Buzu book 3 complete - Chapter 26
Buzu book 3 complete Chapter 26: Buzu book 3 complete Chapter 26. Ƙaton ɗakin taro ne, ta kowane ɓangare mutane ne, daban daban, 'ya'yan sarakuna da manyan…
4,307 words
Ƙaton ɗakin taro ne, ta kowane ɓangare mutane ne, daban daban, 'ya'yan sarakuna da manyan mutane gurinsu daban, ɓangaren danginta daban, abin har ya fara bata tsoro ta ji kanta yana juyawa. Ba iya wannan ba, shi kansa Muhsin da kusan kwana biyar rabon ta da shi, an yi masa ado, kayansa iri ɗaya da na mahaifinsa. Aka buɗe taro da addu'a, da karanto jadawalin abin da za a gudanar a gurin. Aka fara da sake tabattar da rushe majalisar Imam, da zimmar duk wani ɗan sarki Imam ne, amma babu majalisarsu, da kuma cewar lallai su za su gaji sarauta. Aka sanar da sauke wasu daga manyan makusantan Sultan, ba tare da faɗar cikakken dalili ba, sai cewa saboda za a yi gyare-gyare ne a masarautar Agadez. Aka gabatar da roƙo ga gwamnatin tarayya, a kan ta bayar da tallafi su haɗu da masarautar Agadez, a gyara gidan tarihin nan, a faɗaɗa shi a ƙawata shi, ya zamana gurin buɗe idanu sosai ga baƙi. A kuma gina Hotel a ciki ko wajen gidan, saboda samar da masauki ga baƙin da za su din ga zuwa yawon buɗe ido. Daga nan aka sake jaddada dokar, halattawa ƙabilar buzaye auren duk matar da suke so, daga kowace ƙasa. Aka yi ta kaɗe-kaɗe ana shiga ana fita da abinci kala-kala. Daga bisani aka yi wa Imam Hammad naɗi aka ba shi sarautar Sardaunan Agadez, yayin da Imam Zahradeen aka ba shi sarautar Tafawa. Sai kuma abin da ba a taɓa tsammani ba, Sultan ya yi wa Mahmoudu Sarautar Tafeedan Agadez, tare da ba shi auren ɗaya daga cikin 'ya'yansa, wanda za a gudanar a nan take. Gigicewa Mahmoudu ya yi, Nana ma ta waro idanu saboda mamaki. Hammad kuwa ya sani, tare da Sultan suka shirya komai. Kuma ya tabattar ƙanwar tasa ta amince da auren Mahmoudu, ita ma tata mahaifiyar rasuwa ta yi, ita ce 'yar autarsu. Dama ba shi da matsala da Mahmoudu, kuma ya fuskanci su na shiri sosai, shiyasa ya nemi alfarmar Sultan ya yi wannan haɗin. Aka fito da Muhsin, aka gabatar da shi, a matsayin ɗan Hammad, da Duniya ba ta san da shi ba, kuma a ka yi masa naɗin Imam kuma Yariman Agadez mafi ƙarancin shekaru a tarihin Agadez, haka zalika kuma Imam da mahaifiyarsa ta sauya tarihin Agadez baki ɗaya. Nan manyan mutane suka din ga bajinta, da gwangwaje Muhsin da tsadaddun kyaututtuka na ban mamaki. Har sai da Nana ta kalli abin a matsayin Almubazzaranci. Daga bisani aka din ga koɗa Nana ana yi mata kirari, ita ma aka gabatar da ita, a matsayin matar sabon Sardaunan Agadez, kuma mahaifiyar Yarima. Nana gaba ɗaya sai ta rikice, kawai ta fashe da kuka. Aka bata mic a kan ta yi magana, amma ta kasa ƙarshe kawai ta yi sujudu shukur a gurin, jikinta na tsuma tana wani irin kuka. Hammad ne ya din ga rarrashin ta, yana ankarar da ita ranar farin ciki ce a gare su. Ba a bar uwar Yarima haka ba, sai da ta samu sarautar Garkuwar matan ƙasar Agadez. Haka matan manyan mutanen nan, suka din ga guɗa, suna yi mata kyaututtuka. Hammad ya yi godiya ga tarin al'ummar da suka halarci taron, tare da fatan ɗorewar Canjin da aka samu, na halatta auratayya da kuma tabattar da 'yancin kowane kalar fata. Ya yi godiya ga dangin Nana, tare da jinjina mata, da kamba mata a gaban tarin jama'ar nan. Duk bai fito ya bayyana wa mutanen abin da Nanan ta yi yake ta wasa ta ba, amma ya nuna wa Duniya yana ƙaunar Nana, kuma komai zai yi ba zai taɓa biyanta soyayyar da sadaukarwar da ta yi masa ba. "Haƙiƙa yau rana ce mai girima, da ɗumbin tarihi a gare ni, da ma al'ummar ƙasar nan, duk da akwai ranar da ta fi ta da ba zan manta da ita ba, ranar da na mallaki Gimbiya Asma'u a matsayin matata. Ba ni da kalaman da zan yi amfani gurin yi mata godiya, da nuna muku girma da matsayinta a rayuwata ba. Ni dai na san halitta ce mai girma, da ta cancanci na wasa ta, na yabe ta, na so ta na kambama ta ko a ina ne. Asma'u ke rayuwata ce" Ya ƙarasa maganar a raunane. "Allah ya yi miki mafificin tukuici. Haka zalika ba zan manta da ɗan uwana ba, ba sabon Tafawan Agadez ba, dama wannan yayana ne. Ina nufin Tafeedan Agadez. Ba ni da abin da zan iya faɗa, sai dai za ku dauwwama a cikin zuciyata da kuma addu'ata. Sai mai gayya mai aiki uba na gari mai girma Sultan uban ƙasa uban kowa da kowa. Mu na godiya da tarin karamci da dattakunka a gare mu. Iyayena na Nigeria, kafataninku muna ƙara sake miƙa godiya a gare ku" Nana kam kasa jurewa ta yi, ta rasa ma kukan me take yi, na murna ne ko kuma na damuwa. Ba Nana ba hatta iyayenta, sai da suka yi kukan murna, Baba bai taɓa tsammanin a zuriyarsa za a samu irin wannan tagomashin ba. Sai dai shi Allah, mai aikata abin da ya so ne a lokacin da ya so, ya kan ɗaga abu a lokacin da ya ga dama, zuwa ƙololuwar matsayin da zato bai taɓa zata ba. Taro ya watse lafiya, aka tashi cikin farin ciki, duk da zukatan maƙiya ba haka suka so ba. Ai kamar yadda Hammad ya ce, a ranar za ta tare, babu wani abu da ya yi saura da ake jira. Batun sabbin naɗe-naɗen da aka yi, ya sake cika gari, wasu suna ganin Sultan ya nuna son kai, gurin cire manyan mutane masu muƙamai, ya bawa 'ya'yansa. Nana ta so ta huta kafin ta tare, amma Maijidda ta ce a'a, tun da haka mijinta ya ce yana so. Baba duk abin sa, sai ga shi ga babar su Nana, a gurin bikin Nana. Abin mamaki Imrana ne ya sanya su a gaba ya din ga yi musu nasiha, da nuna musu illar gabar da suka din ga ya haifar musu. Nene ta riƙe hannun Nana ta ce "Gimbiyarmu, dan Allah a yi mana godiya, tabbas Hammad ya cika jagora, na ji daɗin abin da ya yi wa Mahmoudu, Ubangiji Allah ya saka da mafificin alkhairi" Gaba ɗaya Nana ta so ta sake sosai a cikin 'yan uwanta. Hammad yana ta shiri a ɗakinsa, Mahmoudu ya shigo, dan bai samu sukunin haɗuwa da Hammad ba, saboda karɓar baƙi. Hammad ya kalle shi ya ce "Ango ka sha ƙamshi" Ya buɗe baki zai yi magana, Hammd ya girgiza masa kai ya ce "Ɗan uwa kai ka ke bi na bashi, dan haka babu buƙatar wani dogon jawabi ko godiya a tsakaninmu, mai girma Tafeeda Allah ya taya riƙo" Ya yi maganar yana fesa masa turaren hannunsa. "Sardaunanmu, godiya ta zama dole a tsakaninmu ai, godiya dole na... Hammad ya tsuke fuska ya ce "To jeka waje ka yi godiyar" Mahmoudu ya yi murmushi ya ce "Wallahi jin abin nake kamar a mafarki, bawa ya zama saraki ikon Allah, amma kana ganin Hanin ta amince da auren nan, tsakaninmu ba soyayya raha ce dai da girmama junanmu" Hammad ya ce "Ka na tsoro ne? Hanin na sonka, da amincewarta aka yi komai". "To kuma tana son baƙar fata" Hammad ya yi tsaki ya ce "Ka na da abin haushi wallahi. Kaf ƙabilar buzaye, ban taɓa ganin baƙi mai kyanka ba, har fararen ma, idan kuma duk baƙar fata gaba ɗaya matata ta fi kowane baƙar fata kyau" A tare suka yi dariya. Hammad ya ce "Kai mutumin kirki ne, mai nagarta na san na yi wa ƙanwata kyakykywan zaɓi ne, dan haka ba ni da fargaba" Suka ci gaba da tattaunawa cikin raha. Nana tamkar wadda za ta yi sabon aure, haka aka zaunar da ita aka din ga yi mata nasiha, Mai jidda ta nanata mata batun riƙe addu'a a duk inda take. Sai da aka kai ta har gurin Sultan nan ma ya yi musu nasiha sosai ita da Hammad. Daga bisani, Hammad ya ɗauke ta daga can gurin Sultan suka tafi, ya ce akwai walimar cin abincin dare tare da ita da danginta kaɗai, washegari kafin su wuce Nigeria. Asal kamar za ta mutu, haka take wani irin kuka tana rirriƙe Hasna. Tafawa ne yake ta bala'i ya ce "Wallahi ko za ki mutu sai ya sake ki, ban ga amfanin ki ci gaba da zama da mutane marasa mutunci ba, babu kunya babu tsoron Allah Jalaludeen ya sauke ni daga kujera ta, ya bawa 'ya'yansa, zai ga matakin da zan ɗauka a kansu." Asal ta girgiza kai ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, amma zan koma gidan Hammad, iya rufin asirin da ya yi mini ya isa, na yi maka biyayya iya yi na, amma ƙarshe na faɗa halaka, kuma buƙatar taka bata biya ba"
"Wallahi Asal ki ka koma gidan Hammad babu ni babu ke, na gaya miki sai dai ki canza uba!"
101 Alhaji Sabo ya ce "Ya na ga ka tsaya cak haka?"
Da kyar ya harhaɗo maganganun ya ce "Sabo, ce mini kai fa Amina ta mutu?"
Ya ce "Eh mana, ranar da ta mutun mutane na ta tambayar ina ka ke, aka ce kana Asibiti, likitoci sun hana a zo gurin ka. Yanzu sai ka maze duk wanda ya yi maka gaisuwa ko ya zo dubiya kawai ka amsa. Ita kuma Shukura lallai ka san yadda za ka yi da ita, ka ɗauki mataki a kanta, ko kuma ka gaggauta bayar da jininta ga ƙungiya kawai" Ya yi shiru bai sake cewa komai ba, har suka isa gidansa, mutane na ganinsa suka din ga zuwa yi masa sannu, suna yi masa gaisuwa. Bai iya amsawa kowa ba, Alhaji Sabo ya ce su yi haƙuri ba ya iya magana, saboda yanayin jikinsa. Har sashensa Alhaji Sabo ya raka shi, suna zuwa ya tarar da hijjabin Hajiya Amina da sallayarta gurin da ta yi sallar walha, kafin ta fita ta bar ɗakin su Sagir su zo. Ya ɗauki hijjabin ya kalli Alhaji Sabo, ya ce "Kana nufin Amina ta mutu? Kalli hijjabinta fa inda ta yi salla"
Alhaji Sabo ya ce "To shi ne me, kowa ma na haka ne ai. Kana ganin zaka iya zama a gidan nan kai kaɗai, ko a samo maka wanda zai tayaka zama?" Ya girgiza kai jiki a sanyaye, duk da mutuwar Yusf ta dake shi, amma bai taɓa jin mutuwar da ta daki zuciyarsa kamar mutuwar Hajiya Amina ba. Kan ƙiftawa da Bismillah. Ya ɗauka aljanin da ya bawa mahaifarta shikenan ya tseratar da ita daga ƙungiyar, abin da bai sani ba shi ne, bai isa ya tseratar da ita daga ajalinta ba. Ya nemi guri a gefen gado ya zauna, kawai ya din ga ganinta tana yi masa gizo. Duk izza da ƙafafa ta matan masu kuɗi, da ta'amalli da 'yan aiki, Hajiya Amina ba ta yadda mai aiki ta dafa masa abinci ba. Duk da son da yake yi mata, baya hana shi ya ci mata mutunci wasu lokutan. Amma ko ta yi fushi na lokacin ne ta ware. Ya yi mata wani irin so, mai wahalar mantawa. So yake yi ya samu damar zubar da hawaye, amma abu ya gagara. Vibrating wayarsa ta yi a kan gadon, ita ma yadda ya tafi ya bar ta, haka ya dawo ya tarar da ita. Ya ƙura mata ido daga bisani ya kai hannu ya ɗauka ya duba. Saƙo aka turo masa da lambar Doctor Sharif, ana sanar da shi Allah ya yi wa mai wayar rasuwar, za a yi jana'izarsa da yammacin ranar. Ya fito daga cikin saƙon, ya ga saƙon Yusuf na ƙarshe, da yake ce masa Daddy idan ka ga saƙona ka kira ni dan Allah na kasa samun ka a waya. Ya tuna yadda suka yi waya, Yusuf yana tsara masa yadda zai yi walimarsa na kammala master's da ya yi, suka da daɗe su na waya cikin raha da barkwanci. Ya tuna yanzu duk ba sa Duniya. "Saura kai, nan da anjima kai ne zaka mutu" Ya ji wata zuciyar ta raya masa. A take zuciyarsa ta tsinke ya buɗe idonsa a razane ya miƙe tsaye yana waige-waige. Wata irin fargaba ta shige shi, wani abu da bai san ko mene ne ba, ya tsirga masa tun daga cikin kansa har ƙafafuwansa. Da sauri ya fita daga ɗakin ya koma falonsa yana mayar da numfashi.
**** Hammad ya kalli Asal da take ta kuka ya ce "Ko ki yi mini shiru, ko ki fita ki koma tun da ba dole na yi miki ba" Ba shiri ta hau goge hawayenta ta ce "Yi haƙuri, na daina" Ta yi maganar muryarta ƙasa-ƙasa. Gaba ɗaya zuciyarta babu daɗi, har ga Allah ba ta son saɓa wa mahaifinta, amma ta san ba a kan gaskiya suke ba. Kuma idan ya kashe mata auren yaya yake son ta yi?. Ta yi shiru ta rakuɓe a gefen motar, kamar mai tsoron wani abu. Ya saka hannunsa ya janyo nata ya ɗora a kan cinyarsa yana murzawa a hankali hannu ɗaya kuma yana tuƙinsa. Ta ɗaga kanta ta kalle shi, ta ga ya mayar da hankali sosai a kan tuƙinsa. Ji ta yi kamar ta kwanta a jikinsa, amma ta tuna girman laifuffukan da yake kallonta da su yanzu, dan haka ta fasa. Ko da suka je gidan, ta tarar an yi wa gidan gyara sosai, an canza furnitures. Ta kalle shi za ta yi magana, amma sai ta fasa saboda gani take kamar fuskarsa a haɗe take. "Ina fatan canje-canjen da na yi ya yi miki, ban ɓata miki rai ba" Da sauri ta ce "A'a sun yi na gode sosai" "A'a faɗi gaskiya dai, na san ki da iyayi da ƙaƙale, idan bai yi ba a mayar da kayan a canzo wasu, tun da kamfanin wata uku suka bayar idan bai yi ba a mayar" Ta girgiza kai ta ce "Yayi sosai da sosai"
Duk barorin gidan ba wani sonta suke yi ba, saboda fi'ilinta da wulaƙanci, amma da suka ga ta dawo sun yi murna, dan duk da wulaƙancinta akwai kyauta. Hannunta a buɗe yake sosai da sosai gurin ungo. Shi ya zo musu da abincin da ya saka aka kawo, daga gidan Abincinsa na Agadez. Ya ci kayansa kamar ya share ta, ganin ta ƙi sakin jiki ta ci, duk da ya ce ya yafe mata, amma wasu lokutan da ya kalle ta wasu abubuwan suke dawo masa. Duk da yafiya aba ce mai wahala wasu lokutan, amma mantawa da laifuka ya fi komai wahala. "Cherié, ba za ki ci abincin ba ne?" Ta ce "Na ci" "Ba ki ci da yawa ba ai, ke da na san ki da son abinci, matso na baki a baki" Haka ya yi ta ƙoƙarin danne komai, kamar yadda ya saba yi a baya. Da suka zo kwanciya ma, kasa sakin jiki ta yi, sai raɓe-raɓe take yi, tana satar kallonsa. Shi kuwa hankalinsa yana kan wayarsa, yana tsokanar Nana da roƙonta dan Allah kar ta kasa bacci, zai zo su haɗe ta mafarki. Emojin dariya ta tura masa, ta ce "Da kenan, ka ke yi mini wannan rufa idon, yanzu ina gane komai, ka yi addu'a ka kwanta sai da safe" Ya yi murmushi ya rufe data. Ya juya ya kalli Asal ya ce "Na canza kamanni ne?" Ta ɗan sunkuyar da kai tana girgiza kai. Ya miƙa mata hannunsa ya ce "Ƙaraso mana" A hankali ta ƙara, ya rungumo ta jikinsa, ya kwantar da ita sosai a kan gadon. Ya tashi ya je ya kashe fitilar ya dawo ya kwanta a kusa da ita. A ƙasan zuciyarsa ya din ga roƙon Allah ya sanya yafewa Asal da ya yi da sake karɓar ta a matsayin mata, kar ta sake yinƙurin cutar da shi. "Ya Allah da kyakkyawar niyya na yafe wa wannan baiwa taka, saboda ina tausayinta. Ubangiji Allah ka sanya ta gyara rayuwarta mu zauna lafiya" Sosai ya sake da ita, tamkar babu wani abu na rashin daɗi da ya faru.
***** Duk yadda Alhaji Zailani ya so kawar da komai a ransa a kasawa yayi. Ya din ga zagaya gidan yana kallon hanyar ɗakin Shukura, da har a yanzu idan ta zo gidan, a nan take kwana. Ya kalli inda Yusuf yake zama mussaman idan zai kalli ball. Suna kallon ƙwallo tare dukkanin su akwai team ɗin da suke supporting. Ya tuna kai komon Hajiya Amina a tsakaninsu, da ƙoƙarinta na ganin kowa ya samu abin da yake buƙata. Amma yanzu babu Yusuf babu Amina, Shukura kuma babu wani abu da ta tsana a yanzu sama da shi. Gidan ya yi masa wani irin zafi Duniya ta din ga juya masa. Dama salla ba wani damuwa ya yi da ita, domin rashin kiyaye ta na daga cikin dalilan da yake kawo musu rashin jituwa tsakaninsa da Amina. Ya din da ga jin sa tamkar a cikin wata Duniya yake, aka bar shi shikaɗai. Bugun ƙofar da ya yi yawa ne ya tashi ya je ya buɗe ƙofar main falon, ya tarar da mai delivery ya kawo masa abinci, kamar yadda Alhaji Sabo ya yi masa order, ya yi shiru yana tunanin ina mai gadi, da har mai delivery ya shigo haka. Ga harabar gidan babu kowa yan gaisuwa ma duk sun watse ya karɓa ya koma ya ajiye ya nemi guri ya kwanta. Rufe idanunsa ke da wuya, ya ga duhu ya yi, alhalin yamma ce da sauran haske. Ya buɗe idanunsa ya yinƙura zai tashi, amma ya ji tamkar an saka igiyoyi an ɗaɗɗaure shi, ya kasa motsa ko da yatsansa. Yana jin yadda zuciyarsa take bugawa ya sare cewa kan shi ma ya mutu ne, ya din ga rarraba idanu ya ga ta ina zai fara ganin mala'iku sun bayyana. Ya hango cewar shi ma yanzu likkafani za a saka masa a je a binne shi a rami a tafi a bar shi. Ya yi wani yinƙuri domin ya tashi amma abu ya gagara. Wata irin dariya ya ji ana yi mara daɗin ji, cikin sauti mai ƙarfi. "Abin da ka ke gudun sai ya faru, ba za ka tsere wa mutuwa ba, dole ka biya wa dodo buƙatar sa, ko kuma ya yi ajalinka. Ɗif ya daina jin muryar, sai kuma fuskar matarsa ta farko da ɗanta na fari, suka fara fitowa a ɗakin. Ya sake rikicewa sai dai bai iya kowane yinƙuri ba, Shukura ta bayyana jikinta duk jini, kamar ba ta daɗe da haihuwa ba, ta tunkaro shi gadan-gadan da wuƙa ta fara ƙoƙarin caka masa. Kamar wanda aka tasa daga bacci ya gan shi a tsakiyar titi, ƙafafuwansa ko takalmi ko babu. Ya kalli jikinsa babu suturar kirki, gari shiru ko ina duhu alamar dare ya tsala. Sai da ya yi da gaske sannna ya gano cam gaban unguarsu ya tafi. Rashin gurin zuwa ya sanya tilas ya sake koma wa gidan nasa, ya ci uwar tafiya da ƙafa ya koma. Sai dai ƙofar gidan a buɗe, babu masu gadi, abin da bai sani ba tuni zancen ya fara zagayawa, a kan abin da ake zarginsa da shi, kasancewar mai aikin gidan na laɓe ta ji maganganun da aka yi. Suna watsewa da aka tafi da Hajiya Amina Asibiti, aka tafi da Alhaji Zailani ta tattara kayanta ta gaya wa mai gadin abin da yake faruwa ta gudu. Alhaji Fatuhu ya ƙi sanar wa Iyalinsa abin da ya faru, sai dai gaba ɗaya ba shi da nutsuwa, ga kayansa ana ta saya babu ƙaƙƙautawa amma ba ya iya taɓuka komai, sai dai ya ɓuya ya yi kuka. Babu tsammani Fadila ta ritsa shi yana kuka, ya kasa cin abinci. Cikin damuwa ta ce "Daddy, ina gama ka da zatin Allah ka gaya mini abin da yake damunka, da ba haka ka ke yi ba fa. Gaba kamar ma a tsorace ka ke Duniyar, kuka fa ka ke yi dan Allah ka faɗa mini mene ne?"
"Wallahi Fadila a tsorace nake da Duniyar, komai tsoro yake bani, ni dama rashin lafiyar da na yi na mutu, ban tashi ba da ban ji wannan abubuwan da damuwa da baƙin cikinsu zai halakka ni ba, bayan warkewr da na yi daga jinya ba" Ba ta san lokacin da ta fara kuka ba ta ce "Dan Allah Daddy mene ne?"
"Fadila ba zan iya gaya miki ba, ku yi haƙuri kawai, Allah ya sanya mu dace" Haka ta gaji da rarrashin ta ƙyale shi.
Shukura kuwa Sagir da Yusra ba abin da suke yi sai aikin rarrashinta, da bata haƙuri, Yusra ce take kula da Haidar da jaririn da ta haifa aka saka masa Ahmad Annur. Sai dai ta kasa yin lafiya, kusan kullum tana kwance, Alhaji Fatuhu duk kwana biyu sai yaje gidan ya rarrashe ta, ya bata haƙuri tare da kwantar mata da hankali.
**** Da sassafe Asal ta nemi Hammad ta rasa, ta tashi ta fita falo, ta hango shi a kwnace a kan kujera yana video call da Nana.
Ta tarar da shi yana cewa "Ba fa na ganin komai ma vie, dan Allah ki cire bargon nan"
"A'a nifa bacci zan yi ka ke takura mini"
"Zan rama ne Asmy, me za ki dafa zan shigo anjima in ganki in sha Allah"
"Ba zan dafa komai ba, ai yau kana gurin matarka ta dafa ta baka"
Ya marairaice ya ce "Ni ko? Shikenan tun da kin daina so na. Ɗan yi kissing goshina" Yayi maganar yana kara screen ɗin a fuskar sa. Da sauri Asal ta koma ɗaki, wani irin abu yana taso mata kamar za ta fita hayyacinta. Ji ta yi tana neman yin danasanin biyo shi ta dawo gidansa, amma ta tuna damarmakin da ya bata bayan da ya aure ta. Amma ta din ga muzguna masa, saboda hure mata kunne da Imam Omar ya din ga yi. Bai san daɗin aure ba sai da ta fara hankali ta fuskanci ba ya tanka duk rashin mutuncin da za ta yi masa. Idan zai yi magana a dankwafe shi. Sai a gaɓar da ta dawo hayyacinta ta gane shayi ruwa ne, take sonsa a lokacin ta fara karɓar sakamakon abin da ta aikata. Yanzu ba ta da wani abin cewa sai abin da ta gani kawai. Ta sha kukanta ta gode wa Allah.
Nana an kai mata hadimai, duk da ba komai ta sakar musu ba. Har gida aka kawo mata dalleliyar motar da aka bata a gurin bikinsu, wanda Imam Zahradeen sabon Tafawan Agadez ne ya ba ta. Banda uban gwala-gwalai da ta samu. Ta fuskanci gold ne kyauta mafi tsada da muhimmanci da suke ba wa mutum mai muhimmanci mussaman ma mace. Lefenta kuwa, sai da ta din ga addu'a, saboda yadda mutane suka camfa duk auren da aka yi ɓarna a gurin yin sa ba ya ƙarko. Sai dai Hammad ya ce mata ai abin da aka yi mata kyautatawa ce, ba wai dukiyar aure ba. Kuma Allah ne ya tsamo ta ya bata rabonta ne. Ya kuma tuna mata a yadda aka yi auren su. Nana abin har kunya yake bata, yadda manyan mata wasu ma sun haife ta suke zuwa gidan, wai sun zo su gaishe ta, kuma in dai za su zo sai sun riƙo abin bata. Ta fara yi wa Nene ƙorafin ita wannan abin da ake yi mata ta gaji. Nene ta ce "Waye ya gaya miki ana shiga dawa dan ƙarya? Ai girma ne ya hau kanki, dan haka dole ki yi haƙuri. Ba kuma a yi wa masu mulki kyauta su mayar su ce a'a, dole ka karɓa. Kuma dole kema ki zama mai yawan kyauta. Sannan ki ƙirƙiro wani abu da zai amfani mata a ƙasar nan, saboda tabattar da za ki iya riƙe muƙamin da aka baki"
Nana ta ce "To Allah ya bani iko, abinka da ba a saba ba"
"Ke yi wa mutane shiru ke da ba a saba ɗin ba, dole a saba yanzu"
Haka Nana ta din ga jin tamkar an ɗaɗɗaure ta saboda takura.
Ranar da Hammad zai dawo, ya dawo tare da Muhsin, ta din ga murna dan har ta fara karaya Zahradeen ba zai bata ɗanta ba, ga shi tana jin nauyinsa, amma ta fara matsuwa da son ta yi magana.
Nana ta ce "Sayyid amma ya dawo kenan ko?"
Sayyid ya ce "To gamu nan dai, babansa sai masifa yake yi, sai da Sultan ya kira shi ya ce ya bamu ɗanmu. 'yan biyu sai kuka suke yi."
Nana ta ce "Ina ma zan iya bar masa shi, amma raba ni da ɗayanku kamar raba ni da rayuwata ne" Hammad ya ce "Idan ma bayarwar ne, ba gara ki ba wa Asal ba?"
Wani mugun kallo ta yi masa, da ya sanya shi yin shiru, ta saɓa ɗanta ta yi ɗaki.
Baba gaba ɗaya ji ya yi kewar Nana ta dawo masa sabuwa fil, kamar a lokacin ta ɓata, daga ita har Imran, amma mussaman ma ita Nanan. Gaba ɗaya ganin da ya yi mata ya ji ɗanɗani haukaci ne. Kusan kullum sai sun yi waya ta what'sapp. Har yake gaya wa Nana an kai wa Gaddafi kuɗin aure. Ta din ga murna sosai. Ta ce "Baba Dan Allah ka yi wa Sarkin baka magana a kansu Suwaiba, dan Allah" "Wallahi Nana a kan yi mini maganar yaran nan, zan daina kira mu yi magana" Gaba ɗaya Nana ba ta jin daɗin hakan da Baba yake yi. Haka take kiran Ummanta ma, su yi waya da su Walida. Sai ga Iliyasu da karɓar waya, su gaisa da Nana yana neman yafiyarta a kan abubuwan da suka faru. Har ga Allah Nana ta tsani mutumin nan, ba zata manta abubuwan da ya yi mata ba, amma ta duba matsayin da Allah ya kaita a yanzu, dan haka ta ga ba girmanta ba ne ma zaman jin haushin wani ba.