ya sanya kin yi tabbataccen tuba" A duk lokacin da ya ambaci Nana, sai ta ji baƙin ciki kamar ya halakka ta. Ya sumbaci goshinta, ya mayar da ita kan gadon ya zaunar da ita, ya ce "Allah ya baki lafiya" Daga haka ya juya ya fita. Wani irin kuka ta saka, gaba ɗaya alamu sun nuna, a yanzu baya ganin mutuncin komai idan ba na matarsa da ɗansa ba. Ƙarara a idonsa da mu'alarsa ake iya karanto tsagwaron son da yake yi wa Nana.
Duk da yadda Sultan ya yi watsi da Imam Zahradeen, amma bai yi zuciya ba ya yi uwa ya yi makarɓiya a kan shirin gudanar da bikin ɗan uwansa. Tuni baƙi suka fara hallara, aka ɗauke Nana daga cikin gidan Sultan, zuwa estate ɗin da yake mallakin masarauta, da galibi ake saukar baƙi a can. Estate ɗin da sunan Hammad aka saka masa, wanda a nan ta fara zama tare da Asal da ƙawayenta a ɗaya daga cikin gidajen. Nana ba ta yi zato ba, ba ta yi tsammani ba, kawai ta tarar da mahaifiyarta da ƙannenta su Walida. Gaba ɗaya Nana ta yi wata irin rikicewa, jikinta ya hau tsuma. Maijidda da kanta ta tashi ta nufi Nana cikin farinciki. Nana ta faɗa jikinta ta rirriƙe ta, cikin dashewar murya ta ce "Um.umm.Umma! Umma ki yi haƙuri dan Allah" Maijidda ta ce "Shhh, kar ma ki kawo wannan zancen, ni yanzu lokacin farinciki ne da murna, dan haka kuka ya ƙare. Abin arziki da farinciki ne ya tara mu. Ni dai na gode wa Allah da ya sanya ina da rabon sake ganinku cikin kwanciyar hankali da kuma ƙoshin lafiya"
"Umma idan ba ku yafe mini ba, hakkinku ba zai bar ni ba, na yi wauta na yi shirme, na bar ku da fargaba da kuma zullumi."
"Duk ya wuce, ya zama tarihi, Alhamdillah tun da Allah ya amsa addu'armu ya haɗa mu cikin aminci da kwanciyar hankali." Tuni idanun Nana suka rine zuwa jawur, ta ƙanƙame Maijidda duk da babu wata shaƙuwar a zo a gani a tsakaninsu, amma wani irin abu ne mara misaltuwa Nana take jin sa a zuciyarta game da Umman nata. Ta ƙwaƙume ta, ta ƙi sakinta ta kwanta lamo a jikinta. Maijidda ta ce "Ai mijin naki ma ya zo mun gaisa, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya. Na ce a kawo mini jikin nawa na gan shi, aka ce mini yana ƙarƙashin kulawa ta musamman, zan gan shi amma ba yanzu ba" Nana dai babu baki, ba ta iya cewa komai ba. Sai yanzu take ƙara jinjina girman laifin da ta aikata. Ta tuna lokacin da aka raba ta da Muhsin na ɗan kwanaki tashin hankalin da ta shiga, ita kuma ta bar gida kusan shekara uku ba ta waiwaya ba, kuma still ana rarrashinta. Nene ce ta zo, tare da hadimai, da tarin kayan abinci, tare da su Anty Fati 'yan uwan Mai jidda da ta su motar isowarta kenan. Babu abin da Nana take yi sai gode wa Allah, sai murna suke yi da ganinta, tare da taya ta murnar matsayin da Allah ya ɗaukaka ta ya kai ta. Nana ta ce "Nene ga Ummana, Umma ga Mamana ta Niger ni yanzu a iyaye bayan ke, ba ni da wata uwa da ta wuce Nene. A hannunta na haifi Muhsin, ban san ya zan misalta miki riƙon da Nene ta yi mana ba Umma. Ki yi mata godiya."
Nene ta ce "Dama idan uwa ta yi wa ɗanta abu, sai an yi mata godiya ai hakkinta ne ta yi"
Ta miƙa wa Maijidda hannu suka gaisa, su Anty Fati suka hau yi mata godiya. Nene ta ce "Ni ina ƙaunar Nana saboda Allah, dan haka duk abin da na yi mata ina jin kamar na yi wa ɗan cikina ne"
Sam ranar Nana bata rintsa ba, ji take yi tamkar mai Jidda ta mayar da ita cikinta, gani take idan ta yi bacci zai zamana abin da yake faruwa mafarki ne.
Aka din ga ɗawainiya da su, Maijidda da ta taho da 'yan kayanta, na ƙara gyara Nana, yadda ta ga Nene na faɗi tashi a kan Nana, sai ta kasa komai. Washegari su Imrana suka iso, mota uku ta 'yan Kano, hatta Suwaiba da ba ta da cikakken hankali, da Jamila da babu cikakkiyar lafiya, haka Mama ta tarkata ta taho da su. Saboda a yi komai a kan idonta. Ana cewa ga motar su Baba can, Nana ta zabura za ta yi waje, Nene ta ce "Nana ya haka? Dole fa ki canza yadda ki ke gudanar da al'amuranki, da da kuma yanzu ba ɗaya ba ne ba. Ki bari za su shigo ai. Ummi ce ta fara shigowa, suka rumgume juna ita da Nana suka fashe da kuka. Su Uwani ma suka shigo gaba ɗaya sai falon ya kaure da koke-koke. Uwani da Ummi kamar su haɗiye Nana, Uwani ta ce "Ummi ke ce haka? Kin ga wani irin kyau da ki ka yi?" Nana ta yi murmushi. Ta riƙo hannun Jamila cike da farinciki, duk ƙasan zuciyarta cike yak da mamakin, yadda ta ga Jamila ta yi wata uwar rama mai ban tsoro. Duk da ba miji ɗaya suke aure ba yanzu sai da Mama ta yi turus ganin Mai Jidda, ba ta taɓa zaton za ta ganta gurin bikin Nana ba. Ta ganta tsaf da ita cikin nutsuwa. Uwani ta zauna kusa da Maijidda da su Anty Fati, suna hirar yaushe gamo. Nana dai kasa hirar ma tayi da su, gaba ɗaya kunyarsu ta hana ta cikakken sukunin haɗa ido da su. Bayan sallar isha'i, barori suka nemi da a yi shiru, Imam Hammad zai shigo. Aikuwa kamar ruwa ya cinye kowa aka yi shiru. Shi ne ya shigo tare da Mahmoudu, da hadaimai biyu, suka tsaya a bakin ƙofa shi kuma ya shiga. Yana ganin Uwani ya saki murmushi, ya tafi gabanta ya durƙusa. Ta ce "Ɗan nan, dama babban mutum ne kai? Ka gane ni?" Ya ce "Ɗa ba zai manta uwa ba ai, kuma ɗan halak baya manta alkhairi. Ba zan manta da ke ba, Allah ya saka da alkhairi" Ta ce "A'a ai ɗa baya yi wa uwa godiya, mun same ku lafiya?" Ya ce "Alhamdillah" Ya kalli Ummi da take ta murmushi ita ma, ya ce "Babbar Yaya, fatan kun sauka lafiya, kuma kun ji daɗin ƙasar tamu"
Ummi ta ce "Alhamdillah, mun same ku lafiya?"
Ya ce "Lafiya ƙalau, ina sake amfani da wannan damar, gurin sake baku haƙuri, da abin da Asmy ta yi, duk laifin a kaina yake, nine mai laifin amma ina bayar da haƙuri dan Allah a yafe mana. Sannan ina sake yi muku godiya sosai da sosai, Sultan ma ya ce a gaishe ku" Waɗanda ba su san shi ba, suka din ga yaba kyawu da kamalar Hammad. Daga nan ya nemi zai tafi da Nana, za ta je gurin su Baba inda suka sauka su gaisa, sannan a dawo da ita.
Su na shiga mota, ya kwanta a jikin Nana yana sauke numfashi ya ce "Da na yi niyyar idan aka gama taron nan, ki yi kwana biyu ki huta, sannan ki tare amma gaskiya yanzu na fasa, ji nake kamar na gudu da ke"
Ta marairaice ta ce "Dan Allah ka bari a kwana biyun"
"Ba zan iya ba, ana tashi kawai a kai mini ke gida, gidanki ya kammala komai an saka mana, mukaɗai muka rage mu shiga" Yayi maganar yana sumbatar bakinta. "Ya naga jikinki ya yi sanyi ne, kamar wata amarya?"
"Wallahi Sayyid tsoro nake ji, ban san da wani idon zan kalli Baba ba, ban kyauta ba abin da na yi ko kaɗan"
"A'a ki kwantar da hankalinki, Baba fa tun kafin su zo, na tura an ba shi haƙuri, yau da suka zo an kai shi har gurin Sultan, ya ba shi haƙuri, nima na je na same shi, shi duk damuwarsa ma ya ganki ne. Babu wani abu in sha Allah" Haka suka ƙarasa jikin Nana a sanyaye duk a tsorace take. A wani sashi na gidan Sultan, aka sauki su Baba, tare da Imrana da Gaddafi. Nana ta tsaya cak, ta sanya hannayenta, ta toshe bakinta, wani irin kuka mai ƙarfin gaske yana kufce mata. Gaddafi ne ya taso ya riƙo hannunta, ya ƙarasa gaban Baba da ita. Sai da Sayyid ya ji wani iri, duk da kasancewar Gaddafin yayanta ne. Nana tun da ta buɗe ido, Baba bai taɓa rungume ta ba sai yau, tana kuka yana kuka. Da kyar maganarta take fita ta ce "Baba ka yi haƙuri, ka yi haƙuri dan Allah ka yafe mini. Baba na yi wauta da rashin hankali Baba ka yi haƙuri na san na sanya ku a tashin hankali"
Sai da Baba ya yi kuka mai isar sa sannan ya iya furta "Babu komai Nana, ni dai na gode wa Allah tun da kina nan cikin ƙoshin lafiya, Alhamdillah, Alhamdillah na gode wa Allah".
Haka ta rungume Nasiru ma tana kukan farinciki, ta ƙara tabattar da duk lalacewar naka naka ne, ta shiga farinciki mara misaltuwa da ganin ahalinta a tare da ita.
Har Alhaji Fatuhu ya tafi ranar, Shukura ba ta yi musu bayanin komai ba, sai dai ta kaɗu ta shiga tashin hankali da mutuwar ɗan uwanta. Hajiya Amina ma babu rarrashin da ba ta yi mata ba, amma ba ta yi mata bayanin komai ba. Washegari da rana, sai ga Yusra tare da Sagir da Hajiya Halima da Siyama. Hajiya Amina ta karɓe su hannu bibbiyu. Ta ce "Sagir na zata zan ganka tun a jiya, na kira gidanku na sanar da Shukura ta dawo. Ya ce "Mummy bana gari ne, ina can Abuja fa, Yusra babu lafiya"
"Wai Yusra haihuwa ki ka yi ne?" Mummy ta yi maganar tana kallon ta.
Shukura ce ta fito, Yusra ta ajiye wa Sagir yaron, ta nufi Shukura ta ce "'yar uwa babu abin da ya same ki ko?"
Shukura ta jinjina kai ta riƙe hannun Yusra ta ce "Yusra na gode sosai da sosai, na gode" Yusra ta rungume ta tana rarrashinta. Shukura ta ce "Mummy, ki kira Daddy a yi komai a kan idonsa, na kira Baban Rauda ma a wayarki" Cikin rashin fahimta ta ce "To wai meyafaru?" Shukura ta ce "Shi zan yi bayani" Tana rufe bakinta, Alhaji Zailani ya fito, ya tsaya yana kallon Yusra da kuma Shukura. Yayi murmushi ya ce "Har gangami ki ka yi na tona mini asiri Shukura? Shikenan, mu jira zuwan Fatuhun, ai tun da ki ka dawo na san za a yi hakan."
Gaba ɗaya suka tsaya su na kallon Shukura.
Hajiya Amina ta ce "Shukura mene wai? Alhaji ka yi mini bayani mana"
Su na cikin maganar, Alhaji Fatuhu ya ƙaraso gidan, ya tarar da su a tsaye a falo. Ya ce "Hajiya Amina lafiya kuwa? Shukura ta kira ni a waya ta ce lallai na zo"
Hajiya Amina ta ce "Wallahi nima ban san abin da yake faruwa ba, shi ma na ji yana zancen za a tona masa asiri na kasa ganewa"
Ya kalli Shukura ya ce "Shukura, mene ne ki yi mana bayani"
Shukura ta yi shiru tana kallon Alhaji Zailani, amma ta kasa magana, kawai ta fashe da kuka. Yusra ta ce "Ina gida wayar Baban Haidar ta lalace, ya saka layinsa a wayata, Shukura ta kira ta ce tana wani Asibiti a can wata ƙaramar hukuma a Kano. Wai garkuwa aka da ita ta kuɓuta, wata mata ta tsince ta, ta kaita Asibiti. Na ce ba zan tafi ba sai tare da ita, da magariba wasu suka zo Asibitin su na nemanta za su kashe ta. Shi ne na tafi da jaririn, ni ban ma san yadda aka yi ba na ganni a gidanmu na Abuja daga Asibitin. Amma babanta ne ya saka a sace ta" Gaba ɗaya suka kalli Yusra cike da mamaki. Alhaji Fatuhu ya ce "Kin san me ki ke faɗa kuwa?" Yusra ta ce "Na sani mana, ba fa ƙarya nake yi ba. Ai ita da kunya ta ce ga abin da ya yi, amma ni dai ku yi haƙuri na faɗa"
Alhaji Fatuhu ya ce "Amma kamar an ce ai ba ta da cikakkiyar lafiyar ƙwaƙwalwa, wataƙila...
Shukura cikin kuka ta ce "Yusra ba ƙarya take yi ba, Daddy ne ya sanya a sace ni, saboda ina bin diddigin yadda aka ce jaririna ya mutu, kuma saboda ya bayar da jaririna a matsayin sadaukarwarsa ta shekara a ƙungiyar asiri. Na so rufa masa asiri na yi shiru, amma ba zan iya ba, mussaman idan ina kallon mutanen da ya zalunta, da yadda yake ganin bayan rayuwarsu. Ni Yusuf ma ina kyautata zaton shi ne ya bayar da shi a kungiyar"
Cikin tsawa Alhaji Fatuhu ya ce "Shut up Shukura, mahaifinki ne fa, ki ke yi masa wannan tonon sililin a gaban mutane. Kuma tayaya za ki haɗa kai da abokiyar zaman ki, ku yi masa wannan ƙazafin?"
Shukura ta ce "Ko zan yi wa kowa ƙazafi yaya za a yi na yi masa? Bana jin komai ko a gaban waye zan tona masa asiri, iyaka dai a yi mini gori wataran hakan ba zai dame ni ba. Ɗana ya ɗauka ya bayar aka yi tsafi da shi aka yi maka asirin da ka rasa komai ka yi rashin lafiyar nan. Suka haɗa baki da Doctor Sharif aka yi mini tiyata aka ba su jaririna. Tayaya zan iya rufa wa mutumin da ya yi mini wannan zaluncin asiri?. Nan Shukura ta din ga faɗar miyagun ayyukan da Alhaji Zailani ya gaya mata ya yi da bakinsa. Wani irin bugu zuciyar Hajiya Amina ta yi, take ta ji jikinta ya yi wani irin sanyi, tamkar an zare mata lakar jikinta. Wani irin gumi ya fara tsatsafo mata ko ta ina. Alhaji Fatuhu bakinsa na rawa ya ce "Zailani, abin da yarinyar nan ta faɗa haka ne, ko kuma ɗimuwa ta shiga ne?" Yayi shiru bai yi magana ba, sai tsare su da idanu da ya yi. Sagir ya ɗan daddana wayarsa, mutumin nan da suka zo tare da Shukura ne ya shigo, tare da wasu ƙarti majiya ƙarfi su uku. Bayan ya yi musu sallama, ya yi musu bayanin shi jami'in tsaro ne, kuma Likita, shi ne ya haɗu da Shukura a lokacin da nutanen da Alhaji Zailani ya tura, suka gano ta, suka yi yinƙurin kashe ta, ya yi amfani da ƙwarewar aiki, ya kama mutum biyu daga ciki. Kuma sun tabattar da Alhaji Zailani ne ya saka su wannan aiki. Bakin Hajiya Amina na rawa, da kyar ta ce "Me na yi maka haka Zailani?" Daga nan ba ta sake cewa komai ba, ta silale ta faɗi ƙasa.
Alhaji Fatuhu shi ma kasa ko ƙwaƙƙwaran motsi ya yi, ji yayi tamkar numfashinsa zai ɗauke. Sai yanzu wasu abubuwan da suka faru suke dawo masa, amma bai taɓa zaton Alhaji Zailani zai iya aikata masa wannan mugun abun ba. Kafin a bar gidan da shi, ya tsaya ya kalli Alhaji Fatuhu ya ce "Kar ka yi mamakin abin da ya faru, domin ban taɓa sonka ba, duba da yadda ka fini ta ko ina, kuma ban yi nadamar abin da na aikata maka ba. Duk abubuwan nan da na yi babu wata cikakkiyar shaida da za a iya kama ni da laifi da ita, balle a hukunta ni. Sai shaidar sace 'yata da na yi, wannan ma na san yadda zan fitar da kaina. Sai dai dole mu yi mutuwar kasko, domin ba ni kaɗai ba ne a ƙungiyar asirin, har da yayarka, da ta sadaukar naka da ɗanka da ya mutu, dan haka ko wani mataki zaka ɗauka a kaina, sai ka haɗa da ni da ita, gara ni abokinka ne kawai, ita kuma 'yar uwakka ce!".
*****
Nana ta so sanya kayanta na Nigeria, a gurin bikin nan, Hammad ya ce shigar buzaye za a yi mata. Ta sha gyara ta yi kyau. Agadez ta ɗinke da tarin jama'a. Tun daga kan gashin kanta, lungu da saƙo na jikinta, babu inda bai ga gyara ba. Sai da ta tuna da lokacin bikinsu na farko, yadda aka kawo mata shadda ta alfarma. Yanzun ma haka ne, rigar ta sha aiki ita kanta shaddar ƙamshi take yi na musamman. Babu babban abin da ya razana Nana, irin sarƙar da aka saka mata ta gold da ta sauka har cikinta. Ta kalli mai kwalliyar ta ce "Ni gaskiya a cire mini wannan sarƙar ba zan iya saka wa ba, fariyar ta yi yawa" Matar ta ce "Ba fariya ba ce shugabata, ado ne na mutanen ƙasar nan, dan Allah kar ki ji wani abu, ai ana kammalawa dole za ki cire ne" Sai da aka yi ta fama da Nana sannan ta haƙura, gani take yi kamar ba ta hanyar da ya dace ta yi wa Allah godiya ba kenan, da wannan fariyar. Ta din ga istigfari, da fatan Allah ya sanya kar hakan ya sanya ta ji wani abu na girman kai ko tinƙaho.