Kenza eBookz

Buzu book 3 complete - Chapter 6

Buzu book 3 complete - Chapter 6

Buzu book 3 complete Chapter 6: Buzu book 3 complete Chapter 6. "Ƙaisar"

3,334 words

"Ƙaisar"

"Na'am" ya amsa ba tare da ya kalle ta ba. "Wai dan Allah me ya same ka?"

"A ina?"

"Na ga yanzu kullum ka na kan gadon nan, kuma a lulluɓe. Giyaz ne ya yi maka wani abin ne?"

Ya girgiza kai ya ce "A'a me ki ka gani?"

"Na san shikaɗai ne yake iya cutar da kai" Ta yi maganar a sanyaye.

"In ji wa? Akwai Aljanu masu ƙarfi da suka fi ni ƙarfi da za su iya cutar da ni. Kawai ni ba na shiga harkar kowa ne, ina gefe ina jin daɗin rayuwar kaɗaicina da litattafaina da haɗa magunguna na"

Nana ta yi murmushi ta ce "Yaushe za ka yi aure ne kai?"

"Sai na girma"

"Au yanzu baka girma ba? Ina Haula ne?"

Tsuke fuska ya yi ya ce "Je ki ɗakin magungunana, akwai wata kwalba taswirarta kamar zanen Duniya, ki ɗaukko ki kawo mini" Nana ta ce "To" Ta nufi ɗakin da yake ajiye-ajiyen kayan maganinsa. Ta tsaya tana ta kallon kwalaben, da yadda wasu magungunan suke yawo a cikin kwalaben, tamkar abubuwa masu rai. Ta ga wanda ya ce ta ɗaukko ta waiwayo kawai ta ga Giyaz a tsaye a bayanta.

"A'uzubikalimatillahi tammat" Ta furta cike da tsoro, a suffarsa ta tsoho tukuf ya bayyana a gabanta.

Ya buɗe baki ya ce "Ban taɓa ganin halittar da na tsana a doron ƙasa ba sama da ke, sai na sabauta rayuwarki, sai na kashe ki na ƙarar da zuriyarku na huta da wannan bala'in. Ya ja da baya ya nuna ta da sandarsa, da take ci da wata irin wuta mai tartsatsi. Nana ta ja da baya, ta saka hannayenta ta rufe fuskarta, tana jiran jin wutar ta fara ƙona ta, amma ta ji shiru. Ta buɗe idanunta a hankali ta ga Ƙaisar ya shiga tsakiyarsu, tartsatsin wutar ya ƙona shi, ya faɗi a gefe jikinsa yana hayaƙi. Nana ta saki kwalbar ta nufe shi da gudu. Cikin tashin hankali da tsoro ta ce "Ƙaisar, me ya same ka?" Sai a lokacin ta ga tarin raunukan da suke jikinsa, ga ƙonewar da ya yi yanzu. Giyaz ya ƙaraso kan Ƙaisar da sauri, ya saka hannunsa ya ɗago shi, amma ya ga jikinsa ya saki.

"Wallahi muddin ɗa na ya mutu sai na kashe ki har lahira"

Cikin dakiya da kawar da tsoro ta ce "Me ka yi masa? Kai wane irin azzalumar halitta ne wai, kowane abu yana alfahari da ɗansa da ƙoƙarin ba shi kariya, amma kai kullum cikin ƙoƙarin cutar da shi ka ke. Ƙaisar ka tashi dan Allah. Ta yi maganar cikin kuka tana ƙoƙarin taɓa shi, amma wani irin matsanancin sanyi ya ratsa ta. Ta buɗe idanunta a hankali cikin sheshsheƙar kuka, har da majina kawai ta ganta a jikin Sayyid ya riƙe ta gam yana kallonta cikin tausayawa. Ta yinƙura za ta tashi amma ya hana ta, ya ce "Ki bari ki ɗan nutsu. Me ya same shi ki ke wannan uban kukan haka? Idan komai ya lafa mini, dole na ɗauki mataki a kansa, dan ba zai yiwu ya din ga bibiyar matata ba, ina baƙin ciki da hakan"

"Ba za ka yi masa komai ba, babu ruwanka da shi, tun da dai duk da tsana da abubuwan da nake yi masa, shi bai gudu ya bar ni ba, kamar yadda ka yi mini ba"

Ya ɗan zura mata ido har zai yi magana sai kuma ya fasa. Ta zame daga jikinsa ta kwanta, zuciyarta cike da damuwa da tashin hankali, tare da fatan Allah ya sanya ba wata mummunar illar Giyaz ya yi masa ba. Ya tashi ya bar mata ɗakin, dama kukanta da sheshsheƙarta ya jiyo, shi yasa ya fito ya je ɗakin nata. Washegari da safe, ya kawo mata kayan da za ta saka su tafi. Ya kalle ta cikin magiya ya ce "Ma vie, na san ni mai laifi ne a gurinki, amma dan Allah ki tattara nutsuwarki guri guda, domin mu samu mafita. Duk abin da za su tambaye ki, ki sanar musu da komai, kar ki ɓoye musu komai saboda makomarmu"

"Ni ba wata makomarmu, kawai ɗa na za a bani na tafi"

Ya ce "To na ji, ga riga da za ki saka, ki je ki yi wanka ki shirya, ina jiran ki" Ta kalli rigar kamar ba zata karɓa ba, sai kuma ta karɓa ta ce "Na gode"

Ya yi murmushi ya ce "Ko mu je ki yi wankan a ɗakina, akwai mayukan shafawa"

"A'a ina da man da zan shafa"

"To su ma nawan ne dai ki ke shafawa, saboda tsabar ƙauna" Ta murguɗa baki ta juya ta ajiye kayan, murmushi ya gaza barin fuskar sa. Ya ce "Kin san me na tuna? Lokacin da ki ke yi mini wanka mu na Nigeria, sauran ki yi mini wanka a Agadez".

"Sai ka je gurin Gimbiya hamshaƙiya, farar fata da take biladama ta yi maka" Ta yi maganar ba tare da ta juyo ba. Ko da ta yi yinƙurin juyowa, sai jikinsu ya haɗu, sam ba ta san ya ƙaraso bayanta ba, saboda cikin takunsa mai kama da hawainiya ya ƙaraso. Dan sam ba shi da hayaniya ko karakaina. Ya saka hannunsa ya zagaye ƙugunta, ƙirjinta ya tsananta bugawa tsoro ya bayyana ƙarara a fuskarta.

"Ma viee banda dalilin soyayyarki, ta sarƙe ni ta ko ina ta hana ni motsi, da sai na saka an sa bulala an zane mini ke. Imam Hammad ki ke yi wa magana a haka? Ki yi mini magana cikin girmamawa, ki daina ɗaga mini murya" Ya yi maganar yana sunkuyo da fuskarsa daidai ta ta har su na jin numfashin juna. Yana murmushi ya ce "Na taɓa yi miki wannan kashedin, kin tuna?" Ya yi maganar yana kashe mata ido. "Dan haka ke za ki yi mini wanka a Agadez da ma"

"Ni ka cika ni ba na son irin wannan abin" Ta yi maganar kamar numfashinta zai ɗauke.

Ya cika ta ya bar ɗakin, ta zauna tana sauke numfashi.

*****

"Jamila ki yi bayani, na kasa gane kan wannan ciwon naki, na fara jin tsoro ki gaya mini me yake faruwa?" Ta girgiza kai ta ce "Babu komai" "Wallahi sai kin gaya mini, damuwarki ta yi yawa, ciwo ya ƙi ci ya ƙi cinyewa mene ne yake faruwa ki ke ɓoye mini" Mama ta yi maganar cikin tashin hankali tana zazzaro ido cikin fargabar abin da Jamilan za ta sanar da ita. Ta girgiza kai hawaye na bin fuskarta ta ce "Dan Allah Mama ki yi haƙuri ki ƙyale ni, ni babu abin da yake damuna"

"Wallahi Jamila sai kin gaya mini uban abin da yake damunki, mene ne yake damunki?"

"Ni ma ban sani ba" Ta yi maganar tana kuka mai ƙona zuciya.

"Wallahi kin sani sai kin gaya mini" Ta yi maganar tana ƙara zazzare wa Jamila ido.

Kawai Jamila ta yi mata shiru, ta ci gaba da sheshsheƙar kuka.

"Za ki gaya mini ko sai na shaƙe ki?"

Jamila ta girgiza kai ta ce "Ciki ne da ni"

Wata irin mummunar faɗuwar gaba ta ziyarci Mama, ta ja da baya ta dafe ƙirjinta, tana wani irin haki, tare da kallon Jamila cike da tsoro.

"Jaa..jam..jamilahh me ki ka ce? Ciki fa a ina? Kuma garin yaya?" Jamila ta ci gaba da sheshsheƙar kuka ba ta yi magana ba.

Mama ta shaƙe Jamila ta ce "Ki gaya mini uban waye ya yi miki ciki kafin na take ki na kashe, da ki janyo mini abin kunya"

"Ke Rabi, kina ina ne? Waye yake yi mini kuka, kuma maganar me na ji ana yi?" Muryar Baba ta katse ta. Da hanzari ta saki wuyan Jamila, ta ja da baya tana hararta cikin ƙunar rai. Ta yi ƙwafa ta fito daga ɗakin su Jamila.

"Me yake faruwa ne?"

"Babu komai, jikinta na shiga na duba"

Baba ya ce "Kuma shi ne take ta kuka haka? Ni na gaji da larurar nan ta Jamila, wannan banke-banken hayaƙin da ki ke yi mata duk ba ne ba"

Ta ce "To in sha Allah za mu je. Ka san mun je, mun kuma zuwa amma abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, amma za mu koma"

***** Nana ta tsaya tsuru da rigar nan a jikinta, ita kanta ta san ba dan albarkacin kaza ƙandagare kan sha ruwan kasko ba, ta san ba ta kai ta saka wannan rigar ba. Ta jikin mudubi ta hango shigowarsa, kayansa royal blue, kalar rigar jikinta.

Ya ƙaraso gabanta, ya fesa mata turare, ya zura hannu a aljihunsa, ya ciro zobuna da abin hannu ya saka mata. Ta yi ƙuri da ido tana kallon hannun nata, rabon da ta sanya wani abu na ado, har ta manta. A tsorace ta ce "Ni dai zan cire wannan abin tsoro nake ji" Banza ya yi mata ya gyara zaman mayafin rigar a kanta. Ya din ga ƙare mata kallo yana mamakin yadda Asal take aibata Nana da muni, dan kawai baƙar fata ce. Idanunta manya sexy eyes, farare ƙal da su, gwanin ban sha'awa, ga shi rigar tamkar dan jikinta aka yi ta.

Ya numfasa ya ce "Ina ƙara tuna miki, duk wani abu da za a tambaye ki, kar wanda ya baki tsoro, kar kuma ki rufa komai, muddin ki na son Muhsin ya dawo hannunki"

"Meyasa kai ba za ka yi musu bayani ba kawai?"

"Da bayanina ya wadatar, ba zan bari a zo wannan gaɓar ba". Ya ciro niƙab ya saka mata. Sannan ya saka hannunsa ya ciro wayarta daga aljihun rigarsa.

Nana ta waro ido ta ce "Wayata, ya aka yi ta zo hannunka? Dama kai ka ɗauka?"

"Eh ni na ɗauka, kin ƙi saurarata, balle na yi miki bayanin komai, mu je" Ya yi maganar yana nuna mata hanya. Bakinta fal magana, amma ya yi mursisi, ya yi mata shiru. Ta tarar da takalma a falon gidan. Nana ta din ga ganin abin tamkar a mafarki.

Su na zaune a baya ita da shi, ana jan su a motar. Ta yi shiru tana zabga addu'a Ubangiji Allah ya bata nasarar karɓar ɗanta, dan ko kaɗan ba ta sha'awar gidan nan, ɗan zamanta a gidan kawai ta fuskanci akwai kitimurmura a gidan.

Tun da aka doshi gidan gaban Nana yake tsananta faɗuwa, haka kurum take jin ba ta ƙaunar gidan. Gefe guda kuma Nana tana ta tunanin halin da Ƙaisar yake ciki.

Tun da aka yi parking suka fito, hadimai suke gaida Imam Hammad yana ɗaga musu hannu. Ya riƙe hannun Nana yana ratsa cikin gidan da ita. Gaba ɗaya aka zubo musu ido, ana son sanin wacece wannan ya riƙo hannunta, saboda kowa ya san ba Asal ba ce, saboda ba ta kai Asal tsawo ba, kuma Asal ba ma'abociyar niƙab ba ce, ko kanta ma ba ta damu da rufewa ba.

Jikin Nana ya hau rawa, bayan da suka shiga ɗakin zama na musamman na cikin fadar Sultan. A can suka tarar da Sultan ɗin, ga Matawalle ga Sardauna, su na jiran isowarsu. Nana ta ja ta tsaya jikinta yana wata irin rawa, har ƙafafuwanta, gabanta ya din ga faɗuwa. Duk ta kowacwa kusurwar ɗakin, akaai na'urar sanyaya ɗaki, amma Nana ta kasa gane wane irin yanayi ma take ji.

Ya kalli Nana ya ce "Ki nutsu mana, kar ki ji tsoro, dan Allah kar ki yi wani abu da zai rusa mana rayuwa, kar haushina da ki ke ji, ya sanya ki makance, ki yanke mana hukuncin da zai cutar da rayuwarmu" Nana dai ta gaza ko ƙwaƙƙwaran motsi.

Ya ja hannun Nana, suka ƙarasa tsakiyar ɗakin suka zauna. Duk suka zubo musu ido.

Sardauna ya yi wa Nana alama da ta cire niƙabinta. Ta saka hannu ta cire tana sunkuyar da kai.

Abdou matawalle ya ce "Wannan kamar na taɓa ganinki ko?" Nana ta sunkuyar da kai.

Sardauna ya dube ta ya ce "Ya sunanki?"

"Nana Asma'u" Ta yi maganar kanta a sunkuye.

"Daga ina ki ke?"

Ta ce "Nigeria"

"Kin san wannan?" Ya yi maganar yana nuna mata Imam,Nana ta ɗaga kai ta kalli Imam, ta kalli Sardauna, ta sunkuyar da kai.

Matawalle ya ce "Ki yi magana mana, kin san shi?"

AREWABOOKS

Nana ta kalle shi, ya kalle ta, ya tsare ta da idanunsa, yana jiran ya ji me za ta ce.

Abdou matawalle ya ce "Mu za ki kalla ki yi wa bayani. Ke ba ke muka gani cikin waɗanda suka kawo abinci ranar da aka yi taro ba?" Ta jinjina kai alamar eh.

"To kin san shi ne dama?" Ya sake jefo mata tambayar.

Ta jinjina kai. Sardauna ya ce "Ki buɗe baki ki yi magana mana, ki daina amsa mana da kai".

"Eh na san shi"

"Waye shi a gurinki?"

Ta yi shiru tana nazarin amsar da za ta bayar, kar ta zama ta kwafsa su hana ta ɗan ta. Cike da karaya ya sake kallon Nana ya ce "Ma viee, talk ki yi magana mana"

"Ni sai na ga Muhsin zan yi magana, dan Allah ka fara nuna mini ɗa na"

Ya ce "To shikenan"

Ya ce "Ina neman alfarma, zan saka a kawo mata Muhsin, za ta yi magana"

Matawalle ya ce "Wane irin abu ne wannan? Ta san a gaban su wa take kuwa?"

Sardaunan Agadez ya ce "Bari Matawalle, a saka a kawo shi, mu ji me za ta ce"

Sardauna ya ciro wayarsa yana ɗan taɓawa, yana satar kallon Nana.

Sultan kuwa rasa abin yi ya yi, ya tuna fuskarta a gurin taron cin abinci da aka yi, ya so ya bibiyi me ya kawo baƙuwa wannan gurin, amma abubuwa suka sha kansa. Wani irin gumi ne yake tsatstsafo masa bayan tuna irin taɓargazar da Hammad ya aikata, ka iya janyowa. Babban abin da ya ƙara sanya masa fargaba, shi ne abin da yake iya gani daga idanun Hammad a kan yarinyar. Ko a yanzu ya tattara hankalinsa a kanta, ta sunkuyar da kai sai zubar da hawaye take, da alama ma tamkar ya manta da zamansu a gurin.

Wata hadima ce ta shigo, hannunta ɗauke da Muhsin. Yana ganin Nana, ya yi wani irin zillo daga jikin hadimar, yana wata irin ƙara yana cewa "Naaa" kamar yadda yake kiranta, Nene kuma ya ce mata umma"

Nana ta yi wata irin zabura ta nufe shi da gudu ta ɗauke shi, ta ƙanƙame shi a jikinta, tana zubar da hawaye cikin damuwa da kewar tilon ɗan nata. Shi na Muhsin ɗin, ƙanƙameta ya yi ya fashe da kuka.

Jikin Sayyid ya yi sanyi sosai, ya din ga jin abin da ya aikata bai kyauta ba, kamar ya shiga hakkinsu da yawa, amma babu yadda ya iya ne, hakan ne kawai masalaha a garesu baki ɗaya.

Sultan ya kalli Abdou matawalle suka haɗa ido, suka mayar kan Nana da ta durƙushe a gurin tana ta uban kuka.

Matawalle ya yi gyaran murya ya ce "Wannan yaron wane ne shi a gurinki?"

"Ɗa na ne" Ta faɗa cikin kuka.

"Shi kuma wannan fa?" Ya nuna mata Hammad.

"Mijina ne" Ta furta cikin sanyin jiki.

"Waye baban yaron naki?" Ya sake tambayarta. Ta kalli Hammad ta ce "Shine"

"Kin tabattar shi ne mahaifin yaron nan, kuma ke ki ka haifi yaron?"

Ta jinjina kai ta ce "Na tabattar"

"Ya aka yi ku ka haɗu ku ka yi aure?"

Ta numfasa ta ce "A Nigeria muka haɗu, a can muka yi aure"

"Waye shaidarki cewa mijinki ne shi?"

Takaici ya fara kama Nana, wace shaida kuma bayan wannan ɗan wata shaida suke nema?.

"Ni ba ni da wata shaida, Allah ne shaidata sai babana da ya ɗaura mana aure."

Sardauna ya ce "Yaya aka yi mahaifin naki ya aura miki wanda bai san daga inda yake ba, ko ku ƙasarku ba ka bincike ku ke aure?"

Jiki a sanyaye Nana ta ce "Ana yi, akwai 'yan uwansa da suke gadi tare, sun san aure muka yi, su Habu"

Matawalle ya ce "Ban gane gadi ba, gadi kamar yaya?"

Hammad ya ce "Ina neman alfarma dan Allah a tsagaita yi mata tambayoyin nan haka, duk a rikice take. Ga wannan wayar akwai video da hotuna a ciki, lokacin da muna rayuwa ne da ni da ita a Nigeria"

Sulta ya ce "Hammad, ya zama dole ka yi mana shiru, a kammala binciken da yakamata, domin tabattar da gaskiyar lamarin nan"

Sardauna ya sake kallon Nana ya ce "Ya aka yi ki ka zo gidan nan yin aiki?"

Ta haɗiye yawu ta ce "Mu na Nigeria lokaci ɗaya na nemi 'yan uwansa na rasa, ya haɗu da larurar zuciya, ina tsaka da jinyarsa na neme shi na rasa. Kawai na yanke shawarar na zo Nijar ko zan haɗu da shi" Mamaki ya kama Hammad, yadda kai da fata taƙi bayanin ainihin ciwon da ya din ga yi bayan hawan jini.

Matawalle ya ce "Ya aka yi da ku ka haɗu ba ki sanar da kowa mijinki ne ba? Kuma me yasa wacan karon da ya kira ki a nan, ki ka ce ba ki san shi ba? Anya akwai ƙamshin gaskiya a maganar nan?"

Imam ya ce "Wancan karon laifina ne, kuma gaba ɗaya a ruɗe take"

"Ba kai ake tambaya ba, ita muke tambaya" Matawalle ya katse Sayyid.

Cikin kuka Nana ta ce "Dan Allah ku yi haƙuri, ni ba na buƙatar na ci gaba da zama da shi, ku bani ɗa na kawai zan tafi na yi muku alƙawarin ba za ku sake ganina a inda yake ba"

Suka yi tsit suna kallon Nana, daga bisani Sardauna ya ce "Haƙiƙa idan ta tabatta kin auri Imam Hammad, to kun tafka babban kuskure mussaman shi da ya san ƙa'ida da dokar masarauta. Sai dai uzuri ɗaya za a yi muku, shi ne shi ya haɗu da larura, ke kuma ba ki san wannan ƙa'idar ba. Babban mai laifi shi ne Mahmoudu kuma sai ya haɗu da tsatsauran hukunci. Babu buƙatar mu ci gaba da bincike da wani bin diddigi. Daga nan za a ɗauke ki a kai ki gidan baƙi na musamman, ki huta kwana biyu zamu haɗa miki sha tara ta arziki, za kuma mu sanya a mayar da ke har ƙasarku. Imam Hammad dole zamu san yadda zamu juya wannan lamarin, mu ɓoye gaskiyarsa, idan haryanzu da aurenka a kanta, zaka sauwwaƙe mata zamu karɓi ɗanmu a mayar da ita Nigeria"

Wani irin mugun kallo Hammad ya yi wa Sardauna. Nana kuwa zabura ta yi tana ƙanƙame Muhsin ta ce "A'a Sayyid ne ɗanku, Muhsin kuma ɗa na ne, ba zan baku ɗa na ba, da shi zan tafi Nigeria"

Matawalle ya ce "Ba zai yiwu ba, mu zamu karɓi Muhsin ki yi haƙuri. Abu ne da muka daɗe mu na nema daga Hammad. Ki yi haƙuri dole mu kare kimarsa da mutuncinsa a Agadez"

Hammad ya miƙe a rikice, jin matakin da za a ɗauka, amma Sultan ya kira sunansa cikin ɗaga murya. Da ido aka yi wa hadimar nan magana, ta nufi Nana gadan-gadan za ta ƙwace Muhsin. Nana ta ƙara ƙanƙame shi tana kuka cikin ɗaga murya ta ce "Ba zan baku ɗa na ba, ku ƙyale mini ɗa na, baku san baƙar azabar da na sha kan na haife shi ba. Zan bar muku naku ɗan har abada nima ku bar mini nawa" Matar ta fi ƙarfin Nana, Muhsin na zunduma ihu, Nana na kuka ta fizge shi. Nana ta bita da gudu tana janta "Ki bani ɗa na, wallahi ba zan bar muku shi ba. Ba za a kassara rayuwarsa kamar yadda aka kassara ta Sayyid ba".

Wasu hadiman ne maza suka shigo, za su tasa Nana a gaba su fita da ita. Amma mugun kallon da Imam ya yi musu ya sanya suka tsaya. Ya ƙarasa inda Nana ta riƙe hadimar, ya saka hannu ya cire hannun Nana daga jikin hadimar da ta riƙe gam.

"Ka ce su bani ɗa na, kuna ina lokacin da nake gantalin nemanka ba ni da ko muhallin zama da tsohon cikinsa? Ka damu da ɗan naka, ka tafi baka sake waiwayata ba? Ka bani ɗa na na tafi na barku"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull