Kenza eBookz

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 11

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 11

Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 11: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 11. Ya yinƙura ya nufo ta yana murmushi. Ta kawar da kanta gefe ta haɗe rai.

3,297 words

Ya yinƙura ya nufo ta yana murmushi. Ta kawar da kanta gefe ta haɗe rai.

Bai ce mata uffan ba, ya rungume ta yana ci gaba da murmushi ya ce "Ya aka yi ne?"

"Ni rabu da ni, bayan ka ƙi yi mini sannu" ta yi magana cikin shagwaɓa.

"Tuna dai, na yi miki fa, to yanzu ya jikin naki, me ki ke ji?"

"Ba komai"

"Kin tabatta?" Ta ɗaga masa kai alamar eh.

Ya zagayo da hannunsa, ya ɗora a kan mararta, ya sunkoyo daidai kunnenta ya ce "Hmm haka ne, na ji da sauƙi, na yi uzuri a wannan karon, amma idan aka ƙara zan ɗauki mataki"

Nana ta ce "Me aka yi da zaka ɗauki mataki?"

"Komai ma"

Ta yi murmushi ta ɗaga kai ta kalle shi ta ce "Har yanzu ba ka gaya mini sunan ka ba"

Ya yi dariyar da ta ƙara masa kyau, ya ce "Sunana ki ke son sani?" Ta jinjina masa kai alamar eh.

Cikin raɗa ya ce mata "BUZU"

"Buzu" ta maimaita a hankali tana buɗe idonta.

Shiru ta yi tana jin mafarkin da ta yi a ƙwaƙwalwarta, sai kuma abun da ya faru da ya rungume ta ɗazu, ya fara dawo mata. Ta nutsu sosai ta ga shi ma a mafarki abin ya faru. Ta ƙarewa ɗakin kallo, babu kowa a cikin sa sai ita kaɗai. Sai dai ta ji mararta ta daina ciwon, ta tashi ta ɗora ruwa ta yi wanka, ta gyara jikin ta, ta rasa abin da yake yi mata daɗi, ga shi ta kasa cin abincin. Dabinon da ya taɓa bata ta ɗaukko ta hau ci.

Bayan sallar magariba, ya shigo ɗakin da leda, kai tsaye ya tafi kusa da ita ya zauna. Ko kallon gurin da yake ta ƙi yi, saboda ta ji haushin yadda ya kasa kula ta duk wannan azabar wahalar da ta sha.

"Ki ci" ya yi maganar yana ajiye mata ledar.

Murguɗa baki ta yi ta ce "Ba na ci" ya yi shiru yana kallon ta. Ta kawar da kanta gefe tana ci gaba da ƙunƙuni. Ƙarshe ma ta tashi ta koma can gefe ta yi zamanta.

Ta ɗago ta ce "Ka ci ni na ƙoshi, ba zan iya girki ba, ba na son ƙamshin abinci" kawai ya yi shiru bai ce komai ba.

Ta kunna kallo a wayarta, tana yi tana cin dabinonta.

"Salamu Alaikum" suka ji ana sallama a wajen ɗakin.

"Wa'alaikum salam warahmatullah. Viens" ta ji ya amsa, ganin abin ta yi banbarakwai. Habu ne ya shigo da sallama fuskarsa ɗauke da damuwa.

Ya yi ajiyar zuciya ya ce "Hankalina duk a tashe, ya kira ni ya ce ba ki da lafiya, ba ki ci abinci ba tun safe" Nana ta waiwaya ta kalle shi, ya maze abin sa.

"Ta ina ya gaya maka?"

"Ta waya" Habu ya amsa mata.

Ta ɗan kwaɓe baki ta ce "Abin da ma bai ce mini sannu ba, kuma yana kallo na kusa mutuwa" Ayshacool Habu ya yi murmushi ya ce "Amma ya damu sosai ai, tun da ya kira ni kuma ya saka na tafi neman abin da za ki ci." Ya ajiye mata ledar ya ce "Ga abin da ya ce na sayo miki"

Ta ce "Ni idan bai ce mini sannu ba, ba zan ci ba"

Habu ya kalle shi yana murmushi, ya yi masa magana da french.

Ba tare da ya kalli Nana ba ya ce "Na faɗa ɗazu"

"Da yaushe?"

"Ki na bacci"

Mamaki ne ya cika ta, jin ya yi doguwar magana, dan haka ta yi yinƙurin jan maganar.

"Dama mutum ya san abin da ake yi ne, idan yana bacci, ni na ƙoshi"

"Sannu" ya faɗa a taƙaice.

Habu ya ce "Lallai abin mamaki, abin ya burge ni, ga kayansa nan an wanke an goge, tun da jikin naki da sauƙi, Alhamdilillah ni zan tafi"

Nana ta ce "Mun gode sosai, ka gaida gida"

"Allah ya sauwwaƙe ya ƙara lafiya" bayan tafiyarsa Nana ta ci gaba da kallo, ba tare da ta taɓa ledar da Habu ya kawo ba, balle wadda ya shigo da ita. Babu tsammani ta ji an fizge wayar hannunta, sai da ta tsorata, a fusace yake kallonta.

"Ki ci abinci" ya faɗa a hasale. Murmushi ne ya so kufce mata, amma a zahiri sai ta kwaɓe fuska kamar za ta yi kuka. Ya janyo ledar da ya fara shigowa da ita, ya buɗe ta kankana ce a ciki. Sai dai ta sha mamaki da ya buɗe ledar da Habu ya kawo ta ga gasashshiyar kaza. Ita dai ta san tsakiyar wata ne, a ina suke samo kuɗin da suke wadaƙa haka?"

"Ci" ta kuma jin muryarsa.

Sai kuma ta yi tsuru-tsuru ganin yadda ya yi mata kwarjini, saboda ya kafe ta da ido. Kamo hannunta ya yi ya ɗora a kan kankanar ya ce "Ci" kamar mara gaskiya ta ɗauka ta kai bakinta.

Duk da gefe guda hankalinta na kan kazar nan, har da haɗiyar yawu, saboda sai tururi take yi ga ƙamshi.

Ya tashi ya ɗauki kofi, ya tsiyayo shayi, a cikin butar shayinsa, ya zo ya ajiye a gefen sa.

"Ki ci" ya kuma maganar yana zaro mata ido.

Ba shiri ta tattarata nutsuwarta, duk santa da kazar, kasa sakin jiki ta yi ta ci, saboda tsoron yadda ya tsare ta da ido, sai dai tana iya hango tausayi da damuwa a cikin idanun nasa.

"Na ƙoshi" ta faɗa a ɗan tsorace.

Ya ɗauki ɗan ƙaramin kofin da ya zuba shayi, ya miƙa mata, a zaton ta shayi ne, sai dai tana sha, ta ji tamkar ta haɗiyi wuta. A take yanayinta ya sauya ta ji duniyar ta fara juya mata!

Ayshercool 08081012143 Ayshacool https://chat.whatsapp.com/FMI9ln54k8E3VhCaqgRAZq

Page 32

Gani ya yi ta rintse idanunta, jikinta ya fara karkarwa, mamaki ne ya kama shi, ya duba cikin kofin ya ga shayi ne a ciki. Ya kai bakinsa ya sha, shi bai ji komai ba.

Murƙususu take yi, a galabaice tana jin tamkar ana yayyanka kayan cikinta, ta yi wani yinƙuri sai ta fara aman jini mai yauƙi. Ta ɗauki lokaci tana yi. Ta ɗaga kai da ƙyar, ta ga Buzu a tsaye a kanta, kafin daga bisani ya rikiɗe mata zuwa wannan tsohon. A razane ta fara ja da baya. Ya ja da baya ya buɗe bakinsa, zai fara feso mata wuta, Ƙaisar ya bayyana yana wani irin huci.

Tsohon ya buɗe bakinsa yana dariya mai razanarwa, hayaƙi na fitowa daga bakinsa, ya ce "Na sani, na san za a rina, ta wannan hanyar ce kaɗai zan hukunta ka Ƙaisar"

Cikin tsawa Ƙaisar ya ce "Kuskure mafi girma da zaka aikata, shi ne cutar da yarinyar nan, cutar da uwar gijiyata tamkar cutar da ni ne, dan haka ni da kai muke wannan rigimar babu ruwanta, domin babu ta yadda za a yi ta biya bashin da ba ita ta ci shi ba"

"Ƙarya ne, sai ta biya shi, ita ce za ta biya ka sanya wannan a ranka. Ka fi kowa sanin ba ma yafiya, ba ma yafe bashin gaba, sai ta biya wannan bashin" ya ɗaga sandarsa ya nuna Nana da ita, amma cikin zafin nama, ta ji an yi sama da ita an watsar a guri ɗaya.

A hankali ta ja jikinta tana tari, ƙaisar ya bayyana a gabanta, cikin ɓacin rai ya ce "Ki sanya a ranki ba a yi komai ba, ƙalubale da tarkuna marasa adadi mun din ga faɗa musu kenan, idan mun tsallake wani, wani sai mun faɗa masa"

Nana ta ɗago kanta a galabaice ta kalli Ƙaisar ta ce "Wai dan Allah waye wannan tsohon? Me na yi masa, Ko shi ne na aura a suffar mutum ne?"

"Sanin waye shi, ba shi da wani amfani a gare ki. Ki yi ta kanki da rayuwar ki kawai. Ko dai ki bar wannan auren mu tsira baki ɗaya, ko kuma yanzu mu ka fara wahala".

Nana ta girgiza kai ta ce "Sanin waye shi yana da amfani a gare ni, waye shi? Meye alaƙa ta da shi da yake tsorata ni, laifin me na aikata masa yake iƙirarin sai na biya? Da wace hujjar zan kashe auren nan? Ko har ka manta irin ƙalubalen da na keto?"

Shiru Ƙaisar ya yi mata yana karkaɗe rigarsa, har ta buɗa baki za ta yi magana, ta jiyo sautin wata ƙara a bayan wata ƙofa, kuma ta ji tamkar ta san muryar da ta yi ƙarar.

"Ihun me nake ji haka?"

"Je ki duba mana" ya bata amsa yana yin gaba, ya nufi kofar da sautin ƙarar yake. Yana shiga Nana ta rufa masa baya, sai dai ta yi turus da ta ga Jamila a ɗaure a jikin wani itace, jikinta babu kaya, fatarta tamkar ta ƙone, ga wasu zarurruka da aka saka, aka ɗaɗɗaure ta da su.

Hankali tashe Nana ta ce "Kai Jamila, me ta yi maka? Meya same ta haka?"

Ƙaisar ya ce "Me ta yi mini ki ke tambaya? Me ya faru bayan kin ci abincin da ta kawo miki? Idan Alhaji Zailani zai kassara yaran da ya haifa a cikin sa, saboda duniya ke me yasa ki ke tunanin dan kun haɗa uba ɗaya da ita ba za ta cuce ki ba? Dole ta karɓi hukuncin abin da ta aikata, ko da kuwa ya kama na kashe ta ne.

Nana za ta yi magana ta ji ana taɓa fulon da take kai.

Ta buɗe idonta ta ga wani irin matsanancin duhu, babu alamar haske ta ko ina. Ta yinƙura ta tashi zaune, tana faɗin hasbunallahu wani'imal wakil.

Ta miƙe tsaye tana laluben hanya, ganin duhun na ƙara tsananta. Walƙiya aka yi mai tsananin haske, da ya gauraye ɗakin, ya bayyana tsaye da sandarsa yana kallon Nana. Rikicewa ta yi ta saka ihu. ta zabura za ta kasa da gudu. Tun da ta tashi tsaye a kan katifarta yake kallonta. Sai da ta yi ihun nan, ta nufi hanyar waje, ya miƙe da azama ya riƙe ta.

Fizge-fizge ta hau yi cikin matsanancin tsoro da razani.

"Me ya faru ne?" Ya yi magana cikin nutsuwa da kamala.

Fashewa ta yi da kuka, cikin rawar murya ta ce "Tsoro nake ji, dan Allah ka daina tsorata ni"

"Me na yi miki?" Ya yi maganar fuskarsa ɗauke da damuwa.

Ta ɗaga kai ta kalli kamilalliyar fuskar sa, ya lumshe idanunsa ya buɗe a kanta. Ta sunkuyar da kanta tana jin yadda sanyi yake ratsa ta, zuciyarta take bugawa, jikinta sai tsuma yake yi. Ayshacool * Da safe babu kowa a ɗaki sai Nana, ta shiga banɗaki ta yi wanka, ta gama ta buɗe ƙofar ta fito, ta ganshi yana gyara mata shimfiɗarta, ya karkaɗe mata. Ya ɗauki tsintsiya ya fara share ɗakin. Ya ɗago suka haɗa ido, ya kawar da kansa ya ci gaba da shararsa. Saboda daga ita sai zanin wankanta ta fito, dan ba ta san yana ɗakin ba.

Nana ta ƙaraso ta ce "Ka bari, zan share ɗakin, bari na shirya"

"Ba komai, ki huta ba kya jin daɗi" ta ɗan ware ido, jin ya yi magana.

Ta numfasa ta ce "Ina kwana"

"Wane kwanan?"

"Gaishe ka na yi fa" ya ɗago ya kalle ta ya mayar da kansa ya cigaba da shararsa, ya gama ya kwashe ya je ya zubar.

Ta shirya yana gefe yana aikin shan shayi, yana haɗawa da dabino yana ci.

Ta bubbuɗe kazar da Habu ya kawo, ta ɗumama, ta ɗibi miya ta haɗa su ta ƙara dafawa, ta zuba ta ajiye a gabansa.

Ya girgiza kai ya ce "Naki ne, ki ci"

Ta ce "Ai na ci, kai ba ka ci ba"

Ya girgiza kai ya ce "Na ƙoshi"

Nana ta sake tura masa kwanon ta ce "A'a ba ka ƙoshi ba, dan Allah ka ci" ta yi maganar tana saka masa cokali a kan kwanon. Ya kama cokalin, ya ɗan yagi kaɗan zai kai bakinsa ya ce "Bismillah" Nana ta ɗaga kai ta kalle shi da mamaki.

Jiki a sanyaye ta ce "Na san wataƙila ina yin wasu abubuwa, da za ka kasa gane kaina, kamar ba ni da hankali wasu lokutan. Na san babu lallai an yi maka bayani, ina fama da rashin lafiya ne" ta yi maganar tana wasa da yatsun hannunta.

Ya ce "Aa yau ba ki yi rashin lafiya ba, kin warke ai tun jiya" sai ta ga kamar bai fuskanci abin da take nufi ba.

Ta tsura masa ido, tabbas ma sha Allah, kyakyawan ne, fari ne mai dogon hanci sosai da ɗan siririn sajen sa, kuma a nutse yake. Babu babban abin da yake ɗaukar hankalinta game da shi, bayan nutsuwar sa, sai wannan kyakyawan dogon gashin da yake da shi, tamkar mace. Duk da ta kasa tantance abubuwa da dama a kansa, amma zuciyarta na ɗauke da tarin tambayoyin da take fatan bakinta ya furta.

Ya ɗago shi ma ya tsare ta da nasa idanun, yana tauna a hankali. Ta sauke nata idanun ta ce "Amm ban san sunanka ba haryanzu ba fa"

Kamar ba zai yi magana ba ya ce "Zan sha ruwa" tana mamakin dalilin da ya sanya yake kaucewa wannan tambayar har sau biyu, sai ta ƙyale shi, ta ɗaukko ruwan ta ba shi.

"To ka bani wayata, na yi kallo"

"A'a" ya furta yana tashi tsaye. ya tafi gaban mudubi, ya fara shiri. Yana tsaka taje gashin nasa, ya hango Nana ta cikin mudubin, tana kallonsa. Ya ɗaukko comb ɗin ya nufo Nana, da sauri ta sunkuyar da kai.

Ya zo gabanta ya miƙa mata comb ɗin, ta tsaya tana kallon sa, ya ƙara miƙa mata. Ta saka hannu ta karɓa, ya gyara zamansa ya juya mata baya, ya ɗan yo baya da kansa. Ta yi shiru tana kallon kan nasa. "Ki taɓa, na ga ki na so" wata irin kunya ta kama Nana, haushin kanta ya kama ta, yadda ta bari har ya iya gane gashin kansa yana burge ta.

Ta dafa kafaɗarsa, da nufin ta tashi, kawai ta gansu a wani ƙasaitaccen ɗaki na alfarma, maimakon ɗakin su. Ta kalli jikinta, ta ganta sanye da wasu kayan na daban. Hannunta dai riƙe da comb ɗin. Duk yadda ta yi ƙoƙarin yin magana ta kasa. Ta saka hannu, ta fara taje lallausan gashin nasa, ta gama ta tufke masa kamar yadda yake yi. Ya miƙe tsaye ya juyo ya kalle ta, ya kama hannunta ya sumbata ya ce "Allah ya yi miki albarka"

Kamar wadda aka jonawa shocking ta zabura, ta ga ɗakin ba kowa, ga dai kwanukan da ya ci abinci, ya wanke ya ajiye mata. Ta tashi tsam ta je ta leƙa ta taga, ta hango shi a zaune a kan kujera, a gefen gate ya kara radio a kunnensa, gefe ga butar shayin sa. Ta dafa bango ta jingina a hankali, hawaye ya fara ziraro mata, a hankali ta ce "Ka yi nasara ƙaisar, ka burkita mini ƙwaƙwalwata fiye da baya. Na fara hauka, ba na iya tantance zahiri, tunani da mafarki. Ka cutar da ni" ta ƙarasa maganar tana sheshsheƙar kuka.

Muryar Ƙaisar ta ji tana amsa kuwwa a ɗakin. "Ba ni ba ne, ko zan saka ki hauka ba yanzu ba, da sauran lokaci, ina ƙara baki lokaci ne. Abin da na yi ta yi miki gargaɗi a kai ne"

"Allah yana tare da ni, ba zan bayar da magani ba Ƙaisar, ba na buƙata ka ƙyale ni na yi rayuwata dan Allah" ta ƙarasa maganar wani kukan yana kufce mata. Ayshacool "Nana" ta ji muryarsa a bazata. Da sauri ya sauke rawaninsa a kiɗime ya ce "Meya faru?" Kasa magana ta yi, ta ci gaba da kuka. Cikin damuwa yake kallonta, ya rasa abin da zai ce mata, ga shi da gaske kukan take mai tsuma zuciya.

"Na yi wani abu ne?" Ya furta yana kallonta. Ta girgiza masa kai alamar a'a.

Ya sake cewa "Ba lafiya ne?"

Ta sake girgiza masa kai. Ya saka hannu ya dafa kafaɗarta, a take wani irin sanyi ya shige ta, har ƙafafuwanta.

Babu tsammani ya haɗa ta da ƙirjinsa, duk da tana jin yadda zuciyarta take harabawa da sauri, amma ta yi shiru ba ta motsa ba, ba ta tunanin a rayuwarta, akwai wanda ya taɓa ba ta wannan damar. Maimakon ta daina kukan, sai ta sake fashewa da sabon kuka, sababbi da tsofaffin damuwoyinta duk suka taso mata. A hankali ta ji ya zura hannunsa a cikin nata ya riƙe.

Duk da a ƙasan zuciyarta, tana jin mafarki ne, amma ta ji daɗin samun damar zubar da hawayen nan da ta samu.

*

Tamkar zai tashi sama, haka yake bala'i yana kumfar baki.

"Ai dama na sani, wallahi haryanzu tana son tsohon mijinta, kuma tana magana da shi ta waya, ina da cikakkiyar shaida a kan hakan"

Wata babbar mace da fuskarta ke ɗauke da damuwa ta ce "A'a Iliyasu, ba na tunanin Mai jidda za ta yi haka"

"Au goya mata baya za ayi ma kenan? Ina da cikakkiyar shaida, ba na son mutuncinta ya zube ne kawai saboda 'ya'yana"

"A'a ba goya mata baya zan yi ba, amma ka yi haƙuri dan Allah"

"A'a a yi magana a buɗe, idan tsohon mijinta take so, to ta koma gurinsa ba dole"

Maijidda na gefe tana ta sharɓar kuka, tamkar ranta zai fita, ya gama bambamin masifarsa ya fice daga gidan.

Matar ta dawo da hankalinta kan Maijidda ta ce "Wai maijidda abin da Iliyasu ya faɗa gaskiya ne? Ana idar da sallar asuba fa ya kira ni a waya ya ce lallai na zo na ji abin da ki ka aikata"

Cikin kuka ta ce "Wallahi Adda ba a yi haka ba, roƙonsa kawai na yi ya bani dama na je na ga halin da yarinyata take ciki, an ce mini an yi aurenta, amma ban sani ba, ko ba komai Nana da Imaran su ma yarana ne, na rasa irin wannan abu ƙiri-ƙiri an raba ni da yarana"

Adda ta ce "To ke mai jidda ban da abinki, ba a gurin babansu suke ba? Ko a kan yara biyu sai ki salwantar da aurenki, da yaran nan shida saboda guda biyu ne?"

Ta ɗago jajayen idanunta ta ce "Adda su ma biyun ni na haife su, ba su da kama ta, su na buƙata ta, shekara goma sha ina tattalin wannan auren, duk da ƙiyayyar da yake nuna wa 'ya'yana amma wallahi zuciyata na Kano tare da Nana da ɗan uwanta"

"Aikuwa sai ki yi haƙuri, Allah ya ƙaddara abin da zai riga ya faru. Yanzu ki bari zan shirya da kaina, ki kawo abin da ki ke da shi da ki ka ajiye saboda aurenta, mu haɗa a kai mata ke dai ki yi haƙuri da zuwa, zuwa lokacin da zai saukko. Bari na kira shi a waya"

Adda ta kira Iliyasu, sai da ta ta tsinke ta sake kira, sannan ya ɗaga.

"Dan Allah malam Iliya ka yi haƙuri, ita ma ta ce a baka haƙuri, ba za ta sake ba"

"A'a ai na daɗe ina fuskantar take-takenta ne, kuma wallahi ba za ta sake riƙe waya ba, kuma wallahi ta sake ta taka zuwa ƙafarta zuwa garin Kano, ta fake da yaranta ta haɗu da tsohon mijinta, a bakin aurenta tun da ni na ɗan iska ba ne"

"Ai ba ma za ta sake ba, ta tuba ta daina ka yi haƙuri ka yafe mata" ya gama bala'insa, Maijidda na jin sa ba abin da take yi sai kuka.

"Maijidda ki yi haƙuri, idan ki ka kashe auren nan saboda yara biyu ya za ki yi da na gaban ki? Duk abu gidan nan akwai ci akwai sha. Idan ki ka koma gidan Gwaggo ma, ita ba cikakkiyar lafiya ba, ga babu guri gara ki yi haƙuri. Ita yanzu tun da ta yi aure ta samu ta zo inda ki ke" Adda ta gama maganganunta, Maijidda ba ta sake tofawa ba.

Readers Also Read