Buzu book 3 complete - Chapter 26
Buzu book 3 complete Chapter 26: Buzu book 3 complete Chapter 26. Zahradeen yana fita, Hammad ya riƙe ta ya ce "Dan me zaki ce za ki bi shi? Meye haka ki…
3,321 words
Zahradeen yana fita, Hammad ya riƙe ta ya ce "Dan me zaki ce za ki bi shi? Meye haka ki ke yi ne?"
"Amma Sayyid na ga yayanka ne fa"
"Ko ma wane ne, dan me za ki bi shi?"
Ta girgiza kai idanunta na cika da hawaye "Ni na gaji da zaman gurin nan? Ni gaba ɗaya ma tsoro nake ji"
Sayyid ya ce "Muje kar ki yi mini kuka" Ya saka Nana a gaba, suka bi ta baya, sai ga su a harabar gidan. Zahradeen har ya kwantar da Muhsin a cikin motar.
Hammad ya buɗe wa Nana bayan motar, sai hararta yake yi, amma ta basar ta shige cikin motar ta kawar da kai. Haka nan take jin kamar ta fito daga kurku sai wani irin farinciki take ji da nishaɗi, a haka ya bar gidan da Nana a cikin motar.
Tafawa kuwa ya ɗauki zafi, ya ci gaba da ziga 'yan majalisar Sultan a kan lallai su sanya ido a hukunta Hamma, sannan ya yi baƙin cikin fito da zoben nan da aka yi.
Matar Imam Zahradeen ita ma haka take kyakykyawar gaske, fara sol da ita, yaransu huɗu, kyawawa su ma. Sai dai Nana ta ga matar ba ta ƙyamace ta ba, ta rungume Nana tana faɗin yau ga Umman Muhsin, baƙar Gimbiya ta farko a kaf faɗin Agadez. Nana dai ta kasa sakin jiki da matar, dan duk mutanen Agadez ɗin tsoro suke bata, kusan kowa ba abin yarda ba ne. Ganin Nana ba ta sake da ita ba, ya sanya ta bar ta a ɗakin da aka sauke ta.
Washegari da sassafe Hammad ya tafi gidan Imam Zahradeen. Zahradeen ya ce ba zai gansu ba sai bayan Azahar, tun da shi ba shi da kara. Nana tare da Muhsin suka kwana, kasa baccin kirki ta yi ta rungume shi, cikin farin ciki tana shafa shi. Aka kawo mata lafiyayyen Abinci, matar Imam Zahradeen ta kawo mata kaya masu kyau, ta ce ta saka. Hammad ya din ga yi wa Imam Zahradeen magiya. Zahradeen ya ce "Ka ga ba fa magana ake ta kai shugabana ne ba, yanzu muna magana ne a matsayin ya da ƙani, dan haka dole ka jira. Sai da aka yi azahar ɗin, suka yi salla, sai ga Mahmoudu tare da Nene. Hammad suka gaisa da Nene cikin girmamawa. Sai dai shigowar su Nene babu daɗewa, sai ga Sule shi ma ya zo, tare da wani matashin saurayi. Mamaki ya kama Mahmoudu, ganin Sule ya zo gidan, sai dai ya yi ta yi wa matashin kallon sani.
Imam Zahradeen ya kalli Hammad ya ce "Ka san wannan?" Ya yi maganar yana nuna masa matashin. Ya yi shiru yana tsare shi da ido, ya ce "Na san shi, amma na manta a ina, na san dai na taɓa ganinsa"
Imam Zahradeen ya kira wayar matarsa, ya ce ta zo da Nana.
Wani irin kyau Nana ta yi, ɗinki ne na buzaye a jikinta, sai ƙamshin turare take yi ta shigo da sallama. Kasa riƙe farincikinta ta yi, ta nufi Nene da sauri. Sai dai ta yi wani irin wawan burki, bayan yin ido huɗu da matashin saurayin, da girma da kamala suka bayyana a tattare da shi bakinta na rawa ta ce "Imrana!!!"
Wata irin sufa Nana ta yi, ta nufi Imrana a gigice, ta rirriƙe rigarsa tana zaro ido, tana son tabattarwa da gaske shi take gani, ko kuma gizo yake yi mata. Cikin rikicewa ta ce "Imrana, Imrana kai ne? Imrana dan Allah mafarki nake yi ko kuma kai ne?" Ya yi murmushi ya rungume ta idanunsa na cika da hawaye ya ce "Ni ne Nana, Imrananki ne" "Imrana ka tafi ba ka sake nema na ba, ka tafi ka bar ni nikaɗai, Imrana" Toshe mata baki ya yi, a hankali jikinta ya saki ya kuma yi sanyi ƙalau. Ƙaisar ta hango a bakin teku, yana kallon ruwan, ta ƙarasa inda yake da sauri, ta ce "Ƙaisar kai ne? Ya jikin naka? Ka warke?" Ta yi maganar tana riƙo hannunsa, sai dai maimakon ta ji ta kama tsoka sai ta ji tamkar ta taɓa ƙanƙara wani irin sanyi ƙalau. Ya dube ta ya ce "Ina taya ki murna" Ta ce "Murnar me?"
Ya miƙe tsaye ya ce "Murnar komai ma, alamu sun nuna Ubangiji yana sonki, tsananin da ki ka din ga shiga, ya zame wa wasu silar alkhairi, kuma sannu a hankali Allah yana warware miki komai" Ta ɗan yi shiru ta ce "Ban fahimci me ka ke nufi ba" Ƙaisar ya ce "Ba sai kin fahimta ba. Ina taya ki murnar ganin ɗan uwanki, sai dai haryanzu da ɗan sauran rina a kaba. Shi wannan mijin naki, zuciyarsa da karsashinsa a kanki kawai yake. Amma bai damu da tsayuwa tsayin daka a kan abubuwa ba, ya kan karɓi abu duk yadda ya zo masa, ya tafi a haka komai zafi da raɗaɗin cutarwar da abin yake yi masa. Kar ki kuskura Sarkin baka ya tafi, baku bankaɗo abin da yake faruwa da shi ba, sannan Giyaz haryanzu yana tare da shi, sai dai a galabaice yake yana jinya. Kin san bamu fiye saɓa alƙawari ba, dan haka abu ne mawuyaci ya rabu da mijinki ta daɗin rai, saboda yarjejeniyar da suka yi da bokan nan. Kamar yadda na sanki, ki ci gaba da addu'a, zan iya cewa kusan komai ya zo ƙarshe, sai dai ban san abin da ka iya faruwa a gaba ba."
"Ma vie" Ya yi maganar yana shafa fuskarta, a hankali ta buɗe ido ta kalli Sayyid, ta sake ɗaga kanta, ta ganta a jikin Imran. Kuka take sosai da sosai, da ita kanta ta kasa tantance ko na mene ne. Imrana da yake share hawayen ya ce "Ki yi haƙuri ki daina kukan nan haka" "Kukan ne yake zuwa" Ta yi maganar wasu hawayen na ci gaba da zubowa. Ya kalli Muhsin da yake ta guje-guje a ɗakin, ya kalli Imam Zahradeen ya ce "Wannan ne ɗan nata?" Ya yi murmushi ya jinjina masa kai. Nana ta sake cewa "Imrana ya aka yi ka san ina nan?" Ya yi murmushi ya ce "Bacci na kwanta, kawai na farka na ganni a nan" Kukan da take yi bai hana ta yin murmushi ba. Ta ce "Nene kin ga yayana, duk duniya shi ne kaɗai wanda muke ciki ɗaya da shi" Nene ta ce "Allah sarki, ga kammanni nan ku na yi da shi" Imam Zahradeen ya ce "Yakamata a fara ba wa baƙi" Nana ta ja jikinta ta zauna, ta ƙure Imrana da ido, gaba ɗaya ya nutsu, babu wannan hauma-haumar tasa. Shi kansa Imam Hammad kallon Imam Zahradeen yake cike da mamaki yana jiran jin bayani daga bakinsa.
***** Jamila ce a durƙushe tana wani irin kakari, ji take yi tamkar barin duniyar za ta yi saboda matsananciyar azabar da take ji. Ta ɗaga kai da kyar ta kalli Mama, a galabaice ta ce "Mama, me ki ka bani a cikin kukun nan na sha, Mama zan mutu zan rasa raina"
Mama ya ce "Ai gara ki mutun na huta Jamila, gara ki tafi asirina ya rufu da wannan masifar da ki ka ɗaukko mini. Ba dai ke taurin kan tsiya ba, ai na san yadda zan yi da ke nima. Ƙwayar zubar da ciki na je na sayo a gurin Mariya Likita na zuba miki, dan ba za ki haife mini shege a gida ba". Jamila ta girgiza kai cikin matsananciyar azaba ta ce "Mama ba ki kyauta mini ba, zan iya rasa rayuwata Mama, kin san azabar da nake ji kuwa?"
"Tun da ki ka iya jure miƙawa maza jikinki, dole ki jure azabar fitar cikin"
"Wayyo Allahna" Ta faɗa a marairaice tana sake durƙushewa cikin azababben ciwo.
***** Fadila ce ta fito daga banɗain da ta shafe a ƙalla awa ɗaya da rabi a ciki, tana tufaka da warwara, sosai an matsa musu a kan su tashi su bar gidan. Har ta gaji da zuwan da wanda ya sai gidan yake yi yana ɗaga musu hankali kamar ba abokinsa ne ba. Ga shi haryanzu bai gama samun cikakkiyar lafiya ba, lallaɓawa kawai yake yi, shi kansa ya rasa inda zai sanya kansa saboda damuwa, ƙarfin hali kawai yake yi. Tana fitowa ta tarar da shi a tsaye da waya a hannunsa. Cikin damuwa ta ce "Lafiya kuwa?" A sanyaye ya ce "Coustom ne suke nema na a Lagos" Ta ɗan yi saroro ta ce "Suke neman ka kuma, lafiya dai?" Alhaji Fatuhu ya ce "Wallahi ban san mene ne ba, ga shi ko kuɗin motar tafiya ba ni da su. Allah ya sa ba wani abin ne mara daɗi ya sake tasowa ba" Fadila ta ce "Jikina ba ya bani wani mugun abin ne, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi ne ya sanya suke neman ka. Bari na kira Umma idan da kuɗi a hannunta ta ara mini"
Ya ce "A'a, kin san ba shi ne da ita ba, ba dan halin da Alhaji Zailani yake ciki na ɓatan 'yarsa ba, ai da shi zan cewa ya biya mana, ya raka ni muje mu ji ko mene ne" Ta ɗan tsuke fuska ta ce "Dan Allah Daddy ka daina gayyato mutanen nan haka, mu din ga shiru tukuna idan alkhairi ne idan Allah ya tabattar sai kowa ma ya ji. Da za a samu kuɗin sai Umman su Raudha ta raka ka. Amma hakan nan za ka yi haƙuri mu nemo kuɗi ko ta mota ne ku tafi tare. Ya hayyu ya ƙayyum Ubangiji Allah ka sanya alkhairi ne. Ya amsa da "Amin." **** Gaba ɗaya Shukura ta yi saranda da da ba zata tsira ba, daga ita har jaririnta, Yusra ta ce mata duk za ta yi ta nemi guri ta ɓuya, ba za ta iya fitar da ita da jaririn lokaci ɗaya ba, ta fuskanci mutanen nan, su na harabar inda Asibitin yake. Shukura na kuka ta ce "Yanzu tafiya za ki yi ki bar ni?" Yusra ta ce "To yaya za mu yi, idan ba haka ba daga ke har jaririn za ku iya rasa ranku, ki bari na fita da jaririn, ki san duk yadda za ki yi ki ɓuya ko ki gudu. Amma Shukura suwaye wannan suke binki haka? Kuma me ki ka yi musu?" Shukura na kuka ta ce "Dogon zance ne, ke dai tafi da shi, idan ban rayu ba ma dan Allah ki kula mini da shi" Yausra ta bata mukullin motar da ta zo da ita ta ce "Idan kin samu dama, ki gudu ni zan san yadda zan yi" ta goya jaririn Shukura na kuka, Yusra ta fice daga ɗakin.
**** Imran ya ci gaba da kallon Nana cikin zallar farin ciki da shauƙi, tare da kallon Muhsin dukkaninsu cikin shiga ta alfarma da kamala. Ya ce "Nana, ashe zan gan ki cikin farin ciki da kwanciyar hankali haka a rayuwata? Allah na gode maka da ban tursasa ki na kashe miki aure ba, ashe alkhairinki yana tattare da auren. Kasancewar daga Nana sai shi a ɗakin, ta ɗan jinjina kai ta ce "Amma an sha gwagwarmaya Imrana, duk da na gode wa Allah da ka bayyana yanzu, ka zo a gaɓar da na fi tsananin buƙatar ka, amma meyasa ka yi fushi da ni baka sake dawowa ba, dama akwai abin da zan yi maka ka yi irin wannan fushin da ni?" Ya girgiza kai ya ce "Babu shi, abin da za ki yi mini da zai sanya na guje ki. Amma ki yi haƙuri kaɗan za ki ji abin da ya faru. Na yi burin na samu wadata ki huta na gatanta ki Nana, amma Allah ya ƙaddara ke ce zan huta a dalilinki." "Ban gane ba, me ka ke nufi?"
Imrana ya ce "Za ki gane ne"
"Imrana ina Baba da su Jamila, na san ba zuwa gurin su Mama ka ke yi ba, da gurin su Ummi, ban san da wani idon zan tunkari gida ba, na tafka babban kuskure da bana tunanin za su iya yafe mini"
"To kar Allah ya sa su yafe ɗin mana, ke dai ba kin riga kin yi gaba ba, su zauna da rashin yafiyar"
Nana ta buɗe baki ta ce "Lallai hali zanen dutse, Imrana kar Allah ya sa su yafe, su Baban?"
"Eh ɗin, ai ke yakamata a ce ma sun nemi yafiyarki, idan sun yafe shikenan, idan ma ba su yafe ba za ki ci gaba da rayuwa wataƙila ma babu wanda ya neme ki a cikin su"
Hammad ya dubi Imam Zahradeen bakinsa fal tarin tambayoyi, amma yanayin fuskar Zahradeen ɗin babu alamar zai amsa masa tambayoyin nasa"
Imam Zahradeen ya ce "Ya na ga ka ƙure ni da ido ne?"
Hammad ya ce "Abubuwan da na gani suka ɗaure mini kai nake son ka yi mini bayani"
Ya numfasa ya ce "Bayani ya zama dole Hammad, amma ina fatan zaka yi mini afuwa da duk abin da za ka ji a bayanin nawa" Imam Hammad ya ce "In sha Allah" Kamar yadda suka taru a falo ɗazu, haka suka sake taruwa bayan sallar la'asar. Imam Zahradeen ya ce "Ina yi wa kowa barka da zuwa wannan gida nawa. Wasu sun san da zuwan wasu, wasu ba su zan da zuwan wasu ba. Cikinmu akwai yan gidanmu na sarauta, akwai wanda ba su da alaƙa da gidan namu, amma a yanzu tilas mun zama abu guda, kuma zan warware wani abu da na san wasu za su gan shi wani iri, amma yi haƙuri da yadda komai zai zo, duk wanda yake gurin nan abin ya shafe shi ne. Imam Hammad, wannan bawan Allah da ku ke gani Sulei yarona ne, zamanku a tare da shi, da duk wani abu da ku ke ciki, wani abu ne na shiri da na yi shi" Gaba ɗaya suka ɗaga kai suna kallon Sule tare da Imam Zahradeen. Bai damu da kallon da suke yi masa ba, ya ci gaba da cewa; wannan matashin saurayin da yake ɗan uwa ga matarka Hammad wato Imran, bayan da ya je ya same ku, ya yi yinƙurin tafiya da ƙanwarsa, hankalinka ya tashi sosai, ka kira Mahmoudu ka gaya masa, shi kuma sun yi maganar da Sulei, shi kuma Sulei ya gaya mini. Gudun kar ya kawo tangarɗa a rayuwar aurenku, ya sanya na saka aka bi diddigi aka nemo shi. Aka kawo mini shi har Agadez, na yi masa bayanin komai, da ko kai waye, da alfarmar da nake nema ya yi mini na yin shiru da bakinsa ya yi haƙuri ya bari ku rayu da ƙanwarsa, kai mutum ne mai asali da daraja, ƙaddara ce ta faɗa maka. Sai dai ya fututtuke yana ganin kamar rainin hankali ne kawai, idan kana da asali da daraja dan me zan barka a wulaƙance kana gadi. Da kyar ya fahimci abin da nake son ya fahimta, sai dai duk da haka gudun ya ƙara burkicewa saboda na ga rigimamme ne, na aika shi waje karatu. Sunansa yana cikin jerin waɗanda ka ke bawa tallafin karatu a Agadez, a cikinsu na saka shi aka kuma fitar da kuɗin dan kai ka biya masa ba ni ba. Fuskar Hammad ta yi wani irin ja, cikin kakkausar murya ya ce "Zahradeen"
"Hammad" Ya miƙe tsaye ya ce "Labarin nan bai cika ba me ka ke ɓoyewa?"
Imam Zahradeen ya yi murmushi ya ce "Wannan rigimar cikin gida ce, ka bar maganar a haka"
"Ba zan bari ba, sai ka yi mini cikakken bayani"
Mahmoudu shi kansa ɗaurewa ya yi, kenan duk wannan abin Sulei, kallon biri yake yi masa yake yi musu na ayaba, ya san komai, ya san waye Imam Hammad, amma ya zauna da su har da yi masa masifar kullum yana ɗawainiya da mutumin da bai san asalinsa ba?" Gaba ɗaya jikin Hammad ya hau tsuma, yana neman ya fita hayyacinsa. Hammad ya riƙe rigar Imam Zahradeen yana tsare shi da idanu cikin tuhuma. Zahradeen ya yi murmushi ya kalli Mahmoudu ya ce "Ni ne nake tura maka saƙon cewar kar ka dawo da Hammad Agadez, lallai ka tafi Nigeria. Kuma ni na shirya yadda aka haɗa ku da Sule har ku ka yi aikin gadi tare. Sule ni yake yi wa aiki, duk wani abu da yake faruwa, da motsinku Sule yana sanar da ni. Kuma nine nake tura maka kuɗaɗe domin kula da Hammad da iyalin da ya aura, kuma aka sanar da ni kwanciyar hankalin da yake ciki. Sai dai bayan kame ku gaba ɗaya na kasa sanin halin da yake ciki, na tura Nigeria a bincika mini, aka tabattar mini da kama ku. Na ci gaba da bibiyar inda Nana take, amma binciken nawa bai cim mata ba, tayi ɓatan dabo, ga kuma alƙawarin da na yi wa ɗan uwanta, na zan tabattar da tana cikin ƙoshin lafiya. Sai dai da Allah ya dubi zuciyata sannu a hankali, komai ya din ga warwarewa, tun kafin ka gane ta, ni na gane ta saboda har hotonta ina da shi. Kuma aka yi sara a kan gaɓa ka zo ka same ni, da maganar cewa ka yi aure a Nigeria. Sai na bika muka tafi a haka, ban nuna maka komai ba, zuwa lokacin da nake ganin ya dace ka san komai!. 96 1k ne via 0069685771 Aisha Adam stanbic 08081012143
Hammad bai iya cewa uffan ba, kawai ya tashi ya nufi hanyar fita. Imam Zahradeen kuma bai motsa daga inda yake ba, ya zuba masa ido. Nana ta tashi a rikice ta ce "Sayyid ina zaka je ne? Kar ka yi fushi, ka tsaya ka saurare shi, kar ka yi wa al'amarin wata mummunar fassara. Bai tsaya ba kawai ya yi gaba, Mahmoudu ma tashi ya yi ya bi bayansa da sauri. Wannan shi ake kira da ga ƙoshi ga kuma kwanan yunwa. Ga farincikin ganin Imrana, amma alamu sun nuna Hammad ya ɗauki zafi da abin da Yayansa ya aikata, duk da ta wani fannin taimakonsa ya yi, amma ta wani fannin abin a saka masa ayar tambaya ne.
***** Sagir kuwa kamar zai haukace, saboda tashin hankali bai fita daga tashin hankalin ɓatan Shukura ba, ga Yusra ma ya neme ta ya rasa, tun safe ana maganar sha biyu saura na dare. Ga shi layin wayarsa yana cikin wayar Yusra, haka a dole yaje police station ya kai rahoton ɓacewar Yusra. Ya fara tunanin kar a fara zarginsa da ko shi ne yake aikata wani abu, matan nasa suke ɓacewa. Ƙarfe shida na safiya, suka ji ana bugun gate, bugu na tashin hankali kamar za a ɓall gate ɗin. Afujajan mai gadi ya buɗe gate ɗin, babu tsammani yaga Yusra a tsaye kamar korarriya. Ya zaro ido yana kallon ta cikin matsanancin mamaki. Gaba ɗaya gari ma bai gama waye ba, ya kalli hannunta ya ga jariri, bai yi magana ba ta banke shi ta wuce cikin gidan. A falo ta tarar da Antynta tare da mai gidanta, saboda bugun ƙofar da suka ji ana yi. Cikin mamaki Antyn ta ce "Yusra lafiya ki ka zo gidan nan da sassafen nan haka? Daga Kanon ki ka taho Abuja" Yusra ta yi shiru ba ta yi magana ba, kallon falon Yusra ta hau yi, tana tunanin yaya aka yi ma ta zo nan. Ita dai ta san ta ɗaukko jaririn ta fito titi, tama tafiya a hankali tana waige-waige, daga nan bata sake sanin abin da ya faru ba, ta ganta a ƙofar gidan Antynta da ta koma hannunta a Abuja. Mai gidan ya ƙarasa gaban Yusra, ya karɓi jaririn da ya fara kuka a hannunta. Yusra ta nemi guri ta zauna tana mayar da numfashi. "Yusra dan waye wannan, a ina ki ka samo shi?" Mai gidanta ya ce "Rabu da ita ta huta, wannan yaron a samo madara a bashi, sannan a kira mijinta mu ji ko da saninsa ta taho, kuma me yake faruwa" Antyn ta jinjina kai cikin damuwa, da fargabar a ina Yusra ta samo ɗa.