Buzu book 3 complete - Chapter 27
Buzu book 3 complete Chapter 27: Buzu book 3 complete Chapter 27. ***** Jamila kuwa ta din ga zubar da jini babu ƙaƙƙautawa, ga azababben ciwon mara da ta…
3,139 words
***** Jamila kuwa ta din ga zubar da jini babu ƙaƙƙautawa, ga azababben ciwon mara da ta din ga yi. Ta kwana ta wuni tana wata irin burgima da kuka mai ban tausayi. Baba ne ya dawo ya tarar da Jamila a cikin wannan yanayin. Baba ya ce "Rabi wai me yake damun Jamila haka ne, wannan wane irin ciwo ne tun jiya?" Mama ta ce "Ba fa wani abin ba ne ba, al'ada ce ta zo mata take shan wahala." "Haba, wahalar ta isa haka, wane irin ciwo ne haka, anya ba za a kaita Asibiti ba" Mama ta ce "Ba sai an kai ta ba, na bata magani za ta warke" Baba dai bai ji ya gamsu ba, amma ya ƙyale su kafin ta hayayyaƙo masa da masifa.
***** Asal duk ta fita hayyacinta, kullum cikin kuka, ta yi wata irin muguwar rama. Tana zaune a ɗakinta, Tafawa ya shigo ɗakin, ta ɗaga kai ta kalle shi. Ya ce "Dalilin me ne ne ya sanya ba kya cin abinci?" Ta yi shiru ba ta ce masa komai ba. "Kar ki saka damuwar abin da yake faruwar nan a cikin zuciyarki, duk yadda zan yi dole sai na tabattar da an hukunta Hammad, ba zai ci bulus ba abin da ya aikata." Asal ta yi shiru, wani irin baƙin ciki na taso mata a zuciyarta, ta din ga tuna yadda mahaifin nata ya din ga ingizata da tursasa ta aikata Wasu abubuwan. Ya yi wa rayuwarta illa duk a ƙoƙarin sa na ganin ya cimma wani burinsa da abu ne mai wahala ya samu cikarsa. Yana magana amma ta lula Duniyar tunani, ta tuna lokacin da aka kusa auren, ya kawo mata wani abu a ƙoƙo ya ce ta sha, sai bayan da ta sha sannan ya ce bai aura mata Hammad dan taje ta haihu da shi ba, domin har abada baya fatan ya haihu balle ya sanya ran samun magaji ya ƙara dagula masa lissafi gurin cim ma burinsa. Wasu irin zafafan hawaye suka zubo wa Asal, ta daɗe da gane rashin haihuwarta na da nasaba da wannan magani da mahaifinta ya bata, duk da a ɓoye ta je ganin likita a kan matsalar rashin haihuwar, aka ce mata hakan yana da alaƙa da ta'amalli da chemicals masu ƙarfi da ta yi. Da fari ta yi tunanin shaye-shaye da take yi, sai dai ko da shaye-shaye ta fi kyautata zaton maganin da Tafawa ya bata ne sila.
Nana ta samu ta sake sosai da sosai da Imran ta din ga bashi labarin abubuwan da suka faru bayan tafiyarsa, wasu guraren sai da ya yi hawaye. Haka kuma ya din ga yi wa Nene addu'a, a kan abin da ta yi wa Nana na taimako. Nene ta ce "Babu komai, ɗa na kowa ne. Kuma in sha Allah Nana daram zata zauna a ɗakin mijinta"
Nana ta kalli Imrana ta ce "Imrana tsoro nake ji, ban san yaya su Baba za su kalle ni ba, ban san me zan ce musu ba, ga shu kai ma tun da ka tafi ba ka je gidan ba?"
Imrana ya ce "Ba za ki daina wannan zancen ba, ba abin da za su yi miki. Nima ban je ɗin ba"
Nene ta ce "Ai dole mu kafa mu tsare, daga nan Agadez a tashi tawaga, su je har gida a bawa iyayenku haƙuri, kaga yanzu kai ne waliyyinta, a tashi manya daga Agadez su je har Nigeria su ba wa iyayenku haƙuri a kan abin da ya faru, sannan kuma a yi. Sannan ya zama dole a yi wa Nana duk wani abu na dukiyar aure, a yi cikakken biki na 'yar gata duniya ta shaida auren yadda yakamata, dan gudun kar ma a zo a samu wata matsala a nan gaba." Imarana ya ce "Wannan gaskiya ne, amma kina ganin za su amince da hakan?" Nene ta ce "Dole za su amince, ko dan son da suke yi wa ɗan su. Tun da ɗansu yana son iyalinsa."
Hammad kuwa gidansa ya koma, sai dai ya rasa abin da yake yi masa daɗi, ya din ga juyi yana tunani, tare da tambayar kansa, kenan duk abin da yake faruwa da sanin Zahradeen. Kasa jurewa ya yi ya tashi ya tafi gurin Sultan. Yana zaune Gimbiya Bilkisu ta sanya shi a gaba, tana ta maganganu a kan kar ya nuna son kai akan hukuncin da zai yanke, kuma ya duba Asal ita ma a yi mata adalci. Babu tsammani sai ga Hammad ya shigo, yanayin yadda fuskarsa ta yi jawur, ya sanya Sultan miƙewa yana tambayarsa ko lafiya? Amma Hammad ya yi shiru bai ce komai ba. Sultan ya kama hannunsa ya shiga da shi cikin ɗakinsa, ya zaunar da shi ya ce "Ka gaya mini mene ne?" Sai gumi da yake ta tsatstsafo masa amma bai yi magana ba. Mahmoudu kuwa daga fitowar Hammad ya biyo bayansa, ya neme shi ya rasa, yana son su yi magana, ya lallaɓa shi su bi abin a sannu su fahimci Zahradeen, dan ya ga alamar ya ɗau zafi lamarin ya ɗaure masa kai. Matar Imam Zahradeen ta yi sallama, suka amsa. Ta kalli Nana cikin sakin fuska ta ce "Gimbiyar Imam Hammad, Imam Zahradeen yana kira" Nana ta yi murmushi ta ce "Nana dai za ki ce" "Ina, wa ya isa faɗar sunan Gimbiya" Nana ta yinƙura ta tashi ta bi bayanta. Bayan sun shiga, matar Zahradeen ta koma, Nana ta zauna a ƙasan Carfet.
Ya ce "Kin ga mijinki ya ɗauki zafi, yaƙi tsayawa ya saurare ni, balle ya fahimce ni, amma na ga ke kina cikin nutsuwarki, za ki fi fahimtata. Amma kafin nan kin ga ke ki ka zauna da shi, ko za ki iya gaya mini abin da ki ka sani, bayan haɗuwarku lokacin yana cikin rashin lafiya?" Ta jinjina masa kai, sannan ta yi masa bayanin, abin da take ganin ya dace ta gaya masa. Ya ce "Shikenan, Sultan ya kira ni a waya, ya ce yana nema na, na san wataƙila ya gaya masa ne, tare da ke za mu je gobe in Allah ya kaimu da safe" Nana ta amsa masa da "To"
***** Hajiya Halima ta kiɗime, tun bayan da Sagir ya kira wayarta yake tambayarta, ko Yusra ta je gidan. Har ta fara shirin tafiya Kano, Yayar Baban Yusra ta kira ta a waya, ta sanar mata ga Yusra ta zo tun ƙarfe shida na safiya tare da wani jariri da ba su san a ina ta samo shi ba. A kiɗime Hajiya Halima suka shirya, suka tafi gidan Antyn, su na zuwa suka tarar da ita cikin yanayin ɗimuwa, ba ta magana ga kuma wani ƙosashshen jariri da ba a san inda ta samo shi ba.
Hajiya Halima ta ce "Ai ni mijinta ya kira ni cikin tashin hankali, yake tambayata wai ko Yusra ta zo, ya neme ta ya rasa. Hankalina a tashe na fara shirin tafiya Kano, kin san uwargidanta fa ita ma an neme ta an rasa.
"Mami" Yausra ta faɗa da ƙarfi. "Na'am Yusra, sannu" "Ku gaya wa Daddyn Haidar yaje ya ɗaukko Shukura, za su kuma sace ta" Cikin rashin fahimta ta ce "Suwaye?" "Nima ban san su ba, amma sace ta za su yi, na baro ta a can" Duk yadda suka yi da Yusra ta yi musu bayanin yadda za su gane, ta kasa sai kukan aje a ɗaukko Shukura kar a kuma sace ta. Hajiya Halima ta kira Sagir da lambar da ya kira ta, ta sanar masa ga Yusra a Abuja tare da wani jariri da ba su san a inda a ta samo shi ba. Cikin kiɗima da tashin hankali, ya ɗauki mota ba tare da ya gaya wa kowa ba, ya kama hanyar Abuja.
***** Bayan su Nana sun hallara a gaban Sultan, ta yi tozali da Giyaz a tsaye da sandarsa a bayan Hammad, sai da jikinsa duk rauni ya ƙara tsufa ya yi wani iri. Jikinsa sai hayaƙi yake yi ya zubo mata ido. Sultan ya dubi Imam Zahradeen ya ce "Zahradeen me ka yi wa ɗan uwanka ne, ya ƙi magana, sunanka kawai ya furta ya yi shiru, a nan muka kwana tare da shi, ko sau ɗaya bai yi magana ba. Imam Zahradeen ya haɗiye wani abu mai ɗaci a wuyansa, yana tunanin ta ina zai fara bayani. Nana ta ce "A je a zo da Sarkin baka gurin nan, idan ba haka ba Giyaz zai iya haddasa matsala" Duk suka kalli Nana Imam Zahradeen ya ce "Waye hakan?" "Ku zo da shi dan Allah, kar a samu matsala wani abin yake son aikatawa" Ganin Nana na neman burkicewa, ya sanya Sultan ɗaukko wayarsa ya ɗan daddana, Hammad dai bai ce komai ba.
Imam Zahradeen ya ce "Kafin na ce komai, ina mai neman afuwarku a kan abin da zan faɗa, kuma ina neman afuwa da ni da waɗanda zan faɗa a cikin maganata. Na ji daɗi sosai da sosai da ka neme mu a keɓantaccen guri kamar haka, ina roƙon ku rufa mana wannan asirin dan Allah" Sultan ya ce "Zahradeen, ka tafi kai tsaye ka yi mini bayani, kana ta zagaye-zagaye daga mu sai mu a gurin nan" Ya ƙarasa maganar yana kallon wayarsa, ya danna ya ce "Ku ba shi dama, shikaɗai ya shigo" Sarkin baka ya shigo da sallama, ya risuna a gaban Sultan ya kwashi gaisuwa, ya juya ya gaida Imam Zahradeen, amma ya yi shiru yana kallon Imam Hammad da kuma Nana. Sultan ya ce "Ga mai maganin an kira shi, ya aka yi?" Sarkin baka ya ce "Uwar gijiyata, meyafaru da Giyaz ne?" "Ƙaisar ya ce mini faɗa suka yi." Ta mayar da idonta kan Sultan ta ce "Allah ya baka nasara, ya ci gaba da maganar a gaban Sarkin baka, shi ma amintacce ne, idan ya fita Giyaz zai iya aikata masa wani abin"
Sultan ya ce "Waye Giyaz ɗin ne?"
Sarkin baka ya ce "Aljanin da aka yi masa asiri da shi ne ranka ya daɗe"
Imam Zahradeen ya fara magana ya ce "Tabbas na san ni mai laifi ne, kuma duk hukuncin da za a yanke mini zan karɓa"
Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Mahaifiyata, Gimbiya Bilkisu, sun haɗa baki da ɗan uwanta, mai girma Tafawa, suka yi masa sihiri, aka haɗa shi da aljanin da zai bar garin da shi gaba ɗaya. Wallahi ban san sun yi ba, sai daga baya take gaya mini, saboda su na son ko ni ko Asadullah wani ya gaji kujerar Hammad. Na nuna mata rashin jin daɗina, ta ce mini aikin gama ya riga ya gama, muddin Hammad ya dawo Agadez sai ya haukace, ko ma ya rasa rayuwarsa. Shi ne na ɓoye lamba, na nemi Mahmoudu, a lokacin bai riga ya bar ƙasar ba, abin dai ya fara taɓa shi ne. Yanzun ma ba ni da yadda zan yi ne, amma ban so na tona wa mahaifiyata asiri ba" Hammad ya sunkuyar da kai hawaye na zuba daga idanunsa, Sultan ya rikice cikin tashin hankali da damuwa ya ce "Yanzu Zahradeen amma ka ɓoye mini wannan abin baka gaya mini ba? Yanzu ƙiyayyar da mahaifiyarka take yi wa Hammad har ya kai ga ta nemi ta zauta mini ɗa ya bar gida?"
Zahradeen yana kuka ya ce "Dan Allah ka yi haƙuri Abie, ban san komai a kai ba, sai daga baya. Kuma gudun kar idan ya dawo ya samu matsala, shiyasa na ce kar ya dawo Niger"
Nana ta ce "Gidan tarihi, a gidan tarihin Agadez aka yi masa sihirin, kuma ba sihiri ɗaya ba ne, mutane daban-daban sun yi masa. Ranar da muka je cikin gidan tarihin tare da shi, na ji ƙamshin turaren Gimbiya Bilkisu a gurin. Sannan bayan ƙamshin turaren ta, na ji ƙamshin turaren wani ma. Gaba ɗaya suka ɗaga kai, su na kallon Nana. "Duk wanda yake ƙamshin nan, da alama yana ziyartar gurin, kuma wanda yake yi musu aikin sihirin a cikin gidan tarihin yake. Idan gidan tarihin nan babu kowa a cikin sa, to wannan mai gadin ne bokan da yake aikin, ko kuma ya san bokan da yake yi.
A rikice Sultan ya ce "Wane gidan tarihin wai, waye mai gadin?" Sai kuma ya rufe bakinsa, suka dubi Hammad a rikice, yadda ya runtse idanunsa yana zubar da hawaye. Nana ta rikice ta tashi ta nufe shi, Sarkin baka ya ce "Kar ki taɓa shi, Giyaz ne yake zungurarsa, zai iya yi miki wani abin ya cutar da ke" Ya tafi gaban Hammad, ya kama goshinsa ya din ga karanta Bismillah da suratul Fatiha, yana tofa masa a tsakiyar kansa. Daga bisani ya ɗaga rigarsa ya ciro jakar nan da ya bawa Nana, ya ce "Idan baka tafi ka ƙyale shi ba, zan illataka da jakar nan kamar yadda Ƙaisar ya yi maka" Nana rikicewa ta yi, duk da ba yau ta saba ganin abin mamaki ba, jakar da take hannunta, ta neme ta ta rasa, ta ganta a gurin Ƙaisar, yanzu kuma ta koma hannun mai ita Sarkin baka. Ya kalli Nana ya ce "A gurin ƙamshin turaren wa ki ke ji?" Nana ta yi shiru tana satar kallon Sultan, tana kuma kallon Zahradeen. "Kar ki ji tsoron kowa, gaya mini" Ta ƙi magana tana jinjina yadda za su ɗauki abin. Ya ce "Muje ki nuna mini gurin, ai babu abin da zai gagara da ƙarfin ikon Allah" Sultan ya tashi a rikice jikinsa yana tsuma, idanunsa sun yi jawur saboda ya kaɗu da abubuwan da suka fito daga bakin Imam Zahradeen. Wani irin mugun tausayin Hammad ya mamaye masa zuciya. Ya kalli su Nana ya ce "Yanzu can gidan tarihin za mu je kenan?" N Sarkin baka ya ce "Eh Allah ya baka yawan rai" Imam Zahradeen ya ce "Ko a yi wa su Matawalle magana, a tafi da wani daga cikin su, ko hadimai"
"Bana buƙata" Sultan ya faɗa fuskarsa babu annuri, ba tare da ya kalli inda Imam Zahradeen yake ba.
Ya dubi Hammad da ya buɗe idanunsa, sai dai baya magana, dan tun da ya zo wa Sultan ya ce masa Zahradeen ne, bai sake yin magana ba. Ya shafa kansa ya ce "Hammad, ka na ji na?" Ya jinjina kai. "Ko zaka bi mu ne?" Ya girgiza kai. "Ka na nan mu je mu dawo?" Ya ɗaga masa kai alamar eh. Ya girgiza kai ya ce "Ina Mahmoudu ne, ban ganku tare da shi ba, a nemo shi ya zo ya zauna da shi tukuna sai mu tafi" Imam Zahradeen ya tafi ciro wayarsa, ya hau laluben lambar Mahmoudu. Sultan da ya kalli Imam Zahradeen sai ya ji ransa ya ɓaci, ya yi mamaki ya kaɗu matuƙa da jin abin da Gimbiya Bilkisu ta yi wa Hammad. Ga abubuwan da Tafawa ya din ga yi masa, da tursasa shi a kan yi masa abubuwan da yake so, da shi da 'yarsa amma hakan bai ishe su ba, suka nemi a ɓatar masa da ɗansa. Sai da Mahmoudu ya zo, Imam Zahradeen ya ce "Imam Hammad ba ya jin daɗi ne, ka zauna tare da shi, zamu je mu dawo" Tiryan-tiryan suka bi ta ɗakin da su Nana suke zaune, suka buɗe wannan ƙofar kamar yadda Nana ta yi musu bayanin ta nan suka bi, suka gangara har gidan tarihin. Mai gadin na ganin Sultan, jikinsa ya hau tsuma ya zube a ƙasa tamkar zai yi masa sujuda yana kwasar gaisuwa. Sai dai gaba ɗaya ya rikice da ganin Sarkin baka. Ko da suka shiga cikin gurin, kawai Sarkin baka ya bushe da dariya, duk suka tsaya suna kallonsa. Ya tsaya yana ƙare wa gurin kallo, yadda aka rarake dutse aka gina wannan gurin, mutanen zamanin da suka yi wannan aikin sun cancanci yabo. Sarkin baka ya sake bushewa da dariya ya ce "Sarki a dawa Sarki a gida, Ni mai Duna ni mai Salamatu, ni mai Mairo 'yar Fulani. Ni ake yi wa inkiya biyu, Garba ga Baka ga Aska, na yi gadon gidanmu, na ƙwaci wanda ban gada ba, na fi 'yan na gada iyawa. Ni Abubakar Garba mai taƙama da ikon Allah. Na ga mutum na ga Aljan, na ga cuta na bada maganinta, idan babu na ce ba ruwan Garba. Ya buga ƙafarsa ɗaya ya ce "Uwar gijiyata, ƙamshin turaren wa ki ka ce kina ji?" Nana ta sake kallon su Sultan, Sarkin Baka ya ce "Faɗi kanki tsaye, ba wanda zai yi miki abin da Allah bai yi miki ba" Ta ɗan sunkuyar da kai ta ce "Akwai wani Imam Omar, wanda ya kawo wa Imam Hammad ayaba tare da Yayan Asal" "Ƙamshin turarensa ne?" Imam Zahradeen ya tambaye ta cikin zaƙuwa. Ta ce "Ni tsoron faɗa nake, ba na son haɗa husuma ne"
Sultan ya sassauta murya ya ce "Ki na ji na? Ba haɗa husuma ba ne ba, mijinki za ki taimaka tun da ke Allah ya yarje miki gano wasu abubuwan da mu ba mu gano ba"
Bakinta na rawa ta ce "Wannan mai kama shi ɗin, da ku ke yawan zama ku uku, mai saka shuɗin rawani, bayan ƙamshin turaren Gimbiya Bilkisu, ranar da muka zo nan, ƙamshin turarensa ne yake tashi, alamar bai daɗe da tafiya ba" A rikice Imam Zahradeen ya ce "Sardaunan Agadez, ƙamshin turarensa ne" Buɗe baki Sultan ya yi, ya fara numfarfashi yana kallon Nana, ya ce "Me hakan yake nufi? Ina fatan ba dai wani abin ya yi ba?" Nana ta girgiza kai cikin tsoro ta ce "Ba ni da tabbas, tun da kowa yana da damae zuwa gurin nan, mussaman a cikin manyan Agadez kamar yadda Imam Hammad ya gaya mini. Amma me zai kawo shi nan cikin dare wajen ƙarfe sha biyu na dare. Kuma a mudubin Ƙaisar na ga wani abu da ya sanya ban ji na yarda da ɗakin can ba, amma ba ni da tabbas tun da maganar aljani ba abar yadda ba ce ba wasu lokutan" Sarkin baka kawai ya nufi ƙofar ɗakin, da Nana ta yi ta nacin a buɗe ta, yana zuwa ya jijjiga ƙofar, amma ya ga ƙaton mukulli a jiki. A nutse ya ƙare wa sauran ƙofofin kallo, ya saki mukullin ya nufi hanyar fita, yana zuwa ya janyo mai gadin nan har zuwa inda su Sultan suke. Ya kalle shi ido cikin ido Sarkin baka ya ce "Waye kai?"
"Mai gadin gidan tarihin Agadez" Ya ba shi amsa.
Sarkin baka ya ce "Kai, mugu shi ya san makwantar mugu. Kai da gani idanun nan nawa ka san babu abin da ban gani ba. Waye da waye suke zuwa gurin nan?"
Mai gadin ya yi wa Sarkin baka wani irin kallo, ya ce "Kowa ma yana iya zuwa"
"Ba kowan ba, muhimman mutanen da ka ke yi wa aiki"
"Ni ba ni da wani aiki bayan buɗewa da rufewa, da kula da ababen tarihi"
"Ka tabattar?"
Ya ce "Eh"