Kenza eBookz

Buzu book 3 complete - Chapter 8

Buzu book 3 complete - Chapter 8

Buzu book 3 complete Chapter 8: Buzu book 3 complete Chapter 8. ***** Tun washegarin dawowar Nana daga gidan su Hammad, yanayin jikinta take jin babu daɗi,…

3,368 words

***** Tun washegarin dawowar Nana daga gidan su Hammad, yanayin jikinta take jin babu daɗi, kamar akwai wani abu mara daɗi da yake faruwa. Sai dai ta danganta hakan da kewa da kuma tashin hankali da take ciki a kan Muhsin. Amma idan ta nutsu sai ta ji wannan damuwar daban ce, wannan a cikin jikinta da ruhinta take jin damuwar, sai dai ta yi iya ƙoƙarinta gurin danne damuwar, da duƙufa da addu'a Allah ya dawo mata da ɗanta. Yau da safe Nana ta fito ta tarar da Nana, ta ɗora tukkwane daban-daban har uku a kan murhu, tana ta harhaɗa wasu irin saiwoyi da sassaƙe-sassaƙe tana ta zubawa tana dafawa. Nana ta ce "Umman Muhsin, yau kuma baya aka tuna wa ake dafa wa magani" Nene ta yi murmushi ta ce "Ba kula ki zan yi ba ai ki ƙarata, daɗin abin ƙwaryar sama ce ke dukan ta ƙasa daga ni har ke" Nana ta yi dariya ta ce "Yasin ni ban bayar da magani ba" "A'a tuna dai, tuna dai yarinya" "To ai Sayyid kawai na yi wa" Nene ta ce "Kash, an zo gurin dan haka ki yi mini shiru" Ta ƙarasa maganar tana janyo wayarta da ta yi ƙarar shigowar saƙo. Ta tsuke fuska ta kira Mahmoudu a waya. Ya amsa tare da gaishe ta. Bayan ta amsa ta ce "Wannan uban kuɗin fa da ka sako mini?"

"A'a ki yi haƙuri ai ba naki ba ne, na kula da Gimbiyar Imam ne"

"Da can ku kuke bani abin kula da ita? Lokacin da take gararambar neman taimakon ba ku neme ta ba ba barin ta ku ka yi tana gantali a titi ba?"

Ya ce "Dan Allah ki yi haƙuri, ba zan iya gaya masa haka ba. Haryanzu fa ma ni ban sake ganinsa ba tun ranar da ya je tare da ita. Ba ya gidansa baya fitowa zaman majillisa, ko hawa ba ya fitowa. Duk da na san an saka masa takunkumi shige da fice amma an tsaurara masa sosai. Ki yi haƙuri har gida za mu zo ban haƙuri. Dan Allah ki taya mu rarrashinta dan ta ƙi saurararsa gaba ɗaya, kuma wallahi hankalinsa a tashe yake nesa ba kusa ba. Ga tarin magauta da yake da su a cikin gidan su ma da ba barinsa suka yi ba. Dan Allah ku yi haƙuri Umma ke kin san sha'anin gidan sarauta kin san komai" "Ni rabu da ni sai daɗin bakin tsiya, ai ko mutum zai danne ya yanka sai ka kare shi" Yayi dariya ya ce "Ai ɗanki ne, kin san ba zai aikata haka ba, tuba muke ranki ya daɗe. Wallahi ina ta faɗi tashin na gan shi ne ma, na san halin da yake ciki. Amma a ƙara ba wa Gimbiyar Imam haƙuri"

"A'a babu ruwana, idan ku ka zo kwa bata da kanku" Suka yi sallama ta kashe wayar.

Ta kalli Nana ta ce "Kafin ki yi wanka, fara ɗibar ruwan maganin nan, ki je ki yi wanka ki gama, sai ki yi wanka da shi. Ki fito ki sha wannan maganin sai ki karya. Nana ta ce "Shi kuma Nene na mene ne?" "Na tsarin jiki da kariya ne, saboda kariya ne" Ta yi maganar tana basarwa, tare da tsuke fuska dan kar Nana ta addabe ta da tambayoyi. Ganin hakan ya sanya Nana amsawa Nene, ba dan tana so ba.

*****

Mahmoudu ne ya iske Sultan a gurin shan iskarsa da yamma. Kasancewar shi ma ba shi da iyaka a shiga da fita a gidan Sultan, saboda Hammad, dan haka ganinsa ba wahala yake yi masa ba. Sai dai yau kasancewar Sultan shikaɗai ne, ya fi sakin jiki da shi.

"Barka da wannan yammaci Sultan"

"Barkanmu dai Mahmoudu, kuna lafiya?"

Ya amsa da "Alhamdillah. Alfarma nake nema daga gare ka Sultan"

"Ina sauraren ka"

"Dan Allah a yi mini izini na ga Imam Hammad ne.

Sultan ya numfasa ya ce "Hammad babu lafiya. Ta so muje ka gani"

Ya tashi cikin ladabi, ya bi bayan Sultan. Suka yi tafiya mai nisa a sashinsa, can cikin wani ɗaki suka je ya buɗe masa ɗakin. Cikin damuwa ya ce "Mahmoudu ya tabatta Hammad hauka yake yi, haukan ma irin wanda ban taɓa ganin kalarsa ba. Na ce ko a Nigeria da ku ka zauna ya yi irin wannan? Yanzu idan ka je kusa da shi zai iya shaƙe ka, tsawon wannan lokacin bai ci abinci ba, a haka kawai yake" Cikin tashin hankali ya ce "Yayi ciwo daban-daban, amma ban ga ya yi irin wannan ba, ina kyautata zaton mutum ɗaya ne ya san matsalolinsa ciki da waje, ya san bakin zaren wannan ciwon nasa" "Wane ne? Mahmoudu ba ma son asirinmu ya tonu fa" "Da asirinmu zai tonu da tuni ta tona, sai dai a zo da Mahaifiyar Muhsin"

AREWABOOKS

Cikin rashin fahimta Sultan ya ce "Ban gane me ka ke nufi ba?"

Cikin girmamawa ya ce "Matarsa da ya zauna da ita a Nigeria, saboda ni kaina na fuskanci wasu abubuwa masu ban mamaki a tsakanin su, bayan sun yi aure." Ya yi maganar yana kallon inda Imam Hammad yake ta mimmiƙewa yana kakari, kamar ana yanka rago. Cikin damuwa ya ce "Yanzu tun wancan lokacin a haka yake?" Sultan ya jinjina masa kai ya ce "Ko ruwa bai sake sha ba, hankalina a tashe yake. Ga Tafawa ya sako ni gaba a kan Imam Hammad sosai da sosai; Yanzu dai mu je ka yi mini bayani gwari-gwari na fahimta"

Bayan sun fito, suka zauna tare da Mahmoudu. Mahmoudu ya numfasa ya ce "Idan ban manta ba, bayan mun dawo daga bikin buɗe gidan cin abincin Imam na Maraɗi, mun dawo ka sanar masa da batun tafiya Damagaran ya wakilceka a taron sarakuna da za a yi a Zinder. Ba zan manta ba an kai ruwa rana sosai a kan tafiyar. A tsukin lokacin ya kan gaya mini cewa, shi gaba ɗaya ji yake yi baya ƙaunar zaman ƙasar nan, yana jin kamar a cikin wani bala'i da masifa yake. Da fari na zata da wasa yake yi, amma sai na fuskanci da gaske yake a lokacin. Na ce masa mu sanar maka ko ɗaga tafiyar za a yi, amma ya ce mini a'a kar na gaya wa kowa, baya son ya ɗaga wa kowa hankali. Tare muke kwana da shi a cikin gidan nan, muna shirin tafiya , kawai ya ce mini na same shi a ɗaya gidan nasa na kusa da gidan tarihi da yamma, mu yi tafiyar. Na ce masa mu tafi tare amma ya ce mini a'a.

Haka kurum bayan tafiyarsa hankalina ya ƙi kwanciya. Kawai na kira shi na ce masa yana ina? Ya ce mini ya tafi zagaye can wajen gidan adana kayan tarihi na Agadez. Kawai na hau raƙumi na bi shi. Sai dai na je gidan adana kayan tarihi na tarar bayanan, aka kira ni da ɓoyayyiyar lamba, aka ce mini an san Imam Hammad nake nema, ya bi cikin sahara. Ba tunanin komai na kewaya bayan gidan inda Sahrar nan take. Na yi tafiya ta kai ta awa huɗu, saboda ina ganin sahun raƙumi a gurin. A tsakiyar sahara na ci karo da Imam Hammad cikin fita hayyaci a sume. Abin ya bani mamaki, na ciro shimfiɗa a jikin raƙumina, na yi na kwantar da shi na dudduba jikinsa na ga babu wata alama ta ciwo. Na jira ya farfaɗo ko na ɗauke shi mu koma gida. Cikin ikon Allah ya farfaɗo, na ce masa meyasa ya taho cikin sahara haka? Ko ba shi da lafiya ne?" Ya yi mini shiru. Na ba shi ruwa ya karɓa ya sha. Na ɗora shi a raƙumina ina mamakin yadda yanayinsa ya canza. Muka doshi dawowa, sai dai muna nufo Agadez ya din ga wani irin ihu, ya faɗi a cikin sahara daga kan raƙumin ya din ga burgima yana kururuwa. Na sauka na riƙe shi ina tambayar ko lafiya? Amma ba ya iya magana sai ihu kawai. Hankalina ya tashi na rasa yadda zan yi da shi. Da mun nausa cikin sahara sosai sai ya yi shiru da mun nufo gida, sai ya rikice. Na rasa yadda zan yi ga yamma tana yi. Ba zai yiwu na ɗaukko shi na taho da shi yana wannan kururwar ba kowa yana ganinsa. Kawai aka kira ni da ɓoyayyiyar lambar nan aka ce, kar na dawo Niger da Imam, idan ba haka ba zai yi hauka tuburan ƙarshe ya rasa ransa gaba ɗaya. Na tambayi waye amma ba a bani amsa ba a ka kashe wayar. Na din ga mamakin waye wannan ya kira ni haka? Kasancewar na ga alamun gaskiya a abin da aka faɗa, da na juya da shi yake rikicewa, kawai sai na nufi Nigeria da shi cike da fargaba da zullumi. Akwai abokan hulaɗarmu na Nigeria, da muke kasuwancin asuwaki da dabino wanda da yawa ba su san waye ni ba, kuma ba su san Imam ba, kawai sai na neme su a waya. Aka ci gaba da kirana da wannan lambar ana gargaɗina kar na saka a masarauta a san da abin da ya samu Imam Hammad, saboda za a ce dole sai an dawo da shi, idan aka dawo da shi kuma zai rasa hankalinsa da rayuwar sa. Haka na ɓad da kamanni da ɓoye waye Imam, na shiga da shi Nigeria muka fara neman magani. Sai ya shafe sati bai yi magana ba, ya manta waye shi gaba ɗaya. Sai dai aka ɓoye lambar asusu, aka din ga turo mini kuɗi cikin asusuna, na ci gaba da harkar safarar dabino zuma da asuwaki tsakanin Nijar da Nigeria, ina tsoron taɓa kuɗin da ake turo mini saboda ban san na waye ba. Sai dai duk gurin masu magungunan da muka je, sai su ce mu yi haƙuri ba za su iya ba shi magani ba. Mun je gurin masu magunguna daban-daban amma bamu samu magani ba. Ya manta komai nasa da ya shafi Agadez. Na samu wani gida da abokan hulɗata suke gadi, muka shiga cikinsu. Zai yi wanka zai ci abinci zai yi salla, amma ba zai yi magana ba sai jefi-jefi. Idan kuma abin ya juyo ba ya ko cin abinci ba ya magana. Sai dai gaba ɗaya al'amuransa sun ƙara rikicewa, ya din ga abu kamar yana gane-gane. Kwatsam aka kawo mahaifiyar Muhsin, ita kuma za ta din ga aikin rainon yaro. Duk lokacin da ya ganta ya kan ƙure ta da idanunsa kamar yana ganin wani abu a tare da ita. Sai da na taɓa tambayarsa ko ya santa ya ce mini a'a amma tana da wani abu da yake nema domin ya tuna waye shi. Tsawon wannan lokacin ban taɓa gaya masa waye shi ba, saboda fatana ya tuna da kansa kuma kar na yi wani abu, da asirinmu zai tonu ko a cutar da shi. Kwatsam! Ban san abin da ya faru ba, muka tarar da ita a sume a cikin ɗakinmu, daga ita sai shi. Babu alamun ya yi mata wani abu na cutarwa, sai dai an ce abinci aka bata ta kawo mana ta suma a ɗakin. Mahafinta ya ce ba zai yadda ba ya ce sai ya aure ta. Ba zan ɓoye maka ba Sultan mahaifiyar Muhsin yar masu ƙaramin ƙarfi ce. Aka din ga dambarwa babanta ya ce sai dai Imama ya aure ta. Ina ta lallaɓawa ina bayar da haƙuri, amma ya ce na biya masa sadakin. Ba ni da ikon yin jayayya da shi, dole aka ɗaura musu auren. Sai dai mai kirna a wayar nan ya kira ni, ya sanar mini da ya san batun auren da aka yi wa Imam Hammad. Tun bayan aurensa da ita, ya fara samun sassauci, ya dawo yana magana, wasu daga halayensa suka canza. Yana kishinta fiye da kima, yana sakin jiki da ita ya yi hira da ita, ya yi wasa da ita abin da ba ya yi ma a rayuwarsa ta nan. Na sani akwai abin da ta din ga ɓoye mini game da zaman da take yi da shi, duk da nima ban bayyana mata waye shi ba. Amma na san ciwon nan yana motsa masa, duk da na yi mata bayanin ciwon nasa amma iya abin da na sani. Sai dai har aka je aka ɗauke mu daga Nigeria bata taɓa nuna mini yana yin wani abu na irin wannan rashin lafiyar ba. Dan haka ko dai tana da maganin ciwon sa, ko kuma rufa masa asiri ta yi."

Sultan ya sauke wani irin nannauyan numfashi ya ce "Gaskiya na ji daɗi sosai da yadda ka rufa wasu abubuwan a gaban su Matawalle duk kusancina da su, akwai abin da ba zan so su sani ba. Amma ya aka yi ta san yana Agadez ta zo, nifa ina jin tsoron raɓa ɗa na da wanda zai cutar da shi"

"Allah ya taimake ka, neman Imam ne ya sanya ta baro Nigeria babu wanda ya sani ta taho da tsohon ciki Nijar. A hannun mahaifiyata ta zauna. Duk da ba komai na sani ba, bayan na baro Nigeria, a bakinta za a ji komai. Amma Umma ta ce mini, ta gaya mata rashin lafiya ya yi sosai bayan an ɗauke mu daga Nigeria"

Sultan ya jinjina kai ya ce "Kuma haryanzu baka san waye ya ɓoye lambar yake kiranka ba?" Ya girgiza kai ya ce "Ban sani waye ba, lokacin da aka rufe ni an karɓi wayata, da aka dawo mini da ita ma, ba a sake kirana ba" Sultan ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Shikenan, amm zan yi magana da Matawalle, a je a taho da ita, idan ma an mayar da ita Nigeria ne, duk inda take a Nigeria a nemo ta. Amma ko waye yake kiran nan naka, yana da masaniya a kan abin da ya same shi. Amma shikenan" Mahmoudu ya ɗan yi Jimm, yana tsoron a gano Nene ta ɗauke ta, dan kuwa ba ya tunanin an sake waiwayar Nana tun da aka ce a je a killace ta, dan da tuni sun farga an baza nemanta, ko dan kar ta je ta faɗi cewa ita matar Hammad ce. Sultan ya sallame shi ya tashi ya tafi. Sultan ya dafe kansa ya yi shiru, saboda yadda al'amura suke ƙara rincaɓewa. Duk tarin yaransa babu wanda yake tausayi kamar Hammad. Kuma yana burin Hammad ɗin ya gaje shi, amma shi ne wanda jarrabawa kala-kala take bibiya.

*****

"Nene, wai wannan naman da nake ta ci kashi-kashi na mene ne, ni gara ki bani hatsi kawai"

Nene ta ce "To mijinki ne ya turo kuɗin ciyar da ke, kin ga kuwa dole na baki ingantaccen abinci."

"Ni k ƙyale masa kuɗinsa, kawai lokaci nake jira idan ba ki yi wani abu ba, na je duk bala'in da za a yi, a yi a bani ɗa na, kan na basu mamaki wallahi. Dan ko zan mutu sai na raba su da shi"

Nene ta ce "Ba ma za ki mutu ba. Za ki karɓi Muhsin, ki koma ɗakin mijinki Gimbiya, ina jinjina lamarin Ubangiji Nana, ashe duk wahalar da ki ka sha, duk zaman da muka yi Gimbiya ce ke Nana"

Nana ta ɓata fuska ta ce "Dan Allah Nene ki daina, sai na ji wani banbarakwai, ni Sayyid nake so, ba Imam Hammad ba, ko kaɗan ba na sha'awar wannan gidan. Azabar tension ɗin da na sha a baya ma ta ishe ni, yanzu hutu nake buƙata"

Nene kawai dariya tana girgiza kai, ta ce "Yaro man kaza, Nana na taɓa soyayyar nan fa nima, ba za ki yi mini wani alaye ba. Amma ni da ke mun sha banban. Allah ya zaɓa abin da ya fi alkhairi ".

Nana ta yi shiru, gaba ɗaya magungunan da Nene take bata, bata taɓa kawo na mene ne ba. Gaba ɗaya tana kwance ta kasa bacci, sai juye-juye take yi, a jikinta take jin yanayinta ya ƙara canzawa fiye da yadda take a baya. Dama lallaɓa rayuwarta take yi a hankali. Shiru ta yi tana tunanin ko wani hali Muhsin yake ciki?. Sai kuma ta tuna ta ji wayar da Nene ta yi da Mahmoudu a kan cewa, an sanya wa Hammad takunkumin fita. Ta tafi tunanin tun daga wane lokaci ya gane ta, amma ya share ya nuna kamar bai santa ba. Guntun tsaki ta ja, ta juya zata gyara kwanciyarta. Ta fara jin wannan ƙamshin na ɗakin nan da take ganinta tare da Sayyid yana ratsa hancinta. "Ina fatan ba da ni ake wannan tsakin ba?" Ba shiri ta buɗe idonta, kamar yadda ta yi tsammani a ɗakin ta gan su sai dai ya rame sosai da sosai.

Tsiwa ta so yi masa, sai kuma jikinta ya yi sanyi ta ce "Ba ka da lafiya ne?"

"Lafiyata ƙalau, kewarki kawai nake yi, shi ya sanya rame" Ya tashi zaune ya matsa kusa da kta da ita ya rungumota jikinsa ya ce "Ma vie komai zai wuce in sha Allah, amma kar ki yanke hukuncin haƙura da ni, ba zan iya jurewa ba, ruhina da gangar jikina sun yi mugun sabo da ke, sabon da ba zan iya misalta miki ba" Ya yi maganar yana kwantar da kansa a kafaɗarta. Duk da wata zuciyar na azalzalarta da ta ture kan sa daga jikinta. Amma ya sake riƙo hannunta cikin sanyin jiki ya ce "Ki yi magana ko na ji daɗi mana"

"Sayyid, ci gaba da rayuwa da kai ba zai haifar wa tawa rayuwar ɗa mai ido ba, zaren ba kalar yadin ba ne, kuma sama ta yi wa yaro nisa" "Ban ma gane me ki ke nufi ba, ni duk wata rayuwa da zan yi. Nutsuwata da kwanciyar hankalina na tattare da ke Ma vie" Ta yi masa shiru daga bisani ta ce "Ni fa gaskiya ka yi mini nauyi, ka ɗaga ni"

Ya yi murmushi ya ce "Lokacin da ki ke so na, ba kya jin na yi miki nauyin, lallaɓa ni ki ke yi. Asmy"

"Na'am"

"Yanayin akwai zafi sosai, ina buƙatar sanyi"

"Ko fifita ba zaka samu ba, balle wani sanyi" Sai dai tamkar a zahiri, haka ya ci gaba da lallaɓa Nana, da daɗaɗan kalaman da sai da ta manta da fushin da take yi, ta saki jikinta da shi. Babu tsammani Nana ta farka tana ta ajiyar zuciya. Ta tashi ta zauna ta jingina da bango. Jin yanayinta abin da ya faru ta yi tamkar a zahiri ba mafarki ba. Ta daɗe ba ta yi mafarki makamancin wannan ba. Tana son sanin ainihin abin da yake faruwa take ganinsu a wannan ɗakin. Mararta ta ƙulle ta kifa kanta a kan gwiwoyinta, ta tsorata da ramar da ta ga ya yi, jikinta ya ci gaba da bata yana cikin damuwa. Ga abubuwan da ta gani a cikin gidan game da shi. Ƙarshe dai kasa komawa bacci ta yi, ga tunanin Ƙaisar da shi ma ba ta san halin da yake ciki ba.

Wayewar garin Allah, haka Nene ta sake zubowa Nana kajin nan da ɗuminsu sai ƙamshi suke yi. Nana tana ta lissafi da son yin gwajin ciki, domin tabattar da maganar Sayyid, dan sai da ta yi mafarkinsa jiya sannan ma ta tuna. Sai dai tana jin tsoro, ga shi tana jin Kunyar Nene balle ta gaya mata. Yaushe ma za ta fara bayanin ta na da ciki, cikin da ba ta san ya aka yi ya faru ba?. Tana cikin ɗaki tana cin naman nan, ta jiyo muryar Nene na waya. Mahmoudu ka kiyaye ni da batun Nanan nan fa"

"Dan Allah Umma ki yi haƙuri, zamu shiga matsala sun farga Nana ba ta nan, yanzu haka nemanta ake yi"

"Su neme ta, me ta yi musu?"

"Babu abin da ta yi, Sultan ne yake son ganinta"

"Sultan, ita ma za a yi mata abin da aka yi mini ɗin ne?"

"A'a Umma dan Allah ki yi haƙuri dai, babu wanda ya san inda take. Ni na ce musu na san inda take, yanzu masalaha suke nema. Wallahi an kasa gane kansa gaba ɗaya. Yau kwana na tara kenan yana sume ko ruwa bai shiga cikinsa ba. Dan Allah ki gaya mini kuna ina?" Gaban Nana ya yi wata irin faɗuwa, ta miƙe tsaye tana sauraren me Nene za ta ce.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull