Buzu book 3 complete - Chapter 7
Buzu book 3 complete Chapter 7: Buzu book 3 complete Chapter 7. Idanunsa fal hawaye ya ce "Na sani, ki yi haƙuri Ma viee, ba a son raina ba komai ya faru…
3,372 words
Idanunsa fal hawaye ya ce "Na sani, ki yi haƙuri Ma viee, ba a son raina ba komai ya faru ki yi haƙuri ki saurare ni" Sai dai tamkar yana ƙara ziga ta, ta ci gaba da cewa "Na yi dana sanin saninka a rayuwata, soyayya da tausayi ba su amfana wa rayuwata komai ba. Da na san abin da zan tarar kenan da na zauna inda Allah ya ajiye ni ban fito neman ka ba. A kan Muhsin zan iya karɓar Ƙaisar da abin da yake so na aikata sai dai masarautar taku ta tarwatse" muryarta tuni ta fara dashewa, saboda ɗaga murya da kukan da take yi mai tsuma zuciya.
Matawalle ya ce "Imam wannan wace irin yarinya ce, mara ɗa'a da rashin tarbiyya? Kai ku fita da ita"
"Kar wanda ya taɓa mini mata, zan fita da ita da kaina" Ya yi maganar yana ɗaga musu hannu alamar dakatarwa.
Nana kuwa tuni ta silale jikinta ya saki, ya riƙe ta a jikinsa ba ta iya cewa uffan sai sauke numfashi da take yi kawai.
Sultan ya yi shiru, yana ƙara jujjuya lamarin a cikin zuciyarsa.
Imam da kansa ya saka Nana a cikin mota, ya babbake ya hana kowa ya taɓa ta. Ya rufe motar ya zagaya zai buɗe ɗaya ɓangaren ya shiga, amma wasu manyan hadimai suka tsare ƙofar.
Ya kalle su ba tare da ya yi magana ba. Ɗayan ya ce "Tuba muke yi, umarni ne daga sama, cewar kar a kuskura a bari ka bar gidan nan"
Cikin mamaki ya ce "Daga sama gurin wa?"
"Daga sama gurina, kar wanda ya bar shi ya fita ko ina daga gidan nan, har sai mun bayar da umarnin hakan, ku kaita inda muka yi umarni, za mu sanya a mayar da ita Nigeria. Ina sake jaddada muku, kar wanda ya kuskura ya bar Imam Hammad ya fita daga gidan nan sai mun ba da damar hakan" Sardauna ya yi maganar cikin bayar da umarni, aka ji motar da Nana take ciki aka fita da ita daga gidan.
Da ya san haka abubuwan nan za su kasance, da babu abin da zai hana ya ɗauki Nana da ɗansa ya bar musu ƙasar gaba ɗaya. Sai dai halin da Sultan zai shiga kawai yake tunani.
Cike da baƙin ciki da takaici, ya koma ya iske Sultan, gabansa ya je ya tsaya cikin tashin hankali ya ce "Me yasa za ka yi haka? Idan ni ne a matsayin da take za ka so a yi mini haka? Ka kalli lamarin nan a matsayinka na uba, ba Sultan ba. Dokar masarauta ba dokar addini ba ce ba. Me yasa 'yan majalissarka za su ziga ka ka yi haka? Babu wata hujja da ake buƙata domin tabattar da Asma'u matata ce, Mahmoudu su suka ɗaura mini aure. Shi ma kun ce a kulle shi ya yi laifi. Aure muka yi da Nana ga yarona ku na gani me yasa za a raba ta da ɗanta kuma a mayar da ita Nigeria haba Abie"
"Hammad, ni ka zo gabana ka tsaya ka na gaya mini magana a haka saboda mace? Dole ne mu girmama tare da martaba al'adun masarautar nan, mu samu mu binne babban kuskuren da ku ka aikata ko dan tsira da mutuncinka.
Hammad ya girgiza kai ya ce "Sultan, Asma'u ba mace ba ce kawai, ba zan binne laifukana saboda al'ada na je lahira ba ni da abin da zan gaya wa Allah ba. Zan ɗauki matata na bar ƙasar nan gaba ɗaya. Na bar muku sarautar da al'adar. Da na rayu babu su ma babu abin da ya same ni, ka gafarce ni"
Mari Sultan ya kifa masa, ya janyo rigarsa yana kallon sa ya ce "Ko ka fara shan wani abu ne Hammad? Ni ka ke gaya wa ka bar mana sarautar za ka ɗauki wata bare ka bar ƙasar nan?"
Jiki a sanyaye ya ce "Ba bare ba ce ba, matata ce kuma akwai ɗa a tsakaninmu. A halin yanzu a Duniya bayan kai ba na tunanin akwai wani wanda zai iya yi mini abun da ta yi mini. Gaskiyar da ba ka sona faɗa Abie ina tare da baƙin aljani, da yake burkita ni. Nana na iya ganinsa kuma itakaɗai take iya fahimtar halin da nake ci. Abie Nana ba mace ba ce kawai, waliyya ce a cikin mata, har shanyewar ɓarin jiki na yi, lokacin da ku ka gano su Mahmoudu aka ɗauke su, ba ta da wani mataimaki sai Allah kuma ba ta taɓa gajiya da ni ba. Asma'u har najasata ta wanke da hannunta. Da jikinta da lafiyarta da lokacikta da zuciyarta ta rayu da ni cikin kulawa da tausayawa. Idan na bari aka yi amfani da rashin gatanta saboda ni shafaffe da mai ne aka cutar da ita ban yi wa kaina adalci ba. Tsakanina da ita ba alaƙa ce gangar jiki ba kawai, akwai tasirin ruhika, da kuma tasirin alaƙar uba da ɗa. Wannan wani abu ne da ni da ita ne kawai muka sani. Abie ba za ku iya raba ni da Asma'u ba, idan ma ku ka raba mu, sai kun nemo ta da kanku" Ya ƙarasa maganar yana ja da baya ya fice ya bar ɗakin.
Sultan ya dafe gaban goshinsa da yake yi masa wani irin raɗaɗi, ya nemi guri ya zauna. Duk yana jin maganganun Hammad a matsayin soki burutsun neman mafitar yadda zai samu ya zauna da Nana. Shi ma yana ganin ba a kyauta ba, a ƙwace mata yaro kuma a kore ta.
Asal kuwa tana can ta gigice, bayan da ta samu labari cewar, an ga Hammad da wata mata ya riƙe hannunta sun shiga sashen Sultan. Ta rasa wa zata dosa domin ta ji gaskiyar lamarin.
Tana cikin wannan gigitar, Tafawa ya kira ta, ta ɗaga jikinta yana ta tsuma.
Ya ce "Asal, wace hadima ce a gidanki, ta kai abinci lokacin da su Asad suka zo?" Sai ta manta me ma ake nufi da hadima, sai da ya yi mata tsawa sannan ta farga ta ce "Wata hadima ce a gidan nan. Ce mini a ka yi an ga Imam Hammad da wata ya riƙo hannunta sun shiga sashen Sultan, ko ka na da labarin wace ce?"
Ya ja tsaki ya ce "Sai me kuma? Ina tambayarki ki na tambayata wani abu daban."
"Abbu dan Allah ka gaya mini idan ka san wani abu, ka ga ka ce mini ya ce yana da ɗa, a tsorace nake"
Tafawa ya ce "Asal, kina nufin kina son Hammad ne?"
Cikin kuka ta ce "Abbu mijina ne fa, ko ba na son sa ina duba makomata nima" Sai dai tana rufe bakinta, Hammad ya banko ƙofar ɗakin da ƙarfin gaske. A razane ta saki wayar hannunta, ta waiwaya tana kallon sa. Da sauri ta tunkare shi tana faɗin "Hammad wace mata a ce an ganku kun shigo tare yau, har kana riƙe da hannunta kun shiga sashen Sultan? Kar dai maganar da aka gaya mini gaskiya ce?" Ko kallon inda take bai yi ba ya nufi kan gadonsa ya faɗa kai.
Ta nufe shi a hasale ta ce "Ka tashi ka yi mini bayani, wace matar a ganku tare? Kuma da gaske ka na da ɗa ko ba ka da shi? Yanzu da mutuncinka da kimarka ka zaɓi ka tozarta kanka ka kwanta da wata mace a waje dan ta haifa maka ɗa. Wallahi Hammad baka isa ba, ina yi maka rantsuwa da zatin Allah kowace matar ce sai na sanya an kashe ta, kuma an kashe mini banza dan duk cikin Agadez da kewayenta na san duk wata 'yar gata a bayana take. Ka tashi ka yi mini bayani"
Wuyanta ya damƙa, jikinsa na wata irin tsuma, gani ta yi gaba ɗaya ya canza ya koma kamar wani horo, jikinsa ya koma jajawurr tamkar tumatir. Babu baƙar ƙwayar idanunsa sai farar nan tas, duk wata jijiya da taje jikinsa duk sun kumbura. ya faɗo daga kan gadon yana burgima, saboda yadda yake jin tamkar wuta na ci a ƙasan fatarsa.
Tofa!
Ayshercool 08081012143.
Kar dai ku gaji da ni, ina yi muku tuni da cewar labarin Buzu ya shiga gasa a YouTube channel ɗin limamin tsakar gida, wanda da yawan likes na kashi goman farko za a yi amfani gurin alƙalanci. Ku taimaka ku je ku danna like a kashi goman farko na labarin BUZU na gode.
82 LITTAFIN KUƊI NE, KARKI RAINA GIRMAN HAKKI, 1K NE VIA 0069685771 Aisha Adam stanbic 08081012143 Hankalin Sultan da muƙarrabansa ya dunguzuma nesa ba kusa ba. Suka gaza gane kan Imam Hammad ta ko ina. Ga Muhsin shi ma yana ta rikici, ba ya cin abinci sam, sai koke-koke ya ƙi saurar kowa saboda rashin sabo.
Cikin tashin hankali Sultan yake kallon Hammad da yake wance kamar itace, ya dubi Matawalle ya ce "Anya Matawalle ba Asibiti zamu kai shi ba. Ina ga wannan ɓoye-ɓoyen da muke yi, lokaci ne ya yi da asirinmu zai tonu. Sai dai ina jin tsoron a san halin da muke ciki".
Matawalle ya ce "Wannan ba abin da ya shafi Asibiti ba ne, ko ka manta haka ya yi ta yi a lokacin da aka dawo da shi daga Nigeria? Sai da muka fita faransa sannan ya daina wannan abin,har tunaninsa ya dawo?"
Sultan ya ce "Haka ne, amma kamar wannan karon, abin ya ninka wancan da ya yi. Ba ya ci ba ya sha fa" Ya yi maganar cikin damuwa.
Matawalle ya ce "Nima abin da ya tsorata ni gaskiya, amma dole mu nemo masu magani da za su duba shi. Amma ya zama dole mu samo waɗanda ba za su furta komai ba, idan ba haka ba nan ma akwai matsala" Sultan ya dafe kansa yana kallon Hammad, tamkar ya fashe da kuka. Asal ta shigo ɗakin da sallama, ta kalle su ta gaishe su cikin girmamawa suka amsa mata baki ɗaya.
Cikin damuwa ta ce "Abie yau ma bai farka ba ko?"
Sultan ya jinjina kai ya ce "Bai farka ba Asal"
Daga nesa inda take tsaya take ɗan leƙa shi ta ce "Baccin dai yake yi?"
Matawalle ya ce "Ƙaraso ki gan shi mana"
Ta girgiza kai ta ce "A'a shaƙe ni yake yi ya kusa kashe ni, daga nan ma ina hango shi"
Babu babban abin da yake sake ɗaga wa Sultan hankali, sama da wannan azababben zafin da jikinsa yake yi mai ban tsoro, kamar ba jikin ɗan Adam ba.
Da yamma Sultan na cikin ɗakinsa, yana ta kai komo, ya rasa mene ne mafita, ya san muddin batun ciwon nan na Hammad ya fita, ba su da wata mafita.
Aka sanar masa da isowar Imam Zahradeen. Ya bayar da iznin ya shiga. Bayan shigarsa suka gaisa. Ya dubi Sultan ya ce "Abie, wai ko ka aiki Imam Hammad wani gurin ne? Ya saka ni wani aiki, na je gidansa Gimbiya Asal ta ce "Baya nan, kuma a iya sanina ban san ya yi wata tafiya ba"
Sultan ya ce "Haka ne, yana ƙarƙashin takunkumi na hana shi zuwa ko ina ne".
Ya ce "Na sani, ina son ganinsa ne, a yi mini alfarmar nan, wani saƙo zan isar masa na aikin da ya sanya ni"
Sultan ya dubi Zahradeen ya ce "Aikin me kenan?" Zahradeen ya sunkuyar da kai ya yi shiru. Sultan ya ce "Shikenan na fahimta, amma a yanzu dai ka yi haƙuri ba zaka samu ganinsa ba, yana ƙarƙashin takunkumi "
Imam Zahradeen ya ɗan yi jimm sannan ya ce "Shikenan, godiya nake ranka ya daɗe" Daga haka ya tashi ya bar sashen. Ya san iya takunkumin hana fita aka ƙaƙaba masa, banda na killace shi a hana ganinsa gaba ɗaya, amma lokaci ɗaya an ce har ganinsa ma ba zai yiwu ba.
***** Nana ce zaune ta saka kwanon abinci a gaba ta yi shiru, Nene ta taɓa ta ta ce "Ki ci Abincin mana, kin bari yana ta shan iska"
Nana ta numfasa ta ce "Nene wai zuwa yaushe zan je na karɓo ɗa na ne, ci gaba da zama fa bai kamace ni a garin nan ba, ni duk hankalina ya yi gida wallahi" "Nana na san duk abin da nake yi, ba na son ki faɗa komar mutanen nan, su ci moriyar ganga su yada kwaronta. Mutane ne masu bala'in son kansu fiye da yadda ki ke tunani, dan haka ki ɗan yi haƙuri. Sai dai Nene na rufe baki, wayarta ta fara ringing. Nene ta ɗauki wayar ta saka a kunnenta tare da yin sallama.
"Barka da wannan lokaci Ummana"
Ta amsa da "Barkanmu dai"
"Umma dan Allah Nana tana tare da ke ne? Idan ke ki ka ɗauke ta ki taimaka ki sanar mini inda ki ka kaita, kan Imam Hammad ya farga ba ta nan, wallahi ban san me zan ce masa ba"
Nene ta ce "Idan ya fargan me ya yi saura a tsakaninsu? Ba dai ɗanku ba ne kun ƙwace? Takardar sakinta kawai muke jira, zan mayar da ita Nigeria har gidansu"
Mahmoudu ya ce "Ummana, wannan wani abu ne da ya shafi Nana da Imam da iyalinshi. Ni fa kamar ya san za a yi haka ya haɗa ni da Imam Zahradeen ya sanya aka killace ku a wannan gidan, kuma lokaci guda sai ki ɗauke ta ki tafi na neme ki na rasa. Dan girman Allah da buwayarsa ki taimaka ki gaya mini inda ku ke"
"Kai ka kiyaye ni, ba zan faɗa ba ɗin, ba ku da wani haɗi da Nana, ka gaya wa ubangidanka ya aiko mini da takardar yarinyata, zan mayar da ita gaban iyayenta ta nemi gafararsu" Ta katse wayar.
Nana ta ce "Nene to idan ya sake ni ba su bani Muhsin ɗin ba fa?"
"Shi Muhsin ɗin da shi aka haife ki ne?"
Idon Nana fal hawaye ta ce "Ni dai a bani ɗa na kan ya sake ni"
Nene ta girgiza kai ta ce "Nana kina cikin jarrabawa, wannan ɗan shi zai sanya ki lalata komai ki kasa ƙwatarwa kanki 'yanci, ai sai ki yi"
Nana ta ɗan ɓata fuska ta ce "Amma Nene, ya aka yi aka saki Mahmoudu na ji sun ce wai sai sun hukunta shi, sun ɗora masa laifin aurenmu, sun sake shi kenan sun fasa hukunta shi?"
Nene ta ce "Oho musu, su kashe shi ma kar su bar shi da rai."
Nana ta waro ido ta ce "Nene wai ke ba kya son ɗan nan naki ne?"
"To Nana idan ma ina son nasa, zan goya shi ne?"
"To Nene dama mutum yana daina son ɗansa ne?"
Nene kawai ta yi murmushi, ta tashi ta bar Nana da wasi-wasi.
*****
Wasa-wasa aka shafe kwana uku curr ba a ga 'yar gidan Doctor Sharif ba, ga matarsa a Asibiti, hankalinsa ya tashi kamar zai haukace. Ga jikin matarsa kullum babu afuwa ga shi ta fara damuwa da ina Hafsa take. Sai dai ya ce mata tana gida ba ta da lafiya. Ya din ga yawo gurin 'yan sanda da gidajen radio, yana bayar da cigiya ko za a ganta. Ya din ga jin tamkar ya ɗora hannu a ka ya zunduma ihu. Gefe guda ga mummunan mafarkin da yake yi da Shukura babu ƙaƙƙautawa har fargabar kwanciya bacci yake yi. Saboda munanan mafarkai ne marasa daɗi.
Ya shiga Asibiti ya tarar da wata katoɓara, an yi wa matarsa insulin allurar sauke sugar, fiye da kima suganta ya yi mummunan sauka, har ta shiga shock. Tare da sauran abokan aikinsa likitoci, suka yi ta fafutuka ƙoƙarin ganin sun ceto ranta. Yana tsaka da wannan tashin hankalin 'yan sanda suka kira shi, ya tafi cike da fatan 'yarsa Hafsa aka gani. Sai dai 'yan sanda suka ce masa Asibiti za su je ya ga wata yarinya da aka tsinta aka kaita domin a duba lafiyarta. Suka ɗauke shi a mota suka tafi. Sai dai suna zuwa aka tafi da shi ɗakin adana gawarwaki. Sam bai kawo komai a ransa ba, idonsa ya rufe kawai Hafsansa za a nuna masa. Sai dai aka fito da gawarwaki biyu. Ɗaya a kango a ka tsince ta, an fafe cikinta an kwashe wasu sassa na jikinta a can wata unguwa. Yarinyar sanye da Uniform ɗin makarantar da ya fasaltawa 'yan sanda. Tamkar ba Namiji ba, haka ya kurma uban ihu ya faɗi ƙasa sumamme, bayan ganin 'yarsa Hafsa a wannan mumman yanayi.
Bangaren Sagir ma bai fitar da rai ba, yana ta addu'a, da ji a jikinsa Yusransa za ta dawo. Ga shi satin haihuwarta ya kama. Ya daure ya lallaɓa ya je duba Yusra. Wadda ita ma jiki yake a rikice. Sai dai da yaje ya tarar da jikinta da ɗan sauƙi, dan har suka ɗan fara hirar hankali. Ta ce "Haryanzu ba a ga matarka ba ko?"
"Haryanzu Yusra, amma kina yi mata addu'a Allah ya bayyanata?"
Ta ce "Ina yi mana, ina so Allah ya sanya a ganta, kuma fa a satin nan za ta haihu, dan ta ma fara naƙuda kaɗan-kaɗan"
Ya ce "Yaya aka yi ki ka sani?"
Ta ce "Mafarkinta na yi mana, tana kulle a wani ɗaki mai duhu, ta ce mini ba ta jin daɗin zaman gurin, baka gani ba abin tausayi"
Idonsa fal ƙwalla ya ce "Duk a mafarkin ki ka ga haka?"
"Eh mana, tana ta kuka ma"
Ya ce "Shikenan, ya isa haka. Ki ci gaba da yi mata addu'a bari na je gida. Amma yaushe za ki zo mu koma gida, ina fama da kaɗaici"
Ta ce "Ko yau ka yi wa Anty magana sai na bika mu tafi"
Ya jinjina kai ya ce "To shikenan, babu laifi"
Shukura kuwa tana kwance a ƙasa, zama babu daɗi, kwanciya babu daɗi duk inda ta motsa cikin nan sai ya tokare ta. Ga ciwon baya da na ƙafafuwa da take yi da take kyautata zaton naƙuda ta fara a tsaitsaye. Sai dai tana yawan ganin Nana cikin mafarki, tana nanata mata ta yawaita addua babu ƙaƙƙautawa babu ji babu gani. Duk da tana yi ɗin amma ta ƙara ƙaimi gurin yi.
***** Ko da aka shiga kwana na biyar da shigar Hammad halin da yake ciki, Sultan ya gama tsurewa babban tashin hankalinsa rashin cin komai da ba ya yi ga abin kullum gaba yake yi. Tafawa ya samu Sultan a kan lallai a sake zaman majalissa, a ji bayanin Hammad a gaban kowa da kowa a kan yadda aka yi yake da ɗa kamar yadda ya faɗa."
Matawalle ne ya amsa masa da cewar "A tunanina wannan maganar ai ta wuce ko?"
"Ta wuce ta je ina? Kun san zata wuce ku ka dakatar da ni daga majalissa. Ya faɗi abin da dole sai ya fito ya kare maganar da ya yi. Ya ce yana da ɗa, ina ɗan yake? Kuma wacece uwar yaron? Idan kuma shaci faɗi ne to ta tabatta ba shi da lafiyar ƙwaƙwalwa da na faɗa ku ke ɓoyewa"
Matawalle ya ce "Imam Hammad ba mahaukaci ba ne ba, ka san abin da zaka din ga furtawa a kansa, ko babu alaƙar jini a tsakaninku shi shugaba ne."
"Eh Hammad ɗa na ne, kuma shugaba ne, amma ba zai yiwu na zuba ido ina ganin ba daidai ba, a ce yana shugaba babu cikakkiyar lafiya ba kuma ku na dannewa ku ɓoyewa ba. Ita larura ai ba abin kunya ba ce, kuma abu ne da yakamata a sani domin a nemi lafiya"
Cikin nutsuwa Sultan ya ce "Imam Hammad ba mahaukaci ba ne ba, ban sna meyasa ka ke aibata shi da da wannan larurar ba"
"Allah ya taimake ka, idan ba haka ba ne, mene ne gaskiyar batun ɗan da ya ce yana da shi?" Tafawa ya yi maganar yana tsare Sultan da ido.
"Abu ne da muke kan bincike a kai, koma mene ne zaka ji daga baya"
Ya ce "Shikenan na ji wannan, ina son zan yi magana da shi, magana ce a kan ɗiyata Asal"
Sultan ya kalli Tafawa cike da takaici, ya san yana sane yake wannan bin ƙwaƙƙwafin da bin diddigin a kan lallai sai ya ga Hammad."
Sultan ya ce "Za ka gan shi, amma nan da wani ɗan lokaci" Hakan ya sanya Tafawa sake tabattar da maganganun Asal. A ransa ya ce "Idan ka san wata baka san wata ba Jalaludeen"