Kenza eBookz

Buzu book 3 complete - Chapter 22

Buzu book 3 complete - Chapter 22

Buzu book 3 complete Chapter 22: Buzu book 3 complete Chapter 22. Mahmoudu ya karɓi wayar ya ce "Zan tura maka" Gaba ɗaya jikinsa ya yi sanyi, ya kuma kasa…

3,359 words

Mahmoudu ya karɓi wayar ya ce "Zan tura maka" Gaba ɗaya jikinsa ya yi sanyi, ya kuma kasa shan shayin. Sule ne ya zo gurin a kan babur, ya kafe baburin, ya sauka ya gaida Hammad cikin girmamawa. Hammad dai ya amsa yana bin sa da kallo. Suka gaisa da Mahmoudu ma, ya ga sun sake sun fara hira. Mahmoudu yana ta satar kallon Hammad, ko zai ɗago ya tuna wani abin, amma ya ga babu alamar hakan. Bayan tafiyar Sule, yake gaya masa ai abokin kasuwancinsa ne na Nigeria. Kawai ya jinjina kai.

Ƙaisar ne ya bayyana a gaban Giyaz, fuskarsa babu annuri ko kaɗan. Giyaz ya ɗaga kai ya kalle shi, ya ce "Ɗan samari ya dai?"

"Zuwa yaushe zaka ci gaba da wannan mugun wasan da ka ke yi?"

Giyaz ya ce "Wanne daga ciki?"

"Kowanne ma? Ka dawowa da mutumin nan tunaninsa ya tuna da yarinyar nan, ga ɗa a tsakaninsu ko iya yanzu ka ɗauki fansar ai, ka ƙyale ta ta huta haka?"

"Yaro yaro ne. Yarinyar da kakaninta suka cutar da mu, ta zo ta ƙona ni ta sanya ni jinya, ita ka ke tunanin na ɗagawa ƙafa ma sassauta mata?" "Ba na son alaƙata da kai ta ƙara tsami, amma zan yi abin da ba ka zato, ba zan zuba ido ka ci gaba da cutar da ita har haka ba" Ƙaisar ya yi maganar cikin ƙunar rai. Giyaz ya ce "To babu laifi, ka yi abin da duk za ka yi"

Hammad kuwa da ya koma gida, ya kasa zaune ya kasa tsaye, hoton yaron nan ya din ga kaiwa da komowa a cikin kwanyarsa. Yaya za a yi a ce a samu yaro yana irin wannan kamanin da shi, ba kamanni sama-sama ba, kamanni na zahiri nesa ba kusa ba. Bayan haka yaron ya yi masa kama da wani wanda ya sani ko ya taɓa gani, amma ya manta waye, ya din ga duba wayarsa ko Mahmoudu ya turo masa hoton yaron, amma wayam bai tuta masa ba. Gefe guda ya so haɗuwa da Nana, amma bai ganta ba. Sai washegari da ta kawo masa Abincin safe ta yi masa ya jiki. Ya ce "Sai yanzu za ki yi mini ya jikin?" Ya yi maganar yana tsare ta da manyan idanunsa, saboda wani irin kyau da ta yi masa. Ga ƙamshin da take yi, har wani ƙara nutsuwa ya yi yana kallonta. "Tuba nake ranka ya daɗe" Sayyid ɗin da take kiransa da shi, ya din ga kaiwa yana komowa a cikin kwanyarsa. Haka da rana da ta yi shigar Atamfa, kamar ya sace ta ya gudu. Ta karya ɗaurin ɗan kwali, ta yi kyau. Ya ce "Amm Asma'u ko?" Ta jinjina masa kai duk da yadda ta ji Asma'un banbarakwai a bakinsa. "Cherié ta ce mini a gidan cin abinci na Maraɗi ta ɗaukko ki ko?" "Eh Sayyid" "Me ya kawo ki Niger ne? Ko takanas ki ka nemi aiki da mu, tun daga Nigeria?" Nana ta girgiza kai ta kalle shi ta ce "Abuna ne ya ɓata na zo Niger neman sa, ina son a yi mini izini, nan kusa na koma Nigeria" Ya jinjina kai kawai ba tare da ya gama fahimtar abin da take nufi ba. A daren ne kuma Nana ta jiyo kakarinsa, Asal ta fice ita kuma ta shiga ɗakin. Ƙara lafewa ya yi tamkar ya shige cikin ta, saboda daddaɗan sanyin da ya mamaye jikinsa. A hankali ya buɗe idanunsa, ya ji yadda ta ƙanƙame shi tana kuka. Ya saurara ya yi shiru ya ji ba muryar Asal ba ce. "Allah ka duba mu, ka yaye masa wannan ciwo, Allah ka yi masa maganin abin da yake damunsa. Yana jin yadda take shafa gashinsa tana ci gaba da kuka tana faɗin "Da gaske ba ka gane ni ba Sayyid, ko kuma wasa ka ke yi mini da hankali kawai. Na fara sarewa Sayyid, idan wasa ne ka tausaya mini haka, wahalar da na sha ta isa, ka duba ni ka duba makomar abin da na haifa maka dan Allah" Ta yi maganar tana ƙanƙame shi tana ci gaba da kuka. Gaba ɗaya sai ya rikice, bayan kukanta da maganganun da take yi da suka rikita masa lissafi, gangar jikinsa kuma wani saƙon take aika masa na daban, har wata tsuma ya fara yi. Sai dai Allah ya taimake shi, bai yi wani yinƙuri ba, ya ji tana magana da Ƙaisar, ta kwantar da shi a kan pillow ta koma gefe. Tunani ya din ga yi ina Asal ta tafi? Ya aka yi Nana ta shigo har turakarsa kai tsaye haka, kuma wasu irin maganganu take yi haka? Ya yi lamo kamar bacci yake yi, amma idonsa biyu. Sai gefin Asuba da ta bar ɗakin, ya tashi ya zauna, yana jin wani irin raɗaɗi a tsakiyar kansa, zuwa ƙirjinsa gaba ɗaya ji yake kamar zai fita hayyacinsa ƙwaƙwalwarsa na nema ta hargitse. Garau ya miƙe bayan sallar asuba, ya sake tuna yaron da Mahmoudu ya nuna masa, da maganganun da ya ji Nana tana yi. Ya kira Al Hussain a waya, ya ce masa lallai yana son cikakken bincike a kan Nana. Ga Sultan ya tura shi wakilicin wani ɗaurin aure, amma kusan baya cikin cikakken hayyacinsa, kansa cunkushe da lissafi kala-kala. Maganganun Nana suka din ga karafkiya a cikin kwanyarsa, da rungumar da ta yi masa ba tare da tsoron komai ba. Ko da ya dawo, har ya wuce ɗakinsa, amma kansa ya din ga wani irin ciwo, kawai ya yanke shawarar zuwa ya turke Nana, ta yi masa bayani dalla-dalla. Sai da ya bari Asal ta yi bacci, sannan ya tashi ya tafi ɗakin Nana. Sai dai da ya je ɗakin ya tarar ba ta ciki, sai wayarta da take kan katifarta a ajiye. Har zai juya ya fita, kawai ya nufi kan katifar ya sanya hannu ya ɗauki wayar. Ya jujjuya wayar, yanayin yadda screen ɗin wayar ya dusashe ya sanya ya gane wayar ta kwana biyu. Kawai ya danna madannin gefe a take hoton fuskar Nana da Muhsin ya bayyana a kan screen ɗin wayar. Mutuwar tsaye ya yi zuciyarsa ta yi wani irin mummunan bugawa da ƙarfin gaske. Alamun tahowar Nana ya ji, babu shiri ya jefa wayar kan katifar ya yi sauri ya kashe fitilar ɗakin.

AREWABOOKS

Ko da Nana ta shigo ɗakin, jikinta ya bata akwai mutum a ciki. Da ta kunna fitilar ta yi arba da shi, ta rikice ta kusa kurma ihu, sai dai duk da a tsorace yake shi ma, amma kasancewar sa Namiji ɗan gwagwarmaya ya sanya ya danne tsoronsa da tashin hankalin da yake ciki, ya yi mata duk tambayoyin da ya yi mata, sai dai bai tambaye ta haƙiƙanin abubuwan da yake son tambayarta ba. Duk amsoshin da ta ba shi, ba su gamshe shi ba, haka ya fice ya bar ta. Tun da ya bar ɗakin kusan kwanan tsaye ya yi, ya din ga kaiwa yana komowa a ɗakinsa ya dafe kansa, ya zauna ya tashi. Duk wani lissafi da ya yi sai ya ji babu mafita. Shi dai bai taɓa ganin Nana ba, amma meye haɗinta da yaron da Mahmoudu ya nuna masa? Sannan mene ne alaƙarta da shi da ta iya shiga turakarsa ta rungume shi take faɗar wannan maganganun da suke nuna da alaƙa a tsakaninsu. Har aka yi kiran sallar Asuba ko gyangyaɗi bai yi ba. Da Asuba da ya dawo daga masallaci, har zai wuce hanyar ɗakinta, ya koma ya nufi ɗakin nata. Ya jima a gurin yana kallon ƙofar. Ya buɗe ƙofar ɗakin a hankali. Ya tarar da ita tana bacci. Sai dai abin da bai sani ba, Ƙaisar ne ya ƙara wa Nana nauyin bacci, amma duk abin da yake faruwa tana gani, sai dai ba za ta iya motsi ba. Cikin sanɗa Hammad ya ɗauki wayar ya yi waje. Bai ko sake nufar ɗakinsa ba, ya fice. Gidan Mahmoudu ya tafi, ya je ya tarar da shi a zaune yana lazumi. Sai da Mahmoud ya tsorata ya ce "Lafiya na ganka da duku-dukun nan?"

"Mahmoudu wane ne yaron nan da ka nuna mini? Kuma wace ce yarinyar da Asal ta kawo a matsayin mai yi mini girki?"

Mahmoudu ya kalle shi ya kalli screen ɗin da yake nuna masa, tabbas Nana ce ba wata ba, amma zai so ya yi magana da Nana kafin gaya wa Hammad wani abu. "Ka yi magana ka tsaya ka na kallo na" Ya yi maganar cikin hasala.

Mahmoudu ya ce "To ai Asal yakamata ka tambaya ba ni ba, ni fa cin karo kawai na yi da hoton na nuna maka" Zai yi magana kansa ya sara, ya saki wayar ya fara ja da baya yana dafe kansa, ya tafi zai faɗi Mahmoudu ya yi saurin tare shi, ya kwantar da shi a hankali. Ya ɗauki wayarsa ya kira Al-Husssain. Bayan sun gaisa Mahmoudu ya ce "Imam Hammad ya yi maka magana a kan yi masa bincike a kan yarinyar da Asal ta kawo Agadez ta din ga yi masa girki ko?"

"Eh ya kira ni, ya yi mini maganar"

"To yaya ake ciki, me aka gano a kanta?"

Al Hussain ya ce "Eh ina kan yin binciken ne, amma dai wani kamfani ne, da suke samar wa mata, guraren aiki suka kawo ta. To na saka Hasna ta tuntuɓe su, dan ni gaskiya ban wani tantance ta ba, na ɗauke ta aiki, saboda ta ce daga Nigeria take. To gidan aikin sun ce, su ma wata mata ce jami'arsu ta kawo musu ita. Amma za a nemo matar yanzu haka su muke saurare" Mahmoudu ya ce "To shikenan, amma duk abin da aka ƙarasa bincikowa, ni zaka sanar, ka gaya masa tukuna" Sanin alaƙar da take tsakanin Hammad da Mahmoudu ya sanya kai tsaye ya ce masa to. Hammad kuwa yana kwnace, sai jujjuya kansa yake yi yana wani irin gumi. Giyaz yake gani yana yi masa wata irin dariya, da ƙara wadda ta cika masa kunne. Ya lallaɓa ya tashi zaune ya toshe kunnunwansa yana faɗin "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" Mahmoudu ya durƙusa a gabansa yana kiran sunansa, amma bai amsa ba ya rintse idanunsa. "Sayyid, Sayyid dan Allah da gaske ba ka tuna ni ba?" Maganganun da Nana ta din ga yi masa ya din ga ji a cikin kunnensa. "Mahmoudu" ya kira sunansa a hankali.

"Na'am Imam"

"Mene ne alaƙata da yarinyar nan?"

"Amm ban sani ba tukuna, ina jiran abin da Al Hussain zai ce ne tukuna"

"Ka kirawo ta ka tambaye ta, wane ne yaron nan? Me yasa kuma yake kama da ni?"

"Za a yi, amma ka yi shiru da bakin ka mu gano komai tukuna" Sai zuwa yamma Hammad ya ɗan samu nutsuwa, sai dai bai sake ganin Nana ba, abincinsa ma ajiye masa ta yi. Da daddare Asal ta ɗauki hankalinsa sosai, saboda yadda ta sha kwalliya cikin jajayen kayan bacci sai ɗaukar ido take yi. Yana ta ƙoƙarin kar ya shiga hakkinta, saboda damuwoyin da suka yi masa yawa. Sai dai bai iya taɓuka komai ba, hankalinsa ya fara gushewa. Wani irin haske ya din ga gani a cikin baccin nasa yana ɓullowa ta cikin wani mudubi, sama-sama ya din ga hango shi tare da Nana a ciki, cikin yanayin wata rayuwa da take nuna tsananin kusanci da kyakykywar alaƙa a tsakaninsu. Sai dai bai gama fahimtar abin cikin mudubin ba, Giyaz ya bayyana ya huro wata irin wuta a take mudubin ya tarwatse, ya ja da baya yana kare kansa. Giyaz ya gani tare da Ƙaisar, tsananin kamaninsu tsufan Giyaz ne kawai ya sanya shi ya banbance su. Farkawa ya yi jikinsa ya ɗauki wani irin zafi. Tashi ya yi yana zagaye ɗakin, amma ya ci gaba da jin zafin ya tsananta kawai ya fita ya je hanyar ɗakin Nana ya zauna. Zuciyarsa kuma sai azalzalarsa take yi a kan ya je ya samu Nana ya yi magana da ita, amma wata zuciyar ta hana shi hakan. Giyaz kuwa faɗa ne ya kacame tsakaninsa da Ƙaisar. "Ƙaisar muddin ka yi ƙoƙarin saka mutumin nan ya tuna yarinyar nan, zan iya hallakaka, ko kuma na saka shi ya haukace gaba ɗaya" Ƙaisar ya ce "Kafin ka halaka ni, ni zan halakka ka muddin za ka ci gaba da shiga abin da bai shafe ka ba"

"Ni zaka hallaka, Giyaz bin Jaddul Jinn?"

Ƙaisar ya ce "Ƙwarai kuwa, a kowane lokaci zan iya baka mamaki"

Hammad kuwa da duku-duku ya sake tafiya gurin Mahmoudu. Yana ganinsa gabansa ya faɗi.

Ya ce "Mahmoudu ka zauna mu yi magana"

Mahmoudu ya zauna yana rarraba ido"

"Ko dai ka gaya mini abin da ka ke ɓoye mini, ko kuma zan tari duk wanda nake ganin zan samu abin da nake nema, komai zai faru sai dai ya faru. Ka yi mini bayanin waye yaron nan, kuma wacece yarinyar nan"

"Matarka ce" Ya ba shi amsa kai tsaye. Zabura ya yi ya ja da baya yana kallon Mahmoudu "Yaushe kuma ta yaya?"

"An yi mini gargaɗi sosai da sosai, a kan kar na kuskura na gaya maka, duk da babu wanda ya san da wannan zancen ma. Amma ko zan rasa rayuwata na yi alƙawarin zan gaya maka iya gaskiyata. Nana matarka ce da ka aura a Nigeria. Bisa ga binciken da nake yi ta ƙarƙashin ƙasa kuma, kai ta fito nema ta zo Agadez" Jiki a sanyaye Ya ce " Mahmoudu ban fa gane me ka ke nufi ba, yaushe na je Nigeriar har na aure ta?"

"Bayanan da Matawalle ya yi maka ba haka yake ba, ka manta da komai naka, na tafi da kai Nigeria. Yanzu duk bayanin da zan yi maka ba komai zaka fahimta ba, amma Nana Asma'u matarka ce"

Hammad ya ce "Mahmoudu, anya ba haukacewa na yi ba kuwa? Ji nake yi kamar ba mutum ne ni ba. Gaskiya"

Ya dafa kafaɗar Hammad ya ce "Mutum ne kai, wasu abubuwa ne dai kawai suke faruwa amma ka nutsu, ka yi addu'a. Dan muddin ba ka tuna komai ba, ba zamu iya tunkarar kowa da maganar nan ba. Mutumin da ya zo muna tare a sahara, tare aka kamo ni da su, tare muka yi aikin gadi da su a Nigeria. Hammad ban san yaya zan yi maka bayanin jajircewa da sadaukarwar da yarinyar nan ta yi saboda kai ba." Nan Mahmoudu ya din ga yi masa bayanin wasu abubuwan da ya sani. Ya yi shiru ya rasa gazgatawa zai yi ko ƙaryatawa, idan ya yi duba da wasu abubuwan sai ya ga yakamata ya gazgata batun, dan Mahmoudu ba zai masa ƙarya ba. Amma ya din ga jin sa kamar ba mutum ba, ko kuma a wata Duniyar yake ta daban. Da daddare yana tare da Asal, tana danna waya, Nana ta kawo Abincin dare. Kamar ya yi mata magana ya fasa, sai dai ƙasan zuciyarsa ya din ga fatan Allah ya sanya gaske ne, Nana matarsa ce, ta kowacce fuska ta yi masa. Tun kan ya ji kan wannan burkitaccen labarin yake jin wani abu na sukan zuciyarsa a game da ita. Babban abin da yake ƙara burge shi da ita, sanin mutuncin kanta da ba ta yadda Asal ta taka ta ba. Saɓanin waɗanda suke kwantar da kai Asal ɗin ta taka su saboda abin Duniya. Ya gaza manta rungumar da ta yi masa a turakarsa. Ta ɗago kai suka yi ido huɗu da shi, amma bai sauke idanunsa ba ya ci gaba da kallon ta. A ɗan diririce ta ce "Na gama zan iya tafiya. Bai amsa mata ba ya tuna yadda take ba shi Nonon raƙumi da habbatussauda, ga abinciccikan da yake matuƙar da take gwangwaje shi da su. Asal ta ce "Za ki iya tafiya" Sai da Nana ta je tsakiyar falon sanan ya ce yana buƙatar lemon kankana da shayin citta da kanumfari kawai, ba zai sha na kimba ba. Nana ta yi shiru ta ci gaba da tafiya, Asal ta ce "Kin ji ai"

A hankali Nana ta ce "Na ce miki ba ni da kunne ne, da ba zaki iya tsinana wa mijinki uban komai ba"

"Ke ba magana nake yi miki ba" Nana ta waiwaya ta ce "Ai na amsa na ce to"

Shi kuwa ya yi haka ne, dan ta sake dawowa ya ci gaba da kallon ta ko Allah zai sanya ya iya tuna wani abin. Amma har ta kawo masa shayin tayi tafiyarta bai tuna komai ba.

Sosai faɗa ya ɓarke a tsakanin Giyaz da Ƙaisar a kan Nana, Giyaz ya din ga ɗaga Ƙaisar yana bu ga shi da ƙasa. Karfin Ƙaisar da na Giyaz ba ɗaya ba ne ba, duk da Giyaz ya kwana biyu a duniya amma yana da matuƙar ƙarfi. Ƙaisar ya baje a gurin, bayan buga shi da jikin dutsen gidan tarihin Agadez,da Giyaz ya yi, ga ƙona shi da ya din ga yi da wuta. Sai dai ganin Ƙaisar ya baje ko motsi ba ya yi, ya sanya ya nufe shi da sauri yana kiran sunansa, ya ɗago Ƙaisar, amma ya shammaci Giyaz, ya fito da jakar gurin Sarkin Baka daga cikin rigarsa, ya naɗe masa wuya da hannun jakar. Wata irin kururuwa Giyaz ya din ga yi, yana tumami a gurin yana burgima. Ihun nasa sai da ya razana da yawa daga cikin halittun da suke cikin gidan tarihin. Ƙaisar ya miƙe da kyar ya tunkari wani ɗaki, aljanun da suke ƙofar ɗakin su ka dare suka ba shi guri. Ya zura hannunsa a ya ɗaukko kwalbar da Giyaz ya ce tunanin Imam Hammad ne a cikinta. Ya ajiye ta a nesa kaɗan ya ja da baya ya din ga hura iskar bakinsa a jikin kwalbar. A take kwalbar ta yi wata irin ƙara ta tarwatse, a take ɗan hayaƙin da yake cikin kwalbar yana zagayawa a cikin wani ruwa ya bar cikin ta. Ƙaisar ya koma kan Giyaz da ya suma a gurin, ya ɗauke jakar da ya shaƙe shi da hannunta, ya ɓace daga gurin.

A hankali yake juyi, ya buɗe bakinsa domin ya jarraba yin magana, ya ji ko maganar ta dawo ya ce "Ma vie" sai dai ya ji shiru. Shi ma shirun ya yi yana ji wani raɗaɗi tun daga cikin kansa har idanunsa. Ya yi juyi ya ji taushin abin da yake kai ya banbanta da nasu. Ya buɗe idanun da suke yi masa raɗaɗi da kyar yana kallon ɗakin. Asal ce ta shigo ya kalle ta, ta ce "Amour ta gama abinci, ka taso ka karya" Ya jinjina mata kansa da ya yi masa wani irin nauyi mara misaltuwa. Tabbas ya san Asal matarsa ce, amma ina Nana. Sai ya yi shiru sannu a hankali ƙwaƙwalwarsa ta tariyo masa yadda aka fita da shi daga gidansu na Buda yana fizge-fizge yana kiran matarsa Nana. Ya rintse idanunsa tare da damƙar gashin kansa yana girgiza kan, saboda yadda ƙwaƙwalwar tasa ta hargiste, tunanin ma ya rasa wanne zai yi. "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ya din ga maimaitawa babu ƙaƙƙautawa. Asal ta sake shigowa ta ce "Amour wai yane? Baccin ne bai ishe ka ba? Sha biyu saura fa na rana, ba ka ko karya ba" Ya yi mata nuni da hannunsa alamun yana zuwa.

"Ok, ni zan je gida, Abbu yana jira na" Ya jinjina mata kai"

Sannu a hankali ya fara samun nutsuwa, ya miƙe tsaye a hankali, ya shiga banɗaki ya watsa ruwa, sai dai jiri ya din ga ɗibarsa. Ya fito ya zura rigarsa ya fita, ya hau kan doguwar kujera ya kwanta. Ya lumshe idanunsa, abubuwan da suka faru a Nigeria suka din ga dawo masa saɗara-saɗara, zuwa dawo da shi Niger da aka yi. To ya ya aka yi ya manta da ita komai nasa ya shafe da ya baro Nigeria, kuma yaya aka yi ya manta da komai nasa da yaje Nigeria. "Anya babu wata maƙarƙashiya ko wani abu da ban sani ba, game da rayuwata ba?"

Bakinta ɗauke da sallama ta shigo ɗakin, hannunta riƙe da kwandon kwanukan Abinci. Wata irin karaya ta ziyarce shi, zuciyarsa ta din ga azalzalarsa ya tashi ya rungume ta, Asmynsa ce, amma zuciyarsa ta din ga gargaɗinsa kar a samu matsala, dan ya san dokar Agadez.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull