Buzu book 3 complete - Chapter 29
Buzu book 3 complete Chapter 29: Buzu book 3 complete Chapter 29. Cikin nutsuwarsa ya kalle ta ya ce "To shi ne me? Ai gara abin kunyar sauke shi daga…
3,212 words
Cikin nutsuwarsa ya kalle ta ya ce "To shi ne me? Ai gara abin kunyar sauke shi daga Sultan, a kan tona muku asiri da ke da shi da ɗan uwanki Tafawa" Ya ƙarasa maganar cikin hasala. Sak ta yi tana ƙwalalo ido waje tana kallonsa. "Kar ki kalle ni kamar ba ki san abin da ki ka aikata ba, Bilkisu kin cutar da ni, kuma kin cutar da kanki. Kin yi yinƙurin kashe mini mata sau biyu, saboda gudun tonuwar asirinku, yayanki ya yi uwa ya yi makarɓiya ya sanya muka rufe Mamman, waya sani ko a ƙarshe ma ke dai ki ka yi sanadin rayuwar tata? Sannan tilon ɗan da ta bari a duniya ki ka sako a gaba da jaraba, ke kina yi yayanki yana yi, gaba ɗaya Hammad bai ji daɗin rayuwarsa ba, saboda azaba da masifar sihiri da makircinki. Kuma idan ki ka kuskura ki ka buɗe baki ki ka musa mini, sai na tona miki asiri sannan ki bar mini gida. Allah ne ya tona muku asiri a silar matarsa ta Nigeria da ya aura, kuma bokan naku yana hannunmu, ya tabattar da abin da ya aikata. Abu ɗaya zan duba na rabu da ke, 'ya'yan da na haifa tare da ke. Amma daga yau na haramtawa kaina ke har abada a matsayin matata, za ki yi zaman 'ya'yanki ne kawai. Kuma kar Zahradeen ya ƙara ayyana ni a matsayin mahaifinsa, kuma kar ya sake zuwa inda nake. Da ke da duk wanda ku ka aikata hakan, na bar ku da Allah. Faɗar abin da ku ka aikata tamkar tona wa zuriyarmu asiri ne"
A rikice ta ce "Dan Allah Jalaludeen ka tsaya ka ji...
"Ba zan ji komai ba, fice ki bani guri kafin na canza shawara" Yayi maganar yana yi mata wata irin gigitacciyar tsawa, babu shiri ta fice tana haɗa hanya. Tafawa ne ya shigo falon hankali a tashe, ya tarar da Asal tare da Asadullah. A fusace ya ce "Gidan uban wa ku ka tafi tun safe?" Da mamaki Asad ya ce "Kai ka kira ni a waya ai, ka ce na zo na kai Asal Asibiti, tun lokacin muna Asibiti, ba ta da lafiya sosai. Ya sharce gumin goshinsa ya ce "To, dara ta ci gida yau, Asirinmu ya tonu a fada" Gaba ɗaya suka ɗaga kai suka kalle shi.
"Eh, yau da bokan da yake yi mana aiki, na gidan tarihi aka zo fada, ya tona komai sunayenmu ne kawai bai kama ba. Kuma na san ya gaya wa Sultan komai, kuma duk a dalilin haukanki da dabbancinki Asal, haka kurum ki ka je ki ka jajubo masifa ki ka kawo ta har cikin gidan sarauta. Binciken da na yi, wannan yarinyar da ki ka kawo a matsayin kuku, ita ce ɗin dai ta yi sanadin tona asirinmu. Dan haka sai ku shirya baki ɗayanku, dan ban san wane irin hukunci za a ɗauka a kanmu ba.
Asal ta ɗora hannu a ka ta ce "Wayyo Allah na shiga uku, Abbu sai da na ce muku mu daina wannan abin, amma kai ka saka ni, Imam Asad ya saka ni, Imam Omar ma ya saka ni da Sardauna, ku ka saka ni a tsakiya wallahi ina son Hammad, idan na rabu da shi ba zan taɓa samun miji kamarsa ba, wallahi ina sonsa"
A fusace Asadullah ya ce "Ke rufe wa mutane baki, ke ta wani shashasha ma ki ke yi?"
"Kai ne shashasha, dan duk saboda gobenka aka lalata tawa, an cuce ni, komai zan yi yanzu Hammad ba zai taɓa yafe mini ba, balle ya saurare ni"
Tafawa ya dubi Asal ya ce "Asal kina da hankali kuwa? Kin san abin da ki ke faɗa kuwa?"
"Abbu na san abin da nake faɗa, shikenan bani da makoma, matarsa ta shiga kundin tarihin baƙar mace ta farko da ta auri Imam a Agadez, ni kuma zan shiga kundin tarihin matar da ta sanya hannun gurin tarwatsa rayuwar mijinta" Miƙewa tayi Tafawa yana kiranta, amma ko waiwayowa ba ta yi ba, ta fice daga ɗakin.
**** Alhaji Fatuhu ne ya yi sallama a falonsa, ga mamaki ya ga Fadila tare da uwargidansa Hajiya Suwaiba, suna zaune abin da bai taɓa gani ba. Suna ganin shi suka zuba masa ido, Hajiya Suwaiba ta ce "Ka ce sai gobe in Allah ya kaimi zaka dawo?"
Ya ce "Eh, fasawa na yi na taho yau"
Fadila ta ce "Amma Daddy lafiya dai ko, Rauda kawo masa ruwan sanyi"
Suwaiba ta ce "Wai dan Allah Baban Rauda Meyafaru a Lagos ɗin ne?"
Ya ce "Sai kun gaya mini, me ku ke tattaunawa ne, ganinku tare ya sanya ni farinciki"
Hajiya Suwaiba ta ce "Abokin nan naka ne ya zo gidan nan, wanda ya sai gidan nan, shi ne muke tattaunawa mu tattara ɗan abin da ya yi saura, a nemo gida mu tashi, tun da mun ga alamar mutumin nan zai iya ci mana mutunci daga mu har kai."
Ya yi murmushi tare da jinjina kai. Cikin damuwa Fadila ta ce "Dan Allah Daddy ka gaya mana, meyafaru muna fatan dai ba wani abin ne ya kuma kunno kai ba"
Ya saki murmushi ya ce "Da baku ganni a haka ba, Alhamdillah an canza sabon controller na hukumar Coustom na ƙasa. An sakar mini kwantena Arba'i da bakwai a cikin kwantenonina, da na mutane da na haɗa na yo order kaya" A rikice suka buɗe ido, suna jin abin kamar a mafarki. Hajiya Suwaiba baki na rawa ta ce "Daddy, kenan suna sane suka kama ka kayan naka, ba wani laifin ka yi ba, yanzu kana nufin an saki kayan?" Ya jinjina kai ya ce "An saki wasu daga cikin kayan, Allah ya karɓi addu'a" Gaba ɗaya suka rungume shi tare da yaransa, yana kuka su na kuka, babu abin da bakunansu ke furtawa sai tsantsar yabo da godiya ga Ubangiji Subhanahu wata'ala mai zaɓar wa kowane bawa abin da ya dace da rayuwarsa.
Baban su Nana ji yayi tamkar ya ɗora hannu a ka ya zunduma ihu, bayan da likita ya sanar masa abin da yake damun Jamila. Duk da Mama ta roƙe si a kan su rufa musu asiri, amma ganin yadda Baban yake ta sintiri hankalinsa a tashe, an rasa takamaiman dalilin da ya sanya ake ta ƙara wa Jamila jini. Ya sanya ya yi wa Baba bayanin, cikin jikinta da ya zube ne, bai fita gaba ɗaya ba, ga jini ta zubar mai yawan gaske. A tsorace Baba ya kalli Mama ya ce "Rabi, wane cikin? A ina Jamila ta samu ciki?" Ta tsuru-tsuru tana jin kamar ta kama Likitan ta yi ta gwara kansa a gurin. "Rabi, dama abin da yake faruwa kenan ki ka ɓoye mini? Jamila da ciki? Kin cuce ni ba ki yi mini adalci ba, kuma ki ka ɓoye mini baki gaya mini ba ki ka nemi kashe ta da ƙwayoyi. Shikenan kanki ki ka yi wa, na fara zargin alhakin Nana ne duk yake bibiyarmu. Nana duk matsi da wahalar da ta sha a rayuwarta bata ɗaukko mini magana ba, ki ka yi mata sharri ki ka saka na amince na aura mata mutumin da ban san waye shi ba, an wayi gari shekara uku, babu ita babu ɗan uwanta, ke kuma naki 'ya'yan babu na mora daga mahaukaciya mai fama da aljanu sai lalattaciya. Abubuwan da ki ke yi wa Nana sharri da kuma yi mata gori a kai, duk sun kama ki a kan yarnki. Amma kanki ki ka yi wa Allah ya yi muku magani" Har ya gama maganar ya fita, ba ta sake iya cewa Uffan ba sai gursheƙen kuka da take yi. Jamila ma da ke kwance sai kukan da take faman yi.
*****
Kasancewar Alhaji Fatuhu yana ɗakin Fadila ne, ta din ga gargaɗinsa a kan ya ja bakinsa ya yi shiru, kar yayi saurin gaya wa jama'a cewar an sakar masa kayansa. Ya ce "Haba masoyiyya, duk yawan jama'ar da suka taru suka jajanta mana, tsawon wannan lokacin, kusan shekara huɗu, kuma sai waraka ta zo mu yi shiru?" Fadila ta ce "Sa gani a hankali, baki yana yi wa abu illa, ka san waɗanda zaka janyo jikinka tukuna, ka lallaɓa ka ga abin da Allah zai yi sannu a hankali ka fara settling komai, amma dan Allah kar ka yi saurin gaya wa jama'a" Ya ce "To shikenan na ji, zan ɗan fita yanzu amma, sannan goben in Allah ya kaimu, gaskiya ki shirya mu je, zamu duba Yaya Sa'a, zan kuma mayar da ita Asibiti in sha Allah"
Ta so musa masa zuwan, amma ta ga bai kamata ba, kawai ta haƙura ta shanyeta amsa masa da to.
A gida Alhaji Fatuhu ya tarar da Alhaji Zailani, ya tarar da shi ya yi wata irin muguwar rama, bai matuƙar ban tsoro. Ya ce "Alhaji Zailani, lafiya kuwa me yake damunka haka? Ko duk tashin hankalin ɓatan Shukura ne?"
Alhaji Zailani ya yi murmushi ya ce "Ba dole hankalina ya tashi ba, 'ya ta ɓace babu ita babu labarinta ba, gefe guda ga ciwon suga ya sako ni a gaba, yanzu an hana ni cin komai sai ganye, kusan ko ruwa na sha sai ya yi sama. Na rasa ma abin da yake yi mini daɗi" Cikin damuwa Alhaji Fatuhu ya ce "Haba kai kuwa, duk lokacin da muka yi waya ce mini ka ke yi kana nan lafiya, ayyuka sun yi maka yawa shiyasa na ce ni bari na zo da kaina, ko zan samu kana gida. Ni nawa jikin Alhamdillah ya yi kyau kai kuma babu lafiya haka. Ka kwantar da hankalinka in sha Allah zaka samu lafiya. Kuma za a ga Shukura da yardar Allah. Amma kai ma ka jarraba na gargajiya ko za a dace, ni na ga alfanun ire-iren magungunan nan wallahi" Alhaji Zailani ya ce "To shikenan, zan gwada da yardar Allah" A baɗini kuwa, Aljanin da yake bawa jini ne, ya fara burkita shi yake shan nasa jinin, saboda rashin bashi abin da ya nema a wannan shekarar. Ga shi ya yi ta mummunan mafarki da Shukura tana caka masa wuƙa tana kuka. Ga shi ya yi ta mafarkin ƙwarangwal ɗin jariri yana sha masa jini, ko yana fizgo kayan cikinsa yana ci. Idan ya tashi sai ya ji jikinsa kamar babu laka, ko hannunsa da kyar yake iya ɗagawa. Da yaje Asibiti aka ce ciwon sugar ne, yanzu ya hau in anjima ya yi ƙasa ko a ganshi normal. Ga shi ya fara surutai idan yana baccinn har Hajiya Amina ta fara tuhumar sa, da yi masa tambayoyi.
****
Hammad na gaba, Nana na biye da shi, suka shiga turakar Sultan, karon farko Nana ta gan shi cikin riga da wando na shadda, babu rawani babu takunkumin yana shan shayi, Muhsin na kusa da shi, ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya da nasa kofin shi ma yana sha. Ba zaka taɓa cewa Sultan ya haifi su Hammad ba, kamar yayansu ba mahaifinsu ba. Muhsin yana kallon su Nana ya hau murmushi, amma bai tashi daga kusa da Sultan ba. Sultan ya kalli Muhsin ya ce "Suwaye waɗancan? Ka san su?" Kawai ya ci gaba da murmushi yana shan shayinsa. Ita Nana a zatonta, Imam Zahradeen ne ya kuma tafiya da shi gidansa.
Ta duƙa ta gaida Sultan, ya saki jiki sosai ya amsa mata, Hammad ma ya gaishe shi, shi ma ya amsa masa yana bin su da kallo, wata nustuwa da farin ciki na ratsa shi. Ya din da gode wa Allah, da bak biye wa su Sardauna ya kori Nana ba. "Ina fatan duk kuna cikin ƙoshin lafiya?"
Hammad ya ce "Alhamdillah"
"Ma sha Allah, Nana Asma'u" Nana ta ɗago da mamaki jin ya kira sunanta cikke. Ta ce "Na'am Abie" "Da farko ina mai baki haƙuri bisa ga abubuwa da suka faru, kar ki yi zaton ko dan muna sanya ran Hammd ya samu lafiya saboda ke ne, ya sanya na saukko. Ko kaɗan dama mun yi magana sosai da sosai da Mahmoudu ina ta tunanin yadda zan ɓullowa lamarin, ba tare da 'yan majalissata sun ga na nuna son kai ba, sai dai cikin ikon Allah a dalilinki, na fuskanci ingiza mai kantu ruwa suke yi mini. Kuma na koyo darussa daban-daban a dalilin faruwar wannan al'amura tabbas; idan bamu karɓi abin da ya faru a matsayin aya ba, to gaba Allah na iya jarabtarmu ta wani abin da ba zamu iya sa shi ba, a kan muguwar Al'adar da babu abin da ta haifar sai kawo mana koma baya. Yanzu dai ina baki haƙuri da abin da ya faru, wanda aka yi miki da gayya da wanda muka yi miki cikin kuskure. A duniya ko a gurina da na haifi Hammad bai samu nutsuwa da kwanciyar hankalin da ya samu a gurinki ba. Ga mu da kuɗi da wadata, amma Hammad bai tashi cikin kwanciyar hankali ba. Ko dan albarkacin wannan abokin nawa, dole na tabattar da kun ci gaba da rayuwa tare" Ya yi maganar yana shafa gashin Muhsin. Ya ce "Dan haka in sha Allah, muddin ina raye, babu wani abu da zai kawo muku cikas a rayuwar aurenku, Ubangiji Allah ya sanya muku albarka. Na ji duk tarihinki, har Nigeria na aika duk an yi mini binciken da yakamata, kuma na gamsu da abubuwan da na ji game da ke, da kuma rayuwar da ki ka yi da Hammad. Ina goyon bayan ku rayu tare, Hammad ba zai taɓa samun mace kamar ki ba Asma'u" Kawai Nana ta fara zirarar da hawayan farinciki. Hammad ya rikice gaba ɗaya ya ce "Abie, yanzu ka yarda na ci gaba da rayuwa da Nana? A matsayin matata duk da yadda al'adarmu ta hana?"
Sultan ya yi murmushi ya ce "Na ma soke wannan dokar, daga yau babu ita a Agadez" Hammad ya tashi ya tafi gaban Sultan ya risuna, amma ya rasa abin da zai ce masa. Sultan ya rungume shi yana murmushi. Ya numfasa ya ce "Hammad, ban san iya adadin abin da ya rage maka na rayuwa ba, amma na baka damar ka yi duk abin da ka ke so wanda bai saɓa wa mahaliccinka ba, da zai sanya ka farinciki. Sannan ka sakar wa Tafawa 'yarsa, dan babu amfani ci gaba da zama da mutumin da yake ƙoƙarin ganin bayanka, yake cutar da kai tsawon lokaci. Ka yi haƙuri kuma ka yi biyayya, Ubangiji Allah ya baka ladan haƙuri da kuma biyayyar da ka yi. Sannan ina roƙon Allah ya baka lafiya ya kuma warware miyagun abubuwan da suka aikata maka."Ɗan uwanka kuma wannan ganin damarka ce ka ci gaba da mu'amala da shi, amma ni na yafe shi a matsayin ɗa na, na girgiza matuƙa da jin abin da suka aikata" Nana zata yi magana Hammad ya girgiza mata kai alamar ta yi shiru. "Ke ma in sha Allah, zamu tura wakilai, zamu je mu ba wa iyayenki haƙuri, kuma kamar yadda mahaifiyar Mahmoudu ta nema, kuma mun amince za mu yi hakan. Duk wata ɗawainiyar aure da ake yi wa mace, da za a aura a Agadez za mu yi miki ita, kuma zamu biki sosai kowa ya san da zamanki"
Nana ta risuna ta ce "Na gode sosai da sosai Abie, Ubangiji Allah ya ƙara girma da sutura, ya kare ku daga dukkanin abin ƙi. Amma ni hukuncin da ka yanke mini bisa adalci da tausayi, da bani damar na rayu da Muhsin da mahaifinsa ya fi komai yi mini daɗi, ina ga ba sai an yi bikin nan ba, har dukiyar auren ma na yafe"
Sultan ya yi murmushi ya ce "Ba biyanki abin da ki ka yi mana zamu yi ba, kyautatawa ce daga gare mu, dan ƙara nuna martaba da daraja da duk wani ɗan Adam yake da shi, fari ko baƙi koma wani kalar launin fata ne. Ina ƙara amfani da wannan damar, gurin ƙara nuna ɗimbin godiyata a gare ki. Kin sadaukar kin jajirce, mun san bamu da abin biyan ki, amma ina kyautata miki zato da yi miki fatan alkhairi" Nana ta sunkuyar tana murmushi ta kasa magana ma. "Na ɗauki darussa daban-daban, a kan abubuwan da suka faru, komai sila ne, kuma wasu lokutan bawa baya samun ɗaukaka ko cimma nasara, sai an jarraba shi, wasu lokutan mai sauƙi, wasu lokutan kuma mai tsanani. Allah dai ya baku zaman lafiya na har abada. Shi kuma mai magani Sarkin baka ko? Ya ce yana nan tare da shi za a je Nigeria. Ɗan uwanki ma an ce mini yana Agadez yanzu haka, da Zahradeen ya kai shi karatu, zan saka a kawo mini shi nan, shi ma na yi masa godiya na ba shi haƙuri shi ma" Nana ta ce "Dan Allah Abie, ka duba girman abin da Imam Zahradeen ya yi, fiye da laifinsa ka yafe masa. "
Yayi murmushi kawai ya ce "Za a duba"
Hammad ma ya ci gaba da yi wa Sultan godiya, dan bai taɓa tsammanin zai yanke wannan hukuncin ba. Sultan ya ce Nana zata iya tafiya, bayan tafiyarta Hammad ya sake yi wa Sultan godiya sannan ya ce "Amma Abie hukuncin nan da ka yanke, ba zai janyo surutu da 'yan majalisar ka ba?"
Sultan ya ce "Hammad, zan yi duk abin da nake ganin shi ne dai-dai, har abada na daina jiran wani ya sarrafa ni, duk abin da nake ganin shi ne daidai zan zartar da shi."
Hammad ya jinjina kai yana sake gode wa Allah. Ya sake cewa "Amma Sultan meyasa ka ce na saki Asal?"
"Me za ka yi da ita? Ko ba ka ji abin da ɗan uwanka ya faɗa sun haɗa kai da ubanta da Bilki suna neman ganin bayanka ba?"
Hammad ya jinjina kai ya ce "Haka ne"
"Amma idan kana son matarka, shikenan ba zan yi maka dole ba"
Hammad ya ce "Ba na son aikata abin da za kalle ni a matsayin mara adalci, amma kamar ku ne ɓoye mini wani abu da kai da Maman Muhsin"
Sultan ya sake yin murmushi ya ce "To idan ma mun ɓoye maka ai ba laifi muka yi ba, tashi ka yi tafiyarka"
*****
Alhaji Fatuhu yaje dubiyar Doctor Sharif tare da Fadila da Suwaiba, sai dai ya tsorata da yanayin da ya gan shi a ciki, tun da ya ga Alhaji Fatuhu yake kuka, amma ya kasa magana, sai da kyar kamar an fizgo maganar ya ce "Ka yi hankali da Alhaji Zailani, kuma ka yafe mini dan Allah" Hakan ma ba komai ake ganewa ba, sai dai maganar ma bata fita da kyau, da kyar suka gane me yake cewa. Daga bisani suka tafi gidan Hajiya Sa'a, tana kwace a cikin najasa, Alhaji Fatuhu ya din ga yi wa masu aikinta faɗa, yana iƙirarin tun da komai ya fara daidaita, gidansa zai mayar da ita. Sai dai haka kurum ƙasan zuciyarsa ya din ga mamakin wani irin nau'in ciwo ne ake ta fama da shi haka.
Maganar da Muhsin ya yi, yana ƙoƙarin karɓar wayar mamansa, ya sanya Hajiya Sa'a waiwayo wa da sauri ta kalli yaron.
Ayshercool 08081012143
98 1K NE VIA 0069685771 AISHA ADAM STANBIC BANK 08081012143
Cikin mamaki Alhaji Fatuhu yake kallon Hajiya Sa'a, saboda yadda ta ƙure Muhsin da ido.
Ya ce "Yaya Sa'a, kin gane ni? Ko Muhsin ki ka gane?"