Kenza eBookz

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 4

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 4

Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 4: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 4. Ƙaisar ya kwashe da dariya, ya ci gaba da rubutun sa.

3,352 words

Ƙaisar ya kwashe da dariya, ya ci gaba da rubutun sa.

Cikin kuka ta ce "Kuma duk saboda kai, Allah ne gatana, kowa nice ba ya so kawai" ta yi magana tana ƙarewa malam Ɗayyabu kallo a jikin mudubin. Sai kuma ta daina ganin malam Ɗayyabu, sai Jamila tare da Hajiya Sa'a da kuma maman khairat.

Da sauri ta kalli Ƙaisar ta ce "Wannan matar ba ita ka ce mini ta bayar da jinin Muhsin a ƙungiyar asiri ba? Amma me yasa da na tashi na manta, na ganta na kasa tunawa?"

"Ashe kin san ainihin abin da ya faru, ki ke cewa na kashe wanda ki ke ƙauna?" Ta yi shiru tana satar kallonsa.

"Shi ma wannan yaron na yanzu, idan ba ki yi wasa ba, ana daf da shafe tarihinsa a duniya, akwai yiwuwar 'yan ƙungiya su nemi a ba su jininsa"

Cikin matsanancin tsoro Nana ta kalli Ƙaisar ta ce "A'a kar mu yi haka da kai Ƙaisar, dan Allah yaro ne fa bai san komai ba."

Ya ce "Ni babu abin da zan yi da shi, kawai dai na gaya miki ne. Hatta ɗan da babarsa za ta haifa a nan gaba kaɗan, an gama shirya yadda za a yi da shi" A razane Nana ta tashi tsaye, amma sai ta ganta a tsakar ɗakinsu. Gigicewa ta yi ta nufo tsakar gida, ta ga tsakar gidan baƙi ƙirin, dare ya tsala. Ayshacool Sai kuma ta fara ƙoƙarin tuna abin da ya razanata, har ta fito tsakar gida, amma ta kasa tuna komai. Ta koma ta zauna jikinta yana tsuma, ta rasa ma wace addu'a za ta yi. Zuwa yanzu idan da sabo ta saba da matsanancin bugun zuciya saboda yawan razana da take yi.

Ta haɗa kanta da gwiwarta, ta rasa ma wani tunanin za ta yi, kasancewar bacci ɓarawo ne, ya sanya ya yi nasarar yin awon gaba da ita.

Sai dai ta din ga ganin Haidar, yana ta kuka tana ƙoƙarin rarrashin sa, amma ya ƙi yin shiru sai tsala ihu take yi. A wani ɓangaren kuma na mafarkin, ta ga Shukura a dokar daji, tana ta uban gudu da tsohon cikin nan, jikinta babu suturar kirki, duk jikinta raunika, kanta babu ko ɗan kwali, ga hannunta riƙe da Haidar sai gudu take tana kururuwa. Bayanta wani mutum ne ya rufe fuskarsa da baƙin ƙyalle yake bin ta, hannunsa riƙe da wuƙa ga jikinsa sai ɗigar da jini yake yi. Kukan Hidar sai amsa kuwwa yake yi, yana kiran sunan Nana.

A wannan karon ma a razane ta tashi, da "Innalillahi wa innalillahi raji'un" daidai lokacin aka tayar da sallar asuba a masallaci.

Gudu-gudu sauri-sauri, ta fita ta yi alwala, ta gabatar da raka'atanul fajar, sanan ta yi sallar asuba. Ta zauna tana tasbihi ta din ga tunanin 'yan kwanakin nan ba ta iya karanta Alqur'ani. Azkar ɗin ma sai ta shafe kwanaki ba ta yi ba, ganin ko ta yi babu abin da yake canzawa. Sai kuma ta tafi tunani, wataran a islamiyya da ta farka ta ga malam Auwal a kanta, yana ta raira karatun Alqur'ani, hakan ya tabattar mata da ƙaisar ya ziyarceta. Bayan ya sanya ta tashi, ta yi alwala ta dawo ta zauna, ya dube ta ya ce "Nana idan kin je gida kina azkar kuwa? Kuma kina karanta Alqur'ani?" Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"To me yasa?"

Cikin rauni da karaya ta ce "Ko na yi Allah ba ya kare ni, na fi shan wahala ma idan na yi" da sauri ya tari numfashinta ya ce "A'uzbillahi, waye ya gaya miki Allah ba ya kare ki? Da ba ya kare ki da Allah kaɗai ya san abin da zai faru da ke. Addu'oin da ki ke yi, da larurar da ki ke fama da ita, ba ya nufin karatun Alqur'ani da azkar da ki ke yi ba sa yi miki amfani, jarrabawa ce, daga Allah. Ke kina ganin Aljani na bibiyar marasa ji? Sun fi bibiyar nutsatsu masu addini, hakan na nufin jarrabawa ce, mai imani ba a barin shi haka babu jarrabawa. Kuma burinsu kenan ki daina ibada, su sake samu su miƙe ƙafa a jikinki, su ci gaba da azabtar da ke. Musulma ce ke, ki zama mai kyautatawa Allah zato".

Ko da ta zo nan a tunaninta, sai ta ce "Astagfirullah, wa a tubu ilaihi"

Ƙarfe tara da rabi na safe, Baba ya fito tsakar gida yana neman Nana. Mama ta ce "Ba fa ta nan"

"Ban gane ba ta nan ba, ina ta tafi? Ba na kafa mata dokar kar ta sake fita ba, ana daf da ɗaura mata aure?" "To ka isa da ita ne? Ai ba ka isa ka gaya mata ta ji ba, ka yi kaɗan"

Ƙwafa ya yi ya ce "Za ta dawo ta same ni, zan ci ubanta a cikin gidan nan wallahi" Bayan ya gama bambaminsa ya fita, Mama ta koma ɗakinta ta ɗauki wayarta ta kira Malam ɗayyabu.

Sai da ta kusa tsinkewa ya ɗaga, "Malam yaya a ke ciki? An gama aikin ne?"

"Eh a kan aikin muka kwana jiya"

"To shikkenan, na gode sosai da sosai, baban nata fa ka yi aikin a kansa?".

Ya ce "Kar ki damu, ba wanda ban yi ba fa"

Ta ajiye wayar, tana kuma tunanin me yakamata ta yi.

Kafin azahar ɗan aiken Alhaji Zailani ya zo, ya kawo uban kayan abinci kamar za a buɗe ƙaramin shagon sayar da kayan abinci. Bakin Baba ya ƙi rufuwa, sai shiga yake yana fita yana washe baki, yana ƙiyasata irin abin da zai yi wa Nana muddin ta bijirewa auren Alhaji Zailani. Yaron nasa ya sanar da Baba cewar, tafiyar gaggawa ta kama Alhaji Zailani, washegari zai dawo, amma ko baya nan bai dawo a goben ba, za a ɗaura auren nan ranar Juma'a, kuma ba ya buƙatar taron jama'a, waliyyai kawai sun isa. Baba yana tsuma ya tabattarwa da yaron Alhaji Zailani, mai suna Sani cewa ya tabattarwa da Alhaji Zailani ba za a samu wata matsala ba.

Nana kuwa gaba ɗaya ji ta yi jikinta ya ƙara sanyi, tun da garin Allah ya waye, komai ba ya yi mata daɗi, tamkar ta mutu ta huta. Duk mutanen gidan sun koma baccin safe, ta shirya ta fice daga gidan. Ayshacool A hanya gari ya ƙarasa wayewa Nana, ta je ta din ga bubbuga gate ɗin, aka zare sakata aka buɗe. Sai dai maimakon ya ba ta hanya, sai ya zura mata idanunsa yana kallonta. Hankaɗa ƙofar ta yi ta shiga a fusace, ta tsani wannan ɗan iskan kallon da yake yi mata, shi kuma kullun fuska a rufe, ba a ganin fuskarsa sai dai ya yi ta kallon mutane. Burki ta ja ta tsaya, tana kallon yadda ƙosassun karnukan nan, suke safa da marwa a harabar gidan. Ta waiwayo ta kalle shi, ya kawar da kansa kamar bai gan ta ba, ya mayar da gate ɗin ya rufe ya saka mukulli, ya nufi ɗakinsu na masu gadi. Karnukan suka yi cirko-cirko suna kallon Nana, su na haushi.

"Dan Allah ka raka ni bakin ƙofar shiga" ta yi maganar a marairaice. Bai kulata ba ya cigaba da tafiya. "Dan Allah idan ba za ka raka ni ba ka buɗe mini ƙofa na koma". Ganin da gaske ba zai rakata ba, kuma ba zai buɗe mata ba, ga karnuka su na nufo ta, kawai ta rufa masa baya da gudu. Ya tsaya ya waiwayo ya kalleta. Ta ja ta tsaya cikin tsananin tsoro.

Sule ne ya fito yana miƙa da alama a lokacin ya tashi, ya kalle su ya ce "Nana lafiya na ganki da sassafen nan? Kuma ya na ganku a tsaye haka lafiya dai?"

"Tsoro nake ji, na ce ya raka ni yaƙi, kuma ya kalle ƙofa ya ƙi buɗe mini na koma gida, kuma so suke su biyo ni su cije ni" ta yi maganar idanunta na cika da hawaye saboda tsoro.

Sule ya yi dariya ya ce "yi haƙuri, ni ban san dalilin da ya sanya ku ke yawan samun saɓani da Buzu ba. Jira ni na ɗaure karnukan sai ki wuce"

Ta goge hawayen ta ce "To na gode sosai" Shi kuwa tuni ya shige ɗakin su, ya bar ta da Sule.

Ko da Nana ta shiga cikin gidan, ɗakin Haidar ta nufa kai tsaye, yana kwance yana ta baccinsa. Ajiyar zuciya ta din ga saukewa, ta durƙusa a gabansa ta dafa kansa, tana karanto masa addu'oin da suka sauwwaƙa a bakinta. Tana ɗan tofa masa. Wata irin razana ya yi a baccin, har da ɗan ihunsa, Nana ta rungume shi, ya ƙanƙameta ta cigaba da yi masa addu'a.

Yau Shukura ta na gida, sun yi hutun makaranta. Har mamaki take yi yadda Nana ba ta gajiya da abin da Haidar yake yi mata na hayyata irin ta su ta yara. Duk motsin da ya yi, ta san me yake nufi, zuwan Nana gidan ya yi ƙiba ya zama ƙato saboda yadda yake cin abinci. Ga kuma karatu da take koya masa, har da addu'oi.

Nana ta ce "Shukura" karon farko da ta taɓa kiran sunanta, Shukura ta kalli Nana da mamakin tsaurin idon da ta yi.

"Na san ba zan dauwwama ina kula da Haidar ba, amma dan Allah ina son ko yaya ki ajiye aƙidar boko, ki din ga jansa a jiki, kuma ki tsayawa azkar ɗin sa da kula da yi masa addu'a. Ke kanki ki ƙara ƙaimin addu'a sosai da sosai, ka na da ido ne kawai amma ba na ganin gari ba, abin da Allah ya so kawai shi muke gani"

"To da na ce miki ba na addu'a ne, da za ki buɗe ƙazamin bakin ki, kina kiran sunana haka kai tsaye ni sarki ce?"

Nana ta kalli Shukura ido cikin ido ta ce "Ni ki ke cewa mai ƙazamin baki! To kar ki yi abin da na ce, idan kin ƙi ji ai ba za ki ƙi gani ba"

Babban abin da ya bawa Shukura mamaki, bai wuce yadda ta ji tamkar an saka mukulli an rufe mata baki ba, bayan sun haɗa ido da Nana ba, ta yi gum ta kasa cewa komai.

Gaba ɗaya Nana ta manta da wani sharaɗi da Baba ya kafa mata ma, hatta batun auren Alhaji Zailani ma sai ta daina jin ya dame ta, mummunan mafarkin da ta yi da su Shukura ne kawai yake damunta. Sai kuma wata irin fargaba da ta rasa ko ta mece ce. Domin ragewa kanta damuwa, tare suka yi girkin dare da Jummai. Hajiya Amina ce ta ce "Nana ki zo ki tafi, na ga alamun hadari a garin nan, kuma tun da ba abin da ki ke yi"

"A'a kar ki tafi" Haidar ya yi maganar yana riƙe rigar Nana.

Nana ta kalle shi da murmushi a fuskarta ta ce "Idan na zauna zaka goya ni?"

"Eh zan goya ki, ki yi bacci" ya yi maganar cike da shirirtar su ta yara.

Da ƙyar a ka yi masa wayo, Hajiya Amina ta ɗauke shi, Nana har za ta fita, Jummai ta biyo ta da kular abinci ta ce "Dan Allah Nana ki ajiyewa masu gadi, na san yanzu su na can waje shan wannan shayin nasu na ibada, ba za su dawo ba sai cikin dare. ki ɗan tura ɗakinsu ki ajiye musu, idan ba su san an ajiye ba, karnuka ne suke zubar musu. Ayshacool Jiya da na ajiye musu a waje ba su sani ba, su ka kwance karnuka, aikuwa su na sako su, suka je in da aka ajiye abincin suka kifar, suka hau ci" Nana ta ɗan yi Jimm sannan ta karɓa ta fita.

Kamar yadda Jummai ta faɗa kuwa, Nana tun kafin ta ƙarasa bakin gate ɗin, take jiyo hayaniyar buzayen a ƙofar gida, alamun duk su na waje a ƙarƙashin bishiyar da suke zama da yamma su sha shayi, su yi wasan takobuna. Amma duk da haka sai ta tsaya a ƙofar ɗakin nasu tana sallama, ko za ta ji an amsa, amma ta ji shiru. Sai ta ɗan tura ƙofar ɗakin, wani irin ƙamshin turare ya kawo wa hancinta ziyara. Ta zura flask ɗin abincin, ta yinƙura za ta tashi, kawai ta ji kukan Haidar a cikin ɗakin yana kiran sunanta. "Anty Nana, ki zo) Ba ta yi nazarin komai ba, balle tunanin ta baro Haidar ɗin a cikin gida ba, kawai sai ta ɗimauce ta hankaɗa ƙofar ɗakin ta shiga. Cak ya tsaya ya waiwayo ya kalli inda take tsaye. Daga shi sai dogon wando, hannunsa riƙe da mataji, yana taje dogon gashinsa da ya kwanta a kan kafaɗarsa zuwa dokin wuyansa. Gefensa butar shayi ce, take ta dahuwa a kan wuta, kuma da alama a cikin wutar aka zuba turaren wutar da yake tashi. Cikin matsanancin tashin hankali tsoro da razani, ta yi yinƙurin juyawa ta fita, amma ƙofar ɗakin da tagogi suka kulle, sautin wata irin guguwa ya karaɗe ɗakin. A take ya rikiɗe daga kamaninsa zuwa wannan tsohon mai kama da Ƙaisar, ya bayyana cikin suffa mai matuƙar ban tsoro, ya buɗe ƙaton bakinsa mai kama da bakin tsohuwar rijiya, ya fara fito da wata irin wuta Jawur tana wani irin hayaƙi, lamar gobarar tankar mai. Iya ƙarfinta ta dafe kanta, ta ƙwala ihu ta faɗi a gurin sumammiya. Jin ihunta ya sanya ya sake waiwayawa ya kalle ta, ya ganta a ƙasa ba ta ko motsi. Ya ƙarewa ɗakin kallo domin ya ga abin da ya razanata amma bai gani ba. Ya mayar da hankali ya ƙarasa taje gashinsa, ya tufke abinsa, ya zira rigarsa, ya shafa turare sannan ya kawo rawaninsa ya naɗa. Ya zauna a gaban shayinsa, ya fara tsiyayowa yana kurɓa a hankali tamkar shikaɗai ne a cikin ɗakin babu wata halitta kuma.

Gidansu Nana tun da aka yi sallar magariba, Nasiru ya shigo gida yake tambayar ko Nana ta dawo. Suwaiba ta ce "wai kai Nasiru Nanan nan uwarka ce ne?"

"Ban sani ba, idan ma uwar ta wa ce ina ruwan ki?"

Cikin hasala ta ce "Idan na kama ka wallahi sai na gwara kanka"

"Ba ki da wannan ƙarfin wallahi" ya yi maganar yana fita. Ya zauna a ƙofar gida yana kallon hanya, amma babu Nana babu alamar ta. Tsoro ne ya fara kama shi, kar ya je ko ta sake ɓata aljanun nata sun kai ta wani gurin. Yana zaune ya hango Baba ya nufo gida, hannunsa riƙe da manyan ledoji. Nasiru ya tashi ya karɓo masa kayan suka shiga gida.

Su na shiga Nana ya fara tambayar Mama, amma ta ce ba ta dawo ba. A take hankalin Baba ya tashi, ya fara tunanin ko dai ta gudun ne? Sai a lokacin ya fara binciken ina ne gidan da Nana take aiki, tun da take zuwa bai taɓa bibiyar ina take zuwa aikin ba. Gaddafi baya nan, dan haka ya ɗauki Nasiru, suka fita neman Nana.

Gurin ƙarfe tara na dare, Gaddafi ya dawo gida, ya shigo cikin gida zai wanke kayansa, yana neman Nasiru zai aike shi. Suwaiba ta gaya masa halin da ake ciki. Ya yi saroro ya ce "Yanzu har ƙarafe tara ba a san inda take ba? Kuma babu wanda ya san gidan aikin nata?"

Jamila ta ce "Ni dai ta taɓa kwatanta mini, can wajen quarters ɗin markaz ne, wai gidan Alhaji Zailani"

"Sako hijjabin ki mu je, mu duba"

Mama ta ce "Ku je ina? Babu inda za ta je"

Ya haɗe rai ya kalli Jamila ya ce "Ba magana nake yi miki ba, sai na taka wuyanki tukuna?" Ba Jamila ba ita kanta Mama sai tsuke bakinta ta yi, dan iya ashariyar Gaddafi ta ishe su.

Sam ba su sha wahalar gano gidan ba, kasancewar Alhaji Zailani sanannen mutum, saboda yawan kyautar da yake yi da taimakon al'umma. A tsatstsaye suka tarar da mutane a ƙofar gidan, buzaye sai magana suke yi da yaren su.

Kai tsaye Gaddafi ya kutsa suka shiga cikin gidan, mutane ne a tsaye a ƙofar ɗakin masu gadi, ga matar gidan a tsaye fuskarta ɗauke da damuwa. Ayshacool Gaddafi ya nufe ta, suka gaisa ya ce "Dan Allah ni yayan yarinyar da take yi muku aiki ne, Nana tun da ta fita tun safe bamu ganta ba, shi ne muka zo nan ko ta zo?"

Hajiya Amina ta ce "Alhamdilillah mu na ta tunanin yadda za a yi, tun bayan la'asar muka yi sallama, ta tafi gida. yanzun nan yarona ya shigo yana gaya mini wai masu gadi sun ganta a ɗakinsu a sume, su suna waje, mutum ɗaya suka bari a ɗakin, shi kuma ba shi da lafiyar ƙwaƙwalwa, ya ƙi magana an rasa wanda zai taɓa ta ma. Yanzu nake tunanin ya za a yi a samo wani daga gidansu, dan ni ban san gidansu ba"

Gaddafi ya ce "Ɗakin masu gadi kuma?" Ya juya ya nufi ɗakin.

Nana na sume a tsakar ɗakin, gefe guda shi kuma yana zaune yana kaɗa ƙafafuwan sa, tamkar ba ya jin hayaniyar da ake yi.

Gaddafi ya nufi Nana da sauri, ya ɗago ta, yatsun hannunta da na ƙafarta duk sun ƙandare kamar wadda ta daɗe da mutuwa, ga jikinta sanyi ƙalau.

Ya ɗaga kai ya kalli Buzun nan da duk abin da ake yi, sabgar gabansa kawai yake yi, ya kalli Nana. Duk da ba shiri suke yi da ita ba, amma ya san Nana ba ta cikin jerin yara marasa ji, amma me ya kawo ta ɗakin masu gadi?.

Hajiya Amina ce ta saka Yusuf ya ɗauki su Gaddafi ya tafi kai su gida.

Cikin damuwa Habu yake dubansa ya ce "Buzu, ya aka yi yarinyar nan ta shigo ɗakinmu, me ya same ta? Me yasa kuma ba ka kira wani daga cikinmu ba?" Ɗaga idanunsa ya yi ya kalli Habu, a dole Habu ya ja bakinsa ya tsuke, duk da tarin tambayoyin da suke bakinsa.

Cike da takaici, da matsananciyar tsana da damuwa, Baba yake kallon Nana yake maimaita a ɗakin masu gadi ka gano Nana?"

"Idan an yi magana a ce aljanu ne suka hanata aure, ga haƙiƙanin abin da ya hanata aure nan ai" Mama ta din ga faɗar maganganu. Jamila ta ce "Mama ba lallai abin da ki ke tunani ba ne ba, kin san ba ta da cikakkiyar lafiya"

"Eh ban sani ba sai yanzu da ki ke gaya mini, rashin lafiya ne za a ganta a ɗakin masu gadi da wani?"

"To ai an ce mahaukaci ne, har fa muka taho yana kallon dandazon mutane, bai yi magana ba, kuma bai fito ba" cewar Jamila, dan ta ƙi yarda zuciyarta ta bata wani mugun abin Nana take aikatawa.

Kawai Baba ya tafi ɗaki, Mama ta bishi tana faɗin "Yanzu baban Jamila, baka gudun a zo a ji kunya? Wallahi tun da ta fara haka, ko an yi auren nan ba za ta zauna ba, kunyata ka za ta yi, tun da ta furta maka ba ta son auren nan, take ta wannan iskancin. Maza nawa ta ce ba ta so? ko dai ka san abin yi ko kuma abin da za ta yi a gaba sai ya fi na yanzu muni"

Wata irin tafasa zuciyar Baba ta din ga yi, tafasar da tun da yake bai taɓa jin zuciyarsa ta yi ba, wata irin matsananciyar tsanar Nana ta mamaye zuciyarsa. Kamar mahaukaci haka ya fito fiuu ya yi waje.

Ayshercool 08081012143 Ayshacool *AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA 08162859027*

*INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK WANI DATTIN MARA SANYI MAI HANA HAIHUWA SA WARIN GABA RASHIN NI IMA JIN ZAFI YAYIN MU AMALAR AURATAYYA FITAR FARIN RUWA MAI WARI KAIKAYIN GABA TUSAR GABA KURAJEN GABA TUSAR GABA BUDEWAR GABA CIWON JIKI RASHIN GAMSUWA* *Maganin sanyi 5k*

*Maganin sanyi* *5k*

*Maganin ciwon Qoda 10k*

*Maganin HepatitisB ASHA NA TSAWON WATA DAYA MUNBADA ANWARKE DA YARDAR ALLAH 40k*

*MAGANIN MATA KALOLI DABAN DABAN INGANTATTU MASU LAFIYA DA KARA KUZARI AKWAI NA MATA AKWAI NA MAZA UWARGIDA DA AMARE KU GARZAYO WURIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA*

*INGANTACCEN MAGANIN GYARAN NONO MAI TADA KOMADAR NONO DA DUK WATA TAMOWA TA NONO ZAI CIKO DA TUWON NONO YA TADA KOMATSEWARSU BANCE ZASU TASHI BA ZADAI SU CIKO SUYI KYAU* *Maganin gyaran Nono 8k*

Readers Also Read