Kenza eBookz

Buzu book 3 complete - Chapter 25

Buzu book 3 complete - Chapter 25

Buzu book 3 complete Chapter 25: Buzu book 3 complete Chapter 25. "Ƙarya ki ke yi, ba ki da abin da za ki kawo ƙarshena a masarautar Agadez, saboda ba ki…

3,371 words

"Ƙarya ki ke yi, ba ki da abin da za ki kawo ƙarshena a masarautar Agadez, saboda ba ki za hujja a kan wannan soki burutsun da ki ke yi" Ta yi maganar tana tsare Nana da ido. Nana ta ce "Kwantar da hankalinki, ba na buƙatar wata hujja ko wani abu, dan har gaban Abada ba zan taɓa tona miki asiri ba. Ai Hammad yana sonki kuma ko ba komai 'yar uwassa ce ke, dan haka ki kwantar da hankalinki, amma daga yau da rana mai kamar irin ta yau, muddin ina tare da Hammad da ke da duk wani abu da yake kawowa rayuwarsa wani tarnaƙi"

Gimbiya Bilkisu ba ta bari Asal ta sake magana ba, ta kama hannunta suka yi waje. Nana ta ja numfashi tana bin bayansu da kallo, kafin tsunduma tunani. Gimbiya Bilkisu ta kalli Asal ta ce "Ke, kina wani wawanci har ki ka bari ta san kina wannan abubuwan? Asal kina da hankali kuwa?"

Cikin kuka ta ce "Ammi yaya zan yi, wallahi ban san da wata alaƙa a tsakaninsu ba, ban sani ba. Kuma ban san za ta kawo wani abu ba. Na shiga uku ba zan iya rayuwa babu Hammad ba wallahi Ammi ina son mijina, kuma ba zan iya buɗe ido na gan shi da wata ba ki taimake ni" "Nutsu ki kwantar da hankalinki, bari na yi wa babanki magana a san abin yi a yau ba sai gobe ba, dole a san yadda za a yi da yarinyar nan ki daina kuka" Da kyar ta din ga rarrashin Asal.

Nana na zaune na zaman jiran dawowar Hammad,furucin Asal ya tsorata ta, ta fuskanci da gaske kowa na iya aikata duk abin da yake so, a wannan gidan domin cimma burinsa. Ita ba ta kanta take yi ba, ta ɗan jaririn ɗanta da ba ta san inda yake ba ta shi take yi. Ta ƙudurce a ranta, idan Hammad ya dawo, bori za ta yi masa sai ya fitar da ita daga gidansa komai zai faru, amma ƙasan zuciyarta yana ta azalzalarta a kan son a buɗe wannan dakin na gidan tarihin. Bayan azahar ya shigo, sai dai yanayinsa ya nuna mata a cikin damuwa yake. Ya nemi guri ya kwantar da kansa a kan cinyarta. Nana ta shafa kan a hankali ta ce "Lafiya kuwa?" Ya jinjina mata kai kawai. "Ka ci abinci ne?" "Na ci" ya amsa a hankali. "To meyafaru?" Ya ce "Babu komai"

Nana ta numfasa ta ce "To dan Allah ina son ka dawo mini da Muhsin, kuma nifa na damu na koma gida, Sayyid hankalina a tashe yake wallahi, na san iyayena sun gaji da nema na" "Asmy kar ki ƙara mini damuwa dan Allah, ina sane da komai, a tsare nake yin komai in sha Allah zai wuce" Cikin damuwa ta ce "Zai wuce yaushe? Shekera ta uku nake shirin yi a ƙasar nan, nima ina da ahali bai kamata na tare a nan ba" Ya tashi zaune cikin damuwa, ya kalle ta zai yi magana, amma bai yi ba ya ciro wayarsa da take vibrating" Da to kawai ya amsa ya tashi ya fita. Nana ta koma ta nemi guri ta zauna cikin damuwa. Da sallama ya shiga ɗakin, ya tarar da Asal ga Sultan, ga Matawalle ga Tafawa da Sardauna sai Gimbiya Bilkisu da take ta ƙoƙarin rarrashin Asal. Gefe ga Imam Asadullahi ga kuma Imam Zahradeen rungume da Muhsin. Asal ji take kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu ganin Muhsin, dan babu abin da ya banbanta shi da Hammad. Yayi mamakin yaushe aka yi masa wannan gangamin har haka? Bayan bai jima da barin gidan Imam Zahradeen ba ya tsaya a gurin Mahmoudu. Sardauna ya ce "Ka je ka zo da babar yaron nan" Babu kara ya karɓi ɗansa a hannun Yayansa Imam Zahradeen, ya tafi inda Nana take. Ya kai mintuna sha biyar, sannan suka dawo tare. Nana suka yi ido huɗu da Asal da idonta ya kumbura, Nana ta sakar mata murmushi ta kawar da kanta gefe. Guri ya tsit sai Muhsin da yake ta hawa jikin Nana yana yi mata surutunsa na yara.

Zahradeen ya ce "Imam Muhsin, ka yi shiru"

Sardauna ya yi murmushi ya ce "Har ya zama Imam shi ma?"

Zahradeen ya ce "Eh mana Allah ya taimake ka. Ɗan Imam ai Imam ne" Suka yi murmushi.

Tafawa ya ce "Yakamata mu yi abin da ya tara mu, ba tare da ɓata lokaci ba."

Sardauna ya ce "Haka ne kam, Imam Hammad" Hammad ya ɗaga kai ya kalli Sardauna. "Duk da mun san aurenka da ita wannan 'yar Nigeria, ƙaddara ne daga Allah, Amma ina fatan ka sanar da ita matar taka, sharaɗin ƙasar Agadez na rashin auren bare?". Gaban Hammad ya faɗi, Nana kuma ta kalle shi suka yi ido huɗu. Sardauna ya dubi Nana ya ce "Ina fatan ya yi miki bayani?" Nana cikin girmamawa ta ce "Eh ranka ya daɗe. Ya yi mini na sani" Sororo ya bi Nana da kallo. Tafawa ya yi caraf da zancen, ganin ana neman a ɓata masa lokaci. "Amm dama na nemi a yi wannan zaman ne, domin na san mene ne makomar 'yata, sannan wane hukunci za a ɗauka a kan Hammad, bisa karya dokar Agadez" Hammad ya numfasa ya ce "Ai ni ba ni da wata matsala da Asal, ban sake ta ban kuma yi wani abu da...

"Kai dalla rufe wa mutane baki, ai na san baka saketan ba, amma mene ne matsayinta? Zaka zauna da ita ne? Ka saki waccan yarinyar ko kuma mene ne?" Hammad ya tsuke fuska ya yi shiru. Matawalle ya ce "Amma mai girma Tafawa, bai kamata a je ga wannan maganar ba. Kana neman sanin matsayar Asal ne?" Tafawa ya ce "Ka bari mu yi magana da shi ka daina saka mini baki" Hammad ya ce "Makomar aurena da Asal, yana daga gare ta, idan tana son zama da ni, ba wani abu dama ni ban ce ba zan rayu da ita ba. Amma ina mai neman afuwarku ina shirye na ɗauki duk wani hukunci da za ku yi mini, amma sau ɗaya a rayuwata, nima ina neman ku yi mini alfarmar nan, ba zan iya sakin Nana ba, mussaman da rabo ya shiga tsakanina da ita. Ba zan iya sakinta ba". Sak suka yi su na bin Hammad da kallo. Sultan ya numfasa ya ce "Hammad, ba kai ka ke da ikon yanke wannan hukuncin ba, sai abin da muka yanke maka. Mai girma Tafawa muna mai baka haƙuri, Hammad ya tabattar da cewa aurensu yana nan daram, dan haka yakamata ta kwantar da hankalinta." "Babu batun kwanciyar hankali a nan, sai zuwa yaushe zamu san matsayarta, yarinyata tana wuni ta kwana babu bacci. Kuma da haka ku ke shashantar da duk wani laifi da zai aikata ba tare da an hukunta shi ba. A wannan karon dole a bar doka ta yi aiki a kansa, kuma a zartar da duk wani hukunci da yakamata a kansa. Ya saki matar nan a yanzu ya bata ɗanta ta tafi inda ta fito shi kuma a hukunta shi" Hammad ya girgiza kai ya ce "Zan karɓi kowane irin hukunci, amma ba zan rama sharri da alkhairi ba" Asal ta rushe da kuka tana rirriƙe Gimbiya Bilkisu. 95 1k ne via 0069685771 Aisha Adam stanbic 08081012143

Tafawa a fusace ya ce "Kun gani ko? Abin har ya kai raini ya shiga tsakaninmu ya faɗi duk abin da ya ga dama. Kamar yaya ba za ka rama sharri da alkhairi ba, waye ya yi maka sharrin waye ya yi maka alkhairin?. Ya yi wa dokokinmu karan tsaye. Kuma dolensa ya yi murabus a gaban majalissa, a ba wa wani tun da ga taka mana doka, ga kuma rashin zobensa sannan wannan ɗan da yake tutiya da shi, babu wanda yake da yaƙinin na halal ne tun da babu waliyyinsa ko ɗaya a lokacin da aka ɗaura auren." "Zan jura komai amma ni ba mutumin banza ba ne ba, kuma kar ka sheganta mini ɗa, ban san da wace kalmar za a yi mana bayanin halin da na shiga har na auri Nana ka yarda ba. Tsawon shekaru ina yi muku biyayya, ko ina so ko ba na so, dokar Agadez ba dokar Allah ba ce ku bari na samu nutsuwar zuciya mana, idan ba so ku ke ku wayi gari ku ga na bar muku duniyar ba. Ta yaya zan yi wa Allah butulci akan abin da nake nema? Yarinyar da ta rayu da ni a lokaci mafi tsananin da babu wanda zai iya zama da ni ina hauka, na haɗu da larurar da hatta najasata ita take gyara mini da hannunta ba tare da ƙyama ta ba. Babu biyayya ga abokin halitta gurin saɓawa mahalicci, Asal na da zaɓin zama da ni ko ta ƙi na bata wannan damar, amma ba zan saki Nana ba ko zaku rataye ni" Sultan ya miƙe tsaye a fusace ya ce "Hammad!" Imam Zahradeen ya miƙe tsaye shi ma, ya dubi Sultan ya ce "Ya kai Abbanmu abin alfaharinmu, a duniya ba na tunanin ka taɓa son wani abu kamar yadda ka ke son Imam Hammad, kuma bana tunanin akwai wani wanda yake yi maka biyayyar da yake yi maka. Tun da ta kai shi ga yin sa in sa da ku, to tabbas ya kai bango. Amma ko sau ɗaya yakamata a ce mai girma Tafawa ya yi maka kara a kan Imam Hammad, amma duk lokacin da wani abu ya faru tsakaninsa da Asal, ƙarara yake goyon bayanta a turasasawa Hammad yin abu dan faranta mata, sau ɗaya ko dan saboda shi yakamata a yi wa dokar Agadez kwaskwarima. Gimbiya Bilkisu ta ce "Zahradeen kana da hankali kuwa? Waye ya sanya da kai?" "Ummi ki yi haƙuri, kina duba mafitar ɗan uwanki da 'yarsa, nima ta nawa ɗan uwan nake dubawa."

"Ni ka ke gaya wa haka Zahradeen?"

"Ina neman afuwarki, amma dan Allah kar ki yi mini mummunar fahimta Ummi."

A fusace Sardauna ya ce "Ya isa haka, ya isa, kun manta a gaban wa ku ke ne? Ya za a yi kowa ya din ga magana yadda ya ga dama, babu ɗaa da girmamawa?" Kowa ya yi shiru. Nana cikin ladabi ta ce "Ina mai neman afuwarku, na san wannan hatsaniyar ta faru ne duk a dalilina. Amma da na san wannan al'amari zai faru, ko haka dokar ƙasar nan take, ba zan yi gangancin auren Sayyid ba. 'yan uwansa ba su yi mini wannan bayanin ba. Haka zalika ban faɗi haka dan a ga laifinsu ba, kamar yadda suka gaya mini shi ya nemi a biya sadakina ya aure ni. Amma kamar yadda wannan shugaban ya faɗa" Ta yi maganar tana kallon Tafawa. "Na amince zan ɗauki ɗana na koma Nigeria, idan ma kun ce ba ku da alaƙa da shi, na yarda zan zame masa uwa na zame masa uba.." "Babu inda za ki je mini da ɗa, kuma kema babu inda za ki je" Ya katse Nana yana maganar cikin ɗaga murya. Cikin kuka Nana ta ce "Sayyid babu abin da ya fi ahali daɗi da muhimmanci, sai da na baro nawa na fito nemanka na gane hakan, ni na baro nawa ahalin kai ga ka cikin gata, sun baibaye ka da soyayya da ƙauna. Dama gudun rasa ahalin ga Muhsin ne ya sanya na fito nemanka da tsohon cikinsa." Ta saka hannu a hijjabinta ta ciro zoben da ya bata ta ce "Wannan zoben ina kyautata zaton shi ne zoben da ake ta magana a kansa, tun mu na Nigeria Sayyid ya bani shi kyauta, domin jaddada soyayyarsa a gare ni. Muhsin kai wa Abbanka zobensa, kuma ina fatan ba za a ƙwace kujerarsa ta shugabanci ba, sanyin halinsa zai zamo ƙwarin gwiwa ga talakawan da ba su da ƙarfi. Na gode matuƙa da kulawa amma kar ku raba ni da ɗana dan Allah" Kuka Nana take yi sosai da sosai. Imam Zahradeen ya dubi Nana ya ce "Ɗauki yaronki ki koma, za a neme ki" Nana ta durƙusa ta ɗauki Hammad da ya riƙe zoben da Nana ta ba shi yana zura wa a baki. Ta karɓi zoben za ta ajiyewa Hammad shi, amma ya haɗa ya karɓe Muhsin. Asal kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu haka take jin yadda a gaban mutane ya nuna wa duniya ita zai iya rabuwa da ita, Nana ce ba zai rabu da ita ba.

Tafawa bai yi shiru ba ya ci gaba da zazzaga bala'i kamar zai ari baki. Har sai da ran Sultan ya ɓaci. Ya yi wa Hammad umarnin ya tashi ya tafi kawai. Yana rumgume da Hammad ya ji muryar Asal a bayansa. Ya tsaya ya waiwaya yana kallonta, tamkar mahaukaciya sabon kamu ta ce "Hammad yau nika tozarta a gaban jama'a ka zaɓi bare baƙuwar haure a kaina, ka ƙasƙanta ni a gaban mutane, Hammad ni?" Ya girgiza kai ya ce "Asal ban ƙasƙanta ki ba, kuma har abada ba zan yi ba. Kamar yadda Nana ta faɗa daga ni har ke mu na cikin ahalinmu, muna da cikakkiyar ahali ita kuma fa? Sannan kuma harshenka alƙalinka Asal. Da raina da lafiyata da ƙuruciyata ki ka kalli tsabar idona ki ka din ga jifa na da kalaman ba kya sona ba kya ƙaunata. Duk da na yi miki uzurin ƙuruciya da yarinta a wancan lokacin, amma haryanzu ina ganin wani abu a cikin idaunki da ban tantance so ne ko ƙiyayya ba. Nana ta so ni a bata san waye ni ba, ta so ni a mutum mara asali da makoma auren shahada da kasada, ta rayu da ni da na ɓacewa duniyarta ta ci gaba da bulayin nema na, ba dan tana sanya ran na saka mata ba. Ki duba ratar za ke tsakanin misalan da na baki" Ya wuce rungume da yaronsa ya tafi. A ƙarshe dai Imam Zahradeen ne ya mayar da Sultan turakarsa sai jiri yake yi saboda ɓacin rai. Ya ɗebo ruwa ya ba shi ya karɓa ya sha yana mayar da numfashi. Sultan ya ce "Zahradeen" Ya amsa da "Na'am Abbie". "Na rasa ta ina zan ɓullowa lamarin nan gaba ɗaya" Zahradeen ya numfasa ya ce "Allah ya taimake ka, da Tafawa ne a matsayin da ka ke, komai za a yi ba zai taɓa ƙin goya wa ɗansa baya ba, dan ya faranta muku ba. Ka rintse idanunka ko toshe kunnenka. Ka kamanta yarinyar nan a matsayin 'yar cikin ka. Ana maganar shekara biyu zuwa ta uku rabonta da gidansu. Ka ga dai yadda yake zare idon nan, bai ƙi ya aikata duk wani abin kunya da zai zubar da mutuncin Agadez ba. Abie shin ba ka tunanin wata aya ce Ubangiji Allah ya saukar mana, domin ya nuna mana fari da baƙi halittarsa ce kuma duk yana kishi da son abin sa? Ka lissafa Allah ya hana shi haihuwa duk da ya yi aure da ƙanan shekaru, aka hana shi ƙara aure. Lokaci ɗaya Allah ya jarabce shi da ciwon da sai da ya keta ya bar Niger ya tafi Nigeria rabon wannan ɗan ya kai shi har can. Kuma duk da haka Allah ya jarabce shi da ciwon da sai tana kusa da shi yake samun afuwa. Yanzu idan muka rintse idanu daga hukuncin da Allah ya zartar dan mutunta al'ada muka tozarta baiwarsa kana tunanin Allah zai barmu? Ka duba ɗan jaririn yaron nan da yake kai komo a tsakanin su cikin farin ciki idan aka raba su, duk gatan da za a nuna masa bai kai ya tashi a tsakanin iyayensa ba. Abie Mai girma Tafawa ɗan uwanka ne, kuma ɗan uwan mahaifiyata ne, amma ina mai tabbatar maka ba zai taɓa ƙaunarka ba, har gara ni yana yi mini kara saboda ɗan 'yar uwassa ne, amma ba zai taɓa son Hammad ba. Kai kuma Hammad ɗanka ne komai za a yi ka banƙara shi ma ya samu abin da yake so" Sultan ya yi shiru cikin nazari, ya numfasa ya kalli Imam Zahradeen ya ce "To yanzu kai me ka ke tunani, kuma meyasa ba ka yi mini duk wannan bayanin tuntuni ba?" Zahradeen ya ƙara nutsuwa ya ce "Ina tsoron shiga lamarin ne a baya, amma Hammad da kansa ya same ni da maganar, kuma ya nuna mini yarda ta hanyar ajiye ɗansa a gidana. Yanzu ka bar wani batun Tafawa da wata majalissa kai ne Sultan, idan ka yi doka dole a bi ta. Ka bar Imam Hammad da matarsa, kuma ka soke wannan al'adar da aka ba wa wannan ƙarfin, ka yi musu fatan alkhairi" Sultan ya girgiza kai cikin jimami ya ce "Ba abu ne da zai yiwu cikin sauƙi ba" "Ka duba dai Abie, ka duba makomarsu baki ɗaya" "Shikenan, ka je zan yi tunanin abin yi" Imam Zahradeen ya ce "To shikenan Abie, amma dan Allah kar ka jira sai ka yi shawara da wani a cikin 'yan majalisarka" Sultan ya ce "To shikenan" Imam Zahradeen ya miƙe tsaye, ya ce "Bari na ƙarasa gurinsu, zan karɓi Muhsin na tafi da shi" Sultan ya jinjina kai kawai.

Hammad ya shiga ɗakin da Nana take, cike da takaicin yadda ta ce, ita ta haƙura da shi, a bata ɗanta ta koma Nigeria, sai dai ya tarar da ita tana kuka. Ya kwantar da Muhsin da ya yi bacci, ya ƙarasa gabanta ya ce "Meyafaru kuma ki ke kuka?" Ta yi shiru ta ci gaba da kukan. "Mene ne?" Ya sake tambayarta. "Sayyid" Ta kira sunan shi a raunane. Ya zauna a kusa da ita ya ce "Mene ne?" Ya yi maganar yana ɗago ta cikin damuwa. Ta ƙanƙame shi tana kuka ta ce "Sayyid na faɗi haka ne dan su daina yi maka faɗa, amma ina sonka wallahi Sayyid, dan Allah kar su raba ni da kai" Ta yi maganar tana sheshsheƙar kuka. Shi ma rungumota ya yi sosai da sosai a jikinsa, yana wata irin ajiyar zuciya. Da kyar ya tattara nutsuwarsa, ya ce "Ki yi haƙuri Ma vie, Ubangijin da ya haɗa mu ne kaɗai zai raba mu. Ni da ke mutu ka raba in sha Allah" Zata yi magana suka ji ana bubbuga ƙofar ɗakin, Nana ta motsa za ta tashi, amma ya riƙe ta kuma ya yi umarnin a shigo. Imam Zahradeen ne ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo, kunya duk ta kama Nana. Ya ɗan tsaya yana kallonsu ya ce "Kuka ku ke ne?" Nana ta yi saurin tashi tana share hawayenta ta ce "A'a".

Imam Zahradeen ya ce "Ga idonki nan duk hawaye. Wai me ki ke gaya masa ne, ya sanya duk ya rikice haka a kanki" Nana ta sunkuyar da kai tana murmushi. Imam Hammad ya ce "Komai ma gaya mini take yi, shiyasa nake jin tamkar raba ni da ita, raba ni da rayuwata ne"

Zahradeen ya jinjina kai ya ce "Na ga alama ai. Amma dan Allah ku kwantar da hankalinku, ku ci gaba da addu'a, in Allah ya yarda a dalilinki za a sauya tsarin wasu dokokin na Agadez. Yanzu dai Muhsin zan ɗauka zamu tafi" Cikin marairaicewa Nana ta ce "Dan Allah ka bar mini shi a nan" Ta yi maganar tana kallon Imam Zahradeen. Ya girgiza kai ya ce "A'a barinsa a nan babu tsaro, tsawon lokacin nan yana tare da ni a can gidana, gobe in Allah ya kaimu za a kawo masa maman Mahmoudu. Idan kuma ba a yarda da ni ba, na bar ku abinku" Nana ta ce "A'a amma dan Allah ka tafi da ni, ina son na zauna tare da shi, kuma na ga Nene." "Wani irin mugun kallo Hammad ya yi mata" Zahradeen ya ce "Ai ko ba ki ce komai ba, dole za ki bar gidan nan, taso mu tafi"

Hammad ya ce "Ya haka? Ku tafi ku je ina? Kuma yaya zaka tafi da ita Sultan bai sani ba?"

Imam Zahradeen ya ce "Idan zaka biyo mu ne taso" Nana kuwa ta yinƙura ta tashi ta ɗauki jakar kayanta dama da hijjabi a jikinta.

Hammad ya miƙe ya ce "Wai bin nasa za ki yi?"

"Ni ba na son zama a nan, na gaji" Nana ta furta tana tura baki.

Imam Zahradeen ya ɗauki Muhsin, ya kalli Imam Hammad ya ce "Ɗaukko mata jakarta"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull