Kenza eBookz

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 2

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 2

Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 2: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 2. Cikin kuka ta ce "Ai dama ban ce kai zaka tsare ni ba, idan ma gatse ka ke…

3,311 words

Cikin kuka ta ce "Ai dama ban ce kai zaka tsare ni ba, idan ma gatse ka ke yi mini ba zan taɓa neman taimakon ka ba, amma na meye za ka din ga razana ni a gaban mutane, sai na fita hayyacina na aikata abin da zai saka a ce ba hayyacina nake ba?"

"Abin da ki ka gani haka yake ko a zahiri, ba yi na yi dan na tsorata ki ba kawai" ya yi maganar yana fitowa daga cikin ruwan, da wani baƙin mayafi a jikinsa, yana jan ƙasa tare da ɗigar da ruwa.

"Biyo ni" ya yi maganr yana yin gaba. Bin bayansa ta yi, suka ƙarasa gaban wani dutse, ba ta san ya aka yi ba, ta gan su a cikin libraryn sa.

Ya ce "Wannan mutumin da ki ka gani yana kuka da hawayen jini, yana daf da faɗawa mawuyacin hali, a saboda abin da abokinsa zai yi masa. Abu ɗaya yake damunsa da yasa za a iya galaba a kansa, ba shi da riƙo da ibada sosai, sai baƙar aƙida da ra'ayin riƙau. Kuma ni ba na zama a guri mai ƙazanta, ko gurin da ake ta'amalli da jini, mussaman na bil'dama, ta yaya zan zo inda ki ke, alhalin inda ki ke zuwa ana ta'amalli da jinin bil'adama? Jininku ya fi jinin kowace halitta ƙarni mara daɗi, amma ya fi kowanne zaƙi da daɗi idan aka sha. Shi yasa masu aiki da jininsin aljnun da suke ta'amalli da jini, da an ba su jinin bil'adama, suke aiki cikin gaggawa, domin babu jinin da ya kai na su zaƙi da daɗi in ji masu sha".

Mudubin da yake gurin ya nuna mata, ya ce "Kalli" cikin tsoro da razani, ta kalli mudubin.

Alhaji Zailani ta gani tsirara, ana kwarara masa jini a jikinsa, yana buɗe baki tare da ziro harshensa waje, jikinsa yana karkarwa.

Wata irin razana ta yi ta buɗe idonta, karaf ya sauka a cikin na Baba.

"Uban me ya dawo da ke gida yanzu? Ko suma kin yi musu wani abun sun kore ki?"

Ta girgiza kai alamar a'a.

"To me ya dawo da ke gida yanzu?"

"Kaina ne yake ciwo"

"Ki sha magani ki koma, idan ma korar ki suka yi, ki san abin yi, dan wallahi ban san ina zan nemo kuɗin nan na biya ba"

Ya gama faɗansa, ya bar ƙofar ɗakin, tana nan zaune ta ji sallamar Inna a tsakar gida.

Ta amsa daga ɗaki, tare da bata damar ta shiga.

"Nana ya na ganki a haka? Ba ki da lafiya ne?"

"A'a me ki ka gani?"

"Idonki ya yi jawur sosai fa"

Nana ta yi murmushi ta ce "Lafiya ƙalau bacci na yi "

Inna ta ce "Bacci kuma? Ina gurin aikin?"

"Daga can nake" ta bata amsa

"Wallahi da can gidan aikin zan je, kawai na fara zuwa nan".

Nana ta karanto damuwa a fuskar Inna, ta ce "Meyafaru?"

"Muhsin fa ya rasu yau ne uku"

Wata irin zabura Nana ta yi, ta ja da baya tana bin ƙwayar idon Inna da kallo, domin ta gazagata abin da yake fitowa daga bakin Innan. "Ba Muhsin Fatuhu ba amma ko?" Nana ta yi maganar cikin tashin hankali, da ya gaza ɓoyuwa a kan fuskarta. Ayshacool Cikin damuwa Inna ta ce "Shi mana, idan ba kya komai ki tashi mu je ki yi musu gaisuwa, an gano gidansu mun je ma daga makaranta".

Tamkar an tsinkewa Nana laka, haka jikinta ya mutu laƙwas, fatan ta a ce bacci take yi kawai mafarki ne. Can kuma sai mafarkin da ta yi da Muhsin ɗin ya dawo mata fes. Zabura ta yi tai waje, Inna ta bi bayanta, tana kiran sunan ta. Baba da yake tsakar gida ya ce "Lafiya ina za ki haka?"

Inna ta ce "Ɗaya daga cikin ɗalibanta ne ya rasu za mu je gaisuwa" gaban Baba ya faɗi cikin tsoro, ya fara fargabar kar dai ta tabbata iskokan Nana ke kashe wanda take mu'amala da su?.

"To Allah ya jiƙan sa"

Inna ce ta amsa ta bi bayan Nana.

Inna ta tare musu abin hawa, suka hau suka tafi. Sam Nana ba ta gane abubuwan da Inna take faɗa, fatanta kawai ya zamana mafarki ne ba gaskiya ba. Saboda akwai kyakkyawar shaƙuwa a tsakaninta da Muhsin, saboda lokacin da aka kawo shi ma, bai kai a ɗauke shi ba, saboda ƙanƙantarsa, har goya shi Nana take yi, Allah ya sa mata ƙaunar yaron a zuciyarta.

Sosai ake zaman makoki a gidan Alhaji Fatuhu, ɗan sa bai taɓa mutuwa ba, sai a kan Muhsin, shi ne ƙarami amma ya shiga ransa. Rumfuna aka kafa a cikin gidan, inda yake karbar gaisuwa, cikin gidan kuma mata ne suke karɓa gaisuwa. Gida ne katafaren gaske, ga girma ya sha kayan alatu.

Alhaji Fatuhu yana tsaye yana gaisawa da wasu, ya ga wucewar Nana da Inna. Jikinsa ne ya yi sanyi, ganin yanayin tashin hankalin da yake kwance a kan fuskar Nana.

Inna har falon ta raka Nana, don yi wa babar Muhsin gaisuwa.

A gigice Nana ta shiga falon, kamar mai neman wani abu, ta tsaya tana rarraba ido ba tare da ta cewa kowa komai ba.

Inna ta taɓa ta ta ce "Ga mahaifiyarsa ki yi mata gaisuwa"

Nana ta kalli matashiyar matar da ba ta wuce shekara ashirin da huɗu ba, idanunta jawur.

Nana ta ƙarasa gabanta ta risuna ta ce "Baiwar Allah wai dan Allah Muhsin ya rasu?"

Alhaji Fatuhu ne ya yi sallama a falon, suka amsa Nana ta waiwaya tana kallonsa ya ce "Nana kin samu labarin mutuwar ɗan ki ko?" Sai mahaifiyar Muhsin ta zabura ta ce "Ke ce Nanan dama? Muhsin har ya rasu kafin ya daina magana sunan ki yake kira, yana cewa a kai shi gurinki" sai a lokacin Nana ta ji kuka ya ƙwace mata, Inna take ba su labarin Nana ta je makaranta ganin Muhsin lokacin ba shi da lafiya ba ya zuwa makaranta.

Cikin kuka maman ta ce "Na gode sosai da sosai, ƙaunar da ki ka nuna masa ce ta sanya, duk wanda ya san shi, zai san sunan ki a bakinsa"

A wannan karon ta yarda da zancen mutane, ta fara lura da duk wanda ya shiga ranta take son shi, sai ya rasa rayuwar sa.

"Wai ke ba za ki daina kukan nan ba, kamar a kan ki aka fara rashin ɗa? Wannan ai rashin tawakalli ne?"

Nana ta waiwaya ta kalli mai maganar suka yi ido huɗu. Matar ta ce "Ahh wannan ba Nana ba ce, yayar Jamila"

Alhaji Fatuhu ya ce "Kin santa ne? Antyn su Muhsin ce a Young talented academy"

Hajiya sa'a ta ce "Na santa, ba ki gane ni ba ne?" Nana ta girgiza mata kai alamar a'a.

"Ba da ke mu ka haɗu kwanaki a gidan maman khairat ba?" Nana ta sake ɗaga ido ta kalle ta, a take ta so ta nemi nutsuwarta ta rasa. Wani abu mai muhimmancin gaske take son tunawa, amma abu ya gagara sai ma wani irin sarawa da kanta ya yi.

Hajiya Sa'a ta nemi ta rasa nutsuwar ta, ganin fuskar Nana tana canzawa kamar ba ta mutum ba, tana wani irin ja tamkar an shafa mata jar kala. Neman guri ta yi ta zauna da sauri, jin jiri zai ɗebe ta.

A hankali Nana ta ɗauke kanta, daga kallon hajiya Sa'a, ta yi musu gaisuwa, ta tashi jiki a sanyaye ta ce tafiya za ta yi.

Mahaifiyar Muhsin ta ce "Bari mu je ki yi wa kakarsa gaisuwa dan ita ma ta sanki a bakinsa. Haka Nana ta din ga yi musu gaisuwa, tana jin tamkar su ma suna zargin ita ta kashe musu ɗa, mussaman da aka ce yana ta kiran sunanta.

Ta rako Nana har harabar gidan, tana ci gaba da yi mata godiya. Alhaji Fatuhu ya ƙaraso ya ce "To Nana Allah ya ƙara mana haƙurin rashin Muhsin"

Ta jinjina kai amma ta kasa magana. Ya kalli maman Muhsin ya ce "Yanzu Alhaji Zailani ya kira ni, yake bani haƙuri bai shigo ba yau, ba shi da lafiya ne wai" Ayshacool "Ai ɗazu Hajiya Amina ta zo da safe tare da mai aikinta sun kuma yi mana gaisuwa ai ba komai sun yi ƙoƙari mun gode sosai"

Gaban Nana ya yi mummunar faɗuwa, ba dai Alhaji Zailanin dai da ta sani ba, tuno abin da ta gani a falonsa ɗazu ta yi. Sai dai ta rasa me ma za ta ce, wataƙila ma ƙaisar ne kawai yake wasa da hankalinta.

Haka suka kama hanyar komawa gida.

Nana na komawa gida la'asar, kasancewar ba ta salla, sai ta shiga ta yi wanka ta kintsa jikinta. Wani abu mai ɗaci ya tsaye mata a wuyanta, har ya fara ƙoƙarin hana ta numfashi. Ba ta ko iya gani saboda azabar jiri da ciwon kai, ta kwanta ta yi shiru ta rufe idanunta, ta din ga tuna mutanen duk da suka rasa rayukansu da yanzu ita ma take kyautata zaton saboda ita ne. Ta fashe da kuka, tana "Wannan wace irin rayuwa ce, gaba ɗaya na kasa tantance ni mece ce ma gaba ɗaya. Allah ya tsinewa tsohuwar da ta gada mini wannan masifar wallahi ba zan yafe ba".

* Malam Gambo mai allon ƙasa ne zaune a kan buzunsa, ya nutsu yana sauraren Alhaji Zailani.

"Ni dai abin nan ya firgita ni malam, ni ban taɓa abu makamancin haka ba, yanayin kamar ɗimuwa ko gushewar hankali"

Malam Gambo ya numfasa ya ce "Me yasa ka yi gaggawa? Wutar ciki ce da kai Alhajin Allah, ai a sannu za ka bi ta, ba kowacce yarinya za ka yi wa irin wannan tayin kai tsaye ba, mussaman idan ba ta saba ba, duk lalacewar zamani akwai na Allah"

"Wallahi kuwa yarinyar ta bani mamaki, akwai taurin kai na tsiya"

"Yanzu ba wannan ba, matsalar da nake gaya maka akwai, ita na duƙufa bincike a kai, kwanaki ba akwai wani wuridi da na yi maka ba, na kira wani aljani ya yi mana aiki ba ya ƙi?"

Da sauri Alhaji Zailani ya ce "Eh an yi haka"

"To wannan aljanin shi ne a kanta, goɗiyarsa ce"

Alhaji Zailani ya waro ido ya ce "Haba, ni fa na ce, wallahi da ta buge ni ta wuce, kamar wani ingarman doki ne ya hankaɗe ni"

"To ya zame maka dole ka kula ka yi taka tsantsan, ka bi a sannu burinka ya cika idan ka ci gaba da far mata zai iya ajalinka!"

"Ajalina fa ka ce?"

"Ƙwarai da gaske, hatsabibin matashin saurayin aljani ne, ba ya neman rigima da kowa amma idan aka taɓa shi faɗa da shi ba ya ƙarewa har abada"

Alhaji Zailani ya jinjina kai cike da gamsuwa, dan kuwa a rayuwarsa babu babban abin da yake tsoro sama da mutuwa, ko zancenta ba ya so gani yake, yana da cikakkiyar lafiya da ba za ta tunkaro shi a daidai wannan lokacin ba.

Sai da Nana ta shafe kwanaki uku, babu lafiya ga wani irin zazzafan zazzaɓi da take fama. A kwana na huɗu ta lallaɓa ta koma gidan Alhaji Zailani. Hajiya Amina na ganinta cikin damuwa ta ce "Nana kwana biyu lafiya kuwa?"

"Wallahi Hajiya ba ni da lafiya ne"

"Allah sarki, ga shi ke ba waya balle a ji halin da ki ke ciki, Haidar duk ya damu yana ta tambayar ki."

Tana rufe bakinta sai ga Haidar ya fito da gudu, ya ɗane jikin Nana. Sai ta tuno da Muhsin, take wata fargaba ta shige ta, kar shi ma abin da ya samu Muhsin ya same shi, saboda sun shaƙu sosai. Jiki a sanyaye ta rungume Haidar.

"Nana anya kin warware kuwa, bari na kira Doctor Sharif ya zo ya duba ki, duk kin yi zuru-zuru". Ita dai Nana ba ta ce komai ba, har mamakin kirkin Hajiya Amina take yi.

Har gida doctor Sharif ya zo, ya duba Nana, ya bata magunguna da allurai, ya saka mata ruwa a gidan. Ganin Nana a kwance duk sai Haidar ya damu, ya koma kusa da ita ya kwanta shima. Nana cike da ƙaunar yaron take kallonsa, tana tuna Haidar, ta din ga addu'a Allah ya kare shi ya kiyaye shi, kar abin da ya samu Muhsin shi ma ya same shi.

Kafin yamma Nana ta ɗan ji ƙwarin jikinta, har ta din ga ɗaga Haidar tana yi masa wasa, saboda yadda duk ya damu, da ganinta a kwance. Hajiya Amina ta fito falon ta miƙowa Nana waya, Nana ta saka hannu ta karɓa tana kallonta.

Ta ce "Tun da shi sirikin nawa, bai kawo miki waya ba, ni ga shi na baki, ki lallaɓa da ita, bai kamata a ce budurwa kamar ki ba ta da waya ba. Ga dubu uku, idan kin fita ki tsaya ki sai layi a yi miki rijista ki saka a ciki, in sha Allah nan da kwana uku za a biya duk ma'aikatan gidan nan albashin su. Ko wani abun ne ya faru kya din ga bugo waya ki sanar" Ayshacool Nana ta juya wayar, da gani ba wani amfani aka yi da ita ba, sai ƙyalli take yi, har da charger.

"Yanzu Hajiya wannan tawa ce?"

"Eh mana Nana, ko ba ta yi miki ba?"

Nana ta girgiza kai ta yi murmushi ta ce "Wallahi ban taɓa zaton zan riƙe waya mai kyau da tsada har haka ba. Allah ya faranta miki, ya kula miki da zuriyar ki, ya dauwwamar muku da farin ciki na gode sosai da sosai"

Hajiya Amina ta yi murmushi ta ce "Nima na gode sosai, ina jin daɗin yadda ki ke kula da Haidar da zuciya ɗaya, na ga kina da yawan ibada da azumi, dan Allah ki yi mini Addu'a idan ina da rabo Allah ya bani haihuwa" Turus Nana ta yi tana kallonta, a wannan shekarun nata me za ta yi da wata haihuwa?.

Ta yi murmushi ta ce "Kin yi mamaki ko? Ai ban taɓa haihuwa ba, ki roƙa mini, idan kuma ba ni da rabo, Allah ya ƙara mini dangana"

Nana a ƙasan zuciyarta murna ta taya Hajiya Amina, na rashin haɗa zuriya da wannan majanunin mijin nata mara addini. Amma a zahiri ta ce "Ki yi haƙuri Hajiya, kin san komai rabo ne, kuma Allah ya fi mu sanin abin da ya dace da mu. Ko kin bar duniya in dai ɗan Adam zai rama halacci ire-irena da yaran da ki ka riƙe, za su yi miki addu'a. Kar ki manta ba ke kaɗai ba ce uwar mumunai Allah ya ƙara mata yarda, ba ta samu haihuwa ba amma uwa ce ga dukkanin muminai, a rashin samun haihuwar nan, ke ba ki san me Allah ya tanadar miki ba, wanda bai bawa waɗanda suka haihu ba" kai tsaye kalaman Nana suka din ga shiga zuciyar Hajiya Amina, da sai da hawaye ya cika mata ido. Ta ji daɗin kalaman Nana, na ƙwarin gwiwa, ta yi mamakin yadda Nana ta iya tsara maganganu cikin hikima.

"Na gode sosai Nana, kin ƙara sawa na ji nutsuwa, Allah ya ba ki zuriya ta gari. Ka da Allah ya jarrabe ki da ƙaddarar rashin haihuwa. Duk ta tawakallinka, akwai gaɓar da mutane mussaman 'yan uwanka mata sun saka ka ji tamkar ba ka da amfani."

"Amin na gode sosai Hajiya. Amma ta ki jarrabawar ki ka sani, da wata jarrabawar gara rashin haihuwa sau dubun dubu" haka su ka din ga hira da Hajiya Amina, har lokacin tafiyar ta ya yi.

Tana shirin tafiya, Shukura ta dawo, Haidar yana kallonta, amma bai damu ya je gurinta ba, ya rirriƙe Nana yana cewa zai bi ta ta tafi da shi ba. Da ƙyar ta lallaɓa shi, ta fita.

Habu na ganinta ya taso zai buɗe mata gate, ya ce "Malama har kin taso?"

Nana ta ce "Eh malam Habu, shekaranjiya na zo zan fita, duk ba kwa nan"

"Eh wallahi mai gidan nan ne ya aike mu"

Ta ce "Allah sarki, yauwwa dan Allah ina wannan ɗan uwan naku?"

Habu ya ce "Wanne daga ciki?"

"Wannan ɗin nan"

"Ya sunan shi?"

Nana ta girgiza kai ta ce "Ban san sunansa ba, ɗaya ɗan uwan naku dai Sule ya ce mini ba shi da cikakkiyar lafiya, kurman nan" Habu ya kwashe da dariya ya ce "Kayya ba kurma ba ne ba yana magana"

Ta ce"To ai shi kullum baya magana, fuska a rufe kamar amarya. Shi ya buɗe mini ƙofar ranar na fita"

"Allah sarki, yana gane komai, kawai da larura ce a ƙwaƙwalwarsa, ba kuma wai hauka yake yi tuburan ba, wasu lokutan ma sai ya shafe sati bai ce uffan ba, yana kwance ma ba lafiya"

Cikin tausayawa Nana ta ce "Allah ya sauwwaƙe, na tafi sai da safe"

"To sauka lafiya, Allah ya tsare" ta amsa da Amin ta tafi.

Ɓoye wayarta ta yi, saboda ta san tsaf Baba zai ƙwace wayar nan, mussaman yanzu da yake neman kuɗi ido rufe.

Bayan Nana ta koma gida, Jamila take tambayarta ashe sun haɗu da Hajiya Sa'a a gidan rasuwa, amma ta ce ba ta santa ba.

Nana ta ce "Ina cikin jimami da alhinin mutuwar yaron ne, shiyasa na kasa gane ta"

Jamila ta ce "Allah sarki, ashe yaron ma sunanki ya yi ta kira kafin ya rasu"

Nana ta kalli Jamila daga sama zuwa ƙasa ta ce "Wannan karon ma ni na kashe shi ko?" Ta yi magana tana tsare Jamila da ido.

Jamila ta ce "A'a ni ban ce ba, kawai labari fa take bayarwa"

Nana ta gyaɗa kai cikin gargaɗi ta ce "Jamila ina son hawainiyar matar nan ta kiyayi rama ta, idan ta ci gaba da ƙoƙarin cin iyaka ta, za ta faɗo cikin wutar da za ta ƙona ta da ita da amfanin gonarta, wannan saƙona ne a gare ta." Saroro Jamila ta yi cikin tsoro, jin yadda Nana take magana kamar an shaƙe ta. Ayshacool Kamar kuma wadda ta razana a cikin bacci, jikin Nana ya ɗan yi girgiza sannan ta ce "Jamila yau wainar fulawa nake sha'awa, zan sai fulawa ki sai mana manja, mu soya mana" da yake sun saba yin haka. Jamila kawai ta jinjina mata cikin tsoro.

Da daddare Jamila ta samu Nana tana shirin kwanciya bacci ta ce "Nana wai Hajiya Sa'an wani abun ta yi miki ne, ki ke cewa na yi mata kashedi?"

Cikin rashin fahimta Nana ta ce "Wace ce Hajiya Sa'a?"

"Wadda ku ka haɗu a gidan rasuwa"

Nana ta ce "A'a wani abin ta ce na yi mata?"

"A'a to ai ke ce ki ke cewa na ce ta kiyaye ki, kuma babbar mace kamar wannan shi yasa na tambaye ki"

Nana ta waro ido ta ce "Ni babu abin da ta yi mini, ni fa ko magana ban yi mata ba, me ta yi mini zan ce ta kiyaye ni?" Sai a lokacin Jamila ta fahimci kamar Nana ba ta san ta yi maganar ba sai ta ƙyale ta.

Ranar da aka bawa Nana albashi, kamar ta taka rawa, ganin ta mallaki dubu ashirin ta ta, ta kanta. Ga dubu ashirin da Alhaji Zailani ya ce a bata, baban Haidar kuma ya ce a bata dubu goma, sai da ta tashi da dubu hamsin. Iya salarynta ta yi murna da shi, wanda aka ce Alhaji Zailani ya bata kuwa, ji ta yi tana ƙyanƙyamin su.

Da murna ta nufo gida, tana tunanin wace bajintar yakamata ta yi a gida, yadda kowa zai amfana. Amma tana zuwa Baba ya turke ta da bala'i "Wai Asma'u ba za ki ƙuƙuta a samu komai a hannunki ba? Ƙanin uban yaron nan ya kira ni a waya, yana idan ba zan dawo da kuɗin ba, hukuma ce za ta raba mu, ba ki da asara ko a jikin ki ko?"

Nana ta saka hannu a aljihun rigarta, kasancewar kuɗin dubu goma goma ne, ta ciro uku ta bawa Baba ta ce "Baba wannan ne kawai a hannuna, nima yau aka biya ni albashi".

Readers Also Read