Buzu book 3 complete - Chapter 30
Buzu book 3 complete Chapter 30: Buzu book 3 complete Chapter 30. "Ba dole na gane wannan tsinannen yaron da Allah ya tsine wa albarka ba? In sha Allah sai…
3,360 words
"Ba dole na gane wannan tsinannen yaron da Allah ya tsine wa albarka ba? In sha Allah sai ya mutu kuma kun rasa. Da shi ne ya mutu da Abbana bai mutu ba, ɗan nawa guda ɗaya na rasa shi, ku ga naku nan yana rayuwa " Cikin rashin fahimta Alhaji Fatuhu ya ce "Yaya Sa'a kin san kuwa me ki ke cewa?" Cikin tsawa ta ce "Na sani mana, na sani, ina sane. Yanzu ga Abba ya mutu a banza, ni kuma dodon ƙungiya ya shanye mini wasu sassan jikina." Gaba ɗaya ya yi iya ƙoƙarinsa gurin ganin maganganun da take yi, ba su yi tasiri a zuciyarsa ba. Ya dubi Fadila da ta takure a gefe, tana zare ido ya ce "Fadila, kar fa ku damu ko ku ɗaga hankalinku, kun san ba a hayyacinta take ba, tana fama da matsalar taɓin hankali." Hajiya Suwaiba ta ce "Duk da haka amma mutum ko ba shi da hankali, yana faɗar abin da yake aikatawa ne, amma babu rami mai ya kawo rami?" "Ƙaryata ni za ki yi kenan Suwaiba? Meye haɗin Yaya Sa'a da wani shan jini, kawai raɗaɗin mutuwar ɗanta ne yake damunta" Fafur ya hana su magana, tare da kare Sa'a, duk da ƙasan zuciyarsa maganar Hajiya Suwaiba ta kama zuciyarsa, da ta ce babu yadda za a yi Hajiya Sa'a ta yi wannan maganganu idan bata da alaƙa da su.
*****
Imam Zahradeen ne zaune a gaban mahaifiyarsa Hajiya Bilkisu, cikin kuka take yi masa bala'i "Yanzu Zahradeen har zaka iya fifita bare a kaina mahaifiyarka, ka zaɓi ka tona mini asiri? Yanzu amfanin me hakan ya yi maka daga kai har ni. Duk fafutukar da na yi domin ka ne, amma a ƙarshe ka watsa mini ƙasa a idona. Ka lalata komai abin da nake harin ba zaka samu ba, saboda kai ne gwanin na iya da son burgewa, ka tona mana asiri ga shi kaima baka tsira ba"
"Ban yi duk abin da na yi, domin tozarta ki ba Ammi, duk abin da na yi, na aikata ne domin kaucewa faɗa wa fushin Ubangiji. Bawa bai taɓa isa ya yi wa bawa abin da Allah bai yi masa ba. Duk ƙoƙarin ku Ammi idan Allah bai ƙaddara mu hau karagar nan ba ba zamu hau ba. A yanzu hakan ku nawa ne ku ke fafutuka, ko da an kawar da Hammad, kuma ba zaku samu zaman lafiya da fahimtar juna ba, kowa na sa yake son ya hau. Ammi Hammad fa shikaɗai ne ɗan uwana namiji... "Tashi ka bani guri, kafin baƙin ciki ya sanya na tsine maka, ka fita ka bani guri" Zuciyarsa cike da ƙuna ya tashi ya bar sashen ta.
Murmushin fuskar Nana ya kasa ɓoyuwa, Ƙaisar shi ma murmushin ya yi, kamar koyaushe gyaran litattafansa yake yi. Ya ce "A karo na babu adadi, ina sake taya ki murna ma a wannan karon, tabbas ko a iya haka kin yi nasara. Kuma aya ce ke mai zaman kanta ga mutanen Agadez ba Agadez ba kawai ga duk wani mai hankali ma. Jaruma ce ke ta gaske uwar gijiyata"
"Ƙaisar"
"Na'am"
"Ina yi maka kyakykywan fatan alkhairi na har abada " Ya ajiye littafin hannunsa ya ce "Har kin mantan Allah ya isan da ki ka yi mini a baya" Ta katse shi ta hanyar cewa "Duk wanda yake rinjayar da laifukan mutane, sama da alkhairinsu, to zai zama mara adalci"
Ya ce "To ai ni ba mutum bane"
Ta yi dariya ta ce "Ni a gurina kai mutum ne. Alkhairinka ya shafe laifukan ka Ƙaisar. Gaba ɗaya ji nake yi kamar ba ni ba, zan rayu da Hammad ɗina, da kuma Muhsin Allah abin godiya kamar komai ba zai wuce ba"
Ya zauna yana faɗin "Babu abin da ba ya wucewa sai ikon Allah"
Za ta yi magana ta farka daga baccin da ya ɗan ɗauke ta. Da Sayyid ta fara tozali ya ce "Amarya" "Ango" Ta amasa masa tana murmushi. "Nene ta ce sai na mayar mata da ke, wai shirya ki za a yi, ba dai yadda zan yi ne, na fi son ta bar mini ke in din ga jin ɗuminki. Ke ba kya buƙatar duk wani gyara, a gyarenki Allah ya yi ki"
Nana ta tashi zaune ta ce "Allah ya shirya mini kai, Nenen zaka gaya wa haka ko? Ni sonake ma na gana da ɗan uwana na yi kewarsa"
Hammad ya numfasa ya ce "Kin san Sultan sun samu matsala da Imam Zahradeen, ina ta girgiza miki kai ɗazu, ki bari sannu a hankali zai saukko zan san yadda zan yi na shirya su. Amma da farko ji na yi kamar ba zan yafe masa ba. Amma na duba girman abubuwan da ya yi na alkhairi a gare ni. Kuma ni duk mutumin da zai yi abin da zai kyautata miki to ni ya yi wa, dan haka na ji zan mayar da komai ba komai ba. Kin san wani abu ma vie" Ta girgiza masa kai alamar a'a. "Wallahi idan na kalle ki, na kalli Muhsin, sai in ji zan iya yafe wa kowa ma, Duniyar guda nawa take? Allah ya yi mini tagomashi da abin da na san ba dabara ta ba ce ba. Ba zan fasa gode wa Allah ba" Nana ta ce "Tabbas Allah abin godiya Sayyid. Amma ina da wani roƙo a gare ka; kamar yadda ku ka soke al'adar haramta auratayya tsakaninku da baƙaƙen fata, ina roƙon ku haramta duk wani nau'i na ta'amalli da Aljanu da shaiɗanu" Ta ɗan yi shiru tana satar kallonsa. Ya ce "Ina jinki" Ta ci gaba da faɗin "Ta'amalli da aljanu, da hana iliminku na addini tasiri a cikin rayuwarku, haɗi da riƙo da munanan al'adu su suka ƙara ta'azzara wasu abubuwan. Ga dai zobunanka masu ɗauke da hadiman aljanu, amma hakan bai hana a cutar da kai ba, cuta mai munin gaske. Su ba su baka kariya ba, su ba su hana a cutar da kai ba. Babu wata halitta da zata baka kariya ko ta hana faruwar wasu abubuwan a rayuwarka. Sai dai duk da wannan abin, ina girmama riƙo da ibadarka mussaman salla. Kai ma'abocin salla ne. Dan Allah Imam ka ƙara ƙoƙari gurin ganin an kakkaɓe al'adar amfani da aljanu a cikin harkar mulki. Ga saɓon Allah, ga gadar wa zuriya masifa da tashin hankali. Ni da kai ɗin nan mislai ne akan kanmu, ba zamu yi fatan ire-iren zuriyarmu su gaji wannan bala'in da muka shiga ba. Dan Allah Hammad ka yi ƙoƙari a yi yaƙi da ta'amalli da su, da kuma duk wani abu da ya shafe su. A ɗayanta Allah, a dogara da shi duk ba kwa buƙatar wannan abubuwan muddin kun riƙe Allah ". Ya numfasa ya ce "Maganganunki duk gaskiya ne Ma vie, kuma tuntuni na fara ƙoƙarin neman maraba da su, ni kaina na daɗe ba na son harkar da muke yi da su, amma in sha Allah zan ƙara ƙarfafa hakan, har abada za a daina amfani da duk wani nau'i na gurɓatacciyar al'ada a Agadez" Nana ta rungumo shi ta ce "Yauwwa farincikina, Ubangiji Allah ya saka maka da alkhairi, ya ƙara kare mini kai daga dukkanin wani sharrin. Allah ya ƙara ɗaukaka mini darajarka zuwa inda zato bai taɓa zato ba. Allah ya yi maka kyakykywan tsari daga sharrin duk wani abin ƙi komai ƙanƙantarsa." Ya tsurawa Nana ido, sannan ya ce "Ta yaya ake so na iya rayuwa babu wannan halittar? Halittar da harshenta kullum cikin yi mini addu'a da fatan Alkhairi take. Mai ɗauke da zuciyar da kullum take ƙoƙarin kusantar da ni ga Allah, baiwar Allah da kullum burinta ta sadaukar Saboda da komai saboda ni. In sha Allah mutuwa ce zata raba ni da ke rayuwata. Allah ya yi miki tukuci da gidan aljanna. Ina ƙaunrki Asma'u." Ya yi maganar yana tsare ta da manyan idanunsa, da ba ta san dalilin canzawarsu zuwa ja ba.
"Nima ina ƙaunarka mijina, irin sosai da sosai, ban san ya zan misalta maka ba"
"Ba sai kin misalita mini ba, na gani a zahiri" Ta sunkuyar da kanta tana ɗan murmushi. Ya ce "Yanzu me za ki shirya mana, na shirin bikin? Sultan ya ce sai an yi biki sosai a Agadez, me za ki shirya mana? Me da me ki ke so?" Ta girgiza kai ta ce "Kai kaɗai kawai nake so, kai kaɗai ka ishi Nana komai" Ya yi dariya ya ce "Zan kawo miki Imrana da Muhsin, har ma da Nene anjima su ɗebe miki kewa" Nana ta ce "Amma kuwa da ka kyauta, na gode sosai da sosai" Ya dungure mata kai yana murmushi.
***** Alhaji Fatuhu kuwa bacci ne ya gagare shi, kamar yadda dariya ta gagari kare, ya gagara yin bacci. Idan ya samu baccin ya fara ɗaukarsa, kawai sai ya ga Hajiya Sa'a, tana kuka tana sake maimaita abin da ta faɗa da suka je. Duk yadda ya din ga addu'a, da ƙoƙarin kawar da tunanin daga zuciyarsa, amma abu ya faskara. Sai dai ya danne ya ci gaba da addu'a. Sai kuma doctor Sharif ya faɗo masa, da shi ma yake cewa ya yafe masa, to ya yafe masa da ya yi masa me? Gaba ɗaya sai al'ajabi, ya hana shi yin farincikin dawowar kayansa. Ga shi ya zo gaya wa Alhaji Zailani, tun da dama shi ne abokin kasuwancinsa, amma ya tuna yadda Fadila ta gargaɗe shi a kan haka.
*****
Sagir kuwa tun da yaje Abuja gidansu Yusra, hankalinsa ya ƙara tashi. Jaririn da ya gani da shi yake kamanni, ya yarda jaririn nan ɗansa ne, amma babu yadda ba a yi da Yusra ta yi magana ba, ta faɗi a ina ta haɗu da Shukura ba. Sai dai ana ta ba wa jaririn madara. Sagir ya ce wa mamanta "Ina ga, zan koma Kano na samu iyayen Shukura na sanar da su cewar, an ga jaririn Shukura" Maman ta ce "A'a kar ka faɗa tukuna, kar a zargi Yusra da wani abu, a ci gaba da addu'a dai da bincike, haryanzu Yusra bata cikin nutsuwarta. Haka ya din ga sintiri tsakanin Abuja da Kano, ga shi ya kasa gaya wa kowa, saboda shi kansa ya san ayar tambaya za a saka wa Yusra. Sai dai al'amuran Yusran su na ba shi tsoro shi kansa, banda yana sonta kuma ya san halin da ta shiga, lokacin da Shukura ta ɓata, da babu abin da zai hana ya ce da sanya hannun Yusra a lamarin ɓatan Shukura, idan ba haka ba a ina ta samu jaririnta?
****
Labari ya cika ciki da wajen Agadez, kan cewar Hammad yana da ɗa, ya auri 'yar Nigeria, haka zalika an soke Al'adar hana auren baƙar fata. Wasu daga cikin al'ummar garin hakan yayi musu daɗi, mussaman baƙaƙe, da suka din ga jin tamkar su zuba ruwa a ƙasa su sha.
Ɓangaren fararen buzayen kuwa, gani suke yi tamkar rage musu kima ne, da kuma rage karsashin Masarautar. Cikin marasa gaskiya a fadar Sultan kuwa, cikinsu ya ɗuri ruwa cike da tashin hankali, saboda tsoron hukuncin da ka iya biyo bayan tonuwar asirinsu. Ga shi Sultan ya ƙi nuna musu ya san su ne, kuma tun daga ranar da aka kawo bokan nan fadar Sultan, ba a sake zaman majalissar ba. Waɗanda ba su san Nana ba, suka din ga sintirin gidan Sultan, su na son ga Nana, amma Nana na kauwwame a sashin Sultan.
Tuni labari ya ishe Asal, wanda hakan ya sake gigitata, tamkar za ta yi hauka. Wani irin so da matsanancin kishin Hammad ya din ga taso mata, ji take yi tamkar za ta yi hauka. Gani take yi ta ƙasaƙanta ta tozarta, a ce Nana ce kishiyarta, matar da ta ɗauka tamkar baiwar da ta saka kuɗi ta saya, amma yanzu ita ke da komai, ita kuma tana gefe ta zama 'yar kallo. Wasa-wasa Asal ta daina cin abinci sai kuka, ga Tafawa ba ta ita yake yi ba, ta zaman jiran tsammanin abin da za a yanke musu kawai yake yi.
Duk matsanancin kishin Hammad, haka ya ƙyale Nana da Imarana, suka kasance tare suna ta hira irin ta 'yan uwantaka, tare bawa junansu labarin gwagwarmayar da suka yi ta rayuwa.
Ya ce "Bari na nuna miki wani abu" Imarana ya ɗan tashi ya fita, sannan ya dawo, ko da ya dawo ya miƙa wa Nana waya. Nana ta karɓi wayar tana kallonsa, ya yi mata alama da ta saka a kunnenta.
Nana ta saka wayar a kunnenta, zuciyarta na ɗan bugawa da sauri.
"Assalamu alaikum, Nana" Muryar Ummansu ce ta doki dodon kunnuwanta, a wani irin rikice Nana ta tashi tsaye, ta rasa ina zata dosa ta ce "Um..umma, muryarki ce ke ce?"
"Nice Nana, kina nan lafiya?"
Nana ta durƙushe a kan gwiwoyinta, ta ce "Umma, bani da bakin da zan yi miki magana, bani da idon da zan iya kallonki, ni mai tarin laifi ce"
"Shhh, Babu abin da ki ka yi mini na ba dai-dai ba Nana. Sai dai tashin hankali da fargaba na shige shi, na rashin sanin inda ki ke, da kuma wani hali ki ke ciki, ga tsohon ciki kin tafi kin bar gida. Amma Imrana ya zo inda nake, tare da Yayan mijinki, sun yi mini bayanin komai. Nana na yi sujuda na gode wa Allah, ba wai domin daular da ki ke ciki ba, ko kina auren wani ba, sai domin murnar kina cikin ƙoshin lafiya tare da ke da yaronki. Sun ce kar na gaya wa kowa, babu wanda ya sani, amma sun zo sun yi mini alkhairi Imrana ya zama babban mutum ya nutsu, kema hankalinki yana kwance. Ni dai fatana su yi su kawo mini ke, ko na wanko ƙafata na taho,amma sun ce na yi haƙuri kaɗan"
Cikin kuka Nana ta ce "Ni dai ki yafe mini dan Allah, tashin hankalin da na sanya ku a ciki, dan Allah ku yi haƙuri Umma" Imrana ya karɓe wayar ya ce "Umma sai anjima, da na sani ban haɗa ku ba, nema take ta rikice"
**** Hajiya Amina tana zaune tare da Alhaji Zailani, tana ta lallaɓa shi a kan ya ci abinci, amma ya ƙi ci, saboda shikaɗai ya san bala'in da yake ciki. Tun da ya yi mafarkin an huda saitin zuciyarsa, dodon ƙungiya yana sha masa jini, ya farka ya ji saitin zuciyarsa ya yi masa wani irin nauyi. Ga jikinsa sai yi masa wani irin raɗaɗi yake yi, kamar ya yi wanka da yaji. Yana jin yadda wayarsa take ta ringing amma ya ƙi ɗagawa. Daga ƙarshe, Hajiya Amina ta saka hannu ta ɗauki wayar, ta saka a kunnenta tana sallama. Jin ta yi shiru ya sanya Alhaji Zailani ɗagowa ya kalle ta, sai dai ta tsare shi da idanunta ba ta ce masa uffan ba.
Jiran Hajiya Amina yake yi ta yi magana, amma ta yi shiru ba ta yi magana ba. Jiki babu ƙwari ya ce "Ya dai? Meyafaru?" Jiki a sanyaye ta ce "Daga makarantar su Yusuf ne, wai yana kwance a Asibiti babu lafiya, yau kwana uku kenan" Ya waro ido ya ce "Yusuf ɗin?" Ta jinjina masa kai. "Ki kira su ki gaya musu, ni ba ni da lafiya, babu lallai na iya driving su dawo mini da ɗana gida" Hajiya Amin ta jinjina kai tare da mayar da hankalinta kan wayar.
*****
Gidan Baba ya zama tamkar maƙabarta, babu walwala ko kaɗan, ko ƙaunar tunkarar gidan baya son ya yi. Saboda matsananciyar damuwa, da takaicin abubuwan da suke faruwa a gidan. Jamila kuwa kullum tana ɗaki, dan ta sha baƙar azaba, sai da ta kwana tara a Asibiti, da kyar aka samo kanta kamar ba zata rayu ba. Ya daina shiga harkar Mama da yaranta gaba ɗaya, ko abincin gidan ya daina ci. Ga damuwa da kewar yaransa Nana da Imrana da suka addabi zuciyarsa. Ya fito daga cikin gida da buta a hannunsa, ya yi alwalar sallar Azahar sai ga wata danƙareriyar mota irin ta matafiya, sabuwa gal sai ƙyalli take yi ta shigo layin. Bai damu ba, ya idar da alwalarsa ya ɗaukko wayarsa, yana son kiran can Buda, saboda yaga kiran wayarsu, bai samu ya ɗaga ba. Sai ya ga motar nan an tsaya da ita a ƙofar gidan. Sai ya yi tsuru yana kallon motar. Sulei ne tare da Mahmoudu suka fito, suka nufo Baba. Ya tsaya saroro har suka ƙaraso inda yake. Suka durƙusa har ƙasa suka gaishe shi, ya amsa musu yana bin su da kallo, kasancewar sun rufe fuskokinsu da takunkumi. Bayan sun gaisa, Mahmoudu ya ce "Baba mu na tare da baƙi ne daga Agadez" Baba ya ɗan yi shiru, shi dai ya san babu wanda ya sani a Agadez, amma ya miƙe ya ce "To bari na kawo muku abin zama" Ya tashi ya shiga cikin gidan, ya ɗaukko tabarma ya shimfiɗa musu, ya koma ya aiki Nasiru ya sayo ruwa. Ya zata iya su Mahmoudu ne baƙin, kawai ya ga Sulei ya je ya buɗe motar, wani dogon mutum mai jiki ya fito da wani matashi, shi ma sanye da rawani suka fito, suka nufo shimfiɗar. Shi dai Baba duk abin ya ɗaure masa kai, tsoro ya shige shi. Ya yi musu barka da zuwa, suka zazzauna, Mahmoudu ya sauke rawanin fuskarsa ya ce "Baba baka gane ni ba?" Baba ya yi shiru ya ce "Kamar dai na sanka, amma ban gane ka ba" Imam Zahradeen ya sauke rawaninsa shi ma, shi ma dai Baban ya yi masa kallon sani. Mahmoudu ya ce "Baba kamar baka gane mu ba ko?" Baba ya ce "Gaskiya dai" "Baƙi ka yi daga Agadez"
"To bawan Allah, ni wa nake da shi Agadez, kuma ba ɓatan kai ku ka yi ba?"
Mahmoudu ya ce "Ba mu yi ɓatan kai ba, na yi mamaki da ka ce ba ka gane ni ba, amma ai ka tuna buzun da ka aura wa 'yarka shekarun da suka gabata" A razane Baba ya ɗago ya kalli Mahmoudu, sai kuma ya riƙe rigarsa, ya ce "Dama ku ne? Ba ku yi mini adalci ba, ku ka tattara ku ka gudu, ku ka bar mini 'ya da jinyar ɗan uwanku, shi ma daga ƙarshe ya gudu ya bar ta, saboda wauta da rashin hankali wai ta tafi Niger neman shi, haryanzu shekara ta uku kenan, babu wanda ya san inda take, baku kyauta mini ba" Baba yayi maganar yana kuka kamar ƙaramin yaro.
Imam Zahradeen ya ce "Baba, ka yi haƙuri abubuwan da suka faru ba a kyauta maka ba. Amma mu na da kyakyawan albishir ne"
Baba ya ce "Kai ba kai ne mijin nata ba?" Yayi maganar yana nuna Imam Zahradeen. Zahradeen ya ce "Baba ai na fi wancan tsufa, shi ya fi ni ƙuruciya, ya kuma fi ni kyau, ni yayansa ne. Zancen da nake yi maka, a kowane lokaci mahaifinmu zai iya aiko da mutanensa daga Agadez da kayan auren Nana za a sake gagarumin bikin aurensu"
Baba ya ce "Ashsha! Yarinyar da nake gaya muku shekara uku babu wanda ya san inda take, kuma babu wanda ya waiwaye ta tunda ku ka gudu kuka bar ta. Kuma ni mene ne haɗina da Sarkin Agadez da zai kawo kayan aure? Ni dai na yi nadamar abin da na aikata na aurar da 'yata ga mutumin da ban san daga inda yake ba" Imam Zahradeen ya lura ran Baba a ɓace yake. Ya sassauta murya ya ce "Baba sunana Imam Zahradeen Jalaludeen Agadez, ni Yaya ne ga Imam Hammad Jalaludeen Agadez. Kuma 'ya'ya ga Sultan Jalaludeen Agadez, wato Sarkin Agadez na yanzu. Buzun da ka aura wa 'yarka, ɗan uwana ne, kuma ɗa ne ga Sultan na Agadez."
Baba ya kalli Imam Zahradeen kamar yana raina masa hankali. Ya ce "Ɗan sarki ne zai zo baro ƙasarsa ya zo Nigeria yana aikin gadi?"
Mahmoudu ya ce "Baba, idan baka manta ba, ko lokacin da aka yi aurensu, a yanayi na rashin lafiya yake, rashin lafiya ce ta kama shi"
"To yaya za a yi a ce ɗan sarki ya zo Nigeria gadi, ni abin ya bani mamaki ne. Kuma na kasa yarda, ni kar ku sake dugunzuma mini hankali bayan halin da nake cikix