Kenza eBookz

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 3

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 3

Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 3: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 3. "Yauwwa ko ke fa, ba zan taɓa su ba kiran su zan yi su zo su karɓi abin su,…

3,374 words

"Yauwwa ko ke fa, ba zan taɓa su ba kiran su zan yi su zo su karɓi abin su, duk da koma me aka yi mini ke ce sila, da kin haƙura kin kwantar da hankalinki shikenan, amma mugun halinki ya sanya ki ke ta yi wa yaron nan wulaƙanci, yanzu kalli halin da ki ka jefa mu" Nana ta daina mamakin ƙarfin hali da son kai irin na Baba, sai dai ta yi shiru ya gama surutansa ta tashi ta tafi.

Abu kamar wasa, ƙaramar magana ta juye zuwa ga babba, domin kuwa Saleh cewa ya yi ba zai karɓi dubu talatin ba, dan ko kwatan abin da ya kashe ba a ba shi ba. Dan haka ya kai Baba police station.

Haka aka turo jami'an tsaro, suka tisa ƙeyar Baba zuwa gurin 'yan sanda. Sai Gaddafi aka nemo, ya bi bayan su.

Gaddafi ya kalli Saleh, ya ce "Yanzu kai Saleh saboda rashin ta ido, ka rasa wanda za ka kawo gurin 'yan sanda sai mahaifina, saboda rashin kara, ko dan zaman amanar da muka yi a ikko, ga yayanka na auren ƙanwata."

Saleh ya ce "Ka ga malam, a batun kuɗi babu wata kara, yarinyar nan ba ƙaunata take yi ba, har tana neman hallaka ni, ban aure ta ba zan bar muku kuɗina ne?"

Duk yadda a ka yi da Saleh a yi sulhu, amma ya ƙi yarda, sai da aka yi yarjejeniya, cewar nan da kwanaki uku za su kawo kuɗinsa gaba ɗaya a ba shi".

Ranar yau na ɗaya daga cikin ranakun da Nana, ba za ta iya mantawa da su ba, domin bayan dawowarta gida, Baba ya din ga yi mata bala'i tamkar zai tsine mata, har da cewar ya yi dana sanin haihuwar su da ɗan uwanta, ya yi dana sanin haɗuwa da mahaifiyar su har ya aureta ta haife su".

Gaddafi ya ce "Dan Allah Baba ka yi haƙuri ka yi shiru haka mana, sai ɗaga murya ka ke yi duk maƙwabta su na jin ka, kuma ka na ta cewa ta nemo kuɗi a biya, ka san dai ba wata sana'a take yi ba, idan kuma ba hanyar banza ka ke son ta shiga ba"

Cikin takaici Baba ya ce "Ka bar ni Gaddafi, ban taɓa haifar ɗan da yake neman ya yi ajalina ba kamar Nana, da me zan ji ne? Ba ta tausayina ko kaɗan duk wata hanya da zan bi na aurar da ita, ta nutsu nima na nutsu ta ƙi, a dalilinta a ka kai ni station a ke nema a rufe ni. Lokacin da aka haife ki babu farin cikin da ban yi ba, na so ki, amma kina neman ki kashe ni. To wallahi idan kuɗin nan ba su samu ba a ka rufe ni, sai kin bar gidan nan, kuma kwana ki bakwai na baki ki fito da wani mijin, ko ki koma gurin uwarki ki bar mini gida"

Ayshercool 08081012143 Ayshacool *AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA 08162859027*

*INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK WANI DATTIN MARA SANYI MAI HANA HAIHUWA SA WARIN GABA RASHIN NI IMA JIN ZAFI YAYIN MU AMALAR AURATAYYA FITAR FARIN RUWA MAI WARI KAIKAYIN GABA TUSAR GABA KURAJEN GABA TUSAR GABA BUDEWAR GABA CIWON JIKI RASHIN GAMSUWA* *Maganin sanyi 5k*

*Maganin sanyi* *5k*

*Maganin ciwon Qoda 10k*

*Maganin HepatitisB ASHA NA TSAWON WATA DAYA MUNBADA ANWARKE DA YARDAR ALLAH 40k*

*MAGANIN MATA KALOLI DABAN DABAN INGANTATTU MASU LAFIYA DA KARA KUZARI AKWAI NA MATA AKWAI NA MAZA UWARGIDA DA AMARE KU GARZAYO WURIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA*

*INGANTACCEN MAGANIN GYARAN NONO MAI TADA KOMADAR NONO DA DUK WATA TAMOWA TA NONO ZAI CIKO DA TUWON NONO YA TADA KOMATSEWARSU BANCE ZASU TASHI BA ZADAI SU CIKO SUYI KYAU* *Maganin gyaran Nono 8k*

*MAGANIN RAGE TUMBI KODA YAKAI GIRMAN CIKIN YAN BIYU INSHA ALLAH KI GWADA MAGANIN AUNTY ZEE DA YARDAR ALLAH ZAKI GODE* *Maganin Rage Tumbi 7k*

*MAGANIN BASUR KODA YAKAI GA YIN TSIRO INSHA ALLAH AGWADA ZA ADACE* *Maganin Basur 5k*

*MAGANIN CIWON SUGAR CIKIN IKON ALLAH MUNBADA ANRABU DASHI* *Maganin ciwon Sugar 10k*

*08162859027* *09070027627*

*Location*KATSINA STATE*

*ACCOUNT NUMBER*

*8162859027* *ZAINAB SHU AIBU* *OPAY*

*OR* *3968303018* *FCMB* *ZAINAB SHU AIBU*

*DAN ALLAH IN KINSAN BAKI SHIRYA BA KARKI YI MAGANA DAN ALLAH KIBARI KI SHIRYA AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA TAKUCE SAI KUNZO*

CHAPTER 23

Cikin maɗaukakin sauti Nana take kuka "Baba ka kashe ni ka huta, idan ma ba ka kashe ni ba, ni zan kashe kaina wai ya ake so na yi ne?" Gane nufin Nana da Gaddafi ya yi, yadda take harin rijiyar gidan da take buɗe, cikin tsananin zafin nama ya rigata isa gaban rijiyar, ya rufe ta, tana ƙarsowa ta yi karo da Gaddafi ta faɗi ƙasa.

Ya kalli Baba ya ce "Yakamata ka din ga haƙuri, ka din ga tausasa lafuzanka, ka san ba ta da cikakkiyar lafiya idan ta kashe kanta, kai fa abin zai dama fiye da kowa. Kuma maganar kuɗin nan, ka bar komai a hannuna ko ba duka ba za a samo wasu, a ba shi ka daina cewa ta fita ta nemo kuɗi a biya. Ka daina biye shawarar da ake baka ta banza, mai baka shawarar ba za ta bari ka yi wa yaranta haka ba"

Ya durƙusa ya ɗaga Nana, kawai ya ji tausayinta ya kama shi. Matsaloli sun yi wa rayuwar ta yawa. Duk da uban nauyin da ta yi, tamkar ta haɗiyi dutse, haka ya ɗaga ta ya kai ta ɗakin su, ya kwantar da ita.

Har ya yinƙura zai tashi, Nana ta danƙo rigarsa, ya kalle ta, idanunta a rufe, sai ruwan hawaye da yake zuba ta gefen idonta.

"Ka ƙarawa ja wa tsohon nan kunne, idan ba haka ba nan gaba kan sa nan zan cilla a rijiya, ya iya bakinsa"

Gaddafi ya ce "Wane tsohon? Baban ka ke nufi?"

Ta tashi zaune, ba tare da ta buɗe idonta ba ta riƙe hannayensa. A take ya ji kamar an jona masa shocking, jikinsa tamkar za a fizge naman jikinsa, ga shi ya kasa motsi, ya kuma kasa magana.

Ta yi murmushi ta ce "Ina fatan yanzu ka gane mai baka saƙon? Ina ƙyale ku ne saboda ku ne abu ma fi soyuwa ga uwar gijiyata, amma aka ci gaba da matsa mata zan yi gagarumar ɓarna."

A hankali ta saki Gaddafi ta silale a gurin ta koma ta kwanta. Tamkar korarrare Gaddafi ya fita cikin tashin hankali, babu wanda ya tsaya yi wa magana ya fice daga gidan. Tun da Gaddafi yake bai taɓa shiga bala'i irin wannan ba. Har a lokacin da ya fita, da ƙyar yake iya sarrafa jikinsa tamkar zai fita hayyacinsa.

Washegari da safe tamkar babu abin da ya faru, Nana ta shirya ta gaida Baba za ta fita amma ya yi mata banza, jikinta babu ƙwari ta tafi gidan Alhaji Zailani. Inda Allah ya taimake ta, tun da wannan abin ya faru, bai ƙara yinƙurin far mata ba.

A hankali take bubbuga gate ɗin, duk da ba ta da tabbacin ma, ana iya jin bugun nata. A yadda take jin duniyar ta yi mata zafi, ji take tamkar ta nemi guri ta kwanta a nan ƙofar gidan. Ayshacool Aka buɗe gate ɗin, tana ɗaga kai suka yi ido huɗu. Dumm! Gabanta ya yi mummunar faɗuwa, babu shiri ta sunkuyar da kanta, ita ba ta shiga ba, ita kuma ba ta koma ba. Kawai ya mayar da ƙofar zai rufe, babu shiri ta tura ta shiga, ta kalle shi tana son ta yi magana, amma ya yi mata wani irin kwarjini da babu wani ɗan Adam da ya taɓa yi mata. Ƙoƙarin gane kamaninsa take yi, amma babu dama rawaninsa ya rufe ko ina na fuskarsa sai idanunsa kawai.

Ta kama hanya ta nufi cikin gidan, sai da ta je tsakiyar harabar gidan, sai ga wasu irin murguza-murguzan karnuka da ba 'yan Nigeria ba, tun da ta zo gidan, ba ta taɓa ganin su ba sai dai ta jiyo haushin su. Sai da daddare ake sakin su, da safe kuma a mayar da su keji. Da guda ɗaya ne karen aka ƙaro biyu. Yau kuma Sule bai samu ya mayar da su da wuri ba har ta zo.

A gigice ta kurma wani irin gigitaccen ihu, ta watsar da takalmanta ta zura da gudu ta yo baya, aikuwa karnukan suka rufa mata baya su na wani irin haushi da zubar da yawu mai ban tsoro. Yana tsaye yana kallonsu, kafin ta ƙaraso gurin da yake har ta fara fita daga hayyacinta. Cukuikuye shi ta yi tana ihu, ta daina ganin komai, sai su biyu a cikin sahara, sai kuma jin sautin haushin karnukan.

Ƙaisar ne ya bayyana, ya yi wata irin girgiza, ya zama wani irin narkeken kare shi ma, haushi ɗaya ya yi sai da gurin ya yi amsa kuwwa a take karnukan suka gudu, kamar barewar da ta ji kukan zaki.

Ya girgiza jikinsa ya koma yadda yake, ya miƙa wa Buzun hannu ya ce "Ko da wasa, idan ka sake yinƙurin razana ta, ko wani abu na cutarwa a gare ta, zan shafe tarihinka a duniya".

Nana ta buɗe idanunta da kyar, ta kalli yadda buzun nan, ya rikiɗe ya koma tsohon nan mai kama da ƙaisar. Sai dai ko motsi ta kasa.

Wata irin dariya tsohon ya din ga ɓaɓɓakawa, gurin ya din ga amsa kuwwa da hargowa. "Kai ɗan samari, ka sake nazarin kalaman da ka faɗa, bayan tsawon shekaru mun sake haɗuwa, mun kuma haɗu a gaɓar da ta dace Ƙaisar" ya yi maganar yana ci gaba da dariya.

A hankali ya ɗago Nana daga jikinsa da ta riga ta suma, ya kalli harabar gidan duk wannan kururwar da ta yi, babu wanda ya fito.

Ya sanya yatsunsa biyu, manuniya da na kusa da shi ya daki goshin Nana sau uku.

A hankali ta motsa ta ɗaga kanta, a falon cikin gidan ta ganta. Hajiya Amina ta ce "Ohh sannu Nana, haka ki ke tsoron kare? Laifin masu gadi ne da ba su mayar da su sun rufe ba, sannu ba ki ji ciwo ba ko?"

Nana ta jinjina kai hawaye na zubowa daga idanunta. Alhaji Zailani ya fito falo, sai baza ƙamshi yake cikin dakkakiyar shadda. Ya tsaya a falon ya kalli inda Nana take ya ce "Lafiya kuma take kuka?"

"Wallahi karnuka aka bari ba a kulle ba, suka biyo ta shi ne har da kakunta, yanzu suka shigo tare da Yusuf"

Ya girgiza kai ya ce "Laifin masu gadi ne ai, bari na fita sai na dawo"

Nana ta ƙura masa ido, tana son tuna wani abu a kansa, amma ta kasa, ta ci gaba da kallonsa har ya fice.

Da ƙyar ta iya jan ƙafafunta, ta tafi ɗakin Haidar. Ta shiga banɗaki domin wanke fuskarta, ta tsaya ta zuba wa fuskarta ido a jikin mudubi. Ta yi shiru tana tuna tun daga tashinta daga bacci yau da safe, zuwa yadda ta zo gidan nan, daga lokacin da karnukan nan suka biyo ta, tunanin ta ya hargitse gaba ɗaya, ta kasa bambance mene ne ya faru a zahiri, menene ya faru ba a zahiri ba, kuma Hajiya Amina ta ce mata, tare suka shigo da Yusuf to ta yaya? Ɓangaren kanta ɗaya ya sara, da sai da ta dafe kan nata. "Wai ko ni ma dai ba mutum ba ce ba? Ko kuma dai ƙaisar ya fara nasarar raba ni da hankalina ne?" Ta furta a hankali cikin tsoro da sheshsheƙar kuka.

Jin ana bubbuga ƙofar banɗakin, ya sanya ta sauri ta wanke fuskarta ta fito. Haidar ta gani a tsaye yana mutsutsuka idanunsa. Ta kama shi ta wanke masa baki, ta yi masa wanka.

* Alhaji Zailani ne a zaune a cikin motarsa, gefensa kuma doctor Sharif ne a ciki a zaune.

"Sharif"

"Na'am Alhaji" ya yi maganar cikin girmamawa.

"A wannan karon ma, taimakon da ka saba nake so ka yi mini"

Doctor Sharif ya ce "Babu abin da zaka nema, na kasa yi maka shi, ka faɗi ko mene ne"

"Yaushe ne EDD ɗin Shukura?" Ayshacool Mama kuwa tun da Baba ya zo mata da maganar nan, ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta rasa abun da yake yi mata daɗi. Wani abu mai masifar zafi ya tsaya mata tun daga ƙirjinta zuwa bakinta. Tana ganin ya za ayi a ce, ga su Jamila a zaune, Nana ta samu hamshaƙin mai kuɗi haka. Ana yin sallar magariba Baba ya fita masallaci, ita ma ta yafa mayafinta ta fice.

*

Jamila ce a zaune a gaban Hajiya Sa'a, fuskar ta ɗauke da matsanancin tsoro take kallonta. Ta dafa kafaɗar Jamila ta ce "Kin tabatta ta sha maganin da aka ba ta a kunun ayar?"

"Ta ce mini ta sha, amma ba a gabana ta sha ba"

"Shikenan kar ki damu, ki kwantar da hankalinki. Za mu ci gaba da ƙoƙari har zuwa lokacin da zamu samu abin da muke so. Abin da nake so da ke shi ne ki zamo mai riƙe mana sirri, za ki samu kuɗi Jamila, irin wanda ba ki taɓa zaton riƙe su, ba za ki yi rayuwar ƙunci da talauci irin na gidanku ba. Nana ita kawai muke buƙata idan ba haka ba, ba zaki zama abin da nake hangen ki zama ba" ta yi maganar cikin bawa Jamila ƙwarin gwiwa.

Mama ce zaune a cikin wata rumfa, tare da wani mutum, ta tattara masa hankalinta gaba ɗaya.

"Ai na gaya miki Rabi, muddin ba ki yi da gaske ba, wallahi ki na ji kina gani, sai dai ke da yaranki ku yi mata biyayya. Tasirin taurarinta ba za su bari na yaranki su haska ba."

Cikin damuwa ta ce "Ai na ga alama, 'yar shegiya kwatsam mutum ya fito wai aurenta zai yi, a zuwa ɗaya ba ka ga uban kuɗin da ya bawa ubanta ba, bai gaya mini nawa ba ne ba, amma wallahi na san da yawa. Kalli aikin raino take yi, amma albashin dubu talatin aka bata, ta bawa ubanta. Wallahi ko buɗe ido ba na ƙaunar na yi na ganta. Ni dai dan Allah ka wargaza maganar nan, kar a yi auren nan. Duk da na ji tana cewa uban ba ta so"

Ya yi murmushi ya ce "Ta kwana gidan sauƙi, yau zan kwana aikin, da ni da almajiraina, za a yi farraƙu mai zafi. Ki zube kuɗi kawai abin da yake hannunki a fara"

Haka ta buɗe jakarta, ta ciro kuɗi ta ajiye masa.

**** Tinkis-tinkis yake tafiya, kamar wani bujimin sa, ya nufi motar da zai hau ya fita, sai dai yana ƙarasawa Nana ta miƙe tsaye. Sai da ya ɗan tsorata da ganinta.

Ya ce "Lafiya dai ko?"

Ta miƙe tsaye ta ce "Wani dalilin ne ya sanya ka je ka samu mahaifina, ka ce masa zaka aure ni?"

Yayi dariya tare da shafa tumbinsa ya ce "Dalilin da yasa ki ka ƙi amincewa da buƙata ta, ya sanya na biyo ta in da dolen ki ki yarda. Amma na yi mamakin yadda ƙwaƙwalwar ki take aiki da har ki ka yi saurin gano ni ne. Sai daga baya na gane ba iya taurarinki nake buƙata ba. Ina buƙatar aljanin da yake tare da ke ma. Kuma wannan ƙwaƙwalwar ta ki ma ina buƙatar ta"

Cike da ƙwarin gwiwa Nana ta ce "Ni na yi maka kala da wadda za ta auri fasiƙi ne? Mazinaci baya auren kowa face 'yar uwassa mazinaciya, ni ba irin ka ba ce ba, kuma Ubangiji mai adalci ne, ba zai yi mini wannan jarrabawar ba"

Ya sake yin dariya ya ce "Akwai abin da ba a kuskurewa ƙaddara. Nima zinar da nake yi ta neman duniya ce, kafin na mutu zan tuba. Kuma tun da baban ki uban kwaɗayi ne da son abin duniya, zan ta ba shi abin da yake so, domin buƙata ta biya. Tun da ke ba ki da wayo, ba ki san inda duniyar ta sanya a gaba ba." Ya buɗe motarsa ya shiga ya zauna, Nana ta bi shi da kallo cikin ɗacin rai. Ya sauke gilashin motar ya kalle ta ya ce "Ki kwantar da hankalinki, na ga kina da abubuwan da zan iya mora da yawa a jikinki, dan haka ko na aure ki zan iya zama da ke na ɗan lokaci amaryata" ya fara jan motarsa ya baro parking space ɗin.

Ƙaisar ta gani ya bayyana, ya sha gaban motar, yana kallon motar, babu tsammani sai ga wannan tsohon da take gani, mai kama da shi, ya keto ƙasa ya fito ya yi jifa da ƙaisar gefe.

Gabanta ne ya faɗi, sai da ta dafe ƙirjinta ta ja da baya, ta ɗaga kanta ta ga har Alhaji Zailani ya bar harabar gidan, sai dai idanunta suka sauka a cikin na Buzun nan da ya ƙure ta da ido ko ƙiftawa ba ya yi. Kamar wadda ya yi wa dabaibayi ta kasa motsi.

"Antyn Haidar, yau ma karen ne, na ganki a nan a tsaye" kamar wadda ta tashi daga bacci, ta kalli Yusuf ta ƙaƙalo murmushi ta ce "A'a ba karen bane, yanzu zan shiga ciki" Ayshacool *AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA 08162859027*

*INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK WANI DATTIN MARA SANYI MAI HANA HAIHUWA SA WARIN GABA RASHIN NI IMA JIN ZAFI YAYIN MU AMALAR AURATAYYA FITAR FARIN RUWA MAI WARI KAIKAYIN GABA TUSAR GABA KURAJEN GABA TUSAR GABA BUDEWAR GABA CIWON JIKI RASHIN GAMSUWA* *Maganin sanyi 5k*

*Maganin sanyi* *5k*

*Maganin ciwon Qoda 10k*

*Maganin HepatitisB ASHA NA TSAWON WATA DAYA MUNBADA ANWARKE DA YARDAR ALLAH 40k*

*MAGANIN MATA KALOLI DABAN DABAN INGANTATTU MASU LAFIYA DA KARA KUZARI AKWAI NA MATA AKWAI NA MAZA UWARGIDA DA AMARE KU GARZAYO WURIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA*

*INGANTACCEN MAGANIN GYARAN NONO MAI TADA KOMADAR NONO DA DUK WATA TAMOWA TA NONO ZAI CIKO DA TUWON NONO YA TADA KOMATSEWARSU BANCE ZASU TASHI BA ZADAI SU CIKO SUYI KYAU* *Maganin gyaran Nono 8k*

*MAGANIN RAGE TUMBI KODA YAKAI GIRMAN CIKIN YAN BIYU INSHA ALLAH KI GWADA MAGANIN AUNTY ZEE DA YARDAR ALLAH ZAKI GODE* *Maganin Rage Tumbi 7k*

*MAGANIN BASUR KODA YAKAI GA YIN TSIRO INSHA ALLAH AGWADA ZA ADACE* *Maganin Basur 5k*

*MAGANIN CIWON SUGAR CIKIN IKON ALLAH MUNBADA ANRABU DASHI* *Maganin ciwon Sugar 10k*

*08162859027* *09070027627*

*Location*KATSINA STATE*

*ACCOUNT NUMBER*

*8162859027* *ZAINAB SHU AIBU* *OPAY*

*OR* *3968303018* *FCMB* *ZAINAB SHU AIBU*

*DAN ALLAH IN KINSAN BAKI SHIRYA BA KARKI YI MAGANA DAN ALLAH KIBARI KI SHIRYA AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA TAKUCE SAI KUNZO*

Page 24

"Baba dan zatin Allah, ka duba lamarin nan, wallahi ba na son mutumin nan, ba shi da kirki dan Allah Baba ka yi mini rai"

"Nana duk rashin kirkinsa, bai kai talauci rashin mutunci ba, idan ki ka ga ba a yi auren nan ba, to sai dai idan wani mijin ki ka kawo, ke ko wani ki ka kawo ɗin wallahi ga dai mai rufin asiri ba zan bawa wani ke ba, gara ma ki yi haƙuri, ki tattara komatsan ki"

"Ya Allah, Ya Allah Astagfirullah" ta faɗa duk a jejjere."

"Mahaifinki ba zai taɓa canza hali ba, sam ta kansa kawai yake yi"

Nana ta ɗaga kai a karo na biyu, da ta sake ganinta a gurin ƙaisar ta ce "Koma mene ne kai ne sila, kana ɗaya daga cikin dalilan da ya sanya Baba son rabuwa da ni ko ta halin ƙaƙa."

Ƙaisar ya ce "Kar ki ga laifina, tun da na baki zaɓi tuntuni, ki ka tsaya wahalar da kan ki" ya yi maganar yana rubutu da hannunsa ɗaya mara ciwon.

Ya ɗora da cewa "Matar babanku ta je gurin Malamin da ya zane ki rannan, a kan a wargaza maganar auren nan, dama ya kan yi mata aiki ire-iren waɗannan, idan Allah ya taimake ki aikin ya ci, sai ki ga an fasa, kalli abin da aka yi" mudubin da ya saba nuna mata, ya nuna mata.

An raba wata 'yar tsana gida biyu, an rubuta sunan Nana a jikin ɓari ɗaya, ɓari ɗaya kuma Alhaji Zailani, ana ta wani surkulle.

Ya ɗora da cewa "Abin da ba su sani ba su duka su ne, shi wannan mutumin ya kai matakin ƙololuwa a ƙungiyar asiri, to wani asiri ne kuma zai kama shi?"

Nana cikin kuka ta ce "Wannan malamin shi ne ya zane ni rannan"

Readers Also Read