Buzu book 3 complete - Chapter 21
Buzu book 3 complete Chapter 21: Buzu book 3 complete Chapter 21. Ya shafa gashin kanta, tare da fatan Allah ya sanya Asal ɗin ta canza gaba ɗaya, tare da…
3,302 words
Ya shafa gashin kanta, tare da fatan Allah ya sanya Asal ɗin ta canza gaba ɗaya, tare da yi musu addu'ar samun rabo na alkhairi. Kamar ya tashe ta, sai kuma ya ƙyale ta kawai ya lumshe idanunsa yana addu'a a ƙasan zuciyarsa yana jiran bacci ya ɗauke shi. Yana tsaye a cikin sahara, ya riƙe akalar raƙuminsa, iskar sahara sai kaɗawa take yi, babbar rigar jikinsa na ɗagawa, ta cikin iskar yake jiyo sheshsheƙar kukan mace tana faɗin "Sayyid" ya waiwaya bai ga kowa ba. Shikaɗai ne a cikin saharar, sai dai bai daina jin sheshsheƙar kukan ba. A hankali ya buɗe idanunsa, wannan shi ne karo na bai san adadi ba, yana wannan mafarkin tun da ya buɗe ido a faransa. Jin kiran sallar Asuba ya sanya ya tashi ya tafi salla. Ranar farko da ya sake cin abinci bayan wanda ya ci da ya dawo, sai ya ji kamar ya san ɗanɗanon abincin, amma ya manta a ina ya san shi. Ranar da ya sake ganin Nana, Asal ta kira ta a kan ta zabga yaji a abinci ya kasa ci, sai da zuciyarsa ta kusa tsayawa, ya din ga jin kamar abu malaman haka ya taɓa faruwa, amma bai san a ina ba. Jikinsa ya din ga tsuma sakamakon jin sanyin da ya fara yi, ga kallon da take yi masa da ya sake burkita shi. Ya din ga matsa ƙwaƙwalwarsa, ko za ta ba shi wani abu, amma ya ji ya fara jin jiri. Bai tsaya kammala karin kumallon ba, ya tashi ya fita ya je ya samu Sultan, baya ya kammala zaman Majalissa, yake ce masa shi fa haryanzu bai ga Mahmoudu ba. Sultan ya ce masa ya yi tafiya ne, amma zai dawo. Haka kurum ya ji bai yadda da hakan ba, amma bai kuma cewa komai ba. Cikin hikima ya tambayi Asal inda ta samo Nana, ta sanar masa da a gidan Abincinsa na Maraɗi take aiki, ganin ta iya girki ya sanya ta kawo ta gidan, domin ta din ga dafa masa abinci. Sai dai a kullum abubuwan da Nana take yi, su na ƙara dagula masa lissafi nesa ba kusa ba. Matsin lamba da Hammad ya yi ya sanya aka sako Mahmoudu, kuma Matawalle ya jaddada masa lallai kar ya kuskura ya gaya wa Hammad komai a kan zuwan da suka yi Nigeria, kuma kar ya gaya masa ɗaure shi suka yi. Hammad bakinsa ya ƙi rufuwa, bayan ganin Mahmoudu da ya yi, saboda yadda yake jin Mahmoud a rayuwarsa ba ya jin Zahradeen yayansa da suke uba ɗaya haka. Sai ya yi ta yinƙurin ya yi wa Mahmoudu bayanin abubuwan ban mamakin da yake gani game da Nana, amma sai ya kasa. Babbn abin da ya sake ɗaure masa kai da ita, shi ne lokacin da ya hana ta cin ayaba. Ta karɓa ta ci, a lokacin ya ga Ƙisar a tare da ita. Ganin Ƙaisar ya ƙara hargitsa masa lissafi, saboda yana ganinsa hoton suffar Giyaz ya faɗo masa, amma ya manta a ina ma ya san fuskokin. Sai daga baya sannu a hankali ya tuna yadda Giyaz y fito masa a gidan tarihi, amma wanda ya gani tare da Nana bai kai wancan tsufa ba.
Gefe guda kuma Ƙaisar da Giyaz su na ta dambarwa, Giyaz ya ce ba zai taɓa rabuwa da Nana ba, ya mantar da Hammad wace ce Nana da duk wata rayuwa da suka yi a Nigeria saboda ta ci gaba da shan wahala. Bokan da ya sanya Giyaz aikin ɓatar da Hammad kuwa, hankalinsa ya dugunzuma bayan da shi ma wands ya ba shi aikin, ya matsa masa lamba da masifar ya aka yi Hammad ya dawo Agadez bayan an ce har abada shi da Agadez.
"Ya kai Giyaz, ina alƙawarin da muka yi da kai? Na baka 'yanci bisa sharaɗin za ka yi mini aiki, amma kwatsam sai na ga wanda na baka aikin a kansa ya dawo Agadez"
Giyaz ya ce "A cikin aikin naka wanne ne ban yi ba? Na mantar da shi waye shi, na mantar da shi, ya bar Agadez ya yi nesa da ita, kuma ya yi. Ni da kai ba na tunanin akwai wanda yake bin wani bashi, na cika sharuɗɗanka kaf da muka yi yarjejeniya a kai"
Bokan ya ce "Amma ai ga shi ya dawo Agadez cikin ƙoshin lafiya a hayyacinsa"
"Eh, ai ba mu yi da kai zai bar Agadez har abada ba, na kuma yi iya abin da muka yi sharaɗi a kai"
"Kar ka fusata ni, ka sanya na sake kama ka na rufe ka, ni bami yi haka da kai ba"
Giyaz ya ce "Ƙarya ne, ni dai ka kama ni ka sake kulle ni, ba za ka iya wannan ba. Kuma duk abu dole na zauna inda zan iya ganin ɗa na. Kuma ina nan ina ci gaba da gudanar da aikin da ka bani bisa yarjejeniya, tun da haryanzu ina nan tare da shi ban bar shi ba"
Bokan ya ce "Waye ɗan naka, kuma a ina yake?"
"Babu wannan a cikin yarjejeniyar aikina da kai, ka bar zancen a yadda na bar shi kawai" Bokan nan ya san faɗa da Giyaz ba abu ne da zai haifar musu da ɗa mai ido ba, sai dai dawowar Hammad mayar musu da aiki baya ne. Mahmoudu tunanin Nana ya addabe shi, tare da ganin rashin dacewar abin da ya faru. Ga shi alamu sun nuna ƙiri-ƙiri Hammad bai san ya je ya yi wata rayuwa a Nigeria ba. Ya kuma san muddin ya ce zai je Nigeria sai Hammad ya bi ba'asi, kuma kwana ɗaya ko biyu ya yi kaɗan ya je ya nemi Nana, balle ya yi masa ƙaryar kasuwanci zai je. Ya sha tambayar Mahmoudu a kan ko akwai wani abu dayake damunsa, saboda yanayinsa ya nuna akwai damuwa. Amma ya kan ce masa babu komai. Hammad ya ce wa Asal baya buƙatar sake ganin Nana. Sai murna take saboda ta zata munin Nana yake gani, shi kuwa mafita yake nema, daga burkicewar da yake yi a duk lokacin da ya ganta. Sai dai kuma kwana biyu da ya daina ganinta sai ya shiga damuwa, ya zamana duk ranar da bai ganta ba, sai ya ji shi tamkar a kurku, wunin ranar bai yi masa daɗi ba sam. Yana zaune a ɗakinsa, yake kallon yatsunsa babu zobe guda ɗaya, wanda shi ya fi kowanne muhimmanci. Shi dai Matawalle ya ce masa duk wanda ya tambayi zoben ya ce an kai zoben gyara ya samu matsala. Ya kalli tagullar hannunsa, ya din ga murza ta a hankali yana zancen zuci. Saboda gaba ɗaya a rikice yake, kasancewar Nana ta kai masa abinci tana ƙamshin turarensa da yake amfani da shi. Shi dai ya san babu wanda ya bawa turaren, kuma mai aiki kamar Nana ba za ta iya sayen turaren ba, kuma babu yadda za a yi a ce satar turaren ta yi har ta samu ƙwarin gwiwar shafawa. Yadda take yi masa wasu abubuwan kai tsaye wasu lokutan abin yana ba shi mamaki sosai da sosai. Ganin ya yi hasken wutar ɗakin tana ɗaukewa tana kawowa, daga baya ta tsaya, sai ga wani ɗan gajeren abu a ya bayyana da tsawonsa bai fi 'yar tsana ba, kansa duk wasu ƙayoyi. Hammad ya zuba wa abin ido, ganin yana motsi. "Tuba nake shugabana na tsorata ka, ni ne aljanin da aka wakilta hidima ga duk wanda ya ɗauke da wannan tagullar, tun da ka ke ba ka taɓa nema na ba sai yanzu, me ka ke buƙata?"
Hammad ya ce "Waye kai?"
"Arun, bawan aljani ga Sultan Azhar, wannan tagullar mallakinsa ce, kuma ni mai hidima ne ga ma mallakin tagullar"
Hammad ya zuba ido sosai, ya ga ɗan abin tsoho ne tukuf sosai da sosai. Domin kuwa gemunsa ƙasa yake ja.
Ya ce "Amma da idan na murza zoben ba kai nake gani ba"
Arun ya ce "Ai ba ni ka ke kira, hadiman wancan zoben daban, nima kuma daban"
"To ina zoben nawa yake?"
"Ka yi kyautarsa ga wanda ka ke matuƙar ƙauna a matsayin tukuicin soyayya"
Hammad ya ce "Soyayya kuma? Ni ɗin?
"Ƙwarai ya shugabana"
"To wa na bawa, kuma yaushe na yi soyayyar, kuma mace ce ko namiji?"
Arun ya sake cewa "Ba na son shiga hurumin da ba nawa ba, ina gudun sake rura wutar fitinar da ke tsakanin gangar jiki buyi, ruhika huɗu, alaƙa huɗu. Gangar jiki ta mutum biyu, ruhi huɗu, na mutum biyu da na aljan biyu, sai kuma alaƙar mata da miji da kuma uba da ɗa, sannu a hankali duk za ka fahimci abubuwan da nake nufi" Daga nan ya ɓace Hammad ya yi shiru yana juya maganganun da suka fi yi masa kama da shirme. Ya tashi ya fita falo, ya san lokacin kawo masa shayin dare ya yi, sai dai tun kafin ya ƙaraso cikin falon yake jiyo sautin muryarta tana waƙa. Daga nesa kaɗan ya tsaya yana kallonta, yana jin yadda zuciyarsa take bugawa da sauri.
*_ina zana ganka_* *_saƙo zana baka*_ *Hotona da naka*_ *_Ko ina zana bika*_ *_Kowa tsane ka, ni na tsane shi sanya a ranka*_ *_Zuciyata na baka duk masu ƙin ka su daina shakka*_ *_Rayuwata na baka_* *_Ni ta ya zan guje ka*_ *_Ka dawo gare ni dan zuciya ta bar kewa*_
Gaba ɗaya sai ya daskare a gurin, gumi ya din ga tsatstsafo masa, ƙwaƙwalwarsa ta shiga Kai komo, kansa kamar zai yi tsawa ya fashe. "Tabbas akwai wani abu, ya san wani abu mai kama da haka, amma yaushe? Kuma a ina?" Ya daɗe a tsaye a gurin, kafin ya saita nutsuwarsa ya shiga falon. Murmushi ta yi ta daina waƙar da ta ga ya fito ta risuna ta ce "Barka da dare" Ya jinjina mata kai.
"Sayyid ga shayinka nan, ina fatan na kammala komai, zan iya tafiya?" Ya yi shiru yana jujjuya Sayyid da take kiransa da shi.
Washegari da sassafe ya kira Mahmoudu a waya, ya sanar masa da yana son ganinsa za su yi magana. Amma Mahmoudu ya ce masa yana hanyar Maraɗi, zai kai wa Nene ziyara ne. Hammad ya yi ta mitar me yasa bai gaya masa su tafi tare, su je su gaishe ta, ya ba shi haƙuri. Sai dai tun da Mahmoudu ya je ya ga Muhsin ya rikice, ya din ga yi wa Nene tambayoyi a kan Muhsin, amma ta ƙi gaya masa haƙiƙanin gaskiyar waye Muhsin. Sai dai yanayin yadda ta ga Mahmoud ya rikice, ya sanya ta tabattar da ya ga abinda take tunani ita ma. Kwanansa ɗaya ya shirya ya nufo Agdez bayan ya faki idon Nene ya ɗauki hotunan Muhsin. Ya nufi Agadez da nufin komai zai faru sai dai ya faru. Hammad kuwa ya lallaɓa Asal ya yi mata wayo ya sanya ta dawo da Nana sashen su, ba tare da ta kawo komai a ranta ba. Amma shi a jikinsa yana jin baƙin abubuwa game da 'yar Nigeria da jikinsa bai ba shi cutar da shi za ta yi ba, amma kasancewarta daf da inda yake yana samun nutsuwa da nishaɗin kallonta. Tun da Mahmoudu ya dawo, Hammad ya lura bakinsa akwai magana, amma ya ƙi ce masa komai. "Mahmoudu na lura bakinka akwai magana, amma ka ƙi gaya mini, duk da ba ma 'yar haka da ni da kai, amma bari ni na gaya maka tawa damuwar". Mahmoud ya ce "Ni babu wani abu da zan gaya maka, amma gaya mini mene ne yake damunka?"
"Ina kukun da nake gaya maka Asal ta samo 'yar Nigeria?" Gaban Mahmoud ya faɗi amma ya dake ya ce "Eh meyafaru?" "Wasu abubuwa nake ji game da ita, da tun da nake ban taɓa ji game da wani mutum ba" Mahmoudu ya yi murmushi ya ce "Ko santa ka ke yi ne?"
"Anya kuwa, ban dai sani ba, amma ba normal mutum ba ce"
"Ka na da mata fa a Nigeriar nan"
Hammad ya kalle shi yana jiran ƙarin bayani. Mahmoudu ya ce "Da wasa nake yi, na dai ce zan aura maka 'yar maka 'yar Nigeria idan ka na so. Amma ina da wani abin al'ajabi da nake son nuna maka, amma tashi mu je ka shirya, ka ce mini za ku yi hawan raƙuma kar a yi ta jiran ka" Babu musu ya tashi suka fita. Kowanne a cikin su yana ta saƙe-saƙe a cikin zuciyarsa. Sai dai bayan an yi hawan raƙuman, da Hammad ya faɗo tare da Mahmoudu aka dawo da Hammad gida. Sai dai ya yi mutuwar tsaye, da hango ta tana leƙen mutanen da suke kaiwa da komowa a falon fuskarta ɗauke da damuwa.
A jere zuciyar Mahmoudu ta buga, addu'a ya fara yi, a kan Allah ya sanya ba mafarki yake yi ba, ko kuma tsabar saka abin a ransa ne ya sanya ta fara yi masa gizo ba.
Ayshercool 08081012143
93 93 LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KUƊIN KARATU KAFIN KI KARANTA. 08081012143
Cikin hanzari Habu ya ja rawaninsa ya nufi barin falon, yana daf da fita Nana ta waiwaya ta ga wucewarsa, sosai ta tsaya tana kallon bayansa har ya fice tana yi masa kallon sani. Washegari da safe Bayan Tafawa ya zo duba shi, ya tafi zuciyarsa a cunkushe babu daɗi, saboda kausasan kalaman da Tafawa ya yi amfani da su, har da ce masa ko shaye-shaye yake yi, shi ya sanya ya faɗo daga kan Taguwa. Wajen ƙarfe sha ɗaya, da ya ji sauƙi, ya lallaɓa ya fito, yana mamakin dalilin da ya sanya Nana hana shi hawa kan Taguwa, da ya hau kuma ya faɗo. Yana fitowa ya tarar da ita da Asal su na mujadala. Sai dai hangota kawai da ya yi, sai ya ji wani sanyi a ransa.
Nana ce take kallon Asal cikin takaici, bayan da Asal ta ce mata ta din ga sanya da hadiman gidan suke sakawa. Nana ta rasa dalilin da ya sanya Asal ke son ƙasƙantar da ita ko ta halin ƙaƙa. Nana ta dube ta ta ce "A gaskiya ba zan iya sanya kayan da hadimai suke sanyawa ba, ko ki haƙura ki kalle ni da kayan jikina, ko kuma ki sallame ni. Tun da ni ba baiwarki ba ce ba, aiki kawai ki ka ɗaukko ni na yi miki"
"Idan na so mayar da ke baiwar tawa ina da halin yin hakan, ke kin san ina da abin da ko nawa za a yi miki kuɗi zan iya bayarwa na saye ki"
"Ko da Goma ta lalace a gaban biyar take har gaban Abada Gimbiya Asal. Kuma wani garin ya fi gaban kunu. Ba ki da arzikin da za ki Asma'u a matsayin baiwarki" Nana ta ƙarasa maganar a zafafe. Hammad ya yi gyaran murya, suka tsaya Asal ta haɗiye maganganun da ta yi niyyar caɓawa Nana.
"Cherié, ba zai yiwu ki ɗaukko wadda ba hadima ba a cikin gidan nan, alhalin kin san kin taka dokar gidan mulki ba, sannan ki ce ta din ga saka kayan hadimai a nan ta fiki gaskiya."
Cikin mamaki Asal ta kalle shi za ta yi magana, amma ya ɗora yatsansa a kan laɓɓansa a dole ta yi shiru. Nana kuwa haɗa su ta yi, tai musu kallon banza ta wuce ta bar su a gurin. Sai dai kallon da ta yi musun, sai da ya kusa ɗimaucewa, ji ya yi tamkar ya bi bayanta. Wani murmushi ya saki ya nufi Asal yana lumshe ido ya ce "Ba girmanki ba ne, ki din ga sa'in sa da ma'aikatanki ai kin wuce nan".
"Amma ka na kallo a yadda take yi mini magana, kuma ka hana ni magana?" Ta yi maganar kamar za ta yi kuka. Ya kamo hannunta ya ce "Yawan musayar yawu da na ƙasa da kai, raini yake janyowa, kuma kar ki yadda ki yi fin ƙarfi a abin da ba ki da gaskiya, nan ma raini zai din ga janyo miki" Ya ƙarasa maganar yana rungume Asal, amma a zahiri hanyar da Nana ta bi, ya bi da kallo ƙamshin turarensa da ta shafa ya ci gaba da karaɗa hancinsa.
Mahmoudu kuwa bai yi bacci ba, so yake ya tabattar da abin da idanunsa suka gane masa, gaskiya ne ba gizo ba. Ya kira wayar Hammad, amma bai ɗauka ba, ga shi tsoron zuwa gidan yake domin kar su haɗu da Nana, ya san komai zai rikice ne. Ga yaron da ya gani a gurin Ummansa, ga kashedin su Matawalle, ga kuma wannan abu da ya tarar. "Anya yaron na ba ɗan Hammad ba ne?" Ya tambayi kansa. Wayewar garin Allah ya din ga kiran Hammad a waya amma bai ɗaga ba. Takaici ya ishe shi, sai can wajen Azahar sannan ya kira Mahmoudu.
"Tun jiya nake kiran ka ka ƙi ɗaga wayata"
Hammad ya ce "Ban jin daɗi ne, sai yanzu na duba wayar, ya ake ciki ne?"
Mahmoudu ya ce "A ina zamu haɗu, ina da magana da kai"
Hammad ya ce "Ina gurin Sultan, haryanzu bai sallame ni ba"
"Idan ya sallame ka, mu haɗu a saharar gidan tarihi mu sha shayi, zan nuna maka wani abu"
Hammad ya ce "To, saura na ga ba wani abin kirki ba ne, ba za ka yi mini ya jiki ba?"
Mahmoudu ya ce "To ya jiki Allah ya kiyaye gaba sai mun haɗu"
Hammad ya yi murmushi ya ajiye wayar.
Da yamma suka haɗu a sahara, lokacin rana ta yi sanyi. Hammad ya ce "Sai wani nema na ka ke yi, me za ka bani?"
Mahmoudu ya ce "Babu komai shayi kawai nake son mu sha tare."
Hammad ya yi shiru yana kallon saharar, daga inda suke su na hango gidan tarihi, kuma suna hango wani sashe na gidan sarauta. Ya na shan shayin a hankali yana son ya tuna wani abu, amma ya kasa. Mahmoudu ya ce "Ya na ji ka yi shiru?"
"Ina tunanin yarinyar nan ne"
"Wacce?"
"Wadda Asal ta kawo, a matsayin mai yi mini girki, abubu da dama su na faruwa da na kasa gane kansu" Nan ya sake gaya wa Mahmoudu yadda ta hana shi hawan taguwa, da abubuwan da yake ji game da ita" Mahmoudu ya ce "Kuma kai ba ka santa ba, baka taɓa ganinta ba ko a wani guri?" Ya ɗan yi shiru Sannan ya girgiza kai ya ce "A nan kawai na taɓa ganinta" "Baka tuna komai ba, da muka zo gurin nan?" Nan ma ya girgiza kai duk da yadda ya ji kansa ya fara ciwo. Mahmoudu ya ce "Gaskiya yakamata a ce duk yadda za mu yi, muyi bincike a kanta, mu san daga ina take, kar mu sakankance wani abin ya faru. Ka san ita kanta Gimbiya Asal ba ta yin abu babu dalili, kar mu je shirin Tafawa ne"
Hammad ya ce "Gaskiya ne, amma ta ce mini daga gidan cin abinci na Maraɗi ta ɗaukko ta a gurin su Al-Husssain"
Mahmoudu ya ciro wayarsa ya daddana, ya miƙa masa ya ce "Ka ga wani ikon Allah" Hammd ya sanya hannu ya karɓa, ya yi shiru ya zuba wa wayar ido. Jiki a sanyaye ya ɗago ya kalli Mahmoudu ya ce "Ina ka samo wannan hoton?"
"Samo shi na yi kawai na nuna maka"
Ya damƙe wayar da ƙarfi, ƙirjinsa ya yi masa nauyi ya ce "Mahmoudu kuma ka tabatta wannan ba ɗana ba ne ba? Duk wanda ya kalli wannan hoton zai yi zaton ma nine" "Ka na da wata matar ne da zata haifa maka ɗa? Ko kuma Asal ta haihu ne bamu sani ba?" Ya girgiza kai ya ce "Ko ɗaya, amma wannan yaron buzu ne, duk inda iyayensa suke ka nemo mini su a faɗin ƙasar nan"
"Me za ka yi musu?"
"Zan yi musu alkhairi ne kawai. Amma Mahmoudu kawai ji nake kamar ina da alaƙa da shi, dan Allah ka tura mini hoton nan"